Showing 12001 words to 15000 words out of 33915 words

Chapter 5 - WATA DUNIYA COMPELET HAUSA NOVELZ BY YAR GATAN MAMA.txt

23 Nov 2025

1517

.07047530638.




ƳAR GATAN MAMA✍🏻.






⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️



⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️

LABARI/RUBUTAWA
KHADIJA S.SAMINU
(ƳAR GATAN MAMA)



Marubuciyar......


A WANI GIDA
RAYUWAR MU!
MAGANIN KAR AYI!
nd now......


⚔️WATA DUNIYA⚔️


⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️






*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*


NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.ƘURAINABU IDRIS YARO YAHYA ALLAH YACI GABA DA ƘARFAFA LAMURANKI AMEEN😍💞💞.


⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️
HASSANA IYAYI(Mmn Masoyi) Allah yak'aramk lafiya da basira yatsareki yabar zumunci🥰🤗Wannan shafin naki ne kiyi yadda kikeso dashi🤗🥰.
⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️
SHAFI NA 25&26





Koda MUSLIM ya fito ya tarar da ZULMAT zaune tazuba uban tagumi tana tinani wanda bazaka iya ganewa saboda yadda take yi da fuskarta da idonta da bakinta zai tabbatarma da tinanin nata akan abu mai muhimmanci ne kuma tanajin daɗin haka.....
Sanda ya ratso yazo daf da ita yaga ayadda ta ɗago da kanta ta zuba idanunta acikin nasa ko ƙiftawa batayi,wani murmushi takeyi ajejjere ba ƙaƙk'autawa.Yunƙurawa tayi daga inda take zaune da niyyar ta durƙusa masa ya dakatar da ita da faɗin....

"Banyiwa soyayya adalci ba idan har na bari kika zuba gwiwoyinki aƙasa da nufin roƙon soyayyata,ni ya kamata na durƙusamiki domin ko yaushe afagen SO namiji ke nema gun mace kuma ita yake lallaɓawa domin samun soyayyarsa agunta!Namiji shi ne bawa agun mace domin shike mata hidima har se yasaka tausayinsa acikin ƙoƙon ranta to asannane zaiyi nasarar samun soyayya agareta,domin daga sanda mace tafara tausayin namiji to da alama gaba kaɗan zata faɗa soyayyarsa.Hmm! Sedai kash!! ni anrigada anyimin matar da zan aura awannan masarauta dan haka ne nake faɗamiki tausasan kalamai naban hak'uri da lallashi saboda naga alamu sun nuna kamar kina shirin fara son......

Cikin kuka mai haɗe da sheshshek'a ZULMAT ta tare MUSLIM da cewa....

"Dakata!! Ka sauraramin da wannan mayaudaran kalaman naka masu tarwatsa nutsuwa da hankalina,daman tsawon lokacin dana ɗauka ina ɗawainiya da soyayyarka baka fuskanci mai nake nufi ba? Kana nufin kacemin daman amahaukaciya ka ɗaukeni? Kana nufin bazaka sharemin hawaye ba sai dai nazama na rasa komai nawa kenan? Na rasa mahaifiyata,na rabu da mahaifina da mahaifata,sannan aƙarshe na rabu da SOYAYYATA!!?.....Bazai yuwuba MUSLIM,tinda nakejin sunanka bantaɓa furtashi ba saboda girmamawar da nake maka,amma yau kanaso kasakamin dafin da bazan warke ba,me nayiwa rayuwa haka takeson wora ni ta inda saina gwanmace mutuwataaa!!"

Ai tana zuwa nan azancenta wani jiri ya ɗebeta ta tafi da baya zata faɗi inda cikin rashin sa'a tafaɗi adandaryar ƙasa yayin da hannunta yabugu da glass ɗin dake ajje atsakiyar falon.

