Showing 3001 words to 6000 words out of 33915 words
Chapter 2 - WATA DUNIYA COMPELET HAUSA NOVELZ BY YAR GATAN MAMA.txt
nasa yakai tsufa daƙyar yake buɗar baki yayi magana,bayan antaimakamasa ya zauna ne yadubi sarki tare da faɗin......
"Allah yaja zamaninka! Inamaka fatan alkairi tare da fatan na same ku lafiya"
Sarki ne ya dubeshi duba na tsanaki sannan yace.....
" Amm! Sannu dai baba,mungode da fatan alkairin dakayi mana,amma zamuso muji daga ina kazo garemu kuma mene kake tafe dashi"?
Dattijon ne ya gyara zama tare da faɗin.....
"Allah yaja zamaninka sarki mai dogon zamani,da farkodai ni sunana NUJBEER ƊAN NAJABURU anhaifeni aƙasar NILDIHAL nataso acikinta,bantaɓa aureba kuma bantaɓa shiga wani gari domin wani daliliba sai wannan garin naka,ni na kasance ina ɗauke da wani babban matsayi acikin manyan bokayen garin NILDIHAL.
Sanin kanku ne a al'adarmu duk farkon shekara da ƙarshen shekara akwai wasu al'amura da suke faruwa damu masu kyau ko marasa kyau,ni NUJBEER ƊAN NAJABURU duk shekara ni ne farkon wanda ke fara ganowa ƙasarmu abinda zaifaru sannan ni ne wanda keyin aiki domin maganin wannan matsalar.
Naƙware nayi shura a aikina,nayi fice na gagara ako'ina nafaɗin wannan duniya tamu,babu wani burin duniya nawa dabai cika ba sai guda ɗaya,wannan burin cikarsa shi ne zaicike dukkan wani matsayi danake nema afaɗin duniya"
Dattijon yaɗago da kansa ya kalli sarki KAMALUD-DEEN ya nisa sannan yacigaba da cewa.....
"Allah yaja zamaninka yakai wannan sarki mai dogon zamani.Wannan buri nawa bawani buri bane se buri guda ɗaya wato burina na ɗaukar TAKOBIN KOGON WATA DUNIYA wanda ake yimai laƙabi da KOGON MAI RABO,wannan kogo yana da mummunan hatsarin gaske wanda musifun dasuke cikinshi sunfi ƙarfin tsaface-tsafacenmu baki ɗaya matsafan wannan duniya.
A'iya binciken dana ɗauki shekaru inayi nagane cewa tsafina da duk wani abu danake tak'ama dashi bazai bari na iya shiga wannan wajeba sedai taimakon abin bautarku,madubin tsafina yanunamin cewa kai kaɗai kaine wanda zanhaɗa kai nashiga wannan KOGO kuma naɗauki wannan TAKOBII"
Koda NUJBEER ƊAN NAJABURU yazo nan azancensa,seyai shiruu! ya ƙurawa SARKI KAMALUD-DEEN idanu yanaso yagane ainihin abinda ke ƙunce afuskarsa.
Sarki yaja dogon numfashi tare da kallon NUJBEER ƊAN NAJABURU yanamai jinjina kansa tare dayin shiru na wasu ƴan dak'iƙu sannan yai gyaran murya yace......
"Umm! Yakai wannan tsoho ma'abocin shekaru da dogon tarihi,munji duka bayananka kuma mungamsu dasu,sedai bamu yanke musu hukunciba ahalin yanzu munason ka koma masaukinka zamu nemaka"
Cike da k'warin gwiwa NUJBEER ƊAN NAJABURU ya amsa tare da bin wani bafade sukanufi inda akabashi amatsayin masaukinsa....
⚔️🌍⚔️🌍⚔
Domin gyara sharhi ko bada shawara atuntuɓeni ta wannan layin👇🏻
07047530638.
MORE COMMENT MORE TYPING⚔️⚔️
ƳAR GATAN MAMA✍🏻.
⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️
⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️
LABARI/RUBUTAWA
KHADIJA S.SAMINU
(ƳAR GATAN MAMA)
Marubuciyar......
A WANI GIDA
RAYUWAR MU!
MAGANIN KAR AYI!
nd now......
