Showing 72001 words to 75000 words out of 80179 words

Chapter 25 - KYAUTAR KODA Hausa Novels by NoorEemaan.doc

11 Nov 2025

3046

matata nake son ci, amma bana so ki wahala"



Murmushi ta yi tace "ba wani wahala my man, zan dafa maka kaji" ta fada tana nufar kitchen, duk da tayi mamakin jin cewa yana jin yunwa, amma ba abin mamaki bane idan akayi duba da chajin jinin da akayi masa, ga kuma maganin Karin jini wanda yake sa shi cin bacci sosai...


Sai da ta bacewa ganin sa kana ya dauke kansa. Bangaren fadeelah kuwa private kitchen din ta ta nufa, tsaye tayi tana tunanin abinda zata girka masa da bazai dauki lokaci ba, Saboda kada fadeel din ta yaji yunwa....


Tuwon semovita da water leaf soup daya sha naman kaza, stock fish, cat fish hadi da crayfish ta shiga hadawa, bayan awa d'aya da mintuna goma sha biyar ta gama komai, har da lemon kankana da saka ice block hadi da watermelon flavor tayi blending dinsu kana ta saka cikin wani jug mai k'yau hadi da kananun cups din sa, gabadaya part din ya dauki kamshi sosai...


Kimtsa kitchen din tayi, ta wanke abubuwan data bata, kana ta dauki tray din ta fito, zaune ta tarar da shi kamar yadda ta barshi, sai dai wanna karon hannun sa dafe saman fusk'ar sa, jin takun tafiyar ta ya sanyi shi bud'e idanunsa yana sakar mata murmushi, martani ta mayar masa, kan center table ta dora tray din....


"Sorry na barka kai kadai ko?" Tace tana zama a gefen sa.



" dont worry, Sannu kinji wiffy na sa ki aiki, kamshin girkin ki yasaka saliva dina diga, saura kadan ki ganni a kitchen din ki "


Murmushi kawai tayi tace "ka cancanci fiye da haka my one, yanzu da abinci zaka fara ko wanka?"



"Hmmmmmmm... wanka zan fara yi" ya fada yana kallon Hada'dd'en POP din saman dakin.


dawo da kallon sa gare ta yayi "kema kina bukatar wanka wiffy" ya fada yana mika mata hannunwan sa, taimaka masa tayi suka nufi bedroom d'in sa, ruwa ta hada masa a jaku'zzie bayan ta saka bath soak, fita tayi ta hango shi tsaye jikin kofar bathroom, kallon shi tayi tace "me yasa baka zauna ba, kafar ka fa"



"Rashin ganin ki yasa na taso domin zuciyata ta samu kusanci da taki zuciyar"



Murmushi ta saki mai sauti, ta hade hannayenta a k'irjin ta, sun jima suna jifan juna da kallon kauna, kana ta riko hannun sa suka shige toilet din, sai da ta tabbatar ya shiga cikin jaku'zzie kana ta ruga a guje ta nufi dayan bathroom, duk da kiran da yake mata kuwa, domin ta fahimci so yake su yi wanka tare...



Dariyar ta ta gimtse sanda suka yi tozali da juna, gashi ya riga ya ganta da towel babu halin gudawa, amma taji kunya kam, domin towel din karamin ne sosai....


Gaban shi tazo ta zaunar da shi, duk yanda take jin kunya haka ta daure ta fara shirya shi, domin idan bata taimaka masa ba, hakika bata kyauta ba, kananun kayan shan iska ta sanya masa, bayan ta shafa masa mai, body spray mai dadi ta fesa masa, kana tayi oiling gashin sa ta taje masa, sosai kuwa yayi k'yau tamkar black America.



Itama lotion ta shafa, body spray data fesa masa itama ta fesa a jikinta, kayanta ta saka wani straight fitted gown mai spaghetti hand, hadi da saka head band golden color, kamar yadda gown dinta ya kasance golden.



Light makeup tayi, daga hoda data shafa, sai kajol(kwalli) hadi da lipstick maroon color daya sata yin wani sihirtaccen kyawu d'aya zai narka zuciyar Fadeel...

Bayan ta mayar da make up kit din mazaunin sa, take ta juyo gare shi...

