Showing 63001 words to 66000 words out of 85263 words

Chapter 22 - MAIRO Complete Hausa Novels by Khadeeja Candy.txt

04 Apr 2026

888

muje"
Tashi tayi ta nufi ɗaki ido ya sakar mata harta shige sannan ya sauke ajiyar zuciya.

          _WASHE GARI..._

@9:21am ya shigo part ɗin Momi. Ita kaɗai ya tarar parlor tana zaune tana kallon tv.
Saman mujera ya zauna yana gaishe ta.
“Momi ina kwana?"
  “Lafiya kalau ya gajiya?"
   “Gajiya tabi tafiya Usman yace kina nema na"
“Eh hka ne"
Momi saida ta gyara zama sannan ta kira sunan shi.
“Qasin"
“Na'am Momi"
“Nace ka faɗawa matarka zaka k'ara Aure?"
“A'a Momi ban faɗa mata ba ina dai da niyar faɗa mata ɗin"
  “To ka sanar da ita da wuri dan hak'inta tane ta sani karka ɓoye mata komai"
“Insha Allah Momi zan faɗa mata akwai kayan da nayi oda ina jiran su iso ne"
   “Toh Allah ya taimaka daman shine kawai"
  “Amin Momi na gode bari n wuce office"
Kai Momi ta ɗaga mishi “Adawo lafiya"
Tashi yayi ya fice.

            ***************
   Manyan akwatuna ne ya shigo dasu guda uku light green masu kyau da ɗaukar hankali.
     Tsakiyar parlor ya aje su haka ya bisu ɗaya bayan ɗaya ya buɗe su sannan ya zauna saman kujera yana k'walama Mansura kira.
   Sai da yayi kusan minti biyar dayi mata kiran sannan ta fito ta nufo downstairs.
         “Dear lafiya kake min wannan kiran?"
“Lafiya kalau alkhari ne ya samu"
  Ya bata amsa yana murmushi. “Wannan lefen waye?"
Ta tambaya yayi da ta k'araso kuda da kayan.
     “Ba lefe bane kaya ne danayi miki oda tun dag Dubai sai yanzu suka iso"
Zaro ido tayi “Oh my god" da sauri ta duk'a tana duba kayan.
Bata iya tsayawa ta duba da hankali ba saboda jindaɗi d gudu ta taso ta rungume Qasin.
    “Oh dear you mean so much to me bansan da bakin da zanyi maka godiya ba"
     “You don't have to"
Hannu yasa aljihu ya ciro cak ya mika mata.
   Da hannu biu ta karɓa tana ɗan mamaki.
“One million Qasin for what?"
   “Just for you"
Dariya tayi mai alamar rashin gamsuwa “Qasin i don't understand please kamin kwari-kwari na minene?"
   Janta yayi ya kwanto saman jikinshi bakinshi dai-dai kunne ta yace “Na faɗan kishiya ne AURE ZAN K'ARA!".
Da k'arfi ta ɗago harta buge mishi haɓa.
  “No-no Qasin bamu saba irin wannan wasan da kai ba Please faɗa min kodai wata ksangilar kuka samu ne?"
  Murmushi yayi “Babu wata kwangila sweetheart naki ne wannan Wallahi da gaske Aure zan k'ara"
Tashi tayi tsaye da sauri taja baya kamar wace taga abin tsoro.
   “Kishiya fa kace Qasin kasan abinda kake faɗa?"
    “Da gaske nake mana gani nayi bai kyau na ɓoye miki ba"
Daga gun da take tsaye ta risina k'asan kuiwoyinta tana kuka.
“Qasin mi nayi maka dan Allah ka yafe min in har wani abin nayi maka ban saniba Wallahi zan gyara duk halayena.
zan chanja rayuwa dan Allah ka janye maganar Aure in har da gaske ne"
_Ashe kinsan baki da halin kwarai_ a rashi yake wannan maganar a fili kuma yace “Mansura babu wani dalili da zaisa na k'ara Aure kawai dai kinsan shi Aure sunna ce ta Manzo Rahama kuma ya umarce mu da yinta"
  Hannu tasa ta yaga cak ɗin ta watsa mishi.
     “Aikin banza ni koda na tashi cikin dukiya na tashi dan haka kuɗinka ba sha'awa suke bani ba kuma wannan kayan daka ɗebo ka kawo ka kwashi abinka ka k'ara gaba dan ni koda ka Auro ni gidanmu ba tsirara kaga ina yawo ba.
Da kake maganar Sunnan ai ba Aure ne kawai Sunnan Manzo ba miyasa baka dabbak'a sauran Sunnonin ba sai wannan,
Indai Aure ka Auro uku rana ɗaya kaga mun zama hudu kenan duk a karkashina zasu zauna Wallahi dan na gaba yayi gaba na baya sai kallar dangi.
   Ni zaka wulakanta? Wato ance mogiyar ganga za'a yada kotenta ko?
toh kaje ka Auro yar Sarkin masar ko yar Sarkin Aljannu k'arshe kenan Wallahi wahala duk akan zata k'are
Kuma kai da farin ciki kun raba hanya"
Tana kaiwa nan tasa k'afa tayi shuri ta akwatin takalma.
   Ido kawai Qasin ya sama ta tunda ta soma maganar har ya shige ɗakin ta daman yasan za'a rina.
        Tana shiga ɗakinta ta faɗa zaune saman gado tana ciyon lips.
  Sam zuciyarta tak'i yarda da abinda ta gani ko kuma nace abinda Qasin ya faɗa mata.
_Taya zai k'ara Aure bayan ban taɓa mafarkin Kishiya ba shima kuma bai taɓa min maganar taba koda wasa kai ba gaskiya bane inajin gwadani ne kawai yake son yi. ta ina ma zai iya zama da mata biyu shi da baya son rigima?_
Ajiyar zuciya ta sauke _Kai amman nayi wauta danayi mishi wannan cin mutuncin amman kuma k'ara danayi mishi kodan gaba kar yayi tunanin k'arin Aure da gaske_
    Duk a zuciyarta take wannan tunanin tana faman sauke ajiyar zuciya.