⚔️WATA DUNIYA⚔️
⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
NA SADAUKAR DA WANNAN LABARIN GABA ƊAYANSHI GAREKI MAHAIFIYATA ABAR ALFAHARINA HJY.ƘURAINABU IDRIS YARO YAHYA,ALLAH YAJA DA RAI AMEEN😍😘💞💞
⚔️🌍⚔️🌍⚔️
SHAFI NA 9&10
⚔️🌍⚔️🌍⚔️
Haka kuwa akayi sukaɗauki hanyar DEENUL-ISLAM wanda shine ainihin garinsu.
Koda suka isa masaurauta yamma takawo jiki sosai domin daf ake da sallar magriba.Mutanen garin kowa sai barka da zuwa yake musu tare da miƙo gaisuwa ga SARAUNIYA SINIYYA da MUSLIM dakuma baƙuwar dasuka gansu tare wato GIMBIYA ZULMAT duk da awajan wasu daga mutanen garin ba baƙuwar fuska bace awajansu kasancewar ba inda ZULMAT bata shiga yaƙi domin kare addininsu na iyaye da kakanni.
Mayaƙan garin kallonsu kawai sukeyi cike da mamakin meyakawo ZULMAT masarautar su.
Basu tsinke da lamarinba saida sukaga sun sakko daga dawakansu sunnufi cikin masarauta.
Nan Sarauniya tayi umarni da akawowa GIMBIYA ZULMAT kayan ƙwalam da maƙulashe,haka kuwa akayi cikin ƙanƙanin lokaci aka cika gaban GIMBIYA ZULMAT da kayanci da sha iri-iri,batare da ɓata lokaci ba tahaucin wanda zata iya sannan tabar wanda zata bari.
Jim kaɗan aka kirayi sallar magriba inda kowa yatafi domin ya gabatar da ita banda GIMBIYA ZULMAT.Bayan SARAUNIYA SINIYYA ta gabatar da sallah ne tasa ashigo mata da GIMBIYA ZULMAT domin tanason suyi magana ta fahimta da ita.
"Ina maiyiki sannu tare da fatan kinji daɗin kalar tarbar da mutane na sukayi miki"
Sarauniya ke faɗin wannan magana sanda Zulmat tazauna agefenta bayan isowarta.
"Yake wannan Sarauniya mai ɗumbin tarihi,haƙik'a nayi farin ciki mara misaltuwa da kalar tarbar dana samu awannan masarauta,kuma najinjina karramawa irintaki da mutanen da suke tare dake yake.
Yake wannan sarauniya! Inamai sanar dake cewa naga alamun mamaki sun bayyana ƙarara afuskar mutanenki sanda idanuwansu sukayi tozali dani,ina tsoron kada su sakaki kikoreni daga wannan gari,domin nasan keɗin kinabin maganar mabiyanki aduk sanda suka kawo miki shawara kinabinta.....ina tsoron kada subaki shawarar dazata saka kice bazaku zauna tare danib......."
Katseta Sarauniya tayi ta hanyar faɗin....
"Ki kwantar da hankalinki yake baƙuwata,inamai tabbatar miki babu wani wanda ya isa ya umarceni da korarki awannan garin gaba ɗaya,namiki alƙawarin zama tare damu duk rintsi duk wuya matuƙar zakibi dokokin da zamu gindaya miki kuma zaki rayu kamar yadda muke rayuwa,sannan kuma zakiyi abu guda ɗaya,inamai tabbatarmiki da zarar kinbi dokokinmu bamai rabamu harsai idan kece kika buƙaci hakan"
"Waɗanne sharaɗai ne yake shugabata"?
"Bawasu sharuɗai bane masu yawa,abu nafarko dai inamai farin cikin sanardake cewa....ALLAH shine mahaliccin dukkan komai kuma shikaɗai akeyiwa bauta,gareshi mukazo gareshi zamu koma,shikaɗai ne mahalicci shiya halicci mutum da aljan sama da ƙasa dama komai da komai.
Sharaɗi na biyu kuma kiyimin alƙawarin zaki zauna damu da zuciya ɗaya,sannan bazaki haɗa kai da wasu afarmakemuba,idan kika saɓa alƙawari zamu yaƙeki"
Nisawa ZULMAT tayi sannan ta jefi Sarauniya da tambaya kamar haka....
"Shin wane abune guda ɗaya da kikafaɗa acikin sharuɗanki wanda ayanzu banji kin maimaita dashi ba"?
