Showing 48001 words to 51000 words out of 150281 words

Chapter 17 - MARTABARMU HAUSA NOVELS LUBNA SUFYAN .txt

23 Nov 2025

3978

A hanya ya hadu da Layla da ta saka hijab, sai yaga tayi mishi kyau sosai, fuskarta fayau babu kwalliya yau.

"Hamma ina kwana"

Ta fadi da bacci cike da muryarta, bata ma jira ya amsa ba ta wuce. Zumudi ya hanata bacci daren jiya. Sai wajen karfe uku da rabi na dare, sai taga kamar tana rufe idanuwanta Mami tazo ta tasheta, ta samu tayi sallah. Nasiha tun da Abbu ya amince da tafiyarta Mami takeyi mata, yau dinma tana gama shiryawa taga Mami a ranta tace

"Ni kam naga ta kaina... Wa'azi da asubar nan"

A fili kuwa murmushi tayiwa Mami har hakoranta suka bayyana. Mamin ma murmushin tayi

"Yar nema, yau ni akeyiwa wannan murmushin da bai kai zuci ba ko?"

Dariya Layla tayi sosai, wani lokacin yanayin kular Mami har mamaki yake bata

"Dan Allah ki rufamun asiri Layla, ki kula da kanki, karki ji tsorona, karkiji tsoron me zance, kiji tsoron Allah dan Shi yana ganin ki a inda ni bana ganin ki. Ki kula da kanki, idan duk kina da matsala kinsan kirana kawai zakiyi ko?"

Kai Layla ta daga mata, yanayin muryar Mamin na sanyaya mata jiki

"Allah ya tsare mun ke a duk inda zaki shiga. Allah ya taimake ki ya baki sa'a, Allah ya banj aron rayuwa inji ki a gidan Radio din da kike buri"

Da sauri ta matsa tana fadawa jikin Mami din

"Karyani Layla"

Mami ta fadi muryarta na rawa, kwalla cike da idanuwanta, a kasan kewar Layla akwai tarin shakku da tsoro da ta kasa kawarwa daga zuciyarta. Babu yanda zatayine, Layla da Abbu sun rinjaye ta, sunki fahimtar tsoronta. Shisa ta zabi ta bi Layla da addu'a kamar yanda Abbu ya fadi

"Allah Shi ne yake tsarewa, Shi ya tsare mana su har zuwa wannan lokacin...ba tsoron mu ko dabara ba"

Numfashi ta sauke a fili tana zagaya hannuwanta ta rike Layla a jikinta sosai.

"Ina son ki Mami, da yawa fa"

Dariya kawai tayi, da Layla da Jabir basa gajiya da fada mata suna sonta, ko a gaban waye Jabir zaice yana son ta, musamman idan tayi mishi abinda yaji dadi. Kalaman na sanyaya mata zuciya ko da bata mayar musu ba, abune da bai yawaita a al'adar mu ba. Su kam sun mayar da shi kamar tun tasowar su sun sabajin ana fadin kalaman a tsakanin iyaye da yaran su. Tana son yaran, tana jin su a ranta, kawai batason dabi'ar nasaran da suka daukarwa kan su.

Musamman Jabir ma yanzun da yake ganin sai ta daga kai take hango shi, kuma kai tsaye zasuyi magana batare da sun tauna ba, suna ganin sun kai matsayin da zasu fadi duk abinda yake ransu, ga taurin kai, idan har suka kafe akan abu dai-dai ne to babu wanda ya isa yace musu ba haka bane ba. Halayen turawa shi suka daukarwa rayuwar su, kamar da suka shiga islamiyya haka suka fito batare da islamiyyar ta ratsa su ba. Addu'a ita take bin yaranta dasu har na Ayya ma, Allah ne shaida bata tashi daga wajen sallah bata hadasu duka a addu'o'inta ba.

Haka sukayi sallama da Mamin, bacci take ji idanuwanta har wani yaji-yaji yakeyi. Shisa sanda Bilal yazo daukar kayanta bata samu ta gaishe dashi ba sai yanzun. Abbu ya gaya mata ya basu mota, kuma tasan motar, tana zuwa ta bude bayan motar ta shiga. Ko kadan batayi tunanin Rayyan yana ciki ba harta ja murfin ta zauna. Numfashi ta sauke, Rayyan kuma idanuwan shi a lumshe suke, dan yasan yau zai samu yayi baccin safe tunda motar gida ce bata haya ba. Kawai yaji ana shigowa, hakan yasaka shi bude idanuwan shi, gyara kwanciya yayi yana juya kan shi ya kafa ma Layla ido.

