Showing 21001 words to 24000 words out of 33915 words
Chapter 8 - WATA DUNIYA COMPELET HAUSA NOVELZ BY YAR GATAN MAMA.txt
biyashi ya shigar damu,da zarar munshiga saimu cakud'a dash my d'akko bayan komai ya kammala saimu komowa addininmu na iyaye da kakanni ya kuke gani?"
Cike da jin dad'in shawarar tasa suka had'a baki tare da sakin wani razanannan ihu mai firgitarwa,bayan ihun ya lafa ne ALJANI ASH ya dubesu tare da cewa......
โ๏ธ๐โ๏ธ๐โ๏ธ
SARKI KAMALUD-DEEN ya yanke shawara tare da umartar Tsoho NUJBEER 'DAN NAJABURU ya karb'i addinin ISLAMA kafin su shiga wata duniyar.....
๐๐ป๐๐ป๐๐ปALLAH KAJIK'AN MAGABATANMU KAYI MUSU RAHAMA,ALLAH IDAN TAMU TAZO KASA MUCIKA DA KALMAR 'LA'ILAHA ILLALLAHU MUHAMMADUR-RASULULLAHI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA,ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMADIN WASALLAM๐
More comments more typingโ๐ป.
Domin gyara sharhi ko bad a shawara atuntub'eni ta 07047530638.
'YAR GATAN MAMAโ๐ป
*____________________________________*
โ๏ธ๐WATA DUNIYA๐โ๏ธ
LABARI/RUBUTAWA
KHADIJA S.SAMINU
('YAR GATAN MAMA)
MARUBUCIYAR
๐๐ป
RAYUWAR MU!
A WANI GIDA
MAGANIN KAR AYI
(Kar a soma)
RANA DUBU
(Ta b'arawo...)
And now....
โ๏ธ๐WATA DUNIYA๐โ๏ธ
*๐๐ฐAINUWA ๐ผRITER'Sโ๐ผ*
*๐ฆSSOCIATION๐ค๐ป*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*๐๐ป
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA 'DAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ALLAH YAJA DA RAI YA BADA RABO MAI AMFANI AMEENโค๏ธ
โค๏ธโค๏ธโค๏ธK'awata kuma Yayata ta amana(AYSHERCOOL) Allah ya k'ara lafiya yasa kankarar zunubai ne,Allah y k'ara basira da hazak'a ameenโค๏ธโค๏ธโค๏ธ
โ๏ธ๐๐๐๐โ๏ธ
SHAFI NA 53&54
โ๏ธ๐๐๐๐โ๏ธ
.......โ๐ป
Koda BOKA NUJBEER 'DAN NAJABURU yaji wannan Batu na Sarki sai ya kalleshi fuskarsa d'auke da dariya sannan yace....
"Yanzu Kai banda abinka inakai ina fad'amin wannan kalma haka mai zafin gaske? Zafin Kalmar nan ya kusa ya k'ona ni,tunda sauran k'arfina akemin tayi amma lokacinma duk Wanda yamin tayin daga wannan maganar baya sake wata Dan a take nake ganin bayansa,kaima na rabu dakaine saboda buri na yana tattare da Kai"
Koda yagama wannan said yabar gaban Sarki tare da komawa can nesa dasu ya zauna ya tsunduma tunani.
WAIWAYE.....
