Showing 21001 words to 24000 words out of 80179 words

Chapter 8 - KYAUTAR KODA Hausa Novels by NoorEemaan.doc

11 Nov 2025

3036

mai cike da kalubale, kin tafi kin barni bana da sauran kowa daya rage min" . ajiyar zuciya ya sauke tamkar yaron goyon daya ci kuka ya koshi kana ya cigaba " ina sonki Mahmah, ina matuk'ar kaunar ki, your son fadeel loves you.
Ina fatan kina cikin farinciki da salama a yanzu, har abada kina cikin k'irjina da dukkanin wani sassa na jikina, kin yi Sadaukarwa mai girman gaske saboda farincikina, ina kaunar ki uwar da babu tamkar ki a duniya, Allah ya jikan ki Mahmah nah..." Nan ya shiga yi mata add'uo'i kana yaja wata alama da wani dan karfe daya gani a kasa, kan siminti, domin iska zai iya d'auke signboard din. Wanna alamar daya zana zai taimaka masa wurin gane kabarin Mahmah....


Mikewa yayi ya nufi gida. Sosai gidan yayi masa girma da fadi ainun, haka ya kudundine kan yar katifar mahmah matsanancin kewar ta na ratsa zuciya da jinin jikinsa......



*** *** ***


*BAYAN WATANIN BIYAR*


A haka rayuwa ke tafiya. Kwanaki na juyewa zuwa satittika, satittika na juyewa izuwa watanni, haka zalika watannin na juyewa izuwa shekara.

Yanzu babu laifi Fadeel ya dau dangana, tun ranar daya bar makabartan nan baya zuwa ko ina daga masallaci sai gida, haka zalika baya iya cin komai daga ya tafasa ruwan black tea (bunu) shikenan, shi ma sai ya ji Cikin sa na kugin yunwa zai sha, gaba daya ya dawo wani mara son hayaniya ko magana baya son yi, kuma har yanzu bai san a wani hali Fadeelah ke ciki ba, duk da sonta na nan daram a ransa...


A yau yayi tunanin gyara gidan, domin tunda Mahmah ta rasu gidan bai ga tsintsiya ba. Tsakar gida, da toilet ya gyara, kana ya nufi dakinsa ya fara gyarawa, bayan ya gama ya dawo dakin mahmah ya gyara mata tsaf, jakar kayanta dake a hargitse ya nufa da niyyar gyarawa wasu takardu suka fado.....


Rubutun Mahmah ya fara tozali dashi, sai wasu takardun asibitin. Ajiye takardun asibitin yayi a gefe, ya dauki na rubutun nata ya fara karantawa Kamar haka:

_my lovely son Fadeel_


_ina fatan kana cikin koshin lafiya, nasan bayan raina zaka ji komai. Ina fatan zaka yafe wa Mahmah'n ka a dalilin boye maka ciwon da nake fama dashi tsahon shekaru, na boye maka ne saboda bana son ka kasance cikin damuwa. Ina fatan dana abin sona baya fushi da Mahmah'n sa?_

Share hawaye yayi kana cikin muryar kuka yace "bana fushi dake mahmah bazan taba fushi dake ba, ina son ki sosai Mahmah na" kara share hawayen yayi, sai dai wani na koran wani, hakan yasa ya cigaba da karantawa bai damu da zubar hawayen ba.


_na hana ka bayar da kodar ka wa yata Fadeelah ba dan komai ba, sai dai ku rayu cikin lafiya da farinciki. Shin idan ban Sadaukar da koda ta ga abar son dana ba wa zai Sadaukarwa mata? Ka sani cewa ina cikin farinciki a lokacin da na bayar da koda ta ga fadeelah. Ina yi muku so mai yawan gaske. Kada ka karaya kan soyaayyar fadeelah ya kai jarumin dana, ka jajirce da dukkanin iyawarka har ta zama mallakin ka, nasan ku biyun zaku zamo the best couple ever da za a yi alfahari da ku a duniya... Ka kasance cikin farinciki dana, ka kula da fadeelah, ku kula da junan ku, ina farinciki da taraiyyar ku, sannan ina muku fatan alkhairi, ka gaida min yan jikokina idan sun zo in sha Allahu. Ina kaunar ka Fadeel, Mahmah loves you, fatan alkhairi._



Kurawa takardan ido yayi hawaye masu dumin gaske na sake zubo masa, shafa wani sashe na rubutun yayi, da ya dan yi jurwaye wanda da alama hawayen Mahmah ne ya diga kan takardan a lokacin da take rubutun..




