Showing 27001 words to 30000 words out of 80179 words

Chapter 10 - KYAUTAR KODA Hausa Novels by NoorEemaan.doc

11 Nov 2025

3139

nufi wajen fadeelah.


Gaban Fadeelah ne ya fadi lokacin da ta yi arba da Jameel, bata manta kalaman sa na karshe a gareta ba.



_I guess we should break up the relationship, domin kina da cutar koda. A tsarina bazan iya auran mace mai wata cuta ko nakasa ba, bazan iya da jinya ba, domin auren hutu da jindadi nayi planing a rayuwa ta_

Kalaman kan yi mata zafi a du? sa'ilin data tuna, duk da cewa bata son shi, Daddy ke son tarayyar su hakan yasa ta daure take kulashi a da. Isowar sa wajen ya katse mata tunanin ta.



"Hey my beautiful fiancy, am happy for you"


Cikin Wauriya tace "Thanks"

Wani hada'dd'en mukulin mota kirar *BUGATTI CHIRON PUR SPORT* hadi da dan kunnen da sarka na zallan gwal(gold) Wanda kudinsa ya kai *MILLION 20* ya bata hadi da cewa "here is your birthday gift" babu abinda sarkar nan keyi sai daukar ido duk da yana cikin wani kyakkyawan box din sa.
Kasancewar ita din ba mai wulakanta mutane bane yasa ta karba kana ta furta "Thank you" domin har ranta kyautar bai burgeta ba.


Daddy kuwa wani madaukakin murmushin farinciki ne ya wad'atu a fusk'ar sa, haka zalika wasu daga cikin mutanen wajen kyautar ta birgesu, dama haka rayuwa take idan kana tunanin ka fi wani, tofah akwai Wanda ya fika tabbas! Domin kowa ji yake ya bada kyauta ta kece raini, sai da Jameel ya gabatar da kyautar sa suka ga nasu bai kai na Jameel tsada ba.



Gaban speaker Jameel ya tsaya yace "am so happy today is my girl birthday, and also my wife to be"



Ihun murna hadi da tafi irin nasu na wayayyu wajen ya dauka, kana aka saki wani romantic waka irin ta masoya.



Take zuciyoyin Fadeel dana fadeelah suka buga da k'arfin gaske a tare, kallon sa fadeelah take tana mamakin rashin Hankali irin ta sa, yayinda Fadeel ya ji wani yanayi mai wuyar fassaruwa, take kansa ya shiga tsara masa, ya fara jin juwa, a haukace ya bar cikin hall din idanunsa jajir tamkar an watsa masa barkono





_poor fadeel_=?+?=???





(Assalama alayk'um habibtie's am so sorry jiya kun jini Shiru, wutar ta lalace sai da magariba aka gyara. Naga texts dinku, ina godiya da kauna.
Gobe ma zanyi kokarin Baku sabon updates, Noor loves you all=???)


#Share fisabilillah
#Comment
#vote



'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*



=?????AUTAR ?O?A=???
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)


Written by
Noor Eemaan



Wattpad
@NoorEemaan


https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.


ELEGANT ONLINE WRITER'S=???=???



EDITING IS NOT
ALLOWEDL'




Page 29-30

(Not edited)

Da kallo Fadeelah ta bishi yayinda idanunta suka ciko da kwalla, sai dai bata basu damar zubo wa ba. Ta sani cewa fushi yayi, domin ta hango kishi mai zafin gaske a idanunsa....



Wani haushi Jameel din ne ya kamata, haka dai aka cigaba da gudanar da birthday party cikin farinciki da annushuwa, banda fadeelah da hankalin ta ke tashe, sai dai mutum ba zai gane hakan kai tsaye ba, domin ita sam bata son damuwar ta ya shafi wasu.



Sai karfe takwas aka tashi daga birthday party'n, suka dawo gida, har karfe tara manyan masu hannu da shuni wandanda basu samu zuwa birthday party ba na zuwa har gida domin taya Fadeelah murnan zagayowar ranar haihuwar ta.



Sai karfe goma ta koma part dinta cike da gajiya, kasancewar tayi sallah a part din Daddy ya sanya ta fada Wanka, ruwan zafi ta shiga watsa wa fresh skin dinta domin gajiyar jikin ta ya warware. *LAURA MERCIER ALMOND COCONUT MILK shower gel* ta sha murzawa a farar kana lallausan fatar ta, bayan ta gama ta fito daure da towel sabanin yawan lokutan da ta fi amfanin da bathrobe.


