Showing 51001 words to 54000 words out of 80179 words

Chapter 18 - KYAUTAR KODA Hausa Novels by NoorEemaan.doc

11 Nov 2025

3040

iya bacci, Saboda tunanin ki da fargaban rasa ki, sosai nayi add'ua kan Allah ya bani sa'an wanna gasar.



*WASHEGARI*

Muka fita da alhajin zuwa inda za'a yi zanen, Hada'dd'en waje ne, mai dauke da duk wani abun bukata na zane, abokan gasan nawa babu wani talaka a cikinsu, domin hudu daga ciki ma turawa ne, amma still ban karaya ba, awanin shida aka bamu domin mu gama.....




Bayan awanin hudu na gama na saka suna na daga dan kasa in a fashionable way, sai dai ban rubuta full ba, *FFM* haka na saka sunana kana na mi?e.

Ta?e na ga abokan gasar tawa suna min dariya, ganin nine mutum na farkon gamawa, a tunanin su ban iya komai ba, Domin babu wanda ya sanni a duniya a matsayin architecture...




Bayan awanin biyu naga sauran masu zanen suka fito, Wani wajen mai kyau aka ?ai mu haWi Wa bamu hada'WWen abinci da abin sha, su?a ce mu jira har a kira result din wanda ya zo na daya.




Sam na kasa ko da shan ruwa ne, burina ?awai a kira result na ji ko na ci, sabanin sauran dake cin abincin su cikin raha da farinciki, ni kuma ina gefe, ban shiga cikin su ba, domin irin kallon kaskancin da suke min, abinda na tsana ?enan raini da wulakanci, duk da kasancewa na talaka bana daukar raini, komai arzikin mutum kuwa, domin sam bana son zuciyata ta mutu kan abun duniya.






*Da Misalin Karfe Shida ?a Rabi Na ?amma*


Muna zaune a wanna wajen Wai da aka bamu, muna jiran jin sak'amak'o, bayan sallar bana ko motsi....

babu zato SaSu tsammani muka ji muryar wata mace ta wani loudspeaker domin maganar ta karade ila'irin wajen kamar haka "The winner is FFM, congratulations to you"






Take na zube kasa nayi sujjadul-shukur, Yayin da hawaye masu dauke da abubuwa da dama suka zubo min, Sosai nayi farincikin hakan, finally ni na ci.




Abokan gasar zanen nawa kuwa, mutuwar zaune suka yi, domin basu taba tunanin cewa zan zo ana karshe ba ma, domin a dakin da muka yi zanen babban ne, sannan akwai tazara mai dan yawa tsakanin mu, babu mai ganin zanen wani...




Mutum daya ne daya kasance ba?in fata dan garin Ibadan ya min murna, kana ya fada min cewa "na maka murna sosai bro, congratulations! tabbas a rayuwa kada ka taba raina ko wulakantawa mutum komai kaskanci shi kuwa, hakika na koyi wani darasi daga gareka.." Yana fadamin haka yana ficewa daga wajen...



Nan sauran suma suka tafi cike da jin haushina ko nace tsana ta, domin naga hakan ta idanun su.




Bayan awa d'aya Alhajin ya fito yace mu koma gida, fusk'ar sa dauke da murmushi kana da sauran mamakina kan kwarewa ta, domin zanen yayi k?au mai ban mama?i



Bayan munyi sallah, mun ci abinci a part di'n alhajin, ya mike ya shige bedroom d'in shi, babu jimawa ya d'awo dauke da wata madaidaicin jaka ya mika min....


Fuska ta da alamun tambaya nace "menene wanna alhaji"




Murmushi yayi yace "hakika kai gifted ne, kana da talent na zane sosai, kayi matuk'ar iya zane, wanna jakar mai dauke da million hamsin naka ne, ma'ana shine hakkin ka na zanen"




Sosai na shiga rudu, domin ban taba tunanin samun koda million Waya ba, cikin rudewa nace "Alhaji nawa ne million hamsin? dan Allah ka fadamin, zai Kai na iya mallakan Fadeelah ta? kudin zai isa da har Daddy zai bani auren Fadeelah?" Na fada hawaye na ciko idanuna, domin a lokacin burina na mallake ki.....




