Showing 51001 words to 54000 words out of 150281 words

Chapter 18 - MARTABARMU HAUSA NOVELS LUBNA SUFYAN .txt

23 Nov 2025

3967

take jikin shi Rayyan ya cire. Sai da ya rankwasheta

"Me nayi? Me nayi ni?"

Layla take tambayar shi kamar zata fashe da kuka, rigar ya zagaya yana kafa mata idanuwa,  hannunta ta zira a ciki, tana saka dayan ma, ya gyara mata zaman rigar data sauka tana rufe bayanta sosai, maballi daya ya kama yana ballewa, bude baki tayi zatayi magana ya katseta da fadin

"Bakin ki zan fasa in kikayi mun surutu...wuce ki bani waje ni"

Wucewar tayi kuwa, kafin ta juyo tana kallon Bilal da yake zaune yana kallon ikon Allah

"Hamma sai anjima"

Kai ya iya daga mata, yana kishin ganinta a haka, bai taba magana a kai ba, bai taba kokarin hanata shigar da takeyi ba, a zuciyar shine bayason abin, amman Rayyan yayi wani abu a kai, a gaban idanuwan shi ya nuna mishi dalilin da yasa idan yana waje Layla bata ganin kowa sai shi. Baisan me yake ji a ran shi ba, ranar kuma da suka koma gida ya manta yake mishi tayin abinci kai ya girgiza yana amsawa da

"Zanci anjima"

Sai lokacin Bilal din ya tuna

"Kana azumi fa ko?"

Kallon shi Rayyan din yayi

"Ni na fada maka?"

Kai kawai ya girgiza mishi, tun ranar kuma yana kula da shi a ranakun litinin da alhamis, azumi baya wuce shi. Ba dai yason kowa yasani ne tunda badan wani yakeyi ba. Har mamakin mutanen da kamar jira suke ayi musu tayin abinci su sanar cewa suna azumi ne, kamar dan wani suke ibadar. Abinda kakeyi dan Allah, a haka sai ladan yayi tafiya batare da sanin ka ba, idan har ka tsarkake niyyarka, ya kamata ibadunka da ba farilla ba su zamana tsakanin ka da wanda kakeyi domin shi. Abincin Bilal ya karasa cinyewa yana mikewa ya dauko ruwa ya sha hadi dayin hamdala.

*

Hanjin shi har daurewa yakeyi sanda suka dawo daga sallar Magriba. Gashi baisan abinda zaici ba. Ruwan zafi kawai ya dora a tukunya da nufin ya sha shayi, baiga Bilal ya dauki kulolin Aysha ba sanda zai fita, balle yace watakila in zai dawo zai taho musu da abinci. Baiso a dame shi shisa yana shiga yaja labule ta ciki ya tura kofar dakin, ko babu wuta gara yayi fifita da wani ya dago labule neman Bilal ya saka shi yin maganar da bai shirya ba, balle kuma yau yan nepa suna jin mutunci, tunda suka dawo akwai.

Ya juye ruwan zafi a kofi kenan ya saka Lipton yaji ana Kwankwasawa, karamin tsaki yaja yana yin shiru, idan aka gaji za'a tafi, yasan idan Bilal ne zai tura dakin tunda yasan yana ciki. Sake Kwankwasawa akayi, ya kara jan wani tsakin. A fusace ya mike tsaye yana bude kofar dakin, ga mamakin shi Layla ya gani tsaye sai maida numfashi takeyi, ta rungumo wani kwando da kuloli a ciki, kamar zatayi kuka tace

"Hamma ka amsa, hannuna zai karye"

Tsautsayine ya sa ta saka riga da siket, da zata hau mashin har kofar gidan su Rayyan. Keken da ta samu kuma yaki shiga da ita lungun. Har ca tayi ta kara mishi kudi saboda kwandon data dauko amman yakiya. Haka ta tako tana tafiya tana kwashe mishi albarka saboda nishin da take dirkawa, ga kwandon hannu daya sai cirewa yakeyi idan ta rike, sai rungume shi tayi. A jigace ta isa gidan su Rayyan din, hannuwanta duk sunyi sanyi.