"Yake baƙuwata! Ba wani abu bane guda ɗayan dana manta banfaɗa ba sai.....Inamai umartarki daki zauna damu bisa gaskiya da amana,kada kicutar dako sauro dake rayuwa awannan gari balle wani bawa dayake cikinsa"
"Na yadda da duka sharaɗanki yake shugabata,sai dai guda ɗaya wanda sainayi tinani akansa.Sannan inamai neman alfarma guda ɗaya awajanki"
Sarauniya SINIYYA ta kalli Gimbiya ZULMAT duba na tsanaki sannan ta kada baki tace.....
"Shin wane sharaɗi ne baki yarda dashiba acikin sharaɗaina?
Wace alfarma kike nema awajena"?
ZULMAT ta gyara zamanta sannan tadubi SARAUNIYA SINIYYA tace.......
"Sharaɗi ɗaya da banyarda dashi ba shi ne:Bazan musulunta ba kuma bazanyi rayuwa kamar yadda kuke yiba.Alfarmar danake nema kuma itace:Inason acanzamin masauki amaidani cikin mutane yanda kaɗaici bazai dame niba"
Nisawa Sarauniya tayi tare da tsayawa takalli Zulmat tsayin wasu daƙiƙu sannan tace......
"Hmm! Yake jarumar baƙuwata,inamai farin cikin sanar dake abinda baki sani ba,inason kisa aranki shi ADDININ MUSULUNCI ba addini ne na takurawaba ba'ayiwa mutum tilas akansa harsai yaji aransa yanason shigarsa,dan haka ni bazan tilastamiki kishiga addininmu ba harsai idan ke dakanki kikai ra'ayi zanfi kowa jindaɗin hakan.
Alfarmar da kika nema awajena kuma zanyimiki ita,zansa ashiga dake ɓangare-ɓangare dake kizaɓi inda kikeson zama da kanki,inafatan hakan yayi miki?"
"Godiya nake yake wannan sarauniya mai tarin alkairai,bisa ga kyautatawar dakikamin naji inason zama tare dake har ƙarshen rayuwata sai dai inatsoron abu guda ɗaya wato babana,nasan idan SARKI ZALIMUZ-ZAMAN hankalinsa yakoma jikinsa zaibuƙaci dana koma mahaifata domin ayanzuma nasan bak'in ciki da ɓacin raine yasa ya koreni,ni kuma naɗaukarwa kaina alƙawarin yadda yatozartani sena tozartashi bazan sake masa biyayya ba kuma sena......"
"Bana sanar dake abinda Allah maɗaukakin sarki yace ba yake wannan jarumar baƙuwa tamu?"
MUSLIM ne yafaɗa yana riƙe da hannunshi inda yajingina jikin ƙofar dayake yana kallon SARAUNIYA SINIYYA da ZULMAT.
Juyowa sukayi atare suna kallonsa sanda yake ƙarasa shigowa cikin turakar Sarauniya,bayansa MUSLIMAT ce hannunta ɗauke da kayan marmari.
Murmushine ya bayyana kan fuskar ZULMAT sanda taga MUSLIM,sake dubansa tayi tare dacewa......
Bayan sunyiwa kansu mazauni ne MUSLIM ya fuskanci ZULMAT tare da cewa....
"Bismillahir'rahmanir'rahim! Allah maɗaukakin sarki yace:
"Yanzu bakwa ganin idan kuka juya baya dagabin Allah zakuyi ɓarna abayan ƙasa ku yanke zumuncinku? waɗannan sune waɗanda Allah ya la'ancesu ya mayar dasu kurame ya makantar da idanunsu" (surat Muhammad:22,23),
Waɗannan da suke warware alƙawarin Allah bayan anƙullashi,suke yanke abinda Allah yayi umarni da a sadar dashi kuma suke yin ɓarna abayan ƙasa,waɗannan la'ana ta tabbata garesu kuma mummunar makoma tasu ce" (Al'ra'ad :25)
Ubangijinka ya hukunta cewa kada kubautawa kowa sai shi,kuma yayi umarni da a kyautatawa iyaye,idan ya kasance ɗaya daga cikinsu ko su duka biyun suntsufa alhali kana (raye)to kada ka gwalesu,kada ka kyare su,ka faɗamusu magana mai taushi,ka ƙasƙantar dakai garesu kariƴayin addu'a da cewa Allah kajiƙan su kamar yadda suka reneni ina ƙarami"
Shiru yayi yatsaya yana kallon ZULMAT ganin yadda ta tsareshi da ido ko ƙiftawa batayi yace da ita....