Sosai alhajin yayi mamakin ganin ban yi murna samun makudan kudaden nan ba, sai ma sunan ki daya ji na kira, hakama matar sa.


Hannuna ya riko yace "hakika akwai abubuwa da dama cikin tarihin rayuwar ka, wacece wanna fadeelah'n sannan waye zai ki baka auren ta?, ka fadamana labarin ka nayi alkawarin taimaka maka da dukiyata da ma duk wani abu da zaka bukata"...




Ban musa ba, na basu tarin rayuwata, dama labarin soyaayyar mu, kin san menene? Ya tambayi Fadeelah, girgiza kai tayi Yayinda ta?e k'irjin shi har yanzu.





Gani nayi alhaji yana zub da kwalla, matar sa kuwa rushewa tayi da kuka, wanda na zallan tausayi ne...



Sa?an wasu mintuna yayi gyaran murya yace "idan kace zaka yi aure da duk kudinan daka samu, Tayaya zaka yi arziki? Tabbas mallakan Fadeelah a matsayin mata shine cikar farinciki ka, amma ba yanzu zaka je gareta ba, business zaka yi da kudin nan, sannan zan maka hanya ta yanda duni?a zata san cewa kai babban architecture ne! hakan zai sa cikin lokaci kankani sunan ka ya daukaka, har ka dinga samun kudaWe masu yawan gaske, idan arzikin ka ya sake bunkasa sai ka fara gina gida, Bayan nan ka zuba motoci, Bayan ka gama hada dukkanin abinda kasan cewa mahaifin ta zai baka auren ta, sai muje kwatsam"...




*******************************



Sosai suna na ya Wau?a?a a duniya, a matsayin *Architecture FFM* duk yanda yan jaridah da yan gidan TV suka so hira dani ban bari ba, kana ban bari sun dauki hoto na ba, ina mamakin wai nine yau yan jaridah ke rububi akai, hakika idan baka da shi a duniya ka zama dan kalllo.....




Sosai na yarda da shawaran alhajin, cikin lokaci kankani na fara bushiness, ga manyan zane na masu kudi da nake ta samu abin har yawa yake min...



In tak'aice miki, cikin watanin kalilan nayi arzikin da ni kaina ban san yawan su ba, abu na farko dana fara yi shine gini na, wanda na zane ne da hannuna, na kuma yi shi a garin lagos domin nan nake sha'awan zama, sannan na zubo motoci da duk wani abun more rayuwa, na zuba ma'aikata, hadi da bodyguard's masu bani tsaro kamar yadda alhaji yace lallai sai na samu bodyguards domin tsaro......





a lok'acin dana shiga katafaran gidana sai dana yi kuka tuno Mahmah nah.
A dalilin rashin babu(kudi) cuta ya cita har ta koma ga Allah, sai bayan ranta nayi arziki da ban taba mafarki ba, sai kuma ma tuna haka Allah ya kaddara mana....







Daga wanna lokacin alhajin ya dauke ni tamkar ?an sa, daga baya yake fadamin duk tarin dukiyar sa, Allah bai basu haihuwa ba, amma mutum bazai gane hakan ba, domin suna zaune cikin farinciki, sun ?uma fawwalawa Allah lamarin su.







A lok'acin dana ji cewa anyi baikon ki da Jameel na kusan zaucewa, domin ina sa ayi min bincike akan abinda ya shafeki..... Babu bata lokaci na samu Alhajina nace dan Allah ya taimaka su je tambayan min auren ki domin bazan jure rasaki ba a karo na biyu...



Sosai alhajina ya kwantar min da hank'ali, yace akwai shiri na musamman da yake yi, yana so komai yazo a bazata, yace na yarda dashi, na bar komai a hannun sa, ban sake cewa komai ba, amma kullum tunanin ki nake, ina fargaban rasaki, ga kuma tarin sonki dake nukurkusata, sau da dama ina son zuwa gareki alhajina ya hana yace na bari komai ya tafi kamar yadda ya tsara....




Makudan kudade da ban san hadadin su ba na bawa matar Alhajina domin ta hada min lefe, cikin kankani lok'aci ta fita kasar waje ita da wata kawarta da kanwarta suka hado....




A ranar da lo?acin dasu Jameel za su kawo lefe duk muna sane, hakan yasa alhajina yace a kawo nawa kafin su jameel su kawo nasu, hakan zai kawo rikitarwa.....



