Showing 33001 words to 33915 words out of 33915 words

Chapter 12 - WATA DUNIYA COMPELET HAUSA NOVELZ BY YAR GATAN MAMA.txt

23 Nov 2025

1522

ta saka AMINATOU💞Bawai baisan ta musulunta bane a'a sanin da yayi nema yasa ze fita da kansa domin yak'arta ya rabata da doron duniyar baki d'aya,Ashe shi tunaninsa gajere ne ita tuni ta rik'a har zata iya aikomasa da sak'on banza da wofi?( Allah k rabamu da rashin rabo amin).Ai yana gama tunani ya kalli Aljanin tare da wuramasa iskar bakinsa a ta ke ya sank'ame awajan.



...Ko da GIMBIYA AMINATU taji sak'onta shiru se ta tabbatar da lallai babu sa'a mahaifinta yana nan rashin rabo na d'awainiya da shi,kuma tana da tabbacin yanzu haka idan bata rigashi ba shi zaizo yaga bayanta harma al'ummar da basuji ba basu gani ba,hakan yasa cikin k'ank'anin lokaci tai shirin yak'i tare da fitowa a shiryenta sai kawai ganinta sukayi kana ta fad'amusu shirinta,babu yadda suka iya haka suka shirya amma babu SARAUNIYA SINIYYA dan rabuwa sukayi da ita saboda tana fama da mura.


Shi kuwa ZALIMUZ-ZAMAN tunda ya zauna a inda yake yaketa faman tunanin yadda zaiyi yayiwa 'yarsa Zulmat kisan hulak'ancin da se duniya ta fad'eshi ta kuma danshi baisan wata Aminatu ba Zulmat kad'ai ya sani,tunani yake d'aurawa kafin yakai k'arshe se ya warware ahaka seda ya kwana uku curr ba tare da kuma yace wa mayak'ansa su koma sai ya shirya ba suma haka sukai kwanakin akan dawakai dan duk Wanda ya sauna yasan makomarsa gun shugaban nasu.

A wannan hali Babbar rundunar gwarazan musulman ta iso cikin garin SILDAN yayin da mayak'an cikinta sukayi yunk'urin afka musu amma GIMBIYA AMINATU wadda suka sani da ZULMAT ta ratso ta dawo gaba yayin da sukai tozali da ita se kowa ya yada makaminsa ba tare da ya shiryama hakan ba.



Gaban SARKI ZALIMUZ-ZAMAN ne yayi wata mummunar fad'uwa yayin da kansa ya sara jikinsa ya hau rawa alokaci guda wanda hakan ya matuk'ar bashi mamaki, "To me hakan yake nufi kenan?Tsoron 'yarsa yake ji ko kuma yau tsoron musulunci ne ya shige shi? Kai bazai yuwu ba" Ya fad'a yana gama mik'ewa tsaye tare da fitowa cikin shirin yak'i...


"Wayyo,me yake faruwa dani ne haka yau? Banga haka amadubin tsafi na ba kuma me yasa hakan ke shirin faruwa da ni,tabbas idan dai-dai idanu na nake gani yau k'arshe na ne yazo amma idan sunsan wata basu san wata ba ina k'arasawa zansare kan maciyiyar amana kamar yadda na sare na uwarta itama naje na tsaface ta shikenan su sauran hatsabibancinsu mai sauk'i ne"

Yana zuwa nan a tunaninsa yaja linzamin dokinsa yad'aga ya tunkare su da matsanancin gudu.Ko da ganin haka ta ke GIMBIYA AMINATU itama ta zaburo ta tunkaroshi cikin zafin nama da zafin zuciya tana kabbara da iyakacin muryarta inda suma sauran abinda ke bakunansu kenan ji kake "ALLAHU AKHBAR!" sunan Ubangijin musulunci ya karad'e kunnuwan mak'iya inda cikin nasara kuma sai zubda kafirai akeyi yayinda wasunsuma duk sunfara karaya dan duk alamu sun nuna yau musulman ne ke da nasara basu ba dan haka jikkunansu sunyi sanyi wasuma suka fara b'oyewa saboda tsira da rayuwa dan sunga halin da mai gayya mai aiki yake ciki...

