Showing 3001 words to 6000 words out of 80179 words

Chapter 2 - KYAUTAR KODA Hausa Novels by NoorEemaan.doc

11 Nov 2025

3053

da kallon kauna hadi da alfaharin kasancewar ta yar sa.


Cikin saurin ta fada jikin sa tace "Daddy daman ka dawo, how comes you didn't tell me? Nayi kewar ka sosai Dad"


Bubbuga bayanta yayi yace "I so much miss you too my little princess, ya kokari?".


Raba jikin su tayi tana cewa "Alhamdulillah Daddy"

"That's very good of you my princess"



"Eh lallai yayi kyau sweetheart, dan kinga Daddy ko ta ni ba a yi ko? zamu gauraya ne"
Mommah tace tana jifan ta da hararan wasa.


"Wayyo Mommah na kiyi haku'ri"
fadeelah ta fada cikin shagwa'ba tana k'arasa wajen ta hadi da rungume ta.


"Don't mind her my princess, kishi take" daddy' ya fada cikin zolaya


Dariya suka sanya gaba-daya, kana suka cigaba da hirar su gwanin sha'awa wanda hakan ya rage mata kaso saba'in daga cikin damuwar ta...


&&&

_Victoria island_
*RSVP restaurant*

A yau ma fadeelah ta sake zuwa restaurant din nan, saboda burin ta da fatan ta mai zanen ta ya bayyana a gareta, soft drink hadi da table water tayi ordering, yayinda bodyguard dinta ke can gefe ta basu daman shigowa, suka zabi duk abinda suke so, duk da haka, duk wani motsin ta na kan idanun su ne, saboda bata tsaro...


Babban glass da ake wa lakabi da "no respect" sanye kan fuskar ta, wanda hak'an yasa mutum ba zai taba fahimtar yanayin da kwayar idanunta ke ciki ba...


Tayi zurfi a tunani taji magana daga bayanta kamar haka "excuse me ma'am, ance in baki wanna" ya fada yana mika mata cardboard paper kalar na ranan, take gabanta ya fadi cikin sauri ta mike hadi da cewa waiter'n "ina yake? Where is he?"


Take dukkanin bodyguard dinta suka yo wajen suna saita bindigogin su, cikin rudewa waiter yace "ya fita yan...zu nan"

A take ta ce "guards! ku duba min inda yake"...


Cikin sauri suka fita tare da waiter'n domin ya nuna musu shi... Ware paper'n tayi, wanna karon tayi mugun kyau fiye da na baya, kuma tsaf kayan jikin ta da glass din fusk'ar ta da komai ya zana...

Tana cikin kallon zanen ne suka dawo hadi da cewa " he is no where to be found ma'am"


Dafe kanta tayi, ta ji wani irin daci a bakin ta, kana ta fara tafiya cikin sauri- sauri ta fita daga restaurant din, ko jira a bud'e mata kofar mota bata yi ba ta fad'a ciki....


Cikin rawar jiki bodyguards din ta suka shige motocin kana suka dauki hanyar gida....




Ajiyar zuciya ya sauke kana ya fito daga maboyar sa, zuciyar sa ce ta karye, daman ba sa'ar yin sa bace bai sani ba? Hannu ya d'ora kan saitin zuciyar sa ya cigaba da cewa "hak'ik'a zuciya baki min adalci ba, ta ya ya ka kamu da son wanna attajirar? Ya ya zan yi da soyaayyar ta d'aya yiwa zuciya ta da'bai'bayi?"
Lumshe idanun sa yayi, tunani barkatai na kai kawo a zuciyar sa, daga karshe dai ya tari mai keke napep ya shiga, yana tunanin dole ya yakice ta a zuciyar sa ko ta halin ka ka ne......



_i most confess this... nayi farinciki sosai da yanda kuka karbi littafin kyautar koda, i do really appreciate, duk wani book dana yi kuna kaunar sa, i love You all fans_d'?



Comment'?

Share fisabilillah'?

Vote'?

