Showing 48001 words to 51000 words out of 85263 words
Chapter 17 - MAIRO Complete Hausa Novels by Khadeeja Candy.txt
har neja"
Murmushi yayi "Babu komai Gwaggo sai alkhari kedai kiyi ta min addu'ah wannan abun da kikeji ba komai bane sai sabo in sha Allahu za ayi nasara."
Ajiyar zuciya ta sauke "Toh Allah yasa addu'ah ai kullum ciki yi muku ita nake Allah ya kaika lafiya ya tsare amman naso tafiyar nan ba yanzu ne da sai na karɓi a dashe na saina baka ka k'ara"
"Babu komai Gwaggo addu'ah kin ya fiye min komai inada yan kuɗin da zasu ishe ni kwana biu kuma kinga in naje ba zama zanyi ba aiki zamu rik'a yi"
"Toh Allah ya taimaka yasa ayi sa'ah ya tsare min kai ya raya ka ya cika maka burinka"
sosai ya jidaɗi addu'ah da Gwaggo tayi masa bayan ya amsa da 'amin' ya tashi tsaye yana faɗin "Bari na shiga gari na ɗanyi bankwana da wasu"
kai Gwaggo ta ɗaga masa "Toh aikan yafi Allah dai ya tsare."
tafiya ya somayi har yakai k'ofa Mairo ta kirashi
"Halilu..."
"Na'am"
juyowa yayi ya kalleta itama shi take kallo bakinta yayi mata nauyi ta kasa magana. ganin hakan yasa shi tambaya ta "Minene Mairo ko wani abun kike son a siyo miki ne ?"
kai ta girgiza alamar a'a "Toh minene faɗi naji ?"
cika idonta sukayi da kwallah "Halilu dan Allah karkaje neja ɗin nan kaji ko kuma kaje dani"
"Saboda mi ?" Gwaggo ta tambaya "Nidai bana son yaje bana so kawai"
cikin muryar tausayi ta bata amsar, hawayen dake idonta suka soma gudana.
dawowa Halilu yayi ya risina daidai gun da take zauna ya kalleta cikin muryar lallashi ya soma magana "Kar dai ace tafiya tace ta saki kuka ai ba daɗewa zanyi ba zan dawo dole naje dake dan haka kibar k'ararda hawayenki kinji ?"
"A'a nidai bana so kawai kar kaje bana son kaje ka bari har wani lokacin"
wannan karon muryarta na rawa tayi maganar.
iskan dake bakinsa ya busar sai zuciyar ta soma masa ba daɗi "Haba Mairo karfafa min gwuiwa ya kamata kiyi fa kinga nan ina zauna babu wani abunda zanyi amman can zan samu aikin yi nayi kuɗi na gina miki gida mai a birni da zaki zauna na rika baki kwai da daɗi kina ci amman kinga inna zauna nan haka zamuyi ta zama babu wani cigaba yanzu fa dana dawo birni zamu koma ko baki so ?"
"Ina so. mana"
Murmushi yayi "Yauwa toh ki zake ranki ki rik'a min addu'ah kinji ki daina kuka ?"
share hawayen tayi ta ɗaga mishi kai "Toh na daina amman dai in kaje karka daɗe"
"Ai bazan daɗe ba zan dawo na ɗaukeki"
Gwaggo daga gun da take tayi dariya tace "Oh Mairo kodai ya saki a jaka ne ya tafi dake ?"
fashewa tayi da dariya "Haba Gwaggo sai kace wata yar tsuntsuwa sai dai in Tsoho za asaka aje dashi"
wannan karon har Halilu saidai yayi dariya.
Gwaggo tasha mur "Wai Mairo mi yasa kika raina Tsoho ne naga dai ba sa'an ki bane ai ?"
"Amman dai kakana ne ko sai abarni dashi shima ai haka yake min"
"Toh shi kenan aiko zamu saka k'afar waddo ɗaya dake"
kai kawai Halilu ya kaɗa ya tashi ya fice.
