Showing 1 words to 3000 words out of 33915 words
Chapter 1 - WATA DUNIYA COMPELET HAUSA NOVELZ BY YAR GATAN MAMA.txt
*____________________________________*
🌍WATA DUNIYA🌍
LABARI/RUBUTAWA
KHADIJA S.SAMINU
('YAR GATAN MAMA)
MARUBUCIYAR.....
👇🏻
RAYUWAR MU!
A WANI GIDA
RANA DUBU
MAGANIN KAR AYI(Kar a soma)
And now....
⚔️WATA DUNIYA⚔️
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️
GODIYA
Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga sarkin sarakuna lillahil wahidul ƙahhar!Wanda bai haifaba ba'a haifeshiba,mai jiya mai yau mai yanzu da anjima.Muna godiya agareka wadda bamui mata iyakaba ya mahaliccin aljanu da mutane,sama da ƙasa dama komai da komai.
JINJINA✊🏻
Jinjina taban girma agareku masoyana,har kullum ina alfahari daku da yabon da kukeyimin,fatana Allah yabarmu tare yashiga lamuranmu ameen.
GATANA ♥♥♥
Gatana MUHAMMADUR RASULILLAHI dukkan wata alaƙa idan ba takaba shirme ce! Hasara ce! Taɓewa ce! bata ƙarko,ƙaunarka itace aikinmu asonka aka haifemu muka girma,dominka muke rayuwa kuma dominka zamu koma gamai kowa mai komai,har kullum fatana kasoni kasoni kasoni Muhammadur' rasulullahi kashiga lamurana kabiyamin buƙatuna kadaɗamin ƙaunarka nida duk wanda yace ameen, sallallahu alaihi wasallama.
GABATARWA!!!
Wannan labari ƙagaggen labari ne,banyishi dan wasuba,nayishi dan Girman Allah dan mutane masoya addinin musulunci da musulmai,ban yarda wata ko wani su juyamin littafiba yin hakan base nafaɗaba,idan anga kuskure ina roƙon asanarmin domin nagyara insha Allahu.Nagode
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI.
⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️
SHAFI NA 1&2.
⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️
✍🏻....
A fusace sarki ZALIMUZ-ZAMAN yajuyo da rinannun idanuwansa ga gimbiya ZALMAT cikin ɓacin rai da ƙunar zuci yace......
"Ki saurareni da kunnen basira kiji abinda zan faɗamiki dakyau,sanin kanki ne bana wasa bana alfarma ga dukkan wanda nagane cewa shi maƙiyinane,ba ruwana da alaƙata dashi inhar zaishiga gonata nikuma zansa fatanya nadatse kansa domin bani nakawo shiba! Da wace hujja za ki amfani ki sanar dani dalilinki na barin MUSLIM araye"?.
ZALMAT ce ta ɗago da kanta sannan ta sauke idanunta afuskar sarki ZALIMUZ-ZAMAN wanda tari ne ta cukuikuye ta tattare kamar jiƙaƙƙen tsumma saboda ɓacin rai,kallon farko datayi masa taga zallar masifar dake fitowa daga ƙwayar idonsa,sunkuyar da kanta tayi akaro naba adadi kafin tasake duƙƙad da kanta ƙasa tace.....
"Yakai wannan sarki mai dogon zamani,inamai sake baka haƙuri tare da baka baki akan kayi haƙuri bisa tseratar da maƙiyinka da nayi,banyi haka danna tozartakaba ya BABANA! Nayi hakane domin nacanzawa maƙiyanka tinani akanka sannan nashiga jikinsu yadda nan gaba ɗaukar fansa akansu bazai bamu wahalaba.
Ya kai wannan sarki mai dogon zamani! Inaso kabani dama nan da wasu ƴan kwanaki ƙalilan inaso nakoma cikin maƙiyanka kuma maƙiya addininmu namusu ɓadda kama nacisu da yaƙi"
"ZALMAT!!! Kidawo da hankalinki jikinki kinutsu kisan me bakinki yake furtawa akan ma'abota addinin MUSULUNCI!! "
ZALMAT ta sake duban mahaifinta Sarki ZALIMUZ-ZAMAN sannan tace....
