Showing 66001 words to 69000 words out of 85263 words

Chapter 23 - MAIRO Complete Hausa Novels by Khadeeja Candy.txt

04 Apr 2026

892

kuje kuka duba mata na bafa"
   Yana k'ok'arin zaunawa yayi maganar.
  Momi tace “D'azun naso muje sai kuma nace k'ila baku tashi daga bachi ba"
   “A'a mun tashi tun ɗazun take tambayarki"
Gwaggo dai kallonshi take tana mamakin yadda yake ta matarshi ko Mairo bai tambaya ba.
  Momi ta tashi tana faɗin “Ku tashi muje mu duba ta"
Duk tashi sukayi suka Momi na gaba suna baya suka nufi part ɗin.
   Suna fita shi kuma ya tashi ya hau sama.
“Maryam... " ɗakin Momi ya shiga yana kwala mata kira
Jin motsin ruwa a bathroom ya tabbatar mishi da wanka take. 
  Zaunawa yayi yna kallon gown ɗin dake gefen shi da alama ita zata saka.
   Bayan kamar minti biyar ta ɗaura tawul ta saka hijab ta fito.
tana ganinshi ta ɗanyi murmushi “lahh Yaya"
Bai amsa ba ya tsareta da ido har ta ɗauki rigar ta koma toilet ta saka sannan ta fito,
    Tsaye tayi bakin kofar toilet ɗin tana kallonshi still tana murmushi.
Sai a lokacin shima yayi murmushi ya mika mata hannu alamar tazo, k'arasa tayi saidai bata mik'a mishi hannu ba,
  Fuskarta ya shafa “Ya kika kwana?"
   “Lafiya kalau"
“Kin karya?"
“Eh tun ɗazun"
    “Toh yayi kyau ni ina nawa?"
  Dariya tasa mishi ta juya ta nufi kofar fita.
Tashi shima yayi ya rufa mata baya suka sauko downstairs tare.
    Ganin ta nufi kitchen yasa yayi saurin dakatar da ita
“Ke ni wasa nake miki dawo naci abinci"
  Juyowa tayi “Da gaske"
  “Eh nayi brackfast tun ɗazu wasa bake miki"
    Dawowa tayi ta zauna saman kujera tana murmushi'
   Murmushi ya mayar mata sannan ya fice gabanshi na faɗuwa.

***
       Da gudu suka shigo parlor suna dariya
“Lafiya?"
Mansura ta tambaya
Rahila ta zauna kusa da ita tana faɗin “Kice yar aiki aka kawo miki ba kishiya ba daman akan wannan ce kike tada hankalin?"
“Itace ina kika ganta?"
  “Gata can Garden ai ki kwantar hankalinki k'awata indai wannan ce sai mun lalata Auren sannan mu haɗa da kirsar k'asa"
“Dan Allah ki taimaka min"
    “Karki damu ba dai wannan Maryam ɗince ba yarinyar da Yarima yake so Wallahi saina lalata Auren nan"
  Kvanwarta ta dafa ta “Ni kuma shawarar da zan baki karki kuskura ki sake su kwana ɗaki ɗaya kuma daga yau kullum ita wanke-wanken ki da shara da moping idan tayi miki kallo biyu ki kasheta mari sannan ki riga chusa kanki gurin mijinki dan nasan har gobe Qasin yana sonki"
Shiru tayi  tana ɗan murmushi kamar mai tunani.

_THE JOURNEY IS BEGIN..._👌🏿


*© KHADEEJA CANDY*
[11/9, 6:59 AM] Khadeeja Candy: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

