Showing 18001 words to 21000 words out of 150281 words
karba, kamar yanda da dukkan zuciyar shi bayason ko yaya ne jikin shi ya hadu da nata, dan a tsorace yake, kokari yakeyi na ganin bai kalli fuskarta ba
"Saki mana..."
Ya furta, amman sai ta maqale kafada, ran shi bashida wuyar baci
"Mtswww, ki saki nace, ta ina ma kika shigo mana"
Rayyan yake fadi yana sake jan takardar, itama ja tayi ta kuwa rabata gida biyu, cikin tashin hankali Rayyan yake kallon takardar da take hannun shi, kafin ya kalli ta hannun Layla din, wani malolon bakin ciki na mishi tsaye a makoshi, baisan lokacin da ya dauketa da wani irin mari ba, dai-dai shigowar Bilal daya karasa da gudu yana tare hannun Rayyan daya daga zai sake mata wani marin, dayan hannun shi kuma yana ture Layla da ta gigice ko kuka ta kasa saki saboda azaba
"Hamma... Me tayi maka? Baka ga yarinya bace?"
Bilal yake tambaya cikin tashin hankali yana juyawa ya kalli Layla da sai lokacin ta samu ta fashe da wani irin kuka
"Ban sani ba, daka shigo baka ga abinda yake hannunta bane ba? Me yasa zata shigo mana daki?"
Hannunta Bilal ya rike yana rasa ta inda zai fara lallashinta
"Amman ai karama ce, me yasa zaka mareta?"
Bilal ya sake tambaya, dan shi sam baiga dalilin da zaisa duk girman Rayyan ya mari 'yar yarinya kamar Layla ba. Duk da saurin hannun shi akan kowa yake sauka. Ko jiya yayi mishi magana daya mari Shamsu saboda bai gani ba ya diga mishi ruwa. Yan kananan yaran gidan babu mai zuwa kusa dashi, wani lokacin ko wasa sukayi yayi sallama da gudu zakaga kowa na neman wajen boyewa. Wanda suka girmi Rayyan ma shakkar shi sukeyi, ko Khalifa yakan rabe gefe yaba Rayyan hanya, bamai so wani abu ya hadasu sam
"Ka fita da ita, wallahi zan kara dukan ta idan taci gaba da kuka"
Bilal hannun Layla ya kama yana janta suka fice daga dakin. Rayyan din nabin su da wani irin tsaki. Yanajin yanda bai daki wahalar kwanan shi biyu da yayi yana wahala ba sam, da Bilal bai shigo ba ya samu ya jibgeta da ya samu saukin tafasar da ran shi yakeyi yanzun
"Mayya kawai"
Ya furta yana jin wata tsanarta a ran shi, a gefe daya kuma Bilal ne yake ta kokarin lallashin Layla daya samu tayi shiru, sai yatsun Rayyan kwance akan fuskarta. Baisan menene maraici ba, duk da yaji idan Ayya tayi baki wata rana suna maganar yanda shi din maraya ne. Itama kuma yaji ance marainiya ce, haka kawai yake jin tausayin yarinyar. Ko ido suka hada saiya tsinci kan shi dayi mata murmushi. Ko kadan basu da masaniya akan yanda kaddara ta bude musu sabon shafi.
*
Littafina na siyarwa ne akan naira #300
Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank
Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:06 PM - 111: Nov 6, 2020
05
*
Kwanakin shi a lissafe suke, yana son makaranta, har kasan ran shi yana son makaranta. Yana kuma son karatu, musamman yanda Allah ya bashi baiwar kwakwalwa, da wahalar gaske ayi abu sau daya a gaban shi bai dauke ba. Kawai abu dayane ya kasa fahimta a shekarun shi goma sha bakwai yanzun a duniya. Duk lokacin da Abbu ko Ayya zasu nuna suna son abu, lokacin zaiji har ranshi babu abinda ya tsana sama da abin, yana so ya bari, yana so yaso abinda suke so ko dan yanda yake ganin halayen shi sun kasa raba zukatan su da tarin kaunar da sukeyi mishi.
