Showing 30001 words to 33000 words out of 33915 words
Chapter 11 - WATA DUNIYA COMPELET HAUSA NOVELZ BY YAR GATAN MAMA.txt
sani ba ashe duk abinda suke yi akan idon SARAUNIYA SINIYYA suke yinsa,,,,,,,WARRR,,,,.
*****Sun d'auki tsawon kwana ashirin da d'aya awata duniyar saboda suna yiwa mutanensu da basu mutu ba magani,yau ne suke shirye-shiryen komawa garuruwansu domin angama duk wata tattaunawa da za'ayi akan Inda za'abar wannan TAKOBI an yanke abarwa Yariman ahannunsa domin antabbatar da shima dukiya bata gabansa,zuwa wannan lokacin GIMBIYA AMINATU ta yi dogon nazari akan soyayyar ta da Yarima ta yanke cewar ta rabu da shi ta rok'i Ubangijin Musulunci daya bata Wanda ya fishi dan haka ta yanke bazata koma garinsu ba saboda bataso tazama silar b'acin zumuncinsu shi da Muslimat danta lura da gaske bazata barmata shi ba.
Bayan ta mik'e ne agabansu tai musu sallama kamar yadda addini ya tanadar sannan ta fara magana kamar haka...
"Ina mai farin cikin zama tare da Ku dan gashi dalilin hakan na had'u da babban rabo na rabauta da addinin musulunci nasamu babban rabo rabon da zanyi farin ciki ace Mahifina ZALIMUZ-ZAMAN shi ma ya samu, ko ba komai zanyi alfahari Ni da Mahifiyata da Mahaifina munkoma ga mahaliccinmu muna masu yarda da shi. Sai dai kash! Inaji ajikina mahaifina bazai tab'a shiga Musulunci ba saboda yadda ya d'auki rayuwarsa, na gode miki dake da jama'arki yake adalar Shugaba domin kin kyautatamini azaman da nayi tare da ke,tabbas ked'in ta dabance kuma naji dad'in yadda kikai k'ok'ari akan d'anki ya soni Wanda sonsa shi ya zamemin silar samun dukkan rabo asalin zuwa na garin DEENUL-ISLAM da sanin mahaifina ZALIMUZ-ZAMAN shi ya turoni domin na shiga jikinku Ku yarda dani sannan nabiyoku yazuwa Wannan DUNIYAR domin bincikensa ya nuna masa rundunar kice zatai nasarar d'aukar takobi, na yarda da duk abinda yace amma k'asan zuciyata ba abinda yaturoni zan aikata ba dan inajin soyayyar Yarima har raina"
Haka dai tabasu duk labarin yadda sukai da zancen sare kan sarakunan da ya cemata, da zancen fansar ran mahaifiyarta da taso d'auka sannan ta d'ora da fad'in...
"Amma a yanzu na fuskanci mahaifiyata baiwa ce ubangiji yayi Mata kuma shi zaibi Mata hak'k'inta ita da baiwarta da ya kashe saboda son zuciyarsa.
Sannan inamai baki hak'uri yake wannan Sarauniya mai adalci akan rabuwa daku da zanyi ayanzu, bazan koma garinmu SILDAN ba sedai zanshiga k'asashen musulmai domin d'aukaka Kalmar ALLAH! Kamar yadda na d'aukaka ta kakannina a baya,badan raina naso ba Zan rabu daku sedan farin cikin Wanda nazo dominshi shi da nasoyiyarshi dan na fuskanci zafin so bazanyi rashin adalci gareta wajan k'wace Mata farin cikinta ba abinda nayi miki abayama ina neman yafiyarki dan girman Allah!"
Ta fad'a idonta akan Muslimat hannunta ahad'e alamar rok'o yayin da idanunta ke zirarar da hawaye.
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Abinda leb'en SARAUNIYA SINIYYA ke maimaitawa kenan saboda yadda taji maganar GIMBIYA AMINATU daga ba zato ba tsammani ji take yi bazata iya rabuwa da Aminatu ad'an sabon da suka yi da ita ,tana tsaka da tunanin ta tsinkayi muryar MUSLIMAT cikin rauni tana fad'in...