Wani lotion mai kamshi ta fara shafawa a jikinta in a slow motion, kallo daya zaka mata ka hango zallan damuwa Cikin idanunta. Bayan ta gama ta bude closet dinta na zallan glass, ta ciro wata T-shirt na company *Herm?s* wine color, ya sauko Mata har saman cinyarta.




Wani black hula ta sanya a kanta ba tare da ta damu da taje gashinta mai tsayi da bai fiye cika ba. domin bata da kuzarin taje kan Saboda halin damuwar da take ciki.




Dad'add'an turaren *TOMFORD OUD WOOD* ta fesa sama_sama kana ta fada kan gado tana sauke ajiyar zuciya. Kurawa hoton da suke manne a bango ido tayi, Wanda ya kusa mamaye bango gaba-daya saboda yawan sa, tsayar da idon ta tayi kan zanen hotunan Mahmah kala biyu data sa Fadeel ya zana mata, sosai take jin soyaayya, kauna, girma, hadi da darajar Mahmah duk da bata raye kuwa. Numfashi ta sauke a fili tace "Allah yasa kin huta Mahmah" hoton zanan Fadeel ta kurawa ido, fuskar sa dauke da murmushi, idanunta suka ciko da kwalla tuno yanayin daya fita daga cikin hall din dazu.



Number Fadeel ta kira, har ya fara ringing ta katse sak'amak'on knocking data ji a bakin kofa
"Yes come in" tace idanunta kafe kan kofar shigowa.



Daddy dake sanye cikin jallabiya kirar Cairo ya shiga bakinsa d'auke da sallama. Amsawa Fadeelah tayi a sanyaye. Kan gadon ta ya zauna hadi da cewa "birthday girl ya gajiya?"



Murmushin karfin hali tayi "wallahi Dad, am so tired" ta fada a shagwa'be. tana dora kanta kan kafadar Daddy'n.


Shafa kanta yake kana yace "kinyi sallama da Jameel kuwa kafin ya tafi?"


Dan bata rai tayi, domin ko sunan sa bata son ji "eh Dad" tayi karya.


"That's Good my princess" cewar Daddy yana kokarin yin magana idanun sa suka sauka kan zanen hotunan fadeelah, Fadeel, hadi da Mahmah.



Cikin mamaki, domin bai taba lura ba yace " my princess hotunan zanen ki sunyi matuk'ar kyau, hakika wanda ya zana ya kware matuka. Amma waye wanna matashin da matar dake gefensa?"



Gabanta ne ya dan fadi, duk da taji dadin yabon da fadeel ya samu daga wajen dad, abin ya dan mata mamaki domin dad ba komai yake yabawa ba. a fili tace "suna da matukar muhimmanci a gareni Dad"

Dan shiru Daddy yayi kana yace "but ya akayi ban san su ba?"

A shagwa'be tace "please Dad!" alamun su bar maganar.

Sarai ya fahimci abinda 'yar tasa ke nufi dan haka yace "it's alright, dama na shigo ne domin duba lafiyar ki good night I love you".


Murmushi tayi, ita kanta tasan kaunar da Daddy ke mata bana wasa bane, a fili tace " love you too Dad" hadi da bashi sumbata a kumatu.
Shi kuma Daddy ya bata a goshi kana ya bar da??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????kin cike da kaunar 'yar tasa.



A karo na hudu kenan ta cigaba da k'iran Fadeel sai dai har wayar ta katse baya daga kiran. Bata hakura ba, ta sake dialing number shi...
Daga bangaren Fadeel kuwa a fusace ya daga wayar, Cikin murya da amon sa ke fidda zallan tashin hankali hadi da halin matsanancin kishi da yake ciki yace "what!?"



Kuka fadeelah ta fashe da shi sak'amak'on kakkausar muryar daya yi amfani da shi.
"Ka...yi haku'ri please"
Daga bangaren Fadeel kuwa lumshe idanun sa yayi yana jin kukan ta har cikin zuciyar sa, ajiyar zuciya ya fara saukewa a dalilin sa na son daidai ta fushin sa.