Nan matar Alhajina dama yan'uwan ta da wasu kawayenta suka k'awo lefen, Bayan kwana biyu muka zo estate dinku Alhajina yayiwa Daddy bayanin cewa yayi haku'ri, mun yi nema cikin nema amma ba laifin sa bane, Dan sa ya na matuk'ar son fadeelah da dai sauran su....



Abu biyu ne ya bani mamaki, Daddy bai ki amincewa ba, ban saniba ko dan alhajina yafi mahaifin Jameel dukiya ne, Allah masani.
Sannan abu na biyu Daddy bai gane ni ba, bai gane cewa nine wanna bakin talaka fakirin bane...



Naso zuwa gareki a ranar da muka zo wajen Daddy, still alhajina ya hana yace na bari sai ranar daurin aure domin inyi miki bazata....



Ajiyar zuciya Fadeel ya sauke kana ya cigaba...

har yau da aka d'aura mana aure, daddy bai san cewa nine Fadeel ba, ina matsayin dan Alhaji Sufyan Rufa'i ne a wajensa.....



BACK TO STORY


Kara rungumeta da kyau yayi, yana jin farincikin mallakar ta a matsayin mata, yace

"wanna shine tarihin Bayan rabuwar mu a tak'aice...."







Muje zuwa da sauran chakwakiyya=??=??=??


A tayani share dan Allah=?O?


Share fisabilillah




Comment



Vote




NoorEemaan
07082281566


I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*




=?????AUTAR ?O?A=???
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)




*WATTPAD*
@NoorEemaan



ELEGANT ONLINE WRITER'S=???=???


EDITING IS NOT ALLOWEDL'

https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.



Page 55-56

Kukan zallan farinci?i Fadeelah ta sanya, a ranta tana mai godiya ga Allah. Ita ba arzikin Wa yayi ya sanya ta farinciki ba, dawowar sa gareta a matsayin miji yafi komai yi mata sugar. Duk da ta san cewa akwai kalubale a gaba, amma bata wani damu ba, tunda sun zama ma'aurata ?anzu burin su ya cika.



Duk da arzikin da yayi a kankanin lokaci abin mamaki ne, taSSas bata manta lokacin da ake yawan labarai a gidan TV kan *The young billionaire architecture FFM* bata mantawa a falon Mommah suna zaune aka has?o labarin, shi Kanshi Daddy sai daya jinjina arzikin wanna matashin, ashe Fadeel dinta ne bata sani ba, duk da yayi fiye da arzikin da Daddy zai so, amma shin zai amince suyi zaman su cikin kwanciyar hankali kuwa? Ta aiyana a ranta, sanin cewa bata da amsa ya sanya ta share, kana a fili tace "Am so happy my one, Allah na gode maka, da gaske kai ka aureni? Wayyo dadi!" Raba jikinsu tayi ta nufi zanen hotunan dake manne a bango.

Daidai kan na mahmah ta tsaya, ta goge kwalla sakamakon tuno Sadaukarwa mahmah a gareta wanda kullum da shi take kwana take tashi, tabbas Mahmah ta zama sashen jikinta, Yayinda Fadeel ya zama jinin jikinta.



Shafa fuskar zanen Mahmah'n take yi tana kokarin controlling hawayen dake zuba a idanun ta.


Cikin murya dake bayyana tarin kauna hadi da kewar mahmah tace "Allah ya jikan ki Mahmah, Allah yasa kin huta, Mahmah ?i?i farinci?i... a yau Fadeel din ki ya cika miki burin ki, mun zama ma'aurata, nasan kina farinciki a inda kike yanzu, ina kaunar ki mahmah nah, muna kaunar ki duka" ta kara sa tana share wasu hawaye masu dumin gaske.


A Sazata ta ji Fadeel ya rungumeta ta baya, hannunwansa duka biyun ya d'aura saman shafaffan cikin ta. Cikin wata murya da amon sa ke fidda tashin wani miki a zuciyar sa yace "Ameen ya tawwabul raheeem, amma kin manta baki fada mata cewa zamu Haifa mata jikoki ba, sannan zamu kasance tare har abada, har mu koma inda take a yanzu, duk runtsi duk wuya muna tare" ?a ?arasa cikin wani cool voice ?ayinda idanunsa suka kara yin jaa...



