Showing 27001 words to 30000 words out of 33915 words
Chapter 10 - WATA DUNIYA COMPELET HAUSA NOVELZ BY YAR GATAN MAMA.txt
SARAUNIYA SINIYYA akan abata Kalmar shahada tanason shiga addininsu kafin su shiga,lokacin da su ALJANI DUUJALA suka ji haka daga inda rundunarsu take sun so zuwa su hanata amma sai sukai tunanin kodai itama irin tasu zatayi suka hanata,batare da b'ata lokaci ba aka lak'anawa GIMBIYA ZULMAT Kalmar shahada tazama cikakkiyar musulma kamar kowa ta dawo sabuwa dal babu wani datti atare da ita,yayin da aka fad'amata sunaye se tace babu sunan da take so se sunan da aka fad'amata GIMBIYA AMINATU..!
Farin cikin mutanen wajen baya fad'uwa domin kowa jinsa yake cikin farin ciki saboda ZULMAT tana da shiga rai ga kuma uwa kyanta da idan kana tareda Ita bakason rabuwa jizakai ta mugun shiga ranka (Kamar yadda nima k'aunarta ta mamaye niπ€ͺ) sai bayan komai ya kammala ne suka rankaya suka takewa mazan baya.
Koda su YARIMA MUSLIM suka shiga tunkafin suje ko'ina suka ga gwarazany mayak'a ajeren ajikint wani dog on bango Wanda kowannensu hannunsa d'auke da Takobi ya zareta yana tsaye kamar sassak'ashi akai agun ba tsayuwa yayi ba.Ko da suka gama shigewa tas se k'ofar ta maida kanta ta rufe yayinda rufewarta keda wuya wad'annan mayak'an da yawansu zaikai kimanin dubu uku da d'ari biyar sukayo kansu bakunansu d'auke da mad'aukakin ihu mai razanarwa kowanne yanason d'aukar ran Wanda ya riska...
Suma cike da jarumta da yak'ini suka d'aga takubbansu tare da d'aga murya kowa yana "ALLAHU AKHBAR! ALLAHU AKHBAR!!" Cikin k'ananun dak'ik'u suka cure waje guda suka fara rafka yak'i naban mamaki...
Sun d'auki wajan awanni bakwai sunayi kafin su sami nasarar gamawa da wad'annan mayak'an sukayi gaba.
Basu yi wani mad'aukakin nisa ba suka Fara jiyo wani irin gurnani Wanda kafin suyi wani tunani suka ga wasu manyan halittu agabansu masu matuk'ar muni da ban tsoro ta ke...
'YAR GATAN MAMAβπ»
NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA MAHAIFIYAYA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ARZAI ALLAH YA K'ARA LAFIYA DA RABO MAI AMFANI AMIN.
βοΈππππβοΈ
SHAFI NA 71&72
βοΈππππβοΈ
Ta ke suka rankayo baki d'ayansu Wanda yawansu zaikai kimanin dubu biyar da d'oriya,wasu irin manyan halittu ne bak'ak'e masu matuk'ar muni Wanda daga kallo d'aya bazakai muradin sake wani ba,suna da tsayi da k'iba dan k'irar samudawa garesu,hak'waransu zak'o-zak'o masu mugun tsini,idanunsu d'ai-d'ai atsakar goshi masu girma jajaye gwanin ban tsoro,k'afafun kofato garesu idan ka kallesu dai duka babu kyan gani sedai kawai nace'astagfirullah' saboda yadda na fad'esuma abin babu dad'i ko kad'an,tsalle suke yi suna wani irin gurnani mai rikitarwa da tsoratarwa don har barazanar toshe dodon kunnuwansu yake yi.
Babu abinda kake iya ji se ihun wad'annan halittu da kuma mazaje da Jaruman mataye wad'anda ashirye suke su bada rayukansu ga ADDININ MUSULUNCI..!