Editing is not allowedL'


07082281566
NoorEemaan



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851


=???KYAUTAR KODA=???
(It's all about love, sacrifice, hatred and destiny)

*First edition*


Story and written by
Noor Eemaan


Wattpad
@NoorEemaan


https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.


_if you see any typing error, avoid it please_



Page 7-8


Yana isa gida ya zauna kan tabarma ko lura da Mahmah bai yi ba, jikin ta a sanyaye ta karaso wajen sa ta zauna hannun sa ta kamo cikin muryar tausayawa tace "fadeel what's it, lafiya kake?"


Kallon mahmah yayi da jajayen idanunsa, kana ya fada jikinta tamkar wani yaro karami yana sauke wani irin numfashi... Ya dauki mintuna goma masu kyau kana ya fara bawa mahmah labarin abinda ya faru yau..... Domin tun yana karami baya da wani abokin shawara sama da ita, idan ka gansu tamkar ya da kani.

Ta tausayawa fadeel sosai, tilon danta, domin ta gani baro-baro cewa ya faWa tarkon son yarinyar, cikin tausasawa tace " 'Dana Fadeel, meyasa ka sare? Meyasa ka sare da wuri haka? Kai namiji ne, namijin ma jarumi, bai kamata wani abu ya baka tsoro ba, dan muna matsayin talaka ba hakan ke nuni da cewa ba zaka iya auren wacce ta fi ka arziki ba, ina me baka umarni daka bayyana kanka a gareta, domin tun kafin na ganta na ji na fara son ta, duk abinda kake so dole nima in so shi, da gwaji akan san na kwarai, ka ji ko?"


Jinjina kai yayi, maganganun mahaifiyar sa na kara masa k'arfin guiwa, nan ya dan saki jiki ya fara bata labarin irin kyau da haduwar fadeelah, mahmah kuwa sai murmushi take tana fatan danta ya samu soyaayyar budurwar daya gama mutuwa akan son ta....



ASALINSA

Fadeel Abdul-basit dane ga Abdul-basit Muzakkir, tun yana da shekaru 7 mahaifin sa ya rasu. Asalin su yan jahar kebbi ne, aiki ne ya dawo dasu nan lagos, toh bayan rasuwar mahaifin fadeel suka fara shiga halin matsin rayuwa, ga yan'uwan baban fadeel basa ko taimaka musu, kasancewar mahmah mai zuciyar nema ce yasa ta fara sana'ar siyar da biredi akan titin layinsu, da wanna kudin ta cigaba da biyawa fadeel danta kudin school har ya samu kwalin degree a bangaren artist.

k'wararren mai zane ne domin a mintuna ?alilan zai zana mutum tsaf... Duk da haka bai yi girman kai ba, domin shi ke zama wajen sana'ar ta ya siyar mata da biredi, A cewar sa ta hutu a gida, amma wani zubin Mahmah bata yarda sai tace su tafi su biyu, har mamaki take domin ta dauka tunda yana da degree bazai iya siyar da biredi a bakin titi ba... har tambayar sa tayi domin ta kasa hakuri ya kuwa bata amsar cewa "mahmah idan naji kunya ko nuna girma kai banyi miki adalci ba, domin da biredin kika siyar har kika biya min kudin makaranta har na gama, dan haka ko da na samu aiki mai kyau da za a biya ni millions ne, toh zan iya cigaba da siyar miki da bread matuk'ar kina so kin kuma bani umarnin yin haka"

Sosai jikin Mahmah yayi sanyi domin kalaman sa sun ratsa zuciyar sa, hakan yasa take alfahari da shi...


Haka suka cigaba da rayuwar su gwanin sha'awa, sai dai Mahmah na boyewa Fadeel wani abu, wanda nan gaba zamu ji ko ma menene...


*CIGABAN LABARI*

Tsaye take cikin shigar sleeping wear's dan guntu da alama tashin ta daga bacci kenan, gaba daya hankalin ta na ga zanen dake manne a bangon dakin, ta rasa wanne yafi kyau cikin zane biyun, hawaye suka wanke mata fuska tuno cewa bata san wanda yake zana ta ba, wanda shine babban burin ta a yanzu...