Can kuwa wajan Gimbiya Aminatu da Sarki Zalimuz-zaman yak'i suke gwafzawa kowa yana Neman ran d'an uwansa cikinsu ba Wanda yake saurarawa wani,kana kallon idanuwansu zaka ga zallar wutar k'iyayya na ci kamar ta k'ona gari ba kawunansu ba.



⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️


Sun d'auki tsawon lokaci suna yak'i tsakaninsu yayin da ak'arshe UBANGIJIN MUSULUNCI ya bawa MUSULMAI nasarar k'arar da mafi yawan kafiran inda ak'arshe ragowar rundunar SARKI ZALIMUZ-ZAMAN suka amshi gaskiya lokacin da suka zubda makamansu sanadin ganin GIMBIYA AMINATU ta sare kansa ya fad'i k'asa suka hangi tutarsu ma ak'asa yayin da suka ga tutar musulmai da kuma dandazon musulmai.Kuka Gimbiya Aminatu take rafkawa har numfashinta na sark'ewa sabida azabar da takeji acikin zuciyarta mahaifinta ya komawa mahaliccinsa ame babban laifi ga uwa uba girman kai da tsantsar zalunci,Idan ba Kalmar Allah ba mai zaisa ta kashe mahaifinta?sedai yanzu zatai alfahari da cewar ta kawo k'arshen zaluncinsa kuma tayi sanadiyar musuluntar mutanensu masu azababben yawa.Bayan komai ya lafa ne musulunci ya kafu agarin sannan suka koma garin DEENUL-ISLAM aka ci gaba da shirye-shiryen bikinsu.




⚔️⚔️⚔️⚔️


Rana bata k'arya sedai uwar d'iya taji kunya,anyi shagali iya shagali bikinsu ya k'ayatar ya samu halartar manyan sarakunan duniya dama Wanda ba Sarki ba inda k'arshe aka d'auki GIMBIYA MUSLIMAT akai masarautar SARKI KAMALUD-DEEN da ita yayin da GIMBIYA AMINATU akai garin SILDAN da ita kasancewar YARIMA MUSLIM shi aka nad'a ya zama Sarki yake mulkar mutanen tsohon azzulumin Sarki acikin adalci da gaskiya.


Anyi komai komai ya k'are inda akabar masoya suke shan soyayyarsu Suna zaune cikin soyayya da k'aunar juna uwa uba mutunta juna da Kuma Gaskiya.


Kowa yana alfahari da wannan had'in bama kamar SARAUNIYYA SINIYYA da kullum se ta godema mahaliccinta bisa wannan baiwa da Yayi musu baki d'aya.


⚔️⚔️⚔️⚔️


Bayan shekara biyu GIMBIYA AMINATU ta haifo santalelen d'anta namiji Wanda aka saka masa YARIMA ABDALLAH! yaro yanashan gata iya gata dan mutanen gari ma sunaji da yaron kasancewar yaron shiru-shiru ba shi da wata hayaniya kullum idan mahaifansa SARKI MUSLIM DA GIMBIYA AMINATU suka kalleshi se sunce ALHAMDULILLAHI🥰💞💞








ALHAMDULILLAHI ANAN NA KAWO K'ARSHEN WANNAN LABARIN NAWA MAI TAKEN⚔️WATA DUNIYA ...INA ROK'ON UBANGIJIN ABINDA NAYI DAI-DAI YASA NA 'DORE AKAN HAKA WANDA NAYI BA DAI-DAI BA YASA NA GYARA DAN ALFARMAR SHUGABA SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA.







DAN ALLAH INA ROK'ON ADDU'ARKU GARE NI "ALLAH KA BAWA BAIWARKA KHADIJA LAFIYA MAI 'DOREWA KA BATA IKON BI DA LAFIYAR TA HANYARKA" NIDA DUK MUSULMI,ABINDA ZAKU CE KENAN NAGODE.






DOMIN GYARA SHARHI KO BADA SHAWARA KU TUNTUB'ENI AWANNAN LAYIN...07047530638.










Allahumma salli ala Muhammadur'rasulullahi sallallahualaihhi wasallama.


'YAR GATAN MAMA✍🏻

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login