Showing 9001 words to 12000 words out of 33915 words

Chapter 4 - WATA DUNIYA COMPELET HAUSA NOVELZ BY YAR GATAN MAMA.txt

23 Nov 2025

1513

wutar take wajan da take zaune yadare inda ta bayyana gaban SARKI ZALIMUZ-ZAMAN.

Dubanta takai ga sarki ZALIMUZ-ZAMAN tare da sunkuyar da kanta wanda hakan yayi dai-dai da rufe bakin ALJANI DUUJALA!!

"Ina yima barka da wannan lokaci ya sarki mai cikakken iko da jarumta!Sannan inayiwa kafatanin baƙinka barka da zuwa tare da fatan suna lafiya"

GIMBIYA ZULMAT ta faɗa kanta aƙsa yayin da ƙasan zuciyarta fal yacika da tsoron yadda zasu kwashe da mahaifinnata.

Ɗagowa sarkin yayi ya kalleta sannan yamata umarni data dawo kusa dashi ta zauna kana yace.....

"Marhaba nake da zuwanki jarumar ƴata,yanzu nake shaidawa aljanun danake da iko dasu tafiyarku garin DEENUL-ISLAM tare da faɗamusu dalilin tafiyar taki,sai dai sunƙaramin tsoro akan wanda nake dashi game da yuwuwar musuluntarki idan kikaci gaba da zama acikinsu domin kuwa an... "

Katse shi gimbiya zulmat tayi ta hanyar faɗin.....

"Ka gafarceni ya babana! Inamai tabbatar maka babu wani wanda ya isa yasa na karya alƙwarin dake tsakanina dakai,akafirci aka haifeni ashi na girma kuma ashine zancigaba da rayuwa,shin mene ne zaisa tsoro yadinga shiga zuciyarka bayan kana da tabbas akaina ya babana"

DUUJALA Yayi wata girgiza kana yatari numfashinta da faɗin.......

"Ke yarinya ce mai ƙaramin tinani,mutanennan suna da wani shu'umin sihiri wanda idan ka haure kwana bakwai atare dasu seka shiga addininsu koda kwa ba kaso seka shiga ta hanyar sihirinsu,domin kuwa zasu cikama zuciya da sonsu ta hanyar kyautatawa tare dayima zantuka cikin salama yadda zakaji bakason barin cikinsu,inajimiki tsoron cin amanar iyaye da kakanninki ta hanyar fita daga addininsu da zummar shiga addinin MUSULUNCII"

"Inaso kasani yakai DUUJALA! Cewa ni ba matsoraciya bace sannan ba raguwa bace kuma ba mara wayau baceba,na je na raɓesune saboda buƙatar mahaifina kuma ko yanzu mahaifina ya janye ƙudurinsa akan TAKOBIN WATA DUNIYA ni kuma zandawo garin haihuwata nazauna domin ni bazan taɓa yin wani abu bada umarnin mahaifina ba"

"Na yarda na amince dake yake ƴata abar alfaharina,nabaki dama akaro na biyu kikoma cikinsu domin kwanaki suna cigaba da matsowa na buɗewar ƙofar WATA DUNIYA,sedai banji kinyimin magana akan yadda kukayi dasu ba"


"Ka gafarceni yakai babana! Ina mai tabbatar maka cewa su waɗannan mutanen abin duniya da dukiya basa gabansu,sedai naji suna maganar zasuje wani domin wani abu ko JIHADA ko JIHADI nadai manta asalin sunansa,naji suna maganar zasui shiri akwanakinnan domin tafiya yinshi,kuma naji sunce garin yana daf da WATA DUNIYA kaga da yuwuwar su shiga suma domin ɗaukar TAKOBIN,nima zanyi amfani da wannan damar domin nabisu,yayin da muka ɗaukone zansare kan sarauniyar kamar yadda ka umarceni na kawoshi gareka ya babana"

"Meyasa baki tambayesu shin zasu shiga WATA DUNIYA domin ɗaukar takobinba"

ALJANI DUUJALA yatari numfashinta da wannan tambayar......