Kwankwasa kofa da ta ji ana yi ne yasa ta yi sauri share hawayenta hadi da bada umarnin shigowa, Daddy'n ta ne ya bayyana, sallama dauke a bakin sa, murmushin k'arfin hali tayi ta isa garesa hadi da rungumesa tana cewa "good morning Dad"
Shafa bayanta yayi yana cewa "morning my beautiful princess, how was your night?" Daddy ya tambayeta cikin tsananin kulawa hadi da son yarsa.

"It pass great my hero Daddy" murmushi yayi kana yace "sai yanzu hankali na ya kwanta princess, domin kwana biyu na k'asa gane miki"

Raba jikinsu yayi yace "kiyi freshing up, kizo muyi breakfast ok, ni da Mommah na jiran ki" ya kare maganar yana bata light kiss a hagu da daman na kumatun ta kana ya fice...

Ajiyar zuciya ta sauke, tana yaba kulawa da son da Daddy'nta ke mata, kara kallon zanen ta yi kana ta fada bathroom.




*1 MONTH LATER*
(BAYAN WATA DAYA)

Motocin fadeelah ke sharara gudu kan kwalta kamar kullum, har sun wuce wanna restaurant din kawai taji gabanta ya fadi, taji hankali da tunanin ta ya kasa barin wajen, magana tayi wa driver'n dake tuka ta, take ya juya alakar motar zuwa restaurant din, ba bata lokaci suma sauran motocin suka biyo bayan motar da Fadeelah take ciki zuwa restaurant din,,,, bayan sun daidaita parking motocin, aka bude mata kofa ta fito cikin shigar suit na mata mai riga da wando hadi da karamin mafayi data yi rolling sai dan hand bag daya dace da kayan, duka brand din *HUGO BOSS* wanda yake cikin tsadaddun companies...


Wanna karon ma ta bawa bodyguards din ta umarnin shigowa tare da ita, bayan waiter yayi serving din ta da juice kadai kamar yadda ta bukata... Hankalin ta naga wayar ta kirar *Samsung Galaxy Fold2*
wanda ya dace da kalar kayanta, domin duk shigar da ta yi toh fa da wayar da take dauka, sannan mafi yawan lokuta wayar na kasancewa kalar shigar ta ne.



Lokaci zuwa lokaci ta kan kalli wajen a tunanin ta ko zata iya ganin mai zanen ta, sosai ta dukufa kan lissafin da take a wayar, da alama Mai Muhimmanci ne, kamar a mafarki, amma kuma ta san ba mafarki bane, kawai ta ga hannu dauke da cardboard paper irin na kullum yana miko mata, gaban ta ne ya fadi take ta fara bin hannun da kallo har ta sauke kan Kyakyawan fuskar sa, gabanta ya sake bugawa da karfi, mikewa tayi ta nuna shi da yatsa, cikin rawar murya tace "it's you, bana ko tantama Kaine! Kaine mai zana ni......"




_In sha Allah gobe ma zanyi k'ok'arin baku update, nasan na barku kuna ta jira, amma sai kun mun hakuri cos two book nake rubutawa at once, so ina buk'atar hutu a brain dina...._
Ina muku pure love d'?


07082281566
Noor




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851


=???KYAUTAR KODA=???
(It's all about love, sacrifices hatred and destiny)


_by Noor Eemaan_=???
'?


07082281566


https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.




Page 9-10

Dan shiru yayi, yana ?o?arin tara courage, at last ya Jinjina kai kawai alamun "eh" yayinda murmushin karfin hali ke dauke a fuskarsa, domin bai san a yanda zata karbe shi ba.

Tana shirin yin magana, bodyguards dinta suka zagaye Fadeel, sai karan saita bindigogin su kake ji, ko daya bai ji tsoro ba, sai bin su da kallo yake, cikin bacin rai Fadeelah tace "drop your guns and go away"


Cikin girmamawa suka ce "we are sorry ma'am" kana suka kalli Fadeel suka ce "sorry sir" jinjina musu kai yayi alamun ba komai.