Kan kayan Mahmah dake hargitse ya dora kansa, lumshe idanun sa yayi hadi da kamkame takardan a k'irjinsa, waka ya fara rera mata kamar haka:




_Rayuwa nayi nazari duk wanda ya zamto a raye, wata ran sai ya rasu ko yana so ko zai zubda hawaye. Duniya ba wajen zama ne ba, aro aka bamu ba jaye-jaye, mu rike Allah gwani mafita ne ga mazon na fiyayyye_.......


_Rayuwa ta sai a hankali, na rashin mahaifiyata. Na zama kamar banda hankali ku dubeni bani da gata. Hakuri ya zama faralli ya Allah jikan mahaifiyata_....


_wayyo! wayyo!! Ya Allah jikan mahaifiyata. Innalillahi wa innah ilaihi raju'un, Allah ya jikan ki Mahmah dan ki tafi wayyo ya zanyi_...........

_innalillahi wa innah ilaihi raju'un Allah ya jikan ki Mahmah dan ki tafi wayyo ya zanyi_......

_Allah nagode. Kullin nafsi za'ikatul mautu, duk mai rai tilas ne ya mutu . Sai dai ni du'a'in neman hutu Allah ya yafe mata_........

_kuka ka daina ka share hawaye abokina. Dani da kai zata zo kanmu watan wata rana, ka zo mu roki Allah, in muyi sallah nasan zaya kalla ya Allah! Mutuwa nazan tana da zafi, hakuri dazaka yi shi ya fi. Wanda ya mutu bazai dawo ba, add'ua zamuyi shi zaya je gareta....ya Allah!_

_innalillahi wa innah ilaihi raju'un Allah ya ji kanki Mahmah dan ki tafi wayyo ya zanyi. Wayyo! Mahmah, wayyo!! Mahmah, wayyo!!! Mahmah nah, wayyo Mahmah nah, wayyo Mahmah nah_....

_duk abinda nakeso cikin duniyar nan Mahmah tana bani, yanzu bata nan na lalace dare da rana kullum tunani. Burin rayuwa in zauna da mahaifiya dan ita ce garkuwa mai share duka damuwa. Wayyo! Mahmah, wayyo!! Mahmah, wayyo!!! mahmah nah, wayyo Mahmah nah!!!! Innalillahi wa innah ilaihi raju'un Allah ya jikan ki Mahmah dan ki tafi wayyo ya zanyi_.......
Haka ya gama wakar hawaye masu zafi na zubo masa, suna bin gefen da gefen fuskar sa suna shiga kunnuwan sa, dumin na ratsa kwanyar sa.
Da haka wani wahalallan bacci ya yi gaba dashi...




Bai jima da yin baccin ba, motocin fadeelah da body guard dinta suka tsaya kofar gidan.
Kofa aka bud'e mata ta fita kana ta shiga cikin gidan bakin ta dauke da sallama... Sai dai shiru babu amsa, hakan yasa ta nufi cikin dakin da ta gani a bud'e.....




#Share fisabilillah
#comment
#Vote




Please Vote and follow me on wattpad @NoorEemaan



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*


=???KYAUTAR ?O?A=???
(It's all about love, sacrifice, hatred and destiny)


_by Noor Eemaan_=???
'?



*Wattpad*
@NoorEemaan



ELEGANT ONLINE WRITER'S=???=???



EDITING IS NOT ALLOWEDL'



*(Please&please kuyi following nawa a Wattpad=?O? @NoorEemaan)*




Page 27-28


(Not edited)

Dai-dai 6akin ?ofar Wakin ta tsaya, ta sake sallama cikin zazzak'ar muryarta. Amma shiru, hakan yasa ta le?o da ?anta cikin dakin.

A ?wance ta hango fadeel, ya rame sosai ya sake yin Wuhu, cikin sauri ta cire tsaWaWWen takalmin kafarta na company *GUCCI* ta shige dakin.

Gabansa ta tsugunna da nufin tashin sa, sai ta tsaya ca?! sa?ama?on ganin takarda rungume a ?irjinsa. A Hankali ta kai hannu ta zari ta?ardan, haka kawai taji zuciyar ta na azalzalarta ta karanta ko ganin abin cikin ta?ardan.