Furzar da wani huci mai zafi yayi "waye shi?" Ya fada cikin zallan kishin Jameel din.

"Please my one ka bar maganar shi, sam bashi da wani muhalli a zuciyata, dan abokin Daddy ne." Ta fada wasu hawaye na sake bin kuncin ta.



"Kenan saurayin ki ne?" Ya sake jefo mata tambaya yana kokarin controlling kishin sa.



"A'a ni ba saurayi na bane, ko da can bana kula shi, kai nake so my one, kuma har abada kai zan so"



Lumshe idanun sa yayi yana jin wani sanyi dadi na ratsa shi, ko ba komai ta nuna tafi son shi kan Jameel.



Wasu tagwayen ajiyar zuciya ya sauke kana yace "am sorry da fadan da nayi miki, I...i can't just control my self, ina kishin ki sosai fadeelah, i love you"


Wani dadi ne ya ratsa zuciyar fadeelah, Cikin muryar ta mai dadi tace "baka min komai ba my one, I love you too"



"Baka manta bako? jibi zaku hadu da Daddy"
Murmushi yayi hadi da cewa " my Darling kenan, ina sane amma, yakamata ki sanar dashi zuwan nawa ko?"




"Toh in sha Allah, zamuyi magana gobe" ta fada still da murmushi kan fuskar ta, haka dai suka cigaba da hirar su irin ta masoya masu yiwa junan su kauna domin Allah.



*WASHEGARI*
Bayan sun gama having breakfast a part din Mommah Kamar yadda suka fi yi a yawan lokuta.


parlour'n ta suka dawo suka zaune, Fadeelah na shirin yi masa maganar Fadeel ta ji saukar muryar Daddy kamar haka "princess alhaji Sa'eed ya kira ni jiya bayan na bar dakin ki, akan Jameel yana son ayi auren ku nan bada jimawa ba, ban wani bashi wata gamshashiyyar amsa ba, domin har yanzu ke yarinya ce karama, bana jin zaki iya d'aukar responsibility na aure" Daddy ya fada Cikin iyakar gaskiyar sa, domin shi kullum ganin fadeelah yake tamkar yar 15years.




Duk da gabanta dake faduwa hakan bai hanata yin murmushi ba, hannun Daddy ta riko tace "Dad ta yaya kake tunanin na yi kankanta da daukar ragamar rayuwar aure ? Dad ka tun ina da shekaru 19 kabar min ragamar kula company din ka. Na taba failing dinka Daddy? I have ever failed you dad? Na taba yin wani abu daya dakusar da company'n? An taba rasa wani abu, ko wasu kudade sun bata, tunda ka bar company'n a karkashin kulawa ta?" Ta karasa a ladabce.



Numfashi Daddy ya sauka hakika babu karya cikin abinda 'yarsa tace "ba ko daya my princess, ina matuk'ar alfahari dake domin kin kawo ababen cigaba a company'n sosai, zan bawa mahaifi Jameel damar turowa"




Gaban ta ne ya sake faduwa, kuka ta fashe dashi daya tayar da hankalin shi, dama Mommah da ta karaso falon yanzu, cikin damuwa daya bayyana a fuskokin su suka shiga tambayar ta meya sata kuka.




Cikin shesheka tace "ni bana son Jameel, akwai wanda muke tare da shi".



Maganar ta ya soki Daddy matuk'a, amma farincik'in diyar sa ta fiye masa komai, don haka yace " yi shiru my princess, ki daina kuka kar kiyi fever, zaki auri Wanda kike so kinji, a ina yake, dan waye shi a kasar nan?"



Cikin muryar kuka tace "gobe Dad zai zo ya gaida ku"



"Alright, Allah ya kaimu" Dad ya fada yana share mata hawaye.

Mommah ce ta janyo ta jikin ta, cikin rarrashi ta shiga debe mata kewa haka dai har ta sake suka cigaba da hirar su gwanin burgewa...