"Kallon fa?"
Wani ƙayataccen murmushi ta sakarmai tare da gyara zama sannan tace.....
"Natsaya kallonka ne saboda yadda nake ganin wani kyawu yana sake fitowa daga cikin fuskarka lokacin da kakeyimin bayani,inajin wani farin ciki yana lulluɓeni sanda zazzaƙar muryarka take bayanin,sedai har yanzu ban fahimci inda ka dosa ba,dan haka cigaba"
GIMBIYA ZULMAT tagama maganar tana kashewa MUSLIM idanu.
SARAUNIYA SINIYYA ce takai dubanta inda MUSLIMAT ke zaune tahaɗe rai tayi kicin-kicin alamun kishin Muslim sun bayyana ƙarara akan fuskarta.
Murmushi MUSLIM yayi jin abinda ZULMAT tace dukda cikin ransa kalamanta basu wani yimai daɗiba kasancewar bashi kaɗaine wajanba amma yayi murmushi sannan yace.....
"Daga Abu Musa Mugira ɗan Shu'ubatu Allah ya yarda dashi daga Annabi (S.A.W)yace:"Lallai Allah ta'ala ya haramta muku saɓawa iyaye,da rowa da neman karɓar dukiyar mutane ta hanyar gadar zare,da binne ƴaƴa mata,kuma ya haramta muku yaɗa jita-jita da yawan roƙon mutane da ɓarnatar da dukiya", (bukhari da muslim ne suka ruwaito) Sannan......."
"Wai kai bazaka faɗi komai ba se kada asaɓawa iyaye ne? suma fa iyayen suna abinda baidaceba kasani,inba hakaba yaza'ai babana ya kore ni daga mahaifata?bayan banyimai wani laifi ba? sannan kace bazan ɗauki fansa akansa ba"
ZULMAT takatse shi da faɗin hakan.
Gaba ɗayansu suka juyo suka kalleta jin tambayar da tayi.MUSLIMAT ce tai karaf tace..........
⚔️🌍⚔️🌍⚔️
Domin gyara sharhi ko bada shawara atuntuɓeni ta wannan layin......🙌🏻🙌🏻
07047530638
MORE COMMENT MORE TYPING.
ƳAR GATAN MAMA✍🏻.
⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️
⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️
LABARI/RUBUTAWA
KHADIJA S.SAMINU
(ƳAR GATAN MAMA)
Marubuciyar......
A WANI GIDA
RAYUWAR MU!
MAGANIN KAR AYI!
nd now......
⚔️WATA DUNIYA⚔️
⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
NA SADAUKAR DA WANNAN LABARIN GABA ƊAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ALLAH YAJA DA RAI YAƘARA LAFIYA AMEEN.
⚔️🌍⚔️🌍⚔️
SHAFI NA 11&12
⚔️🌍⚔️🌍⚔️
Na sadaukar da wannan shafin baki ɗayanshi gareki AUNTY SAILUBA Allah yabar ƙauna😘😘Son So fisabilillahi😍😍.
Comment ɗinki nasani nishaɗi😘😘⚔️⚔️⚔️.
⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️
Gaba ɗayansu suka juyo atare suna kallonta jin tambayar da tayi.MUSLIMAT ce tai karaf ta kalleta tare cemata......
"Shin bakiji bayanin da akayimiki game da girman iyaye bane kike wannan kalami akan mahaifinki?ko kuma har yanzu baki gane bane ba"
Murmushi GIMBIYA ZULMAT tayi mai sauti wanda saida fararen hak'oranta suka bayyana kana ta kauda kai daga kallon MUSLIMAT tamaida kallonta ga SARAUNIYA SINIYYA tace .....
"Yake shugabata! Alfarmar canzamin masauki da kikace zakiyi ɗazu inamai tabbatar miki dana samu masaukin da nakeson zama"
Kallonta SARAUNIYA SINIYYA tayi tare da maidata mata murmushi mai sauti sannan tace.....
"Ina ne masaukin naki ya baƙuwata?"