Itama zama ta gyara tana dan juyawa taga an mata quri

"Wayyoo Allah..."

Ta furta da karfi saboda gabanta ya fadi sosai

"Hamma"

Ta furta har lokacin da tsoro a muryarta

"Baki da hankali? Da safe zaki zo kina mun ihu a kunne?"

Ita bata neman tashin hankali, tasan ko tafiya zasuyi zai zauna a gaban mota ne. Shisa ma ta bude bayan motar ta shiga abinta. Baccine a idanuwanta har sun mata nauyi

"Kayi hakuri, dan girman Allah Hamma, wallahi bansan kana nan ba sam sam, ina kwana"

Ta karashe a gajiye, hararta yayi yana jan wani tsaki dai-dai lokacin da Bilal ya shigo motar ya zauna. Juyawa yayi yana kallon su hadi da sauke numfashi

"Me kuke nufi?"

Ya bukata, tunda shi yasan su duka Abbu ya baiwa mota, baice ya zama direban su ba balle su kame a bayan mota gabaki daya

"Wani ya dawo gaba"

Ya fadi yana kallon Rayyan daya kauda kai

"Magana fa nakeyi"

Cikin ido Rayyan ya kalle shi

"Kana shamun kamshi tun da safe"

Ya fadi kamar wani dan karamin yaron da kaiwa dukan tsiya kazo kuma kana yiwa dariya. Layla Bilal ya kalla, ita kuma ta kalli Rayyan din kamar tana neman izinin shine kafin ta koma, shikuma ya rigada ya lumshe idanuwan shi. Numfashi Bilal ya sauke yana runtsa idanuwan shi ya bude su a lokaci daya. Tuqi zaiyi, yana bukatar gabaki daya natsuwar shi, idan ya biye musu zasu birkita mishi lissafi, hakan yasa shi gyara zama, addu'a yayi yana jan motar suka fice daga gidan, sun kama hanyar da zata fitar dasu daga Kano kenan Rayyan ya bude idanuwan shi yana ganin Layla a zaune a kusa da shi

"Mayya ce ke? Dole sai inda nake zaki zauna?"

Wani abu taji ya tokare mata zuciya yanayin yanda Rayyan din yayi magana. Inda ta tashi ta koma gaba ya bude ido kamar yanda yayi tana da tabbas zaice wani abu, dole saiya nemi dalilin da zai sata dana sanin tafiyar nan, bayan tun da satin ya kama take tunanin yanda zata zauna mota daya da shi, nishadin duk da takeyi ya dishe mata shi

"Hamma ka tsaya in dawo gaba"

Layla ta fadi da wani yanayi a muryarta, ta mudubin gaban motar Bilal ya kalle su

"Na dora wayata a kujerar, kuyi zaman ku"

Kafin ta karayin magana ya kunna radio din motar yana kure maganar

"Ka fasa mana kunne Bilal!"

Rayyan ya fadi a masife, ko kallon su Bilal baiyi ba, balle kuma suyi tunanin zai saurare su, ba yanda za'ayi su rabashi da nutsuwar shi yana tuqi. Matsawa Layla tayi tana kara bada tazara tsakaninta da Rayyan din, jingina kanta tayi da jikin motar tana rufe idanuwan ta, duk yanda take jin ranta na mata susa bai hana bacci dauketa ba, Rayyan kallonta yakeyi duk da yasan bacci ya kamata yayi. Yanajin inama ace haka zata zauna, yanda zuciyar shi tayi wani luf a kirjin shi abin ya mishi dadi, amman yasan tashi zatayi, bude idanuwanta zatayi ta hargitsa mishi komai kamar yanda ta saba. Baisan me yasa zata zo da idanuwan mage ba.

Idanuwan shi na kafe a kanta, tana ta baccin ta, a cikin baccin ta juyo kwanciya, ganin da yayi kamar wuyanta zaiyi ciwo yasa shi girgiza kai kawai, babu wani abu da zatayi dai-dai, baccin ma ba zatayi shi dai-dai ba. Yana wannan mitar a zuciyar shi ya mika hannu ta baya dan ya dauko ruwan da Bilal ya ajiye, sai jin kan Layla yayi saman hannun shi, kamar ya mika ne dan ta kwanto, da dayan hannun shi ya tallabe wannan, yana zare shi a hankali, ruwan ya dauka sai ya dan janyo jikin shi yana gyara zama yanda kanta zai kwanta a kafadar shi da kyau.