Sara suka had'e da yanke-yanke shi kad'ai sukeyiwa junansu inda wad'annan halittun suke had'awa da wani siddabaru domin b'acewa suke yayinda d'aya cikin jaruman suka kawo musu Sara da suka sedai su nemesu su rasa.Cikin ikon Ubangiji haka suke wannan artabu tare da rud'ewa jikake suna "ALLAHU AKHBAR! ALLAHU AKHBAR!!" Fad'uwar kafirai kawai kakeji k'asa babu k'ak'k'autawa.
Sun d'auki tsawon lokaci kafin su gama da wad'annan mugayen halittun,da yawa cikinsu sun sami raunuka amma ahaka suka dage domin cigaba da tafiya.
Tsawon dak'ik'a d'ari Tara da sittin da uku suna tafiya batare da wata Matsala ba kawai suka Fara hango wata mulmulalliyar guguwa tana yowa sama tana k'asa tare da tawowa inda suke da gudun gaske....
Cike da k'arfin zuciya da jarumta suka had'a baki suka cigaba da kabbara cikin d'aga murya tare da d'iba da azababben gudu suka tunkari guguwar...
Isarsu gareta ke da wuya suka nemeta suka rasa.Inda sunayin gaba kad'an wucin wuta ya addabesu domin ji sukeyi kamar zasu k'one saboda azababben wucin wutar,koda suka isa inda wutar keci wuta ce bata wasa ba Dan se ahad'a Mayan gidajen zamaninmu saba'in kafin kagano iyakar inda wutar ta tsaya.Kabbara suke yi suna Kiran Ubangiji babu gazawa take wannan wutar tayi sama kamar anjefata inda sunakai dubansu wajen zuka ga wajan yazama wani wawakeken rafi cike da ruwa kamar kasa hannu ka d'ebo sedai babu hanyar wuce wa....
'YAR GATAN MAMAβπ»
NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ARZAI ALLAH YABADA TSAWON RAYUWA MAI AMFANI AMIN.
βοΈππππβοΈ
SHAFI NA 73&74
βοΈππππβοΈ
Wannan shi ake Kira ga samu ga rashi,ko wannensu ya tsaya yana tunani tare da rok'on Ubangijin sammai da k'assai da ya dafamusu ya kawo musu d'auki daga sharrin dake wannan DUNIYA.SARAUNIYA SINIYYA da dokinta ke kusa-kusa da wajen ta d'aga sharb'eb'iyar takobinta tare da jansa ta d'aga murya tare da girmama Ubangijinta Wanda yafi kowa ta danna cikin ruwan ba tare da jin komai ba,ganin haka yasa GIMBIYA ZULMAT take Mata baya inda suma suka rufa musu baya bakunansu suna fad'in "ALLAHU AKHBAR! ALLAHU AKHBAR!!" Haka suka rud'e suna fad'i ba k'ak'k'autawa.Ga mamakin wasunsu koda suka shiga se suka jisu kan dandanyar k'asa inda kuma wasunsu hakan ba bak'on abu bane awajansu dan sunsan kad'anne daga makircin mak'iya Ubangiji,wasu kalolin halittun ruwa ne suka dinga firfitowa yadda suke da yawa kai bama zaka fara tunanin sanin adadinsu ba,duk wasu dabarun yak'i yi sukeyi amma halittun k'ara tuttub'owa suke yi suna sake wani irin yawa inda suka fara karaya ganin yadda mutanensu suka fara zubewa k'asa wasu mugayen raunuka wasu kuma matattu.
