Showing 135001 words to 138000 words out of 150281 words
shiga dakin babu ko sallama ba
"Yaushe abin nan zai wuce mana Abbu? Me yasa mutane ba zasu kyale mu ba? Ina ruwan su da rayuwar mu?"
Hannu Abbu ya dan bubbuga a gefen shi yanawa Jabir din alamu daya je ya zauna, bai musa ba kuwa ya karasa yana zama inda Abbu ya nuna mishi, idanuwan shi sun kada sunyi ja, watakila da yayi kuka zai samu sauki
"Nagaji da ganin Mami na kuka kullum, ina jina so helpless..."
Dan murmushi Abbu yayi
"Ka kalleni Jabir, ban san inda nake samun karfin bude idanuwa ba a duk safiya, saboda wannan ne karo na farko da ko kalaman lallashi bani da su, damuwar ku gabaki daya ta tarar mun, ni ya kake tunanin ina ji? Um Jabir? Dan Allah ka dan kara daurewa, komai zaiyi sauki In shaa Allah"
Jabir ya dade zaune a dakin ya hade kan shi da gwiwa yana neman sauki koyaya ne. Kamar yanda shima Abbu yake tsaye a wajen yana neman sauki a yanzun, daga shi, Ayya sai kuma Mami a asibitin, da yake dare ya farayi sanda suka fito din, wajen sha daya. Addu'ar duk da tazo bakin Abbu ita yakeyi, kafin wayar shi da take aljihun shi ta fara ringing, yana fito da ita yaga Rayyan ne, yana dagawa ya saka a kunnen shi muryar Rayyan din ta daki kunnen shi
"Ina ta kiran Ayya bata daga ba, Mami ma haka, Layla fa? Nakudar ce ta sake dawowa ko Abbu? Ina magana da ita naji shiru, sai kira nakeyi itama bata dagawa"
Dan siririn numfashi Abbu ya sauke
"Gamu nan a asibiti m..."
Rayyan bai bari Abbu ya karasa ba yace
"Me suka ce? Ga shi dare yayi ni ba zan iya tahowa ba yanzun"
Duk da halin da Abbu yake ciki sai da yayi dan murmushi
"Ka kwantar da hankalin ka. Babu abinda zai faru sai alkhairi da yardar Allah, zan dinga kiran ka ina fada maka yanda ake ciki, kayi mata addu'a kai dai kaji"
Sai da ya amsa sannan sukayi sallama, su Mami ya kalla
"Rayyan ne"
Kai Mami ta jinjina, ko lokacin da ake maganar soyayya a dangin su, zancen baya wuce
"Anya akwai matar da tayi sa'a irin Maimunan Ahmadi?"
Ko da ta aure shi ta sabajin yanda ake fadin
"Maimunan Ahmadi"
Shisa sam bata jin kishin haka, zata so a yanzun na minti daya idanuwa da hankulan kowa su dauke daga cikin Layla su koma kan ita da Rayyan, tana da tabbacin tsantsar kaunar da take tsakanin su zai saka su fara sabon mamaki, ba kowanne namiji bane zaiyi abinda Rayyan din yayi. Ko ita maganar ta daketa da tajita daga farko, sai ta dinga ganin kamar mafarkine, duk da tasan da yawa zasu ce tayi azarbabi, kamar ta jira taga yanda zaman Rayyan da Layla zai kasance a karkashin inuwar aure kafin ta yanke hukunci akan tarin kaunar da suke yiwa juna. Sai dai ta kasa, tana da yakini mai girma akan kaunar Layla da take gani tattare da Rayyan din.
Watakila kuma idanuwanta ne suka rufe saboda nauyin da Rayyan din ya dauke mata na tunanin wanda zai zamo miji a wajen Layla, wanda zai kauda kai daga tabon da yake tare da ita harya ganta din, da tarin kalubalen da zata iya fuskanta daga wajen dangin shi idan har ta samu din ma. Duka rayuwar 'ya mace zagaye take da martabar da tabuwarta yake dai-dai da nakasun da zai taba gabaki daya ahalinta. Kuskure daya tak zai iya canza komai ta fannin da gyaruwar shi zatayi wahala. Dukan su a tsaye suke duk kuwa da kujerun da suke a wajen, babu mai natsuwar zama, kowa da abinda yake sakawa yana kwancewa a cikin zuciyar shi.
