Showing 6001 words to 9000 words out of 85263 words

Chapter 3 - MAIRO Complete Hausa Novels by Khadeeja Candy.txt

04 Apr 2026

884

jikinta tana shafa bayanta
lafewa Mairo tayi in banda ajiyar zuciya babu abunda take sauke
sun daɗe a haka Gwaggo sai buga mata baya take tana son tayi bachi ita kuma taki tayi bachin sai faman sauke wahalallen numfashi take.
kai Gwaggo ta girgiza tace “ni kan Mairo kina bani mamaki ace bakida aiki sai kuka sai ja magana sai masifa haka kawai ki wahallarda kanki dubi yadda kika wuni kina kuka”
nan sabon kuka ya zo mata “to bake bace kika ki yarda kimin giɗa ba kuma na faɗa mki bazan sake ba”
da in'in niyar kuka take maganar tana numfashi da karfi kamar zuciyar zata fito

bubbuga bayanta Gwaggo ta shigayi tana faɗin “halinki nake tsoro Mairo karkije ki sake yin wani abun kuma kina ganin yadda Halilu ya sa miki ido jira kawai yake kiyi wani abun bama hHlilu kaɗai ba harda makota jiraye suke dake Mairo ke kuma gaki baki jin magana”
ɗagowa tayi idonta cike da hawaye tace “wlh Gwaggo na daina na faɗa miki bazan sake ba in kuma na sake Allah yasa na mutu”
rufe mata baki Gwaggo tayi “Subhanallahi Mairo miye haka karki sake faɗan irin wannan maganar kinji”
kai ta ɗaga mata “na daina Gwagho zaki doramin ko gobe zakimin giɗar?”
shiru Gwaggo tayi tana tunani dan tasan Halin Mairo in kuma bata dora mata ba wata sabuwar masifa ce.
kallonta tayi tace “kinmun Alkawari bazaki sake ba bazaki yi abunda zaisa a dake kiba?”
da sauri tace “eh nayi”
“shikenan zn dora miki”
“gobe ko Gwaggo?”
“eh Allah ya kaimu”
“amin”
rumgumeta tayi “na gode Gwaggo”
“Allah yayi miki Albarka”
“amin gwaggo zaki sayamin hancin ligidi?”
“eh  shi kike so?”
“eh”
“to bari na bada a siyo miki”
kwantar da ita Gwaggo tayi ta nufi kafit (wadurup ta da tsohuwar yayi) ta bude fanteka (kwala) ta ɗauko kuɗi ta sa hijabinta ta fice.

© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*
 
    *_KHADEEJA CANDY_*

*7*

_Washe gari..._
tun da asuba Mairo ta tashi tana yin sallah ta shiga karatun gajerun  surorin data iya inta kare ta sake maimaitawa har rana ta fito.

_8:14pm..._
Gwaggo na motsa kunu (koko) Halillu ya shigo gaishe ta har lokacin Mairo karatu take.
mamaki yayi sosai bayan sun gaisa da Gwaggo yace “yau yarki abun k'warai akeji?”
murmushi Gwaggo tayi “ai daman tana abun k'warai indai karatu ne ai kasan Mairo ba baya ba”
“a makarantan ba agida yaushe rabon da tayi irin wannan karatum tunfa da asuba nake jinyo ta ɗakina”
“to ai daman Mairo abunda take ai kuruciya ce data girma dainawa zatayi”
“ai da girmanta Gwaggo yanxu inta kara kaɗan ai aurarda ita za'ayi”