Baki Fadeel ya bud'e yana kallon ta, sosai tayi masa k'yau tamkar an sanja masa ita, kasa hakuri yayi har sai da ya ware mata karfaffan hannayen sa, da murmushi a fuskar ta shige jikinsa ya mayar da hannu sa ya rufe.

Ajiyar zuciya ya sauke yace "my Darling kin yi kyau sosai, fiye da yanda bakina ba zai iya fadi ba, I love you the mother of my unborn children"


"I love you too Fadeel" tace tana lumshe ido Saboda k'amshin turaren jikinsu dake ratsa kofofin hancin ta.

Sun jima suna hirar soyaayar su, kana suka nufi parlo domin ya ji abinci, kasan centre carpet ta suka zauna bayan ta shimfud'a ledar cin abinci, a baki ta dinga bashi har ya koshi, sai ta siyaya masa lemon kankana ya sha sosai kuwa yana santi, ta dinga shan dariya kuwa, shima kuwa ya ciyar da ita har ta koshi...

Har dare haka ta dinga dawainiyya da shi hadi da bashi kyakyyawar kulawa...


***********


Ta bangaren Jameel kuwa, sosai damuwar sa tayi yawa, ya rame sosai, har hakan ya daga hankalin su minister... Baki jameel da minister suka hada kan kawar da mutum daya daga duniya, tsakanin Fadeel da Fadeelah ta hakan ne zuciyar jameel zai kwanta, wanda ya san ya rasa ta ko bata duniyar akan wani ya rayu da ita yana raye, tunda kidnapping dinsu ba abu bane mai sauki tunda kullum suna cikin tsaro...




A ranar sa suka gama hada plan dinsu, da yamma haulat ta kawo musu ziyara kamar kullum suka aikata zinar su son ransu babu tsoron Allah...



Da bayan magariba sunyi wanka, haulat ta fada mota, suka yi sallama... Haulat ta yi nisa da tafiya, ta yi karo da wata akori_kura, take motar tayi raga_raga, take haulat ta amsa kiran ubangiji, nan fa go slow ya hadu sosai, wani mutum ne yaga tsadaddiyar wayar ta yashe a kasa screen din ta fashe sai dai ba sosai ba, dauka yayi, luckily babu security kan wayar, number jameel ne Karshen kira hakan ya shi kira number'n...


Zaune jameel yake da wasu tantiran samari yana fada musu yanda aikin zai kasance kamar yadda shi da minister suka tsara... Ringing din wayar sa ne ya katse masa maganar sa...

Ganin number haulat ya sashi dagawa, abinda yaji mutumin ya fada ne ya sanya gaban shi wata mahauk'aciyar bugawa ba tare da ya shirya wa hakan ba.


Wani nauyi yaji kansa yayi masa, ba tare da bata lokaci ba ya figi mota sai inda aka yi masa kwantance. Ai ganin gawar haulat ya so juye k'wak'walwar sa, hakika bai taba jin mutuwa data shige shi kamar na haulat ba, ya kasa yarda haulat da suka gama zina mintuna da suka wuce ce ta mutu, kuka yake da idanun sa sosai, take kuwa ya kira lambar iyayen haulat din kasa da mintuna ashirin suka zo hankali su a tashe, ganin gawa 'yar tasu ya sanya hankalin iyayen ta tashi sosai, ubanta ne yayi k'arfin hali, amma uwar har da birgima a kasa, jameel kuwa tamkar ruwa ya cinye shi, babu abinda ke fita a idanunsa kamar hawaye, cikin dumbin al'ajabi, asibiti aka kaita, aka sake gwada ta, nan aka tabbatar rai yayi halinsa, a asibiti duk suka kwana, jameel ya manta wani abu mai suna bacci, daya rufe idanunsa haulat yake gani, cikn dare d'aya gabadaya ya burkice...


Da misalin karfe takwas na safe aka sadata da gidan ta na gaskiya, ganin an rufe haulat da kasa ya sake daga masa hankali, take ya zube a Kasa yana kuka, duk gayu da kwalisar haulat yau babu shi, gata kwance cikin kabarin ta daga ita sai halin ta...


