Showing 18001 words to 21000 words out of 80179 words

Chapter 7 - KYAUTAR KODA Hausa Novels by NoorEemaan.doc

11 Nov 2025

3034

suka nufi chemist aka yi treating ciwon kansa...


&&
Bangaren Daddy kuwa zaune yake yana kuka sosai, tamkar karamin yaro, bai taba tunanin akwai abinda kudi baya iya siya ba sai yau, domin duk mahaukatan kud'add'en sa basu yi masa rana ba, tunda ga yarsa na kwance a gadon asibiti cikin mayuwancin hali domin bata san wanda yake kanta ba, da taimako na'urori take numfashi.


Wani matashi ne ya fito daga wani daki, ya kalli Daddy cikin girmamawa yace " yallabai kana iya shigowa"
Mik'ewa yayi cikin sauri ya nufi dakin gabatar da shirye_shiryen, kasancewar yazo gidan TV ne.



Zaune yayi idanunsa na zub da kwalla yana fadin "a taimaka min, wani ya siyar wa 'yata da *kodarsa* ko daya ce, tana cikin matsanancin halin ciwo, banda wata 'yar sai ita, jama'a ku taimaka min, ku taimaka min, ku taimaka min dan Allah!!!" Ganin kuka yaci k'arfin sa, yasa aka katse daukan, hadi da watsa shi duniya... Domin bukatar Daddy kenan.

kudi masu zunzurutun yawa ya saka, daga million hamsin, zuwa ko nawa mutumin ke so ya fada zai bayar, ko da duka dukiyar sa ne zai bayar.
Su kansu yan gidan TV sun zub da hawayen tausayin sa, domin duk fadin lagos kowa yasan tarin dukiyar *professor Imran mai naira* sannan an sa izzar sa hadi da jin kansa, amma yau shi da kansa yazo gidan TV neman taimako.

Abin da matuk'ar mamakin ba shakka son da yake yiwa yarsa mai yawan gaske ne.




Sosai aka watsa daddy duniya har wasu gidajen Tv da radio, gari ya dauka ko ina maganar ake, sai dai har bayan kwana biyar ba'a samu wanda ya zo da niyyar zai siyar da kodar sa ba.

Wanna kenan.





*** *** ***


Yau kwanan Mahmah biyar a kwance jikin ya matsa mata sosai, domin har tashi bata iya yi, Fadeel ya dawo tamk'ar wani zararre, uwar sa mafi soyuwa agareshi na Cikin wani hali, ga Fadeelah'nsa a gadon asibiti, sosai yayi rama, domin baya iya cin komai, haka zalika Mahmah sai abu mai ruwa take iya kai baki, shima da kyar take hadiya...

da daddare ta dan samu sauki har ta dan yi hira da Fadeel, ya kuma ji dadi domin tunda ta kwanta bata iya magana. Sai dai wasu maganganun da take yi, mai kama da wasiyya, sai dai sam bai kowa komai a ransa ba.


"Mahmah please ki bari na kai ki asibiti, zan fita ko ina ne domin neman kudi"


Murmushi mai ciwo tayi, ita a jikinta tana jin lokacin mutuwar ta yazo, cutar dake damunta yayi mugun cin karfinta, domin yazo gabar da ba za a iya yin komai akai ba. Toh meye amfanin zuwa asibiti???



A fili tace "my son Fadeel, kada ka damu sannan bana so ka fita nema saboda ka kai ni asibiti, babu bukatar hakan, ina maka so mai tarin yawa dana farincikina. Allah ya dauwamar da farincikin a rayuwar ku, kai da 'yata Fadeelah, I love you son" ta kai karshen maganar cikin murmushi irin na marasa lafiya.




Wasu hawaye ne suka zubo masa, duk da ba a cikin nutsuwar sa yake ba, amma yaji kalaman ta har Cikin kashin sa, ya ma kasa magana sai sumbatar hannunta hadi da goshinta da yayi, itama kuma ta daga hannunta ta shafa tarin sumbar sa d'aya kara yawa hadi da hargitsewa saboda gyaran da baya samu...


Ta kara cewa
"ka bani labarin soyaayyar ka kai da 'yata"

Duk da baya cikin farinciki amma sai daya yi murmushi daya taho da zubar hawayen sa, Kamar yadda ta bukata, ya fara bata labari so da tarin kaunar da yake mata, hadi da labarin irin soyaayyar da suka gudanar.