NUJBEER 'DAN NAJABURU gawurtaccen matsafi ne Wanda yayi suna sunan da duk Wanda yazo azamaninsa saiya sanshi saboda hatsabibancinsa,yasha gwagwarmaya tsakanin mabiya addininsa da mabiya addinin musulunci,bai tab'a fad'uwa ba kasancewar ya mallaki duk wani abinda zai taimakamai tsakaninsa da wani mahaluk'i dake doron duniya,ya kashe bil'adama yanda ko shi kansa bai isa ya k'iyasta adadin ran da ya kashe ba,ba wani buri ne dashi ayanzu haka ba illa burin d'aukar Takobin wata duniya wadda bincikensa ya tabbatar masa idan ya d'auketa to tabbas ko shed'an la'ananne se ya sarawa shed'ancinsa domin shi zai zama yana mulkar dukan wash masuji da tak'adaranci da tsafi afad'in duniyar nan,sannan bincikensa ya tabbatarmai akwai wani kogo acikin WATA DUNIYA Wanda ake kiranshi KOGON HATSABIBAI acikin wannan kogo akwai wata rijiya mai baki arba'in da d'aya,rijiya ta kowacce acikin akwai babban sirri da take d'auke dashi,rijiya ta bakwai tana d'auke da wani shud'in ruwa Wanda matuk'ar ka d'ebeshi ka wanke tundaga tsakar kanka had yatsa! To tabbas zaka dawo sabon mutum ma'ana yaro,idan ka dawo yaro zaka sake wanke jikinka dashi yadda zaka zama saurayi,idan kuma harka maimaita akaro na uku to babu makawa zaka koma tsoho fiye da yadda kake ayanzu wannan k'uduri yananan azuciyar NUJBEER 'DAN NAJABURU yana son yadawo k'arami ya k'ara dire hatsabibancinsa adoron k'asa.
Wannan kenan...
Koda NUJBEER 'DAN NAJABURU ya tashi sai sarki ya shiga dogon nazari akansa tare da mamakin girman Kai irin nashi,ahaka dai har lokaci ya k'ure suna tunani.
โ๏ธ๐โ๏ธ๐โ๏ธ
Bayan ALJANI ASH ya gyara zamansa akan dutse ne yai gyaran murya sanann yace...
"Shin kun manta Ubangijin Musulunci ance yana ji yana ganin komai?
Bakwa tunanin yajimu yazo ya wargaza mana shirinmu?
Da-dai wata shawarar ba wannan ba"
"Ka jika da wata magana kamar ba jarumi ba,wa..wa yace maka Ubangijin Musulunci yana jinmu yana ganinmu,ka duba kogonnan da kyau ka gani baabu wata k'ofa da wani zai lab'e ya jimu ko ya ganmu dan haka tsoro yafita aranka,Kai idanma baka yadda ba bara na mama misali...Lokacin iyayenmu da kakanni ina waje suke samu suyi sirri su had'a kalolin makircinsu kuma burinsu ya cika,idan har yana jinsu ya Hana burinsu cika mana"
Bayan ALJANI DUUJALA ya gama wannan maganar haka sauran aljanun sukaita kawo hujjoji mababanta domain Aljani Ash ya yadda su canzamai tunani,tun yana musawa dai harya yadda sabida sarkin yawa yafi sarkin k'arfi.
โ๏ธ๐โ๏ธ๐โ๏ธ
"Sannan ya kashe ki, ya rage kafirci da kafirai irinki?"
Wani mugun kallo Gimbiya Zulmat ta watsamata sannan ta sunkuyar da manta k'asa idanunta sunyi jajur saboda b'acin rai jikinta yahau rawa kamar mazari,yunk'urawa tayi cikin zafin nama Wanda seda hantar cikin Muslimat ta kad'a saboda yadda ta razana da ganinta.....
Domin gyara sharhi,ko bad a shawara
07047530638.
'YAR GATAN MAMAโ๐ป.
*____________________________________*
โ๏ธ๐WATA DUNIYA๐โ๏ธ
LABARI/RUBUTAWA
KHADIJA S.SAMINU
('YAR GATAN MAMA)
MARUBUCIYAR
๐๐ป
RAYUWAR MU!
A WANI GIDA
MAGANIN KAR AYI
(Kar a soma)
RANA DUBU
(Ta b'arawo...)
And now....
โ๏ธ๐WATA DUNIYA๐โ๏ธ
*๐๐ฐAINUWA ๐ผRITER'Sโ๐ผ*
*๐ฆSSOCIATION๐ค๐ป*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*๐๐ป
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ARZAI.