"Saboda matuƙar na fito da abinda yakaini fili garesu zasu fuskanci makirci ne ya kaini kuma bazasu bari burina yacika ba,hakan danai shiyasa suka saki jiki dani batare dasun kawo komai ba".

ZALIMUZ-ZAMAN ya numfasa tare da cewa....

"Har yanzu inatsoron kyautatawarsu gareki tasa kishiga addininsu"

"Bazan shigaba ya babana! Domin na tambayesu game da addininsu sunce bazasu takuraminba harsai naji inason shiga da kaina,kuma sanin kankune babu ranar dazata fito naji araina inason shiga addininsu".

Hakadai sukaita musayar zance atsakaninsu kafin aƙarshe kaifin harshe irinna zulmat tare da dagewa akan alƙawarinta yasa suka rabu da ita.Su ALJANI DUUJALA suma suka kama gabansu bayan yarjejeniyar zasu dinga zagawa domin ganin abinda zulmat takeyi agarin da kuma bata kariya saboda kar wani abu yasame ta.
Bayan tafiyarsu ne itama takoma garinsu Muslim tare da komawa ɗakinta kamar bataje ko'ina ba.


⚔️🌍⚔️🌍⚔️

Yau saura kwana takwas kenan alissafin NUJBEER ƊAN NAJABURU na sauran kwanakin tafiya WATA DUNIYA,yauma kamar kullum yaje wajan sarki inda ya zauna sukayi hira.Sarki KAMALUD-DEEN ne ya dubi NUJBEER ƊAN NAJABURU fuskarsa ɗauke da murmushi yace.......

"Inamai farin cikin ganinka cikin k'oshin lafiya yakai wannan tsoho mai dogon tarihi,nikam da bazan b'ata maka raiba dana yimaka wata tambaya"

"Tambayeni kanka tsaye,domin babu shamaki tsakaninmu kasancewar ka mutuntani baka nunamin girman kai kamar sauran sarakuna ba"

Sarki ne yayi murmushin jin daɗi kana yace....






MORE COMMENT MORE TYPING.



👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻

DAN ALLAH INA NEMAN WATA ALFARMA AGAREKU,ALFARMAR ITACE"ALLAH KABAWA BAIWARKA KHADEEJAH CIKAKKIYAR LAFIYA MADAWWAMIYA,ALLAH KABATA IKON AMFANI DA LAFIYA DAN SON DA KAKEWA ANNABINKA MUHAMMADU SAW"ABINDA ZAKU CE KENAN DAN GIRMAN ALLAH.NAGODE ALLAH YABADA IKO AMEEN👏🏻.


DOMIN GYARA,SHARHI KO BADA SHAWARA ATUNTUƁENI TA WANNAN LAYIN....👇🏻
07047530638.




ƳAR GATAN MAMA✍🏻.
🌍WATA DUNIYA🌍




LABARI/RUBUTAWA
KHADIJA S.SAMINU
('YAR GATAN MAMA)







MARUBIYAR....👇🏻


RAYUWAR MU!
A WANI GIDA
MAGANIN KAR AYI..!
RANA DUBU


nd now👇🏻

⚔️WATA DUNIYA⚔️


LABARIN DA AKA GINA SHI AKAN SOYAYYAR ADDININ MUSULUNCI DA MUSULMAI DA K'IYAYYAR KAFIRCI DA KAFIRAI.AKWAI CIN AMANA,SOYAYYA,K'IYAYYA,YARDA,SADAUKARWA D SAURANSU.
INA ROK'ON ALLAH YADA'DA MANA KISHIN MUSULUNCI AMIN💞💞







*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*



NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ALLAH YAJA DA RANKI YAK'ARA MIKI LAFIYA🥰🥰.



⚔️🌍⚔️🌍⚔️
SHAFI NA 21&22
⚔️🌍⚔️🌍⚔️



Sarki KAMALUD-DEEN ne yayi murmushin jin daɗi kana yace.......