"Yakai BABANA! Ina sane da ƙiyayyar dake tsakaninka da waɗancan ƙananun mayaƙan,idona bai rufeba yakai BABANA! Burina akullum mune zamui nasara akansu basu zasui nasara akanmuba,kabani wannan damar domin na yiwa kaina na yiwa akwatin sihirinka alƙawarin sena kawoma kawunan maƙiyanka ka yi dariya ka tofamusu yawun ƙasƙanci sannan ka ajjesu a wukaƙantaccen waje wanda mutanenka zasu dinga kallonsu kaima kana kallo kana alfahari dani".
ZALIMUZ-ZAMAN ya kalli ƴar tasa ZALMAT cike da so daƙaunarta cikin shauƙi da jindaɗin kalamanta yace...
"Yake Ƴata! Inamai tabbatar miki na amince da buƙatarki kije kifara shirin tafiya garin DEENUL-ISLAM!.
To amma banji kinyimin maganar ɗauko TAKOBIN KOGON ƊAUKAKA ba,shin ko kin manta ne"?.
"Ban manta da itaba yakai BABANA,ina sane da ita domin ma itace tafarko acikin lissafina"
"To yanzu idan kintafi DEENUL-ISLAM! waye zaidinga baki kariya kenan"?,
"Akwai buƙatar kahaɗani da jajurtattun mugayen aljanun daka mallaka yakai Babana,sannan kabani wani ɓangare daga TASKAR SIHIRINKA saboda kare kaina alokacin da wata musiba ta afko inda nake azaune"
"Ina alfahari dake Ƴata ZALMAT! Har kullum kece ke ƙoƙari akan maƙiyana,bisa wannan gudummuwa da kike bani,nayi alƙawarin baki kujerata aduk sanda kika kawomin kawunan sarakuna guda uku,sannan kika danƙamin TAKOBIN KOGON ƊAUKAKA ahannuna,awannan lokaci nikuma zansauka daga kan wannan kujera tawa nabaki domin kema kigudanar da mulkinki kiyaƙi MUSULMAI"
ZALMAT ce ta ɗago da saurin gaske tare da kallonshi cikin rawar baki take faɗin....
"Kawunan waɗanne sarakuna kakeso nakawo maka ya Baba na?
Sannan a'ina ne zansamo wannan takobin da kake faɗa?
Kuma zuwa nan da wane lokaci kake buƙatar nacika waɗannan aiyuka daka bani"?
ZALIMUZ-ZAMAN ne ya karkace ya bushe da wata mahaukaciyar dariya wadda seda ilahirin ɗakin ya amsa ,ya daɗe yana ƙyaƙyatawa kafin ya gimtse bakinsa ya kalleta yace.....
"Yake Ƴata! Ban ƙayyademiki lokacin da zaki kawominba,saboda nasan yadda dukansu suke da mummunan hatsari wanda duk wanda ya shigesa baya iya fita koda kuwa zai mallaki gaba ɗaya dodannin tsafin dake faɗin wannan duniya.
Kema nabaki wannan aikine domin na jarrabaki sannan nabar tarihi cewa ƳATA ZALMAT tayi abinda dubun dubatar sarakuna suka kasa,ciki kuwa harda ni kaina...
Kawunan sarakuna Uku dana ce kikawomin ba kowaɗanne sarakuna bane illa!! SARAUNIYA SINIYYA!,SARKI KAMALUD DEEN! da SARAUNIYA ZULFA.Waɗannan sarakunan uku duka suna mabanbantan waje kuma kowannensu yana da ƙarfin mulki da mayaƙa sannan kuma guda biyu daga cikinsu suna ɗauke da Addinin musulunci, bazan cika burikana na duniya ba senaga kawunansu agabana.
Sannan wajan da zaki samo wannan TAKOBI ba ko'ina bane illa 🌎WATA DUNIYA 🌎"
SARKI ZALIMUZ-ZAMAN yana kawowa nan azancensa ya miƙe tare da shigewa yabar ZALMAT azaune.