Robar ruwan ya bude yana sha sosai, ya mayar ya kulle, yanajin Layla ta kara gyara kwanciyar ta a jikin shi, tana kwantowa sosai. Wani irin dokawa zuciyar shi takeyi kamar zata fito daga kirjin shi

"Mayya..."

Ya furta a hankali yana sauke numfashi, sosai ya jingina kan shi da motar yana lumshe idanuwan shi, bugun zuciyar shi yake saurare da yake ji har cikin kunnuwan shi, kafin wata natsuwa daya kwana biyu baiji ba ta saukar mishi, bacci mai sanyi na dauke shi, baisan sanda ya jingina nashi kan dana Layla da yake kafadar shi ba. Kawai abinda ya sani wannan karin baccin nashi babu mugayen mafarkai ko daya. Ta gaban mudubi Bilal ya hango su, yanajin kamar an soka mishi wani abu a kirjin shi, sosai zuciyar shi ke dokawa kamar mai shirin samun matsalar bugun zuciya.

Shi yake bukatar kulawa
Shi yake cikin matsala
Shi yake bukatar Abbu da Mami su fadawa Rayyan daya kula da shi

*

Littafina na siyarwa ne akan naira #300

Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank

Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:07 PM - 111: Nov 26, 2020

12

Kan shi ciwo yake kamar zai rabe gida biyu. Dan bai iya takawa gida ba, sai da ya hau mashin. Da yake ba surutu yake son yi ba, canjin dari da ya baiwa mai mashin dinma da hannu yayi mishi alama daya tafi

"Allah yasa kar in ga kowa, Allah yasa kar kowa ya ganni"

Rayyan ya furta a cikin kan shi. Bayason mutane, baya kuma son 'yan cikin gidan da suke haya fiye da sauran mutane, saboda suna saka shi yanayin magana a lokuttan da ko kadan bayason yi. Gashi yanzun Bilal yace ya dinga yiwa mutane murmushi idan sun mishi magana, baisan ya zai fara ba, motsa labban shi kawai yakeyi wasu lokuttan, tunda bayajin yin fara'a sam-sam. Ya gaisa dasu, baisan kirkin me Bilal yake so ya dinga musu ba

"Ko rashin lafiya ta kamaka ba fata nake ba, su dinne mutanen farko da zasu taimaka maka tunda kuna gida, kasan abubuwan nan, kasan hakkin makota Hamma"

Bilal din ya fada mishi

"Bana son su"

Shine amsar daya baiwa Bilal din

"Su ma na tabbata ba son ka sukeyi ba. Ka dinga murmushi dan Allah in zaka gaisa da mutane, ka dan saki fuska ba kamar an maka dole ba"

Bilal saiya dinga mishi magana kamar baisan dolen akayi mishi yake gaisawa da su ba. Hakkin musulunci kawai yake saukewa. Kamar barawo haka yake sanda wajen shiga gidan, sam baya so wani ya gan shi. Kusan da gudu ya karasa dakin su yana daga labulen ya shiga da sauri

"Subhanallah..."

Bilal da yake zaune ya bude kular abinci ya fadi, dan sosai Rayyan din ya bashi tsoro

"Assalamu alaikum..."

Cewar Rayyan, amsawa Bilal din yayi yana girgiza kai kawai. Taliya ce da miya sai soyayyen dankalin turawa, rabon su da dora tukunya a wuta harya manta, sai dai ko in sunyi marmarin shan shayi zasu dafa, amman Aysha na musu kokari matuka ta fannin abinci tunda tazo makarantar. Bilal baiyi mishi tayin abinci ba, tunda yasan sai yayi wanka, aikam ficewa daga dakin Rayyan yayi. Sai bayan yayo wankan ya dawo ya sake kayane ya zauna yana mayar da numfashi Bilal yace

"Abinci fa?"

Kai Rayyan din ya girgiza mishi

"Babu abinda kaci fa duk yau"

Tunda tare suka fita, kuma yasan babu abinda Rayyan din zaici a waje banda biskit, idan ya samu kalar wanda yakeci din kenan.