"Yakai wannan tsoho mai tarin shekaru ma'abocin hikima da basira inason jin wani abu daga rayuwarka idan bazan matsa maka ba"


"Hhhhh! Ai wannan abu ne mai sauƙi,zanbaka tarihina amma ba yauba kasancewar yau inada muhimmin abu agabana,kuma ni awannan lokaci banda muradi sai kwanaki su cika mutafi ɗaukar takobi wanda shi ne cikar buri na,zanbaka amma se munje WATA DUNIYA"


Koda yafita yakoma masaukinsa haka sarki yaita tinani akansa tare da jinjinawa girman taurin kai irinna NUJBEER ƊAN NAJABURU ahaka shima ya shiga turakarsa.


⚔️🌍⚔️🌍⚔️

Koda MUSLIM yashiga turakarsa neman waje yayi ya yada haƙarƙarinsa domin ji yakeyi duk jikinsa babu ƙwari tamkar ankwance wasu notika ajikinsa saboda kalaman MUSLIMAT,tabbas yanason MUSLIMAT kuma ita yake da burin ya aura,amma ya zaiyi da soyayyar da ZULMAT take yi masa? ya tambayi kansa,ya lura da duka zuciyarta take ƙaunarshi tinda harta kasa ɓoyewa agaban kowa,kuma ya daɗe da sanin haka saboda yasha gani a ƙwayar idonta aduk sanda suka haɗu afilin daga,yana kyautata zaton silar sonsa kaɗai zai iya sawa ta rabauta da shiga addinin MUSULUNCI,idan kuwa hakane zai bata dukkan wata kulawa domin ya temaketa tasamu rabo shima yasamu addininsa yasamu ƙaruwa,zai jure kowane ɓacin rai dazai fuskanta awajan MUSLIMAT,zaiyi komai zaiyi amfani da soyayyar da ZULMAT takeyimasa domin ya jata yazuwa addinin MUSULUNCI.Haka yaita wannan tinanin ahaka wani nannauyan bacci ya ɗaukeshi.


Koda ZULMAT ta zauna ita kaɗai tinani ne yacika zuciyarta kan yadda zata cika alƙwarin mahaifinta inda gefe guda kuma take tinanin abinda zai rabata da MUSLIM dan ayanzu ji take soyayyarsa ta mamaye zuciyarta,sonsa yarigada yagama shiga lungu da saƙo na zuciyarta,ko yaya ta rufe ido zanen fuskarsa take gani,idan ta kwanta bacci babu abinda takeyi se mafarkin yana nuna mata wata soyayya tare da kalamai masu wuyar mantawa.

Wani tinani tayi aranta wanda hakan yasa cikin hanzari ta fito daga ɗakin tanufi waje.Fitarta keda wuya ta haɗu da wata kuyanga wadda ta tawo hannunta ɗauke da wani kwando me kyau ancikashi da dangin tufa inibi dabino da sauransu.


"Barkanki dai wannan baiwa"

Abinda tace da baiwar kenan wanda hakan yai sanadiyar tsayawarta ta juyo tana duban zulmat yayinda ta amsa da cewa.......

"Barkanki dai "

"Ina fatan banɓatamiki lokaci ba,sannan ina neman wata alfarma wajanki idan bazaki damu ba"

"Wacce alfarma ce wannan kike nema awajena ya shugaba ta"

"Inaso ki nunamin ɓangaren da zai sadani da ɓangaren MUSLIM"

"Wannan ba abin damuwa bane ya shugabata! Yanzu hakama can zani domin nakaimai wannan kayan marmarin"

Murmushi Zulmat tayi tare da karɓar kwandon tace zata kaimasa inda itakuma baiwa mesuna HUMAIRA'U ta juya ɓangarensu.
Tafiya take da mamakin wannan baƙuwa mai tsabar kyau da kwarjini wadda ta tsaida ita,bata ganin gabanta saboda yadda mamakin yalulata duniyar tinani har tayi wani ɓangaren banasu ba.

"Haba HUMAIRA'U yazaki tawo kanki asama kibigeni haka batare da saninkiba?"

Babu zato Humaira'u taji wannan zancen yadira amasarrafar sarrafa satinta,ɗagowa tayi cikin hanzari ta dubi mai maganar tare dakai dubanta ƙasa inda matar take kallo.

