Showing 9001 words to 12000 words out of 80179 words

Chapter 4 - KYAUTAR KODA Hausa Novels by NoorEemaan.doc

11 Nov 2025

3034

*NIKE* dan karamin hijab fari half sunnah ta sanya, wata yalwataccen jallabiya kirar saudiya ta dora kan pajamas din kana ta tayar da sallah...

Bayan ta iddar ta cire jallabiyan ta haye gado, take wayarta ta dauki kara, lumshe ido tayi kana ta bud'e a nutse murmushi dauke kan fuskarta domin tasan Fadeel ne, domin shi kadai ta sanyawa wanna ringing tone din, latsa Kore tayi ta kara wayar a kunnenta hadi da furta "Assalama alaykum" cikin zazzakar muryarta.

"Wa'alaikumu salam" ya amsa yana kara curewa kan 'yar yololuwar katifarsa da alama muryar tace ta haddasa masa shiga wanna yanayin

"My darling yakike, ya gajiya, Fatan kin je gida lafiya?"duka ya jero mata tambayar a lokacin daya.
A shagwa6e tace "Alhamdulillah, wallahi my one na gaji sosai, amma yanzu na fara warwarewa sak'amak'on jin muryar muradina, muradin raina, Yes my heart desire".
Murmushi ya saki cikin wani sabon shauki yasake k'amk'ame jikinsa kana yace "I hope ina tare dake, I hope yanzu mu ma'aurata ne dana yi miki tausa" ya karasa cikin rada.

Murmushi mai sauti ta saki, tana ji ina ma Ina ma su din ma'aurata ne, da hakika sun gina rayuwar aure mai cike da so hadi da birgewa.

"Darling kaunar ki zata haukata ni, kinsan har mafarkin nake akan ki kullum, jiya da asuba Mahmah tazo tashina Saboda na makara taji ina ta kiran Fadeelah cikin bacci, dan Allah ki rike mun amanar kanki bazan iya juran rasa ki ba a rayuwa, ji nake tamkar dan soyaayyar ki kadai aka halicce ni" ya karasa cikin iyakar gaskiyar sa.

Pillow ta k'amk'ame a kirjinta, maganganun sa na shiga jini da tsokar jikinta har wani tashi sigar jikinta ke yi alamun maganganun na shigar ta sosai.



Cikin wani salon so tace "my one, kasani cewa babu kowa a birnin zuciyar Fadeelah fiye da Fadeel dinta, sannan Abadan da'iman muna tare, mutuwa ce zata raba mu in sha Allah"


Ajiyar zuciya mai karfi ya sauk'e daya sanya taji wani sabon so da tausayin sa, cikin muryar rada yace "Darling mutuwar ma nafison ta d'auke mu a lokaci daya, ko kuma ni na fara mutuwa domin bazan juri rasa ki a rayuwa ta ba..."

Katse shi tayi da cewa"gwara ta dauke mu a lokaci daya, mu tafi tare, nima bazan juri rasa ka ba my one, we are made for each other I love you"


"I love you so much too my Darling, ki kwanta kiyi bacci, ki yi mafarkina bye muaaahh" ya karasa da sakar mata sumbata ta wayar


Wani sanyi dadi ke ratsa ta hakika babu abinda ya kai kasamu masoyi mai son ka tsakani da Allah. "love is sweet when it's new, sweeter when its you fadeel, and sweetest when it's pure" ta fada a bayyane fuskarta d'auke da murmushi, addu'ar kwanciya bacci tayi kana ta rufe jikinta da duvet babu jimawa bacci mai dadin gaske masu cike da mafarkin Fadeel ya d'auke ta...


*WASHEGARI*
suna zaune a dinning table suna breakfast, Fadeelah sai murmushi take ita kadai har Daddy ya farga yayi gyaran murya hadi da cewa "My beautiful princess, wanna murmushi fa ke kadai? kwanan nan na kasa gane miki fa, You seems over happy" ya fada shi ma da murmushi kan fuskarsa alamun farincikin daya tsinci 'yarsa a ciki yayi masa dadi...



"Atoh professor nah, taya ni tambayar ta, domin yanzu hardly kaga fuskar sweetheart ba murmushi, ya dai kamata ki gaya mana what's the secret behind" Mommah tace tana kai Irish omelette bakinta.