Tinani ne yashiga zarya cikin ƙwaƙwalwarta lokaci guda taji gabanta yana tsananta faɗuwa,"Ni yanzu ZALMAT ta'ina zanfara kenan acikin waɗannan ayyuka da suka riskeni yanzu?
🌎🌎🌎🌎🌎🌎DEENUL-ISLAM!
Cike da jarumta MUSLIM yake sanyawa SARAUNIYA SINIYYA magani aguraren dataji raunuka sanda suke yaƙin ceton rai tare da rundunar SARKI ZALIMUZ-ZAMAN,babu abinda Sarauniya SINIYYA take iyawa banda ambaton Ubangijin talikai,bayan sunɗau wasu lokuta ne ta buƙaci MUSLIM yabata ruwa tasha.Cikin sadaukarwa yatashi ya kalli gabas,yamma,kudu da arewa yaga bai hangi ta inda zaisama mata ruwan dazata shaba gashi se wahalalliyar shaƙuwa ce take sarƙe mata numfashi.Tajigata ainun dan daƙyar take iya buɗe idanunta wanda suma suke mata zugi kamar anzuba mata barkono.MUSLIM ne yana tsaka da roƙon ALLAH ya hanyi wani siririn kogo wanda yake da tabbacin jaririma bazai iya shiga cikinsa ba balle kuma shi ƙarfaffan namiji maiji da ƙwanji,ruwane kawai yake kwarara tacikin siririn kogon dan yana iya hango yadda ruwa ke zuba kamar da bakin ƙwarya.Wani daɗine ya ratsashi sanda sukai ido biyu da ruwan,cikin ƙarfin hali yasake jan ƙafarsa wadda takemasa zugi da raɗaɗi sakamakon ciwukan da sukai mata ƙawanya.
Yana isa daf da bakin kogon ya hangi wata narkekiyar macijiya sai azababben sheƙi da walwali takeyi tana ƙoƙarin tura kanta jikin wannan siririyar ƙofar kogon.Caccaka kanta takeyi iya ƙarfinta tana samarwa kanta hanya inda cikin ƙanƙanin lokaci batare da MUSLIM ya ankaraba yanemi macijiyar yarasa bayan tayiwa kanta hanya ta wuce inda zata,cikin ikon Allah ya hangi ruwan yanata kwaranyowa tacikin wannan hanyar yana fitowa harya yiwa kansa hanya yana gudu kamar ana hankaɗoshi.
ALLAHU AKHBAR!✊🏻Kalmar data fito daga bakin MUSLIM kenan inda ya yunƙura cikin sauri yayi inda zai sadashi da ruwan domin yad'iba yakaiwa SARAUNIYA SINIYYA tasha.
Isarsa inda ruwan yake keda wuya ya..........⚔️.
Kaɗan daga cikin ⚔️🌍WATA DUNIYA 🌍⚔️kenan ina fatan zakuyi haƙurin bibiyata sannan ku sambaɗamin ruwan comment wanda zaibani k'warin gwiwar cigaba dakawo muku shi akan lokaci nagode.
⚔️⚔️⚔️⚔️⚔️
Domin gyara sharhi ko bada shawara atuntuɓeni ta wannan layin👇🏻
07047530638🌍⚔️
Allahumma Salli ala Muhammadir'rasulullah..!!!Sallallahu alaihi wasallama💖
ƳAR GATAN MAMA✍🏻.
⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️
⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️
LABARI/RUBUTAWA
KHADIJA S.SAMINU
(ƳAR GATAN MAMA)
Marubuciyar......
A WANI GIDA
RAYUWAR MU!
MAGANIN KAR AYI!
nd now......
⚔️WATA DUNIYA⚔️
⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️
SHAFI NA 3&4
⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️
Isarsa inda ruwan yake keda wuya yasaka maɗebinsa tare da kanfato ruwan yatafi da sauri domin yakaiwa SARAUNIYA SINIYYA,yana zuwa yatarar da ita kwance inda yabarta babu alamunma akwai numfashi atare da ita.