Mikar da takardan tayi sak'amak'on dan cu?ur?uWewan da yayi ta fara karantawa...... Tun kafin tayi nisa da karatun ta fara hawaye tamkar an balle famfo. Sai da ta zo karshen karatun ta kasa rike kukan da ya kufce mata, dama Mahmah ce ta Sadaukarwa mata da *kodar ta?* Saboda su kasancewa a raye cikin farinciki? Kaunar da Mahmah ke mata ko tace take musu ya kai haka? Meyasa doctor Mahfouz bai sanar mata? Surutai ta dinga yi a ranta, yayinda kukan ta ke karuwa domin abin ya taba zuciyar ta matuka.



A hankali Fadeel ya Fara bud'e jajaye kuma ?umSurarrun idanun sa sakamakon kukan ta da ya ji ya sauke su kanta, Kallonta yayi na yan mintuna ya maida idanunsa ya lumshe.....


Bakinta ne ya fara rawa, so take ta furta masa wata kalma ta kasa, kallon sa take yayinda zuciyar ta ke kara karyewa. Ya dawo kamar bashi ba, ya fita a kamanin sa ainun. Gashi yaki kulata, sai dai hakan bai mata ciwo ba, domin mutuwar uwa ba karamar abu bane...



Cikin sauri ta bar gidan ta fada mota hadi da bawa driver umarnin ya kaita asibiti. sanin cewa asibiti daya take zuwa ya sa shi cewa "yes ma'am" Cikin sauri hadi da girmamawa. H???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?aka motocin suka bar unguwar a jare kamar ko yaushe.



Bangaren fadeel kuwa, yana jin fitar ta ya bude idanunsa ya bi kofar da ta fita da kallo. Wasu hawaye masu dumi suka biyo kuncin sa, idan yace bai yi kewar ta ba yayi karya, amma baya son kowa ya rabe shi a halin da yake ciki, yana bukatar privacy, yes yana bukatar kebancewa.



A hankali ya mike ya dauko kayan zanen sa, ya fara zana Mahmah kana ya zana fadeelah cikin mintuna ashirin. Hotunan biyun ya ajiye kan cinyoyin sa bayan ya gama zanen, ya kafe su da ido hawaye na zuba daga idanunsa, daya kalli zanen mahmah sai ya fashe da kuka, idan kuma ya kalli zanen fadeelah sai ya sa dariya, haka ya dauki tsawon lokaci yana yi tamkar wani mai tabin k'wak'walwa.
Hakika yana farincikin Fadeelah ta rayu, yana kuncin Mahmah ta mutu.



***

Tun cikin mota ta kira doctor Mahfouz ta sanar dashi tana tafe. Bayan isar su asibitin direct office d'insa ta nufa. Ta kuwa tarar dashi a ciki. Bata tsaya bata lokaci ba ta fara jero masa tambayoyi...

Doctor Mahfouz bai yi kasa a guiwa ba ya shiga sanar mata da komai da komai. Har wani sama _sama numfashin ta keyi saboda kukan da take. Cikin kukan tace "doctor meyasa ka boye min? Ka boye mana? da ban samu wasikar nan na karanta ba ta ya ya zan sani? I know fadeel won't tell me, Kwanan Mahmah nawa da mutuwa?" Duk ta jiro masa tambayoyi cikin matsanancin damuwa da mamakin irin tarin kaunar da Mahmah ke mata, domin sam abin yaki bace wa a zuciyar ta.



Ajiyar zuciya doctor Mahfouz ya sauke kana yace "yau watanta biyar da rasuwa. Wato Fadeelah ni kaina abin yayi matukar taba ni, a lokacin da aka rasa wanda zai siyar miki da kodar sa hankali na ya tashi sosai, a ranar da matan nan(mahmah) tazo da maganar a sanya miki kodar ta kyauta bayan ranta". Shiru yayi kana ya cigaba... "Maimakon nayi farinciki samun kodar da aka yi sai naji ba dadi sak'amak'on matsanancin tausayin matar daya kama ni, domin ban taba ganin Sadaukarwa hadi da kyawun zuciya irin na baiwar Allah nan ba"



Hawaye masu zafi ke sauka a kuncin Fadeelah, matsanancin tausayi hadi da zafaffan soyaayya Mahmah na ratsa ta. Ashe tayi watanin da mutuwa? (Kasancewar yau kwana fadeelah biyar da farfadowa, sam bata zaci ta dauki watanin kwance a gadon asibiti ba)


Ba tare da ta sake cewa komai ba ta bar asibitin, hadi da bawa driver umarnin su koma gidan su Fadeel.