"Idan ba zaka amsa ba ka matsa daga kofar"

Tayi maganar cikin tsiwa ganin Rayyan din yana tsaye yana kallonta. Hannun shi daya daga yasata tunanin kwandon zai karba, tallafe mata kai yayi

"Rashin kunya"

Ya furta yana matsawa, ba zai karba ba tunda tayi mishi surutu, karasawa tayi cikin dakin tana ajiyewa a kasa, inda ya tashi ta zauna tana mayar da numfashi

"Banfa samu mashin har gidan nan ba, akan hanya napep ta ajiyeni, da kafata na shigo wajen nan..."

Dakin Rayyan ya bude saboda yanda zuciyar shi take dokawa ba zai rufe daki daga ita sai shi a ciki ba. Ya rasa lokacin da ganinta ya fara hargitsa tunanin shi har haka, kuma bai saka idanuwan shi cikin nata ba, ya koyi kallon har fuskarta batare da idanuwan shi sun shiga cikin nata ba

"In da na tashi nan zaki zauna?"

Ya bukata yana karasawa wajen ya rankwafa, hannunta ya kama ya fisga yana dagata

"Hamma dan Allah, wallahi nagaji, nagaji ni"

Hannun ya sake rikewa sosai

"Da daddare kika biyo hanya?"

Duk da ko fita kayi yanzun din za kaita cin karo da mutane, unguwar tasu dalibai sunfi yawa, dare sai kaga kamar rana ne, amman wani abu a zuciyar shi baison yanda ta fito da magriba haka

"Abinci zan kawo maka, ba kana azumi ba? Dan Allah ka sakeni"

Ta karasa muryarta na rawa, tun azahar yau ta gama darasinta, tana komawa hostel ta fara aikin yi mishi girkin nan saboda ta siyo kifine sai tayi mishi sauce ta dafa wake da shinkafa. Anisa da suke daki daya taso tayata, tunda wani lokaci har girki sukan hada, tace karta damu zatayi in yaso sai Anisa din tayi wanke-wanke. Ba tsafta bace bata da ita, kawai halin jujun Rayyan ta sani, zai iya tambaya idan ita kadai tayi girkin, kuma ba zata iya kallon shi tayi karya ba, yana ganeta, ta sha gwadawa bakinta yanayin jini

"Karya ne"

Yake fadi a duk lokuttan yana kara kai mata wani dukan, sakar mata hannu yayi yana komawa wajen shi ya zauna. Tsaye tayi a wajen tana murza hannunta, shikuma ita yake jira ta zuba mishi, hakan ta kula da shi, bata dauko faranti ba, a dakin ta samu da cokali, sai da ta dauki ruwan leda tana fita wajen dakin ta daurayo su sannan ta dawo

"Kazama, a bakin kofa kika zubar mun da ruwa ko?"

Bata kula shi ba, turo labbanta tayi kawai, sai lokacin ta cire hijabin da yake jikinta tana ajiyewa kan teburin da yake cikin dakin. Bai taba mata maganar kayan da take sakawa ba, amman tasan bayaso, har wata zuciyar na fada mata kishi yake shisa, ba karamin dadi take ji ba kuma. Jacket din shi guda hudune a wajenta yanzun, kuma duk idan ta saka kayan da baisone yake bata. Kamar yana yawo da jacket dinne yanzun ko zai ganta da kayan da bayaso, dan kwanaki a jakar shi ya fito da jacket din. Kuma Rayyan sam bai damu da yawan mutanen da suke waje ba idan ya tashi yi mata abu, kamar ma baya ganin su haka yakeyi.

Abincin ta zuba mishi tana neman waje ta zauna, ya fara ci yaga yanda take bin duk cokalin da zai kai a bakin shi da kallo, kai ya girgiza yana ajiye farantin da ya daga, ya gyara zaman shi sosai

"Me yasa zakiyi girki ba zakici ba?"

Tasan baya tambayeta dan ta bashi amsa bane, shisa tayi shiru, ita batama san tanajin yunwa haka ba sai yanzun da taga yana cin abincin. Cokali ya dauka yana mika mata, zata saka cikin abincin ya dakatar da ita da fadin

"An taba marin ki cikin ido? Ba zaki tashi ki wanko shi ba, kazama kawai"

Mikewa tayi tana daukar sauran ruwan da ta ajiye a gefe ta daurayo cokalin ta dawo. Tare suka cinye abincin tana kara zuba musu wani. Abin bai mata wani iri ba, zuwanta makarantar wannan ne karo na wajen biyar da suke cin abinci tare, na farkon ta kusan raba dare data juya yanayin su tare take hangowa sai wani murmushi ya kwace mata da ba zata ce ga dalilin shi ba. Da yake yana cin abinci da sauri, kafin taci guda daya yaci uku, baisan dalilin da zaisa ka tsaya yanga in zakaci abinci ba. Da kanshi ya dauki kular yana kara mata ya zuba mata miya a kai, abincin da yawa tayi.

