Showing 6001 words to 9000 words out of 80179 words

Chapter 3 - KYAUTAR KODA Hausa Novels by NoorEemaan.doc

11 Nov 2025

3053

basa ganin mutuncin talaka, maganar Fadeelah ne ya katse mata tunanin ta...

"Akan me kike mata wanna fadan kamar sa'ar ki?"

Kan nurse a kasa domin ta san wacece fadeelah da irin arzikin su

"magani zata siya shine ta miko dubu daya da dari biyar"

"Nawa ne kudin maganin" inji Fadeelah.

Nurse tace "Dubu goma ne"

"Daman akan wasu dubu goma kike gaya mata wadannan maganganun? Toh ki bata maganin" Cewar fadeelah tana hararan nurse kana tace
"Guards! Ku bani jakar kudi" Cikin sauri daya daga cikin bodyguard dinta ya miko jaka mai cike da kuka, fiye da dubu goma ta bawa nurse hadi da cewa "be careful, kina daf da rasa aikin ki matu?ar kika cigaba a haka" Fadeelah tace tana sake hararan nurse din domin ba karamin haushi ta bata ba.

Juyowa tayi ga Mahmah tace "kiyi hakuri dan Allah Mama"

Murmushin karfi hali Mahmah tayi tace "nagode sosai yata, Allah ya biya ki da Alkhairin sa ya baki miji na gari"

Da ameen fadeelah ta amsa kana tace "Mama ga wanna ba yawa Ko dan zuwa asibiti" ta fada tana miko mata rafa biyu na 1k.

"A'a yata ki barshi" inji mama har cikin ranta.

"Dan Allah Mama ki karba, idan ba haka ba bazan ji dadi ba" Fadeelah tace tana sanya kudin cikin ledar maganin hadi da ficewa daga asibitin....


Addu'a Mahmah ke bin ta dashi har ta bace wa ganinta, dama akwai sauran masu kudi wadanda suka san darajar talakawa a duniya? take taji son yarinyar a ranta, tana fatan danta Fadeel ya samu mai Kyakyyawar zuciya kamar wanda yarinyar.


Fita Mahmah tayi daga asibitin ta tari keke- napep, a ranta tana cewa dole zan bawa Fadeel labarin wanna yarinyar....




_Idan kunga typing error kuyi hkr ban tace ba (editing) saboda na gajiya..._



Kuyi manage wallahi nayi typing, yau ma ya goge, dan dai nayi alkawari yi muku yau da bazan yi ba,
sai gobe, saboda haushi wlh...
Ku cigaba da bina domin labari bai soma ba=??



Noor na muku sahihiyar kaunad'?



Vote and follow me on wattpad
@NoorEemaan


Share fisabilillah


Comment domin kara
min k'arfin guiwar typing


Editing is not allowedL'


I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*




=???KYAUTAR KODA=???
(Its all about love, sacrifices hatred and destiny)

_by Noor Eemaan_=???
'?

07082281566



Saboda Allah da manzon sa (s.a.w) vote and follow me on=?G?
Wattpad
@NoorEemaan>??


ELEGANT ONLINE WRITER'S=???=???


Congratulations once again sweetheart (nimcyluv) Allah ya kara daukaka. Alkhairi Allah ya kai muku writers da readers a kokarin ku na nuna wa the famous writer na'imah sulaiman(nimcyluv) kauna=?O?=???


https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.



Page 11-12

............Cikin adaidaita sahun ma tunanin Fadeelah na nan daram a ranta sa, babu abinda yafi daukar hankalinsa gami da Fadeelah kamar nutsuwa, mutunci da sanin daraja dan Adam...


&&

Daidai kan layin su mai adaidaita sahu ya sauke ta, ta mika masa dari biyar yace babu canji, babu ko dar tace ya rike sauran canjin(su mahmah an samu kudi yau lolz).
Godiya mai adaidaita sahu ya dinga zuba mata, ji tayi wani yanayi mai dadi na shigarta, wai yau ita ce da bawa wani kyautar kudi, ina ma ta yi arziki data yi farinciki domin zata cigaba da tallafawa marasa shi, ba shakka a duniya ka fi wani, wani ya fika, duk yanda ka kai ga cewa kai talaka ne, sai ka ga Kai mai arziki ne akan wani ko wata...