Kallonsa Mahmah take tana murmushi, har ranta soyaayyar fadeel dinta da Fadeelah na burgeta, tana musu fatan Alkhairi a rayuwa...



*** *** *** ***



Washegari har tara na safe fadeel yaga Mahmah bata tashi ba, domin da asuba bayan ya d'ora Mata alwala tayi sallah, tace zata yi bacci ya taimaka mata ta kwanta.

Kunu daya dama mata ya nufi dakinta da niyyar tashinta ta sha.




Gabanta ya tsugunna ya kira sunan ta shiru, "Mahmah!!!" Ya sake kira a karo na uku nan ma shiru. Ga dai fuskar ta d'auke da murmushi Kamar ka kirata ta amsa.

Hannunta ya rike, take yaga ta saki, gaban sa ya fadi, sake rike dayan hannun yayi yaga ta kuma saki, hannunsa ya d'ora a k'irjinta yaga bata bugawa.

"_innalillahi wa innah ilaihi raju'un, mahmah!!!_" yace cikin karaji yana jijjjiga ta, sai dai shiru bata ko motsa ba, sam k'wak'walwa hadi da zuciyar sa taki yarda da abinda take gaya masa, hakan yasa shi daukar ta zuwa asibiti domin a duba ta.



Cikin tashin hankali ya shigo asibitin, Mahmah dauke a kafadar sa yana kuka sosai, daidai lokacin doctor Gabriel ke k'ok'arin shiga motar sa domin aikin dare yayi jiya yana son tafiya gida, kallon daya yayi wa fadeel, take yaga Mahmah a kafadar sa, gabansa ne ya fadi, fasa shiga motar yayi ya nufi wajen Fadeel kana ya kwala wa wasu nurses kira, aka dora Mahmah cikin gadon nan na asibiti aka turo ta cikin sauri zuwa emergency...





Hannu Fadeel doctor Gabriel ya kamo zuwa office d'insa yace ya zauna yana zuwa,
Kana Cikin sauri doctor Gabriel ya nufi dakin da aka shigar da Mahmah...
Nan ya shiga dubata cikin kwarewa, sai dai ina rai yayi halin sa, Mahmah is gone forever, Mahmah ta tafi, tafiya ta har abada.

_kullin nafsin za'ikatul maut_ (dukkan mai rai sai ya dandani zafin mutuwa) domin babu alamun numfashi a tare da ita.



Kansa ya dafa, yace "Jesus Christ! is innocent woman is dead!!!" Sosai kuwa yaji mutuwar ta, duk da kasancewar sa ba Musulmi ba, amma yaji wani tsoran Allah na shigar sa.



A sanyaye ya koma office d'insa ya tarar da Fadeel zaune abin tausayi, zama yayi yana kallon Fadeel cikin tausayawa, duk da bai taba ganin sa ba sai yau, amma suna yanayin kama da Mahmah ya aiyana aransa afili kuwa hannu Fadeel ya riko yace "my friend sai haku'ri domin...."
Ai kafin ya karasa Fadeel ya katse shi da cewa "don't tell that my Mahmah is dead doctor, because I will squeeze your Bone's like an Orange (kada ka kuskura kace Mahmah nah ta mutu, domin zan ma_matse kasusuwanka tamkar na lemon bawo" Fadeel yace cikin fitar hayyaci kana cikin kuka har wani shidewa yake.


Girgiza kai doctor yayi cikin tausayawa yace "the truth is that..." sai ya dan shiru kana ya cigaba "your mother is dead!"



Afirgice Fadeel ya mik'e yana kokarin furta wata kalma, amma ina sai ya tafi luuuuuuu sakamakon wani irin jiri daya debe shi, take ya fadi tsumamme....


Cikin wani sabon tashin hankali doctor ya dauke shi zuwa emergency aka fara bashi taimako gaggawa...


Bayan yayi masa komai harda alluran bacci sai da ya nufi office din doctor Mahfouz, sai dai sam baya nan.
Fita ya sake yi ya nufi dakin da aka kwantar da Fadeelah, gaba d'aya ta sake fita kamanin ta, maganar Daddy yaji yana cewa cikin kuka "doctor tayaya zaka ce idan ba a samu *koda* nan da minti talatin ba zan rasa 'yata, bazan juri kallon 'yata ta mutu ba, ka cire duka nawa kodar ka sa mata, banda wata 'ya sai ita Mahfouz!"