&&

Tsabanin dazu da ta tarar dashi a kwance, yanzu a zaune ta tarar dashi, ya kimtsa jakar kayan mahmah dake a hargitse dazu.


Gabansa ta tsugunna cikin muryar kuka tace "my one" sai kuma kuka, sauran maganar ya makale, idanunsa a kasa, yana jin kukan ta har zuciyarsa...

A karo na biyu ta budi baki tace "ya... Ka... Karin haku'rin mu?"

Ya dauki mintuna biyu kana cikin shakakken murya yace "Alhamdulillah"

Wasu hawayen ta share ta sake cewa "Allah ya jikan mahmah, Allah ya sa aljanan ta zama makoma a gareta, Allah yasa kin huta mahmah"


Har ?ahon zuciyarsa ya ji dadin aWWuar ta ga mahaifiyar sa, a fili ya furta "Ameen"



"Nagode sosai my one, Mahmah ta bani kodar ta domin na rayu, bansan da wani baki zanyi godiya ba, sai yau na sani, Mahmah Allah ya sanya haske da salama a kabarin ki, ina kaunar ki sosai Mahmah, nagode nagode...." haka dai ta cigaba da maganganun kala kala abin tausayi.



Idanunsa ya bud'e ya sauke su kanta, yan sirarran lips din ta ya kurawa wa ido na second hamsin kana yace " shhhhhhhhh! Kiyi shiru, Mahmah is gone, tafiya ta har abada, add'ua kadai take bukata" yana gama fadin haka ya mayar da idanunsa ya lumshe.



Fadeelah kuwa jinjina masa kai kawai alamun gamsuwa tamkar yar yarinya. Ta kai mintuna goma a dakin, babu mai magana, Mikewa tayi cikin sanyin jiki tace "ni...z...zan tafi, Allah ya jadadda rahamarsa ga Mahmah" tama rasa wani irin godiya da ?alar aWWuar Wa?a dace tayi, domin gani ta?e Wuk ?almar Wata yi amfani da shi yayi kaWan.



Shiru yayi na yan mintuna kana a takaice yace "Ameen Bye"


Idanunta taf da kwalla ta bar dakin, duk bata ji dadin halin shariyar d'aya nuna mata ba, amma sam bata ga laifin sa ba, domin rasa uwa a duniya abu ne mai matukar ciwo, uwar ma irin Mahmah mai tarin kyawawan halaiyya.





A ranar Fadeelah ta sha kuka sosai, irin wanda bata taba yi ba, irin wanda ko lokacin da take shirin Sarin Wuniya bata yi k'watank'wancin sa ba, a daren ranar ta yi sallah'n dare, tayi add'ua sosai kan Allah haskaka makwancin Mahmah, ta jima sosai tana addu'o'i har aka kira sallar asuba...



*** *** ***


*BAYAN SHEKARA DAYA*

Alhamdulillah zuwa yanzu Fadeel har ma da Fadeelah sun dawo da zafaffan soyaayyar da suke wa juna. Duk da cewa kowace rana, ko wani seconds tunanin Mahmah na ma?ale a zuciyoyin su, bare ma fadeelah da take jin mahmah a zuciyar ta irin sosai dinnan domin duk wani motsin ta, mahmah na nan makale a ranta. Hakika mahmah bata cancanci a manta da ita ba...


Kamar yau zaune suke a bakin beach suna shan hirar soyaayyar su, gwanin burgewa, dago kyakyyawan idanunsa yayi ya kafe su kan Fadeelah dake waya tana fadin kalar cake da yanayin design da take so ayi wa cake din. (Kasancewar gobe birthday dinta)

Bayan ta sauke wayar suka hada ido dashi, wani murmushi ta sakar masa hadi da cewa "kallon fa?"

Ajiyar zuciya ya sauke kana yace "kullum kara kyau kike, kullum da irin sabon salon yanayin maganar ki, tafiyar ki, murmushin ki, in fact komai naki kara kyau suke kullum, gaya min menene sirrin?"

