Showing 84001 words to 87000 words out of 150281 words

Chapter 29 - MARTABARMU HAUSA NOVELS LUBNA SUFYAN .txt

23 Nov 2025

3983

da kuma rashin mutuncin su da takeyi mata dan ta dan rage damuwa Abbu ya shigo, suna gaisawa da Rukayya ta tashi tana barin dakin, da yake girkin Mami dinne. Ta so yaci abinci tukunna ta fada mishi, amman yasan ta, ya karanci damuwa a fuskarta

"Lafiya dai Maimuna?"

Kai ta girgiza a hankali

"Duk yau tun da safe banyi magana da Bilal ba, inata kiran wayar shi ba'a dauka, sai babu jimawa kuma Rayyan ya kirani yana tambayar ko nayi magana da Bilal din, kaga kenan shima basuyi magana ba..."

Cikin tashin hankali Abbu yake kallonta tunda ta fara maganar, shima yau aiki kawai yakeyi, amman tunanin yaran nashi ya addabe shi, musamman da Bilal din bai kira shi ba, ko da suna wani meeting da yammaci, lokaci zuwa lokaci ya dinga duba wayar shi ko, dan yasan zai kira shi, cikin hira zai fada mishi Rayyan ya sauka Bauchi lafiya tunda yasan shi Rayyan din ba zai taba kira ba. Ta hanyar Bilal yakan san Rayyan yana lafiya. To kuma hidimar da yayi yau tana da yawa, amman yanata tunanin su, har Layla ba suyi magana ba, garama ita Layla ya kira bayan azahar bata daga ba.

"Kuma yanzun Maryama tabar nan, tace bata samu Layla a waya ba"

Wannan karin da kallon da yake mata hade yake da mamaki, duk da batun yanzun yasan akan yaran su Ayya zata iya ajiye duk wani tashin hankali a gefe ba, yaji dadi, sosai yaji dadi har cikin ran shi

"Ki kwantar da hankali, in shaa Allah nasan lafiya. Yanzun haka wayoyin suka kai wani waje... Idan har zuwa anjima ba'a samu ba, gobe da safe sai in kira aje a duba su, kinga yanzun ba zaka kure mutane cikin daren nan ba dan suna jin kunyar ka"

Kai Ayya ta jinjina mishi, duk da haka sai da ya kara zama a wajen nata ya tabbata ya ga murmushi a fuskarta sannan. Yana fita daga dakin nata wayar shi ya zaro yana kiran abokin shi da yake Zaria, amman bai daga ba, bayason ya karasa rikita Ayya, amman akan yaran shi ya fisu rauni, sosai zuciyar shi take bugawa, yunwar da ya yini da ita ta dauke daf, dakin shi ya nufa inda ya sami Mami ta shirya mishi abinci, shigowar da tayi yasa shi daukar plate, da kanta ta karasa ta zuba mishi abincin, yasan bataci ba shisa ya saka cokulla biyu, batayi mishi gardama ba, haka suka dinga tura abincin ba dan yana musu dadi ba.

"In shaa Allah babu wani abu, da yardar Allah lafiyar su kalau"

Kai kawai Mami ta iya daga mishi, amman yanayin jikinta yana kara tabbatar mata da babu lafiya, kawai addu'a takeyi a zuciyarta. Abbu ma haka, daren duka ukkun cikin wani irin yanayi sukayi shi, kowa da abinda yake tunani.

*

Tabbas yara raunin iyaye
Yara karfin gwiwar iyaye
Yara kwanciyar hankali da natsuwar iyaye
Yara tashin hankali da firgicin iyaye.

Allah ya bawa dukkan iyaye karfin zuciyar kaddarar da zata gifta ta kan yaran su.

*

Littafina na siyarwa ne akan naira #300

Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank

Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:07 PM - 111: 13 Dec, 2020

(An kirkiri Airport a Zaria domin tafiyar labari badan akwai ba)

20

Lokaci zuwa lokaci wanda yake kujerar kusa da shi a cikin jirgin yakan ja karamin tsaki saboda yanda Rayyan din yake bubbuga kafar shi a kasa cikin kosawa. Gani yake kamar jirgin baya sauri, baisan menene a nannade tare da harshen Bappa da kalaman shi ba, amman sunyi tasirin da suka saka shi daukar shawarar shi na tsayawa yayi abinda ya kaishi Bauchi ya wuce wajen, sai su duba idan akwai jirgin da zai tashi daga Bauchi zuwa Zaria, da yake a yar jakar shi duka katikan shaidar shi suna ciki, na makaranta, katin zabe da kuma katin shaidar dan kasa. Bappa na dubawa kuwa yayi nasarar ganin akwai jirgin da zai tashi karfe biyar da rabi na ranar.