Murmushi mai tafe da hawaye ya taho wa fadeelah a lokaci daya, cikin muryan kuka tace "eh mahmah! Zamu haifa miki jikoki, sannan kullum sai na basu labarin ki, na sani cewa baza su taba ganin ki ba sai Wai a hoto, amma zasu rayu da son ki a jinin jikin su, sannan ni da Fadeel zamu kasancewa the best couple ever, we love you Mahmah" ta karasa tana juyowa hadi da rungume Fadeel.



Shi ma rungumeta yayi ya shiga bubbuga bayanta har tayi Shiru tana sauke ajiyar zuciya. A hankali tace "My one menene ma'anar FFM?"

Murmushi mai sauti ya saki, lumshe idanun sa yayi yace "it means *FADEEL, FADEELAH, MAHMAH*" ya amsa a tak'aice...


"Wow!" Tace tana jin farinciki samun masoyi kuma miji kamar Fadeel.



Slowly cikin zazzakar muryar ta tace "Am so happy for you, I love you so much"


Wani shaukin sonta ne ya shiga ratsa jijjiya da jinin jikin sa, martani ya mayar mata kamar haka "I love you too, fiye da tunanin mai tunani, ina matukar kaunar ki my Darling wifffy"



Murmushi ta saki, komai na Fadeel dinta ya sanja, magana, tafiya, kallo, murya, komai nasa ya dawo cikin wani aji da salo mai tafiya da hankalin duk wata lafiyayyen mace.....



Hannun sa ta kamo suka zauna kan hada'dd'e kuma katon gadon ta, kallon ta yake yana jin wani farinciki a ransa, ta yi masa kyau fi da tunanin mai tunani, still hakan bai hana shi ganin ramar da ta yi ba.


"I love your hennah Darling" Fadeel ya fada yana sumbatar had'add'en jan kunshin hannun ta.


Murmushin zallan farinciki tayi, ta kai idanun ta kan kunshin, tunda aka yi mata kushin bata ga kyaun sa Sa, haslima haushin sa take ji, sai a yanzu ta fara ganin kyawun K'unshin, wanda baya rasa nasaba da bayyanar gwarzon masoyinta kuma mijinta fadeel.



Kallon shi tayi tace "my one amma ka kai ziyara wa yan'uwan mahmah da na baba ko?"


Take yaji ranshi ya baci a dan kausashe yace "ban je ba, ba kuma zan je ba, Tayaya kike tunanin zan iya zuwa? Sun manta damu, sun manta cewa ina raye ma, sun ma san mahmah ta rasu? Basu sani ba, saboda rashin zumunci, ?o Wan sun ga a cikin dangin talakawa ne mu shiyasa basa ziyartarmu, tell me tayaya zan je wajen su, sam bazan je ba, idan ina dake, ina da komai Fadeelah, idan kika Haifa min 'ya'ya sune zasu kasance duniya ta Wa dangin na, hakan ya ishe ni rayuwa Alhamdulillah! Ki bar zancen su please" ya karasa yana sauke numfashi....





Ganin yadda yake magana ya sanya fadeelah sanin cewa ranshi ya baci matuka, domin bata taba ganin fushi ko bacin ran shi ba sai yau, Hakika dangin sa basu da zumunci, amma a hankali zata dinga yi masa magana domin ya je garesu, saSoWa hannun ka baya taba rubewa ka yanke ka yar.



Hannun sa ta riko a fili tace "na bari toh, saki fuskar ka please" ta karasa a shagwa'be.

Murmushi ya saki yace "na saki toh, are you Happy now?"

"Yes! My one" ta amsa cikin wata had'add'iyar murya daya sanya shi jin wani yanayi na musamman a tare da shi, a hankali ya matso daf da ita, baya tayi kadan, sai ya bi ta ya kwanta a kanta, hakan yasa ta zube kan gadon...



Dan waro ido fadeelah tayi ganin bai taba kwantanta irin haka da ita ba, ko da su biyu ne ?adai a wajen. Amma tuna matsayin sa a gareta yanzu ya sanya ta sauke boyayyen ajiyar zuciya, amma sosai ta ji wani kunyar sa ?a shige ta.