"Zanci sai anjima"

Rayyan ya furta yana kwanciya kan katifar da yake zaune a gefe, sai yaji wani dadi a ran shi daya kwanta din, kamar gajiyar daya kwaso ta dan sake shi. Wayar shi da Bilal ya janyone yaga yau din Alhamis, numfashi ya sauke

"Azumi kakeyi ko?"

Ya tambaya

"Me yasa baka gajiya da surutu? Dan Allah ka kyaleni ni"

Rayyan yayi maganar cikin alamar gajiya. Murmushi kawai Bilal din yayi. Bai taba gane azumin alhamis da litinin baya wuce Rayyan ba sai wannan dawowar da sukayi. Sai yake tuna ranakun da Rayyan din zai wuni baici komai ba, duk surutun da zai mishi. Sai sun dawo sallar Magriba tukunna, ko in yayo alwala ya shigo daki an kira, Bilal zai ga ya sha ruwa, ko yaci dabino. To bai taba kawo komai a ran shi ba, tunda Rayyan na da shan ruwa, kuma dabino kamar biskit ne a wajen shi, da wahala ka raba jakar shi da su, ko cikin kayan shi ka duba zaka samu.

Zurfin ciki irin na Rayyan baya gajiya da bashi mamaki, shima ranar alhamis din daya san azumi Rayyan yakeyi, alhamis din kuma daya tabbatar da abinda ya dade da sani, wajen Rayyan din yaje daga nasu bangaren, ya same shi a can karkashin wata bishiya, inda yake shimfida darduma ya zauna idan basu da darasi ba kuma yason komawa gida. Tunda wani lokaci ko baiyi niyya ba idan ya zauna cikin aji sai an sami wani mayen yayi mishi magana. Ko mintina biyar da isa baiyi ba sai ga Layla da tun daga nesa take fadin

"Hamma Rayyann!"

Tana daga mishi hannu da fara'a a fuskarta, yana kallon Rayyan din ya lumshe idanuwan shi yana bude su a kan Layla da take karasowa, doguwar rigace ta atamfa a jikinta, dinkin da ake kira "Fitted gown" a turance, dan tabi jikinta sosai, sai mayafi data dan rataya a wuyanta, ga dauri ta kafa, fuskarta da kwalliya marar nauyi. Da wahala ta wuce ka baka sake kallonta ba, kafin kaga idanuwanta jikinta ne zai fara jan hankalinka, balle kuma idan ka tsayar da hankalinka akan fuskarta da take da wani irin kyau mai sanyi. Dan Bilal sai da yaji jikin shi ya dauki dumi, hakanne yasa shi sauke idanuwan shi daga kanta

"Hamma..."

Ta sake furtawa tana dariya, kwana biyu bata gan shi ba, Bilal din kuwa kullum sai yaje ya dubata yana tambayar ko tana bukatar wani abu. Amman yau kwana biyu bata saka idanuwanta akan Rayyan ba, tunda suka zo makarantar ita take yawon nemo shi duk rana. Jiya da gangan taki zuwa inda yake, ko shi zai nemeta, amman shiru, yau ta kasa hakuri ne, sai da ta zagaya ta gefen da Rayyan yake tukunna ta kalli Bilal

"Hamma ina wuni"

Murmushi yayi mata

"Layla..."

Ya furta yana yin shiru tunda hankalinta gabaki daya ya koma kan Rayyan

"Jiya banganka ba"

Ta fadi tana nazarin fuskar shi, shiru yayi ya kyaleta, baisan ko a satikan nan da tazo Zaria ta fahimci yanda yake matuqar sonta a kusa da shi bane, shisa jiya ta hana mishi ganinta. Kwana yayi yana juyi duniyar ta hade mishi waje daya. Ya gwada kiran wayarta yafi sau ashirin yana fasawa, saboda baisan me zaice mata ba, ba shida wani dalili da zaiyi amfani da shi. Shisa ya hakura. Yau da safe harya nufi hanyar department dinsu sai ya dawo kuma. Shine yanzun take ce mishi jiya bata gan shi ba, kamar bata san inda yake ba idan ta tashi ganin na shi.

"Hamma..."

Ta kira ganin da tayi na cewa yau miskilancin yake ji fiye da ko yaushe, zama tayi gab da shi bata damu da yanda rabin jikinta a kasa yake ba, rike Rayyan ko in hango shi tayi ta rungume shi bai taba damunta ba, hankalinta sam bai taba gaya mata cewar shi din ba muharramin ta bane ba, saboda bata dora abin akan mizanin addini, al'ada kuwa ba damun Layla tayi ba sam. Yanzun ma kanta ta kwantar akan kafadar Rayyan duk da tasan zai iya kwadarta bai hanata ba

"Hamma..."