Dariya tayi cikin jin kunya, kana tace "babu komai Daddy, Mommah"

"Haka dai kika ce, amma bari idan tayi tsami zamuji koma menene, ko professor nah?" Ta fada tana kallon Daddy.

"Haka yake my first Lady" Daddy yace cikin salon su na manya.



Fadeelah kanta a kasa tana cin chips dinta daya bayan daya, yayinda take tunanin shin ta gayawa Daddy'n ta cewa ta samu mahadin rayuwar ta, a life partner ko a'a?....
'?




_In sha Allah gobe ma zan sake baku sabon update da sannu zamu shiga cikin labarin..._
_Amma two pages as promise tunda reposting muke_


*Thanks my people da kulawar ku gareni a sakamakon jina shiru da kuka yi jiya, i was damn busy ko data ban kunna ba jiya, wadanda suka yi min mgn private dama groups, ina godiya sosai*



Share

Comment

Vote

Editing is not allowedL'


I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*


=????YAUTAR ?O?A=???
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)


_by Noor Eemaan_=???
'?


Wattpad
@NoorEemaan



ELEGANT ONLINE WRITER'S=???=???



Page 15-16

Sau ba adadi ta budi baki da niyyar yin magana, sai taji wani abu mai nauyi ya rufe akinta, karshe dai ta yanke hukunci bari zuwa nan gaba sai ta sanar da shi komai...




Bayan ta gama breakfast ta koma bangaren ta, da tunanin idan ta dawo zata leka part din kakanin ta da sauran ahalin gidan su gaisa domin yau kwana hudu kenan bata leka su ba, kasancewar akwai tazara mai yawa tsakanin parts din... Da wanna ta shiga toilet, cikin jaku'zzie ta fada, lumshe ido tayi ruwan dumin na ratsa ta, *L'occitane verbena shower* ta fara murzawa a farar fatar ta, kasancewar ta kusan yin latti yasa tayi wankan a gurguje ta fito daure da pink towel, lotion take shafawa idanunta kafe kan hotunan zanenta dake manne a bango, murmushi take saki ba tare da tasan tana yin hakan ba.



Inner wears ta saka, kana ta dauko wata hadaddiyar gown na company *Giorgio Armani* banda walwali babu abinda rigar ke yi, dan veil din rigar ta yana a kanta kana ta dauko takalmi wage da handbag duka na company Giorgio Armani din.



Duk da bata son yin make-up sosai, amma haka nan ta ji yau tana sha'awar yi, a tsayen ta fara goga hada'dd'en powder dinta daya dace da skin color d'inta sannan ta sanya k'walli hadi da goga pink lip gloss, fadin kyau da haduwar fadeelah bata baki ne, ita kanta sai data yaba duk da ta san ita din mai kyau ce, amma tabbas *idan kana da k'yau ka kara da wanka* inji malam bahaushe.

*DKNY(golden delicious millions dollars fragrance)* shine turaren da Daddy ya kawo mata tsaraba daga USA wanda kudin sa 1 million ne, sannan shine turaren mai mafi tsadar gaske wanda babu kamar sa a yanzu. Fesawa tayi Sama_sama tana yaba kamshin turaren mai sa nutsuwa, hakika DKNY yaci kudin sa, glass ta sanya a fuskarta brown kana ta fito bayan ta dauki wayar ta kirar *falcon supernova*
Ganin tayi latti sosai yasa bata koma part din su Daddy ba, direct ta nufi inda motoci ke fake suna jiran ta, kamar kullum motar da ake tanada domin ita kadai ne, wanna karon *Bugatti La voiture Noire* aka bud'e Mata kalan fara, yayinda duk suke gaishe ta cikin girmamawa, fuskarta a sake kana da murmushi ta amsa, zama tayi aka rufe mata kofar, gate man ya wangale masu gate suka fara ficewa dayan bayan daya....