Yasan Bilal in dai ba wani abu yaci a wajen Aysha ba, zaici, in baici ba da safe sai su dumama suci abinsu. Layla na karasawa, ruwa kawai ta sha, batama gama ba Rayyan ya mike

"Tashi muje"

Kallon shi tayi da tashin hankali a fuskata

"Ina zamu je? Hamma kabari abinci ya tsarga mun, yanzun fa nagama ci"

Kallon da yayi matane yasata mikewa ta dauki hijabinta tana buga kafarta, duka Rayyan ya kaimata tana kaucewa dan ta gan shi

"Zaki wuce ko saina kwada miki mari?"

Ya bukata, fita tayi daga dakin, shima takalmi ya zira a kafafuwan shi yana fita, baisan ko Bilal ya dauki mukulli ba, shisa ya janyo kofar kawai, gidan su ba'a taba yin sata ba. Kusan ko yaushe Bilal kan yabi halayyar yan gidan. Ko baka rufe daki ba, wani zai janyo maka. Haka sukeyi, in shanya kayi hadari ya hado ma za'a kwashe maka, inka dawo a kawo maka. Suna da kirki matuqa. Shisa bayajin dadin yanda Rayyan yake hade musu girar sama da ta kasa. Shiya fara yin gaba Layla na biye da shi, cikinta take ji har wuya, inda tasan ba zai bari abinci ya natsa mata ba, da bata cika cikinta haka ba.

Ganin har sun kai titi suna tsallakawa yasa ta fadin

"In mukai nisa fa ba zamu sama abin hawa ba"

Dan juyawa Rayyan yayi ya kalleta, hannunta yake shirin kamawa ta kauce

"A kafa? Hamma a kafa? Tafdin... In dai rakani zakayi nagode...amman ni wal..."

Da sauri yace

"Karma ki rantse, zakiyi azumi yarinya... Ki zo mu tafi"

A kafa yake jin tafiya, saboda yana son dan takawa tunda ya cika cikin shi, kuma ko ba haka ba, a ranshi yana jin yin tafiyar tare da ita, ko tana so ko bata so ba matsalar shi bane ba, duk yau ganinta ne yadan nutsar da shi, amman da wani kunci ya wuni, wasu ranakun idan yana azumin yakan ji shi wasai, har Qur'ani yakan dauka ya karanta. Amman wasu ranakun bawai bayaso ya dauka bane, kawai wata irin kasala kan rufe shi duk idan ya yunkura sai ya kasa, haka zai hakura yaita juyi, inya gaji ya kunna sigari ya bukama cikin shi.

"Ni dan Allah kabarni, wallahi nagaji, kuma na saka dogon takalmi"

Layla ta furta tana shirin yin kuka, tun kafin ta fito take murnar zuwa ta gan shi, amman yanzun harya isheta, ta ina zata fara shafawa a kafa ana zaune lafiya. Zagaye suka fara

"Layla..."

Ya furta cike da kashedin da yasata tsayawa waje daya, yasan ko bata zagin shi a ranta, tana tunanin hanyoyin da zata jibge shi idan ta samu dama ne saboda kallon da takeyi mishi, hasken wutar lantarki ya sake ma idanuwanta launi, sai da gabanshi ya fadi daya kalle su, musamman da irin kallon da take watsa mishi, hannunta ya damqa yana janta tana tirjewa kamar karamar yarinya. Bai damu ba, cigaba yayi da janta har suka karasa wani shago, yana rike da hannunta har lokacin ya siya silipas, babu karamar lamba, dan koshi sun mishi yawa, sakinta yayi ya fito dasu daga leda yana ajiye mata

"Ni ce zan saka wannan?"

Ta bukata tana ware mishi ido, kamar duk ranar bataga wani abu daya daga mata hankali irin shi ba, takalman kafafuwan shi dana fata ne yan zire ya cire yana saka silipas din

"Hamma..."