         _9pm_
Bayan Sallar Isha'i Qasin ya shiga ɗakin Mansura.
Kwance ya tararda tana kuka da sauti marar k'ara.
A hankalin ya zauna saman gadon ya kai hannu yana shafa bayanta.
“Dear kuka kike ne"
  Cikin muryar kuka tayi magana.
“Dear please faɗa min gaskiya zuciya tak'i aminta da da abinda ka faɗa min sai dai kuma jiki yana bani kamar haka ne"
  “Wallahi da gaske Aure zanyi kinji kuma na runtse"
  “Saboda mi?"
“Saboda yana Sunnah"
Kanta ta dafe.
  “Inna lillahi wa innnna ilaihi raji'un Qasin wane irin abune ya same ka haka?"
“Babu abinda ya sameni"
“Wace yar iskarce zaka Aura?"
  “Kin santa ai MARYAM CE!"
“Wace Maryam ɗin?"
Ta tambaya cike da son sani"
“Maryam tamu mana ta k'auye"
Tashi tayi tsaye ta nuna mishi hanya
“Tashi ka fice min ɗaki ai daman nasan k'arshen tika-tika-tik kuma ta tsuniyar gizo bata wuce ta k'ok'i.
   nasan zamanta gidan nan bana banza bane ni zayi ma munafurci. daman ras nake kallon ku kuma ga fili ga mai doki.
   Aure ko muje zuwa mahaukaci ya hau kura.
Sai kayi nadamar Auren nan dan haka gara ma tun wuri ka janye k'udirinka"
   “Bazan janye kudirina ba Mansura sai dai kiyi hakuri dan na riga na nema kuma an bani"
   Dariya tasa mishi 
  “Ai dole a baka kan dangin matsiyata anga kuɗi ai koda asiri za'a janyo hankalinka ballantana kuma gashi..."
  Tassssssssss ya wanke mata fuska da mari.
Ya nunata da yatsa
    “Ki tsayarda kalamanki dan naga kina k'ok'arin wuce hankalinki kar garin neman gira ki rasa ido"
   Yana kaiwa nan ya juya ya fice.
Faɗawa tayi saman gadon ta fashe da matsanaucin kuka.

       Gabah ta shigayi dashi  duk yadda yaso ya lallasheta k'in bashi haɗin kai tayi sai ma bullo mashi da wasu sabbin mugayen halaye nata data yi.
  A haka ya hak'ura yasa mata ido,
Bata tabbatar da gaske Auren zaiyi ba saida taji ta jishi a waya yana faɗawa wasu abokaninshi.
   Dawowa tayi ɗakinta bayan ta gama laɓen ta dinga safa da marwa.
   “Kan Uba wai da gaske Auren zaiyi kenan duk abin nan da nake mishi ba zai daina ba ko hmmm Wallahi sai ya gane shayi ruwane dan saina gasa mishi giɗa a hannu wannan ai kunyata ni zaiyi duk ɗakin mu ace ni kaɗai mijina zai yima kishiya,
Duk kicihim Momi ne bakar munafuka ita ce take kitsa mishi komai tunda da can ai bai yi tunanin k'arin Auren ba sai yanzu gaskiya ba zan iya juyewa ba naga Qasin da wata ba ni ba dole ne na nemi mafita"
   Ita kaɗai take maganganunta tana rawar kai kamar wata taɓaɓɓiya.