kuka Mairo ta fara wadda ba hawaye ta daina karantun “wlh Gwaggo bana son aure ba zanyi ba”
dariya Halilu yayi “au daman ba karatu kike ba kunnenki na kanmu ai daman nasan karatun munafirci ne”
kamar ta fasa kuka ta kalli Gwaggo “kice ya kyaleni ya tashi ya bar miki ɗakinki”
kofi Gwaggo ta janyo ta zubawa Halilu ta mika masa “karɓi ga kununka kosai na can gindin murhu a kwano”
dariya yayi bayan ya karɓa yace “dan tace ki koreni shine zaki koreni Gwaggo?”
“to naga fitina kake son jami muna zaman mu lafiya”
“ai ni gaskiya ce na faɗa kuma Mairo da kike gani aurene kawai zaiyi mata hankali ta daina abubuwan nan da take”
haɗashi da Allah Gwaggo ta shiga ganin Mairo nason yin kukan da gaske daker ta samu ya fita.
juyawa Mairo tayi zata cigaba da karatu Gwaggo ta shafa bayanta “taso haka yar Gwaggo ki karya (breakfast) ai kinyi karatun da yawa”
murmushi tayi “to gwaggo aI zaki mun giɗar ko?”
“sosai ma ai dole nayi miki bana miki alk'awari ba anjima kaɗan zanyi miki”
daɗi ne ya lumluɓe Mairo da sauri ta ɗauki kayan karatun ta aje gefe ta kwanto jikin Gwaggo ta soma bata kunun tana sha cike da jindaɗi.

_2:00pm....._
Mairo ta fita tallar giɗar k'inbi tayi hanyar da tabi ranar duk da zuciyarta na raya mata ta ɗan lek'a taga ko yana nan gashi har k'anshin goribar birni takeji tana tuna yadda take cinta.

haka dai ta daure ta nufi bakin kasuwa gurin data saba zama tana siyarda giɗar. wata yarinya na zaune a gurin tana ganin Mairo ta tashi da sauri ta koma gefe dan tasan halin Mairo indai matsifa ce saida ka barmata balle yau da fuskarta take a haɗe kamar anyi mata mutuwa.

koda la'asar tayi Mairo siyar da bakin rai ta nufo gida tana tureture baki kamar ta fasa kuka sai wata tafiya take kaɗan kaɗan.
haka ta ido gida ko sallama babu tun a bakin kofa tayi jifa da turen ta ta karaso idonta ciki da kwallah ta zauna kusa da Gwaggo dake Sallah,

tana sallamewa ta kalleta “lafiya Mairo waya taɓa ki?”
soshe soshe ta shiga yi tana tunano karyar da zatayi “ni..ni...ni....ɗan ta malele zan siya?”
shafa kanta Gwaggo tayi tana murmushi “haba Mairo sai kace wani abu harda su kwallah? ɗauki kuɗi kije ki siyo ki haɗa da kifi yadda zaki jidaɗin cinsa”
kai ta ɗaga “tho amman sai in zanje makaranta”
“tho inkin huta ki watsa ruwa sannan kije makaranta kinji”
kai ta ɗaga mata ta mika mata kuɗin giɗar.
“eyeee Mairo yau duka aka siyar gaske naji kin jefar da ture tun kofa”
murmushi Mairo tayi “yau nawa zaki ban?”
“hamsi zan baki ashiri kisa a susu talatin ki siye ɗan ta malele”
ta karasa maganar tare da mika mata 50 ɗin.,

da zumuɗi ta karɓa ta tashi ta nufi ɗaki da guɗu yau an sami abun sawa a susu mai tsoka.

    '''*** *** *** *** *** ***'''
     tun daga lokacin kullum sai Gwaggo tayiwa Mairo giɗa ita kuma bata fashin zuwa gurin siyarwa so ɗaya ta je gurinda aka bata goribar birni koda taje bata tararda kowa ba tsoro taji sosai babu abunda take rayawa a ranta sai aljani ne

“kai aljanine wannan mutunen da gaskiyar Gwaggo tunda gashi ban sake ganinshi ba kuma duk goriba karfine da ita amman tashi taushi ne da ita kuma na riga naci”
a fili take wannan maganar can ta tsaya tana tunani “inda ba aljani bane ai bazai zo cikin dajin nan ba har ya zauna kuma fa....”