Cike da karaya yake shafamata ruwan afuskarta yana addu'ar Allah yasa tatashi.Ya ɗauki tsawon lokaci ahaka da ita batare data farfaɗoba Dan haka ya shiga zullumi yana tinanin yadda suka tsinci kansu shida Sarauniya SINIYYA kwatsam ya hangi wata guguwa mai ƴarfin gaske ta tawo ya saitin inda suke,bai ankaraba segani yayi ta taddasu inda ƙasa tashige masa idanu lokaci guda yarufe idon tare da ambaton Ubangijin talikai yana neman yayi musu taimakonsa.
Dajin gaba ɗaya ya hargitse bishiyo sek'ara sukeyi inda halittun dajin kegudu suna iface-iface saboda yadda guguwar ke ƙoƙarin raba bishiyun da mazauninsu,sunɗau tsawon daƙik'u ahaka kafin daga bisani guguwar taɗauke tamkar bata taɓa faruwa ba.MUSLIM ne yakai dubansa ga gefen hagunsa inda yakejin wani wuci mai shiga jiki yana ta shi awajan,hankalinsane ya tashi sa'ilin da yayi tozali da wani jibgegen Aljani me matuƙar muni da ban tsoro na tashin hankali.
Duk wasu nau'o'i na muni wannan jibgegen Aljanin yahaɗasu,baƙik'k'irinne mai azabar muni yadda idan ka kalli cikin idanunsa sekaji inama -inama saboda yadda kanka zai sara sakamakon ganin munin wannan mushrikin Aljani.
Kallon inda MUSLIM yake tsugunne Aljanin yayi tare da bushewa da wata mahaukaciyar dariya wadda seda ilahirin dajin ya amsa inda wannan dariyar ta tsorata halittun dake cikin dajin......
Dariya yake ba ƙaƙƙautawa inda fuskarsa ke wani cakuɗewa tana cukuikuyewa yanda ba wanda zaizo yakalleshi awannan halin saboda muni,idan kuma mutum yayi nasarar kallon wannan Aljanin to tabbas bazai yadda yasake ba saboda yadda mara imanin Aljanin ke wangale bakinsa dake ɗauke da wasu jajayen haƙora zaro-zaro kamar takubba.
Duk wannan abubuwa dasuke faruwa basu sa SARAUNIYA SINIYYA ta farkaba daga dogon suman da tayi.
Ba tare da MUSLIM ya luraba wannan gibgegen Aljanin mai bantsoro ya bayyana agabanshi sekace anjefoshi,kallon MUSLIM yayi sosai kafin yaɗaga takobinsa sama cikin zafin nama yayo kan MUSLIM da ita.
Tana daf da isowa jikin MUSLIM kenan ya daka wani wawan tsalle yaigefe guda takobin ta sauka awani waje daban....
Cike da ɓacin rai wannan jibgegen Aljanin yasake ɗaga takobinsa tare da kurma ihuu! yayo kan MUSLIM.Takobin tayi nasarar zuwa inda MUSLIM yake domin bata sauka ko'inaba se acinyarsa.
Cike da murnar samun nasara Aljanin yasake ɗaga takobinsa sama domin yasake daɓawa MUSLIM akaro na biyu,wata mahaukaciyar mulmulalliyar guguwa ce tataso wadda tai silar faɗuwar takobin daga hannunsa yana tangal-tangal tare da kare idanuwansa.
MUSLIM ne yai ƙarfin halin ɗago kansa domin yaga wane gagarumin abune yadakatar da mutuwarsa adaidai wannan lokaci?
Idanunsane sukayi tozali da Gimbiya ZULMAT ɗiyar sarki ZALIMUZ-ZAMAN tsaye afarfajiyar sararin samaniya ɗauke da wata sharɓeɓiyar takobi wadda tsininta ya tokare zuwa ƙasa inda MUSLIM da SARAUNIYA SINIYYA suke idanunta sunrine sunyi jajir kamar gauta saboda tsananin ɓacin rai.
Wata iriyar girgiza dajin yakeyi kamar ana juyashi,yayinda wasu daga cikin bishiyun dajin suke barin mazauninsu su faɗi ƙasa,ba komai ya haddasa wannan bala'inba illah wani wahalallen ihu da Gimbiya ZULMAT dakeyi tana saukowa izuwa dandanyar ƙasa tana mai ɗaga takobinta sama da nufin ta sauketa akan wannan Hatsabibin Aljani mai matuƙar muni da bantsoro.