Har suka gama abinda sukeyi a camp wajen azahar suka dawo hotel room din Rayyan bai daina mamakin yanda akayi Bappa ya saka shi zama a Bauchi har wannan lokacin ba, saboda gabaki daya hankalin shi yayi Zaria. Bai sake gwada kiran lambobin su Bilal ba duk ranar, wayar shi dai tana hannun shi, yana gudun kar ya sakata ko da a aljihune wani a cikin su ya kira ya zamana bai samu ba. Har airport din ma Bappa ne ya raka shi, a hanya ya tsaya ya sai mishi strawberry yoghurt, da yake yana da sauran biskit a jaka saiya hada ya dan sakama cikin shi, jiri har dibar shi yake idan ya mike, kuma yasan yunwa ce.

Bappa ya zauna da shi har sai da lokacin tantancewa yayi sannan suka mike a tare

"Nagode... Nagode sosai"

Rayyan ya tsinci kan shi da furtawa, saboda shine kalaman da zai iya fitowa da su da kalar karamcin da Bappa yayi mishi. Kai kawai ya jinjina ya furta

"Sai munyi waya"

Shima na shi kan ya jinjinawa Bappa, bai tabayin aboki ba balle ya san yanda yake. Amman yanajin da rayuwa ta hada shi da Bappa da wuri, watakila da sun zama abokai. Bayason mutane, amman Bappa yana mishi daban, ba shi da lokacin tunani akan abin saboda su Bilal da suka kara taso mishi suna danne duk wani kwanciyar hankali da yake tare da ita. Da su a manne cikin kan shi suka sauka garin Zaria. Kafafuwan shi kamar basa mishi saurin da ya kamata yau haka yake ji lokacin daya karasa bakin titi da yake da yar tafiya daga cikin airport din. Mashin ya samu zuwa gida

"Dari biyar"

Mai mashin din ya fadi, kai kawai ya daga mishi yana hawa

"Kayi sauri dan Allah"

Rayyan yayi maganar da wani irin yanayi a muryar shi, har sai da mai mashin din ya dan duba ta mudubi ko zai ga Rayyan din da kyau, ko a cikin abokai lokacin daya fara koyon tuqin mashin din "Dan asabe ganganci" ne lakabin shi, yanzun ma sunan Dan Asabe ya bace sai ganganci din, yanda yake jan mashin idan yana tuqi kowa mamakin samun kwastomas din shi yakeyi. Musamman idan ya busa hayaqin wiwi din shi, bakin shi babu hakora wajen biyar saboda hatsarin da yakan yawaita samu. Tabbas yau ko labari yaje ya bayar na cewa wani ya nemi ya kara gudu da shi a mashin babu wanda zai yarda.

Daman ance in da ranka zaka sha kallo, yau ya dauko mahaukaci. Sai yake jin shi a tsorace da Rayyan din, wani mahaukacin tas zaka gan shi, saika saki jiki kaji saukar duka. Haka suka lallaba harya sauke shi. Kafafuwan Rayyan din yaji suna mishi rawa, kamar suna son ce mishi ba zasu iya karasawa da shi cikin gidan ba. Zuciyar shi bata kara gudu ba sai da ya karasa tsakar gidan, har wani numfashin tashin hankali yake fitarwa, dakyar ya karasa dakin su yana ganin kofar a ture, daga hannu yayi cikin tunanin ya kwankwasa ko ya tura, ko kuma ya gwada saka mukulli. Karshe ya tsaya kan shawarar turawa, yaga dakin ya bude, duk da gidan akwai hasken wutar lantarki, dan ga mutanen cikin gidan nan sunata shige da fice, dan ko sun mishi magana ma bai kula da su ba.