bata karasa maganar ba ta watsa da gudu saboda motsin da taji cikin itacen dake gurin tana faɗin “karku biyoni na daina bazan sake zuwa ba wayyoh Gwaggo”
ihu take tayi da kuka tana gudu rabin giɗarta na zubewa,
har tabar gurin bata daina kuka ba dan gani take kamar sun biyota saida ta isa baki kasuwa sannan ta ɗan natsu ta soma numfasawa daidai,

tun daga lokacin bata kara tunanin zuwa gurin ba
duk ta ɗauko tallar giɗarta sai dai ta nufi bakin kasuwa inta siyar ta tayi ta shiririta ita da abokanin talla ko inta dawo ta biya gidansu jummala suyi gantalin da suka saba daman haka take so,

fagen neman magana da matsifa ba babba ba yaro kowa ta raina musamman inta ga ta girmeka ko kana tsoronta,
        Gwaggo in banda goya mata baya babu abunda take.
Halilu yayi faɗa harya gaji amman a banza kamar ma kara turata yake,

gashi Gwaggo ta hana ya daketa sai in ya faki idonta ko ya haɗu da ita can waje.
harta saba inta ganshi saita chanja hanya haka suka rika wasan ɓoya ita dashi.

*_3 months later....._*
yau da wuri Mairo ta siyarda giɗarta kuma yau bata jin wasa saboda dukan da Halilu yayi mata jiya dan yanzu har bakin kasuwa yake zuwa da ya tarar tana wasa ya fatattaketa da duka har gida,

duk yadda abokanin shashacinta sukaso ta tsaya kiyawa tayi dan tsan sai yazo gurin kuma Gwaggo tace mata da ta siyar ta dawo gida dan kar halilu ya daketa,
sallama tayi musu badan sunso ba dole suka kyaleta wasu kuma suka wuce gida dansu inba da Mairo ba basa jindaɗin wasa,

_Aysha adon gari ga Hajara adon gari ni Maryam adon gari inba ni ai ba gari Khadija Abubakar nake Candy kunji laqani gani tafe da'ayari yan mata a dandali_(MY UP COMING SONG INSHA ALLAH)
Mairo na tafe tana rera wak'a mak'ale da turenta na giɗa.

tunda kamin ta k'araso ta hango wata kafirar mota baqa mai shek'i fake kofar gidansu yara sun zagayeta sai shafa suke.

© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*
 
    *_KHADEEJA CANDY_*

*8*

da gudu Mairo ta karaso gurin ta shiga korar yaran duk da bata san mai motarba ɗan kawai ta ganta kofar gidansu ne kuma taga yara sun zagayeta suna shafa ita yar neman masifa,

shafa motar itama ta shigayi tana dariya tana kallon kanta ta madubin motar harda zira halshe tana lasa glass tana tale idanunta (fitar da ido)
tafi kafin minti 3 ahaka sai fana dariya take kamar wata taɓaɓɓiya,

yaran sai kallonta suke suna son su kwakwayeta suna tsaron tayi musu masifa tunda taɓa motar ma ta hana su.

can ta juyo ta kallesu ta hade rai taja tsaki “mtssss ku dan Allah ku ba mutane guri kauyawan banza kawai kowa ya bar mana k'ofar gidan mu ko naa muku hegen duka”
maganar take tana wani ɗageɗage da marmaɗen ido.
          duk ja yaran sukayi da baya dan sunsan halin Mairo indai masifa ce ba baya ba
yarinya ɗaya aka bari tana watsawa Mairo harara harda kai hannu ta shafa motar tana faɗin “an shafa kema ai yar kauyece da hegen kanki”
kai Mairo ta girgiza tana dariya “hee ni kike faɗawa wannan maganar  zaki ko ci ubanki yanzu”
ɗankwalinta ta cire ta k'ulle kuɗin giɗar dake hannunta ta ɗaura ɗan kwalin a k'ugunta (kwankwaso) tayi cikin yarinyar suka hau faɗa da juna,

kaye huɗu yarinyar tayiwa Mairo dan ta fita girma kuma k'arfi ba ɗaya ba gashi  daman can  Mairo ba wani k'arfi ne da itaba sai yar banzar masifa.
ɗukan k'warai Mairo tasha a hannun yarinyar tun tana iya jurewa har takai ga fasa kuka tana faɗin “azzaluma wlh sai naci ubanki hegiya-”
Mairo bata rufe baki ba yarinyar ta kai mata wani mugun shuri.
nan Mairo ta faɗi ta fashe da kuka
da gudu yarinyar tabar gurin gudun kar Gwaggo ta ji ta fito.