Cikin zafin nama ya kaucewa sarannata ta hanyar ɓacemata tanemeshi ta rasa,tana huci tare da sauke numfashi awale tasaki takobin nata tare da sakin jiki ta zauna adandanyar k'asa tana kallon yadda MUSLIM yake yatsina fuska yana kallon raunin cinyarsa da alama ba ƙaramin ciwo Aljanin yajimasaba.
Kallonsa ta sakeyi akaro naba adadi kafin ta yunk'ura ta tashi taje inda yake tsakanin zama da kwanciya ta kalleshi tare dayimasa sannu,baiko kalleta ba ballantana tasa ran zai amsamata,hakanne yasa tabar inda yake takoma inda SARAUNIYA SINIYYA ke kwance kamar matacciya tacigaba da sakamata magani araunukan jikinta.
Taɗau lokaci ahaka kafin daga bisani ta taso tadawo wajan MUSLIM ɗauke da magungunan shima tahau sanyamasa batare data nemi izini awajansa ba.Yanajin yadda azaba take ratsa ilahirin jikinsa sanda take sakamasa maganin amma dake namijin mazaje ne bai nunamata afuskaba balle ta fahimci ya zafin ciwon yake,sai da ta tabbata tagama sanya masa maganin sannan tatashi taɗaukomai tulun ruwan sha ta miƙamai,kamar bazai karɓa ba kuma seya tsinci kansa da karɓa harda yimata godiya sannan yakai bakinsa.
Gefe guda takoma ta zauna tare da tsunduma cikin tinani mai nisan gaske.
Batare dasuka duka sunluraba suka hangi wata jibgegiyar..........
⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️
Domin gyara sharhi ko bada shawara atuntuɓeni ta wannan kayin👇🏻
07047530638.
Allahumma Salli ala Muhammadur'rasulullah❤️SAW 💖
ƳAR GATAN MAMA✍🏻.
⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️
⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️
LABARI/RUBUTAWA
KHADIJA S.SAMINU
(ƳAR GATAN MAMA)
Marubuciyar......
A WANI GIDA
RAYUWAR MU!
MAGANIN KAR AYI!
nd now......
⚔️WATA DUNIYA⚔️
⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️
SHAFI NA 5&6
⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️
Batare dasu duka sun luraba suka hangi wata jibgegiyar damusa wadda girmanta ya zarce tinani,tsoro ne yakama MUSLIM saboda kallon yanayin dayake ciki na rashin ƙwarin jiki ga kuma saran dake cinyarsa bazai bari yayi wani yunƙuri dazai kare SARAUNIYA SINIYYA ba.ZULMAT ce ta miƙe tsaye da wani mugun sauri tare da nufar inda damusar da tawo.
Kallon kallo akafara tsakanin damusa da GIMBIYA ZULMAT kowannensu na neman ran ɗan uwansa.
Batare da ZULMAT ta kula ba damusar nan tadaka tsalle da nufin ta sauka akan GIMBIYA ZULMAT,cikin zafin nama ZULMATA ta kauce mata wanda hakan ya dalilin faɗuwar damusar ak'asa ragwaf......
Faɗa sukeyi sosai tsakaninta da wannan damusa ba ƙak'k'autawa,tashi sama GIMBIYA ZULMAT takeyi tana dirowa tare dakai sara suka ga wannan damusa,k'arar da ZULMAT keyi yaisanadiyyar farkawar SARAUNIYA SINIYYA daga dogon suman da tayi,idanunta fes ta saukesu akan Zulmat dake ta faɗa da Damusa.
Sake buɗe idanunta tayi sosai saboda mamakine yakamata ganin GIMBIYA ZULMAT na faɗa da damusa a inda suke amma batai yunk'urin kashe suba.
A'iya saninta ZULMAT babbar mak'iya Addinin Musulunci ce ita da mahaifinta,"to amma me yasa take ƙok'arin karemu bayan bata tare damu"?,"menene dalilinta nayin hakan"?.
SARAUNIYA SINIYYA ce kewa kanta waɗannan tambayoyi dukda tasan batada mai bata amsoshinsu.