*_©KHADEEJA CANDY_*
[11:27PM, 3/17/2017] Khadeeja Candy: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
*_KHADEEJA CANDY_*
Candynovel.wordpress.com
*48*
Tunda Halilu ya dawo, sallar A'suba ya shiga kintsa sauran kayansa.
daf da zai gama Gwaggo ta shigo masa da kari "Halilu ana nan nata shirin ?"
juyowa yayi bayan ya aje jakarsa gefe. "Eh wallahi har kin tashi Gwaggo ?"
"Eh tunda nayi sallah na shiga haɗa maka abun kari naji kace da wuri zaka wuce."
kunun data aje gaban shi ya buɗe ya shiga motsawa "Toh ai kara tafiyar safen Gwaggo tun kinga garin nesa ne kara muje da wuri"
Ajiyar zuciya kawai Gwaggo ta sauke ta tsora masa ido.
biu da ludayi yayi ya aje Gwaggo ta kalleshi "Ba dai ka k'oshi ba ?"
"Gwaggo bazan iya sha da yawa ba ki cikina a ɗaure yake wannan ma dan kar naje babu komai a ciki nane"
Gwaggo ta tura masa dumame "Toh kaci tuwon mana ai bakaje da yunwa ba dai"
"Bazan iya ci ba Gwaggo inna ji yunwa zan siye wani abun ko a hanya ne"
"Toh Allah ya sauwake ko ni haka nake in zanyi tafiya bana iya cin abincin kirki"
kuɗi dake ɗaure a gefen zaninta ta ciro ta mika masa "Ga wannan jiya na aro gun Faɗime ka ɗan k'ara"
kamar bazai k'arɓa sai kuma yasa hannun ya karba yana godiya "Allah ya saka da Alheri amman dama baki wahalar da kanki ba Gwaggo na faɗa miki inada yan kuɗin da zasu ishe ni." "Babu komai Halilu in banyi maka ba wa zaiyi maka Allah dai ya raya mani kai ya tsare ya baka abunda kake buk'ata."
"Amin Gwaggo Mairo bata tashi bane ?"
saida yayi tambayar kunya ta zo masa da sauri ya sunkuyarda kansa.
murmushi Gwaggo tayi "Bata tashi ba daman bana son ta tashi dan in taga tafiyar ka zata iya fasa min kuka"
shima murmushi yayi "Mairo manya ana girma na cin k'asa Allah dai ya shirya"
kamin Gwaggo tace Amin sukaji an buga gida.
da sauri ya tashi ya fita, bayan kamar minti ɗaya ya dawo ya ɗauki jakar yana faɗin "Ga abokan tafiyar nan sun zo zamu wuce..."
ganin idonta sun cika da kwallah yashi risinawa ya kalleta "Haba Gwaggo kar kimin haka mana dan Allah karkiyi kuka bafa rabuwa mukayi ba tafiyace kuma in sha Allahu zan dawo"
sam Gwaggo kasa hak'uri tayi saida kukan nata ya fito fili,
nan shima nashi idon suka cika da kwallah amman bai yarda ya bari ta gani ba kasancewar shi namiji. tsit ɗakin yayi in banda shashekar kukan Gwaggo babu abunda kake ji.
saida hawayen suka ɗan tsaya mata sannan ta kalleshi da jajayen ido "Allah ya tsare ka Halilu ya kaika lafiya"
dak'er ya iya amsawa da Amin ya tashi ya nufi k'ofa nan ma ya daɗe tsaye sannan ya fice.
. Sai takwas da yan mintuna Mairo ta tashi da murjar ido ta fito ɗakin ta ɗauki buta ta shiga banɗaki., bayan ta fito ta nemi guri ta zauna zata fara alwala.
Gwaggo ta kalleta "Yau Mairo anyi ranar sallah."
