Showing 48001 words to 51000 words out of 80179 words

Chapter 17 - KYAUTAR KODA Hausa Novels by NoorEemaan.doc

11 Nov 2025

3045

magana yanzu bata son yi, amma tana kokari matuka wurin boye damuwar ta tunda yanzu gida ya cika da jama'a...


Wanna kenan.





*******. ********. *******.




TWO WEEKS LATER





*RANAR DAURIN AURE*


Zaune take a dakin Mommah, tana sanye da wata tsadaddiyar material wanda fadin kudin sa bata lokaci ne, a yau shine karo na farko data fara saka manyan kaya (in kun tuna shigar Fadeelah english wears ne, amma ba matsatsu ba) wanda yayi mata kyau ainun, duk da cewa tayi rama sosai saboda damuwa da fargaba da take kwana take tashi dashi, amma hakan bai boye kyawunta ba.



Light makeup ne a fuskar ta, kana hannu Wa kafar ta ya sha jan Kunshi wanda duka sai da taga bacin ran Mommah sannan ta yarda aka yi mata su.



Tunda aka fara event din bata ko saka ango nata a ido ba, domin an sanar cewa baya kasar, sai daurin aure da zai hallata, duk inda ka shiga labarin bikin da event din ake Saboda uSan dukiyar da aka narka wurin gabatar da kala- kalan event din.
Wanda kaf ba a taba irin bikin ba a fadin Nigeria, abinda mutanen ke ta fada kenan.





Babu abinda take ji sai faduwar gaba mai tsanani, domin ta san cewa ta rasa masoyinta Fadeel har Abadan kenan, hak'ik'a basu cikawa Mahmah burinta ta ba. Take wasu hawayen masu zafin gaske suka zubo mata.




Babu jimawa yan daurin aure suka fara dawowa, inda aka d'aura auren akan sadaki naira na gugan naira har million bi?ar, sosai gidan ya cika Wa hayaniya, saboda yalwar jama'a.

A hankali ta mike ta zuge labulen Mommah, nan ta hango tarin jama'a da ba za su fadu ba cikin shigar fararen kaya...





Ganin hayaniyan jama'a sun fara yawa a part din Mommah, hakan yasa ta bi ta kofar baya ta koma part din ta, domin wani mugun ciwon kai ke barazanar tarwatsa kanta.




Tsaye yake tare da alhaji Sufyan Rufa'i cikin shigar tsadaddiyar shadda fari kal Yayi dinkin babban riga. agogo, takalmi, hula, duka mai tsadar gaske ne, babu abinda ke tashi a jikin sa sai k'amshi, sosai yayi kyau mai tarin yawa ya kuma fito sa? a angon sa....



Cikin marairaicewa yace "Alhajina I want to see her, kaji yanda k'irjina ki dukawa Saboda da ita"




Murmushi alhaji Sufyan Rufa'i yayi, fuskar sa fes cikin annushuwa domin ya cika masa alkawari, kamar ?aWWa ?ayi wurin taimakon sa Womin mallakar muradin ransa, yanzu duk abinda zai biyo baya a shirye suke...





Hannu sa ya kamo yace "for sure zaka je gareta, domin ita din taka ce yanzu, mallakin ka ce, Allah ya baku zaman lafiya mai dorewa, ina tayaka murna sosai, mu ma anjima zamu koma abuja in Sha Allah"


Rungume alhajin yayi yana jin kwallan farincikin ya cika idanunsa, sai dai sam bai basu damar zubowa ba, Saboda tarin jama'a dake wurin ...




A hankali ya motsa labb'ansa yace "Alhajina Kalmar godiya tayi kadan in yi amfani da shi wurin gode maka, domin kaine silan wanna farincikin nawa na yau..."




"Shhhhh! Ka cancanci haka, babu godiya a tsakanin mu, maza je ka gareta kaji" alhajin ya fada yana raba jikinsa da nasa.




Wani security daya zo gifta wa alhaji ya kira shi yace "ina ne part din amarya?"