Bayan barin su wajen fadeelah tace "da gaske Kaine mai zana fuskata? oh my God! Yau ina cikin farincikin"

Tace tana kallonsa idanunta sun kasa boye tsananin farincikin da take ciki, wanda hakan ya sanya Fadeel cikin tsananin surprise, yet happy deep down inside his heart "zauna dan Allah, na cika ka da surutu" Fadeelah tace tana nuna masa wajen zama.

Zama yayi yana sauke boyayyen ajiyar zuciya, yayinda fargaban rasa ta ke barin zuciyar sa a hankali "Me zaka ci ko sha, a kawo maka"

"A'a ki barshi nagode"

Shagwa6e fuska tayi tace "Allah bana jin dadi idan nayi niyyar yin abu wa mutum yace baya so"


Murmushi ya saki yana karantar halayen ta daga yanayin maganar ta, kana yace "kiyi hakuri amma bana jin ci ko shan komai"

"Ok fine, ba matsala" Fadeelah tace domin ita din ba mai son takurawa mutum bace.


Ruwa ta dan kurba tace "shin zan iya tambayar ka?"

"Kwarai kuwa ina jinki" ya amsa yana jin bugun zuciyar sa na karuwa.


Gyara zama tayi tace "meyasa kake boye kanka?"

Numfashi ya sauke, domin abinda yayi tunanin zata ce daban, sai da ya hadiye wani yawu, kana ya tuno yanda Mahmah ta karfafa masa guiwa akan ta yace "saboda ina tsoron rasa ki, domin a ranar dana fara ganin ki a daidai wanna wajen na kamu da tsananin son ki, naji tsoran bayyana kaine ganin cewa ke ba aji na bace..."


Fadeelah bata bari ya karasa ba, ta katse shi da cewa "Kai rago ne! da har ka kasa bayyana soyaayyar ka a gareni, ka azabatar da zuciyoyin mu, dame na wuce ajin ka? A rayuwar nan babu wanda ya wuce wani sai wanda yafi tsoron Allah, komai kudi da dukiyar da yake da shi kuwa, wanna dalilin naka be min ba, baka yi tunanin nima ina sonka ba, lemme say this ina sonka, ina kaunar ka mai zana ni" ta karasa maganar tana jifan sa da wani kallo daya sanya Fadeel jin sa on top, kana ya mike zumbur saboda farinciki yace "da gaske kina sona, zaki iya aure na?"

"Yes! Ina sonka kuma zan rayu da kai a ko wani hali"....


Sosai suke cikin farincikin ganin dukkanin su na son juna, hira suka sha har karfe bakwai da rabi kana suka farga cewa dare yayi.

Har bakin inda aka faka motocin ta suka karasa tare, bodyguards dinta kuma na tsaye dan nesa dasu.


"Zamu rabu bamu san sunan juna ba" Fadeel ya fada yana dage girar sa daya, murmushi tayi tace
"I'm Fadeelah" shima yace
"I'm Fadeel" sai suka saka dariya a tare ganin sun kira sunan su a lokacin daya.

"Fadeel da Fadeelah masu tagwayen suna, kin sani an hallace mu ne domin mu so juna, Kisa a ranki cewa har abada ni mai sonki ne, please ki kulamin da kanki, domin ke din ta musamman ce a cikin dubban mata"


Wani zallan farinciki ne ya sake bayyana a fuskar ta, she loves admiration, ta kuma lura yaba mutum da bashi kulawa is one of Fadeel's attitude, ba kuma tare da ta san zancen zuci ya fito fili ba tace "dama haka so yake da dadi?"

"Yeah darling, musamman in tare dake ne" Fadeel ya bata amsa.


Kunya taji ya saukar mata, domin bata yi tunanin ya ji taba.