"Professor sai hakuri fa, kalli abinda na'uran ke fada, nayi iya k'ok'ari na..." Suna cikin wanna halin, kirjin Fadeelah ya fara sama da kasa har wani jijjiga gadon yake. Yayinda na'uran ya tsawaita kara...


Cikin saurayi doctor Gabriel dake tsaye yace "an samu kodar, a shirya shiga da ita aiki yanzu"


Gaba daya suka juyo gare shi, take murmushi ya wad'atu kan fuskokinsu, tsabanin dazu da wasu ke kuka wasu na cikin damuwa, domin Mommah har bata iya bud'e idanun ta saboda zafi ".



Wani kallo da doctor Gabriel yayi wa doctor Mahfouz take ya fuskanci Mahmah ta mutu, duk da yaji dadi Fadeelah zata rayu, amma yaji mutuwar Mahmah matuka.


Babu bata lokaci aka shigar da Fadeelah aiki, cikin gaggawa domin mintunan daya rage mata sauran kadan.


Bangaren doctor Gabriel kuwa, bayan an cire kodar Mahmah, ya nemo wasu dattijai mata da maza wadanda suka yi zurfi a ilimin addini, suka nufi gidan Mahmah, yayinda gawar mahmah ke cikin ambulance din asibitin.
Domin ayi mata wanka, duk da kasancewar shi ba muslumi ba amma, yasan duk wani muslumi idan ya mutu ba a son ajiye shi, an fi so ayi gaggawar kai shi gidan sa na gaskiya. Wanna kadai zai iya yiwa Mahmah, tunda danta yana gadon asibiti a kwance.

Kasancewar lokacin da Mahmah ke zuwa asibiti, adreshin gidan ta na rubuce a file dinta hakan yasa bai sha wahalar gano gidan ba.


Babu bata lokaci aka shigar da ita ciki, take yan unguwar suka fara shiga gidan musamman da suka ji jiniyar motar asibiti.

Bayan anyi wa Mahmah wanka an shirya ta cikin li??afani kana aka fito da ita hadi da yi mata sallah, duka doctor Gabriel na cikin motar sa, wani tsoron Allah na shigar sa, yayinda hirar da suka yi da Mahmah ya shiga dawo masa a fili ya furta " hakika madam kinyi Sadaukarwa mai girman gaske". Sai ga Hawaye a idanun sa.


Bayan an dawo daga kai ta mutanen da suka hallaci jana'izar ta suna da yawan gaske, sai dai fatan mu ce Allah ya jikan ta.

Doctor Gabriel ya bawa dattijan nan daya samo kudi masu yawa, suka ki karba, domin suma imani da tsoron Allah ya kara shigar su.

Amma mamakin take yaji addinin musulunci ya burge shi sosai.
Inda mutanen ke zaman makokin ya nufa, take yace yana son shiga musulunci, kabbara mutanen wurin suka sa, yayinda limamun unguwar tasu ya musuluntar da doctor Gabriel, aka ce wani suna yake so a sanja masa take yace *Aleeyu haidar* domin a sunan muslimai yana kaunar sunan sosai...


Take doctor Gabriel yaji kamar an yaye masa wani zunzurutun nauyi akansa, wani yanayi mai dadi kana marar mitsaltuwa na shigar sa, nan liman ya kara wayar da kan shi game da addini musulunci ya kuma ce masa dole ya nemi islamiyya na manya domin ya kara sanin menene addini musulunci. Take ya amsa da in sha Allah domin ko liman bai fada ba, yana da niyyar hakan, domin shi mutum ne mai riko da addini, ko da a lokacin da yake cikin addinin su na kirista ne(Christian), haka zalika yanzu ma daya shiga addinin muslunci, addini mai haske, zai dage da ibada.



Haka yayi sallama dasu ya tafi cikin yanayi mai dadi da yake jin kansa a ciki, duk da murnan sa ragagge ne, saboda mutuwar Mahmah.


Asibiti ya koma domin yana son kula da Fadeel, hakika bai cancanci a bar shi ba kowa tare da shi ba...