Ta furta da wani yanayi a muryarta, tayi kewar shi, jiya kawai da bata gan shi ba kewar shi take ji har cikin ranta. Rayyan bai tsammaci zata kwanta mishi a kafada ba duk da ta zauna kusa da shi, wani irin tsalle zuciyar shi tayi kamar zata fito waje saboda wani irin yanayi da yaji ya tsirga mishi, tureta yayi tana shirin dawowa ya matsa da sauri

"Azumi nake Layla"

Yai maganar yana mikewa tsaye gabaki daya, turo labbanta tayi. Shi kuwa Rayyan numfashi yake mayarwa, tun rannan yake tsintar kan shi a wannan yanayin duk idan jikin su ya hadu waje daya. Bilal kallon su yakeyi, zuciyar shi kamar zata fado kasa, idan Rayyan baya kallon Layla da wata fuska data wuce yan uwantaka ya tabbatar ba zai tunanin azumin shi ba dan ta kwanta a jikin shi, tunda tanayi lokutta da dama, bai taba damuwa ba, karshen abinda zaiyi shine ya kamata ya bambare yana fadin

"Mayya ce ke? Duk wajen nan sai kin hadu da jikina? Me yake damun ki?"

Ita yake fadawa kalaman, amman Bilal sukeyi wa zafi, musamman idan yaga Laylan ta sake komawa ta mannewa Rayyan din duk da zafin kalaman shi da suke shimfide a idanuwanta. Ya rasa yanda zaiyi da su, ya kuma rasa ta ina zai fara hanasu wannan rike-riken junan da sukeyi. Yana kallo Layla ta mike itama tana shirin tafiya

"Ina zaki je?"

Rayyan ya bukata yana tsareta da idanuwa

"Ina da lecture, kawai zan ganka ne daman"

Kai ya jinjina, farar riga ce kal a jikin shi da wandon jeans, saiya dora jacket a sama, ko maballan bai balle ba, kawai ya dora ne, taku hudu yayi yana karasawa inda Layla take tsaye, mayafin da yake wuyanta yaja yana daga shi, wani dan ziriri ne, kai kawai Rayyan ya girgiza. Shi baiga amfanin mayafin ba tunda babu abinda ya rufe, bayason yanda maza suke kallonta duk idan ta wuce, wancen satin da yake wando ta saka saita dora kimono a kai, duk da haka sai da yace wa wani dan ajin su

"Ko zaka dauke ta hoto ne?"

Ganin irin kallon da yake bin Laylan da shi bayan ta wuce, murmushi kawai gayen yayi yana barin wajen. Kawai bayaso wasu maza na kallon ta, shisa ya bi bayanta, ya taba ganinta da rigar kuma yaga da madauri baisan me yasa bata saka ba. Hannunta ya kama ranar

"Ina madaurin rigar nan?"

Cike da rashin fahimta tace

"Yana cikin jakata"

Jakar ya karba da kanshi ya bude ya dauko, sannan ya mayar mata da jakar cikin hannunta. Da kan shi ya zagaya madaurin yana soka shi a mazaunin shi ya taho da shi ta gaba ya daure mata yanda ya taba ganin ta daure, saida ya rankwashi kanta daya gama yana sakata fadin

"Wayyoo Hamma"

Ta dafe wajen dan taji zafi sosai, kara kai mata rankwashi yayi ta kauce, idanuwanta cike taf da hawaye ta kama hanya. Dan sam Rayyan baya damuwa da mutanen da suke waje, bama ya damuwa da yanda saboda idanuwanta yanzun tana cikin 'yan matan da aka sani a fadin makarantar cikin kankanin lokaci, ga turancinta da yake burge mutane. A ajinsu ma kowa so yakeyi yai kawance da ita, har maza suna mata magana, kawai dai ba kowa take kulawa ba, a matan ma baifi mutum biyu suke yawo tare ba, saboda ta kula duk sunfi kowa wayewa a cikin ajin, kuma daku nan su da juna babu nisa a hostel, floor daya suke, hawa na ukku. Suna ma zuwa wajenta a dakin su.

Jacket din da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login