"Ya ra'ufu ya rahimu! Nikam yau naga ta kaina,tayaya naimiki wannan aika-aikar?"

Humaira'u tafaɗa tana duban matar,hannunta aka saboda yadda abin ya kiɗimata,ba wani abu baneba illa ɓarin kayan abinci datayiwa matar.Wani haɗaɗɗen biski ne da miyar taushe wadda taji gyaɗa anshanana mata man shanu ƙamshi ya karaɗe ilahirin wajan,shine sanda ta tawo tana tinani sukayi tawo mugama tazubar mata su ak'asa.Tsinkayar muryar matar tayi tana tambayarta da faɗin....

"Tayaya zansan meya sameki tinda kintawo gaba-kaɗi kina duban wata bakya kallon gabanki? Ke kam ma mekike tinani haka dan Allah awannan lokacin,shin kodai wani abune yafaru awannan masauratar bamu sani ba?"

Ta ida magana tana tsugunnawa domin takwashe burabuskon sama-sama domin dayawa yahaɗu da ƙasa,bata da zaɓin daya wuce itama tasunkuya ta tayata danhaka itama ta tayata suka kwashe danma an auna arziƙi miyar akwai ragowa da yawa domin sanda mazubin miyar yatashi faɗuwa ba kifewa yayiba zama yayi adandanyar ƙasa wanda hakan yai sanadiyar miyar tayi tsalle tafito daga ciki,mazubin biskinne yakife inda gabaɗayanshi yazube awajan,haka suka kwashe wanda zai kwasu tukunna Humaira'u ta dubeta da cewa......

"Hmm! FANTA yau ni naga abinda nagani,wata zankaɗeɗiyar matashiyar budurwa nagani wadda aƙalla shekarunta zasui ashirin da bakwai wato na haihuwa,duk inda ake neman kyau to wannan yarinya tana da madararsa,wato idan kika kalli idanunta zaki gansu dara-dara cikinsu farare karrr! Tana da cikar fuska domin datayimin murmushi bakiga yadda kundu-kukinta suka tashiba kamar fanke inda ƙasansu kuma gefen bakinta suka lotsa(dimples)ke abindai sekin gani,ke nifa bazan iya fasaltamiki kyan wannan halitta ba domin ubangiji yazuba baiwar kyau atare da ita,kuma wani ƙarin abinma a......"

"Kinga Humaira'u kimin yadda zangane wai awane ɓangare kika ganta"

"Ashsha! Ke kinji irinta,bakwa tsayawa kuci ribar zance in anayi,aɓangaren sarauniya na ganta tana neman ɓangaren yarima Muslim nikuma zankai masa kayan marmari ke intak'aicemiki magana karɓar kwandonma tayi ta tafi ɓangaren nasa,ni wallahi hankalina ya gaza kwanciya kar wani mummunan abin yafaru tsakaninsu kinsan kyawawan mata da janye hankalin maza kuma ma......."

"Kedai JAKADIYA da wuya kigama faɗar labari baki sako sharri acikinsaba,inbanda abinki yarima Muslim ɗin dayake da tsoron Allah zaki danganta da haka?To ai wannan da kikegani ba ƙaramar kai bace domin itace GIMBIYA ZULMAT ƴar sarki ZALIMUZ-ZAMAN dake garin SILDAN kuma yau kimanin kwanakinta shida awannan masarauta domin ya riskeni anyi zaman fada anan sarauniya take shedawa jama'arta tayi bak'uwa kuma itace baƙuwar,tazone saboda mahaifinta ZALIMUZ-ZAMAN yayi mata korar kare daga garinsa yac.....

JAKADIYA HUMAIRA'U ta riƙe haɓa tare juyawa ta kalli gabas,yamma kudu da arewa sannan tagyara tsayuwarta tace....