*
Motar farko ya samu daga Kaduna zuwa Kano, asuba ma a tasha yayita. Da yake Bappa ya kai shi, amman gani yakeyi kamar motar bata sauri, yau ne ya sake jin takaicin rashin iya tuqi, da yana da mota a hannun shi iya gudun da yake so zaiyi. Abbu ma da safen nan kira biyu yayi mishi bai daga ba, ga shi yanzun sun fara shiga wajajen da babu network me karfi, ko shi tun yana gwada kira harya hakura ma, ko baccin kirki bai samu ba, lokaci zuwa lokaci yake kira yaji ko ta haihu.
"Har yanzun dai, da ta sauka din zan kiraka In shaa Allah"
Shine amsar da yake samu wajen Abbu. Ba dan baisan yawan yan gidan su gabaki daya ba, amman a daren sai da ya tsinci kan shi da kirgasu, saboda yana son yaga sau nawa Abbu ya jure tashin hankali irin wanda yake jin shi a ciki. Yama fi jinjinawa matan, dan yana da yakinin idan shine a matsayin su babu abinda zai hada shi da ciki. Yara ne ya ga na yan uwa sun ishe shi, amman da yake Allah yayi wa mata wata irin jarumar zuciya, sai ka sha wahalar nan kuma gobe ma ka sake maya wata. Babu kalar tunanin da baiyi ba, ciki harda na yanda da yasan cewar kaso kusan casa'in cikin matsalar shi bata da alaka da asibiti, da saiya tafi fannin mata wato Gynecology ko dan rana irin wannan.
Sanda ya sauka garin Kano, daga tasha kan shi tsaye asibitin da Layla take wanda na kudine ya tari mashin yana nufa. Tun bai karasa sauka ba yake kiran Abbu da ayi mishi kwatancen inda suke din, shisa sanda ya karasa Abbu din ma ya fito bakin kofar asibitin yana jiran shi
"Da ka zauna ai Rayyan"
Abbu yace bayan sun gaisa, kai Rayyan din ya girgiza mishi
"Hankalina ba zai kwanta ba Abbu. Gara ina nan din dai"
Da gaske yakeyi, dan duk abinda suke fada mishi jinsu kawai yake, yafi so yana gani da idanuwan shi. Sauran duk da tayi ba'a dadewa haka ake ce mishi ta samu bacci ba haihuwar bace da ta tashi zasu tafi gida, ko kuma gasu a hanya zasu koma. Amman yau har yanzun da suke takawa suna shiga cikin asibitin babu wani labari.
"Ayya..."
Cewar Rayyan cikin sigar gaisuwa, ita da Mami suka juya a tare, kafin su amsa shi daya daga cikin Nurses din ta fito da murmushi a fuskarta
"Ta sauka lafiya"
Ta fadi tana saka su tattara hankulan su zuwa kanta gabaki daya. Lumshe idanuwan shi Rayyan yayi yana sauke wani numfashi da baisan yana rike da shi ba. Duk wani abu da suke fadi baya karasawa kunnuwan shi sam. Ba zaice ga asalin abinda yake ji ba, kafafuwan shi ne sukayi wani irin sanyi, baisan lokacin daya tsugunna ba, banda numfashi kamar wanda ya sha gudu babu abinda yakeyi, baisan lokacin daya dauka a wajen ba sai da yaji Abbu ya dafa kafadar shi
"Ka zo ka fara karbar ta"
Kalmar "ta" na fada mishi 'ya mace ce Layla ta haifa, zuciyar shi yake ji cikin tafukan kafafuwan shi a lokacin daya mike yana bin bayan Abbu zuwa dakin da aka dawo da Layla din da akanwa lakabi dana hutu. Amman baya ganin komai, idanuwan shi kafe suke kan yarinyar da take hannun wata Nurse da taketa murmushi ta karaso tana mikowa Rayyan yarinyar, hannuwan shi duka rawa suke lokacin da ta saka mishi yarinyar, yana mamakin rashin nauyinta, dan ji yake kamar zata subuce mishi idan yayi wasa. Yawu yake nema a cikin bakin shi da yayi wata irin bushewa lokacin da ya kafa yarinyar da take ta mutsilniya a cikin farin towel din da take nade ciki har wuyanta.