Idanunta na kan wayarta tana danne-danne, da alama chatting take kamar ance ta dago kanta ta ga wani kamar Fadeel ya taho a kafa, zare glass din idanunta tayi, "tabbas my one ne" ta aiyana a ranta idanunta kan Fadeel din tace wa driver "stop the car!" ba musu mai tuka ta ya tsaya, take sauran suma suka tsaya... Bata jira ba, ta balle murfin motar ta fito, har ya dan gota su domin sam bai lura da ita ba...

Tana jikin motar ta hard'e hannunta kan kirjinta ta kira shi a shagwa'be
"my one"
cak! ya tsaya, kana ya juyo murmushi d'auke kan fuskar sa. Takowa yayi ya dawo gabanta yace "my darling?"
Bata rai tayi cikin wasa tace "Shine kayi fuska ko, bayan ka ganni"
Murmushi ya kara saki shagwa'bar ta na tafiya da shi matuk'a "my Darling afuwan, sam ban ganki ba" ya fada cikin yanayin na dan ji nauyi, domin har kokarin boye kafarsa data yi butu-butu da kasa yake alamun ya sha tafiya sosai....


Dariya ce ta so kamata domin ta fahimce shi sarai, shi bai san duka wanna bai dameta ba, shi takeso, ba wai kyau, qualities ko wani abu daya shafe shi ba.

Kura masa ido tayi tana yaba kyawun sa, sam bashi da haske ko kadan, amma yana da mugun kyau da wasu fararen ma basu da shi, kallon kafar tasa ta sake yi kana ta dawo da kallonta kan fuskar sa tace "ina kaje haka?"
Shafa kansa yayi yace "Mahmah ce ta aike ni kai kudi gidan biredi, fatan sauraniyar Kyawawa ta tashi lafiya?"

Murmushi tayi, tausayin sa fall zuciyar ta tace "alhamdulillah, kai fa?"
"Same" yace a tak'aice.

Murmushi tayi wani lokacin tana son wanna halin sa na rashin son dagon magana, sannan tasan idan tace ya hau mota su ajiye shi gida ko bashi kudin mota tofah bazai yarda ba, ta rasa wani irin mutum ne dashi daya dau duniya da matukar saukin gaske, a fili tace "my one akwai maganar da nake so muyi da kai, it's very important"


"Ok ba matsala zamu yi waya, then muyi fixing wurin haduwa ko?"

"Toh shikenan bye na makara office" tace tana daga masa hannun ta.

"Zan yi kewar ki sosai darling, take care I love you"

"I love you too" tace tana shiga motar ta.

Yanda bud'e murya yanda zata ji yace "Darling kinyi kyau sosai, karki bari kowa ya kalli min Kyakyyawar fuskar ki fa..."


Dariya tayi domin yadda ya bata rai sai ya dawo mata kamar wani yaro karami.


Kamar kullum a nutse ta shiga cikin company, duk suka gaisa da ma'aikata(staff) d'inta, kana ta wuce office

"wallahi abokina yarinyar boss na matukar tafiya da ni, naso ace tazo a matsayin wacce bata fi karfina ba, da ba shakka zan gabatar mata da kaina a matsayin masoyinta, domin sosai nake sonta" Cewar wani matashi dake sanye da kaya mai dauke da tambarin company.


Abokin nasa yace "kasan Allah, ina jin na fika son yarinyar nan, kowa a company nan maganar ta yake, mutane da dama sun ce matukar cutar dake damunta ya kai minzanin da ya gaza, to zasu iya Sadaukar mata da nasu ciki har dani, ban taba ganin mai son jama'a hadi da talakawa kamar yar boss ba".


Haka suka cigaba da hira duka dai kan Fadeelah, haka kullum yawanci ma'aikatanta suke hira a kanta, a duniya babu inda za a ce mutum bai da makiya, amma a company'n din su Fadeelah za a iya cewa kaf dinsu masoyan ta ne.




Please follow and vote me on wattpad=?O?>?z?
@NoorEemaan



Share'=?O?

Comment'


Vote'

EditL'L'L'



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*


https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.



=?????AUTAR ?O?A=???
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)



_byNoor Eemaan_=???
'?
07082281566


Wattpad
@NoorEemaan

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.


Page 17-18

Bayan sun dawo daga company, wanka kawai tayi ta nufi part di'n family'n babanta, kasancewar da yar tafiya hakan yasa tayi amfani da mota.