Razani firgici da tsantsar tashin hankali ne suka dirarwa MUSLIM cikin daƙiƙu goma sha biyar wanda hakan ya haddasamai bugun zuciya mai tsananin gaske, wanda lokaci ɗaya yaji wata irin nadamar abinda yayi mata ya lulluɓeshi saima duk ya tsani ya kansa,cikin jarumta ya durƙusa ya tallafo kanta tare da runtse idonsa dan yadda yakeji acikin ransa abin bazai faɗuba.Hankalinsa ne yakuma tashi sanda yai tozali da jinin dake zuba ahannunta,sam bai lura da bigewarta da glashing ba sai yanzu"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!" Ya furta afili tare da tashi da sauri yai umarni da asamo likita ya dubata.

Kafin kace me tini zancen suman ZULMAT ya mamaye ko'ina na cikin masarautar domin gulma yau take ranarta wannan haɗu da wancan waccan haɗu wancan tini zance yaje inda mai zancen baijeba,hankalin SARAUNIYYA SINIYYA yayi mugun tashi saboda yadda lamarin ZULMAT yai tsamari,tin da hantsi ZULMAT tafaɗi gashi yanzu gari yarufe rana ta nufi maɓoyarta amma bata farfaɗoba,anbada tabbacin farfaɗowarta kowane lokaci amma har yanzu bata farfaɗoba Sarauniya se kaiwa take tana komowa saboda tashin hankali da ɓacin rai daya lulluɓeta jin abinda yafaru yai sanadiyyar faruwar hakan.ZULMAT ba ita ta farfaɗoba harse bayan isha'i Sarauniya ta tsinkayi muryarta data dishe tana maganar cikin harharɗewar magana tana cewa.....

"Soyayya bata yimin adalci ba,da ace zata yimin adalci da bata kamu da son wanda mahaifina yafi tsana arayuwarsa ba,ni ce wadda mahaifina yafiso amma hakan baisani na fifitashi akan SOYAYYATA ba!Na fifita wanda ba addinina ɗaya dashi ba ashe shirme nakeyi bansa niba? meyasa zaka yimin haka?meyasa bazakaji tausayi na ba?me yasa!Me yasa!!"

Da hanzari SARAUNIYA SINIYYA ta juyo ta fuskance ta fuskarta ɗauke da alhini da kuma nuna ɓacin ran da take ciki amma hakan bai hana agane farin cikin farkawar ZULMAT ɗinba akan fuskarta,dai-dai fuskarta ta sunkuyo daga inda take tsaye hannunta sak'ale a bayanta ta furta "Alhamdulillah! Gimbiya Sannu da jiki,muna fatan bakyajin komai yanzu ajikinki?"

Rinannun idanuwanta ZULMAT ta ɗago ta sauke su kan fuskar SARAUNIYA SINIYYA wasu siraran tagwayen hawaye masu zafi suna biyo gefen fuskarta, bakinta na rawa ta kuma duban sarauniyar sannan tace....

"Ashe bazaki iya sakawa ɗanki yasoni ba?ashe bazaki ji tausayi na ba?ashe maganganun da kukeyi basa aiki akanku se iya kanmu kafirai?ashe bazai soni ba,kifaɗamin mena rasa ajikina da namiji bazai soni ba?mena rasa!! Yau kodai ya furtamin yana sona ko kuma nacakawa kaina wuk'a naje inda mahaifiyata da kakannina suka tafi domin bazan bari nacigaba da rayuwa ba sena kashe kai....."


⚔️🌍⚔️🌍⚔️


MUSLIMAT ba ita ta farka ba harseda wata yunwa ta matsawa cikinta kasancewar ko karin kumallo bata yiba yau saboda ɓacin rai,sallah ta gabatar sannan tukunna taɗauki kayan marmari dake lufude cikin kwando a ajje tahau ci baji ba gani,bata samu nutsuwaba har seda taji tayi nak ba masaka tsinke sannan takoma gefe tazuba tagumi tana nazari.

"Agaskiya bana jin ko ZULMAT zata musulunta silar samun soyayyar MUSLIM zan barmata shi,domin kuwa nima ina sonshi fiye da yadda nakeson kaina,rashinsa arayuwata zai zama dai-dai da rasa rayuwata nikuma bazan yi gangancin rusawa kaina farin ciki ba koda kuwa hakan zai silar barina wannan masarautar..."