Ganin ya nufo labb'anta ya sanya ta runtse idanun ta, dakatawa yayi yana murmushi mai sauti ganin yadda tayi, hannunsa ya kai ya shiga shafo tattausan labb'anta yace "bana son gulma faaa, na san kin ji ma kina son Fadeel ya sumbace ki ai, dan haka ki bud'e idanun ki" ya karasa cikin wani romantic voice.


"Ya Allah! Fadeel zai kashe ni da salon sa, hadi da kunyar sa, komai nashi ya Sanja ya dawo gwanin burgewa fiye da baya" ta fada a ranta.


A fili kuwa tace "yaushe ka koyi sharri my one? ni ban taba wanna tunanin ba, Allah faaaaa" ta karasa tamk'ar yarinya yar 13years...


?ata zata ba, unexpected ta ji ya kamo lallausan lips di'nta mai fidda k'amshin Mouth Wash na Lavender ya fara kissing di'nta in a passionate and romantic way...



Sarkin kunyar kuwa bata san lokacin data shiga bashi hadin kai ba, gaba daya sun shiga wani yanayi mai wuyar fassaruwa, ji suke dama sun dauwama a duniyar da suke ci?i ?anzu, Womin yanayi ne mai dadi da bazai fadu ba. Sosai ?uma suka birkita gadon dama kansu....



Bayan mintuna goma sha biyar... har ?anzu suna abu daya, ganin ya fara zurmewa da yawa ya sanya Fadeelah zare labb'anta da suka yi mugun jaaa, domin fadeel bai mata da wasa ba, tamkar lollipop yake sha...



Ganin ta cire labb'anta ya sanya shi lumshe fitinanun idanun sa masu dauke da zallan sonta hadi da kwadayin kasancewa da ita, kansa daya gama hargitsewa ya dora kan k'irjin ta yana sauke numfashi domin babu k'arfi ko daya a jikinsa....
Hannunta na kan gashin sa tana murzawa a hankali Yayinda idanun ta ke a lumshe, sosai suke jin shauki hadi da jin dadin kasancewa a haka.



"Wiffy" Fadeel ya kira ta slowly

"Uhm" ta amsa cikin murya kasala

"Kinyi enjoying kiss din ko?" Ya fada cikin tsokana...

"Ya salam! My one dama baka da kunya, please kabari kana bani kunya faaaa"


Bayan lokuta masu yawa daya k'asance cikin kunci da damuwa sai yau ya yi dariya mai sauti, domin ba kadan ba ta bashi dariya. "Toh mena yi na rashin kunya yanzu?"

"Ni dai ka bari bana so" ta fada tana turo cute lips d'inta


Dagowa yayi ya bata light kiss a lips d'inta, hakika fadeelah'n sa daban take cikin mata, duk da kasancewar ta wayayya domin daidaikun kasa ne bata je ba, kana duk wata wayewa tana da shi, ha?a ma ilimi, amma hakan bai hana ta zama mara ?un?a ba, sosai kuma hakan ke burge shi domin kunya ado ne ga mace....


A fili cikin tsokana yace "ba wani bakya so, Bayan kamar zaki cinye min ba....."


Da gudu ta sauka Waga kan gadon ta ruga toilet.... Kwanciya yayi a gadon ya shiga dariya, domin sosai Fadeelah'n ke bashi nishadi yau.



Fadeelah kuwa ajiyar zuciya mai dauke da murmushi take ta saki a bathroom.... Ta kai mintuna biyar a wanna yanayi kana ta tube kayan jikinta tayi wanka da hada'dd'en *shower bath* dinta, kayan jik'in ta ta mayar, domin bata son fita da bathrobe ya ganta haka, sosai kima, girma, haWi da kunyar sa ta karu a Idanunta musamman yau din daya zama miji a gareta...


A hankali ta rike handle din kofa ta fito, waro ido Fadeel yayi yace " me zan gani ni fadeeel, amarya ba makeup a fusk'ar ta, tukunna ma wanka kika yi? ko dai ko dai" ?a karasa ci?in zolaya


Turo baki tayi kana tayi murmurshi domin ta dauka wani abu ne ya sa shi waro ido, a ranta tana mamakin dama Fadeel dinta ya iya tsokana haka, bata bashi amsa ba, domin ta san kawai so ?a?e ya sata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login