     *_KHADEEJA CANDY_*
Candynovel.wordpress.com

*Vote me on Wattpad* @khadeeja_Candy

*58*

Kuka Mairo take sosai kanta na saman ciyar Gwaggo sai yanzu take jin ba daɗi kamar kar su Gwaggo su tafi.
  “Kiyi hak'uri Mairo ai Aure haka ya gada"
  Da kuka Gwaggo tayi mata maganar tana buga bayanta,
   Momi ta mik'a hannu ta rik'ota “Yi hak'uri kinji Maryam ai ba nisa zatayi miki ba duk lokacin da kika so ganin su ai sai a kaiki kuma suma akai-akai zasu rik'a zuwa"
  K'ara rushewa tayi da kuka ta kwanta jikin Momi,
    Gwaggo ta share hawayen ta ta kalli Momi “Ga Amana nan mun baki ki rik'e ki kula da ita in kikaga tayi ba dai-dai ba ki ɗorata a hanya"
  Momi ta ɗaga kai “In'sha Allahu zan rik'eta Amana"
“Toh Allah ya tayaki rik'o ya bata ikon yi miki biyayyah"
   “Amin Gwaggon yara"
   Momi ta faɗa tana ɗan dariya.
   “Bari naje na dubo girkin can karya kone"
Momi na tashi Gwaggo ta janyo hannun Mairo.
   “Mairo ki rike hajiya Uwa kinji kinga dama can Uwar ki ce barre yanzu dan haka ban saɓa mata ko ta baki umarni ki k'i bi kiji?"
  Kai ta ɗaga mata idonta a kumbure
   “Kuma bari kiji na faɗa miki duk kikaga Qasimu yayi miki wani abu da baki so ko matarshi toh ki faɗa mata dan naga sunan wannan matar kuma karki saurara mata duk tayi miki can mutunci Ki mata Idan kuma ta nemi zaman lafiya toh ku zauna da tayi miki wani abu Ki fada ma maman shi in kikaga bata ɗauki matakiba ki bugo min waya"
   Nan ma kan ta ɗaga
“Kuma ki bi mijinki sau da k'afa banda rashin kunya duk huɗubar da nayi miki karki zubar da ita"
   “Toh Gwaggo amman dai zaku k'ara zuwa ko?"
  “Zuwa ai dolene Mairo dole ne na rik'a zuwa ina ganin yadda zamanku zai kasance dan naga wannan matar tashi ba kirkirne da itaba koda yake naga kowa gidan shi daban (Part)  dan jiya ya kaimu munga gidan"
   Kwantawa tayi jikin Gwaggo tana shan majina

***
      Kwance take saman jikinshi suna kallo,
  “Dear"
   “Na'am"
“Amman dai ba zaka raba mana gida da ita ba ko?"
Cike da mamaki ya kalleta “Miya kawo wannan maganar kuma keda baki son maganar ta?"
  “Ba komai kawai dai naga hakan zai sa na ɗan rage abinda nake ji a kanta"
   “Toh Allah yasa ni daman banida niyar raba muku gida"
    “Toh Allah ya haɗa kan mu"
   Da mamaki yace “Amin dear Allah ya cigaba da shirya min ke"
Ya faɗa yana shafa saman kanta.
         Sun daɗe a haka sannan ya tashi ya shiga bathroom.
Wanka yayi ya shirya cikin k'ananan kaya ita kuma har lokacin tana kwance.
Kiss ya mana mata ya fito ya nufi part ɗin Momi,
Koda ya shigo ya tararda su Gwaggo parlor driving na saka musu kayansu both
   Saida ya gaida su sannan ya zauna kusa da Momi yana kalln Mairo “Mi akayi mata?"
   “Ba mata komai ba wai dan zasu tafi take kuka"
   Murmushi kawai yayi bai sake cewa komai ba har aka k'are saka kayan.
   Sallamar k'warai Qasin da Momi sukayi musu daman Abbah tuni yayi musu tashi sallamar dan tun washe garin zuwansu ya wuce Abuja.
   Har motar su ta tashi Mairo bata daina kuka ba daker Momi ta lallaɓata tayi shiru.
   “Haba ko ke fa amman tun ɗazu kukan nan ne kawai kike kinsan kuka fa baya da kyau"
    “Toh Momi ba na daina ba"
   “Yauwa toh nima ba gashi na jindaɗi ba Allah yayi miki albarka"
  “Amin Momi"
  Qasin ya ɗan murmusa “Maryam tashi kije kiyi wanka mai ɗinki na nan zuwa ta auna ki"
  Da sauri ta tashi ta nufi upstairs.
Momi ta k'ara mata “Kuma kici abinci"
Daga can ta amsa da “Toh"
   Tashi yayi yana faɗin “Nima bari na lek'a office"
    “Ok sai ka dawo"
Hannayenshi yasa aljihu ya fice.
   