Mamakintane ya ninku sanda taga Damusar nan nawani shu'umin tsalle tana dira kan Gimbiya ZULMAT yayinda ita kuma tafara kasa kare kanta,sunɗau wasu ƴan daƙik'u ahaka kafin Gimbiya ZULMAT tasamu nasara cakawa wannan DAMUSA mashi agefen idanunta guda ɗaya.
Wani razanannen ihu Damusar tayi wanda saida ya haddasawa dajin girgiza gaba ɗaya, ihu Damusar taci gaba dayi tana zagaye inda sukaifaɗa da ZULMAT,bazato babu tsammani sukaga Damusar tayi wata girgiza ta koma wani murtukeken Aljani mai bantsoro wanda atake yazube awajan saboda jigata.
ZULMAT ce takai dubanta gareshi tare da kecewa da wata muguwar dariya ganin tayi nasara akansa.Matsawa tayi inda SARAUNIYA SINIYYA take zaune tana yimata sannu tare da ɗaukar tulun ruwa ta miƙamata domin tasha,batai musu ba ta amsa fuskarta lulluɓe da wani yalwataccen murmushi mai ƙayatarwa.
Kai ruwan bakinta tayi bayan tace...
"Bismillah!"
Tasha mai yawa kamar bazata barshi ba sannan tayiwa ZULMAT umarni data miƙawa MUSLIM yasha,baiyi musu ba ganin SARAUNIYA tasha yasa shima yasha yaƙoshi.
Bayan sunɗau wasu mintuna ahaka ne Gimbiya ZULMAT ta kalli SARAUNIYA SINIYYA tare da faɗin.......
⚔️🌍⚔️🌍⚔️
Tinda SARKI ZALIMUZ-ZAMAN ya tashi yashiga turakarsa yakasa zaune yakasa tsaye saboda yadda ƙwaƙwalwarsa take neman hargitsewa da tinani,ganin zai wahalar da kansa yanzu ne yasa yaɗau tulun giya yahau sha babu ƙaƙƙautawa ,saida yayi mankas sannan ya ajje tare da bajewa saboda yanaso yasamu hutu kafin yatashi yaɗora daga inda yatsaya.
Bayan yatashi ne yakoma inda kayan tsaface-tsafacensa suke yahau dube-dube akan ayyukan daya bawa ƴarsa ZULMAT domin yanason yasan tsakaninsu da mak'iyansu waye zaiyi nasara.Buga ƙasa yakeyi yana maimaitawa lokaci guda yana kallon madubin tsafinsa tare da karanto wasu ɗalatsiman tsafi masu wahalar ganewa.
Ya haɗa gumi sosai kamar wanda aka tsamoshi daga cikinruwa saboda ruɗanin daya shiga sanda yaga.........
⚔️🌍⚔️🌍⚔️DEENUL ISLAM.
MUSLIMAT ce tashigo turakar SARAUNIYA SINIYYA domin neman izini bisa shawarar dasuka yanke tsakaninta da MUSLIM akan tafiya ɗakko ⚔️TAKOBIN KOGON ƊAUKAKA⚔️ta iske basu dawo ba tunfitar dasukayi sa'ilin tana can tana bawa jakadiya sak'o.
Neman waje tayi ta zauna tare da............
⚔️🌍⚔️🌍⚔️
"Sarauniya ina mai neman afuwarku bisa abubuwa marasa daɗi dasuka faru tsakaninmu yaƙin daya gabata,sannan inamai neman alfarmarku daku zauna tare dani bima'ana inason nashiga cikinku saboda wani dalili"
ZULMAT ce take faɗin wannan magana idanunta nakan SARAUNIYA SINIYYA tanason ta gane ainayin abinda ke ran sarauniyar.
Gyaran murya Sarauniya tayi tare da gyara zamanta sannan tasake duban ZULMAT tace......
"Shin wane dalili ne yasa kikeson kishiga jikinmu kizauna damu?,
Kuma yabatun mahaifinki da saninsa zaki zauna tare da..........✍🏻
⚔️🌍⚔️🌍⚔️
Domin gyara sharhi ko bada shawara atuntuɓeni ta wannan layiin👇🏻
07047530638.