Ba k'aramin lokaci suka d'aukaba kafin Ubangiji yabasu nasarar gamawa da wannan halittun agajiye suka yi gaba. Ko da suka yi gaban basu tsinci Kansu ako'ina ba se wani waje wanda aka masa wani irin gini mai hawa-hawa wanda hawansa idan kad'aga kai baka isa ka gano k'arshenshi ba dan tsayin nasa ya wuce afad'eshi, wasu tagogine ajikin ginin k'anana-k'anana abin har ya b'aci dan idan agininmu ne na nan abin zai zama asaka bulo d'aya atsallake d'aya haka wajan yake kaidai kawai sedai ka kalla.Haka suka cigaba da kutsawa ciki suna cigaba da ambaton UBANGIJIN MUSULUNCI babu gajiyawa atare da su ko kad'an,sunyi tafiya mai suna tafiya,yayin da suka Kai rabin ginin kawai suka fara jiyo haniniyar dawakai tako'ina kamar kunnuwansu zasu fashe,kalle-kalle suke yi amma basu ga ta inda ake tunkaro suba kawai sai jin harbi sukayi da mashi kamar ruwa sakinsa kawai ake tako'ina,cikin jarumta da kuma k'warewa afannin sanin kalolin makirci NUJBEER 'DAN NAJABURU ya bud'e tafukan hannayensa tare da rufe idonsa take kafin k'iftawar ido wasu kibbai da masu masu azababben yawa suka hau fitowa ta hannun nasa suna isa wajan wad'ancan cikin k'ank'anin lokaci wad'anda suka turoma suka koma can garesu inda suka b'arar da su baki d'ayansu.
Kabbara dandazon MUSULMAI suka d'auka tare da cigaba da tafiya,batare da sun ankaraba wasu k'ananun aljanu masu had'arin gaske suka dinga fitowa ta tagogin jikin wannan ginin,ko wace taga seda aljanu d'ari suka fito daga cikinta, k'ananun kawuna garezu inda suke da k'aramin jiki se kuma jikinsu shima k'arami yayinda wasu k'ayoyi ke shimfishe ajikinnasu se kuma harsensu dogo tsininsa kamar mashi kaifinsa kamar takobi,tunkarosu sukayi da azababben gudu yayinda cikin ikon UBANGIJIN MUSULUNCI kafin su iso inda suke sukadinga zubewa ak'asa shirif-shirif matattu.
Hamdala suka yi tare da godewa UBANGIJIN MUSULUNCI bisa d'aukin da yake ta kawo musu batare da ya bari sun fad'i ba....
ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMADUR'RASULULLAHI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMAπ
'YAR GATAN MAMA.
NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA 'DAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ARZAI ALLAH YAJA DA RAI YAJIK'AN MAGABATA AMIN.
βοΈππππβοΈ
SHAFI NA 75&76
βοΈππππβοΈ
Sunsha matuk'ar wahala wadda tasa duk suka fara canza kamanni dan yanzu ya zamana da k'yar suke cigaba da tafiyar,babu komai a ran mafiya yawansu banda tsoron me ze je yazo domin inda suka shiga ayanzu dole tsoro ya shiga zuk'atansu dan wani irin kogo ne mai azababben duhu na masifa ga wasu irin sautinka da suke tashi a cikinshi ba tare da sunga me fidda sautikanba,kowannen su hannunsa d'auke da itacen wuta yana haska gabansa,ba abinda sukejin k'afafunsu na takawa se k'asusuwa mabanbanta Wanda suka kasa gane na mutane ne ko kuma a'a? Wata iriyar azababbiyar iska ce mai matuk'ar k'arfin gaske ta taso daga cikin kogon tayo Kansu.
Kabbara suka had'a baki suka sake yi wadda daman can ita ce d'auke abakunan nasu, kamar k'iftawar ido haka iskar ta d'auke sedai ta samu nasarar zubar da mutane da yawa dan ta zubda mutune sama da ashirin yayin da sauran da suka rage suka tsaya akan k'afafunsu ta k'yar sannan suka cigaba da tafiya...
Suna yin gaba kad'an suka ga hanyar ta rabe biyu hagu da dama inda saitin inda suke ya had'e jikinsa Kai bazaka tab'a cewa hanya ceba,kallon kallo suka Fara yi tsakaninsu kowa na tararrabin hanyar da zaibi ta kaishi ga asalin inda yake son zuwa dan kowa ya tabbatar da wajan ya koma haka ne domin ajuyar musu da hankali su kasa gane ainahin inda zasu bi,tsakaninsu kawai suka yanke shawarar subi hanyar da ke dama da su wadda take bak'ik'k'irin baka gano komai acikinta se azababben bak'i na tashin hankali.