      Sai goman dare ya dawo gidan.
Kai tsaye part ɗin Momi ya nufo hannun shi rik'e da bak'ar leda.
    A parlor ya tararda Mairo zaune sqman doguwar kujera idonta na akan tv.
“Ke aljana dare ne ranar kallon ki ko?"
Da sauri ta kalli k'ofar
   “Yaya har ka tsorata ni Wallahi"
  Zaunawa yayi kusa da ita “Allah ko?"
Murmushi tayi “Eh mana ina wuni"
   “lafiya kalau mai ɗinkin tazo?"
“Eh tazo Yaya ashe ko'ina aunawa take"
  “Eh mana saboda kar ɗinkin ya matseki ko yayi miki yawa"
Yayi maganar yana k'ok'arin bude ledar
  Cinyar kaza ɗaya ya ɗauka ya mika mata ledar da gorar yagot
  “K'arɓi ki ci dan nasan baki ci abinci ba kuka kika wuni kinayi ai yau sai kinyi mafarki su"
   Dariya tayi “A'a ba zanyi mafarki su ai sun riga sun tafi"
  “Ko sun tafi sai kinyi mafarkinsu"
.  “A'a Allah ba zanyi ba"
   “Toh mu k'ulla in kikayi mafarki su saina miki horo"
   “Eh na yarda amman ni kuma in banyi mafarki su sai na maka horo ka yarda?"
  “Eh na yarda yarinya gobe zaki yabawa aya zak'inta"
   Dariya tasa mishi “Kai dai zaka yabawa aya zak'inta zaka ji jiki"
    Dariya yayi sosai harda kwantawa a kujerar “Lallai yarinya nime zanji jiki? Zaki dai ji jiki idan ranar jin jikin tazo"
   Hannu ya kai kan ledar da sauri ta tashi tare da ledar “A'a Yaya ka ci naka fa wannan nida Momi zamuci"
    “Ai Momi bachi take kuma yayi miki yawa ba zaki iya cinyewa ba"
  “Wallahi idonta biu tana ɗakinta"
  Tashi tsaye yayi da sauri “Da gaske Momi ba tayi bachi ba?"
Gira ta ɗaga mishi as respond tana murmushi.
   Da sauri ya fice yana kallon stairs.

       _Washe gari_
   Tunda akayi sallar A'suba Mairo ta dawo parlor ta zauna sai rabon ido take can kuma ta tashi ta kunna tv.
   7 da yar mintuna Momi ta sauko k'asa da sauri Mairo ta risina ta gaisheta “Momi ina kwana"
Momi tayi murmushi “Lafiya kalau an dasa dag inda aka tsaya kan kallo ko?"
   “A'a Momi daman wannan film ɗin nake so kuma sun k'are"
“Toh muje kitchen a hada breakfast"
Remote ɗin dake hannunta ta aje suka nufi kicin ɗin tare.
   Aikin kawai suke amman hankalinta na wani guri da taji motsi sai taje ta lek'a.
Kacar taga sun gama aikin ta ɗauko ta kawo saman dining,
    “Momi naje na kira Yaya Qasin?"
Momi ta aje kula tare da kallonta “A'a ai kinsan ba nan yake breakfast ba"
  Ta marairaice fuska “Dan Allah Momi daga yau bazai k'ara ba wani abu zan faɗa mishi"
    “Indai wani abun zaki faɗa mishi jeki amman breakfast kan ba nan ba"
    "Toh"
Da gudu ta juya Momi ta kwala mata “Maryam zo ki ɗauki ɗan kwali"
“Toh bari nazo"
Momi ta girgiza kai “Oh Allah ya shirya"
   Da gudu ta faɗo parlor Mansura bata lura da Qasin dake tsaye jikin windo ba ta nufi k'ofar ɗakin shi.
“Ke..."
Da sauri ta juyo suna haha ido ta gaidashi
“Ina kwana?"
   “Lafiya kalau an tashi lafiya"
  Ido ta ɗan sakar mishi sanye yake da gundun wando mai kamar na bachi jikinshi babu riga.
   Kasa tayi da kanta ta juya ta nufi k'ofar fita.
Gudu yayi ya kamota “Ina zaki?"
   “Yaya jikinka babu tufafi"
   Kallon jikin nashi yayi sannan yaja suka zauna saman kujera.
    “Miya kawo ki nan?"
Fuskar zolaya tayi mishi tana dariya “Banyi mafarki su ba"
   Hancinta yaja yana murmushi “Oh kedai faɗamin gaskiya  Dan nasan fa sai kinyi mafarki su"
  “Banyi ba ai na faɗa maka sai kaji jiki"
  Dariya yayi ya rumgume ta Yana faďin “Wai ke baza kibar cewa sai naji Jilin nan ba ko?"
Wani yarrr taji kamar an tsoketa da alura. Duk tsigar jikinta ta tashi.da sauri ta ɗago tana kallon fuskarshi,
  Bai kula taba ya sake maida ita cikin faffaɗan k'irjinshi ya rumgume ta tsam-tsam.