Sanin cewa saurayin dake gefen alhajin shine mijin ma'am din su, hakan yasa cike da girmamawa yace "muje zan nuna masa yallabai"




Jinjina kai alhajin Yayi, ya kalli dan nasa yace "all the best the young billionaire ku je"



Murmushi saurayin ya sakar wa alhajin kana suka tafi da security'n. Suna zuwa daidai kofar da zai sada mutum da part din Fadeelah'n security ya tsaya cikin girmamawa yace
" nan ne kofar shiga part din ta"




Murmushi wanna saurayin ya sakar wa security kana ya murda kofar ya shige.....



Kwance fadeelah take tayi rub ta ciki tana kuka sosai, Idanunta sai yaji suke mata Saboda tsananin kuka ga uban kumburin da suka yi, kuka ta?e tana surutu cikin fitar hayyaci, ga jikin ta daya dauki zafi da alama zazzzabi na shirin saukar mata...



Cikin nutsuwa ya murda kofar bedroom din ya shiga, lumshe idanun sa yayi sak'amak'on dad'add'an k'amshi turaren ta daya kama dakin, kana ya ware idanun sa da suka sanja launi zuwa ja a kanta...




Wani abu tamkar mashi ya soke masa k'irjin sa sakamakon jin kukan ta, da alama bata ma san ya shigo dakin ba...



Ya jima yana kallon ta, ba tare da ya iya furta wata kalma ba, ganin bata daina kukan ba ya sanya shi ware kyawawan labb'ansa ya furta


"my darling Fadeeeeeeeeeelerh"



Cak! Kukan ta ya dauke sakamakon jin muryar da ko a wani hali take zata gane, sai dai sam bata yarda shi din bane, tafi yarda cewa gizon da kunnewan ta suka saba yi mata ne.




Cigaba tayi da rera kukan ta, wani murmushi daya taho da hawaye ya saki kana ya kara cewa



"Fadeeeeeeeeeelerh! It's me your Fadeel"



Wata zabura tayi ta sauko daga kan gadon kasancewar ta bawa kofar baya ne Wama, waro ido tayi cikin mamaki.... Shin da gaske fadeel abin kaunar ta ne ke tsaye a gabanta ko a'a? Shin ba gizo ko mafarki data saba yi bane?
Murza idanun ta tayi da dukkanin hannun ta, still yana tsaye a gabanta, hawaye da murmushi dauke a fuskar sa...




Ganin kamar tana tamtama ya sa shi ?ara cewa "my Darling nine! your Fadeel da gaske ni ne a gabanki" Fadeel ya fada yana ware mata hannuwan sa, kana ya kare maganar cikin muryar sa da amon sa ke fidda aji, so, kauna, kewa, hadi da matsanancin tausayin ta.



"Fadeeeeeeeeeeeeeeeeel"

tace cikin zunzurutun mamaki hadi da zallan farinciki kana ta buga tsalle ta rungume shi, a karon far?o tun da suka fara so?aa??a, ta fashe da kuka sosai harWa sheshe?a...


Cikin wani zafin nama ya taro ta, domin da ba dan yayi namijin kokari ba, da sun zube a kasa domin babu kwari a jikin sa, Saboda da dukkanin k'arfin ta ta rungume shi.




Hugging dinta so tight shi ma yayi, ya kasa controlling hawayen dake zuba a idanunsa, yalwataccen gashinta Wa ya rufe fuskar ta ya mayar baya, kana ya dora lips d'insa cikin kunnen ta yace......








*Team fadeel and Fadeelah, Fadeel is back! I know you guys are happy, dan haka ina son jin ra'ayinku akan page din yau*




Shin Ta yaya Fadeel yayi arziki?


Daddy zai amince Wa auren kuwa idan ya san cewa Fadeel daya dauka dan alhaji Sufyan Rufa'i ne, ba kowa bane face wanna talaka fakirin daya raina?



Sannan Jameel zai hakura kuwa?


?a ?a Mommah zata ji, idan ta san cewa Fadeel din fadeelah'n ta ne angon? Da dai sauran su....





Muje zuwa fans=??






Thank you for reading my Novel *Kyautar koda*



NoorEemaan ce
07082281566



#Share fisabilillah


#Comment


#Vote




show me love=?
?
please vote and follow me on wattpad @NoorEemaan



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*

=?????AUTAR ?O?A=???
(it's all about love, scarife, hatred, and destiny)



*WATTPAD*
@NoorEemaan




ELEGANT ONLINE WRITER'S=???=???