"Allahu akhbar! Allah sarkin buwaya,wato aduniya indai kana neman wani abu seka sameshi matuƙar ka miƙa lamuranka gareshi.Na yadda da haka,kinga yanzu dana tawo hankalina atashe yake, kawai sonake nasamu wanda zanfaɗawa mu shiga bincike muji daga ina tafito? ashe kece zaki buɗamin inda aka rufemini,ni dake kinsan kwana biyu banida lafiya danko tafiyar da sarauniya tayi ba dani akaiba shiyasa bansan meke faruwaba amma yanzu gaki.To metayiwa sarkin ya koreta? Kuma me tazo tayi anan,ita sarauniyar ta yadda da ita,anya ba wani abune ya kawotaba ta laƙe da haka?"

"Ke illarki seki jerawa mutum tambaya kamar akurkuku,yo da ke akasa aɓangaren tuhuma ba'asan me zaki ba yadda kike jeron tambaya sekace nakashe yarima"

JAKADIYA HUMAIRA'U ta karkace baki tare da haɗe rai tace....

"Kinga FANTA sauri nake zanshiga mugana da sarauniya,inbazaki faɗanba nasan nayi".

Kallonta FANTA tayi sheƙek'e tare da gyara tsayuwa tace.....

"Atafiyar dasu sarauniya sukayi domin ɗaukaka kalmar ALLAH shine fa suka haɗu dasu mayaƙan SILDAN suka yaƙesu aka kashemana mutane da dama,ƙarshedai ita ɗiyar tasa ta dakatar da yak'in tare da temakonsu ta tseratar dasu,kuma naji daga majiya mai ƙarfi cewar son yarima takeyi shiyasa ta temakesu,tojin haka da mahaifinta yayi shine fa ya koreta dan taji haushi, ita kuma seta dawo nan domin tarama abinda yayi mata.Kuma kingama idan darabo ta silar haka ta musulunta kinsan ance so yana canza mutum"

Gwalalo ido jakadiya tayi tare da jinjina kai ta dubi Fanta tace....



DAN ALLAH INA NEMAN ALFARMA AWAJANKU MASU KARATU,DAN ALLAH KU ROƘAMIN LAFIYA DA CEWA"ALLAH KA AZURTA BAIWARKA KHADEEJAH DA CIKAKKIYAR LAFIYA SANNAN KABATA IKON AMFANI DA LAFIYAR DAN ARZIƘIN MASOYINKA MUHAMMADU SAW"ABINDA ZAKUCE KENAN DAN ALLAH,ALLAH YABIYAWA KOWA BUƘATUNSHI AMEEN NAGODE🥰🥰💞💞.




MORE COMMENT MORE TYPING.......



DOMIN GYARA,SHARHI KO BADA SHAWARA ATUNTUƁENI TA WANNAN LAYIN....👇🏻
07047530638🌍.







ƳAR GATAN MAMA✍🏻.




🌍WATA DUNIYA🌍




LABARI/RUBUTAWA
KHADIJA S.SAMINU
('YAR GATAN MAMA)







MARUBIYAR....👇🏻


RAYUWAR MU!
A WANI GIDA
MAGANIN KAR AYI..!
RANA DUBU


nd now👇🏻

⚔️WATA DUNIYA⚔️


LABARIN DA AKA GINA SHI AKAN SOYAYYAR ADDININ MUSULUNCI DA MUSULMAI DA K'IYAYYAR KAFIRCI DA KAFIRAI.AKWAI CIN AMANA,SOYAYYA,K'IYAYYA,YARDA,SADAUKARWA D SAURANSU.
INA ROK'ON ALLAH YADA'DA MANA KISHIN MUSULUNCI AMIN💞💞







*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*




NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYANSHI GA MAHAIFIYARA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA,ALLAH YA SAKAMIKI DA ALKAIRINSA AMEEN🥰🥰💞💞.



⚔️🌍⚔️🌍⚔️
SHAFI 23&24
⚔️🌍⚔️🌍⚔️



Gwalalo ido jakadiya tayi tare da jinjina kai tadubi Fanta tace.....

"Lallai wannan ake kira cakwakiya,ashe abinda ke faruwa kenan kum..."

Katseta Fanta tayi ta hanyar cewa.....

"Kingani tafiyata kar abincina yayi sanyi garin samawa gulma wajan zama"

Tafaɗa tare da ɗaukar kayan abincinta tai gaba tabar Jakadiya riƙe dabaki.Itama bata da zaɓin daya wuce tatafi harkar gabanta dan haka ta wuce tai hanyar sashen SARAUNIYA SINIYYA!!....


