Showing 36001 words to 39000 words out of 80179 words

Chapter 13 - KYAUTAR KODA Hausa Novels by NoorEemaan.doc

11 Nov 2025

3055

fadeelah hadi da cewa "my princess!" A razane ta dago jin muryar Daddy, domin sam bata ji shigowar sa ba.


"Daddy!" Tace cikin raunin murya.


Wani iri yaji a jikinsa, yana kara jin tsanar Fadeel din a ransa, ace 'yarsa da gatan ta da komai, amma kan wani talaka can ta sanya damuwa a ranta.



Zama yayi kan gado yana rike hannun ta, a dan tausashe yace "my princess meyasa kike sanya kanki cikin damuwa uhm?" Ya kamata kin san cewa ni mahaifi ki ne mai so da kaunar ki, ke yarinya ce karama baki san yaudara da butulcin namiji ba, wasu mussaman ma talaka, Jameel shine yafi dacewa dake, yanzu ki shirya Jameel yazo yana part din baki na farko, yace ya kira wayar ki a kashe, maza tashi my princess " ya fada yana bubbuga bayanta kana cikin lallashi...



"Okay Daddy" tace cikin k'arfin hali, nasihar Mommah na amsa kuwa a kunnen ta.



Ba k'aramin dadi professor Imran mai naira yaji ba, a tunanin sa, ta fara cire Fadeel din a ranta.


A fili ya furta "that's my princess" hadi da bata K'yak'yyawar sumbata a kumatu kana ya bar dakin.



A sanyaye ta mike, sai yanzu hawayen da suka cika idanunta suka zubo, share su ta yi, dama sanye take da wata roba gown na company *Balenciaga* wardrobe dinta na zallan glass ta zuge, wata haWWaWi?ar kimono ash color da dan veil din shi ta zaro domin ya rufe siraicinta, saSoda rigar ji?inta ta fidda duk wata sura ta jikinta, Saka kimonon tayi, ta yafa veil din ta bar dakin...



Zaune yake a hada'dden falon baki na farko, ya dora kafa daya kan daya, sanye yake da suit blue color na company *dolce and gabbana* daya yi matuk'ar haska farar fatar sa, kan nan ya sha gyara hadi da askin zamani, farin Bluetooth na makale a kunnensa, komai na jikinsa tsad'add'en ne, a kallo daya mutum zai fahimci hakan.



Sosai take jin haushin jameel d'in, sam baya burgeta ko daya, amma Saboda sanin darajar sallama yasa tayi kasa_kasa, glass cup mai dauke da campaign dake hannun sa ya dire kan hada'WWen glass table dake gaban sa, kana ya amsa sallamar fusk'ar sa dauke da murmushi....



Daure fusk'a tayi, ta zauna nesa da shi, k'anta a kasa tana murza zoben azurfa hannun ta, wanda fadeel ya bata ranar birthday dinta.



"My wife to be" Jameel ya fada cikin wani salo, Yana jefan ta Wa wani shu'umin kallo.

Wani zallan haushin sa taji, jin ya kira ta da sunan matar shi, ta sani cewa Jameel din ba laifi domin za a iya saka shi cikin sahun maza masu cikar halitta, amma farar fatar sa ce ta taimaka wurin fidda kyaun sa, domin babu wani kyau a fusk'ar sa.

Wani mugun muninsa take gani, domin Fadeel yafi shi duk wani abu, kama daga kyau, nagarta, kyaun hali da sauran su..



"Ok you okay babe?" ya sake tambayarta Yana mikewa izuwa gareta.


"Yeah!" ta amsa a tak'aice, domin muryar sa kadai ma bata son ji.


Daidai gabanta ya tsugunna, ya kamo lallausan hannun ta, saurin fisgewa tayi tana jefan sa da harara.



Bai damu ba, sai ma wani murmushi daya saki kana cikin hausar shi da Sai gama kwari Sa yace "haba babe meyasa kike behaving like a local girl, gaki wayayya amma, bakya abin wayayyu, you know ina sonki, kuma ni zan aure ki so menene a ciki uhm!" Ya karasa yana kawo labbansa bakinta da niyyar kissing di'n ta.