EDITING IS NOT ALLOWEDL'


https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.




Page 51-52

"Shhhhhhhhhhhh! It's okay, my Darling stop crying, am so sorry ok?"



Kara k'ank'ame shi tayi tamkar zata shige cikinsa, ta kasa yarda cewa Fadeel din ta ne, ta kasa yarda cewa shine tsaye a gabanta tana rungume dashi a karon farko, ta kasa yarda cewa a lokacin data fidda tsamanin ganin sa, amma finally ta ganshi, a lokacin da hakan bai da amfani, a lokacin da ta zama matar wani, ta sani cewa a lokacin da ma bata yi aure ba, Daddy bai amince dashi ba, bare yanzu da aka d'aura Mata aure, Ga samu ga rashi, ta ai?ana a ranta...


Tuno hakan ne yasa gabanta faduwa sosai, kara k'amk'ame shi tayi sosai, duk da tasan cewa haramun ne rungume shi data yi, musamman yanzu da take da aure, amma bata da zabi daya wuje tayi hakan, domin ba k'aramin kewar sa ke dawainiyya da ita ba, kana tana jin farinciki sosai hadi da sanyi a ranta a sak'amak'on ganin sa Wa ta yi, sai dai murnan ta ragagge ne domin yanzu ta zama matar wani, wanin ma da bata sani ba.


Tuno hakan da ta sa?e yi ne yasa ta ture shi da k'arfi, ta zube kasa tana kuka....



Taga-taga yayi kamar zai fadi, kana ya ja tunga ?a tsaya, domin da dukkanin k'arfin ta ta ture shi, ga ba kwari a jikin sa, cikin mamaki yake binta da kallo, miyesa ta sanja all of a sudden?



Sosai hawaye ke zuba a Idanunta, numfashin ta har wani seizing yake Saboda uban kukan take "go, go, go away, bana son ganin ka, so kake in mutum dama, shi?asa ?a zo ?anzu, idan na mutu ?a huta, domin banga amfanin rayuwa babu muradina a tare Dani ba, ashe kana da zuciya da zaka iya rabu da ni tsawon lokaci haka? Baka san halin da zan shiga ba, ka tafi without even a second thought, ka Wawo a lokacin da nake bukatar ka, amma zuwan ka babu abinda zai tsinana min, banda damuwa da zaka kara min, domin ni matar aure ce yanzu, an d'aura min aure da waniiiiiiiiiiii" ta karasa tana kuka sosai har wani buga hannunta take a kasan tiles....



Tsad'add'en murmushin sa ya saki, duk da kalaman ta sun taba shi matuka, ya ?uma tausa?a mata, amma kalaman ta na karshe ya yi sanadin wanna murmushi nasa.




A hankali kana cikin takunsa mai ban sha'awa ya iso gaban ta ya tsaya, a hankali ya tsugunna gaban ta, hannayenta ya riko, ta kwace, da karfi ya sake riko hanna?en ta wanna karon, sak'amak'on ha?an ya sa ta kasa kwacewa, "look at me" ya fada yana kokarin sanya Idanunsa cikin nata...




Shiru tayi masa tana cigaba da kukan, ba zato taji ya rungumeta da kyar, tana zillewa, dukan bayansa take tana cewa ya sake ta, Yayinda har yanzu kukan take...



"Shhhhh! Ki daina dukan mijin ki, SaSu kyau fa"



Cak! ?ukan ta ya dauke jin Kalmar *MIJIN* daya ambata...



Cikin sauri ta dago tace "miji? Yana ina" ta fada tana kallon dakin, ko zata ga mijin.



Dariya ta bashi, hakan yasa shi sakin murmushi yana cewa
"look at me! nine mijin ki, ni zaki kalla"


Waro ido tayi, cikin rashin yarda tace " ni San ?arWa Sa, ka sa?e ni, ta yaya hakan ta faru?"



"Zaki ji komai Darling, tafiyar mai tsawo ce, haka ma labarin, ina so ki yarda dani ki bani nutsuwar ki, you know fadeel dinki bai taba miki Karya ba ko?"