"Wallahi Gwaggo jikin ne yayi min nauyi kuma duhu dubun nan da nake gani saina ɗauka ko safiya bata waye bane."
Gwaggo ta ɗan kalli gajimare "Eh da yake yau an tashi da hadari kuma yayi bak'i sosai ina ganin ruwa ake a wani garin kusa."
taɓe baki kawai tayi ta cigaba da alwala bayan ta k'are ta shiga ɗaki ta saka Hijab ta shinfiɗa ɗan kwali ta soma Sallar, tana k'arewa, ta fito ɗakin da sauri ta shiga ɗakin Halilu.
fitowa tayi kinit kinit da fuska kamar ta fasa kuka ta nufo Gwaggo,
tun kamin ta k'araso Gwaggo ta tare ta "Toh karki fara mani kukan nan naki ni ban iyawa"
"Miyasa baki tashe niba da zai tafi kuma kika barshi ya tafi"
da rawar murya tayi maganar alamar tana son yin kuka.
"Shine a yace karna tashe ki na kyaleki baya son kukan nan naki" aiko kamar jira take Gwaggo ta kai aya ta fara sana'ar ta ta "Ni wallahi Gwaggo sai na miki kukan tunda kika ki tashi na" abunda ta dinga faɗa kenan tana murjar kafafunta akasa kamar wata k'aramar yarinya,
*BIRNI.........*
Koda Momi ta sauko downstairs ta nufo dining room ta tararda Siraj zaune yana haɗa ma kansa tea.
"Kai kaɗaine a dining ?"
juyowa yayi ya kalle ta "Eh sun wuce makaranta tun dazu wai suna da lakca k'arfe takwas good morning Momi"
"Morning too yau kayi saurin tashi tunda A'suba fa na ganka parlor nan nama ɗauka ko aikin ne naku ya taso."
ta faɗa yayinda take k'ok'arin zaunawa.
dariya yayi "Haba Momi aiki tunda asuba ?"
"Eh mana in an kawo patient irin wannan lokacin kuma ace duty ɗinka ne ai dole kaje ba ɗaga k'afa dole a tashi da wuri"
shafa kanshi yayi "Taf ai kan ba amin haka ko patient ne wasu likitocin saji dashi sai goma ko sha ɗaya nake shiga office."
"Hmm. kaidai Allah ya kawarda ɓacin rana ai inta kama dole kayi toh yanzu wai miya tashi ka tun da safe. ?"
"Wani mummannan mafarki nayi..."
Momi ta tsayarda zuba madarar da take. "Mummannan mafarki kuma har kasa gabana yayi dakan uku uku ?"
dariya yayi "Kai Momi kin cika tsoro bafa akanki nayi ba akan Abbah ba akan kowa na gidan nan ba."
"Toh akan wa faɗa min gaskiya Siraj ?"
"Momi ai ance in anyi mafarkin daba na k'warai ba ba'afaɗa"
"Toh miya rage a kariga ka faɗa."
saida ya ɗan cije baki sannan yace "Mafarkin nayi wai Maryam ta Auri wani mutum..."
Ajiyar zuciya Momi ta sauke ta lumshe ido,
bayan ta buɗe ta ɗanja tsaki "Mtsss Siraj ka iya tada hankalin bawa ni Wallahi na ɗauka ko wani abun ne"
"Wani abun ne mana Momi kai Allah dai ya tsare."
kallon mamaki Momi tayi mashi "Ya tsare. mi abunda Allah ya kaddaro ai babu mahani in Allah ya rubuta saita Auri wani ai sai ta Aura"
tea dake gabansa ya kurɓa "Eh haka ne amman dai kada Allah ya kaddaro ta Auri wani bayan..."
sai kuma yayi shiru ya kasa karasawa.
kai Momi ta girgiza "Allah yayi muku saukin wannan rayuwa kun ɗauki kiyayyah kun ɗorawa Yariman nan na san ai danshi ne kake wannan abun"
hannayensa ya ɗaga sama "A'a Momi karfa ki lakamin laifi kedai kika amfato sweet son ɗin nan naki baki ji a baki na ba."