"Ki gafarce ni yake kyakkyawar bak'uwarmu ma'abociyar hak'uri da kyawawan d'abi'u,tabbas na cutar da ke da kalamai marasa dad'i tare da mugun kallo bayan ke baki tab'a kallo na se cikin sigar salama! A zamana dake na aikata babban zunubi Wanda nakejin tsoro kada ubangiji yak'iyin yafiya agareni bazanso zama SHADDADU 'DAN A'DU ba daya dad'e yana sab'on ubangiji yana bashi dama amma ak'arshe taurin Kai da son zuciya ya hanashi zuwa ga alkairin da ke kiransa harseda ya halaka kum.."
Katseta Aminatu tayi ta hanyar tambayarta wane ne SHADDADU 'DAN A'DU? Nan taja hannunta suka sauna sannan tafara da fad'in...
"K'ISSAR IRAMA ZATUL IMAD..!
Wannan k'issar ita ce ta Shaddadu d'an A'du tafara daga.
'Allah ta'ala ya fad'a acikin alk'ur'ani cewa,"Ba ka ga ni bane yadda Ubangijinka ya aikata da A'DAWA da Irama zatul Imad,Wanda ba'a halicci wani gari a duniya kamarsa ba?"
~~~~~Alhamdulillahi nakusa gama wata duniya Ubangijin Musulunci ina godiya a gareka~~~~~
'YAR GATAN MAMAβπ»
NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ALLAH YA K'ARA MIKI LAFIYA DA ARZIK'I MAI AMFANIππ»ππ
END.......βπ»ππ»ππ.
βοΈππππβοΈ
SHAFI NA 79&80
βοΈππππβοΈ
K'ISSAR IRAMA ZATUL IMAD....ππ»ππ
Taci gaba da fad'in...
" Safiyanu ya ruwaito daga Mansur d'an Abiwa'il ya ce,"Wani mai suna Abdullahi d'an kulabata,ya fita Neman rak'uminsa da ya b'ata.
To yana cikin yawo a daji cikin Sahara a k'asar ADON,sai yai kicib'is da wani birni mai ganuwa da benaye da gine-gine masu tsawo.Yayin da ya kusa da garin sai ya zaci zai sami wani agun amma sai baiga wani mai shiga ko mai fita agunba.
Saboda haka sai ya sauka daga kan Taguwarsa ya d'aureta ya rataya takobinsa ya shiga ta k'ofar ganuwar.Yana shiga sai yaga wasu k'ofofi manya guda biyu,bai tab'a ganin irinsu a duniya ba,wajan tsawo da firma.
Sai yaga itacen da akai k'ofar dashi na turaren Udu ne,an lullub'eshi da yak'utu yalo da ja,hasken su ya game ko'ina.
Yayin da yaga ba kowa sai mamaki ya kamashi,ya bud'e k'ofar garin ya shiga sai yaga wasu irin benaye da aka gina su da Zubarjadi ya Yak'utu,an lullub'e su Lu'u-lu-u,sannan a kowane bene akwai d'akuna da aka gina su da zinare da azurfa da Yak'utu da Zubarjadi.
Yayin da yaga haka kuma baiga kowa agurin ba sai tsoro ya Kama shi.Sannan sai ya dubi layukan da suke cikin garin,sai yaga a kowane layi ga bishiyoyi nan sunyi 'ya'ya a k'ark'ashinsu ga k'oramu nan tana gudana suna d'aukar ido saboda tsananin kyau da haske.Sai ya ce "Lallai wannan ita ce Aljannar da Allah ya siffata wa bayinsa a duniya.Na gode wa Allah da ya shigar dani Aljanna."
Sannan sai wannan mutumin ya d'ebi duk abinda zai iya d'auka na daga zinare da azurfa da lu'u-lu'u da yak'utu da mirjani acikin wannan gari,sannan ya fito ya hawo taguwarsa yai ta tafiya har ya iso k'asar YAMAN ya sanar da mutane inda yaje da abinda yagani.Ya said a wasu daga cikin kayan da ya samo,bayan sun canza Kama saboda tsawon zamani.