******
Koda GIMBIYA ZULMAT ta isa ɓangaren YARIMA MUSLIM tsayawa tayi abakin ƙofa tare dayin shiru talula duniyar tinani.......

"Shin koya zai tarbeni idan naƙarasa? Ina sonsa! Ina ƙaunarsa!! Zan iya komai akansa ciki kuwa harda kashe kaina idan ya buƙaci hakan daga gare ni,zan iya kashe duk wani wanda yace zaiyi tarayya dani cikin soyayyarsa,itama MUSLIMAT na barta araye ne saboda tarigani faɗawa cikin soyayyarsa kuma na bata nan da wani lokaci idan abinnata yayi nisa ma'ana taci gaba da nuna ƙaunarsa agabana!Zan aikata inda kakannina da mahaifiyata suka tafi kuma baazata dawo ba, YUSH-SHIBAYIL AMNASH-YUSH-SHIBAYIL AMNASH Katemakeni akan soyayyata kasa yasoni sonda ko mahaifiyarsa bai yiwa irinshi ba,YUSH-SHIBAYIL AMNASH-YUSH-SHIBAYIL AMNASH karka watsamin ƙasa a idona.... "

Shiru tayi kuma na tsayin daƙiƙa saba'in da uku kafin ta buɗe baki ta furta afili tace.......


"Ya abin bautar MUSULMAI kasa bawanka yasoni ka tallafawa soyayyata!!"


Gama faɗin haka keda wuya ta tura ƙofar dazata sadata da inda MUSLIM yake,seda taratsa faluka har uku kowanne ya ƙawatu da kayan ado na alfarma sannan takai jikin wata ƙofa wadda samanta aka rubuta 'TURAKAR YARIMA MUSLIM' ganin haka ya tabbatar mata nan ne inda take nema dan haka ta tura ƙofar tare da tsayawa ta kasa shiga.

MUSLIM daga inda yake zaune akan sallayar daya idar da salatid-dhuha hannunsa ɗauke da alƙur'ani mai girma yaɗago da kansa ya sauke kyawawan idanunsa akanta wanda suke rikitata ta mance komai aduk sanda tayi tozali dasu,kallonta yakeyi batare daya buɗe baki yayi maganaba sai tinanin dayakeyi aransa mene ne ya hanata ƙarasa shigowa? cigaba da kallonta yayi harseda tafara tinanin to kodai baiji daɗin shigowarta babu neman izini ba? Hakan data tina yasa tayi saurin juyawa tare da neman waje afalon dake kusa da ɗakinnasa ta zauna domin ta jirashi koda kwa zaiɗauki lokaci bai fitoba tasa aranta bazata tashiba kuma bazata takuramasa ba tinda taga shima kundinsu ne wanda abin bautarsu ya saukar musu yake karantawa,saboda suma aduk lokacin da suke duba kundin tsaface-tsafacensu basajin daɗi idan wani abu yagifta batare dasun isa inda sukeson kaiwa ba.

Ganin ta juya yasa MUSLIM cikin hanzari ya ajje ƙur'anin hannunsa tare da biyo bayanta.Tana tsaka da tinani ƙamshin tirarensa dake sanyamata kasala ya bayyana mata masoyinta kuma muradinta ya iso inda take dan haka batare da jinkiri ba taɗago kanta ta sauke idanunta afuskarshi........


⚔️🌍⚔️🌍⚔️

Koda MUSLIMAT ta isa ɓangarenta mukulli tasaka ta kulle sashen nata tare da shigewa can ƙuryar ɗakin tahaye ƙarshen gado ta haɗa kai da gwiwa tahau rusa kuka iya ƙarfinta.

Tin tanayi sauti yana fita har seda muryarta ta dishe tadena fidda sauti saboda tsabar kukan datai wanda da hawaye yana ƙarewa tabbas yau se nata ya ƙare.Kamar an tsikareta haka ta tashi daga kan gadon ta isa bakin kwabarta tare da buɗewa tashiga watsi da duk kayan da suke ciki wanda aƙarshe can ƙasan kayanta ta ɗauko wani kundi na tarin hotuna.