Momi ta soma shan tea tana faɗin "Ai ko baka faɗa ba na san haka kake nufi."
Murmushi yayi ya tashi tare da cup ɗin tea ya ɗauki jaridar dake gefensa ya fice.
''' *** *** *** '''
Kishingiɗe yake tsakar parlorshi sanye da wando pencil da riga yellow, idoshi a lumshe yana tsutsar minti yana mayarda numfa a hankali,
"Yes enter..."
shine abunda ya furta bayan mai bugun k'ofar ya dade tsaye.
wani wassgegen mutum ne naga ya kunnu kai cikin ɗaki da gamammiyar fuska kamar an masa mutuwa.
nesa dashi ya tsaya yace "Oga nazo maka da Albishir mai daɗi"
saida ya kusan minti uku da yin maganar sannan ya amsa masa har lokacin idon shi a lumshe suke. "Wane irin Albishir kazo dashi ?"
cike da isa yayi mashi tambayar shi ko jiki na rawa ya bashi amsa,
"Halilu ya mutu..... "
_Halilu ya mutu.! Halilu ya mutu..!! Halilu ya mutu...!!!_
haka maganar ta rik'a yima Yarima yawo a kwakwalwa sai a lokacin ya buɗe ido ya kalli Mutumin "Nace maka duk yadda zakayi kayi na ganin ka raba tsakanin su amman banyi da kai ka kashe shi ba."
da sauri ya bashi amsa "Oga ba kashe shi nayi ba accident ya samu a hanyarsa ta zuwa Neja neman aiki" wani tsire baki Yarima yayi "Ya a'kayi kasan ya samu accident ?"
"Oga idun mu yana kansa fa tunda ka bamu aikin nan ko ina yarana nake sawa su kula dashi a motar da sukayi accident ɗinma harda yaron mu"
Wani irin kyakkyawan murmushi ya shinfiɗe fuskar Yarima wadda na tabbatar har a zuciyarsa yake.
tashi yayi tsaye ya k'arasa kusa da mutumin ya dafashi fuskarsa ɗauke da annashuwa "Kazo min da albishir mafi daɗi kuma goron mai tsokane jeki waje ka jirani amman ka tabbatar mutuwa yayi ba dogon suma ba."
*©KHADEEJA CANDY*
[11/9, 6:57 AM] Khadeeja Candy: [6:01PM, 3/23/2017] Khadeeja_ce👌: *©KHADEEJA CANDY*
[11:27PM, 3/17/2017] Khadeeja Candy: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
*_KHADEEJA CANDY_*
Candynovel.wordpress.com
*49*
Da gudu Qasin ya shigo part ɗin Momi kai tsaye upstairs ya nufa.
zaune ya tararda ita hawaye na mata zuba, jiki a sanyaye ya zauna "Momi yanzu Abbah ya kirani sai anyi rasuwa k'auye"
Kai ta daga masa "Eh Halilu ne Allah yayi masa cikawa..."
ta karasa maganar,
nan shima Qasin ya kawarda fuskarsa yace "Abbah yace na ɗaukeki muje kamin ya iso inya so sai yaje shida Siraj da Usman"
kai kawai ta iya ɗaga masa ya tashi ya fice.
Part ɗinta ya nufa a gaggauce ya shirya ya fito shida Mansura bayan ta shiga. mota ya shiga ya kira Momi suka kama hanya.
''' *** *** *** '''
Tunda Qasin ya doso unguwar soka soma hangen mutane,
ba karamin mamaki Qasin ya cika dashi ganin motocin Yarima.
yanayin parking ya kalli Momi "Momi ke kika faɗa masa anyi rasuwa ?"