Sai labarin wannan mutum ya yad'u har ya Kai kunnan KHALIFA SAYYADINA MU'AWIYA d'an ABU SUFYANU,da khalifa yaji wannan Batu sai ya aikawa magajin garin Sana'a yace azo masa da wannan mutumin.
Bayan da aka zo dashi Sayyadina Mu'awiya ya keb'e da shi ya tambayeshi abinda ya gani a tafiyar da yayi.Mutuminnan ya gayamasa duk abinda ya gani awannan birni da yanayin garin da kamanninsa.Sai sayyadina Mu'awiya bai gaskata labarin ba saboda girman abinda yaji,yacew bana zaton wannan labari naka gaskiya ne.Sai mutumin yace,to ai inada irin kayan da na d'ebo a garin, yace "Mene ne?" Yace "Lu'u-lu'u ne da almiski da za'far." Yace " Kawo mu gani." Da ya bashi ya sinsina sai yace baiji K'amshin almiskin ba,sai yasa a dandak'ashi,da aka dakashi sai K'amshi ya game wajan wajan,sannan sai khaifa gaskatashi.
Daganan sai khalifa yace "Ya za'ai is an sunan wannan garin da tarihinsa da ya Gina shi? Ni dai nasan babu wani mutum da akaba shi irinw abinda akaba ANNABI SULAIMANU(AS),kuma ko shi bai gina irin wannan birnin ba."
Sai wasu daga cikin waziran khalifasuka ce "AI yanzu babu Wanda zaka tambaya a sami cikakken labarin wannan gari a wajansa,sai Ka'abul Ahbari,kasa a kirashi ka sa mutumin ya b'uya ta yadda idan shi Ka'abun yana bada labarin ya zama yanajin abinda yake fad'a,domin irin wannan gari a irin wannan kamanni labudda zai kasance yana da wani labari me zaman kansa."
Sai Sayyadina Mu'awiya (Allah ya k'aramasa yards) ya aika aka Kira Ka'abul Ahbari.
Yayin da yazo Khalifa ya tambayeshi yace,"Ya Aba Ishak'a na Kira ka ne akan wani al'amari da nake fatan kana da masaniya akansa,Ka'abu yace, ya Sarkin Muminai,ka dace da Wanda zai baka labari tambayi abinda kaso." Sai yace,"Ka bamu labari akwai wani gari aduniyan man Wanda aka gina shi da Zinari da Azurfa,ginshik'ansa kuma na Zubarjadi da Yak'utu?Sannan ga k'oramu suna gudana k'ark'ashin bishiyoyi?
Sai Ka'abu yace," Na rantse da Wanda raina yake cikin ikonsa,na zaci babu Wanda zai tambayeni wannan gari,amma yanzu Zan baka labari ya Sarkin muminai game da wannan birni da Wanda ya ginashi."
****Amma shi wannan gari kamar yadda labari ya risk I sarkin muminai,Wanda ya ginashi shi ne Shaddadu d'an A'du,shi kuma garin sunansa Irama zatul Imad, Wanda ba'a tab'a gina wani birni a duniya tamkarsa ba,Sai Mu'awiya yace,"To bamu labarinsa ya Aba Ishak'a."
Sai Ka'abi yace,"Sunan Wanda ya Gina garin SHADDADU 'DAN A'DU, 'DAN IWASA , 'DAN IRAMA, 'DAN SAM, 'DAN ANNABI NUHU(AS)
Shi Shaddad ance mutum ne me yawan 'ya'ya,ance 'ya'yansa sunkai dubu hud'u.Ya auri Mata dubu, ya rayu tsawon shekara dubu.
Yayin da A'du ya mutu yabar 'ya'ya guda uku sune Shaddadu da Shadidu,da Irama,amma Shaddad shine babba saboda haka shi ya gaji sarauta,yayin da lamarinsa yai k'arfi yaci Sarakuna da yak'i ya mallake k'asashensu har mulkinsa ya game duniya baki d'aya.Gabas da yamma kudu da Arewa.
