Showing 12001 words to 15000 words out of 80179 words

Chapter 5 - KYAUTAR KODA Hausa Novels by NoorEemaan.doc

11 Nov 2025

3035

edited)

Cikin tashin hankali mara mitsaltuwa Fadeel ke wanna maganar.

Wasu hawaye ne suka sake zubowa a idanun Fadeelah tamkar an balle famfo. A karo na barkatai take son furta masa damuwar ta, damuwar da bata son tuno dashi, haka zalika duk wani family'n nata basa son tada maganar cutar ta saboda muninsa....


A karo na biyar ya sake cewa "please Darling say something, kada kisa zuciyata ta buga saboda damuwar da kike ciki, ki gaya min ko akwai wani abu dazan iya taimaka miki dashi please" ya kai karshen maganar tamkar zai rusa mata da kuka.



Hannu tasa tana goge hawayen fuskar ta, amma kara zubowa suke, a sanyaye kana cikin muryar kuka tace "ina...In...ina... d'auke da cutar *Koda* Yes kidney tsawon shekaru masu yawa, karshen zuwa na asibiti likitana yace bazan kara watanin biyu masu kyau ba zan mutu, zan mutu matuk'ar ba a samu wanda zai siyar min da kodar sa ba domin tawa tayi chronic, tayi muni sosai.... Shiru tayi tana jan numfashi kamar zata shide kana ta cigaba

Abu ne mai matuk'ar wahala a samu, domin shekaru masu yawa kenan da ake neman wanda zai siyar min da kodar sa amma...amma..." Shiru tayi saboda wani kuka daya sake taho mata, ajiyar zuciya ta sauk'e kana ta sake cewa "Ban sanar da kowa a gida abinda likitana yace karshe ba, not even Daddy, na kuma yi hakan ne domin kada hankalin su ya tashi, kaine mutum na farko dana fada wa...."

Sauran maganar ya makale sak'amak'on wani mugun kuka daya sake taho mata. har wani biyu biyu take gani saboda wani mugun ciwon kai daya saukar mata lokaci d'aya.


Kan Fadeel na kasa yayinda wasu hawaye masu zafin gaske ke bin kuncin sa suna diga kan tiles dake shimfud'e a kasan wajen.



Bai taba jin maganar dake barazanar tarwatsa zuciya da kwakwalwarsa kamar wanna ba. Fadeelah'nsa na dauke da cutar koda Sannan bazata kara watanin biyu masu kyau ba.


Ji yayi duniyar na juya masa baya, mikewa yayi da kyar yana dafe kansa kana a haukace ya fara takawa domin barin wajen yayinda zuciyarsa ke bugu tamkar zata fasa kirjinsa ta fito...



Wani sabon kuka ne ya sake zuwar wa Fadeelah zubewa tayi a kasa, cikin fitar hayyaci take cewa "Fadeel! Fadeel!! Fadeeeeeeeel!!! Please kada ka juyamin baya" sam bashi da alamar juyowa haka ta cigaba da kiran sunan shi tana kuka har ya bace wa ganinta.


Tamkar Fadeel d'in a gabanta tace "abinda nake gudu kenan, shiyasa na boye maka wanna ciwon nawa, ina tsoron kada ka juyamin baya, kamar yadda *Jameel* ya yi min, duk da ba shi da wani muhalli a zuciya ta amma naji ba dadi matuk'a, dan Allah my one come back to me bazan jure rashin ka ba, ka dawo muyi kyakyyawar sallama domin ina daf da mutuwa". Ta kai karshe maganar tana sake sakin kuka mai ratsa zuciya, kanta ta dora kan table din wajen ta cigaba da kukanta har idanun ta ya fara yaji kana ta tsagaita tana sauke ajiyar zuciya...



Ta kai awa daya a zaune, sannan ta mike domin barin wajen.
Babban glass baki ta kafa a fuskar ta, domin sam bata son kowa ya ga ta yi kuka, domin ta kasance mutum ce da bata son idan tana cikin damuwa ta sanya wani.

Sai dai ta makaro domin duk Wanda yaga fuskarta zai san tayi kuka Saboda wani mugun ja da yayi...


*** *** *** *** ***


Ikon Allah kadai ne ya kai Fadeel gida lafiya, domin a kafa ya taka har gidan. Saboda tashin hankalin da yake ciki sam bai ji wahalar tafiyar ba.