Yana tura dakin ya ga duhu, makoshin shi ya bushe kamar an zuba ya shi, switch ya laluba ya kunna, duk yanda ya sha cin karo da tsayuwar bugun zuciya a karance da kuma a videos bai taba tunanin haka abin yake ba sai yanzun da ganin Bilal a kwance a kasa kamar gawa ya saka tashi zuciyar tsaya na dakika kafin ta soma aiki tana wata irin bugawa, wannan karin kafafuwan shi duka sunyi sanyi, gwiwoyin shi kamar an buge su da guduma haka yake ji, kasa yayi gabaki dayan shi. Da rarrafe ya karasa inda Bilal din yake yana dora hannun shi a jikin Bilal din

"Bi.. Bilal..."

Rayyan ya kira cikin rawar murya, tashin hankalin shi na karuwa, dan gani yayi kamar Bilal din ya rabe mishi gida biyu, idan zuciyar shi bata daina gudu ba yana gab da sumewa, dakyar ya iya birkito Bilal yana dora hannun shi kan kirjin Bilal din inda yaji zuciyar shi na dokawa a hankali a hankali cikin yanayin daya fara nutsar da na shi bugun zuciyar.

"Bilal..."

Ya sake kira can kasan makoshi, Bilal din da yake jin shi a wata duniya yana bude idanuwan shi dakyar kafin ya sake mayar da su ya rufe. Tun jiya yake nan kwance, dakyar yaja jikin shi da safiyar yau din ya shiga bandaki, daya fito ma jiri ya dinga dibar shi har ya karasa daki, towel din shi na wanka ya ajiye a kasa ya dauki ruwa yai alwalar asuba a kai, dakyar yayi sallah sabo da ciwon kan da yake fama da shi ko numfashi dakyar yake fitarwa, sanyi yakeji, amman ya mika hannu ya janyo bargo ya kasa, anan yake kwance tun safiyar yana jiran ikon Allah ya cika a kan shi.

Saboda tun jiya ya rigada yasan karshen duniyar shi yazo, baisan har rayuwar tashi gabaki daya tazo karshe ba sai yau. Akan kunnen shi aka kira azahar aka idar, amman ya kasa motsin kirki balle ya gabatar da sallah ko da daga zaune ne. Babu tunanin da baiyi ba, Ayya ita ce tafi kowa tsaya mishi a rai, yana tunanin wanda zai kula mishi da Ayyar shi a lokuttan da shi ka dai yake gane tana bukatar kulawa, wa zai kirata yayi mata hira, zai so ace ya samu dama, har addu'a yayi ya samu damar da zai roki Rayyan daya canza in zai iya, ya kula mishi da Ayya, ya kuma yafe mishi.

Ko yanzun zuwan Rayyan din sai yake mishi kamar a mafarki, labban shi sunyi nauyine balle yayi magana, daya bude idanuwan shi ma hasken dakin kara mishi ciwon kai yayi, sai yaji kamar an soka mishi allurai ta cikin idanuwan, shisa ya mayar da su yana rufewa babu shiri

"Bilal..."

Rayyan ya sake kira, amman yaki yin wani kwakkwaran motsi, bawai ciwo bane Bilal bayayi, har yini sun tabayi a asibitin makaranta aka kara mishi ruwa, amman zuwa tara na dare kamar ma baiyi jinya ba, haka yake hidimar shi, bai taba ganin shi cikin hali irin wannan ba. Tunanin zuwa asibitine yazo ran shi, amman bai taba raina karfin shi ba sai da ya daga Bilal dan ya dauke shi yaji kafafuwan shi banda rawa babu abinda sukeyi, a hankali ya mayar da Bilal din ya kwantar, dakyar ya karasa mikewa yana fita daga dakin, ba zaice ga sanda ya cire takalman shi ba, sai da ya taka tsakar gidan su yabi takan ruwan da yaji har tsakiyar kan shi sannan ya gane babu takalma a kafafuwan shi. Abinda ko a daki da wahala ka same shi babu su, akwai wanda yake ajiyewa dan yawo a cikin daki kawai.

Yakan ce Bilal din na tako kasa ya shigo musu da ita, ko idan wani a cikin abokan shi yazo neman shi yana shigowa da kasa, shikuma bayaso ya taka kafar shi yaji kasa a cikinta ko ya take

"Kai da za'a saka a cikin kasa Hamma wanne gudunta kakeyi kuma?"