"Inda JARUMI MUSLIM yake da zama nan ne masaukin naw....."
"A'uzu billahi minash'shaiɗanir'rajeem! Kin saɓa lamba,domin baki faɗi abinda zai yuwuba sam! Inaso tun wuri kijanye ƙudurinki akan MUSLIM domin zuciyarsa bashi da gurbin da zai ajjeki acikinta,zuciyarsa tawa ce ni ɗaya babu wajan ajjek....... "
MUSLIMAT ce tsaye kan ZULMAT tariƙe ƙugu tana haki kamar wadda tai tseren doki.
Wata sassanyar ajiyar zuciya ZULMAT ta sauke yayinda ƙasan zuciyarta ke ayyana mata wasu abubuwa game da MUSLIM dama ita kanta MUSLIMAT ɗin,ƙasa ta sake yi da kanta tare dasa hannunta tana jujjuya zoben azurfar dake maƙale aɗan yatsanta.
SARAUNIYA SINIYYA kam cike da ɓacin rai takalli MUSLIMAT tare da faɗin.......
"Ashe daman baki da hankali? Meyasa bazaki magana cikin tausasawa ba? Kifita daga nan kibamu guri bamason mukuma jin wata magana daga bakinki.......
⚔️🌍⚔️🌍⚔️
Cike da ƙwarin gwiwa NUJBEER ƊAN NAJABURU ya amsa tare da bin wani bafade suka nufi inda aka bashi amatsayin masaukinsa.
Bayan tafiyarsa SARKI KAMALUD-DEEN yai shiru inda ƙwak'walwarsa tashiga kaikawo game da lamarin wannan tsoho,a haka dai zaman fada nayau yatashi jiki asanyaye domin shi lamarin tsohon yafirgita shi,kallon waziri sarki yayi tare da faɗin.....
"Umm! Shikuwa wannan bawan Allah awaɗannan shekarun nasa mai yake jira inba mutuwarsa ba?"
Waziri ne yayi gyaran murya tare da gyara zamansa tukunna yasadda kansa ƙasa yace....
"Allah yaja zamaninka! Duba da cewa wannan bawan Allah kafiri ne,kuma yatafi da rayuwarsa gaba ɗaya wajan neman duniya,kaga kuwa dan yanzu yace yanason zuwa ɗaukar wannan TAKOBI ba abin mamaki bane ba Allah ya temake ka"
Koda sarki yaji haka sai yayi shiru sannan yace..."Allah yasa mu dace" da "Ameen" Waziri ya amsa tukunna yayiwa sarki sallama shima.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya awannan gari na SARKI KAMALUD-DEEN suna tare da tsoho NUJBEER ƊAN NAJABURU suna jiran sabon wata yakama inda awannan lokacinne zasu tafi WATA DUNIYA domin su jarraba sa'arsu ta ɗaukar TAKOBIN KOGON WATA DUNIYA wato TAKOBIN ƊAUKAKA.
Wannan kenan......
⚔️🌍⚔️🌍⚔️
Koda MUSLIMAT tafito ɓangarensu tawuce zuciyarta na tafasa kamar ta tsaga ƙirjinta tafito dan baƙin cikin abinda akai mata,yauce rana ta farko da Sarauniya ta taɓa haɗe mata fuska tare da korarta daga turakarta,yauce rana tafarko dataji tanajin haushin MUSLIM har cikin zuciyarta,yauce rana ta farko dataji baƙin cikin dabata taɓajin irinshiba domin kuwa yaune ta tabbatar da tana da kishi kamar sauran mata,'yama za'ai sarauniya takawo wata ƙasurgumar kafira sannan ta kusantata da Muslim?'tambayar da tayiwa kanta kenan batare da tanasa ran akwai mai bata amsaba.Haka daren yau ya ƙare mata cike da saƙe-saƙe akan lamarin ZULMAT domin gani takeyi soyayyace tsakanin MUSLIM da kuma ZULMAT ɗin.
Bayan fitarta kuwa aɓangaren su sarauniya,sarauniya lallaɓa gimbiya zulmat tayi akan tayi haƙuri tazauna aɓangarenta zataimata duk abinda take buk'ata.