Ance, mutane hud'u ne suka mulki duniya gabadayanta,biyu muminai biyu kafirai,muminan su ne Annabi Sulaimanu da Zulk'arnaini (AS)
Kafiran sune,Shaddadu da Namaruzu d'an kan'ana.
An ruwaito cewa,shi shaddadu mutumne me yawan karanta littattafai wad'anda aka saukar ga Annabawan da suka gabata, saboda haka duk lokacin da yaga siffar Aljanna a duniya.
Saboda haka saiya tara waziransa ance yana da wazirai dubu,yace yanaso su Tara masa injiniyoyi da k'wararrun magina,na gabashin k'asa da yammanta.
Yayin da suka tara su,sai ya umarcesu da su yawaita abayan k'asa su gano wurin da ya dace me kyan k'asa da k'oramu da bishiyoyi yanaso zai gina Aljanna awajan.Wad'annan masana suka shigat duniya sukaita yawo harsuka sami wani wuri a k'asar YAMEN Wanda zai dace da wannan buk'ata ta sarki.Saboda haka sai Sarki ya tura jnjiniyoyin man guda dubu a k'ark'ashin kowane d'ayansu akwai guda dubu, sukaje suka Tsara yadda za'agina garin,suka zanata asuffar murabba'a,farsakhi arba'in daga kowanne b'angare.
Yayin da suka gama tsarawa da fidda harsashi, sai suka sanar dashi.Saboda haka sai Sarki Shaddad yace was Waziransa,shin wai baku San cewa ni ne nake mulkar duniya gaba d'ayanta ba? Suka ce k'warai kuwa Kaine,yace to inaso lallai kuje Ku taro gaba d'ayan zinare da azurfa da yak'utu da zubarjadi da almiski da za'afaran,da sauran dukkanin kayan ado na duniya baki d'aya."
Suka ce"An gama" Sukaje suka Tara na k'asashensu sannan suka tura na sauran k'asashe aka tattaro gaba d'aya har Wanda suke hannun mutane,jama'a suka koma suna cikiniki da fatu memakon dirhami.
Bayan da aka gamatara wad'annan a'loli sai maginan suka rik'a yin bulo da zinare da azurfa suka rik'a yin ginin dashi har suka katangance gaba d'aya garin.
Bayan da aka gama sai kuma suka rik'a gina benaye da gidaje da d'akuna shima na zinare da azurfa, suna musu diraku na zubarjadi Kore da yak'utu ja,suka sa wad'annan gidajen da benayen suna fuskantar bishiyoyi wad'anda aka lullub'esu da yak'utu da lu'u-lu'u,sannan ga k'oramu nan suna gudana ak'ark'ashin benayen.
Maginan nan suka k'awata garin nan da kayan ado iri-iri,Wanda duniya bata tab'a ganin irinsu ba.An ce tsawon shekarun da sukai suna gina wannan birni shi ne shekara d'ari uku.
Bayan da suka kammala ginin sai suka sanar da sarki,shi kuma sai ya umarci duk Sarakunansa da waziransa da sukai shinfid'u na alfarma da dukkan kayan alatu na amfanin yau da kullum. An ce sai da suka shekara goma suna safarar kaya zuwa garin. Ka'abu ya ce, yayin da suka gama kai wad'annan kayayyaki suka sanar da Sarki,sai ya zab'i wazirai daga cikin makusantansa ya ce,su shirya tarewa zuwa IRAMA ZATUL IMAD.
An ce sai da suka shekara ishirin suna shirye-shiryen tarewa agarin. Sannan sai Sarki Shaddadu ya tashi da shi da wad'anda ya zab'a da matansa da kuyanginsa,sai da ya rage tsakaninsa da shiga birnin tafiyar yini da kwana sai Allah ya turo masa Mala'ika ya ce da shi.
"Idan ka furta cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah,Zan barka ka shiga garin,in ko baka yarda ba,Zan d'auki ranka yanzunnan."
Da Shaddadu yaji haka,sai yai girman kai ya kafirce.Nan ta ke Mala'ika yai musu tsawa suka mace baki d'aya.