Kafafuwan shi yake ji suna son karayin sanyi, dakyar ya iya dan rankwafawa da kan shi saitin kunnenta yana mata kiran sallah a ciki kafin yayi mata hudu da
"Maimunatu"
Kamar yanda yasan burin Bilal kenan, maganar shi kenan, zancen shi akan yara baya wuce farawa da samun 'ya mace da zai sakawa sunan Ayya, yana dagowa ya sake kallon yarinyar yana jin yanda a duniyar shi bai taba sauke idanuwa akan halitta mai kyawunta ba, bai taba ganin wankakke abu da babu dauda a jikin shi ba sai ita, kafin yaji wani abu ya tsirga mishi yana saka shi tallafeta a kirjinta kamar yana son kareta daga tunanin shi, yana son kareta daga furucin mutane akan laifin da bata da alaka da shi
"Idan baka dawo danni ba, dan Ayya, ka dawo dan ita Bilal, dan Allah ka dawo haka"
Ya furta a cikin kan shi yana jin wani irin radadi na ratsa duk wata gaba ta jikin shi, ko da su Ayya suka shigo dakyar suka iya raba Rayyan da yarinyar daya fara kira
"Nur"
Saboda da gaske ita ce hasken daya gani a cikin yan watannin da rayuwar su gabaki daya tayi wani irin sauyi. Ko da taje hannun Ayya, bata san lokacin da hawaye suka fara zubar mata ba, Mami ta mikawa ita tana ficewa daga dakin gabaki daya, waje ta samu ta zauna a bakin kofa, kuka takeyi da ta kwana biyu batayi irin shi ba. Kuka takeyi na abubuwa kala-kala, kuka take musamman akan rashin danta, kuka takeyi na hakkin Rayyan da har yanzun ta kasa samun karfin gwiwar kallon idanuwan shi ta fada mishi balle ya yafe mata. Anan bakin kofa ta samu kujera tayi zamanta, Mami ma tayi kuka ba kadan ba, jikar tace ta farko ta rike, jikar da tazo mata ta wani fanni mai wahalar gaske.
"Ina nemar kariyar Allah a kanki daga dukkan wani abu mai muni, daga saukin shafar da kaddarar iyayenki zatayi miki"
Shine addu'ar farko da tayi bayan ta karbi yarinyar. Abbu ma tunda ya karbeta yayi mata addu'a ya basu ita, saboda shine yake da karfin zuwa yaji ko akwai sauran kudaden da zasu biya. Da yake Layla din ba wata matsala ta samu ba, sai jigata da tayi, wajen azahar aka sallame su gabaki daya suka dunguma zuwa gida. Rayyan bai samu sunyi wata magana da Layla ba, ko idanuwa ta kasa hadawa da shi har suka sauka gida, yana gani Mami ta jata suna shigewa bangaren su, har daki ta kaita, sannan ta koma dan ta hada ruwan wanka, zaune Layla take inda Mami ta barta, sai Nur a gefe da take bacci kamar bata da wata damuwa a fadin duniya.
Sai lokacin hawayen da suke cike da idanuwan Layla suka zubo. Nur take kallo, wasu hawayen suna kara zubo mata, bata dauka zata haifota batare da ta rasa tata rayuwar ba, ta sallama da lamarin duniya gabaki daya, saboda duk wani ciwo da ta taba tunanin taji nafila ne akan zafin nakuda, jikinta babu wata gaba da bata amsa da ciwon ba, ta sha wahalar da bata taba hangowa ba, wahalar da take fatan ta zame mata kaffara saboda tana kokarin ganin ta cika duka sharuddan tuba, tana kuma da yakinin Allah mai Rahma ne
"Ga kaddarar mu Hamma, kaddarar da mu duka bamu hango ba. Allah ya yafe maka, Allah ya yafe mana"
Ta furta a hankali, tana kai hannu ta share siririyar kwallar da ta zubo mata. Babu wani abu da yake da sauki a cikin rayuwa banda bautar Allah, ita ce zakayi ka samu natsuwa, ita ce kuma zakayi a kyauta. Amman yanzun take ganin kacokan wahala ce a cikin zaman duniya, a da tunanin yanda zata bada labarin kaddarar da ta gifta tsakanin ta da Bilal ne, kafin fuskantar su Mami, sannan kuma rayuwa da cikin da kowa yake nunawa 'yatsa. Tunanij ta gabaki daya ya sauya lokacin da kukan Nur ya dira a kunnenta a karo na farko, ta sake gane komai ba komai bane in dai ba zai taba yarinyarta ba lokacin da aka saka mata ita a cikin hannunta.