&&&

WASHEGARI

4:00pm

Tsaye Fadeel yake a dan nesa da tafkekken gate din su Fadeelah, kamar yadda fadeelah tayi masa kwantance, ga sojoji da Daddy yayi hayan su birjik zagaye da katafaren estate din. Girma estate din ya tsorata shi, domin duk wanda yaga estate din yasan ba kananun kudi aka kashe wurin gina shi ba. Duk da jikinsa yayi sanyi amma sam baza ka fahimci hakan ba Saboda jarumta da dakiyar sa. Maganar Mahmah kan soyaayar Fadeelah na karfafa masa guiwa...




Unguwar shiru baka jin motsin komai, babu kananun gida ko daya a unguwar, wayar sa kirar ITEL daya sa aka gyara masa, ya yi dialing number fadeelah ya sanar da ita yana waje, saurin kashe wayar yayi sak'amak'on wani ihun murnar Fadeelah daya cika dodon kunnen sa.. Mayar da wayar aljihu yayi yana sakin murmushi daya sanya beauty point (dimple) din sa lo'bawa.

Shakka babu Fadeel yana da mugun kyau, duk da kasancewar shi baki, domin bashi da haske ko kodan, dogo ne mai faffadar k'irji, idanunsa manya fararen kal, lips d'insa karami ne ja masu dan tudu kadan, yana da kwantaceccen saje daya Kara kawata fusk'ar tasa, dukkanin jikinsa gargasa ne daya kwanta luf_luf gwanin burgewa... (Kadan daga cikin kyau da haduwar Fadeel kenan)




Cikin girmamawa daya daga cikin masu tsaron gidan ya bud'e wa fadeelah gate. Yayinda bodyguard dinta shida suka biyo bayanta domin yi mata rakiya, kamar yadda Daddy ya basu umarnin Kula da lafiyar ta. Tsayawa tayi cak! Hadi da ce musu "ku koma, ba nisa zan yi ba"



Cikin girmamawa suka koma cikin, tun daga nesa suke jifan juna da murmushi na zallan kauna.
Shima Fadeel ganinta ya sa shi fara tako wa domin cin mata, kallonsa take, domin wani mugun kyau ya kara mata, wata shadda ce a jikinsa mai saukin kudi dark blue anyi masa dinkin zamani daidai rufin asiri, yayinda kafarsa ke sanye cikin wani takalmi na fata shi ma mai arahar gaske, sumar sa da bai fiye laushi ba, tamkar dai na wasu mazan mu yan Nigeria, ya taje shi.
Duk da duka kayan jikin sa masu araha ne, amma kayan yayi masa kyau, domin iya daukan Wanka a jini yake, kana iyawa ce, duk arahar kaya kuwa.




Sai da suka bata mintuna biyar duk suna hirar su kana tayi masa jagora suka nufi cikin gidan.
A fakaice Fadeel ke bin motocin da ke parking space sun fi hamsin da kallo, kuma duka babu karamin mota, gidan kanshi abin kallo ne, idan wani attajiri ya shigo gidan zai sarawa ginin, hadi da tsaruwar gidan, balle shi talaka.


Su kansu ma'aikatan gidan sun yi mamakin ganin fadeel, domin tunda suka fara aiki basu taba ganin wani talaka ya rabe gidan ba, amma gashi yau sun ga talaka da diya mafi soyuwa a ran professor Imran mai naira.



A falon Daddy ta sauke shi kamar yadda Daddy'n ya bukata.
Abubuwa kala_ kala na ci dana sha fadeelah ta sa aka kawo masa, snacks, drinks, abinci, fruits, da dai sauran su, amma bai taba ko daya ba


"My one please kaci kafin Daddy ya sauko, yana sama"


Murmushi yayi, duk da baya jin zai iya cin komai, amma Saboda kar taji ba dadi yace "don't worry Darling zan ci"



Murmushi tayi tace " toh, bari na kira Mommah nah ku gaisa "
Tana fadin haka ta fita da dan saurin ta, da kallon so ya bita kana ya sauke ajiyar zuciya.



Babu jimawa suka shigo tare da Mommah, cikin girmamawa ya gaida ita, Mommah ta amsa a sake, ta danyi mintuna biyu kana ta basu waje tana ganin dacewar fadeelah da wanna matashin... Domin sam bata lura da kayan jikin sa ba, kasancewar ta mace da bata fiye yiwa mutum kallo mai yawa ba.