Wani babban store da ake siyar da dukkanin kayan abinci ta nufa dake daidai kan layin na su, da dubu dari da ashirin tayi siyayyar kayan abinci data san zai dade musu, zuciyar ta fall da saka wa Fadeelah albarka, yan shagon suka bada akori-kura aka zuba kayan sannan ta shige gaban akori-kuran suka nufi cikin layin su yan shagon na ta zuba godiya, a ranta tace "talaka bawan Allah" dama haka masu kudi ke jin wanna alfaharin musamman idan ana zuba godiyar nan, a fili kana a sanyaye tace "Allah ya iya mana" direban akori-kura ya kuwa amsa da "ameen Hajiya" murmushi ya subuce mata jin an kirata da hajiya lallai idan baka dashi ka sha kallo...


Daidai kan kofar gidansu mai akori-kura ya tsaya kana ya fito ya shiga sauke mata kayan, sai daya sauke duka kana ya fara shigar su cikin gidan, ya kuwa samu Fadeel zaune gaban murhu yana fifita wuta da alama girki yake... Da kallon mamaki Fadeel yabi mai akori-kura, ba tare da ya iya furta koda kalma daya ba, domin ya gama bayar wa batan gida mai akori-kuran yayi, ajiye muficin yayi ya bi bayan mai akori-kuran... Wani zallan mamakin ne ya sake kama shi ganin Mahmah a tsaye. "Mahmah" ya kira sunan ta muryar sa na bayyana mamakin da yake ciki..


Murmushi mahmah ta sakar masa ba tare da tace komai ba, kallon ta kawai yake kamar yaga sabuwar halitta, ganin idon mai akori-kura ya hana shi yin magana
Bayan mai akori-kura ya gama shigar da kayan, Mahmah ta zaro dubu biyu ta bashi, da wani mamakin dauke a fuskar sa ya sake bin Mahmah da kallo ko ina ta samu kudi? godiya sosai mai akori-kura ya dinga zuba wa yayin da Mahmah ta ja hannu shi suka shiga gidan, kan tabarma ta zaunar da shi ita ma ta zauna kana tace "nasan damuwar ka Fadeel, na kuma san tambayar dake bakin ka...."


Nan ta shiga bashi labarin haduwar su da Fadeelah, amma ta biyo abinda doctor Gabriel yace, shima yayi mamaki ya kuma ji haushi da tsanar nurse din, domin babu abinda ya tsana kamar a wulakanta masa uwa koda kallon banza ne, baya so.


Ajiyar zuciya ya sauke a fili kana yace "amma Mahmah da baki karbi kudin ta ba, ni bana so wani ya miki abu matukar bani bane, ina kuma fatan Allah yasa na kai minzanin da za kiji dadi har ki bawa wasu, sai wani yaba ta kike dan baki ga fadeelah ta bane, na tabbata ta fi wanna komai da kika lissafo" ya karasa cikin yanayi na shagwa'ba...


Dariyar Farincikin mahmah ta saki, saboda Kalmarsa ta karshe.
Ta san shi sarai yana da zuciyar nema sannan baya dogara da mutum, wanna karsashin nasa na burgeta sannan tana alfahari da hakan, kuma zata cigaba da alfahari da hakan ko da bayan ranta ne.


"Fadeel my son kamar yadda na gaya maka banso karban kudin ba, kai ma kasan halin mahmah'nka, sanya wa tayi cikin ledar maganina batare da ta jira ba ta tafi, kuma a duniyar nan kana ganin akwai macen da zan yaba ko zan so da zata wuce Fadeelah'n Fadeel dina?" Ta karasa cikin sigar tambaya kana ta cigaba "kawai yarinyar na da girmama na gaba da ita hadi da sanin mutuncin dan Adam, hakan yasa maganar ta ya shiga zuciyata matuka, amma duk da haka na fi jin Fadeelar Fadeel dina a zuciyata"


Murmushin farinciki ya saki kana ya rungumeta cikin kaunar ta yace. "Muga maganin ki Mahmah, har yau kin ki gaya min wani irin ciwo kike" Fadeel ya fada da damuwa saman fusk'ar sa.
Ledan maganin ta boye domin sam bata son ya sani, ta rufe zancen da cewa "wai me dan albarka ke dafa wa Mahmah'n sa ne?"