Wani imani da tsoron Allah ya shiga ratsa Jameel, nadamar munanan aiyukan sa ya fara yi sosai, ko bacci baya iyawa cikin dare, ji yayi duk wata k'yalek'yalar rayuwa ta daina burge shi, take ya soke contract din kisan daya so a yi wa su fadeel....


Ganin jameel ya yada makaman yakin sa ya hakura ya sanya shi ma minister ya zubar da komai cikin nadama, tabbas mutuwar Haulat ta daki jameel, minister da mummy'n sa kasancewar duk sunyi mata sani na sosai...


Jameel kuwa sai yanzu ya fara jin son haulat a ranshi, ya kuma yi nadama da bai karbi soyaayar ta da hannu biyu-biyu ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ba, sosai lokutan da sukayi having ya shiga dawo masa, nan ya hakura da Fadeelah ya kuma fadawa minister cewa ya hakura har abada...


***********************



THREE MONTHS LATER



Zuwa yanzu fadeel yasamu sauki sosai, yana iya taka kafar sa yanda yake so, da taimakon Allah da kulawar da Fadeelah take bashi, domin sosai tayi kokarin wurin bashi kulawa da kuma girka masa abinci masu Karin jini hadi da kara lafiya, tabon jiknsa kuwa saura kadan? domin akwai cream mai goge tabo da duk dare kafin su kwanta fadeelah take shafa masa....


Kamar yau sune zaune a falo, kallon ta yayi yace "wiffy Kin san ina nakeso muyi honey moon?"



Girgiza kai fadeelah tayi tana murmushi kasancewar yanzu ta saba da shi sosai duk da babu wani tarayya aure da ya shiga tsakanin su har yanzu, amma ta rage kunyar sa ba kamar da ba....


Kusa da kunnen ta yazo ya rada mata "suprise!"


Dariya tayi bayan ta saka masa dafaffen kwai cikin bakin sa tace "I like surprises"

"Really?" Yace yana dage girar sa.

"Yeah" ta amsa masa itama.

"Then tashi muje" ba musu ta mike... yace "ki zura hijab kawai kan kayan jikin ki, duk sauran abubuwan da zaki bukata akwai a can" dan karamin jaka kuwa ta saka musu wayoyi, charges, Bluetooth ta rufe zip din jakar suka fito, mota suka fada kamar kullum tare da rakiyar escort suka fita...


Abinda ya bawa Fadeelah mamaki shine Wa ta ga sun nufi unguwar su Fadeel na Wa, so take tayi magana domin ta tabbatar da unguwar ne, amma tayi Shiru... Tsayuwar motocin su a wani hada'dden gida Duplex daya tsaru sosai tamkar a turai ya katse mata tunanin ta...



Juyowa yayi gare ta, yace "Fadeelah kin tuna wanna gidan?"


Cikin sauri ta girgiza kai domin har ga Allah bata fahimta ba...

Kallon gidan yayi, ya hadiyi wani abu mara dadi yace "gidan da muka rayu da mahmah ne a ciki, na sanja ginin gidan ne, domin har abada bazan manta da gidan nan ba, haka kuma idan Allah ya azurta mu da '/y'ay'a zamu dinga zuwa nan muna kwana biyu, haka zai sa mu dinga tunawa da mahmah" ya karasa yana dora kan shi a kafadar ta...


Sosai tayi mamaki ganin mugun chanjin da gidan yayi, hakika duk abinda ya samu gyara komai lalacewar sa zai gyaru, a yau ta sake tabbatar da hakan, shafa kansa take itama tana jin kewar mahmah na ratsa zuciyar ta sosai, iya motar da suke ciki yayi horn, take mai gadi ya wangale musu gate ya Shigar da hancin motar ciki, bud'e musu mota akayi suka fito, kana driver ya juya ya fita, su kuma suka nufi cikin gidan hannunsu sarke dana juna....







Share fisabilillah



Comment


I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*


=?????AUTAR ?O?A=???



(It's all about love, scracifes, hatred and destiny)




Wattpad
@NoorEemaan



ELEGANT ONLINE WRITER'S=???=???

https://facebook.com/groups/943534712916776/masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.