Bilal ya taba fada mishi, ya saka shi kwanaki maganar na mishi yawo, shisa ya daina cewa komai kan shigowa da kasar, amman zai iya sharewa sau goma, kuma da takalma a kafar shi in yana zaune, ko safa wasu lokuttan. Amman yau bashida wannan lokacin, Abdul kamar yanda yaji Bilal din na kira yaci karo da shi

"Rayyan"

Abdul din ya fadi cikin gaisuwa

"Ka taimaka mun, Bilal bashi da lafiya"

Rayyan ya fadi cikin wani yanayi yana dorawa da

"Zan kai shi asibiti..."

Cikin tashin hankali Abdul yace

"Subhanallah... Bilal din? Yana ina?"

Dan dazun nan suke maganar sun ga motar shi yayi parking, amman har daki Sulaiman yace ya kwankwasa yaji shiru ba ayi magana ba, kuma sun nemi wayar Bilal din a kashe, sunata mamakin inda ya shiga tun safiyar jiya, saboda shi din na mutane ne, kuma anyi wasan kwallo mai zafi, an lashe club din Barcelona da Bilal din yake bi, sunata neman shi ayi adawa. Amman shiru bai leqo su ba, har Abdul din yake cewa

"Su fa yan Barca haka suke, in su suka ci su addabi kowa, amman basa daukar dabi duk idan aka cinye su"

Anata dariya da fadin yanda Bilal ya san bambanci dabi irin na kwallon, da kuma yanda baya taba bari gardamar tayi nisan da zai zamana wani yaji babu dadi, in an matsa mishi da yawa yakan ce

"Ai shikenan, ku bani panadol in watsa ko zanji dama-dama"

Shikenan gardamar sai tazo karshe a kama dariya kuma. Kaf gidan babu wanda zaice ga rana daya da Bilal yayi mishi wani abu. Yanzun ma hanyar dakin su Rayyan ya nunawa Abdul da hannu yana juyawa. Har ya fara bin shi yayi tunanin kiran sauran yan gidan, in har yau Rayyan ya tsaya yayi magana mai tsayi da shi Bilal din na cikin yanayi sosai. Kafin kace me, kusan duk wanda yake gidan a lokacin ya fito sun nufi dakin su Bilal din har babu wajen da wasu zasu tsaya, Abdul da Rayyan ne suka kama shi, baima san duniyar da yake ba, daya daga cikin su ya dauki mukullin motar daya gani ajiye kan tebir suka fita da shi, sai dai su shidda suka iya tafiya asibitin duk kuwa tarin mutanen da suke son binsu.

Motar babu waje, mutum biyune a baya, sai Bilal na ukku da suka saka a tsakiya. Har Rayyan daya shiga gaba zai kulle kofar yaga wani da zai iya kirga ranakun da magana ta taba hadasu ya kutso, dole ya matsa mishi ya shiga ya rufo suka tafi. Babu fadan da ba'ayi musu ba a asibitin, da yake na kudi kawai suka nufa a maimakon na makaranta. Nan da nan aka fara bawa Bilal din taimakon gaggawa, Rayyan yaso tsayawa cikin dakin, amman bayason yin gardama da likitocin a bata lokaci wajen bawa Bilal taimako. Daga shi sai Sulaiman aka bari dan sauran da suka tabbatar Bilal din ya samu taimako duk sai suka tafi, da zasu barwa Rayyan motar ya girgiza musu kai

"Ban iya tuqi ba, ku tafi da ita kawai..."

Yana kula da kallon mamakin da sukeyi mishi, babu dai wanda ya furta komai. Da gaske yau yaga ranar mutane da Bilal kan fada mishi, wajen dubu sha biyar aka bukata tashin farko, shi kuma dubu uku da dari biyune a jikin shi tunda jirgi ya biyo, sai dai jakar shi na goye a bayan shi har lokacin. Akwai kuma ATM din shi a ciki, kudin duk ya kwashe ya biya jirgi, sauran dubu takwas a ciki. Kafin yayi wani yunkuri ma su Abdul sun harhada kudin hannun shi, shima saiya kara da dubu ukkun aka bayar.