Cikin ido ya kalleta

"Kina gwada hakurina Layla, kin sani ko? Wallahi ba zan sake magana dake ba"

Dogayen takalman kafarta ta cire, ta saka nashin, da kanshi ya kwashe nata ya saka a ledar daya zaro silipas din yana bata, karba tayi ta rike baqar ledar. Hannunta ya sake kamawa suna tafiya. A hankali har suka fara hango makaranta, ba hira sukeyi ba sam balle tace tafiyar tana mata dadi, amman yanayin Rayyan din ya nuna yana cikin nishadi. Musamman yanda ya kalleta yaga tana ta turo baki

"Ki maida hankali, kilan bakin ki ya rigaki zuwa hostel"

Ya furta yana kara sauri, yana kallon yanda take kokarin kamo shi tana kara turo baki, sai da tasa murmushi ya kusan kwace mishi, tunda dai babu yanda zatayi da shi. Har kusan kofar hostel din ya karasa da ita, inda sukaci karo da su Bilal su kuma, Aysha zata rako shi, sunyi tsaye suna hira

"Hamma!"

Ta kwala mishi kira tana murmushi, kallon su Bilal yakeyi da mamaki suna karasowa inda suke, hannun Layla da yake cikin na Rayyan ya kalla, bai amsa Layla ba saboda wani sanannen abu da yaji ya mishi tsaye a makoshi. Kirjin shi harya fara zafin da yakan mishi duk idan ya gansu tare haka

"Ayshan Hamma"

Layla ta fadi tana mata murmushi

"Layla..."

Aisha tace cikin gaisuwa, tana kallon Rayyan

"Ina wuni"

So yakeyi yayi mata murmushi koya ne, amman sam bayajin yi

"Lafiya kalau. Sannu da kokari, mungode"

Ya fadi, yana saka Bilal kallon shi cike da mamaki, Layla ma mamakin takeyi, shi kuma tun rannan yake so yayi mata godiya saboda tana ma Bilal kirki. Tun satin daya wuce yake hada kalaman da zai fada mata in sun hadu, sai yaune ya samu ya fada, baisan me yasa su Bilal suke kallon shi kamar sunga wani abu a fuskar shi

"Bakomai"

Aisha ta furta a kunyace, Layla zatayi magana Rayyan yaja hannunta sunayin gaba, ta cika surutu, baiga abinda zata fada ba kuma, bayan an gaisa. Tsayawa yayi yana sakinta hadi da fadin

"Tam sai da safe"

Kafin ta amsa ya juya, inda su Bilal suke tsaye ya karasa yana dan matsawa gefe hadi da jiran Bilal din, shima hakan yagani yayi sallama da Aisha din yana samun Rayyan. A hanya suka tsaya sunayin sallar isha'i sannan suka nufi gida. Sai da Rayyan ya tsaya wani shago ya siyi sigari.

"Ba zaka daina sha ba ko Hamma?"

Bilal yai tambayar da wani yanayi a muryar shi, sai da Rayyan ya zari kara daya ya kunna yana zuqa ya fitar da hayakin tukunna yace

"Me yasa kake magana a kai?"

Tunda yasan ba dainawa zaiyi ba, shima ya kamata yabar asarar bakin shi. Ba so ya daina bane bayayi, ko yanzun kamar dole ake mishi haka yake zuqar sigarin, kafin su karasa gida yasha kara hudu, yana shirin daukar ta biyar ne Bilal ya fisge kwalin daga hannun shi yana sakawa a aljihu, Rayyan baice mishi komai ba, haka da suka shiga daki ma baice mishi komai ba. Asalima kan tebir ya zauna ya fara rage tarin assignment din da yake gaban shi, yana kallon Bilal ma yayi nashi kafin ya fara danne-dannen waya da bazai wuce hira yake da Aisha ba.

Nan Bilal yayi bacci yabar shi, kwayoyin shi ya sha ganin Bilal din yayi bacci, amman har karfe uku da rabi ko gyangyadi, sai wajen hudu yadan kwanta, yasan ko da babu sallar asuba, da wahala baccin ya wuce awa daya. Rufe idanuwan shi yayi, baya ganin komai sai hotunan Layla kala-kala a cikin kan shi.