     Nan ta buɗe mishi sabon shafin iya shege,
  Tun abin baya damunshi har ya soma sosa mishi rai.
  Ana sauran kwana biyu ɗaurin Auren shi ya samu Momi yana koka mata akan sabbin halayen da Mansura ta tsiro dasu marasa kyau.
   Momi batayi mamaki ba dan daman tasan ba kirki ne da ita ba,
  “Hak'uri zakayi Qasin daman nasan sai tayi haka koma nace abinda yafi haka tunda daman can ba halin k'waraine da ita ba"
  Qasin ya sauke ajiyar zuciya.
“Allah ni Momi har naji son Auren ya shiga raina"
Momi tace “Toh ai dole ansan kan kishi kumallon mata ne amman wani lokacin mu muke jawa kanmu.
Sai kaji mace da ance za'ayi mata kishiya shi kenan fa ta dingi tada hankalin miji kenan kuma hakan ba zai sa ya daina neman Auren ba saima k'ara chusa kanshi da zaiyi,
  Mata da yawa baza gane in ance mijinki zaiyi Aure ai sai ki ɗinga yi mishi biyyah da nuna mishi so da goyon baya koda a zuciyarki baki son.
sai kiga yaji tausayi wata k'ilama ya fasa Auren ko in yayi yaji bazai iya zalumtarki ba kuma ba zai yarda wacan ta raina ki.
Kuma duk abinda wacan zata faɗa ba zai yarda ba koda gaskiya dan bai gani a zahiri ba,
Amman irin wannan kishin ai ni a ganina k'uruciyace kawai da rashin wayewa"
  Qasin yayi Murmushi.
   “Toh ai Momi ba duk matane suke gane wannan ba"
“Lallai kan sai mai hankali da hangen nesa ko nace mai wayau kai dai yanzu kasa hak'uri zai wuce In'sha Allah dama taga anyi Auren zata saki ai yanzu dan tana cikin zafin ne"
    “Allah yasa"
“Amin ka ci abinci?"
    “A'a"
“Toh ga tuwo can kan dining"
Tashi yayi ya nufi dining.
    Plate yaja ya zuba abincin son ranshi.
Ci yayi saida yayi nass sannan ya sha ruwa ya tashi yana hamdala tare da gyatsa. Rabon da yaci abinci ya k'oshi irin haka har ya manta.

   '''**********'''
*_RANAR JUMMA'AH..._*

Tun da safe Qasin ya shirya cikin farar shadda yayi ma jikinshi wanka turare.
D'akin Mansura ya nufo yana taɓa k'ofar ya jita kulle. Kiranta ya shigayi.
“Mansura Mansura buɗe zamuyi magana"
  Ya ɗan daɗe tsaye gurin wai ko zata buɗe amman sam ko motsinta bai jiba bare alamun buɗewar.
    Ganin hakan yasa ya nufo parlor ɗin Momi tsokanarshi Usman da Nura suka ringayi suna ce mishi Yaya Ango.
Sai da ya taka musu burki sannan suka saurara mishi Siraj sai bace komai ban in banda murmushin da yake.
Sai kusan 10 Abbah ya fito suka kama hanya tare da wata tawagar ta yan'uwa da abokanin arziki.

     K'arfe biu da rabi aka ɗaura Auren Qasin da Maryam bisa ga sadaki naira dubu ashirin.
  Ango kan baki har kunne sai gaisawa yake da mutane suna mashi barka, Daga nan suka kwasa sukayi gidan Gwaggo.
Siraj dai tun gurin ɗaurin Auren ya kama hanyar gida bai yarda yazo gidan Gwaggo ba wai a cewar shi yana da wani aikin a asibiti.
    Gwaggo tasha adonta da sabuwar atamba baki a washe sai farinciki take.
   Kayan abincin dake both Abbah yasa aka shigo dasu takeaway da Momi tayi kuma aka rabawa yan ɗaurin Auren.