Wani tura tayi masa kana ta mike a fusace tace "if you think aikata abinda Allah ya haramta shine wayewa, toh kayi kuskure, don't ever in your life ka sake ko da kawo yatsa jikina ne" Fadeelah ta karasa tana sauke numfashi, domin bata saba daga murya ba, tasan cewa Jameel manemin mata ne, amma bata yi tunanin abin nasa ya kai haka ba, take kuma tunanin Fadeel ya fado mata, idanunta suka ciko da kwalla, domin bai taba kawo hannu jikinta ba, duk zaman da suke ?i a waje daya always, ?o da su biyu ?adai ne kuwa.




Hakika tasan soyaayyar fadeel dinta tsaftataciyya ce da babu algus. Tana cikin wanna tunanin taji saukar muryar sa.



"It's fine, amma idan na aure ki baki isa ki min Katanga da taba ko yin duk abinda nake so dake ba" ya karasa a dan zafaffe domin yaji haushin yanda ta hana shi morar jikinta, Womin duk matan da yake tarayya dasu basu taba hana shi ba....




Wani kallon ta watsa masa kana ta bar part din, ba tare da ta sake ?ula shi ba.



Sosai Jameel yaji haushin yanda fadeelah ta bar shi zaune, abinda babu macen data taba yi masa haka "me kika dauki kanki?" ?a fada a bayyana idanunsa kan kofar data bi ta fita, ?amar zai samu amsa.



Mikewa yayi shima ya bar falon bakin, inda masu tsaron sa suke ya nufa, fadawa yayi mota, suka bar gidan a guje
Da tunanin dole ya samu Daddy'n sa akan yana son ayi aurensu da Fadeelah nan kusa, domin yaga tana kokarin jefa shi wani hali.......
'?





Hakuri dai=?)?=?O?
kunyar ku ma nake ji fans, musamman yan group din kyautar koda da Papi ne! Kumin afuwa ban Baku update jiya kamar yadda na ce ba, nasan kun sha jira nayi busy da yawa ne jiyan.




'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*



=?????AUTAR ?O?A=???
(it's all about love, scracife, hatred and destiny)





*Written by*
Noor eemaan





*Wattpad*
@NoorEemaan




ELEGANT ONLINE WRITER'S =???=???





EDITING IS NOT ALLOWEDL'

(Don't forget to vote and follow me at Wattpad @NoorEemaan)


https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.



Page 37-38

(Kila kuga typing error>??)


Sosai motocin Jameel suke sharara guWu kan kwalta, ha?an yasa cikin kasa da mintuna ashirin suka isa giWansu, buWe masa mota akayi, bayan an faka motocin, cikin isa da gadara ya fito ya nufi bangaren da?a san zai samu Daddy'nsa.




Zaune ya tarar da i?a?ensa manne da juna suna kallon a tashar *zeeworld*, ganin tilon dansu ya sanya suka faWaWa murmushin su, ba tare Wa ko sallama ba, ya zauna tsaki?ar su, sam i?a?en nasa basu damu ba, sai ma bashi Wu??anin hankalin su suka yi hadi da tamba?arsa me yake damunsa.




Cikin sangarta irin ta ?a?an wasu masu gidan rana yace "Mom! Dad! ina son a Waura mana aure da fadeelah cikin satin nan"


Kafin Daddy'n jameel yayi magana, mummy'nsa tace "what! haSa son sanin ?anka ne cewa ?oWa a ?au ?ake son a daura maka auren da mata Wari kasan muna arzi?in yin haka, amma bikin ka ne fa, bikin dan mu abin son mu, kuma a yi shi cikin week dinan impossible, dole muyi biki da kaf cikin Nigeria da wajenta su san da bikin dan minister" Mummy'n Jameel ta fada cikin alfahari da isa irin su ta wasu masu gidan rana.