kuka Mairo tayi tayi tana kallon kofar gidan ganin babu wadda ya fito yasa dole ta tashi rik'e da ɗankwalinta a hannu kanta kuma duk k'asa ta shiga gida,
da kuka ta shiga gidan ta nufi gurin Gwaggo dake bakin murhu tana eza wuta.
da sauri ta ɗago ta rikata “lafiya Mairo Halilu ne ko?”
kai ta girgiza mata ta shiga faɗa mata abunda ya faru,
ɗankwalinta Gwaggo tasa tana share mata hawaye “haba Mairo miye na wani korar yara dansun taɓa mota kuma in banda fitina inake ina faɗa da wannan yariyar?”
turo baki Mairo tayi ta ɓata fuska kamar ta fasa kuka

“shigar mata kikayi ko Gwaggo?”

“a'a wani nan na shigarwa wata na bar Mairo dukan da ta miki ne ban jidaɗiba”

“kuma harda wani mugun shuri tayi mun ina jin zafi har yanzu”

“barta da Allah kijin”
kai ta ɗaga “Gwaggo motar wace kofar gida?”

“yan birni ne suka zo ganin gida”

kusa da ita Mairo ta matso “yan bunni Gwaggo gurin wa sukazo ina suke”

“sun tafi ganin sauran dangi”
“lahh daman Gwaggo kina da yan uwa yan bunni?”

“eh kema ai en'uwanki ne tun kima karama marabinsu da nan”
risinawa Mairo tayi zatayi magana sukaji Sallama.

Gwaggo ce ta amsa masa Mairo kan ido ta sakar masa kamar bata taɓa ganin mutane ba,

harya karaso tsakar gidan shi take kallon tana masa dariya shidai kallon kawai yake kamin ya kalli  Gwaggo yace “Sannu da aiki Gwaggo”
“yauwa sannu qasin kai kaɗai ka dawo?”
“eh ina gabansu ne suna hanya suma”
tabarmar dake shinfiɗe k'arkashin ecce ya nufa ana k'ok'arin zaunawa yayiwa Mairo magana
“ke baki eya gaida mutane ba?”
tasowa tayi da gudu tazo kisa dashi ta zauna.

“na eya ina wuni?”
“lafiya kalau ya sunaki?"
saida tayi dariya sannan tace “Mairo sunana Mairo”
murmushi yayi ya kalli Gwaggo “Gwaggo ni bansan wannan yarinyar ba yar gidan nan ce?”
daga can Gwaggo ta amsa mishi “eh gidan nan take ear uwarka ce ai yar wajen margayi ce”
“wane margayi?”
“malam tanimu wadda koda kukazo gaisuwarsa bakayi aureba ita kuma tana k'arama”
shiru yayi yana kallon Mairo data washe masa hak'ora,

“na ganeta Gwaggo daman ke kike rik'onta?”
sallamar dasu Abbah sukayine ya hana Gwaggo amsa masa tambayarsa.
“amin wa'alaikassalam alhaji harku dawo?”
“eh wlh kinga kara mu kama hanya da wuri tunda munga dangi”
momi ce ta amsa mata.
bayan sun xaune Gwaggo ta nufosu tana faɗin

“ai nikan ban yaba miku ba ace mutum shekara ds shekaru rabonsa da gida amman yazo ɗai rana ai kamata yayi ace kuzo ko sati ɗaya kuyi ko biu”