Zaune suke a dakin shiru daga shi har Sulaiman din suna kallon Bilal, har sai wajen karfe tara na dare, Abdul shi kadai ya dawo, ya kawo musu darduma da kaya guda biyu dan su ya fara gani baisan kona waye a ciki ba. Harda brush ya dauko musu da McLean ya taho da shi. Tare suka mike da Sulaiman suna fadin

"Allah ya kara sauqi yasa kaffara ne, zamu dawo da safe in shaa Allah"

Kai Rayyan ya jinjina

"Mungode...nagode sosai. Nagode"

Murmushi Abdul yayi

"Haba maza ai ana tare"

Ya fadi suna danyin dariya, sosai Rayyan yaso yayi murmushi amman baya cikin yanayin. Kai kawai ya iya jinjina musu, suna ficewa daga dakin. Mikewa yayi shima ya shiga bandaki ya dauro alwala, magariba da isha'i yayi, yau Bilal kawai yaiwa addu'a ya tashi ya dawo yana jan kujerar sosai ya matsa kusa da gadon Bilal din

"Me ya same ka haka Bilal?"

Yayi tambayar a zuciyar shi yana sauke numfashi, saboda likita yace mishi jinin Bilal din yayi wani irin hawa. Har sai da yaji tsoro da yaga takardar. Kwata-kwata Layla ta makale a wani waje cikin kan shi saboda Bilal ya danneta, sai yanzun ne ta fado mishi, wani sabon tashin hankalin na dirar masa, watakila itama bata da lafiyar. Ya laluba wayar shi baiji ta ba, saiya kula cikin kayan da Abdul ya kawo harda wayoyin su shi da Bilal da cajar waya ya hado. Shikam zuwa yanzun baisan kalar godiyar da zai musu ba, sai dai in Bilal ya tashi shi zaifi sanin abinda ya kamata.

Wayar Bilal ya tashi ya saka a caji dan yaganta a kashe, aikam cajin ne babu. Sai da yaga ta dauka sannan ya dawo ya zauna. Gwada lambar Layla yayi inda yai nasara ta shiga, har ta kusa yankewa sannan aka daga, wani irin numfashi ya sauke

"Layla..."

Ya kira daga lungun zuciyar shi, yanajin kamar yabi ta cikin wayar ya leqa inda take yaga lafiyar ta.

"Layla..."

Ya sake kira, muryarta can kasa ta amsa

"Hamma"

Lumshe idanuwan shi yayi yanajin yanda zuciyar shi ke rawa, nutsuwar da ta kwace mishi yake nema koya take, iya wadda zai samu karfin yi mata magana yaji inda ta shiga haka. Amman ya kasa samu

"Hamma ban da lafiya"

Layla ta fadi ta dayan bangaren, cikin wani mawuyacin yanayi da ya saka Rayyan din mikewa, sai dai ya kasa kara yin motsi saboda Bilal da yake gani a kwance shima, tunani yake ko akwai hanyar da zaibi ya raba kan shi gida biyu yabar daya anan asibitin dayan kuma yaje wajen Layla, dan sai yake jin kamar kuka take kokarin dannewa, zuciyar shi ciwo takeyi, ciwon daya kama ta nan take, dakyar ya iya cewa

"Kina ina? Me ya same ki? Waye a wajen ki?"

Ya kusa dakika biyar kafin ta amsa shi

"Bani da lafiya Hamma..."

Ta sake maimaitawa kamar bataji tambayoyin da yayi mata ba, wannan karin yaji sautin kukanta da ya kara mishi ciwon da zuciyar shi takeyi, dan baisan yanda zaiyi ba, baisan wa zai kira ya taimaka mishi ba. Ya bude baki zai sake yin magana ta riga shi da fadin

"Anisa...muna asibiti tun da safe. Hamma kana ina?"

Numfashi Rayyan ya sauke, a muryarta yake jin yanda take bukatar shi

"Ina asibiti, Bilal ba shi da lafiya. Me yasa zaku min haka Layla? Ya kuke so inyi? Ya zakuyi rashin lafiya lokaci daya?"

Ya karasa maganar yana bi da rokon yafiyar Allah dan yaji kamar yayi sabo, kamar yana kokarin dora ayar tambaya akan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login