Had'a baki suka yi tare da d'aga takubbansu suka ruga da azababben gudu izuwa wannan duwun,k'ara suka Fara ji me had'e da kuka had'e da shasshek'a ana fad'in " Ku temake ni bayin Allah zasu cutar dani...Allah ka kawon d'aukink"
Ai kawai se maganar ta katse suka sake jin ihu had'e da k'arar da tafi ta baya,basu tsaya ba suka ci gaba da tafiya suna kiran UBANGIJIN MUSULUNCI!
Wani waje suka iso Wanda yake da d'an haske dan kana iya ganin gabanka da bayanka,babu zato bare tsammani kawai suka hangi wani matashi Wanda shekarunsa zasui talatin da biyar zuwa da shida sanye da kayan bayi irinna jikin bayin masauratar SARKI KAMALUD-DEEN yana kwance ak'asa jini na zuba daga sassan jikinsa jikinsa d'aure da kakkaurar igiya an mammatse shi da ita dagani yana cikin azaba se fad'i yake yi " 'Yan uwana kuzo Ku temaka mini ku kwance ni kada na rasa rainaaa"_Wasu daga cikin bayin da ke sanye da irin kayan jikinsa suka yi kansa inda sauran suka ci gaba da tafiyarsu zuciyarsu banda ambaton UBANGIJIN MUSULUNCI babu abinda take yi.
Ko da suka isa inda wannnan mutumin yake yana ta kukansa duk yabi ya basu tausayi matuk'a gaya, suna zuwa jikinsa domin suyi dabara su kwance shi kawai basu zata ba suka dinga jin wata mahaukaciyar dariya wadda ta ke barazanar toshe kunnuwansu yayin da k'asar wajan ta dare biyu suka shige cikinta inda shi kuma mutumin da suka je temako yazama wata murtukekiyar halitta ya had'iyesu baki d'ayansu.
Ko da suka ci gaba da tafiya basu tsinci Kansu a ko'ina ba se gaban wani DUTSE me mugun girma da tsayi Wanda suka yi imanin cikinsu babu wani Wanda zai iya hawansa ko makamancin haka, YARIMA MUSLIM ne ya d'aga takobinsa me azababben tsayi tare da cakawa ajikin dutsen.... Ga mamakinsu base suka ga ya b'ace ba kamar dama babu shi awajanβοΈ
βοΈβοΈβοΈβοΈWani haske suka Fara hangowa daga nesa dasu can saman wani d'an k'aramin mulmulallen DUTSE βοΈβοΈβοΈβοΈ
βοΈβοΈβοΈβοΈTAKOBIn ce akansa tana cikin murfinta Wanda jikin murfin nata ke d'auke da zinare da lu'u-lu'u,matsawa wajan suke yi a hankali yayin da idonsu ya sauka kan mulmulallen dutsen wanda ya kasance zallar GOLD me azababben kyau haskensa ya haske wajan...
Kowa ya zo inda yake son zuwa amma ya ja ya tsaya ya kasa taka k'afarsa ya k'arasa gaban dutsen kamar wanda yake gano mutuwarsa awajan.
NUJBEER 'DAN NAJABURU da ya gama galabaita yaja k'afarsa da k'yar tare da kallon sauran mutanen suke tare ya kuma rik'e Takobinsa da kyau sannan ya tunkari inda TAKOBI n ta ke domin so yake ya d'auka kafin kowa ya dawo daga duniyar tunanin da ya shiga,nishad'i ne ya Kama shi yayin da zuciyarsa ta cika da far in ciki ganin babu abinda ya sa me shi ya isa jikin Gold d'in tare da fad'in sunan UBANGIJIN MUSULUNCI a rarrabe jikinsa na rawa ya d'ora hannunsa jikin dutsen da niyyar ya d'auki Takobin kawai batare da ya Lura ba tuni wasu macizai sun zagayeta sun fiddo harsunansu waje yayin da kafin yayi yunk'uri wata iska mai k'arfin gaske ta d'ebeshi ta watsar da shi can gefe daban.