Murmushi yayi yace "taliya zan dafa miki kada ki dawo kina jin yunwa, gashi wutar ma taki kamawa sosai"


"sannu dan albarka, ai sauke wanna girkin zanyi, tunda har kalanzir(kerosene) na siyo galan daya, sai inyi mana jar miya da naman kazar nan, ai Allah ya yayi wa wanna yarinyar albarka, yaushe rabon mu da miyar stew (dage dage)" ta kai ayar maganar tana shiga daki domin boye maganin kamar kullum gudun kada Fadeel ya gani, kana ta fito ta fara kokarin dora musu girki....


*** *** *** ***

A dan gagauce ta fito daga bathroom sanye da bathrobe fari kal, tsadaden lotion daya dace da kalar skin dinta ta fara murzawa a lallausan farar fatar ta, bayan ta gama ta sanya inner wears farare kal, ta bud'e closet dinta mai murfin glass gaba dayan sa, take uban kayan sawar ta ya bayyana wanda koda shekaru ashirin nan gaba zasu ishe ta a wadace, hannu ta dora a kugu tana bin kayan da kallo, karshe dai ta ciro wani pencil trouser hadi da wani fashion riga mai hannun armless, sai kimono mai shara shara hadadde black color, sai dan mafayin rolling karami duka na company *PRADA* bayan duk ta sanya kayan tayi rolling batare da ko digon makeup a fuskar ta ba, amma tayi kyau sosai mai jan hankali kuwa, bangaren da take ajiye zallan takalma ta nufa, wasu hills masu tsini ta sanya kirar *HELLS STUART WERITZMAN* wanda tsadar sa zai kai *$104,765* da ganin takalmin ma ba sai an fada ba kasan tsadadde ne, turaren *Majesty* mai dadin kamshi ta fesa sama sama hadi da daura agogon zallan zinari kana ta Wauki wayar ta wanna karon kirar *Gold striker iPhone 3Gs supreme da kudin sa yakai $3.2million*, dan hand bag ta dauko kalar takalmin kana ta fice cikin sauri kamar ba takalmi mai tsini bane a kafarta, wanda hakan zai tabbatar wa mutum cewa ta saba da saka su...


?angaren Mommah ta nufa ta same ta tare da Daddy zaune suna dan taba hira, sallama tayi duk suka amsa cikin kaunar ta fuskar su dauke da murmushi kana ta nufi Daddy ta bashi sumbata a kumatu haka zalika Mommah... Babu bata lokaci Daddy ya mike yana gyara zaman tsadaddiyar rigar shaddar jikinsa da aka yiwa Winkin zamani, sai shekarun sa suka sake buya, hannu Fadeelah ya kama suka fice bayan sun yi sallama da Mommah...


Suna fitowa farfajiyar gidan suka tarar bodyguard's dinta dama na Daddy tsaye jikin tsadaddun motoci jere reras har guda goma, cikin sauri bodyguards biyu suka bud'e masu kofofin wata mota kirar *FERRARI LA FERRARI* fari, kana bodyguards suka shiga sauran motocin taran suka fara fita daga gidan a jere, motar da su Fadeelah ke ciki shine a tsakiyar motocin taran domin tabbatar da tsaro.