"ki taim??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????aki bawan Allah da number, domin idan ba haka ba zan iya zaucewa kafin gobe matukar ban ji wanna d'ad'addan muryar ki tamkar busar sarewa ba"

Wani tsadadden murmushi na zallan farinciki ta saki, kana tace ya bata waya ta sanya masa number'n, take ya sanya mata wayar sa kirar *itel* mai madannai wanda kudin sa ba zai haura dubu uku da dari biyar ba, wanda da kyar ya hada kudin ya siya, a hakan ma second hand ce.

Bayan ta sanya masa ya ga lambar special ce, bai taba ganin tsararren lamba Irin wanna ba, Fadeelah ta nemi ya shiga mota su fara sauke shi, amma yaki, dole ta shige mota tana waiwayon sa, hannu suke dagawa juna har motocin suka bace a idon Fadeel....


Shi ma Fadeel keke-napep ya tara ya shige, wayarsa manne a hancinsa yana shakan dadaddan kamshin turaren ta, da kamshin ya kama wayar sa...

Isar sa gida ya fara rawa tun daga tsakar gida yana kiran "mahmah! Mahmah!! Mahmah!!! Where are you?"
Sai ya fara waka kamar haka

Sai ya Wora da cewa still cikin amon sautin waka
_Mahmah ki tayi ni murna_
_na samu mahadin rayuwata da ni da Fadeelah a Soyyaya_
Ya kara sa wakar ta sa da rungume mahmah data fito tun dazu tana taya shi rawar.


Hannun shi ta kamo suka zauna tace "my son Fadeel ka bani labari"

Nan kuwa ya fara bata labarin komai, ba tare da ya boye mata komai ba, sosai mahmah taji dadi ta kuma yi musu addu'ar fatan Alkhairi, har 12 na dare suna zaune suna hira wanda zallan labarin Fadeelah yake bata...


&&

?angaren fadeelah kuwa tana kwance kan gadon ta yi ruf da ciki, yayinda ta kurawa hotunan dake manne a bango ido, wanda yanzu sun dawo uku har da wanda yayi mata yau, wani murmushi take saki lokaci zuwa lokaci bata taba tsintar kanta cikin annushuwa kamar yau ba, tun tana kallon har ta fara jin bacci, duvet ta rufawa kanta, babu jimawa bacci ya dauke ta cike da mafarkin Fadeel...


*** *** *** ***


Babban asibiti ne a lagos wanda yawanci masu hannu da shuni ke zuwa. mahmah ce zaune a office din doctor Gabriel yana mata bayani kamar haka "madam condition dinki kara gaba yake, domin tun farko ya kamata a tari wanna cuta ayi miki maganin sa, maganar gaskiya yanzu baza a iya komai a kai ba, sai dai ki cigaba da shan maganin ki domin samu sauki kawai, duk da kin gaya min rashin kudi ne yasa baki yi saurin taran ciwon ba, kuma kamar yadda nayi alkawari zan cigaba da duba ki kyauta, kawai siyan magani ne naki, Allah ya baki lafiya"
doctor Gabriel ya karasa maganar hadi da mayar da medicated glass din sa ido

Hawaye Mahmah ta share tace "nagode sosai doctor Gabriel, Allah ya biya maka dukkanin bukatun ka na Alkhairi, i do really appreciate"

"Ameen madam" doctor ya amsa yana cigaba da aikinsa

A sanyaye Mahmah ta fito daga office din sa ta nufi pharmacy din hospital, kudi hadi da takardan da doctor Gabriel ya bata ta mika wa wata nurse, amsa nurse din tayi a wulakance kana ta cilla kudin hadi da takardan jikin Mahmah tace "ke dallah bar wajen nan, wanna asibiti yayi miki kama da na talakawa? Da zaki wani miki wata tsohuwar dubu da dari biyar dinki, ki bar wajen nan ko..."

"Ke! Baki da hankali ne?wanna matar sa'ar ki ce, baza ta iya haifar ki ba, hakika baki cancanci zama nurse ba, domin su da tausayi aka san su"

Fadeela da ta zo wucewa ke wanna maganar cikin tsananin bacin rai, yayinda bodyguards dinta ke tsaye da ita kamar kullum.

Kan Mahmah a kasa tana hawaye, ganin yanda wasu mutanen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login