Ganin babu wani expression mara dadi daga Mommah ya sanya Fadeel jin relief a ransa, yana fatan kada ya samu matsala daga wajen dad ma.
Hirar soyaaya suka cigaba da yi, bayan mintuna talatin suka fara jin karar takun takalmin Daddy na saukowa daga saman upstairs (bene)...



_may be ku jini gobe, may be not_=??



Vote and follow me on wattpad fisabilillah @NoorEemaan




#Share
#Comment
#Vote


'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*


=?????AUTAR ?O?A=???
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)

*First edition*


Story/written by
*Noor Eemaan*


*wattpad*
@NoorEemaan



ELEGANT ONLINE WRITER'S=???=???


https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.




TO MY LOVELY AND BEAUTIFUL FANS=???=???
May Allah protect us all from bad calamities, disease and guide us all in the right path.
AMEEN.



EDITING IS NOT ALLOWEDL'



Page 31-32

Haka kawai Fadeel yaji gaban sa ya fadi, duk taku daya da Daddy zai yi da bugun zuciyar sa yake fita, amma bai dago k'ansa ba.
Bayan Daddy ya gama saukowa, yayi wa kansa mazauni kan Waya Waga cikin had'add'un kujerun falon yana gyaran murya idanunsa kafe kan Fadeel.


"Barka da saukowa Daddy, ina wuni?"
Fadeel ya fada cikin calm and cool voice dake nuni Wa girmamawa ga Daddy.


Shiru wajen ya d'auka, Daddy bai amsa gaisuwar ba, sai idanunsa Wake ?afe kan na fadeel. Tun daga yanayin shigar Fadeel din, ya ji bai yi masa ba, tun dazu yana tsaye bakin window part d'insa, yaga shigowar Fadeelah da Fadeel. Ya kasa yarda cewa wanda ke shirin zama suru?insa, mijin diyar sa mafi soyuwa aran sa ne, ya shigo cikin ?atafaran estate din sa a kafa? Yake
Kuma sanye da wata shadda dako masu gadin gidansa zasu iya bawa wani kyautar sa. "impossible" ya aiyana a ransa.
Domin ya sake tabbatarwa yace "my Princess dan bamu waje"


Fadeelah da idanunta suka ciko da kwalla ganin Daddy bai amsa gaisuwar fadeel ba ta jinjina k'anta hadi da Mik'ewa ta bar falon tana waigensu...



Wani kallo dake nuni da kaskanci yayi wa fadeel, kana cikin murya a dan kausashe yace "Waye kai? Waye mahaifin ka a kasar nan?"



Wani abu mara dadi Fadeel ya hadiya, cikin girmamawa yace "Sunana Fadeel Muzakir, ni dan asalin....."



"Ba wanna nake son ji ba, waye mahaifin ka, wani mukami yake dashi a kasar nan? Ban tambaye ka asalin ka ba" Daddy ya katse shi a zafaffe.



Take idanun Fadeel suka sanja launi zuwa ja, duk da haka yace "iyayena duka sun mutu, sannan su din ba kowa bane a kasar nan ina......."
Saurin katse shi Daddy yayi da cewa "what!? Kana nufin kai din talaka ne fakiri? kuma kace kana son 'yata, wait a minute! wanna katafaran estate din yayi maka kama dana talakawa irin ka, ko ma'aikatan gidana babu talaka, domin bana hada inuwa dasu, kayi babban kuskuren zuwa estate din nan, 'yata ba sa'ar yin ka bace, ina so kasani daga yau sai yau, kada na kara ganin ka rabi 'yata domin baka ko kama kafar ma'aikatan ta ba. Wai meyasa ku talakawa kuke da kwadayi ne? kai a ganin farko daka mata tayi maka kama da mai arahar da za ka iya aure? Kasani cewa ni PROFESSOR IMRAN MAI NAIRA bazan iya bawa talaka fakiri auren ?ata ba, ka fita daga harkan ta, kayi nesa da rayuwar ta, idan ba haka ba. Hmmmm zan batar da kai ta yanda ko sunan ka baza ka iya tunawa ba, zan batar da kai ta yanda ko hanyar garin Lagos aka ambata zaka girgiza, idan kuma kudi kake so ko million nawa zan baka ka fita daga rayuwar 'yata, kayi nesa da ita, tunda ka siye zuciyar ta"



"Ba....bb...na...bukatar komai sai auren

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login