Ya wuce Bilal da aji daya, amman zai iya tuna lokuttan da Bilal din yake daukar nashi litattafan ya duba ko an basu wani aiki da baiyi ba dan ya taya shi. Da gangan zai bar takardun shi babu rubutun komai, kawai dan yanda Abbu ya nuna yana bala'in kaunar su da karatu, bawai dan tambayoyin sun gagare shi amsawa ba. Ba a makaranta kawai hakan ya tsaya mishi ba, duk wani lamari na rayuwa da zamantakewar yau da kullum, kar dai Abbu ko Ayya su nuna ga yanda suke so, dan zaiyi abu daban da wannan din ne. Bai fara kawo sakamako mai kyau ba sai da yazo aji hudu a makaranta, ranar da kalaman Abbu suka tunzura shi
"Nasan asarar kudina kawai nakeyi Rayyan, da ka daina zuwa makarantar nan zaifi mun, amman dai zanci gaba da biya dan in nunawa Yaya Ayuba cewa zancena gaskiya ne, babu abinda zaka iya ganewa indai bangaren makaranta ne"
Daga ranar hatta Malaman shi mamaki sukeyi, irin yanda lokaci daya ya canza haka. Har kaguwa yayi lokacin jarabawa yayi dan ya kawowa Abbu, aikam na biyu yazo a ajin nasu lokacin. Da kan shi yazo ya nunawa Abbu, karba yayi batare daya nuna wani jin dadi a fuskar shi ba
"Dan kayi wannan baya nufin za'a dore"
Shine kalaman Abbu, sune kuma kalaman shi a duk lokacin da zai kawo mishi wani abu daya danganci kokarin da yayi a makaranta. Tunda ko hira baya zama suyi, idan hirar shi tayi tsayi da wani to Bilal ne. Yanzun ma makaranta zasu tafi, harya gama shiryawa tsaf, amman Bilal ko wanka bai fito ba. Takalman shi ya dauko yana fitowa bakin kofa ya ajiye, silipas din da yake ajiye ya zira ma kafafuwan shi da nufin ya shiga bangaren Ayya ya dauko musu ruwa. Shi kayan sanyi ba damun shi sukayi ba, bama yaso sam, da an kawo pure water yake zuwa ya sungomo leda daya yazo dakin su ya ajiye. Ya duba ya kare shisa ya fito.
Yana karyo kwana suna cin karo da Layla da tsayin shi bai hana idanuwanta sauka cikin nashi ba
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
Ya furta da karfi, zuciyar shi na wani irin dokawa, bayason ganin yarinyar sam, sai yaga kamar mage ce ta gitta mishi, yanzun ma ko ina na jikin shi bari yakeyi, har zuciyar shi.
"Ina kwana"
Ta furta a hankali, duk da tasan ba amsawa zaiyi ba, zuwa yanzun da zata iya hana kanta gaishe da Rayyan ko shiga sabgar shi da ta daina. Amman duk abinda zata shirya ma kanta da ta sauke idanuwanta kan Rayyan din komai yake kwance mata. Kallonta yayi ran shi a bala'in bace
"Dan ubanki ban hanaki zuwa inda nake ba? Mayya ce ke? Sau nawa zan gaya miki idan ina waje ki daina zuwa?"
Rayyan ya furta har lokacin zuciyar shi bata daina dokawa ba. Wasu irin hawayen bakin ciki Layla taji sun taru a cikin idanuwan ta, bashi bane mutum na farko daya kirata da "Mayya" ba, ba kuma shi bane zai zama na karshe, ko Ayya takan fada wasu lokuttan, su kadai ne suke fada a cikin gidan gabaki daya. A waje kuwa da wahalar gaske ka furta kalmar bata fasa maka baki ba, ta karfi da yaji ta zama mafadaciya ta gaske. Kullum saiya mata kashedin zuwa inda yake, amman a haka yake aikenta, a haka yakan sakata aiki, tana iya dawowa daga aiken shi ya hauta da masifar ta daina zuwa inda yake kamar bashi ya kirata ba. Har mamakin shi takeyi, sai kace mai jinnu.
Bata zabi zuwa duniya da kalar idanuwanta ba, asalima idan da an bata zabi zata dauki irin na kowa, bata kuma zabi fitowa daga jikin mahafiyar ta ba, balle a dinga alakanta su da Maita, kalma mafi ciwo a duniyarta gabaki daya.
"Hanya ce, kuma kowa wucewa yakeyi Hamma..."
Layla ta fadi itama nata ran a bace
"Rashin kunya zakiyi mun?"