Wata nutsuwa hadi da farinciki ke ratsa sassan jikinta, cikin sauri ta daga masa kai alamun


"eh"


Kara kamkame ta yayi a jikinsa, haka ita ma, tagwayen ajiyar zuciya ya sauke kana yace....



*WAIWAYE ADON TAFIYA*

(Yanda akayi fadeel yayi arziki)



Cikin kunnen Fadeelah ya dora bakin sa, kana ya fara bata labari kamar haka...




"A lokacin dana bar estate Win nan, ban zame ko ina ba sai gida, cikin tashin hankali da bazai mitsaltu ba.



Fadeelah I cried! Nayi kuka da ban san tsawon kwanakin dana dauka ina yi ba.


kalamai marasa dadi da Daddy yayi min ke ta amsa kuwa a kunnewa na, San taSa damuwa da talaucina ba sai ranar.




Sosai hankalina ya tashi, na fara tunani ta yadda zan samu arziki domin in cika mana burin mu, sannan in cikawa Mahmah alkawarin ta, sannan sunan bakin talaka fakiri ya kau....."


Kuka fadeelah ta saka daya fadi kalaman karshen nan, dago ta Yayi, ya kura wa hawayen dake zuba daga Idanunta ido, cikin damuwa yace

" idan kuka zaki yi, toh bazan cigaba da baki labarin ba"

Dif kukan nata ya dauke, rungume shi tayi, tana fadin "na daina" cikin muryar kuka.



"Kwana na hudu a daki, ban san ina kaina yake Sa, even ruwa bana iya hadiya Saboda tsananin dacin da yake min, a kwana na biyar na fita da kyar duk da uban jirin dake diba na, garin lagos ya min zafi sosai, tunanin yin nesa da garin nayi, ko zan samu abin yi domin Daddy ya bani auren ki, cikin k'arfin guiwar hakan na fice daga gidan, bayan na rubuta wasika na soka jikin kwado Saboda nasan zaki zo duba ni idan kika jini Shiru kwana biyu, sai....."




Katse shi tayi da cewa "meyasa baka kira ni ka fadamin ba, kasan halin ciwon dana kasance a ciki my one?"




Tsad'add'en murmushin sa mai cike da aji yayi mata, kana yace "I know cewa kin kasance cikin mayuwancin hali, like wise nima, ranar dana zo gidan ku wayar dama chajin sauran kadan, so a daran ranar ma ta mutu, Saboda halin matsanancin damuwar da nake ciki ya sanya ko tunanin wayar bai zo min ba, balle na kai caji"





Jinjina kai fadeelah tayi cikin gamsuwa.

Gyaran murya yayi, domin bayan lokuta masu tsayi, sai yau yayi magana mai yawa.




"Ban san ina nake jefa kafana Sa, kawai tafiya nake cikin fitar hayyaci da kuma rashin gwarin jiki, nayi tafiya mai nisa sosai, kana na fara jin horn na motoci a bayana, sai dai halin fitar hayyaci da nake ciki ya hanani motsawa, nama rasa ta ina zan bi in kauce, abu na karshe dana ji, shine buge ni da mota tayi kana sallatin jama'a daga nan ban kara sanin inda kaina yake ba.....





Wata na daya a asibiti, kana na bud'e idanuna, na ganni daure da na'urori hadi da Oxygen domin taimaka min wurin numfashi, hakan ya tabbatar min da a asibiti nake, abu na farko da idona ya fara sauka a kan shi shine wani mutum tare da matar sa, fusk'arsu dauke da alamun damuwa...



Kokarin cire Oxygen din nake, mutumin ya lura, cikin sauri suka yi kaina suna murmushi, domin watana daya cur bana motsi, hakan yasa su farinciki yanzu.



"sannu! Sannu!! Yaro" suka fada a tare, kana alhajin ya cire hannun na daga kan oxygen din.




Wasu mutanen masu sanye da suits tsaye da alama escort d'in wanna mutum ne. Daya daga ciki ya danna wani madanni dake manne a bango, hakan ya bada kara, kasa da mintuna biyar wani doctor da nurse suka shigo fusk'ar su dauke da murmushi, cire min Oxygen din doctor yayi, hadi da na'urorin dake jikina, kana ya hada wasu allurai ya min.
Nan naji doctor yana fadawa wanna mutumin cewa idan na farka daga baccin alluran nan da suka min komai zai yi normal, sannan yace wai ina karfi, Allah ya nufa ina sauran kwanaki a duniya, domin mutane da suke k'asancewa cikin irin wanna halin nawa suna jimawa a kwance, wasu ma suna mutuwa iWan ?wana ?a ?are......