Mahmah na zaune a kujera tana shan ruwa taji ya shigo a haukace bako sallama, dakinsa ya nufa ya rufe da sakata. Kan kafitar sa ya fada, ya fashe da wani mugun kuka tamkar mace, kuka yake yana surutai shi d'aya, cikin damuwa Mahmah ta ajiye cup din hannunta ta nufi kofar dakinsa.



k'wank'wasawa take tana fadin "Fadeel my son, ka bud'e, meya sameka? Wani ya mutu ne ko wani abu ya faru? Ka bud'e ka gaya wa Mahmah'nka damuwarka kaji"



Ko motsi bai yi ba, domin bai san mahmah na nayi ba, kuka yake mai tada zuciya, kuka yake jin cewar fadeelah'nsa na daf da barin duniya, shi kam ya zai yi da rayuwar sa, idan Fadeelah ta bar duniya meye amfanin zaman sa babu ita???



*** *** *** ***

Bangaren fadeelah kuwa, koda isar su gida bata jira sun bud'e mata kofar mota ba, ta fita hadi da daga musu hannu alamun bata bukatar rakiyar su.
Cikin bin umarnin ta suka tsaya cak! A guje tayi bangaren ta tana kuka.

Yar aikin Fadeelah mai suna Elizabeth kadai ce a hada'dd'en falon d'aya kasance mallakin Fadeelah tana goge centre table, bata ko ji gaisuwar da Elizabeth d'in ke mata ba, Saboda halin tashin hankali da take ciki, bedroom d'inta ta shige hadi da murza key.




Da mamaki Elizabeth tabi Fadeelah ta da kallo, tayi matuk'ar mamakin ganin ta a wanna yanayi, domin sanin kowa ne cewa Fadeelah yar gata ce sannan mai yawan fara'a .


A fili ta furta "what's wrong with ma'am?" Sanin cewa bata da bai Mata amsa yasa ta cigaba da goge_gogen ta tana jin ba dadi domin har ranta tana kaunar fadeelah...



Da misalin 8:00pm kukun Fadeelah tsaye a bangarenta yayi bugun duniya shiru bata bud'e ba, ya kuma san tana ciki domin Elizabeth ta bashi tabbacin tana nan..

?arshe dai ya ajiye tsad'add'en tray di'n mai d'auke da aSincin ta akai ya fita.
(kasancewar shi ke mata girki, Emmanuel sunan sa, ?wararren chef ne d'aya iya gir?e_gir?en zamanin Wana nan namu na Nigeria da ma k'asashen ketare. Amma akwai ranakun da take warewa da a bangaren Mommah take cin abinci) wanna kenan.



Zaunen Elizabeth da Emmanuel suke a boy's quarters, tattaunawa suke kan fadeelah, cikin damuwa da tsoro Elizabeth tace "Emma anya bazamu gaya wa boss abinda ke damun ma'am ba, kasan halin boss ko, wani abu na samunta, kama mu zai yi fa, kasan yana ji da 'yar sa ko ehen"



Jinjina kai Emmanuel yayi cikin pidgin English yace "Eli na true you talk ooh, I swear boss no get joy at all, he fit shot us with that his big gun, stand up let's go and meet him" ya karasa cikin turanci mai k'yau.



A jere suka nufi bangaren daddy, suka tarar dashi zaune tare da Mommah data zo sanar dashi bata ji shigowar Fadeelah ba, ganin su Elizabeth ya hana mommah magana.
A dan tsorace su Elizabeth suka hada baki wurin fadin "Good evening boss"


Sai d'aya debi mintuna biyar idanunsa kafe kan jarida kana ya dago yace "Evening, how may I help you?" Murya na rawa suka sanar dashi, domin sosai suke jin tsoron sa, muryar sa mai dan kauri da tarin kwarjini ma ya isa ya sanya mutum a firgici.



"What!?" Yace yana mik'ewa da hanzari kana ya nufi side dinta cikin gudu-gudu Mommah na biye dashi cikin tashin hankali, fatan su kada su ji wani abu ko su ga Fadeelah'n cikin mayuwancin hali...





?wan?wasa kofar su Mommah keyi da iya karfi, sai dai ko motsin Fadeelah'n basu ji ba.