Alhaji Sa'id da ya bi matar sa da kallon murmushi ganin yadda take magana tana fari hadi girgiza yace "my son gaskiya ne abinda mummy'n ka ta fada, kuma fadeelah taka ce domin mun gama magana da professor Imran, in sha Allah zan tafi Qatar amma da zaran na dawo za a yi bikin ku, domin bazai yu bikin dana ayi shi bana kasar nan ba, tafiya Qatar ta zame min dole, amma da zaran na dawo komai za a yi shi fiye da yanda kake so my son kaji ko?"








"Cikin gamsuwa da maganar iyayen sa ya jinjina kai, so da sha'awar fadeelah ne suka rufe idanun sa, har yake so ayi bikin cikin gaggawa, domin shi kanshi zai so bikin sa ya zagaye duniya, ya zamana duk inda mutum ya shiga aji zancen bikin ake tattaunawa akai, da wanna tunanin ya hakura.





*** *** ***





Zaune fadeelah take a bedroom d'in Mommah, yayin da ta dora k'anta akan kafadar Mommah, babu abinda ke fita a fuskar ta sai zallan damuwa, Mommah dake shafa k'anta tace " sweetheart har yanzu dai wayar Fadeel din baya shiga?"




An tabo mata inda yake mata kaikaiyi, kwallan da suka taru a oily eyes dinta ta yi saurin share, kana tace "har yanzu bana samun sa Mommah, ya jefa ni cikin wani hali, meye laifina Mommah? Kila ma ya daina sona" ta karasa tana rushewa da kuka hadi da rungume Mommah gam-gam a jikin ta.





Cikin tausayawa Mommah ta shiga bubbuga bayan fadeelah, hakika soyaayyar su tazo da wani irin salo mai wuyar fassaruwa, amma zanen kaddarar su ce tazo da hakan, a tausashe kana cikin murya rarrashi tace "stop crying fadeelah, ki bar komai a hannun Allah, ki cigaba da add'ua da karatun qur'ani domin shi maganin damuwa da duk wata masifa, sannan ina da yakinin cewa duk in da Fadeel yake a halin yanzu kina makale a ransa, daina damuwa domin baya maganin komai, gaba d'aya kin sanja, kin rame kamar ba diyata ba yar gayu da, oya tashi ki je ki shirya mu fita outing" Mommah ta karasa tana mikar da ita tsaye.




Bata musa ba, ta nufi bangaren ta, toilet ta fada ta sakar wa k'anta ruwan dumi hadi da murzawa lallausan fatar ta da shower gel na *Versace Pour Homme Dylan* ta d'auki mintuna talatin a bathroom kana ta fito daure da pink towel da wani daure a k'anta, lotion mai k'amshi ta murza kana ta fito da wasu had'add'un English wears na company *Valentino* riga ce mai digon hannu daya sauka har saman cinyar ta, a gaban rigar zuwa kasa akwai botira(buttons) , sai wando dogon rigar mai bud'ed'en kasa duka yellow ne, wani hill cover shoe ta saka baki, tayi parking gashin ta a tsakiya da yellow ribbon, sai mayafin rolling irin na larabawa ta yana a k'anta shima baki, handbag karami baki mai walwali ta dauka sai glass golden color mai dan fadi ta sanya, hannunta daure da agogo na kamfanin *Gucci* shima baki, sai perfume mai k'amshin vanilla ta fesa, babu ko digon makeup a fusk'ar ta, amma tayi wani irin sihirtaccen kyawun mai tafiya da hankalin dukkanin wani lafiyayyen namiji, cikin takun nutsuwa ta bar dakin bayan ta gama kallon zanen hoton su fadeel da Mahmah kana ta bar dakin idanunta cike da kwalla sai dai bata bari ya zubo ba.








Zaune ta tarar da Mommah cikin shigar tsad'add'en leshi wanda kudinsa ya kai million daya da rabi, anyi mata dinkin boubou irin na manyan mata, sosai tayi kyau itama ta sha make-up domin Mommah ba dai iya daukar wanka ba, sannan ta na son makeup a fusk'a.