Ban Kara jin cigaban maganganun sa ba, sak'amak'on baccin da yayi gaba dani.

Sai Sa?an awanin biyar na tashi, na tsinci mutumin nan yana fadawa matar dake kusa dashi wanda bana tamtama matar sa ce cewa ya saka gasa (competition) na manyan masu Zane na duniya domin a zana masa katafaran company dazai gina, domin so yake ginin ya zama special, sannan ya saka zunzurutun kudi masu yawa-yawan gaske...



Karon farko dana bude baki cikin rawar murya nace "zan shiga gasar alhaji"



A mamakance suka juyo gareni domin basu san na farka ba, cikin mamaki alhajin yace "zaka shiga kace? Kasan wadanda zasu yi zanen kuwa? Ba kananun masu Zane bane, manyan architecture's ne"

Alhajin yafada cikin iyakar gaskiyar sa, domin bai yi tunanin na kware a zane ba.



Cikin k'arfin guiwa na bud'e baki nace "alhaji banyi alkawari, ko nace nawa zanen zai fi na kowa ba, amma ina mai tabbatar maka nawa zanen daban zai k'asance fiye da na sauran"


na fada masa cikin dakewa, domin wanna shine hanyar kadai da nake saka ran samun kudi domin na mallaki ki, ban damu da ko nawa bane, muddin zan samu kudi da zan fara business ko wani abu da zai bani riba mai yawa domin nayi gaggawar mallakar ki...




Murmushi alhajin ya min domin karsashina ya birge shi, matar tasa ta kalleshi, kana tace "alhaji a bashi dama ya gwada bajintar sa" cikin gamsuwa ya jinjina Kai, dama ko bata fada ba, yana da niyyar bashi ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????daman.




Nan alhajin ya bani hakurin cewa motocin escort d'insa ne suka bige ni, sosai nayi mamakin saukin kai irin nasa, domin kallo daya nayi masa na fahimci cewa shi din mai arziki ne irin sosai dinnan...



Bayan sati daya aka sallameni a asibiti, alhajin yace na fada masa ina ne giWan mu ko na kira wani nawa domin yasan halin da nake ciki...




Sosai rauni ?a bayyana akan fuska ta, domin ya tuna min da miki dake binne a zuciyata, cikin k'arfin hali nace "banda kowa, iyayena sun rasu"




Sosai alhajin ya tausayi min, nan yace yana neman alfarma na bi su gidan shi, tunda an sallame ni, na kasa yi masa musu, domin haka kawai naji mutumin ya kwanta min, kana ina ganin girman sa sosai....



Haka na koma gidan sa, mai girman gaske, nan na kara tabbatar da arzikin alhajin, sosai kuma dabi'arsa ta saukin kai da daraja dan Adam ke burge ni, ina ji ina ma ha?a sauran masu kuWi ?e Wa halin ?warai irin nasa...."



_to be continue after sallar isha, ngd sosai da comments Winku masu sugar_=??





Share


Comment


Vote


NoorEemaan
07082281566





I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*



=???KYAUTAR KODA=???
(Its all about love, scracife, hatred and destiny)



*WATTPAD*
@NoorEemaan



ELEGANT ONLINE WRITER'S=???=???
'?



EDITING IS NOT ALLOWEDL'


https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.




Page 53-54


Sosai Alhajin yake ja na a jikinsa, hatta idan zasu ci abinci sai ya kira ni mun ci tare, tunda nazo gidan ban ga wani d'a ko 'ya tasa ba, daga shi sai matar sa, su kadai ke rayuwa a cikin gidan...




Sati daya a gidan, da yamma alhajin ya kira cewa, na shirya gobe ne zamu yi gasar zane. Da toh na amsa kana na koma part din da suka bani, ?ar?i manta kullum tunanin ki, hadi da matsanancin kaunar ki na nan daram a raina, bana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login