Rayyan ya bukata yana sata kallon shi da idanuwanta da bayaso, tana kara hautsina mishi lissafi, ita kadai ce ta raina shi haka duk gidan, ita kadai ce take kallon shi kamar bata tsoron shi, take kallon shi kamar shi din bai isa ba
"Idan nace ba rashin kunya nai maka ba zaka yarda ne?"
Tayi tambayar tana sake tsare shi da manyan idanuwanta, kamar da take mishi da mage na kara bayyana, baisan lokacin daya dauketa da wani irin mari ba. Kafin ta wartsake ya kara dora mata wani duk a kunci daya. Ba marin shi bane ba ta saba sha ba, kawai a lokutta irin haka sai ta rantse da Allah a duniya babu wanda ya tsaneta sama da Rayyan, kullum kuma neman dalilin tsanar takeyi ta rasa.
"Matsa daga nan kafin in tattakaki, wawiya kawai"
Rayyan ya karasa maganar da wani irin tsaki, yana saka hannu ya tunkudeta harta kusan faduwa tukunna ya wuce. Gabaki daya ta hargitsa mishi lissafi, da yasan zai ganta, sam ba zai fito ba, ruwan daya hakura saiya dawo makaranta sai ya dauka. Abbu yagani, ran shi a bace yake ko magana bai mishi ba ya raba zai wuce
"Rayyan gaisuwar ma ba zan samu ba kenan yau ko?"
Baice komai ba ya shige abin shi, kai kawai Abbu ya jinjina. Da gaske ne jarabawa ta rayuwa takan zo ma bawa ta fanni daban-daban. Inda wani ya bashi labari tashi jarabawar zata so ta bangaren Rayyan ne ba zai taba yarda ba. Yana tuna kalar shakuwar shi da yaran a lokacin da yake dan karamin shi. Sai da ya dauka a cikin yaran shi gabaki daya mazan babu wanda zasu shaku dashi kamar shi da Haris, lokaci daya Rayyan ya sauya kamar wanda jinnu suka shafa.
Yanzun Rayyan ne zai nuna sam bayason magana da shi, zai karya idan yace abin baya mishi ciwo, yana kula da yanda idan ya nuna yana son abu to Rayyan din yaki abin kenan, kamar a duniya yana rayuwa ne dan ya bakanta mishi. Karatun shi ma sai da dabarar da Yaya Ayuba ya bashine da yai amfani da ita tukunna ya samu kan shi. Shisa ko da wasa yaki nuna mishi yana jin dadin yanda yake maida hankali. Yanzun ma ya kula sam ya daina jin ya Rayyan din yake ciki a makaranta. Ko wani abin akace su siya saidai Bilal yazo ya fada mishi.
Bai cika tashi tsayuwar dare ba, amman matsalar Rayyan tasa dare dai-dai ne baya tashi dan kawai yayi mishi addu'ar samun salama. Zuciyar da yake da ita tafi komai dagama Abbu a hankali, zuwa yanzun ko sallama akayi dashi a unguwa yasan ba zai wuce an kawo karar Rayyan din ba. Ko lokacin samartaka fada bai taba hadashi da wani ba, ammam sai gashi zuwan shi police station takwas duk akan Rayyan. Kuma ba yan waje kawai ya tsaya ba har cikin gida babu mai rabar shi, kusan kullum sai yayi ban hakuri cikin gidan akan Rayyan.
Yama daina mishi fada, nasiha ce wasu lokuttan, wasu lokuttan kuwa sai dai yabi shi da addu'a kawai, yanzun ma
"Allah ya shirya"
Ya fadi yana wucewa. Rayyan kuwa dakin Ayya ya shiga, idan kasan gidan su a baya, kazo yanzun zakayi mamakin yanda aka gyara ginin yayi dai-dai da zamani, saboda rufin asiri dai-dai misali Abbu yana da shi. Ya taka matakin Professor kamar yanda burin shi yake, ga kasuwancin shi da Allah yake saka mishi albarka saboda shi mutum ne mai yawan taimako da kyautatawa iyalan shi. Shisa sam baya kukan rashi, rayuwa sukeyi mai natsuwa. Duk da tsayin shekaru bai canza zaman da yake tsakanin Maimuna da duka yaran suke kira da Ayya sai kuma Maryama da suke kira da Mami.
"Rukayya babu ruwa ne a dakin?"