Yanzun gabaki daya babu wani tunani a cikin kanta banda na kare Nur daga duk wani abu da zata iya, a lokaci daya darajar su Abbu na kara daguwa a idanuwanta, ashe haka iyaye suke ji, ashe haka 'da yake, cikin awanni kalilan ta dandani fargabar da take cikin kula da amana mai girma har haka.
*
Littafina na siyarwa ne akan naira #300
Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank
Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:09 PM - 111: Jan 22, 2021.
32
Yafi mintuna sha biyar tsaye yana juya hular da ya kamata ace tana sanye a kan shi. Yau na daya daga cikin ranakun da suke da muhimmanci a rayuwar shi, ranar daya kamata yayi ta da mutanen da suke da muhimmanci a wajen shi, bai ma su Abbu gardama ba da sukace ya bari Layla tayi arba'in, yarinyarta ta danyi kwari sannan. Duk da ba wannan dalilin bane ya saka shi jiran, har a kasan zuciyar shi Bilal yake jira, a cikin kwanakin babu ranar da zata wuce idan ya kira gida baiyi tsammanin zasuce mishi Bilal din ya dawo ba.
Watakila harda kewar Bilal da yake ji a duk wata gaba ta jikin shi, kamar zuciyar shi na son gaya mishi baiji mutuwar Bilal yanda ya kamata ba saboda yana tunanin kamar bai rasa shi ba. Tun lokacin daya fara tunanin aure yasan baya bukatar wata hayaniya, a daura mishi aure kowa yayi fatan alkhairi ya tafi. Idan akwai abinda ya hango bai wuce shi da Bilal zaune a daki suna cin abinci suna hira bayan an daura aure, amman bayajin zai samu hakan yau. Baiyi kokarin danne Layla ba, ya tambaye ta
"Wanne irin biki kike so Layla? Dan Allah ki fada mun, bikin ki ba zai dawo sau biyu ba..."
Ita ma din tana daya daga cikin mutanen da basa son wata hayaniya ta biki, tuni suna fada ita da Jabir, bikin su daga su sai mutanen da suke da kusanci da zuciyoyin su suke bukata a lokacin bikin su
"Bikin da zan zama matar ka Hamma, daurin aure, shi kawai nake bukata"
Duk yanda idanuwanta ke kara gudun zuciyar shi sai da ya jima yana kallon cikin su yana neman gaskiyar maganarta. Bayason taji cewa kamar ita din bata cancanci kalar bikin da take mafarki ba
"Wai me kakeyi ne har yanzun?"
Bappa da a gidan ya kwana duk kuwa yanda Rayyan din yace mishi ba wani abu za'ayi ba, ya koma gida da safe ya dawo
"Ina ruwan ka dani ne Rayyan? Gidan nan naga na Abbu ne, kuma baice in tafi ba..."
Har a zuciyar shi yaji dadin zaman Bappa din, tunda kusan kwana yayi yana kallon ceiling cike da tunani kala-kala har wayewar garin
"Ku fa ake jira"
Haris ya fadi yana leko kan shi, turarukan daya hango na saka shi shiga cikin dakin sosai. Dauka yayi ya sake feshe jikin shi, Rayyan na bin hular da take kan shi da kallo, zuciyar shi na matsewa a cikin kirjin shi
"Hular Bilal ce ko?"