ƳAR GATAN MAMA✍🏻.
⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️
⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️
LABARI/RUBUTAWA
KHADIJA S.SAMINU
(ƳAR GATAN MAMA)
Marubuciyar......
A WANI GIDA
RAYUWAR MU!
MAGANIN KAR AYI!
nd now......
⚔️WATA DUNIYA⚔️
⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️
SHAFI NA 7&8.
⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️
"Shin wane dalili ne yasa kikeson kishiga jikinmu kizauna tare damu?,kuma yabatun mahaifinki da saninsa zaki zauna tare da mu?".
"Yake wannan Sarauniya mai dogon zamani,inamai tabbatar miki da cewa,zancen gaskiya mahifina ZALIMUZ-ZAMAN bashi da masaniya dangane da komowata cikinku da zama,sedai yana sane da taimakon MUSLIM danayi sa'ilin da ake gudanar da yak'in daya gabata,haƙiƙanin gaskiya ran mahaifina yaɓaci sosai,hakan yasa yake tinanin nima maƙiyarsa ce kamar ku tinda har zan iya taimakonku alokacin da kuke buƙata,komawata gareshi keda wuya ya fatattakeni yatozartani gaban jama'ar gari ya umarci afita dani domin ayanzu baida maƙiyar data kaini"
ZULMAT na zuwa nan azancenta tasa gefen hannunta tare da goge ruwan hawayen daya wanke mata fuska sannan taci gaba da faɗin......
"Yake wannan Shugaba mai adalci inason kiyimin adalci kizauna dani da zuciya ɗaya saboda ayanzu bani da wani abin dogaro idan ba ke da mutanenki ba,nazaɓi nadawo nazauna tare daku ne saboda nasan kuɗin bazakuƙi karɓata ba sannan....."
Katseta Sarauniya tayi ta hanyar faɗin.....
"Babu komai! Zan zauna tare dake kizama tamkar ɗana MUSLIM awajena,amma akwai sharaɗi guda ɗaya"
"Wane sharaɗi ne ya Shugabata"
Zulmat ta faɗa bakinta na rawa....
"a'a karki damu kanki,bawani abune mai wahala ba,inason nasanar miki cewa mu ma'abota addinin musulunci ne kuma kema yazame miki dole matuk'ar da gaske kikeson zama damu ki karb'eshiii"
Sarauniya na zuwa nan azancenta ta tashi tafara haɗa kayansu na matafiya domin so take suɗau hanya zuwa gida.
Haka kuwa akayi suka hau dokunansu sannan sukaɗauki hanyar zuwa DEENUL-ISLAM wanda shi ne ainihin garinsu.
⚔️🌍⚔️🌍⚔️
"Gyara kintsi dakyau! Gyara kintsi dakyau!! Allah yaja da ran SARKI KAMALUD-DEEN mai dogon zamani mai gaskiya da ruƙon amana,uwa uba mai son talakawa mai kishin addininsa wato MUSULUNCI"
Sarki ne yayi gyaran murya tare da faɗin.....
"Uumm! Barka dai,muna godiya da wannan yabo da akaimana.Amma me akeso afaɗamana haka dawurwuri?"
Waziri ne ya gyaran zamansa sannan yamaida kansa ƙasa yace.....
"Allah yaja zamaninka,daman wani bawan Allah ne ya iso wannan gari mai albarka sannan ya buk'aci akawoshi wajanka"
"Shin anbashi masauki mai kyau?
Anbashi abincin dazaici yasha?"
"Allah yaja zamaninka babu abinda ba'ayi masa ba,yanzu haka ya kimtsa kai kaɗai yake son gani"
"Tom babu damuwa,ashigo mana dashi ciki"
Bayan SARKI KAMALUD DEEN yabada umarni ne akatafi ashigo da baƙon daya sauka agarin......
Basu ɗauki wani lokaci ne segasu sunshigo dashi izuwa turakar sarki.
Wani dattijon mutum ne tsoho tukuf wanda shekarunsa sunkai kimanin shekara casa'in da haihuwa,domin kuwa tsufan