        ******************

“Mansura wai mi yake damunki kin min waya nazo kuma nazo kink'i yi magana sai kuka kike miya farune"
  Kasa mata magana tayi har saida tayi kukan mai isarta sannan ta tashi ta shiga bathroom ta wanke fuskarta.
       Bayan ta fito ta zauna gefen gadon tana murzar hanci
“K'awata mijina aure zaiyi!"
   “Aure?" ta daki k'irji tare da zaro ido.
“Saboda mi? mikayi mashi?"
    “Wallahi ban mishi komai ba kawai dai ya nace shi sai yayi kinsan mahaifiyar shi bata sona ina ganin itace ta kitsa komi"
   “Subhanalllahi mi yake damun Qasin haka baki buɗa mashi wuta ba?"
“Babu abinda banyi mishi ba amman kamar k'ara zuwa shi nake sai da yayi yau fa aka ɗaura mashi Aure"
   “Amman Mansura kinyi wauta Miyasa baki faɗa tun da wuri ba?"
        “Kunyar faɗa nake ji ace duk ɗakin mu ni kadai mijina yayi ma kishiya kuma bai faɗa min da wuri ba sai ana sauran kwana kaɗan a ɗaura Aure"
   “Taf amman Qasin ya iya cin mutunci wacece matar?"
   “Wata yar'uwarshi ce yar k'auye k'aramar yarinya kuma k'azama"
   Tsananin mamaki ta cika dashi “Yar k'auye Qasin ɗin ne zai Auro miki yar k'auy?"
“Hasbunallahu wani'imar wakin toh yanzu miye abinyi?"
  “Nima ban sani ba shiyasa na kiraki da son nayi na haɗa kayana na bar mishi gidan kawai"
  “A'a karki kuskura yin haka ai in kikayi haka kin k'ara bashi dama kenan kiyi zamanki zanje na samu Mommy zan faɗa mata komai"
Kai ta ɗaga mata.
       “Toh Rahila dan Allah kuyi wani abu bana son ganin Qasin da ko wace mace kuma kinga zanji kunya ace yayi min kishiya"
     “In'sha Allahu zamu san abinyi ki kwantar da hankalinki kawai"
  Maganar Rahira take tana buga kafaɗunta. Ita kuma ta fashe da sabon kuka.

*****
Saida yamma suka ɗauko hanya koda suka iso gida dare ya soma yi.
D'akinshi ya wuce ya watsa ruwa ya fito ya shirya cikin k'ananan kaya ya sake ɗaukar keys ɗin motar shi ya fice.
    Bayan kamar mintu arba'in ya shigo rik'e da ledodi ya nufi ɗakin Mansura,
   Yana shigowa ta tashi tsaye da sauri idonta sunyi kumburi sunyi ja “Ba nace karka sake shigo min ɗaki ba?"
K'arasowa yayi ya aje ledar ya rungume “Mansura kina wahalarda kanki nifa ba cutarki zanyi ba banyi Auren nan dan na wulakanta kiba"
   Rigarshi ta rik'e da k'arfi “Qasin da gaske an ɗaura maka Aure yau? Da gaske Aure kayi?"
   Saida ya sauke ajiyar zuciya sannan yace “Anyi Mansura yau na zama mijin macce biu"
Rushewa tayi da kuka ta sulale k'asa zata faɗi.
     Da sauri ya ɗauketa ya ɗora saman gado yana lallaɓata.
   Wani irin shure-shure ta shigayi tana murzar gadon kamar mahaukaciya. Tun yana iya bata hak'uri har ya gaji ya taso ya baro mata ɗakin.

     
   _Washe gari..._
Tun da safe Qasin ya tura mota da direba k'auye.
Bai koma part ɗin shi ba ya nufi part ɗin Momi. Kitchen ya tararda ita ita da wasu suna aikace-aikace,
  “Momi good morning har kin tashi?"
  Murmushi Momi tayi “Ai dole na tashi tunda Amarya za'a kawo mana Abbah kan tunda safe ya aika Usman da mota wai yaje ya ɗauko ta"
    Qasin ya rik'e baki “Oh aiko za'asha bam-bam dan nima na aiki Hafizu da Mota"
  “Da safen nan?"
“Eh yanzu-yanzu bari na kira shi nace ya dawo"
  “A toh kirashi gaskiya tun baiyi nisa ba"
  Da sauri ya fitarda wayarshi ya shiga danna kira.