Momi bata bashi amsa ba ta buɗe motar ta fice Mansura ta rufa mata baya.
_"inna illahi wa inna ilaihi raji'um_"
Shine abunda Gwaggo keta furtawa tana dafe da kai hawaye na mata zuba mutane sai hak'uri suke bata Mairo na ganin Momi ta nufe ta gudu tana kuka. rumgumeta Momi tayi suka faɗi zaune ko wanne su na kuka, ganin kukan da suke yasa Mansura ita ta soma kukan mutane dake shigowa suma auka fasa nasu aka sara mai bawa wani haku'uri,
haka gida ya kacame kowa sai yabon halinsa yake.,
guraren la'asar aka ɗauki gawarsa zuwa mak'abarta bayan anyi masa sallah.
Bayan an dawo mutane suka soma yima Gwaggo gaisuwa uffan bata iya cewa ba in banda zubar hawayen da take.
A lokacin su Abbah suka iso shida Siraj da Usman harda Nura. Ba karamin tashi hankalin Abbah yayi ba ganin yadda Gwaggo ta koma nan da nan shima hawayen suka soma masa zuba sai hak'uri yake ba Gwaggo dan yasan tafi kowa jin mutuwar,
"inba wadda ya saniba babu wadda zaice ba nice na haifi Halilu ba bai taɓa min musu ba bai taɓa kin mun biyayyah ba mutum ne da kowa ga yaba da halinsa duk abunda zai ɓata min rai yana gudunsa yana da burika dayawa aranshi na ya kautata min yayi rayuwar jindaɗi ashe Allah bai nufa ba aahe rayuwar yar kankanuwace ba mai tsoyo ba..." cikin kuka Gwaggo take wannan maganar a'na bata hak'uri.
_Gwaggo bata taɓa haihuwa ba hakan yasa lokacin da yayanta ya rasu ta ɗauko Halilu ta rikashi tun yana karami a hannunta ya tashi Mairo ma tunda aka haife aka kawo ata ita itace ta raine ta kasancewar ta tashi babu uba kuma mahaifiyarta gurin haihuwarta ta rasu_
Sai a lokacin Yarima ya shigo cikin gida da sunan gaisuwa har kasan tabarma ya zauna yana gaida Gwaggo "Sannun mu inna Allah ya jikan shi yayi masa rahama yasa ya huta."
duk suka amsa da Amin Abbah ya Kalleshi cike da jindaɗi abunda yayi "Allah yayi maka albarka Yarima ya biya ka"
"Babu komai Abbah ai yima kaine Hajiya ma tana nan zuwa gobe tace nayi muku gaisuwa kamin ta iso"
"Muna amsawa Allah ya kawota lafiya"
nan ya juyo ya kalli Qasin da fuskar da shi kadai zai iya fassara abunda ke rashi "Sannun mu Qasin Allah ya baku hak'uri..."
'Amin' ciki ciki Qasin ya amsa ya ɗauke kansa yana kallon k'ofa nan ya juyo kan Siraj yana yi mashi tashi gaisuwar.
Haka Siraj ya amsa gaisuwar yana jin kamar ya shak'o wuyanshi.
Hannu yasa Aljihu ya ciro kuɗin da zasu kai dubu ɗari biyar ya aje gaban Gwaggo yana faɗin "Ni zan wuce kuma za a shigo da abinci yanzu Allah ya baku hak'uri"
"Amin Yarima Allah yayi maka albarka ya taimake ka akan dukan k'uduri ka na Alheri.. "
Momi ce tayi mashi Addu'a idonta cike da kwallah,
Saida ya haɗe yawu sannan ya kalli Qasin "Ina Maryam ina son nayi mata gaisuwa ?"
haka Qasin yaji maganar kamar izgilanci uffan bai iya ce masa ba Siraj ne kawai ya iya cewa "Ai basai kayi mata ba tunda kayi mana ya wadatar..."