Ankai ruwa rana kafin ta yarda,domin tirjewa tayi ita lallai da Muslim takeson rayuwa awannan garin domin ta fuskanci shi kaɗaine yake iya tausasa harshensa idan zaiyi magana,saɓanin yadda kowa yake yi agadare.Saida Muslim yasa baki tukunna tayadda ta zauna anan.
Wannan kenan.....
⚔️🌍⚔️🌍⚔️
Sarki ZALIMUZ-ZAMAN ya haɗa gumi sosai kamar wanda aka tsamoshi daga cikin ruwa saboda ruɗanin daya shiga sanda yadda ƴarsa ZULMAT na yaƙi tana kare maƙiyansa.
Cikin ɓacin rai da ƙunar zuci yai fatali da kayan tsafinnasa yafito domin ganawa da mutanen dake son ganinsa.....
Bai sake tsinkewa da lamarin ZULMAT ba saida yazauna yana dube-dubensa,nan ya hangi yadda ZULMAT tasaki jiki tazauna cikin maƙiyansa suna yimata wasu zantuka(magana akan musulunci) daban wanda seda yaji kamar yakashe kansa dan bak'in ciki.Baiyi wata -wata ba yajuya madubin tsafinsa tare da rufe idonsa yana karanto wasu ɗalatsiman tsafi masu wahalar rik'ewa.
Gimbiya ZULMAT tana tsaye gefen tagar ɗakin da akabata amatsayin masaukinta wanda shike kusa da turakar Sarauniya SINIYYA taji masarrafar sarrafa sautinta wato kunnenta na amsa amon kiran da mahaifinta SARKI ZALIMUZ-ZAMAN yake mata,sake gyara tsayuwarta tayi sosai nan ta tabbatar da gaske nemanta yake yi,ko ba'a faɗamata ba tasan hankalinsa atashe yake domin tana da tabbacin yaga duk abinda yake faruwa da ita.Rufe idonta tayi tare da ɗaga ƙafarta tagama shigowa cikin ɗakin,gadan -gadan tanufi bangon ɗakin kafin ƙiftawar ido segata agaban sarki ZALIMUZ-ZAMAN......
"Cikin girmamawa da neman afuwa gareka babana mai mulkin kafiran wannan nahiya tamu"
Gimbiya ZULMAT ta faɗa tanamai sadda kanta ƙasa lokacin data buɗi ido taganta agaban sarki zalimuz-zam.Cikin matsananciyar damuwa da ɓacin rai sarki zalimuz-zaman yaɗago yadubeta da rinannun idanunsa wanda launukansu yakoma zuwa jajaye kana yace......
"Inamai tinatar dake da kakkausar murya cewa....Bana amince da komawarki cikinsu domin idan kinga abu zai cutar dasu ki temake suba,a'ah! Na yadda da zuwanki ne saboda inason kisamu sauk'i wajan ɗaukomin TAKOBIn nan,domin allon tsafina ya tabbatarmin da MUSULMAI ne kaɗai zasu iya ɗaukar wannan TAKOBI,ke kuma zaki shiga cikinsu ne domin idan sunɗauka ki yak'esu da k'arfin tsafina da naki ki karɓota ki kawomin ita,ta hakanne zaki samu damar mallakar wannan masarauta kamar yadda nai miki alk'awari amma kinje kintsaya kina sakarci da rashin...."
"Cikin neman afuwa da tausasawa nake son nayima bayani yakai babana! Shin wane sarki ne ko sarauniya dake faɗin wannan duniya zaibaka tsoro? Kaine fa kake da mugayen matsafa da hatsabiban Aljannu wanda idan kayi niyya zaka iya sakawa suk'arar maka da kowa dake wannan duniya,shin mene kuma zaisa kadinga kokwanto? Kai ne ka mallaki tsofaffin gumaku wanda idan kaso atsafinka saika dawo dasu sababbi yanzu,shin wane mai mulkine zaija dakai? Ya babana! Inamai farin cikin sanar dakai cewa....Lallai burinka zai cika matuk'ar ina numfashi adoron ƙasa bazaka faɗi ba,koda kuwa kafaɗi bazakasha ƙasaba yakai babana! Abu guda ne nakeson sani,shin yaushene za'afita domin zuwa WATA DUNIYA 🌍domin inason nasani kar lokacin yayi asamu wata matsala"
Nisawa sarki ZALIMUZ-ZAMAN yayi tare da samun waje ya zauna dan se yanzu ne yasamu nutsuwa jin yadda ƴartasa take kambama girmanshi tanasashi nishaɗi sannan yace......