"Wow! My sweetheart kinyi kyau sosai" sai kuma ta jefa mata hararan wasa tace "ohh ni Shuhudah naga ranar da zaki yi makeup"




Murmushi fadeelah ta saki kana tace "Mommah Allah bana son makeup, fusk'a ta nauyi take min"




Dariya ma ta bawa Mommah Wai fuskar ta d'auki yake, hannun ta ta kama suka fice, a jere motocin bodyguard din fadeelah shida suke, Yayinda a tsakiyan shidan akwai wata rantsatsiyyar mota black color kirar *Pagani huayra Bc roadster wanda kudinsa ya kai ?3,764000*



Suna kokarin shiga motar, bodyguards din Mommah suka karaso wajen suna tambayar ta ko su dauko mota? Tace a'a ana fadeelah zasu fita, cikin girmamawa suka ce toh, hadi da musu fatan dawowa lafiya, bayan motocin sun fita, har sun hau babban kwalta Mommah ta kalleta tace "sweetheart akwai wani wajen shakatawa da kike sha'awar mu je?"





"Yes! Mommah ina son muje VICTORIA ISLAND, RSVP RESTAURANT"

Dan kallonta Mommah tayi kana tace "akwai wajen shakatawa da suka fi RSVP restaurant amma meyasa kika zabe shi?"



Lumshe ido tayi kana ta bude, kwalla taf Cikin su tace "Mommah ina son wajen, domin a nan na fara haduwa da fadeel"




Jinjina kai Mommah tayi fusk'arta dauke da murmushi, Yayin da kasan zuciyar ta tausayin fadeelah ne fall cikinsa, ko wani bawa ta tasa kaddara, Hakika ciwon so ciwo ne mai zafin gaske, musamman idan masoyan sun kasance masu tsananin son juna kuma an samu matsala daga bangaren iyaye, misali ga fadeelah bata da matsalan komai tun tana karama har ila yau babu abinda ta rasa a duniya, Sai dai Allah ya jarrabe ta da son Fadeel wanda ya kasance talaka, ita kam tana yi wa fadeelah sha'awar auren Fadeel domin yaron ya kwanta mata, ajiyar zuciya ta sauke tana musu fatan mallakar juna, matuk'ar akwai alkhairi a tarrayar su ......






Bayan sun isa RSVP restaurant suka yi ordering abin sha kana Mommah ta shiga debe mata kewa, har karfe biyar suna wajen kana suka komo gida....








Da isar su estate suka hango Daddy zaune a farfajiyar gidan rike da news paper Yayinda idanunsa ke sanye da glass, lokaci zuwa lokaci yana dan kurban tsad'add'en campaign na mixed fruit.







Ganin su Mommah ya sanya shi rufe news paper yana murmushi, basarwa Mommah tayi kamar bata gan shi ba ta nufi part d'in ta, murmushi professor yayi yasan cewa matar tasa tana da hakuri, amma wanna karon tayi fushi da yawa, domin tun ranar da fadeel yazo estate din har yau basa shiga harkan juna.
fadeelah kuwa ta nufi wajen shi, domin ta gaishe shi...






Ku min haku'ri wallahi abubuwa sun min yawa kwana nan, wanna ma tsatsaye nayi muku shi domin faranta ranku my lovely fans.=???




Thank you for reading kyautar koda=???





#Share
#Comment
#Vote



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*


=???K?AUTAR ?O?A=???

(It's all about love, scracife, hatred and destiny)





*Wattpad*
@NoorEemaan




ELEGANT ONLINE WRITER'S=???=???








EDITING IS NOT ALLOWEDL'


https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.



Page 39-40



?ujerar Wa?e kallon wanda Yake Zaune ta zauna, kana tace
"Daddy barka da hutawa"



"Yawwa my princess, ina ?u ka je ne ke da Mommah'n taki"




Murmushi tayi tace "mun fita outing ne"


"Yayi kyau, naji dadin ganin K'yak'yyawar 'yata cikin walwalwla"



Wani murmushin ta kara yi tana wasa da zoben hannunta, haka dai fadeelah tayi ?o?arin sake wa da Daddy suka dan taba hira kana ta koma part di'n ta....