โ๏ธ๐โ๏ธ๐โ๏ธ
SHAFI NA 55&56
โ๏ธ๐โ๏ธ๐โ๏ธ
Jikinta ne yahau rawa inda k'irjinta ke dukan dubu-dubu saboda tunanin me GIMBIYA ZULMAT zata yi Mata,ga mamakinta se gani tayi tazo ta wuceta taje kan YARIMA MUSLIM tana bashi kulawar da bata bawa kowa awajanba,duk inda zata tab'a ajikinsa se tayi kamar tayi kuka saboda ji takeyi tamkar ciwon ajikinta yake,ta bawa kowa mamaki barin MUSLIMAT da tayi bata kulata ba,kowa tunaninsa ya bashi zuwa zatayi taimata abinda bazata manta ba amma se suka ga sab'anin haka.SARAUNIYA SINIYYA tunda ta dawo cikin hayyacinta se tayi sujjada ga ubangijinta tana mai yi masa godiya bisa tseratar da su da yayi ta silar baiwarsa ZULMAT ta jima tana rok'awa Zulmat samun gwaggwab'an rabo wato rabon shiga musulunci,dukkan abinda ke faruwa akan I donta ya faru sedai ta sawa ranta bazata sakewa MUSLIMAT magana akan ta rage abinda takewa ZULMAT ba tunda ai kishi ba hauka bane ba.
WAIWAYE..DEENUL-ISLAMโ๐ป
A wani gari mai sun a DEENUL-ISLAMโ๐ป Anyi wani sarki Mai cikakken k'arfin mulki ya shahara matuk'a da gaske wajan gudanar da gaskiya acikin mulkinsa,yana da tsantsar tsoron Allah da k'ok'arin kamanta adalci atsakanin mabiyansa,hakan yasa jama'ar garin suke matuk'ar sonsa saboda yadda bashi da son zuciya ko kad'an a al'amuransa.SARKI ABDALLAH! Yana da Mata guda biyu GIMBIYA SUWAIBATU da GIMBIYA MAIMUNATU.
GIMBIYA SUWAIBATU ita ce matarsa ta lalle wadda al'ada ta zab'a masa ita amatsayin abokiyar rayuwa,ita kuma MAIMUNATU se bayan ya zama Sarki ne aka tilastamai se ya k'ara aure kasancewar sarki baya zama da mace d'aya.
Allah ya bawa SARKI ABDALLAH son haihuwa Dan 'ya'yan 'yan uwansa kamar nasa ya d'auke su yana ji dasu yanda bazaka iya tantance nasa ne kona waninsa ba.Ubangiji sarkin hikima da iyawa,da ya tashi sai bai azurta GIMBIYA SUWAIBATU da haihuwa ba tsawon shekara goma sha d'aya lokacin GIMBIYA MAIMUNATU tana da shekara d'aya agidan SARKI ABDALLAH! Kuma cikin ikon Allah se gata da ciki ,bayan ciki ya cika watanninsa ya isa haihuwa Maimunatu ta haifi d'anta namiji mai kama da Sarki Abdallah sak Murna da farin ciki ba kalar Wanda Maimunatu batayi ba haka ma Suwaibatu tayi murna iya iyawarta tabada gudummuwa sosai awannan haihuwa.
Lokacin da ta haihu Sarki bayanan sunyi wata tafiya se dawowa yayi ya tarar da abin farin ciki ya same su,yayi farin ciki sosai sedai bai nuna yadda ya kamata ba agaban mutane hands hakan yai sanadiyar sanyawa Gimbiya Maimuatu jin wani Abu azuciyarta har danginta suka zugata suka cemata duk shirin Suwaibatu ne saboda bata da k'wan da zata kalla shiyasa ta shiga ta fita ta hanashi farin ciki saboda ba haka taso ba.