Ya bukata muryar shi can kasan makoshi. Kai kawai Haris ya daga mishi yana ficewa daga dakin. Kamar yanda ya fadawa Rayyan cewa zaije Zaria ya kwashe kayan su haka akayi. Rana daya ya ware, da wani irin karfin zuciya ya shiga garin Zaria har zuwa unguwar su Bilal. Harya shiga cikin gidan ma haka, ya san duk yawancin yan gidan, da Abdul ya fara cin karo daya karaso da sauri suna gaisawa yana dorawa da
"Ina Bilal? Lambobin shi gabaki daya a rufe, mun kasa samun lambar Rayyan, kaima taka tayi wahala saboda babu yan set dinku da sukayi saura, wallahi tunda aka dawo muke tunanin ko lafiya....sai yanzun muke tunanin kalar zaman da mukeyi da yanda ya kamata ace kowa yana da adireshin gidan kowa ko da halin ziyara bai samu ba"
Wani murmushi mai ciwo Haris yayi, zuciyar shi daya dauka ta dake yaji tana rawa, muryar shi ma a raunane yaji ta lokacin daya kalli Abdul da fadin
"Ya rasu, hatsari yayi. Ya rasu..."
Ya karasa maganar wani abu na tokare mishi makoshi
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Din da Abdul ya furta cike da tashin hankali na saka shi raba Abdul ya wuce cikin gidan. Da yake ya karbi mukulli a wajen Ayya, shiya dauko ya saka yana bude dakin, bai shiga tashin hankali ba sai daya kunna kwan dakin yana ganin yanda yayi wata irin kura kamar mutane basuyi rayuwa a ciki ba. Dakin yake karewa kallo, yana hango wajeje da lokuttan da suke zaune a ciki shi da Bilal, sai yaji har kirjin shi ma zafi yake. Ba zaice ga mintinan daya dauka a cikin dakin ba kafin yaji shigowar yan gidan su Bilal din da babu wanda yace mishi komai, dakin suka fara taya shi sharewa.
Kusan babu wani abu da yayi, su suka dinga hada komai, duk yanda ya so ya kwashe komai saiya kasa, daga takardun da yake tunanin suna da muhimmanci sai suttura ya dauka, sauran hatta da katifa nan yabar ma su Abdul da yake ganin yanda mutuwar Bilal din ta dake su sosai. Lambar shi suka karba da fadin zasu shiga Kano suyi wa Ayya gaisuwa. Kai kawai ya jinjina musu yana ficewa ya shiga motar shi da aka loda kayayyakin a ciki. Sai daya zauna sannan yaji jikin shi na rawa ba kadan ba.
Rayuwa aikin banza, babu wani abu da yake da tabbaci a cikinta, ba mutuwar Bilal kadai yake ji ba, harda tashi mutuwar yake hangowa, duk tarin burukan da suka ci shi da Sa'adatun shi mutuwa zata iya yanke musu shi, ga Bilal nan da Aisha, ya tabbata yarinyar bata taba hango auren wani ba Bilal ba, soyayya tun firamari ake yinta, ta ina zata fara yanzun? Wa zata budewa zuciyar ta, wanne waje ma zai samu bayan ko ina cike yake da kaunar Bilal? Hawayen da yaji ya share a kasan zuciyar shi yana fadin
"Allah ya jikan ka Bilal, kai din mutumin kirki ne. Allah ya sa mutuwa hutun ka ce"
Sai dai daya ajiye kayan Bilal a dakin su akwai wanda ya dauka, duk yanda yaso ya barwa Rayyan komai saiya kasa, ciki harda wannan hular da ya saka a kan shi, tare sukaje suka siya da Bilal ba zai manta ba, shi da kan shi ya dauketa ya dora ma Bilal din a kai
"Hamma ni fa bana son wannan zanen, ina da shigen shi"
Maganar Bilal din ta dawo mishi a lokacin
"Ni ina son shi, tunda ni zan biya"
Dariya Bilal yayi
"Jiba ikon Allah, dan zaka sai mun shine ba zan zabi abinda nake so ba? Yaushe aka taba yin haka?"
Shima dariyar yayi
"Yau za'a fara idan ba'a taba ba"
Sai kuma ya dinga yawan ganin Bilal din da hular, duk kuwa yanda manyan kaya ba