Cikin hanzari ta buɗe ta shiga fiddoda hotunan mabanbantan mutane tare da ƙaremusu kallo tana k'ara sautin kukanta,bata tsayaba harseda takawo kan wani hoto dake ɗauke da jabun MUSLIM,SARAUNIYA SINIYYA da wasu mata guda biyu dakuma wasu maza guda biyu da kuma ita kanta MUSLIMAT ɗin.....

Kallon hoton takeyi tana sakin wani kuka mai cin rai tare da toshe bakinta da gefen zanin dake jikinta,ajje hoton tayi ta ɗauki wani daban wanda hotontane itada Muslim suna yiwa juna murmushi,tashi tayi takoma inda tafara zama tare da duƙunk'une jikinta ta takure kanta tana sauke ajiyar zuciya ajejjere tana cigaba da kallon hoton wasu siraran hawaye na zirarowa ta gefen idanunta.Ahaka ta wanzu tsawon awanni kafin batai auneba wani nannauyan bacci yayi awon gaba da ita.


⚔️🌍⚔️🌍⚔️
Koda JAKADIYA HUMAIRA'U ta isa b'angaren sarauniya bata tarar da kowa ba se wata amintacciyar sarauniya mai suna SHATU tana niyyar fitowa ita kuma zata shiga.

"Barka dai Jakadiya,yana ganki haka afirgice incedai ko lafiya?"

"Ahaf! Kaga ƴar halak inakwa nemanki,amma bara nafuto tukunna nadawo gareki"

Jakadiya ta faɗa tare da sa kai turakar sarauniyar,bayan ta nemi izinin shiga anbata ne tazauna ta sunkuyar da kai tare da cewa.

"Amincin Allah ya tabbata agareki ya adalar shugaba mai mulkar mutanen wannan masarauta"

"Tare dake Jakadiya,mungode"

"Allah yaja zamaninki! Daman wata jita-jita naji game da baƙuwarki.Allah ya temake ki kozan iya jin gaskiyar lamari daga bakinki?Allah ya temake ki ko'ina na wannan masarauta zancenta akeyi tare da yaɗa jita-jitar cewa wai son yarima takeyi hakan yasa tazo domin ta kawomasa ziyar...."

Ɗaga mata hannu sarauniya tayi tare da faɗin.......

"Munji zancenki kuma....kamar yadda kika faɗa ba musulma bace ba,sannan akwai wani dalilidai bayan soyayyar yarima amma ki rabu da jita-jita zaifi domin duk waɗanda suka kamata susan dalilin zamana da ita nafaɗamusu sun sani".

"Yanzu ranki ya daɗe kina nufin zaki bata auren yarima kenan?Sannan ita Muslimat ta yadda ta rabu da yariman?

"Duka su biyun inada cikakken iko dasu,dan haka zan iya bawa Muslimat umarni akan ta barwa Zulmat MUSLIM ta aura domin da soyayyar da take masa kaɗai zamu iya janta yazuwa addininmu na musulunci..."

Sarauniya nagama wannan maganar taɗan lumshe idonta tsawon daƙik'a hamsin tukunna ta buɗe.Ganin haka ya tabbatarwa Jakadiya Humaira'u sarauniyar ta ƙosa da maganar dan haka tayi mata sallama ta tafi......

⚔️🌍⚔️🌍⚔️

Koda MUSLIM ya fito ya tarar da ZULMAT zaune tazuba uban tagumi tana........





👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻
DAN ALLAH INA NEMAN ALFARMA AWAJANKU"ALLAH KABAWA BAIWARKA KHADEEJAH CIKAKKIYAR LAFIYA KABATA IKON AMFANI DA LAFAIYAR"ABINDA ZAKUCE KENAN DAN ALLAH ,NAGODE.



MORE COMMENT MORE TYPING.



DOMIN GYARA,SHARHI KO BADA SHAWARA ATUNTUƁENI TA WANNAN LAYIN..

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login