Wannan hud'ubar ta samu mazauni mai girman gaske azuciyar Maimunatu Wanda hakan ya jawo ta Dena yadda d'anta yadena zuwa hannun Suwaibatu koda kwa gata-gata ne saita hanata ko tace yunwa yake ji ko makamancin haka.Wannan Abu da MAIMUNATU ke yiwa SUWAIBATU yafara damun SARKI ABDALLAH saboda ko agabansa yana ganin yadda take hanata d'aukar MUJAHEED(sunan Yarima) gashi yaron jininsu ya had'u da GIMBIYA SUWAIBATU da ya ganta ya ringa wangale baki kenan ta d'aukeshi amma Maimunatu ta Hana.Abin duniya yabi ya ishi GIMBIYA SUWAIBATU kullum kuka da rok'on Allah ya bata haihuwa ko itama ta kalla taji dad'i.
Allah maji rok'on bawansa kwatsam MUJAHEED na da shekara biyu da Rabi Sega GIMBIYA SUWAIBATU da juna biyu,zo kuga murna da farin ciki gun Sarki da duk wani masoyinsu,kowa yayi farin ciki da samun wannan ciki na GIMBIYA SUWAIBATU ciki harda wad'anda basason ta haihu abaya seda sukayi farin ciki saboda suna so suga yadda Maimunatu zatayi Dan tunda ta haihu ta samu lasisin hulak'anta Wanda ranta keso saboda gani take itace magajiyar wannan masaurata bayan ran Sarki tunda SUWAIBATU juya ce๐ฅต Tarairaya da tattali SUWAIBATU ta shashi wajan Sarki da Mahifiyar Sarki wato FULANI saboda akwai kyakkyawar alak'a tsakaninsu SUWAIBATU bata yards ta hulak'anta FULANI ba ganinta take kamar mahaifiyarta sab'anin MAIMUNATU da bata kallon kowa da gashi.
Sannu-Sannu bata Hana zuwa sedai adad'e ba'a zona,lokacin baya k'arya dankwa cikin GIMBIYA SUWAIBATU ya isa haihuwa ko yau ko gobe amma ji kake shiru gashi ciki harya shiga wata na sha d'aya yana son fita amma haihuwa shiru sedai cikin yayi girman gaske Dan ko tashi yanzu ya gagareta,ganin haka yasa FULANI tasa aka kwashi GIMBIYA SUWAIBATU ta koma b'angarenta dan gani takeyi ba wata baiwa da zata iya kula da ita sai ita da kanta.
Wata goma sha d'aya da kwana goma dai-dai GIMBIYA SUWAIBATU ta tashi cikin dare da wani azababben ciwon ciki Wanda yai barazanar tafiya da rayuwarta,taci matuk'ar wahala wadda bazata fad'u ba kafin Allah ya bata nasarar haihuwar yara biyu kyawawa MACE da NAMIJI.....
ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMADUR'RASULULLAH๐
More comments More Typing.
Domin gyara sharhi ko shawara 07047530638.
'YAR GATAN MAMAโ๐ป
*____________________________________*
โ๏ธ๐WATA DUNIYA๐โ๏ธ
LABARI/RUBUTAWA
KHADIJA S.SAMINU
('YAR GATAN MAMA)
MARUBUCIYAR
๐๐ป
RAYUWAR MU!
A WANI GIDA
MAGANIN KAR AYI
(Kar a soma)
RANA DUBU
(Ta b'arawo...)
And now....
โ๏ธ๐WATA DUNIYA๐โ๏ธ
*๐๐ฐAINUWA ๐ผRITER'Sโ๐ผ*
*๐ฆSSOCIATION๐ค๐ป*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*๐๐ป
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ARZAI.ALLAH YA SAKA MIKI DA ALKAIRI AMIN.
.....KA FA'DI ALKAIRI KO KAYI SHIRU.....
......DAI DAN WANI KARKATACCEN WANI.....
.....ABINCIN WANI GUBAR WANI.....