ɗariya sukayi Abbah yace “har yanzu dai Jamila baki chaja ba halinki nanan na masifa”

“yau ni wani haline dani daga faɗar gaskiya”
momi tace

“karki damu jamila insha Allahu zamuzo muyi sati anan yanzu bamuzo.da shirin kwana ba kuma kinga sauran yara suna makaranta sai anyi hutu tukuna”

taɓe baki Gwaggo tayi “nidai nawa idone ai rana bata karya”
dariya suka sake yi har Mairo sai a lokacin ta gaishesu.
duk suka amsa Abbah ya shafa kanta “Maryam am girma ko?”

“ashe zaka iya gane ta ai ɗaukar ka manta”
cewar Gwaggo

murmushi yayi yace “haba dai yar tawa zan manta ko yanzu da mukaje gurin tsoho saida mukayi maganarta”
mansura ta kalleta tana murmushi tace “oh Abbah itace yarinyar da ake magana”

momi tace “eh itace yar marainiya”
“Allah sarki Allah ya jikan mahaifa”
duk suka amsa da Amin.

sun ɗan juma suna fira daga bisani Gwaggo ta kawo musu abinci.
gudun masifar Gwaggo yasa dole suka ci badan sunso ba koshi kaɗan sukaci dan tuwon dawane ba wani sonshi suke sosai ba.

kuɗi Abbah ya ciro aljihunsa masu ɗan ɗama ya ajewa Gwaggo “gashi ayi wata lalurar”
“haba Alhaji bancin abin alkharin da aka kawo?”
“babu komai jamila a daici da hak'uri”
godiya sosai Gwaggo tayi masa momi da mansura sukayi mata sallama.
suna shirin fita Mairo ta laqe kafaɗa ta bata fuska ita saita bisu.

Gwaggo ce ta shiga lallasarta “haba Mairo wane irin binsu kuma bunni fa zasuje”
“eh ina son zuwa bunni nidai saina bisu”
“kinason ki daina ganina?”
“a a ai dawowa zanyi”
Abbah ne ya dafata “kiyi hakuri Mairo kinga Jamila bata so kije ki bari har wani lokacin inmun dawo sai muje dake kinji?”
kuka ta fasa “a a ni saina biku yanzu”
Qasin ya kalli Gwaggo yace “Gwaggo ki bari aje da ita tunda tana son zuwa”
faɗa Gwaggo ta soma “babu inda zataje ita kenan ina ganinta ina jindaɗi saiku ɗauke ta to baza taje ba”
juyowa Gwaggo tayi gurin Mairo ana lallasarta ba

aiko.kamar tana kara turata sai uhu take kaar wadda aka yiwa wani abu.
Abbah tsaye yayi yana lallaɓata shima
duk yadda Momi taso su tafi kiyawa yayi dan bayason barin Mairo tana kuka gashi Gwaggo ta hana aje da ita.

suna Halilu ya shigo aiko da gudu Mairo ta tashi tayi bayan Gwaggo tana kuka,
nan ya shiga tambayar abunda akayi mata momi ce ta faɗa masa,

nan ya hau Mairo da masifa “Allah in baki yiwa mutane  shiru ba saina miki shegen duka yar iskar yarinya”
kara buɗe baki Mairo tayi tana kuka kamar wata karamar yarinya,

Gwaggo ta kalli Halilu “kaga ko ana neman tayi shiru kaxo kana mata masifa ko”

“to Gwaggo in tana son xuwa ki barta taje mana in kuma ba zataje ba su su kama hanya kar dare yayi musu”

“to waya hanasu tafiya ai sune suka hure mata kunne tace saita bisu”

Qasin yace “a a Gwaggo karkiyi zargin kowa itace kawai dan kanta tace saita bimu”
momi dai haushine yasa ta fice ita da mansura suka bar Abbah da Qasin.