&&&


*JAMEEL*

Kwance yake a part dinshi, tare da wata K'yak'yyawar budurwa suna aikata laifi mai girma gaske ( *zina* Allah ya tsare imanin mu) babu abinda kake ji sai saukar numfashin su, gabadaya sun birkita gadon.....







*Bayan yan mintuna*

Kwance suke manne da juna, Yayinda wanna budurwar ke sharar hawaye, kana cikin kuka ta fara cewa "my Jameel me na rage ka dashi? Da har zaka auri wata, lokacin dana samu labarin 'yar gidan professor zaka aura na shiga tashin hankali sosai, idan ?udi da arziki ne nima kasan ba baya nake ba, dan Allah kada ka barni, ina sonka sosai my Jameel, ka sani kai ka fara sani na a 'ya mace, amma meyasa zaka barni dan Allah!!!!"



Cije leben sa masu kyau da taushi ?ayi, domin leben sa shine ?awai abun burgewa da k'yau a fusk'ar sa, a ransa yace ba zaki gane ba, duk da bansan yaya take ba, amma ina da yakinin ita din ta daban ce.... (Kalubale garemu yanmmata, shi namjin idan ya gama da rayuwar ki, sai ya je ya nemo wacce take kamilaliyya mai daraja ya aura, Allah ya tsare imanin mu da mutuncin mu)





A fili yace " haba my haulat, kin san ina son ki nima, kuma auren Fadeelah ba shi ke nufin zamu rabu ba, zamu ?asance tare, Saboda haka daina mun asarar hawayen ki" ya fada cikin tsantsar mur?ar yaudara yana share mata hawaye....





Luf tayi a jikin shi tana sauke ajiyar zuciya, tsakanin ta da Allah take kaunar Jameel, haka dai ya cigaba da kwantar mata da hankali, har suka sake ai?ata masha'ar su, sai karfe biyar na yamma ta bar gidan, har bakin motar ta ya raka ta, kana ta tafi, ko dar babu, domin iyayen sa sun san duk abinda ke faruwa, domin acewar su wayewa ce, hakan yasa Jameel ke cin karan sa babu babbaka, domin babu mai hanashi....




Sai da motar haulat ta gama barin haraban gidan, ya dauke idanun sa hadi da tabe baki kana ya nufi bangaren mummy'n sa...







****** ****** *****





Bangaren Fadeelah kuwa har yanzu damuwa na nan daram a ranta, domin kullum cikin kuka da damuwa take, saidai tana matuk'ar kokari wurin boye damuwar ta ta, sai dai kallon d'aya mutum zai mata ya fahimci tana da damuwa mai tarin yawa....



Kullum tunani da damuwar ta Fadeel, ina yake? Wani hali yake ciki? Kullum tunanin ta kenan, kamar yau tsaye take gaban hoton zanen Fadeel da ke bango tana zubar da ?walla masu zafin gask'e hadi da radaddi...



"My one, please ka dawo gareni, I have missed you a lot, can't you see am dying SaSoWa rashin ka" shiru tayi tana sauke shesheka kana ta Wora da cewa

"Ka barni cikin kewa da zafin son ka, dama kana da zuciya da juriyar yin nesa dani? Hakika ina cikin ciwo mai yawan gaske dan Allah ka dawo! Ka dawo gareni ina buk'atar ka, dan Allah Fadeel!!!".


Ta karasa tana zubewa kasa, Yayinda hawayen ke zuba a fusk'ar ta kamar famfo...



Haka ta jima tana kuka kana ta shiga hada'dden bathroom dinta domin wanke fusk'ar ta.... Da wani mini towel ta fito fari tana tsane ruwan fusk'ar ta.... Wayar ta ce ta fara ringing, a sanyaye ta kai hannu ta dauka, ganin number'n mai kiran ne yasa ranta ya bace, duk da bata yi saving number shi ba, amma ta shaida number'n...



Kamar ta kashe wayar, sai kuma ta barta ta cigaba da ringing kusan karo na biyar



Daga bangaren Jameel kuwa tsaki yayi ganin ya kira bata daga ba, shi da yanmmata ke rubibi amma yau shi ke kiran wayar fadeelah har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login