EDITING IS NOT ALLOWEDL'



Page 73-74


Sosai cikin gidan ya burge fadeelah, madaidaicine, haka zalika ba tarkace cikin gidan da yawa, komai tsaf gwanin burgewa.






Babban bedroom din cikin dakin ya jata, nan ma taga komai ya hadu sosai gwanin sha'awa, jakar data rataya ta ajiye akan dressing mirror.




Bathroom ya ja ta suka yi wanka, kasancewar yanzu ta saba wanka tare dashi.



Bayan sun fito sun kimtsa sun saka kananun kaya, dama fadeelah ba Shiri take da manyan kaya ba. Farare kaya kal suka saka, Riga da wando, fadeelah ta saka head band shima white, tamkar turawa haka suka dawo gwanin kyau.



Da misalin karfe 6:40pm bayan sunyi sallar magriba ya ja ta zuwa kitchen... "Zauna ki tayani hira" ya fada yana ja mata kujera ta zauna.




Ba musu ta zauna kana tace "menene zaka yi" murmushi yayi yace "kazar amarci zan hada miki da kaina, kamar yadda kike na musamman, haka ya dace ki ci kaza na musamman, sam baki dace dana titi ko restaurant ba" ya fada yana kunna gas din.




Murmushin karfin hali fadeelah ta saki, amma tsoro ne fal zuciyar ta, musamman daya ambaci amarci.

Cikin karfin hali tace "ok bari na tayaka"

"No! bana son ki yi komai wiffy, ki zauna kawai ina kallon ki" ya fada yana bud'e madaidaicin fridge ya dauko mata lemo exotic da glass cup, zuba mata yayi ya mika mata, kana ya ja wani dogon stool ya dora exotic din a kai.




"Ko yanka albasa ka bari in maka" tace tana sipping juice din.





"A'a my Darling babu fa abinda zaki yi" ya fada yana cigaba da yankan albasar sa.




Murmushi tayi kawai, tana kallon yadda yake komai cikin kwarewa, kasa hakuri tayi tace "my one dama kana girki ne sosai? naga you re so perfect"




Murmushi yayi ya dan waiwayo yace "yeah! Ina taya Mahmah girki sosai, amma ba komai na iya dafawa ba, bari na baki labarin yadda nayi girkina na farko a duniya, lokacin Mahmah ta tafi unguwa" nan ya shiga bata labari...



Fadeelah har da kwalla Saboda dariya, sosai labarin ya bata nishadi, shima yaji dadi sosai ganin Fadeelah'n shi cikin farinciki wanda burinsa a kullum kenan.




Bayan awa biyu ya gama hada had'add'iyar kazar sa har biyu, sosai kamshi ya cika ko ina, a cikin wani babban tray ya jere su, har da garnishing yayi....




Wani wankan suka sake, suka yi sallar isha, kana ya sake jan su sallar raka'a biyu wanda ma'aurata kan yi a daren su na farko, dorawa yayi da yi mata masu tambayoyi daya shafi addini, sosai fadeelah ta bashi mamaki, Bai taba tunanin tayi zurfi a ilimin addini har haka ba, tunda kowa ya sani professor Imran mai naira dan boko ne! a yau ya sake tabbatar wa ita din daban take cikin y'ay'an wasu masu kudin.



Kanta ya dafa ya shiga karanto add'uar, a sanyaye kana a hankali take amsawa da AMEEN.




Bayan nan, ya mike ya dauko mata wata had'add'iyar white silky night gown da iyakacin sa bai karasa guiwa ba, da kan shi ya mikar da ita ya sanya Mata, tamkar mara la?a haka ta tsaya ta kasa motsi, bayan ya saka mata da Kanshi ya kama mata dogon gashin kanta, kana ya riko hannunta suka fice batare da ya saka kaya ba, illa farin towel daya d'aura a kugun shi....


Ta cikin kitchen ya bi da ita, sai gasu a wani corridor, wanna fadeelah ma bata san da hanya a wajen ba, sun danyi tafiya kadan, ya tsaya a wani kofa, tura kofar yayi sai gasu a wani hada'dden falon daya hadu matuka.