Halilu yace “ni wlh da kina yarda da kinbarta taje su da kansu zasu dawo da ita dan mugun halinta”

kin yarda Gwaggo tayi saida taga su Abbah zasu wuce gashi Mairo na kuka kamar ranta ya fita sannan ta amince.
aiko Mairo kamar ta zuba ruwa k'asa tasha da gudu ta nufi ɗaki ta shiga haɗa kayanta cikin bakko (ghana most go).


© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*
 
    *_KHADEEJA CANDY_*

*9*

bayan Amimcewar Gwaggo saida akaje gurin tsoho tare da Mairo aka faɗa masa shima kin amincewa yayi saida yaga abun na Mairo bana wasa bane sannan ya yarda sosai Abbah ya jidaɗi daman tun rasuwar kanensa yaso a bashi ita Gwaggo ta hana,

sai goshin magariba (kusan magariba) suka kama hanya
so huɗu ana tsayawa Mairo nayin amai jikinta sai rawa sanyi yake nan da nan zazzaɓi ya rifeta saida aka kashe ac ɗin motar,

*_9:37pm....._*
suka isa Sokoto koda Qasin yayi farkin Mairo na rungume jikin momi tana bachi.
saida kowa ya fita sannan momi ta tasheta
a firgice ta fito motar tana ɗaga kanta hankes ya cika mata ido,
gidan sama ne mai hawa ɗaya ko ina an manna gulof murza ido Mairo ta shigayi dan gani take kamar mafarki take.

bayan momi ta fito Qasin ya rufe motar shida Mansura suka nufi part ɗinsu daman Abbah tuni ya wuce nashi part ɗin,

Mairo na tsaye tana kalle2 momi ta rik'a hannunta zasu shiga ciki Mairo tayi tsaye tana kallon kofar farlon da alama tsoro take ji,

faɗuwa gaban momi yayi tana tsoron kar kuma tace bazata shiga ba.
“lafiya zomu shiga ciki mana”
shiru Mairo tayi ta lakkafe kafaɗa
saida Momi ta maimaita sannan tace “nan ne gidan?”
“eh nan ne zo mu shiga ciki”
tsaye tayi kamar bazata shiga ba
momi bata bi ta kanta ba taja hannunta suka cigaba da tafiya.
jiki a sanyaye Mairo ta shiga farlon tayiwa hannun momi mugun rik'o Usman na kwance saman doguwar kujera yana bachi siraj kuma na kallo,

shine ya taso ya tari momi da far'ah “sannu da zuwa momi”

“yauwa sannu siraj baka kwanta ba?”

kayan dake hannunta ya k'arɓa yana faɗin “eh ban kwanta ba wacece wannan momi?”

kallon Mairo momi tayi “qanwarka ce”

“daga can aka zo da ita?”

“eh bari na shiga ciki”

Up stairs momi ta nufa Mairo na rik'e da  hannun Momi,
suna shiga bedroom Momi ta faɗi zaune saman bed ita da Mairo,
har lokacin tana  rike da hannunta

bayan sun ɗan huta Momi ta nunawa Mairo tawel “jeki ki ɗauki ga tawul can ki ɗaura sai kiyi wanka kici abinci ki kwanta”
kai Mairo ta girgiza “a'a nidai Gwaggo wanke min kafafu kawai take in zan kwanta bata min wanka”
“to mu wanka muke in zamu kwanta tashi ki cire kayanki”
tashi Mairo tayi ta nufi gurin da Momi ta nuna mata.
itama Momi tashi tayi ta shiga cire kayanta

saida ta gama wanka sannan ta kira Mairo tayi mata
tare suka fito  Mairo bata tsaya jiran komai ba ta faɗa saman bed
Momi kuma ta nufi waduraf tasa kayan bachi ta ɗaura zane sama bayan tasa hijab ta kabbarta sallah.

koda Momi ta gama sallah Mairo tayi bachi.
tana cire hijab ɗinta ta nufi down stairs.
bata daɗe ba ta shigo ɗakin da plate din abinci a hankali ta shiga tada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login