Rayyan daya shiga kitchen ya duba bai gani ba ya fito falon yake tambaya. Da saurinta ta mike, har ranta tana kaunar Yayan nata, haka ma sauran yan uwan nasu, amman baya shiga cikin su, baya shiga sabgogin su, zatayi karya idan tace batajin kishin Bilal wani lokacin, saboda kusancin da yake tsakanin shi da Rayyan din. Ayya ba fada takeyi ba, amman sunsan cewa ba daga jikinta Bilal ya fito ba, saboda ko a makaranta da asalin sunan Baban shi yake amfani. Sai take ganin kamar ya kamata ace sunfi shi kusanci da Rayyan din.
Fridge taje ta duba tana dauko mishi leda daya na ruwa ta fito ta kawo, tun kafin ya karba yace
"Ba mai sanyi ba Rukayya... Bana son ruwa mai sanyi"
Kai tadan rausayar, bai shiga cikin su bama balle su san me yake so ko meye baya so.
"Hamma duk an saka a fridge... Sai dai ko idan zaka ajiye ya huce..."
Karbar ruwan yazo yi
"Kabari in kai maka daki"
Kai ya girgiza yana karba
"Zaka karya in hada maka tea?"
Kai ya sake girgiza mata, saboda ya fara jin maganar da sukeyi tayi mishi tsayi. Bayason kananun surutai marassa dalili
"Ko zaka ci wani abin"
Daga idanuwan shi yayi yana mata wani irin kallo daya sata komawa ta zauna. Kusanci take nema a tsakanin su ko yayane, kamar ko da yaushe bai bata wannan damar ba, zai fita daga dakin kenan Ayya ta fito daga dakin baccin ta
"Rayyan..."
Ta kira tana saka shi runtsa idanuwan shi kafin ya budw su a hankali
"Ayya ina kwana..."
Ya fadi yana dan juyawa
"Kaci gidan ku... Daka shigo bakasan inda nake ba halan?"
Kai ya jinjina
"Ayya....ruwa kawai na zo dauka, ban san kin tashi ba kuma"
Kallon shi kawai tayi, tasan karya yake, da bata fito ba sam ba zaije su gaisa ba. Idan zaiyi yini biyu bai sakata a idanuwan shi ba baya damuwa, Bilal ne idan shigowa goma zaiyi gidan saiya zo ya nemota, wani lokacin sai taga kamar yana son rage mata damuwar Rayyan ne, musamman idan yasan Rayyan din yayi wani laifi. Haka zai wuni yana lallabata kamar shi yayi mata wani abu. Kuma da gaske yana rage mata damuwa ba kadan ba.
"Allah ya shirya mun kai"
Cewar Ayya, Rayyan na ficewa daga dakin. Kan shi tsaye dakin su ya wuce ya ajiye ruwan. Dai-dai shigowar Bilal
"Yaushe zaka daina cin zalin yarinyar can ne? Kai baka duba maraicin ta?"
Dan fitowa yayi yaga Layla na tsaye tana hawaye, ga yatsun Rayyan kwance a kan fuskarta. Bai tambayeta me ya faru ba, hakuri kawai ya bata dan yasan a gidan babu wanda zai daketa idan ba Rayyan din ba. Duk idan kaga hawaye a idanuwanta to shine.
"Karka kara batamun rai Bilal..."
Rayyan ya fadi, shiru Bilal din yayi ya kyale shi. Idan ma surutu yayi yana iya kara jama Layla wani dukan. Duk saurin hannun Rayyan saika shiga harkar shi tukunna. Amman banda Layla, da alama ko numfashi tayi kusa dashi laifine. Har mamaki Bilal yakeyi, kuma ko aike Rayyan din zaiyi, gashi tunda yasan idan ya aike shi ba zaiki zuwa ba, takanas zai leka ya kira wani yaro cikin gidan ya bashi kudin yace a kai Layla ta siyo mishi, kuma da wahala aiken ya kare da dadi, dan sai ya nemi wani dalilin da zai daketa.