Babban hall din da sukan yi meeting ko wani sanarwa wa ma'aikatansu da kuma sauran bushiness partners suka nufa... gaba daya kowa ya hallara su kadai ake jira, zama suka yi nan aka gaisa cikin wayewa kana suka fara tattauna abinda ya kawo su.
(Kasancewar duk meeting ko wani abu daya shafi dukiyar Daddy to da fadeelah yake zuwa domin a dukkanin kadarorinsa sunan ta ne)
WANNA KENAN


*** *** *** ***

Zaune suke a *ORIENTAL HOTEL* gaba d'aya sun manta kowa a duniya saboda hirar soyaayyar da suke babu kama hannun yaro, hakan yasa suke jin kansu tamkar su kadai ne a duniyar, kallo daya zaka musu kasan cewa su di'n masoyan asali ne masu so da tattalin junan su.
Cikin zakin muryar ta tace "har yanzu baka zo gidanmu ba, ban san meyasa ba, kuma Mommah da Daddy na basu da matsala" ta karasa a yangance, wanna mutum zai yi tunanin kirkirowa tayi, sam ba haka bane dabi'ar ta ce hakan.


Murmushin ?arfin hali ya sakar mata, har ga Allah yana fargaban zuwa gidan su Fadeelah domin bai san a wani yanayi iyayenta zasu karbe shi ba. Kullum da kalar waya, kayan sawa, mota da zata yi amfanin da shi, duk da kasancewar sa talaka amma yasan tsadaddun abubuwa, domin a makaranta yayi rayuwa da mutane kala kala hakan yasa yake da sani kan abubuwan rayuwa da dama, duk da hakan yana fatan halayen iyayen Fadeelah ya zama irin na yarsu, saboda ba zai taba juran rasa ta ba, da kyawawan idanun sa ya tsare ta domin kwantar mata da hankali yace "Darling am sorry, in sha Allah zan zo gaida su Daddy soon"

Murmushi farinciki ta saki kana tace "da kuwa ranar nayi farinciki"
Martanin murmushin ya mayar mata zafaffan soyaayyar ta na ratsa shi, yana kallonta ta bud'e handbag dinta, waya ta miko masa tana kallonsa da murmushi, da kallo yabi wayar dake sanye a tafin hannunta banda daukar ido babu abinda take yi wanda ya kasance kirar *SUPERNOVA IPHONE 6* "ka rike ka dinga amfani dashi, kaga idan ma muna son ganin junan mu sai muyi video call ko?"


Bakin ta dake motsi kawai yake bi da kallo kana ya girgiza kansa alamun "a'a" bata fuska tayi kamar zata yi kuka tace "baka son abun hannuna ko?"


Girgiza kai yayi yace "ta ya ya zan ki abinda ya fito daga hannun abra kaunata? Kiyi hakuri kin ji bazan iya karba bane, I prefer na cigaba da amfani da wanna" ya fad'a yana daga dan itel d'insa.


Kallonsa take with much respect, ba kadan ba take matukar son wanna halin nasa, sam bashi da mataciyar zuciya kamar na wasu samari da suke son mace ta dinga yi musu hidima, tabbas ta ga Samari da yawa da suke son ta dan dukiyar ta, hakan yasa bata soyaayya amma daga haduwar ta da Fadeel ta fuskanci cewa ba duka aka taru aka zama daya ba. Duk da bata so yanda yaki karba ba amma ta jinjina masa kai kawai hadi da cewa "ok ba matsala"

Murmushi ya saki kana ya yi tunanin yin abinda zai faranta ranta, take ya fito da cardboard paper ya fara zana fuskar ta kamar yadda yake a duk lokacin da suka hadu.

Gyara zama tayi fuskar ta dauke da murmushi yayinda ya cigaba da zana ta.


Sai misalin karfe takwas na dare suka yi sallama... bakin mota ya rako ta ta shige tana daga masa hannu, kasancewar daga company Win su tace bodyguards dinta su wuce gida, duk da sun san sun karya dokar daddy, amma kuma basu yi jayayya da Fadeelah ba...

Daidai tangamemmen gate din estate dinsu ta danna horn mai gadi ya bud'e mata, babu bata lokaci ta danna hancin motar ciki, sai da ta daidaita parking ta fito hannun ta dauke da cardboard paper, gabanta ne ya dan fadi ganin bodyguards dinta tsaye cirko cirko kansu a kasa yayinda Daddy ke tsaye gaban su fuskar sa daura tamau da alama balbale su da fada yake...