โ๏ธ๐๐๐๐โ๏ธ
SHAFI NA 57&58
โ๏ธ๐๐๐๐โ๏ธ
Bayan GIMBIYA SUWAIBATU ta haifi yarannan biyu bata kuma sanin inda kanta yake ba har tsawon kwana uku bata d'auki yarannan ahannunta ba dan haka yaran suna k'ark'ashin kulawar FULANI mahaifiyar Sarki ABDALLAH.Acikin rana ta hud'u da haihuwarta ne aka fara ganin haske game da rashin lafiyar tata,d'aya bayan d'aya FULANI ta dinga d'ora Mata Yaran da ko suna Sarki yak'i sakamusu yace sai sunan da ta zab'a,ganin yadda tak'i sakewa da yaran yasa FULANI ta fita domin ta fuskanci har yanzudai SUWAIBATU tana nan da kunya yadda ake buk'ata sab'anin MAIMUNATU wadda da kanta ta d'auki MUJAHEED ta mik'awa Fulanin.
GIMBIYA SUWAIBATU kamar jira take yi nan tahau rungumar yaran tana sumbatarsu had'e da sanya kuka Wanda ko ba'a fad'aba ansan na farin ciki ne,tun Sarki na kallonta har ya dakatar da ita da fad'in...
"Haba ke kuwa Uwar biyu kukan ya isa haka mama,kodai kina tuna yadda aka dinga miki rowar yaro ne?, kiyi farin ciki Ubangijinki ya wanke miki bak'in ciki ya baki biyu mace da namiji babu ta inda kika samu tawaya,nikam ki dena kuka haka matar amana dan ni yanzu haka Zan iya kyautar yarannan idan zasu dinga sakamin ke kuka...Kinsan fa ina k'aunarki kamar nay..."
Dariya ce ta k'wace Mata jin maganarsa sannan ta bud'i baki tace...
"Nasan kana sona kana k'aunata kuma nima ta b'angarena hakan ne,sedai Zan rok'eka wata alfarma"
Jinjina Mata Kai yayi alamun yana sauraronta dn haka taci gaba da fad'in....
"Ina neman alfarmarka ko bayan raina dan Allah kada ka fifita yarannan da MUJAHEED d'an wajan MAIMUNATU kayi adalci atsakaninsu domin dukansu d'aya ne awajanka sannan..."
Katseta yayi ransa ad'an had'e kana ya jefeta da....
"Bazan iyaba...Idan nace Zan iya nayiwa kaina k'arya kema kinsani, na dad'e ina neman haihuwa daga gareki,har na samu bandena rok'on nasamu gudan jini na daga gareki ba seda na samu zaki fad'an kalar son da zan yiwa yara na?
Ko kusa ma banson irin wannan maganar kowanne zai zauna amatsayinsa.Sannan maganar mutuwa ran kowa ahannun Allah yake dan haka kidena wannan maganar,wane suna kika zab'awa Yarima da Sarauniyar namu?"
Dukda bataji dad'in maganar tasa ba haka ta lullub'awa fuskarta murmushi mai d'aukar hankali sannan tace...
"Macen inaso asanyamin sunan Babata,duk da ina tantama akan sunan inatsoron Karna kasa tsawatar Mata idan tayi laifi,shi kuma asanya masa MUSLIM Ina rok'on Allah ya dawwamar dashi acikin musulmai yasa yazama mai kare musulmai,ko bayan raina kafad'a masa wasiyyata"
Ta fad'a tana had'a hannunta alamar rok'o.Jikin SARKI ABDALLAH ne yayi sanyi jin yadda duk magana saita ambaci mutuwa dan haka sai ya karb'i yaran yai musu hud'uba sannan ya ajjesu ya matso kusa da ita ya rungumeta yana lallashinta dan ya fuskanci zafin ciwon data tashi ne ya Sanya Mata haka,suna ahaka shima wasu siraran hawaye suka zuba agadon bayanta Wanda suka fito a idanunsa batare da ya sani ba.