Babu Wanda ya isa garin a cikinsu.
Ka'abu ya ce "Wannan shi ne labarin IRAMA ZATUL IMAD ya sarkin muminai.
Amma akwai wani mutum d'aya da zai shiga garin a wannan zamanin naka,har ma yazo ya ba da labarin abinda ya gani,zai shiga daji yana Neman Rak'uminsa da ya b'ace. Daga nan Allah zai nuna masa garin har ya shiga.Amma kafin shi da bayanshi ba wanda zai sake shiga.
Allah shi ne mafi sani.
MUSLIMAT ta sake rik'e hannun GIMBIYA AMINATU da kyau ta share hawayenta sannan ta ce " Kinji k'arshen K'ISSAR IRAMA ZATUL IMAD! Kinji yadda Ubangiji ya dinga bawa Sarki SHADDADU 'DAN A'DU damammaki yana yadda yaso.Ubangiji bai gajiya ba yasake turowa amasa tayin shiga musulunci amma son zuciya da girman kai suka hanashi.
Tunda kikazo garinmu kika ce kinason masoyina naji na tsaneki na dinga cuzgunamiki abaya da ace nabar miki shi da zai zama ta silata zaki shiga ADDININ MUSULUNCI! Amma dake rashin rabo nima yana bibiyata haka na k'ek'ashe k'asa nak'i amincewa buk'atarki na dinga jifanki da munanan kalamai Kafira 'yar kafirai kaico na...Na manta ba ke kika haifo kanki akafirci ba haifoki akai kuma nima da Ubangiji ya so se ya sakoni acikin kafiran dan shi ne mahaliccin kowa da komai,nayi bak'in ciki da baki shiga addininmu ta silata ba,amma bazan yadda na k'ara kuskuren danai ba wajan rabaki da YARIMA MUSLIM domin ni kaina nayi imanin kinfini son sa.
Na riga da na tabbatar da soyayyar da kikemasa ta gaskiya ce,kafin asamu Wanda ke yiwa wani irinshi za'a kwana a tashi ana dubawa ba'a samu ba,dan ni kaina na sani bazan iya rabuwa da rayuwata ba saboda soyayyar da nake masa,ke kuwa naga iya fiye da haka dan haka nake miki albishir da ki yarda dani ki yarda yanzu da zuciya d'aya nake tare da ke,a yanzu inajinki kamar 'yar uwata ta jini,sannan inamai baki hak'urin abinda na miki a baya,kuma inayi miki albishir da na barmiki YARIMA MUSLIM kuyi aure Ku zauna tare nikuma kuyimin addu'ar samun nagari kamar shi ko Wanda ya fishi...
Koda ta gama maganar tashi tayi daga jikin GIMBIYA AMINATU tare da komawa can gefe ta zauna ta sunkui da kanta tana wasa da zoben azurfar hannunta.Bayan tashinta Gimbiya Aminatu kasa motsawa tayi se baki data bud'e dan wani mad'aukakin mamaki ne ya cikata tun sanda MUSLIMAT ta fara yi mata maganar...
Wani irin farin cikine mara misaltuwa ya shiga ratsa ilahirin magudanar jinin jikinta,ji tayi tazama wata sakayau kamar yau tazo duniya dan murna bata shiryaba kawai taji wasu tagwayen hawaye suna zubowa daga idanunta,zuciyarta ce ta bata kamar bata yiwa Muslimat adalci ba idan tayi Mata haka dan haka itama ta mik'e tsaye tare da cire rigar k'arfen jikinta ta ajjeta gefe dan ta fara damunta tukunna ta fara takawa ahankali domin zuwa inda Muslimat ta zauna ta nutsu kamar me d'aukar darasi...
Idanuwa ne suka tsinci Kansu akanta suna kallonta,dan sanda ta tawo seda ilahirin wad'anda ke wajen suka kalleta tare da jinjinawa sarkin da yayi mata kyakkyawar sura.GIMBIYA AMINATU (ZULMAT) tana da kyawu madararsa domin duk irin yadda ake fad'ar kyawun mahaifiyarta LUSH-SHIFAH ta fita sau uku,tana da kyan d'aukar hankali yanda ko sarki ne ke kan doki yai tozali da ita se yaji inama Fulani ceππ»lol...