Kan wani lallausan center carpet ya zauna, kana ya ja ta tana daga tsaye ta fada kan cinyar sa, tray din dazu daya zuba kaza ya janyo gaban su, Fadeelah tayi mamakin yadda akayi tray din yazo har nan dakin bata sani ba, amma data tuna waye Fadeel dinta sai taga kadan daga aikin sa ne, dan karamin knife(wuka) ya dauka ya yanki kazar, "ahha" yace yana kai yankar kazar bakin ta, a sanyaye ta bud'e cute lips d'inta ya sanya mata.




Murmushi yasaki ganin yadda gabadaya ta tsorata, a fili ya ce "my Darling why the sudden change? Kina tsoro ne? You know your Fadeel is gentle, so trust me bazan yi hurting dinki ba, kinji" a hankali ta daga kanta alamun gamsuwa tana murmushi, Kumatun ta ya ja yace "fear fear girl kawai" dariyar da bata yi niyya ba ta saki ya cigaba da bata kazar, sai daya tabbatar ta koshi ya bata juice ta sha kadan, ta bukaci ruwa, wajen dispenser ya nufa ya siyaya mata ruwa ta sha, kana ya dawo ya ji kazar shima sosai ya kora da juice, gani tayi ta ya mike da tray din ya fita, da kallon kauna ta bishi tana sauke ajiyar zuciya.




Jim kadan ya dawo, in a romantic way ya dauke ta cak! Ya nufi wata kofar, ya ture da kafar sa suka shiga.


"close your eyes " yace yana dire ta kasa.



Rufe Idanunta tayi, bayan seconds goma yace "open your eyes" ba musu ta bud'e.


"Wow!" Ta furta ba tare da ta sani ba, oh Fadeel kullum cikin suprising dinta yake, sosai bedroom d'in ya hadu sosai wutar dakin sai sanja yake daga blue, red, zuwa yellow, hakan yasa dakin yin duhu ya kuma kara masa kyau, babban gadon kuwa da aka lailaye da bedsheet fari kal sai jajayen rose flower shimfud'e a gadon, anyi designing heartd'?da shi, daga kasan kuma aka rubuta I LOVE YOU FADEELAH .



Da wani india romantic music dake tashi a hankali cikin dakin, sosai dakin ya hadu wanda fasaltashi wasting of time ne.




Sosai taji dadin abinda ya mata, hakan yasa ta rungume shi ta ce "I love you too Fadeel, I love you zaujee"



Wani yanayi mai dadi ya shiga ratsa su, goshin su ya hade waje d'aya, follow by tip din dogon hancin su, sai labb'ansu daya hade da juna, wani a ajiyar zuciya Fadeel ya sauke, Yayinda ya kama tattausan labb'anta ya fara sha a hankali cikin nutsuwa, tun yana yi a hankali har ya dawo a zafaffe, sosai tsayuwa ta gagare su, hakan yasa suka zube a bakin gado, wani remote dake gefe yayi nasarar dauka ya kashe music din dake tashi, take wajen ya dauki Shiru sai fitar numfashin su dake tashi cikin sexual sounds.





Sosai fadeel yayi nisa sosai, ya shiga duniyar gajimare, baya ji baya gani, abinda ya saka a gaba yake yi, uwar tsoro kuwa ta sakar masa jiki, sai daya dauki wata hanyar ta dawo nutsuwar ta, Fadeel daya ce he will be extra gentle kuwa kasawa yayi, sosai ya fita a hayyacinsa.





_*4:40am*_

Manne yake da ita yana baccin sa cikin nutsuwa wanda bai taba jin dadin bacci irin na yau ba. A hankali ya fara jin kukan ta na tashi cikin dakin, kasancewar suna da kusunci sosai, a hankali ya bud'e idanunsa ya sauke kan fusk'ar ta dayayi jajur haka zalika labb'anta, Idanunta a rufe suke, Yayinda hawaye ke zuba a fuskar ta, sosai ta kara yi masa kyau, sai dai kukan ta da baya so, a hankali ya fito da harshen sa ya shiga lashe hawayen fuskar ta, kana ya shiga fada mata kalamai masu saka nutsuwa....




Luf tayi a jikin sa, amma still taki bud'e idanunta, jin ana kiran sallah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login