      Can zuciyashi ta yayo mishi Mansura dake bachi.
ba zai iya da matsifar taba duk da yasan ba haramun ya aikata ba amman yasan in yanzu ta tashi daga bachi ta gani ba k'aramar drama ra'ayiba.
D'agota yayi “Momi ta haɗa breakfast?"
  “Eh tare mukayi amman tace karka zo wai ba nan kake breakfast ba" Ta bashi amsa idonta a kulle gam.
  Murmushi yayi “Toh jeki gani nan zuwa"
Saida ta sauka saman jikinshi sannan ta buɗe idon ta fice.
      Koda ta dawo ta tararda Momi na break ita Usman da Nura kujera taja ta zauna tana murmushi.
   Batayi minti biyar da zaman ba ya shigo sanye da doguwar jallabiya, a kujerar da ya saba zama ya zauna bayan sun gaisa da Momi.
  “Mi zakayi?" Momi ta tambaye shi ganin ya janyo plate
   “Breakfast Maryam tace nazo naci abinci"
Momi ta watsama Mairo harara.
Da sauri Mairo ta kalleshi “Lahhh" ganin babu alamun wasa a fuskarshi yasa tayi shiru ba tace komai ba.
   Sai suka magama cin abinci sannan ta kalleshi “Yaya ni naci yanzu mi zakayi min?"
  Momi tace “Ke kikaci mi?"
Da sauri ya tari numfashinta “Wai abinci take nufi jeko kiyi wanka kamin na tashi sai na faɗa miki"
   Tashi tayi har ta juya sai kuma ta juyo “Wai Momi ina Siraj?"
   “Yana Abuja Asabar ɗin da za kuzo ya tafi da safe yanzu can yake aiki"
    Bata sake cewa wani abuba ta nufi ɗaki.

Bayan su Usman ta tashi Momi ta kalli Qasin a natse tace “Yanzu matsayinka ya canja nauyi biu ne a kanka ko wace dolene ka bata hak'inta ban zalumci shi aure sai anyi hak'uri tun a Mansura ka gani balle Maryam da ba wani wayau ne da ita ba.
Amanace aka baka bana son naji wani saɓani a tsakaninku"
   Sai da ya nisa sannan yace “In'sha Allahu Momi babu abinda zai faru zan rike ta amana zanyi adalci a tsakanin su"
  “Toh Allah ya taimaka ya baka iko kuma bana son tayi zama mai tsayo agurina dan haka kasa himma gurin shirye-shiryenka ku tare"
    “Ai ni banida wani shiri Momi inba kayanta dake gurin ɗinki ba sai kuma kayan ɗakin da Abbah yayi mata oda ne basu iso ba amman nasan cikin watan nan komai zai kamala In'sha Allah"
“Toh Allah ya taimakamin haka nake so Allah Baku hak'urin zama"
Amsaba yayi da “Amin” Ya Tasha ya fice.
Wanka Mairo tayi ta shirya cikin bak'ar abaya.
Sai lek'e-lek'e take har bayan Azahar bata ga Qasin ba ganin Momi na bachi yasa ta nufi part ɗin shi,
    Sallama ta ɗingayi tun daga bakin k'ofar har takai tsakiyar parlor.
   Mansura ta fito kicin “Ke Uban mi kika zoyi part ɗina"
   “Ubaki!" Kai tsaye Mairo ta bata amsa Tana wani turo baki.
Mansura ta daki k'irji “Kan uba ke ni zaki zaga?"
      “Aini ban zage ki ba ke kikace uban mi nazo ni kuma nace ubanki kuma ni bama gurinki nazo ba Yaya nake nama"
    “Aini ban zage ki ba ke kikace uban mi nazo ni kuma nace ubanki kuma ni bama gurinki nazo ba Yaya nake nema"
   K'ofar ɗakin shi Mansura ta nuna mata “Shiga yana nan ciki"
Juyawa tayi ta nufi k'ofar ɗakin.
    Tana shiga Mansura ta rufa mata baya, tana shiga ta cakumo wuyanta “Uban kike zagi?"
Nan Mairo ta marairaice fuska “Ba ubanki ba ba keba dan Allah kiyi hak'uri"
Mansura  bata saurara mata ba ta watsa mata mari.
  Uhu Mairo tasa mata ta fashe da kuka Mansura bata saurara mata ba ta danneta a kasa tana dukan ta har sai da ta fasa mata baki,
     Da gudu Mairo ta baro part ɗin ta nufo part ɗin Momi tana kuka bakin k'ofar parlor ta faɗi tana murje-murje.
   “Wayyo na bani na lalace ta kashe ni wayyo Gwaggo Momi wayyo Allah wayyo Babana"
  Da gudu Momi ta fito tana tambayar ba'asi,
Zaro ido tayi tana faɗin “Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un miya fasa miki baki haka Maryam"
Cikin kuka ta nuna part ɗin Qasin “Mansura ce ta dake ni"
Momi ta rik'a ta “Mi kikayi mata?"
     “Ban mata komai ba wai dan naje neman Yaya Qasin shine tace na shiga ciki yana ɗaki dana shiga sai ta rufeni da duka Momi na shiga uku kasheni zatayi"
    Kai Momi ta girgiza cike da ɓacin rai ta rik'a Hannunta suka suka shiga ciki,
Bathroom Momi ta shiga da ita ta wanke mata bakin da fuska sannan suka fito.
   Waya Momi ta ciro ta danna ma Qasin kira.
    