Duk abinda ya faru akan idonsu Sarauniya dan haka kowa ya sake tsayawa yayin da tsoronsu ya ninka na da...
βοΈYARIMA MUSLIM ne ya d'aga Takobinsa tare da rugawa wajan da azababben gudu inda GIMBIYA ZULMAT ta mara masa bayaβοΈ
Ko da isarsa wajan Macizan sun nunku sunfi na baya yawa, cikin jarumta ya d'agata tare da sare kan wasu daga macizan,inda sake d'agawar da zaiyi ya ga Takobin ta rabe biyu.GIMBIYA ZULMAT ce ta dira gabansa tana wani irin wuci tare da mik'awa Yarima Takobin hannunta ita kuma tana d'aga hannunta se ga wannan makirar Takobin ta bayyana ahannun nata tana ta shek'i da d'aukar idanu, tana zuwa hannunta ta saita ta inda Macizan suke wanda ga mamakinta sunk'ara yawa kamar wasu gero saboda yadda suka cakud'e waje d'aya suka lullub'e Takobin.Tana saita su da ita wani haske ya fito daga cikinta ya sauka Kansu wanda ta ke suka Fara zubowa k'asa babu k'wari...
Matsawa ta ke yi gabansu suma suna matsawa yayin da wasu tuni sungudu wasu kuma lokacinsu ya riske su...
Isarta jikin Gold d'in ke da wuya ta saka hannunta jikin Takobi tare da rufe idonta tace "ALLAHU AKHBAR..!"
Ga mamakin su se suka ga ta Ciro TAKOBIN 'DAUKAKA! Tsayawa tayi akan k'afafunta sosai hawaye na bin idanunta jikinta na rawa kamar mazari yayin da kukanta yafara k'arfi idanunta sunyi jawur...
'Dago dara-daran idanuwanta tayi tare da sauke su kan YARIMA MUSLIM ta nemo jarumta ta sakar masa wani lallausan murmushi tare da d'aga hannunta da TAKOBIN 'DAUKAKA ta ke kai ta mik'a masa tare da girgiza masa kai alamun tabbatarwa, kallonta yayi sosai da sosai tare da d'an had'e mata rai kad'an...
Fuskar da tayi bazai karb'a ba yasa ta saka hannunta d'aya tare da ruk'o hannunsa d'aya ta d'ora masa ita sannan ita kuma ta juya ta koma inda su Sarauniya suke.
Motsin NUJBEER 'DAN NAJABURU suka ji daga bayansu,ko da suka juya se suka ganshi jikin wata rijiya hannunsa d'auke da guga ya d'ebo wani shud'in ruwa acikinta,kafin su ankara suka ga yad'aga ruwan ya zubashi ajikinsa tundaga tsakar kansa.Mamakine ya cikasu ganin ya dawo d'an k'aramin yaro me azababben kyawu......
Allah ka tsarkake mana zuciyoyinmu ka barmu ahanyarka da'iman.Allah bamu nufi kowa da sharri ba Allah ka lalata shirin duk wanda ya shiryamana mugunta karka bashi sa'a akanmu ya Allahu amin.
'YAR GATAN MAMAβπ»
NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ARZAI ALLAH YA K'ARA MA IYAYENMU LAFIYA AMIN.
βοΈππππβοΈ
SHAFI NA 77&78
βοΈππππβοΈ
Mamakinsu ya kuma k'aruwa sanda ya sake d'aga ruwan ya kuma zubashi tun daga tsakar kansa har k'afafunsa,ai baikai ga sauke hannunsa ba ya dawo babban mutum me kimanin shekaru sittuna au saba'unaπ€ͺ'tabd'ijam shi da yakeson zama saurayi me ji da rayuwa hakamadai ai ana jika' Ai da gama wannan tunanin suka ga ya sake d'aga gugar yana murmushi ya juye duka ruwan akansa batare da yayi ragowa ba,,,,,,,,,WARRR,,,,,,,,,Hhhh! Ai kawai maimakon yadawo matashi se ya zama wata mummunar halitta shi ba biri ba shi ba mutum ba,ta ke ya lek'a kansa cikin rijiyar inda ba b'ata lokaci yayi tozali da suffar da ya koma batare da wani nazari ba ya tak'ark'are ya saki wani razanannen ihu mai firgiyarwa wanda se da ya tsoratar dasu gaba d'ayansu,wani irin kuka yake yi mai had'e da gunji gwanin ban tsoro yana safa da marwa daga nan ya shek'a da gudu yayi can...