Kuma na rana daya bata taba kin zuwa aiken shi ba, duk wasu kananun ayyukan shi ita din yake sakawa. Shirin makaranta ya karasa suna fita tare da Rayyan din, su duka sabon sune sai sunje makaranta suke karyawa. Gara Rayyan ya siyi biscuit a hanya
"Hamma kai da biscuit"
Bilal ya fadi yana dariya. Ba zaka taba raba aljihun Rayyan da biscuit ba, ko jakar makarantar shi ka duba zaka samu, kuma bayason mai zaki. Haka zai ta daukar abin shi dai-dai yana ci. Babu wanda baisan amanar da take tsakanin shi da biscuit ba, har Abbu wasu lokuttan yakan siyo sai ya baiwa Bilal din yace yaba Rayyan. Yanajin wani iri duk lokacin da Abbu ko Ayya zasu kyautatawa Rayyan din sai abin ya biyo ta hannun shi. Sai yake jin kamar suma zasuji ya kwace musu kusancin daya kamata ace yana tsakanin su da dan nasu.
"An hana ci ne?"
Kai Bilal ya girgiza mishi
"Kaima idan kana ci kasa hannu, ban hanaka ba ai"
Kai dai Bilal din ya sake girgizawa, shi bama komai yake ci ba. Babur suka tare suna hawa su biyun zuwa makaranta daya kamar yanda suka saba.
*
Bilal bai bude ledar da Aisha ta bashi ba sai da yazo gida. Harya natsu ma, duk gidan shi da Bilal ne suka fara makaranta daya daga firamari har yanzun suke sakandire a ALIC. Kuma yasan Aisha tun tana firamari, yana mata magana ne saboda tana mishi yanayi da Layla, daga rawar kanta har idan tayi dariya. Idan alewa yagani zai siya yakan siyi guda biyu ya bata daya. Aji dayane a tsakanin su, yanzun yana aji hudu ita kuma tana aji uku, kusan duk wanda yake ALIC yasan Aisha da Bilal. Danma shi wani lokacin yana tare da Rayyan, ita kuma tsoron Rayyan take ji, ba ita kadai bace, kusan duk wani wanda yake cikin makarantar tsoron Rayyan din yake ji.
Garama Aisha saboda Bilal yana dan mata magana wasu lokuttan. Amman idan baka ganshi da Rayyan ba zaka gan shi da Aisha. Wata irin shakuwa ce mai karfi a tsakanin su, zuwa yanzun har yan gidansu sun san Bilal, musamman wani lokaci da tayi rashin lafiya ta kwanta asibiti, yaje yafi sau biyar, hatta da Baban Aisha sai da yasan shi a lokacin. Da yake yana da wani irin shiga rai, haka cikin kankanin lokaci ya shiga ransu suma. Har wata Yayar Aisha din ta dinga tsokanar shi
"Bilal din Aisha..."
Murmushi ya dingayi saboda kunyar da ta dinga sakawa yanaji. Yanzun ma bude ledar yayi, biskit ne kala-kala da cin-cin, a cewarta bikin abokin wasanta akayi. Kayan bikin ne ta kawo mishi. Bayason kayan zaki haka, kawai dan Aisha ce shisa ya dauki cin-cin daya ya saka a bakin shi. Baiji shigowar Rayyan ba sai hannun shi da yagani cikin ledar yana daukar biskit guda biyu
"Kai ba zakai sallama ba"
Waje Rayyan ya samu ya zauna, kamar baiji maganar da Bilal din yayi ba
"Ina ka samo biskit kai kuma?"
Murmushi Bilal yayi
"Aisha ce sukayi biki, shine ta kawo mun"
Kai Rayyan ya jinjina
"Yara kanana daku wai soyayya. Allah ya shirya"
Yanayin yanda Rayyan din yai maganar ne ya ba Bilal dariya. Zaka rantse da Allah wata shekara goma ya bawa Bilal din ba daya da doriya ba
"Waye yace maka soyayya mukeyi?"
Tabe baki Rayyan yayi
"Zan fadama Ayya su fara shiri, ba zakai karatu ba, gara Abbu ya kaika kasuwa kawai a aurar da kai...ka kawo biskit din nan ko guda biyu a kai ma Ayya dan ta ga abinda surukarta ta bayar..."
Dariya Bilal din ya sakeyi yana fadin
"Hamma..."
Dariyar shima Rayyan yakeyi
"Jibi yanda idanuwanka suka cika da kunya. Bilal... Allah ya shiryeka to"
Biskit daya Bilal ya dauka yana jifan Rayyan din da yake dariya dashi. Bai cika magana ba, amman randa duk ya saka shi gaba da tsokana sai ya rasa bakin ramawa. Musamman yanzun akan