Yarinya taci sunan FULANI wato HUSNIYYA inda ake kiranta da SINIYYA shi kuma MUSLIM.Anti shagalin suna Wanda ba'a tab'a irinshi ba a fad'in garin dama masu mak'otaka dashi taron ya samu halartar many an mutane inda yara suka tashi da many an kyaututtuka na bajinta da ban girma,anyi komai ya k'ayatar da mutane kad'e-kad'e da bushe-bushe babu kalar da ba'aiba marok'a sunci abinda sukaci awannan shagali domin Sarki yayi b'arin dukiya kamar baya sonta.Wannan kenan...
FULANI tana matuk'ar k'aunar takwararta SINIYYA jinta take har ranta dan haka kusan awajanta take rayuwa dan seta buk'aci babarta sannan take maidata.
Bayan GIMBIYA SUWAIBATU tayi kwana arba'in da haihuwa da kwana uku kwatsam ta tashi da wani matsanancin ciwon ciki Wanda yad'aga hankalin mutanen masarautar baki d'aya.Kwana d'aya tayi da ciwon nan tace ga garinku man......
Domin gyara sharhi ko bada shawara 07047530638.
'YAR GATAN MAMAโ๐ป
*____________________________________*
โ๏ธ๐WATA DUNIYA๐โ๏ธ
LABARI/RUBUTAWA
KHADIJA S.SAMINU
('YAR GATAN MAMA)
MARUBUCIYAR
๐๐ป
RAYUWAR MU!
A WANI GIDA
MAGANIN KAR AYI
(Kar a soma)
RANA DUBU
(Ta b'arawo...)
And now....
โ๏ธ๐WATA DUNIYA๐โ๏ธ
*๐๐ฐAINUWA ๐ผRITER'Sโ๐ผ*
*๐ฆSSOCIATION๐ค๐ป*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*๐๐ป
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA 'DAYA GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA ARZAI,ALLAH YAJA DA RAI๐.
.....Kowa yayi da kyau,zaiga da kyau.....
......Sharri d'an aike ne duk daran dad'ewa zai dawo maka daga inda ka aike shi....
.....Mu aikata alkairi ko badan kawunanmu ba don zuriyarmu,domin du Daren dad'ewa wannan alkairin namu zai zama abin ado ga Iyayenmu, 'yan uwanmu da 'ya'yan da zamu aifa yanzu ko nan baba...Ba iya nan alkairin zai tsaya ba,,,sai ya bimu har gidanmu na gaskiya inda babu makawa sai munje....
โ๏ธ๐๐๐๐โ๏ธ
SHAFI NA 59&60.
โ๏ธ๐๐๐๐โ๏ธ
Kwana d'aya tayi tana wannan azababben ciwon cikin tace ga garinku nan...
'Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un' Wannan mutuwa ta GIMBIYA SUWAIBATU ta kad'a ilahirin jama'ar masauratar DEENUL-ISLAM dama kewayenta,dan kafin kace me tuni zancen mutuwarta ya zaga ko'ina yaje har indama ita kanta bata jeba.
FULANI ta rud'e kuka kawai takeyi dan ita kanta ta kasa dauriyar da zata lallashi Mai Martaba ta bashi baki.Sarki ABDALLAH kuwa yana can baisan inda kansa yake ba dan ya suma har wad'anda ke tare dashi basusan adadi ba,kasancewar mutuwar tata bayan magriba ne akace abarwa safiya idan an idar da sallar asubahi asallaci gawarta.Cikin dare surutai Sarki ya ringayi har baisan me yake fad'aba danshi ayanzu ji yakeyi tamkar ba'a tab'a yimasa mutuwa ba aduniya sai yau,ya shiga matsanancin rud'ani ayau dan gizo GIMBIYA SUWAIBATU ta ringa yi masa gata tazo gabanshi tana fad'in " Zo kusa Dani mijina ina tare da Kai" Babu zato kawai sedai kawai aganshi ya rungume gawar yana dariya had'e da kuka harsai an rabashi da ita yake gane ashe ba gaske bane sai kansa ya kuma sarawa kamar zai fashe.