*_(Kusani cewa, a rayuwa wani kaddara baya samuwa sai da wata kaddaran, toh hakan ke faruwa a novel din kyautar koda ku dai cigaba da bin alkalamina...)_*




_Yau nayi typing mai yawa, billahi banga comment dinku na k'ok'arin tarwatsa waya ta ba, zan dauki hutu=?9? ina jiran ra'ayinku akan page din yau, Mahmah is dead_.=?+?





#share
#comment
#vote



Noor Eemaan loves you all my beautiful fans

'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*


#Nurrr


=?????AUTAR ?O?A=???
(it's all about love, scracife, hatred and destiny)


Story/written by
NoorEemaan
07082281566




https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.


*Wattpad*
@NoorEemaan


ELEGANT ONLINE WRITER'S=???
'?




EDITING IS NOT ALLOWEDL'


*(Assalama alaykum my lovely fans, nasan wasun ku baku ji dadi da Mahmah ta mutu ba, domin wasu sun gaya min, wasu ma sun ce sai da suka zub da hawaye, ni Noor a lokacin da nake typing wajen sai dana yi kuka domin wajen is very heart touching I know. Amma littafi na riga ma tsara shi, rubutuwa ya rage min kawai, domin haka labarin yake, soyayya ce, sadaukarwa, tsana/kiyayye hadi da kaddara. A rayuwa ba a taba samun farinciki kullum, haka ke faruwa a *kyautar koda*.
*Da sannu zaku fahimci darassin dake cikin labarin, ina godiya sosai da add'uar ku gareni hadi da comments dinku masu sugar*=?9?
*Allah ya bar kauna da zumunci*)
Noor Eemaan loves you alld'?



Page 25-26

(Not edited)

Kwanan Fadeel hudu a gadon asibiti ya farka da sunan Mahmah Wau?e a bakinsa, yayinda idanunsa ke a rufe.


doctor Aleeyu(Gabriel) dake tsaye yana kokarin cire masa karin ruwa yayi saurin dawowa gaban gadon yana fadin "sannu ka tashi?"


A hankali fara bud'e idanunsa, saurin mayarwa yayi ya rufe sakamakon wani haske d'aya cika idanun sa... Ya d'auki mintuna goma kana ya fara ware idanun sa a hankali ya sauke su kan doctor Aleeyu...


Take k'wak'walwarsa ta tariyo masa komai, wani ihu ya saki kana ya fara buga kansa da karfen gadon yana fadin "Mahmah don't do this to me, please Mahmah ki dawo gareni, banda kawo sai ke, ki dawo please, doctor kace Mahmah na ta dawo gareniiiiiiiii" ya ja Kalmar karshen gwanin tausayi.


Cikin sauri doctor Aleeyu ya rike shi hadi rungume shi yana bubbuga bayansa alamun rarrashi...
"Shikenan Mahmah ta mutu, shikenan Mahmah ta mutu, shikenan bani da uwa a duniya likita? "

Haka ya dinga maimaitawa yana kuka sosai gwanin tausayi. Doctor ya dauki tsawon lokaci yana rarrashin Fadeel kana yace masa ya yi sallah dake kansa domin yau kwanan sa hudu a kwance.




Ba musu ya miki, sai dai ya kasa tsayuwa kan kafafunsa Saboda rashin kwarin jiki hakan yasa doctor Aleeyu taimaka masa har zuwa toilet.

Bayan duk ya iddar da sallar dake kanshi ya shiga yiwa mahaifiyar sa add'ua, yana kuka sosai, shima doctor Aleeyu sai ya kama kuka domin duk wanda ya kalli Fadeel dole ya tausaya masa.

Hankici(handkerchief) doctor Aleeyu yasa ya share hawayen fuskar sa, kana a fili yace "abokina kayi hakuri, tabbas mutuwa na da daci musamman ga wanda aka yi wa, nima da kake ganina banda uwa banda uba a duniya, duk sun mutu kuma a rana d'aya sak'amak'on hatsarin da suka yi. Hakika ban taba ganin mutum mai kyawun zuciya hadi da tawakkali da yarda da kaddara Kamar mahaifiyar ka ba, hakan ya janyo hankalina na shiga musulunci a ranar da ta rasu..."