Can suka fara jin sautin k'ukan ta na tashi ?asa_?asa, kara rudewa Daddy yayi yace "my princess, ki bud'e mana ?inji, it's me your Daddy, and your Mommah too is here" ya kai karshen maganar yana kallon Mommah da idanunta har sun fara kowa ruwan hawaye.




A sanyaye Fadeelah ta zuro kyawawwan ?afafunta ?asa, ba ma ta ganin gabanta sosai saboda wani jiri da take ji, bud'e kofar tayi ta basu hanyar shigowa, cikin damuwa duk suka shiga jero mata tambayoyin akan meke damunta?



Kuka ta fashe dashi d'aya kara tayar musu da hankali, kan hadadden gadonta suka zaunar da ita yayinda suka zauna a gefe da gefen ta, ya zamana tana tsakiyar su.



Ganin har Mommah ta fara kuka yasa tayi shiru tana kokarin daina kukan. Sai da ta dauki mintuna goma masu kyau sannan muryar ta a shake tace "doctor Mahfouz said bazan kara watanin biyu masu kyau ba zan mutu domin kidney dina yayi failing, the last time dana je check up, sai tayi shiru na yan mintuna kana ta cigaba ya sanar dani cewa dayan kodar ma ta fara tabuwa, kuma har yanzu ba'a samu wanda zai siyar min da kodar sa ba"


_"innalillahi wa innah ilaihi raju'un"_

Mommah da Daddy suka hada baki wurin fad'in hakan. Kuka Mommah ta fashe dashi, yayinda wasu zafaffan hawaye suka biyo kuncin Daddy, tabbas da ba dan yayi namijin kokari ba, ba shakka kukan shima zai fashe dashi...

Sun dauki tsahon lokaci a wanna mayuwancin hali kana daddy yace "when last kika je asibitin?".



Cikin muryar kuka Fadeelah tace "Wancan watan ne " shiru Daddy yayi, gaba d'aya ya rasa abin yi, kenan a lissafi saura wata daya. Wasu hawayen ne suka biyo kuncin sa, tabbas yasan cewar cutar Fadeelah nada muni amma bai yi tunanin munin ya kai har da za a ce ga sauran watanin da zata kara nan gaba a duniya ba.

Tabbas bai ga amfanin tarin dukiyar sa matuk'ar yana kallo tilon 'yarsa na mutuwa a hankali ba tare da zai iya yin wani abu a kai ba. miliyoyin kudade ya saka kan wanna zai siyar da kodar sa wa tilon yarsa, daga nan gida Nigeria har kasan waje amma, har yau ba a samu ba.... (Ba komai kudi ke siya wa mutum ba)




*BAYAN SATI D'AYA*

Har yau Fadeel bai fito daga dakin sa ba, tun ranar, k'asancewar akwai dan karamin toilet a dakin sa yasa yake alwala a ciki yayi sallar sa a nan, gaba d'aya ya rame ya fita hayyacin sa.



Yana kwance kamar kullum idanunsa na siyayyar da ruwan hawaye yaji Mahmah na sake buga kofa.

Lumshe idanunsa yayi yace "Mahmah ki gafarceni, bazan bud'e miki ba, ki je Mahmah, mutuwa zan yi banga amfanin tawa rayuwar ba"

Mahmah dake tsaye bakin kofa ta dan ji sanyi a ranta, domin tun ranar d'aya rufe dakin sai yau taji muryar sa, cikin dan fada_fada tace "Fadeel ni Mahmah'nka ce, shin akwai wanda zaka raba damuwar ka dashi kaf duniya sama dani? Gaba daya ka sauya hali, yanzu umarnin nake baka ka bud'e kofar nan, ko nayi nesa da garin lagos na barka tunda baka bukatata a rayuwarka..."




Cikin sauri ya mike jin furucin Mahmah na karshe, bud'e mata kofar yayi kana ya tsaya kansa a kasa, kallonsa mahmah take yayinda idanunta ke zubar da hawaye ganin yadda yayi rama.
Jikinta ya fada yana sakar mata kuka tamkar wani yaron goye, wani dan sanyin _sanyin yake ji a ransa adalilin runguman d'aya yiwa mahaifiyar sa



Mahmah bata hana shi kukan ba, kanshi kawai take shafawa, sai daya yi mai isar sa kana ta riko hannunsa har kan tabarma suka zauna. A nutse ta shiga kwantar masa da hank'ali kana tace
"meya sanyaka cikin wanna halin tsawon sati daya yau Fadeel?"