Tun farkon dare FULANI tayi iya k'ok'arinta wajan saita nutsuwarta tare da godewa Ubangiji bisa wannan sak'on dad'i da ya iso musu dashi na d'aukar GIMBIYA SUWAIBATU,ta hana kowa zuwa inda yaran suke ciki harda GIMBIYA MAIMUNATU dake gurshek'an kuka Wanda FULANI tace na tsantsar munafunci ne,bayan ta Fara bawa yaran kulawar da ta dace ne ta umarci SARKI ABDALLAH da ya yiwa matar tasa wanka amma taga hakan bazai yuwuba saboda bashi da nutsuwa ita kuma bazata bari abarta haka batare da anyi mata sutura ba dan haka ta Kira mutum biyu daga makusantanta da kuma wata amintacciyar baiwarta wadda girma ya kamata ta buk'aci akawo komai da za'a buk'ata domin suyi Mata sutura.
Bayan sun d'orata akan wani tudu d'aya daga cikinsu mai suna MARYAMU ta zauna ta fallafeta yayin da ita kuma FULANI tazama ita ke wanketa HANSATU na zubo ruwa yayinda BAIWAR FULANI ke nad'e ruwan daga wajan.Sun fara da Bismillah da kabbara sannan suka yimata Sarki da alwala kamar yadda akeyi sannan suka samu sabulu mai k'amshi suka wanketa da shi,saida suka wanketa sau uku (MAARA)sannan suka had'a tsarkakken ruwa suka saka ganyen magarya da d'an kafur suka d'auraye ta,bayan sun gama suka shimfid'eta akan doguwar sallaya mai kyau sannan suka d'akko auduga Fara kar suka toshe duk wata k'ofa dake jikinta Kama daga Gabanta,hancinta,idonta,kunnenta....Sannan suka d'auko likkafani shima fari kar burin duk wani mumini suka sakamasa turare me d'an karan k'amshi sannan suka saka Mata kamar yadda mukeyi bayan anrufe ko ina na jikinta ne aka saka mad'auri tunda k'afarta aka nannad'eta dashi tazama cikakkiyar Gaea sannan aka zuba yashi akan faranti aka d'ora akan cikinta gudun kumburin ciki๐ญ๐ญ(Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Allahumma arzuk'ni bish-shahadati indal-mauti...Allah kasa mu cika da kyau da imani kayi mana suttura duniya da lahira.Allah ka ciremana dirtyn dake cikin zuciyoyinmu ka ciremana hassada da k'yashi da magance mana cin naman juna kasa mu zauna d kowa lafiya.....Allahu akhbar Allah kayiwa dukkanin Wanda ya shaida da LA'ILAHA ILLALLAHU MUHAMMADUR'RASULULLAHI SALLALLAHU ALAIHI WASALAMA Rahama ka yalwata k'abarinsa dan arzik'jn masoyinka MUHAMMADU!!!).Bayan komai ya kammala ne wasu daga makusantanta suka shigo suka kwana tare da ita.
Kamar yadda aka fad'a kuwa akayi bayan an idar da sallah aka sallaceta,gazkiya GIMBIYA SUWAIBATU ta samu al'ummar Annabi SAW fiye da tunanin mai tunani,acikin masauratar akwai wani b'angare da Sarki ya ware domin shi da zuriyarsa ananne aka sakata ad'aya daga cikinsu Wanda yake agefen dama dana Sarki idan Ilahu yayi kiransa yabar wasiyya nan za'a sakashi.
Anyi komai cike da jimami har kowa ya watse akabar masarauta da 'yan cikinta,yara FULANI ta yanke shawarar