Da Abba Yusuf ta fara cin karo wanda ya kasance yaya ga Daddy'n ta, kyakyyawan farin mutum ne mai yawan fara'a sabanin Daddy'n Fadeelah da bai cika fara'a ba.


Gaban sa ta tsugunna cikin girmamawa tace
"AbbaYusuf ina wuni"

Murmushi yayi har farin hokarin Makkah sa ya bayyana sai walwali yake yace "A'a Fadeelah kina lafiya, kinyi wuyar gani, ko nayi surukine ya boye min ke?"


Dariya tayi cikin jin kunya tace " Abba Yusuf, aiki ne wallahi, amma nazo kwanaki mama(matar Abba Yusuf) tace min baka dade da fita ba"


"Kwarai kuwa, anyi haka, ya aikin? Toh Allah ya taimaka 'yar albarka"

"Alhamdulillah Abba Yusuf, Ameen nagode"

Bai kara cewa komai ba ya fada motar sa ya bar gidan.


Da kallo ta bi Abba Yusuf, sosai take kaunar sa, domin ya fita daban cikin yan'uwan Daddy'n ta.


Bangaren kakarta ta fara zuwa, sallama tayi aka amsa hadi da ba???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ta izinin shigowa. Zaune dattijuwar matar dake kan wasu had'add'un kujera daya kara kawata falon, duk da kasancewar matar tsohuwa ce domin zata kai irin shekaru 79.


Fara ce sosai bata da yawan fara'a, yar gayu ce sosai, domin duk da shekarun nan nata sanye take da riga da skirt na tsadaddiyar atamfa daya sha dinkin zamanin fuskar ta kuwa ya sha make-up irin na wayayyun mata, yayinda take sanye da medicated glass, tun kafin Fadeelah ta karaso take cewa "my beautiful grand-daughter"


Murmushi Fadeelah tayi tace " Grandma" hadi da rungume ta kana ta gaisheta, a sake grandma ta amsa gaisuwar ta domin kaf cikin jikokinta tana matuk'ar ji da Fadeelah.

"Ai Daddy'n ki bai jima da barin nan ba, har Ina cewa kin guje ni kwana biyu ashe yar halak kina tafe"


"Murmushi tayi hadi da cewa " Grandma wallahi naso zuwa abubuwa ne suka min yawa, akwai wani branch da Daddy zai bud'e a Kaduna ya sa abubuwa suka kara min yawa yanzu"


"Eh kwarai ya gaya min haka, toh sannu Allah yayi miki albarka, ya Samira(Mommah)?"


"Alhamdulillah, tana lafiya. Grandma yau baki yi kunun aya ba?"




Murmushi grandma tayi tace "grand-daughter kenan, ke da kunun ayar nan, toh yana fridge dazu nayi wani domin na shanye na safe"

"Ai a wajen ki na gado son kunun aya, tunda Daddy baya sha" Fadeelah ta fada cikin tsokana tana bude fridge.



Murmushi kawai Grandma tayi tana bin jikarta mafi soyuwa a ranta da kallo. Dawowa tayi ta zauna da mug hadi da glass cup ta siyayi kunun aya mai sanyi domin har wani rabar sanyi jikin glass cup d'in yake, a nutse take shan kunun yayinda suke hira da grandma har ta shanye suka yi sallama.
Part din sauran yan'uwan taje ta gaishe su kana ta fada motarta ta koma part di'n su.


Bangaren Mommah ta koma, ta tarar da ita a zaune tana kallon tashar Bollywood, jikinta ta fada tace " Mommah nah sannu da gida"


Shafa lallausan gashinta Mommah tayi tace "Sweetheart yakike yau kam kin dade"

"Mommah na dade da dawowa fa, part dinsu Grandma naje"



"Kin kyauta kam, kin same su lafiya?"

"Lafiya lou suke, sun ma ce suna gaishe ki"


"Ina amsawa, nima na kwana biyu ban leka ba, amma idan professor ya dawo zan nemi izini naje, tashi ki ci abincin gashi can cikin warmers, yau girki kala uku nayi miki da kaina ba da taimakon chef's ba, kuma duka favorite dinki"


"Awwwwnn my sweet Mommah, nagode sosai muaaahh" ta bata sumbata a kumatu tana nufar dinning table.