Tattausan murmushi ta sakar masa, Wanda na zallan jin dadi ne kana tace "kaine sirrin duk wani canjin nawa my one, you re the reason behind" sai kuma ta shagwa'be fuska kana tace "yakamata ku hadu da Daddy fa".
Ajiyar zuciya ya sauke kana yace " in sha Allah, kwana biyu da gama birthday dinki zan zo har gidan in gaida Daddy"

"Yeeeeeeeehhh amma naji dadi sosai, Allah ya nuna mana jibin"

Murmushi ya sakar mata kawai, wasu lokutan yana matukar son yanayin yarintar ta hadi da shagwa'bar ta, domin idan bai manta ba, gobe ne zata cika shekaru ashirin da uku a duniya, amma idan tayi wani abun kamar yar shekara goma, kuma sosai hakan ke yi mata kyau.

Haka dai suka cigaba da hirar su kana suka yi sallama cike da kewar juna, tana sake jaWaWWa masa ya zo wajen birthday partyn nata da wuri, Womin shi kaWai take bukatar gani, jinjina mata kai yayi murmushi d'auke a fuskar sa...



*WASHEGARI*

Misalin karfe 4:00pm had'add'un motocin fadeelah ke shiga cikin tsad'add'en hall din da daddy ya kama musamman domin shalelen sa (fadeelah). Bayan motocin duk sun gama daidaita parking, cikin sauri daya daga cikin bodyguard dinta ya bud'e ?ofar wata rantsatsiyar mota fara kirar *PININFARINA BATTISTA*. A hankali ta ziro farar kafarta mai sanye da tsad'add'en takalmi kirar *VALENTINO GARVANI*. Fitowa da dayar kafar tayi, kana ta fito gaba d'ayan ta. "Wow!" yawancin mutanen dake haraban hall din suka ce, a dalilin ganin Fadeelah.

Domin wasu had'add'un English wears ne a jikin ta kirar *DOLCE AND GABBANA*. Kayan basu fidda siraicin ta ba, amma ya dace da yanayin jikinta matuka, Duk da light makeup ne a fusk'ar ta amma, tayi wani irin sihirtacen kyau mai burgewa haka zalika agogo, sarka da dankunne ta duka na company D&G ne.




Gaba daya wadanda aka gayyata babu talaka, masu hannu da shuni ne bana wasa ba, In ka dauke Fadeel bawan Allah dake can gefe, cikin wasu kananun kaya masu saukin kudi, da flat takalmi na fata, kirar sa hadi da iya daukar wankan sa ya sanya kayan suka yi matukar dacewa da jikin sa.



Manyan masu kudi hadi da kusoshin gwamnati ke ta taya ta murnan zagayowar ranar haihuwar ta, amsawa take yayinda hankalin ta ke kan dube-duben ta inda zata ga Fadeel.
Sai dai sam bata gan shi ba, hawaye ne ya ciko idanun ta. Daidai lokacin daddy ya karaso da manyan abokan sa , ya sumbaceta kana suka nufi cikin hall din gabadaya.



Ajiyar zuciya fadeel ya sauke, sam bayason abinda za a yi masa kallon kaskanci, amma baya da zabi daya wuce ya shiga din, kodan farinciki Darling d'insa (Fadeelah) fitowa yayi daga maboyar sa ya nufi cikin hall din.

Babu abinda ke tashi sai zazzakar muryar wata matashiyar budurwa dake ?iwa fadeelah wakar HAPPY BIRTHDAY TO YOU. Yayinda wasu yan mata suka shiga fesa mata wanna abin mai Kamar kumfa fari mai flavour din vanilla. Wani lumshe ido Fadeelah tayi domin kamshin abin yayi mata dadi sosai domin duk wani abu mai vanilla tana son shi.


Fadin tsaruwa hadi da haduwar cikin hall din bata lokaci ne, kalar kayanta, kalar cake, hadi decoration din wajen duk iri daya ne.



Nan aka shiga gabatar da shirye_shirye masu kayatar wa, sannan iyayenta, family, da abokan arziki suka shiga kawo mata kyaututtuka masu tsadar gaske. Amsa take tana murmushin karfin hali saboda rashin ganin Fadeel.


Fadeel dake tsaye kam a baya yana ganin duk yanayin ta, a hankali ya fara ratsa mutane yana son isa gareta, daidai lokacin wani babban dan kasuwar kasar AMERICA ya kira Daddy a waya, hakan yasa ya dan yi nesa daga wajen taron.


Daidai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login