*

Littafina na siyarwa ne akan naira #300

Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank

Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:07 PM - 111: Nov 28, 2020

13

Kwance Bilal yake yana nazarin wani lissafi, saboda har an fara test tun satin daya gabata, jarabawa nata karatowa. Amman Rayyan zaune yake yana zane, wani lokacin zaka rantse da Allah hutu Rayyan yake zuwa yi Zaria ba karatu ba, saima lokacin jarabawa, idan baka gan shi yana zane ba, to zaka iya ganin shi yana kwance shiru, tunda shi dai baya hada hanya da wata kafar sada zumunta, har dan whatsapp din da akeyi ma bayayi. Asalima wayar shi da screen din ya fashe yar karamar Nokia ya siya ya saka sim din shi a ciki.

Idan wani abu na makaranta ne daya kama sai an duba yanar gizo, da kwamfuta din shi kirar laptop yakanyi amfani. Kuma yana daya daga cikin mutane hudun da suke jagorantar ajin su ta fannin karatu, inda Rayyan dinne na biyu, idan da zai maida hankali ma tsaf zai zama gwarzo a ajin.

"Wai ba test kace kuna da shi ba?"

Bilal ya bukata, kai Rayyan ya jinjina mishi

"Ba zakayi karatu ba?"

Raba idanuwan shi da takarda Rayyan yayi ya kalli Bilal din, kallon da yake fassara "Da ni kake?". Kafin ya mayar da hankalin shi kan zanen da yakeyi

"Lokutta irin haka kana sakani inajin kamar bani da kokari"

Dan numfashi Rayyan ya fitar

"Kana da kokarin ne? Tun dazun kake kallon takarda daya"

Bude baki Bilal yayi, kafin ya mike zaune

"Kasan wanne lissafine? Kake kira takarda daya kamar wani abu marar wahala"

Fensirin hannun shi Rayyan ya ajiye, ya dan juya zaman shi yana mika hannu ya fisge takardar da take hannun Bilal, duba tambayar yayi, batare daya dago ba yace

"Ina misalin? Wanda akayi?"

Tashi Bilal yayi ya dauko jakar shi yana fito da littafi ya dubo wani misalin yana mikawa Rayyan daya karba, sosai ya nutsar da hankalin shi yana ganin yanda aka fitar da abin. Kafin ya fara duba wanda Bilal yake nazari, a idanuwan shi yaga yanda komai zai kasance, juyawa yayi ya ajiye akan tebir, cikin mintina kasa da sha biyar ya gama fitar da shi yana jefawa Bilal din

"Ba zaka maida hankali sanda ake maka abu a aji ba, kana can kana wasu tunane-tunane..."

Rayyan din ya fadi a fadace, dauka Bilal yayi yana duddubawa, murmushi yayi

"Bayani zakayi mun dalla-dalla..."

Hararar shi Rayyan yayi yana sake hade fuska, dariya Bilal yayi mai sauti wannan karin yana tashi ya janyo kujera ya zauna gefen Rayyan din daya ke watsa mishi wani kallo

"Ni kyaleni"

Ya fadi saboda surutu Bilal zai sa shi yayi, watakila sai yayi mishi bayani sau biyu ko fiye da haka, amman sai ya zaqulo wata tambayar yayi mishi. Haka kuwa akayi, har saida ya kule daya fahimci Bilal din ya gane, surutun kawai yake so ya saka shi. Ganin yayi Rayyan din yayi banza ya kyale shi yasa Bilal komawa kan gado abin shi, so yake ya sake fitar da lissafin a wata takarda daban dan yaga koya fahimta, shekarar shi ta farko ya fadi jarabawa guda daya. Rayyan yaita mishi fada kamar zai mare shi, wani lokacin ko bai niyyar karatu ba yakan dauko yayi saboda masifar Rayyan da ba karewa takeyi ba.

Ranar ne karo na farko da yaji kamar yayi dissapointing din Rayyan din, yanayine da baya so ya kara faruwa. Duk da kwakwalwar su ta bambanta, yana iya kokarin shi. Rayyan zanen shi yaci gaba dayi, amman baya tafiya yanda yake so, saboda yau ya kasa rufe gabaki daya tunanin shi kamar yanda yakanyi a lokutta irin haka. Layla ce manne a ran shi, tun jiya bai ganta ba, har wayarta ya kira amman a kashe. Yanzun ma wayar da take ajiye kan tebir ya dauka ya duba ko ta turo mishi sako,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login