"Hhhhh! Ina alfahari dake ZULMAT,domin kin ɗakko wayo da dabarata dakuma mugunta irin tawa,ke inama tinanin ke kinfini iya tsara komai dan haka nabar komai ahannunki.
Batun ɗaukar TAKOBI kuma sabon wata mai kamawa ne,yau muna ashirin ga wata aƙa'idar tafiya WATA DUNIYA🌍zaku shigeta ne ɗaya ga watan dazai kam .........
⚔️🌍⚔️🌍⚔️🌍⚔️🌍
Inajin comment ɗinku masu comment na ⚔️WATA DUNIYA⚔️marasa comment kuma ina sane daku wallahi zanyi abinda yadace🥺.
Allah yasa mugama da duniya lafiya😘💃🏻💞💞
Domin yabo sharhi ko bada shawara atuntuɓeni ta wannan layin.....👇🏻
07047530638💞💞.
ƳAR GATAN MAMA✍🏻.
⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️
⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️
LABARI/RUBUTAWA
KHADIJA S.SAMINU
(ƳAR GATAN MAMA)
Marubuciyar......
A WANI GIDA
RAYUWAR MU!
MAGANIN KAR AYI!
nd now......
⚔️WATA DUNIYA⚔️
⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
⚔️🌍⚔️🌍⚔️
SHAFI NA 13&14
⚔️🌍⚔️🌍⚔️
🔥WANNAN LABARI ƘIRƘIRARREN LABARI NE,MALLAKINA NE,BAN YARDA WANI KO WATA YAJUYAMIN LABARI BA TAKOWACE SIGA.🔥
🔥🔥ALLAH YASAKAMA IYAYENMU DA MAFIFICIN ALKAIRI YASADASU DA RAHAMA DUNIYA DA LAHIRA YA HAƊASU DA ANNABIN RAHAMA AMAFARKINSU KO AFARKE,WANDA IYAYENSU SUKA RIGAMU GIDAN GASKIYA ALLAH YAJIƘANSU YASA CAN TAFIMUSU NAN YA KYAUTATA NAMU ZUWAN🔥🔥
🔥🔥🔥YAU MUNWAYI GARI MUNTSINCEMU ASABUWAR SHEKARA😭😭ALLAH MUNROK'EKA DAN ISARKA DAN KAƊAITAKAR SARAUTARKA ALLAH KA YAFEMANA KURA-KURAN DA MUKA AIKATA WANDA MUKA SANI DA WANDA BAMU SANIBA NA SHEKARAR DATA GABATA KASA MUYI AIKI NA GARI ASABUWAR DATA FARA DAGA YAU,ALLAH KASA MUCIKA DA KALMAR LA'ILAHA ILLALLAHU MUHAMMADUR'RASULILLAHI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA😭🔥🔥🔥
🔥🔥🔥ALLAH YADDA NAFARA RUBUTA WANNAN LABARI LAFIYA ALLAH KASA NAGAMASHI LAFIYA,ALLAH KASA NA RUBUTA ABINDA ZAI AMFANENI YA AMFANI AL'UMMATA,ALLAH IDAN HAR ARUBUTUNA ZAN RUBUTA ABINDA ZAI ƁATAR DA AL'UMMAR ANNABINKA ALLAH KA KARYA BAKIN ALƘALAMINA NA KASA,ALLAH KARKA BANI DAMA KO IKON RUBUTA ABINDA BA DAI-DAI BA NIDA DUKKAN WANI MARUBUCI DAKE FAƊIN WANNAN DUNIYA,ALHAMDULILLAHI 🔥🔥🔥
ZALIMUZ-ZAMAN ya kece da wata mahaukaciyar dariya wadda seda ɗakin ya girgiza sannan yace da ita........
"Hhhh! Ina alfahari dake ZULMAT,domin kin ɗakko wayo da dabarata da kuma mugunta irin tawa,ke inama tinanin ke kinfini iya tsara komai dan haka nabar komai ahannunki.
Batun ɗaukar TAKOBI kuma sabon wata mai kamawa ne,yau muna ashirin ga wata,aƙa'idar tafiya 🌍WATA DUNIYA🌍zaku shigeta ne