Bai boye mata komai na cutar Fadeelah ba ya sanar mata... shiru tayi yayinda zuciyarta ta karye, taji tausayin Fadeelah matuk'a.
ta kuma sake tabbatar da cewa Fadeel, so mai zafin gaske yake wa Fadeelah'n tunda har ya shiga wanna damuwar mai yawa, zata iya cewa halin ta ya gado matukar tana son abu bata mai son wasa, haka zalika Fadeel...




A kuma daidai lokacin ne Fadeelah ta shigo layin gidan su Fadeel, kallon mutanen unguwar take cikin tausayawa, domin unguwar talakawa ne sosai, sai dai hakan bai hana su hada_hadar su cikin farinciki ba.

Tausayin masoyinta Fadeel ya sake kamata, daidai lokacin motar ya tsaya a kofar gidansu. Bin gidan take da kallon tana aiyana cewa yanzu Fadeel dinta na iya rayuwa cikin wanna gidan? Hawaye suka zubo mata, tunda tasan cewa kwanakin mutuwar ta na kara matsowa sai gabadaya ta sake dawowa wata shiru_shiru mara son hayaniya, bud'e mata kofa bodyguard dinta yayi ta fito a sanyaye ta tunkari cikin gidan yayinda gabanta ke bugawa domin bata san a wani yanayi Fadeel zai karbe ta ba...




_Gobe ma zanyi k'ok'arin yi muku update, nagode muku kwarai da add'uar da kuka yiwa yar kanwata da bata da lafiya, alhamdulillah jikin da sauki Allah ya bar kauna da zumunci my beautiful people_=?
?


#Share fisabilillah
#Comment
#vote

Editing is not allowedL'


I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*



=???KYAUTAR ?O?A=???
(its all about love, scracife, hatred and destiny)


*wattpad*
@NoorEemaan


ELEGANT ONLINE WRITER'S=???=???


https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.


Page 21-22

Sai da ta zo daidai soron gidan ta tsaya, gabanta na matsanancin bugawa... Tana iya hango Fadeel dinta da wata mata zaune kusa dashi wanda bata tantama mahaifiyar sa ce. A Kallo dayan da ta musu ta hango tarin damuwa a fuskokinsu.


Wasu hawaye ne suka sake zubo mata sakamakon mugun ramar da ta ga Fadeel yayi, jitayi tayi zuciyar ta ya karye, juyawa tayi domin barin gidan hakan yayi daidai da dago kan da Mahmah tayi...



"Wacece nan?"

Fadeelah taji saukar muryar Mahmah. Cak! ta tsaya yayinda gabanta ya fadi.


"Shigo mana" ta sake juyo muryar mahmah.


Waro ido tayi kana ta juyo a hankali, nufo su tayi bakinta dauke da sallama.

Waro ido Mahmah tayi idanunta kafe kan fuskar Fadeelah, har abada bazata taba manta wanna kamilaliyyar fuskar ba. Kallon_kallo aka shiga yi tsakanin su ukun.
ita Fadeelah, kallonta da Mahmah keyi ya dan tsorata ta yayinda Mahmah ke mamakin menene ya kawo Fadeelah gidansu? Fadeel kuwa mamaki yake ta yadda aka yi Fadeelah tasan gidan su.

"Fadeelah!" Suka tsinci muryar Fadeel ya kira ta, cikin wani amo mai wuyar fassaruwa.

Wasu hawayen farincikin ne suka zubo wa Mahmah, dama wanna ce Fadeelah'n fadeel dinta, wanna yarinyar mai Kyakkyawar zuciyar ce? ita ce kwanakin mutuwar ta saura wata daya? Hakika bata cancanci mutuwa a yanzu ba, domin rasa irin su a al'ummah babban rashi ne....


Durkusawa fadeelah tayi a kokarin ta na son gaishe da Mahmah, cikin sauri mahmah ta dago ta, ta rungumeta hadi da cewa "yata" sai kuma Mahmah ta fashe da kuka, wanda na zallan tausayin Fadeelah'n ne.