(Not edited)

In sha Allah zanyi kokarin baku update gobe, nagode sosai da kaunar da kuke nunawa books dina=?
?



Share fisabilillah
Comment comment comment



Saboda Allah vote and follow me on wattpad @NoorEemaan >?z?d'?




Editing is not allowedL'


I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*


=?????AUTAR ?O?A=???
(Its all about love, scracife, hatred and destiny)


*First edition*


_by NoorEemaan_=???
'?


Wattpad
@NoorEemaan


ELEGANT ONLINE WRITER'S=???=???


Juma'at Mubarak to all Muslims ummah,
Allah ya sa damu da Alkhairi cikinta, yasa muyi kyakyyawar karshe, mu kuma cika da kyau da imani. NoorEemaan na kaunar ku my fansd'



_I must say this....=?? What a coincidence! a ranar da nayi typing wanna page din Friday ne, which is last year, ikon rabbi kuma Gashi nayi reposting again still that Friday_=?;?


https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.


Page 13-14


............A sanyaye ta karaso gaban su, daidai lokacin Daddy ya dagawa bodyguards dinta hannu alamun su tafi, ba musu suka fice kasan su a kasa alamun girmamawa, yayinda suka ji relief na ganin Fadeelah, akasin hakan kuma da sunan su gawa a hannun Alhaji Imran.



Bin bayan Daddy Fadeelah tayi har main parlour, hannun sa goye a bayan sa ya juyo gareta kana ya jefa mata tambaya kamar haka " a iya sanina 'yata mai bin umarni na ce, sannan bata da wurin zuwa daga company sai gida, sannan yaushe kika fara fita ke kadai ba tare da bodyguard ba princess? Did you know thousands of enemy we have out there? (Kin san dubanin makiyan da muke dashi a gari?)" Ya karasa a dame, yana nuni da yatsa, duk yanda yaso yi mata fada abin ya gagara, matsanancin soyaayyar 'yarsa ta hana shi yi mata fada domin sam baya son ganin bacin ranta koda na sakan daya ne.


Ajiyar zuciya ta sauke, domin abinda tayi tunani daban, tabbas ta san cewa kaunar da yake mata yasa yake bata tsaro domin kula da lafiyar ta. Cikin zallan son mahaifin ta kana murya a sanyaye tace "am so sorry Daddy, bazan sake fita ba tare da bodyguard ba, na fita shakatawa ne, ganin ba nisa nayi sosai da gida ba yasa nace su taho gida" ta karasa cikin shagwaba da marairaita ta yadda zai fi tausaya mata.



Murmushi mai taushi ya sakar mata, wanna maganar da ta yi ya wanke masa dukkanin damuwar daya dauki awanni cikin sa, "its ok my princess, sannan ki dinga barin wayar ki a bude saboda irin haka, domin dana samu wayar ki da hankalina bai tashi haka ba"



Murmushi tayi, domin soyaayya ta dauke mata hankali har ta manta da wata aba wai waya "in sha Allah Daddy zan kiyaye, ina Mommah nah?"



"Tana part d'inta tun rana kanta ke ciwo, ita ma hankalin ta gaba daya ya tashi da rashin dawowarki... ni nace taje ta kwanta ta samu huta, yanzu zanje part dinta domin sanar da ita kin dawo saboda hankalinta ya kwanta, ke ma je ki huta good night" ya fad'a yana bata sumbata a goshinta....




Handbag dinta kadai ta ajiye kana ta dauki gum(gam) data siya takanas domin manna hotunan da yakan zana na fuskarta a duk haduwar su.


Tsaye tayi tana bin zanen da kallo wanda yanzu sun dawo shida reras, har yau ta kasa gane wanne yafi kyau cikin zanen domin dukkansu ba baya wurin kyau, murmushi take saki akai- akai hirar da suka tayi dazu ke dawo k'wak'walwarta, daga karshe ta cire kayanta ta fada wanka bayan ta kunna wayoyinta, ta jima sosai a toilet duk cikin sunan wanka kana ta fito daure da towel, lotion mai k'amshin gaske ta shafa kana ta sanya pajamas masu kyau pitch color na company

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login