*© KHADEEJA CANDY*
[11/9, 6:59 AM] Khadeeja Candy: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

     *_KHADEEJA CANDY_*
Candynovel.wordpress.com

*Vote me on Wattpad* @khadeeja_Candy

*59*

Yana isowa Momi ta nuna mishi fuskar Mairo tana masifa,
  “Dubi fuskar yarinyar nan kalli yadda matarka tayi mata duka"
   “Duka kuma?" Ya tambaya “Mi kika mata?"
“Ban mata komai ba wai dan naje neman ka"
    Zaunawa yayi saman kujera “Ke kuma Maryam miye na zuwa nemana in banda abinki"
  Momi ta tari numfashi shi “Miya kai wannan wace irin magana ce ko babu Aure tsakanin ku ai zata iya zuwq part ɗinka balle yanzu da take Matarka,
  Yadda fa kake Auren Mansura haka kake aurenta kuma duk hak'in da kasan yana kanka na Mansura haka na Maryam yake kanka.
   Kawai ka takawa matarka birki karta sake dakar min, ya dan amanace agurina ba zan sa mata ido tana dukanta ba tunda ba haihuwarta tayi ba"
    Tunda Momi take mashi faɗan idonshi na kan fuskar Mairo da ta ɗan kumbura.
  Hannu yakai ya taɓa kumatunta. Nan ta saki uhu ta fashe da kuka,
  Momi tace “Kagani ko zafi take ji taji mata ciyo sosai"
   Ajiyar zuciya ya sauke “Tashi muje pharmacy"
  Tashi tayi tana kukan da ban raba shi dana munafurci ba ta shiga ɗaki ta ɗauko mayafi suka fice.
      A pharmacy dak'er ta tsaya aka sa mata maganin sai ihu take tana kiran Abban ta,
     Bayan sun dawo ya kawota part ɗin Momi tare da maganin da aka bata. Da zai fice saida Momi ta k'ara jaddadamishi “Kafa jawa matarka kunne karta sake dukanta dan itama haihuwarta akayi kamar kowa ba sassak'ota akayi ba"
  "In'sha Allahu Momi zanyi mata magana ayi hak'uri"
Kawarda fuska Momi tayi shi kuma yasa kai ya fice.

        Tun daga yanayin shigowarta ta fahimci yana cikin damuwa dan ko Sallamar shi kamar a kasale yayi ta.
Bayan ta amsa ya zauna kusa da ita. “Sannu da zuwa"
  “Yauwa sannu Mansura mi yasa kika daki Maryam mi tayi miki?"
Taɓe baki tayi “Oh an daki yar'gol ko shine kabi ka haɗe rai toh an dake ta ɗin ko zama mata zakayi?"
   Wani kallo yayi mata mai cike da jin haushi. “Bazan rama mata yanzun ba amman duk kika sake dukanta zan rama mata dan ita mutunce kamar ke kuma abokiyar zamanki ce ba yar aiki ko ya ba dan haka karki sake sa mata hannu"
  Yana kaiwa nan ya tashi ya nufi bedroom ɗinshi. Tintsirewa tayi da dariya ta taɓa hannu “Lallai Qasin ni zaka faɗawa haka saboda kayi yar tsakin Amarya? Wato anci moriyar ganga za'a yada korenta ko toh baka isaba wallahi dan kowa yaci tuwo dani miya ya sha kuma indai dukane sai na mata shi sai dai in bata shigo part ɗin nan ba"
Haka ta dinga faɗa ita ka ɗai cikin parlor

Washe gari Mairo k'in cin abinci tayi duk yadda Momi ta lallaɓata k'in ci tayi ita la dole ga mai ciyo a baki.
   Saida Qasin ya shigo ya sata a gaba sannan ta ɗanci ko shi bawani abin kirkiba.

    Haka sukayi ta lallaɓata shida Momi har suka samu ta warke.

   _Ranar Assabar..._
Duk da yake yau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login