***

               Saida ya gama breakfast sannan ya dawo part ɗin shi,
Bedroom ɗin shi ya shiga yayi wanka ya shirya cikin shadda brown color. Da takalmi bak'ak'e ya ɗauki hula itama the same color da shadda yasa ya feshe jikinshi da turare ya nufo ɗakin Mansura.
  D'aukar numfashi ya tararda tanayi idanunta a kafe tana matsar yatsunta.
Da gudu ya k'arasa yana kiran sunanta,
   “Inna lillahi wa innnna ilaihi raji'un Mansura"
  D'aukarta yayi da sauri ya fice daga ɗakin. A Motashi. yasa ta ya nufi asibiti.
Yana isa aka cewa da ita emergency safa da marwa ya ringayi a bakin kofar ya ciro wayar shi ya sanar da Momi da yan gidansu.
  Cikin yan mintuna suka iso cike da tashin hankali bayan isowarsu da minti talatin Momi ta iso ita da wasu k'awayenta.
  Da sauri ya tareta “Momi kin iso?"
  “Eh ya jikin nata?"
“Da sauk'i alura akayi mata bachi take yanzu"
   Kujera Momi ta nufa ta zauna tana gaisawa da yan'uwan Mansura.
  Wata sister Mansura ta kalli Momi tace “Ance ɗanki yayi Aure"
Momi ta kalleta dan tasan gatsa mata magana ne tayi
    “Eh jiya aka ɗaura Aure Amaryar ma tana kan hanya"
  Momi ta mayar mata da amsa tana ɗan hararar ta.
    Shiru tayi bata sake cewa komai ba har na wani lokaci
Can Momi ta tashi tana faɗin “Tunda abun da sauk'i ni bari naje gida kar su iso su tararda gidan ba kowa"
   Kai Qasin ya ɗaga mata “Okey Momi"
Sallama Momi tayi musu sannan ta fice.
   Har gun Mota Qasin ya rakata daf da zata shiga mota tace mishi “Sai fa kayi hak'uri da yan'uwan nan nata dan tama ta kishi suke dan haka karka kula su"
     “In'sha Allahu Momi ni miye nawa ma na biye mata"
  Shiga tayi motar ya rufe mata direba yaja suka fice.

_4:30pm_
Suka iso da far'ah Momi ta fito tana taron su.
Gwaggo ta fito Mota tana k' arewa gidan kallon “Oh Allah mai haɗin zumunta ban taɓa zuwa gidan nan ba sai yau daman haka gidan naku yake aljannar duniya"
    Himdatu tace “Shi yasa Mairo take son zama nan ashe da gaskiyarta tasan daɗin da take ji"
   Momi tayi murmushi
“Wai nikan zaku shigo ne ko sai kun gama kallon gida?"
  Hannu Momi ta kai ta riko hannun Mairo dake sun-sun da kai ta nufi kofar parlor “Nidai naja yata in kunga dama saiku shigo"
   Dariya sukayi sannan suka kunno kai cikin gidan.
    Abinci kala-kala Momi ta jera musu k'asan carpet nan suka baje hazarsu sai da aka kira Magariba sannan suka tashi,
     Sai bayan sallar I'sha Abbah ya shigo suka gaisa nan ne Gwaggo take tambayar Qasin'
   “Wai nikan nace ina Angon ne tunda muka zo ban ganshi ba?"
Momi tace “Wallahi yana can asibiti aina kira shi na faɗa mishi yace likitan ne yace ya tsaya ya zo da matarshi dan taji sauki"
    “Daman bata da lafiya ne?"
   Gwaggo tq tambaya
  “Lafiyar kalau kishi ne kawai ya motsa ta ɗinga ɗaukar numfashi shine  ya kaita asibiti amman dai yanzu ance sun da sauk'i zata ma iya dawowa gida"
“Oh daman kishi ne da ita har haka?"
   “Kishi ma kuwa ai sai dai ace Allah ya sauwak'e kawai"
Abbah ne ya kawarda maganar ta ya tado wani labarin.

***        ***      ****
Sai kusan sha ɗayan dare suka dawo bayan mahaifiyarta ta haɗata da yan'uwanta biyu wai su kula da ita.
  Da kanshi ya kaita ɗakin shi ya haɗa ruwan wanka sukayi wankan tare,
  Bayan sun fito ya saka mata kayan bachi sannan shima ya saka ya kwanta kan gado rumgume da ita yana aika mata da sak'onni.

    _Washe gari_
  Sai goma da rabi ya shigo part ɗin Momi duk zaune ya tararda su suna kallo.
  Haka ya samu kanshi da jin kunyarsu ɗaya bayan ɗaya ya bisu yana gaisarwa.
   “Momi ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login