Shiru Fadeelah tayi itama hawaye na zuba a idanunta, duk da tayi mamakin ganin Mahmah na kuka, Fadeel kuwa mamaki yake a ina Mahmah ta san Fadeelah har haka? Domin yanayin ta ya nuna ta san ta din.

Riko hannun ta mahmah tayi suka zauna kan tabarma bayan ta shimfud'a wani zanin ta mai kyau akan tabarman Fadeelah ta zauna.

Da ido Fadeel ke binsu ya kasa ko da furta kalma daya ce, da hannu Mahmah ta kira shi alamun yazo ya zauna kusa da su.
Bai yi musu ba ya zauna gefen Mahmah. Cikin sanyi da muryar ta mai dadi tace "Ina wuni Mahmah"
Murmushi dauke a fuskar Mahmah tace
"lafiya lau 'yata, kina lafiya?"
"Lafiya alhamdulillah" ta amsa cikin girmamawa.

Wani murmushin mahmah ta saki, domin sosai take jin dadi a ranta, ganin cewa Fadeel d'inta ya samu mace mai sanin ya kamata, yarinyar da take so sosai, ashe itace muradin ran danta.

" 'yata kin manta ni ko?" Mahmah ta tambaya.

Dan satar kallonta Fadeelah tayi a kunyace kana tace "eh Mahmah ban shaida ki ba"

Wani murmushi Mahmah tayi kana ta fara bata labari ko ince ta basu, saboda taga kamar fadeel yana cikin rudu.

Jinjina kai Fadeelah tayi, ba shakka alkhairi danko ne, gashi ita ta manta fuskar Mahmah amma, ita ta tuna ta ta,
tabbas ta tuna ranar sai dai Mahmah'n ce ta manta, domin ranar tana cikin matsanancin damuwa, Saboda a ranar ne doctor Mahfouz ya sanar da ita sauran kwananinta a duniya.


Bangaren fadeel kuwa, sai yanzu ya gane inda Mahmah tasan Fadeelah, yayi mamaki ya kuma yi farinciki jin cewa duk yabon hadi da kauna da Mahmah take yiwa yarinyar da suka hadu a asibiti Fadeelah'nsa ce. Sai dai murnan sa ragagge ne idan ya tuna cewa kwanakin mutuwar abar kaunarsa saura kwanaki kalilan a duniya.

Dan janta da hira Mahmah keyi domin ta saki jikinta, hadi da yi mata nasiha kan ta fawwalawa Allah komai, yana sane yana kuma ji, Sannan damuwa bata maganin komai. Da wanda zuciyoyin su ya dan yi sanyi.


Mik'ewa Mahmah tayi tace " 'yata me zan dafa miki?"

Murmushin k'arfin hali ta saki kana tace "ba komai Mahmah nagode"

"A'a A'a dole kici fa, ko kin bani zabi na girki miki duk abinda nayi niyya?"

Kasancewar bata son musu yasa tace "toh Mahmah"

Wajen madafa mahmah ta nufa ta fara kiciniyar dora musu girkin...

Ajiyar zuciya ta ji kusa da ita, hakan yasa ta kalli gefen ta, Fadeel taga ya matso kusa da ita, bata ce komai ba tayi kasa da kanta.

"My Darling" ya kira ta, shiru bata amsa ba.
"My Darling" ya sake kira nan ma shiru
'My Darling pleaseee" ya kira a karo na uku cikin magiya.

Idanun ta suka ciko da kwalla, a sanyaye kana a hankali tace "meye laifina? Me nayi maka daka zabi ka hore ni ta wanna hanyar? Ka tafi ka barni ba tare da ka tsaya munyi Kyakyyawar sallama ba, bayan kasan kwanaki mutuwa ta na kusanto ni, a haka kake cewa kana sona? Gashi ni na kasa jurewa nazo domin inyi sallama da kai ko hakan zai sa na samu salama a kabarina" Ta karashe maganar cikin wani mugun kuka daya taho mata. Saurin toshe bakinta tayi, domin bata son Mahmah taji sautin kukan nata..

Hawaye ke bin fuskar sa, ba kadan ba kalaman ta suka shige sa, bazata fahimci halin da yake ciki ba, shi kadai yasan halin tashin hankali da yake ciki right now.

Cikin murya kuka yace "am so sorry Darling, is not what you think, I swear you have no idea akan irin tashin hankalin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login