Sanda taje ta tsugunna gabanta idonta na zubda hawaye,memakon ta fad'amata batai mata adalci ba idan ta rabata da masoyinta?ai kawai seta rungumeta tana k'ara sakin kuka tare da fad'in...
"Nikam kin gamamin komai nagode miki har bansan me zan ce ba,kema Ubangijin musulunci ya mallaka miki wani kamar shi dannasan ba namijin da ya fishi"
"Allah ya ga zuciyarta ya bata nagartacce kuma adalin namiji mai ji da mulki,ya ajje girma da iko yace shi yanason abashi auren GIMBIYA MUSLIMAT!"
Sarkin zancen SARKI KAMALUD-DEEN ke wannan maganar yayin da idanun kowa ya koma kansa.
Agurguje.....π
Farin ciki ya shiga zukatansu dajin wannan abin arzik'i dan haka suka tafi da shirin nan da lokaci k'alilan za'asha shagalin biki harnasu MUSLIM.
A hanyar komawarsu ne suka had'u da ALJANI ASH! inda ya taresu yana kuka yana basu labarin yadda ubangiji ya halakar da rundunar ALJANI DUUJALA! a k'ok'arinsu na hana su gimbiyar d'aukar TAKOBI,nan yake fad'a musu watay runduna ta MACIZAI sunzo domin suma su halakar da su se Allah y halakar da su da wuta inda duk suka Kama da wuta suka zama toka,shima ya tsirane saboda sanda sukaje basajar musulunci shi da gaske ya karb'a shiyasa baibisu d'aukar TAKOBI n ba.
GIMBIYA AMINATU tayi mamaki tare da jinjinawa UBANGIJIN MUSULUNCI sannan ta rubuta TAKADDAR GAYYATA IZUWA ADDININ MUSULINCI YA KAIWA BABANTA ZALIMUZ-ZAMAN!...
βοΈππππβοΈ
Ko da tagama masa bayani se ya juya ya d'auki hanyar garin SILDAN cikin k'iftawar ido ya isa garin har cikin turakar SARKI ZALIMUZ-ZAMAN...
βοΈππππβοΈ
Su ma basu wani d'auki lokaci ba suka isa garin DEENUL-ISLAM inda farin ciki ya cika zuk'atan mutanensu kowa ka gani fuskarsa shar dashi ya wage baki kamar gonar audugaπ
Bayan shigar kowa b'angarensa ai tuni zancen musuluntar GIMBIYA AMINATU da aurenta da YARIMA MUSLIM da zancen auren MUSLIMAT da SARKI KAMALUD-DEEN ya bi ya karad'e kunnwan jama'ar masarautar sukaita k'ananun maganganu Hardai SARAUNIYA SINIYYA bayan ta huta ta sanar da kanta inda suke murna wasu kuma dai ta ciki na ciki kawai.
...Ko da isarsa garin se ya tarar da mayak'ansu duk a shirye shi kad'ai ake jiran fitowarsa ba abinda kakeji se haniniyar dawakai,ganin haka ya tabbatar masa da ya samu labarin duk abinda ya faru kenan,dan haka kawai ya sake komawa suffarsa ta wani farin tsuntsu mai tsananin kyawu ya rik'e takardar da bakinsa ya k'arasa turakar da ita,bai sake ba seda yaje dai-dai fuskar S.ZLMZ-ZMN sannan ya saketa inda shi kuma tundaga tawowarta ya tsaya cak yasan sak'o ne aka turomasa.Hannunsa ya d'aga ya dakatar da ALJANI ASH! da ke shirin fita tare da sa shi yadawo suffarsa yadda zai iya ganinshi...
"Bud'e miniii"
Ya fad'a da mad'aukakiyar muryarsa mai firgitarwa.Babu musu shikuma ya bud'e tare da karanta masa sannan ya sakamasa ita afuska yaji K'amshin tilon 'yarsa ZULMAT yaga rubutunta,amma ga mamakinsa se yaga