Dan daga murya Mommah tayi tace "kuma duka zaki cinye domin nasan ki da rashin cin abinci shiyasa gaki bakya hauki kullum"
Mommah ta karasa a zolaye.

Dariya Fadeelah tayi ta zauna tana cin abincin daga dinning table din suke dan taba hira.


&&&


*Bayan sati daya*

"Ohh Mahmah har na haddace labarin yarinyar da kuka hadu a asibiti, kullum sai kin yi min hirar ta, ni wallahi dama labarin Fadeelah kike min kullum" Fadeel dake zaune kusa da mahmah ya fada a Wan shagwabe



Dariya Mahmah tayi ita kanta tana mamakin so da kauna da take yiwa yarinyar data hadu da ita a asibiti da ko sunanta bata sani ba. Kullum sai ta yi hirar ta, maganar ta ya kasa barin baki da zuciyar ta. A fili tace "Fadeel my son Ina mai tabbatar maka da cewa da zaka ga yarinyar nan data kwanta maka a rai ko dan Saboda nutsuwa da sanin mutuncin dan Adam"


Shiru kawai yayi domin yasan matukar Mahmah na son abu tofah ta dinga maganar abin kenan...

Ana haka wayar sa ta fara ringing yana dubawa yaga "my Darling" murmushi ya saki kana ya mike yana kara wayar a kunnen sa,
"ok gani nan zuwa yanzu nan Darling" shine amsar da Fadeel ya bawa Fadeelah


Dan shafa kansa yayi alamun jin kunya yace "Mahmah zan fita"


Dariya tayi tace "yaushe Fadeel dina ya fara jin kunya ta, toh ka gaishe ta, idan ka dawo zamuyi wata magana"


"A'a Mahmah zan iya tsaya muyi maganar dake"



"A'a ban amince ba, ka bar min suruka da jira jeka dai ka dawo, Allah ya kiyaye hanya sai ka dawo"

"Toh Mahmah na ameen, I love you"

"Love you too son" tace tana cigaba da jajjaga attaruhun dake gaban ta.



*Banana Island*
shine inda fadeelah tace su hadu, wanda ya kasance hadadden wurin shakatawa ne.
Tun daga kofar wajen ya ga bodyguards dinta reras jikin motocin ta, shi kanshi a wasu lokutan yana mamaki yanda ya iya kamuwa da son diyar miloniya haka, dan dai so daban yake babu ruwan sa da kudi, kyau, ko wani abu na mutum amma yasan Fadeelah ba sa'ar yin sa bace domin wusiyar rakumi tayi nesa da kasa.

Sai dai ko kadan baya jin zai karaya har abada har sai ya mallake ta...



gaisheshi suka yi, domin sun gane shi yanzu sosai, amsawa yayi a mutunce ya nufi cikin wajen.

Tun daga nesa suke jefan juna da kallo mai dauke da tsantsar so hadi da kauna.



Bayan sun yi gaisuwa irin ta masoya.Ta gabatar masa da abinci, lemo hadi da ruwa gora data yi musu ordering.
Saboda kada ta ji ba dadi ya sa shi shan ruwa kadai kana ya kalleta a tausashe yace "my Darling kince akwai magana mai muhimmanci da zamuyi"


Diamond ring di'n hannunta take murzawa yayinda k'lanta ke kasa, a sanyaye ta dago hadi da cewa "eh" wanda yayi daidai da zubar wasu hawaye masu zafin gaske a idanunta.



"Subhanallah! My Darling meya faru haka, mai yayi zafi? Please ki gayamin kafin zuciyata ta buga, bana son ganin damuwa a tare dake ko kadan, hazantar gaya min damuwar ki dan Allah" Ya fada cikin zallar damuwa yayinda ya dawo gabanta ya tsugunna.




_comment Winku na kadan fa, ko in ajiye labarin ne_>??


Share'

Comment'

Vote'

EditL'

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*


=???K?AUTAR ?O?A=???
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)


*Wattpad*
@NoorEemaan


ELEGANT ONLINE WRITER'S=???=???


https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.



The destiny has begin

Page 19-20

(Not

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login