Halin da ya fara shiga ne yakuma sanya musu wani azababben tsoro suka rink'ayin baya-baya kamar masu tsoron mayen da ke jin yunwa,,,,WARRR,,,,,,wasu kalolin k'uraje ne sukahau fitowa daga ko wane sashi na jikinsa inda sukadinga fidda wani irin ruwa mai tsutsotsi manya mabada k'yank'yami ta ke wasu macizai sirara suka hau fiddowa takowace b'ula dake wajan tare da tawowa inda yake, ai da ganin haka bai wata-wata ba ya arta da wani irin gudu kamar ya kai kamar ya fad'i haka ya k'arasa gaban d'aya rijiyoyin ya fad'a cikinta yayin da su Sarauniya suka ji babu dad'i amma babu damar taimakonsa tunda shi yakai kansa.
.......
Koda ta dawo inda su Sarauniya suke se ta tsaya tana kallonsu murmushi d'auke afuskarta yayin da idanuwanta basu bar zubda hawaye ba,duk da sun so sanin me ya sakata kukan haka suka k'yaleta saboda babu damar wata tambaya ahalin da suke ciki.
Sake rik'e Takobin yayi sosai a hannunsa ransa cike da mamakin GIMBIYA AMINATU da atunaninsa itama buk'atar Takobin ce ta kawota'to amma me yasa ta bashi?'
Ya tambayi kansa bayan babu mai bashi amsa sai ita kanta ita kuma ya fuskanci yanzu tana cikin damuwa domin ko ba'a fad'amaka ba fuskarta ta nuna hakan dan haka kawai yaci gaba da kad'aita UBANGIJIN MUSULUNCI tare da biyo bayansu domin su koma can inda suka baro ragowar jama'arsu Wanda sunsan zuwa yanzu sunacan suna tunanin angama da su ne.
Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Kalmar da dandazon Musulmai suka rud'e suna fad'a kenan saboda hangosu da suka yi nesa da su suna tawowa garesu...
Farin ciki yau ya mamaye zuk'atan Musulman domin yau sunsamu sunga bayan zaluncin da ke WATA DUNIYA domin wannan Takobin ita ce suke k'arar da duk wata rundunar Musulmai da ita to yanzu kuma gata ta dawo hannun Musulmai kaga shikenan zalunci yazo k'arshe.
SARKI KAMALUD-DEEN ne ya tashi fuskarsa d'auke da mad'aukakin murmushi ya je ya rungume YARIMA MUSLIM yana musu barka da arzik'i.SARAUNIYA SINIYYA bayan ta samu waje ta zauna MUSLIMAT ta iso inda suke tare da yi musu ban gajiya yayin da k'asan zuciyarta ke cike da k'unci jin GIMBIYA AMINATU(ZULMAT)ce ta samu nasarar d'aukar Takobin sannan ta bawa MUSLIM ita duk takaici nema ya kamata dan ji takeyi kamar taje ta shak'e Aminatu ko ta tsira soyayyarta ma ta tsira! Wani mugun kallo ta wurgawa Aminatu asirrance ba tare da kowa ya gani ba sedai ita wadda tayiwan daman idonta akanta yake dan haka kawai GIMBIYA AMINATU ta lumshe idonta tare da yi mata wani k'ayataccen murmushi Wanda seda gaban MUSLIMAT d'in yai mummunar fad'uwa dan ta yi imanin da YARIMA Aminatun taiwa wannan malalacin murmushin ba abinda zai hana ta shiga ranshi dan dole se hankalinsa ya kwanta, hakan yasa ta sake had'e rai tare da sunkuyar da kanta gudun karwani ya fuskanci me sukeyi batare data