Fadeel ya dago jajayen idanunsa ya kalli doctor Aleeyu, jinjina masa kai doctor'n yayi alamun "Haka ne"

tabbas idan yace bai ji dadin cewa wani ya shiga musulunci ta silar Mahmah ba yayi karya, sai dai bazai iya nuna jin dadin sa a fili ba Saboda matsanancin damuwar da yake ciki



A hankali ya budi baki yace "dan girman Allah doctor ka gaya min wani irin cuta ke damun Mahmah tsawon shekarun nan bata taba gayamin ba" Fadeel ya kai karshe yana sauke wasu tagwayen ajiyar zuciya gwanin tausayi.



Furzar da iska doctor yayi daga bakinsa kana yace " hakika mahaifiyar ka bata son ka san da cutar ta , kuma duka Saboda kada hankalin ka ya tashi ta boye maka, a yanzu dai babu bukatar boye maka"

Numfashi ya sauke kana ya cigaba "mahaifiyar ka na dauke da *cutar daji ta makwogwaro* (lung's cancer) tsahon shekaru kenan, a lokacin data fara zuwa asibitin nan cutar ya fara cin karfin ta. Sai dai ba kudin yi mata aiki a lokacin domin kudin aikin ya kai million biyu da rabi. Rashin kudin aiki yasa cutar ta ci karfin ta sosai......" nan dai ya cigaba da bawa Fadeel labarin abinda ya sani gami da cutar Mahmah, hadi da Sadaukar da *kodar ta* da ta yi.




Babu Abinda ke fita a idanun Fadeel sai hawaye masu zafin gaske, dama haka mahaifiyar sa ta sha wahalar rayuwa? Haka ta boye masa ciwo duk don farincikin sa? Ta Sadaukar da kodar ta just because ya zama cikin farinciki, ya rayu da abar son sa fadeelah.

Kuka ya ci sosai, har ya fara ganin biyu_biyu sakamakon wani mugun ciwon kai da ya saukar masa, jajaye kuma kumburarrun idanun sa ya dago ya kalli doctor yace "please wani kabari aka binne Mahmah na? Ina son zuwa, ina son yi mata add'ua, ina son zuwa please doctor!!!!" Ya kai karshe cikin wani kukan daya ci karfin sa.



Wasu hawaye doctor Aleeyu ya share na zallan tausayin Fadeel. Cikin dauriya yace " a gaskiya bansan wani makabarta bane, kasancewar lokacin ban karbi musulunci ba, hakan yasa ban bisu ba, amma bari na kira wani a nan asibiti yake aiki tare suka je" ya fada yana kara wayar sa a kunne.....



Babu jimawa matashin yaron yazo, ya fadi sunan makabartan da unguwar da yake, ya kuma ce zai iya raka Fadeel d'in.

Da kyar fadeel ya budi baki yace "nagode zan iya zuwa da kaina"


Ba musu matashin ya koma bakin aikinsa, Mikewa Fadeel yayi da kyar yace "thank you doctor for everything" kana yana hada hanya, haka ya fita daga asibitin a haukace.... Doctor Aleeyu (Gabriel) nayi masa magana kan cewa zan iya tafiya kuwa? amma ina yayi nisa bazai ji kira ba....




Tafiya yake cikin makabartan tamkar wanda yake kirga kasa dake shimfud'e a kasan wajen, hawaye ke zuba a idanunsa, wani tsoron Allah hadi da imani na kara shigar sa, wanda ya sanya kofofin gargasan jikinsa bu-budewa yanayin daya sanya wani sanyi sanyi ke shiga jikinsa. Aransa yake aiyana cewa shima wata rana haka zai kasance anan, haka zai tafi, tafiya ta har abada, kamar yadda Mahmah ta tafi ta barshi.





Tun daga nesa ya hango signboard mai d'auke da sunan Mahmah. Gaban kabarin ya tsugunna, wanda aka mulmule da siminti dake da sauran sabonta har yanzu, domin duk wanda ya gani zai san cewa mamacin bai dade ba.

Wani kuka ne ya taho masa mai karfin gaske daya kasa rike shi, sosai yake kukan mai taba zuciya, kana ya rarrashi kansa tuna cewa ba a son ayi wa mamaci kuka.

A fili ya fara furta cewa "Mahmah you re gone, gone forever, kin tafi kin barni, ki tafi kin barni a wanna duniya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login