"A'a bari a kira masa ita yana da kyau ita ai yayi mata"
Momi ce ta tashi da sauri ta faɗan haka ta nufi ɗakin da Mairo take.
Daker Momi ta samu ta lallaɓata ta fito. da sauri Yarima ya karasa kusa da ita yana kallon fuskanta ya soma mata gaisuwar "Sannu Maryam Allah ya jikashi kinji Allah ya baki wani ya baki hak'uri..."
Kai kawai ta ɗaga mishi tana kuka, ya ɗan daɗe tsaye sannan yayi musu sallama ya fice.
*FEW HOURS LETTER..........*
Qasin ya tashi ya shiga ɗakin da Mairo take,
Zaune ya tararda ita rakuɓe gefe ɗaya tana shasshekar kuka guri ya samu nesa da ita ya zauna ya kafa mata ido.
Sai a lokacin ya lura da ramar da tayi wani irin tausayin ta ne ya mamaye masa k'ok'on zuciya _she's too young for that yarinyar nan tun tana k'arama ta tashi babu iyaye tayi rayuwar k'auye yanzu kuma mijin da aka aura miki ya rasu kai gaskiya kina cikin halin rayuwa Maryam_ a zuciyarsa yake wannan tunani yana ɗan motsa baki.
Can ya tashi ya k'arasa kusa da ita "Maryam..." a hankali ya kira sunanta.
ɗago kai tayi ta kalleshi da jajayen idonta "Kin ci abinci ?" ya tambaya
Kai ta girgiza masa alamar a'a "Toh miyasa ?" dak'er ta iya buɗe baki tace "Bana iya cine"
"Ai daurewa ake yi Maryam ke bakinsan komai na duniya ɗan hak'uri bane mi kike ao yanzu kici ?"
"Bana son komai bazan iya ciba"
"A'a ai zaki wuni haka ba tun ɗazun baki ci komai ba kuma yanzu ace ki kwanta haka faɗamin mi kike so ?"
Fashe masa tayi da kukan shagwaɓa "Nidai bana son komai kawai ka kyale ni"
"Bazan fa kyale kiba sai kin faɗa min abunda kike so kici ko kuma duk abunda na kawo miki ki ci"
"Qasin miye haka ne tace bata so ba zaka kyale taba"
Kamar daga sama yaji maganar Mansura dake tsaye bakin k'ofa. Juyowa yayi ya kalleta tare da jan tsaki "Mtss wai Mansura mi yake damunki ne ke ko ina sai kin nuna bak'in halinki ?"
"Babu wani bak'in hali sai gaskiya Yarinyar nan dai naga tak'aba take dan haka dole ne ka ɗaga mata k'afa"
Hannu ya ɗaga mata "Mansura yau yau fa akayi mutuwar nan ba jiya ba ko shekaran jiya dan haka kar k'wak'walwar ki ta yayo miki mummunan zato akaina kosan irin abunda kike yi dan ke ba yarinya bace"
Shiru tayi ta tsura masa ido dan tasan halinsa sarai zai iya yimata tatas in halin nashi ya motsa,
Kallon Mairo yayi "Ke mi kike son ki ci ?"
ganin faɗan da yayi ma Mansura kuma fuskarshi a haɗe yasa ta ɗan ji tsoro share hawayenta tayi murya k'asa k'asa tace "Shayi nake so"
kai ya ɗaga mata "Ok bari naje na nemo miki yanzu kinji ?"
ita kan ta ɗaga mishi tana kallon Mansura data wani mugun haɗe fuska,
hak Qasin ya tsara gefenta ya fice.
*©KHADEEJA CANDY*
[6:02PM, 3/23/2017] Khadeeja_ce👌: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
*_KHADEEJA CANDY_*
Candynovel.wordpress.com
*50.*
Koda Qasin ya dawo ya tararda Mairo waje ta ɗora kanta saman cinyar Momi da alama wata maganar