⚔️🌍⚔️🌍⚔️

Yau saura kwana uku alissafin NUJBEER ƊAN NAJABURU na tafiya WATA DUNIYA dan haka kowane shiri da zaiyi ya gamashi domin kuwa ya shiryawa wannan tafiyar fiye da yadda bawa nagari yakewa kansa tanadi wajan ambaton Lillahil'wahidil'ƙahhar....

⚔️🌍⚔️🌍⚔️

ALJANI DUUJALA!bayan tafiyarsu DUNIYARSU suna isa yatara kafatanin aljanun dake ƙarƙashin ikonsa tare dayimusu bayani kamar haka.....

"Inamai jinjinawa UBANGIJINMU SHALBAYN bisa sa'a dayake bamu adukkan ƙudurinmu na fili dana boye.JINJINA GA SHALBAYN!JINJINA GA SHALBAYN!!"

Nan gungun aljanun dake wajan suka ruɗe tare da haɗa baki cikin girmamawa wajan faɗin...

"JINJINA GA SHALBAYN!JINJINA GA SHALBAYN!!JINJINA GA SHALBAYN!!!"

Wata mahaukaciyar dariya ALJANI DUUJALA yahau ɓaɓɓakawa wadda yaɗauki tsawon daƙiƙa sittin da ɗaya da rabi yanayi sannan ya gimtse bakinsa yace.......

"Ina alfahari da kasancewarku ƙarƙashin ikona sannan inamai umartarku da ku bani aron hankulanku saboda muyi magana akan abinda yataramu"

Wani ALJANI mai bayyanannen muni ya karkace baki tare da maimaita abinda shugabannasu yace cikin wata iriyar murya mai sanya firgici.........




👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻

DAN ALLAH INA NEMAN ALFARMARKU"ALLAH KABAWA KHADEEJAH LAFIYA MAI ƊOREWA DAN ƘARFIN IKONKA"ABINDA ZAKUCE KENAN DAN ALLAH.NAGODE🥰😍


MORE COMMENT MORE TYPING.



DOMIN GYARA,SHARHI KO BADA SHAWARA ATUNTUƁENI TA WANNAN LAYIN👇🏻
07047530638.




ƳAR GATAN MAMA✍🏻.






⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️



⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️

LABARI/RUBUTAWA
KHADIJA S.SAMINU
(ƳAR GATAN MAMA)



Marubuciyar......


A WANI GIDA
RAYUWAR MU!
MAGANIN KAR AYI!
nd now......


⚔️WATA DUNIYA⚔️


⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️






*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.ƘURAINABU IDRIS YARO YAHYA ALLAH YAJA DA RAI YAƘARA LAFIYA.



⚔️🌍⚔️🌍⚔️
SHAFI NA 27&28
⚔️🌍⚔️🌍⚔️



Wani ALJANI mai bayyanannen muni ya karkace baki tare da maimaita abinda shugabansu yace cikin wata iriyar murya mai sanya firgici azuciyar mai imani,shugabannasune bayan Aljanin yagama bayaninsa yamiƙe daga ƙasaitacciyar kujerar dayake kana yace...

"Yaku tattarin ALJANUN DUUJALA! Ina son muyi magana ne akan sarki ZALIMUZ-ZAMAN amma kafin nace komai inason nasan suwaye zasu iya zuwa garin DEENUL-ISLAM suyi duk mai yuwuwa domin ganin GIMBIYA ZULMAT bata musulunta ba?sannan inaso nasanar daku cewa alƙawarin dana ɗaukarwa ZALIMUZ-ZAMAN na temakamasa yasamu TAKOBI bazan cika shiba"

Ajejjere suke kallonsa tare da jinjina lamarin dayazo musu dashi,ɗaya daga cikin aljanunne ya kalleshi tare dacewa....

"Kaine jiya kaine yau kaikake da isa da iko damu dan haka muna sauraronka yadda kace haka za'ayi...!"

Aljani DUUJALA!Ya karkace baki ya shek'e da wata razananniyar dariya kana yace....

"Sannunka GUNZAIL naji daɗin wannan magana taka dan haka nakeso naji tabakin Aljani AR'TIYAN domin banason daga baya wani yace zai kawo wata shawara wadda baazan ɗauketa ba saboda lokacin da aka kawota bakin alƙalami ya rigada ya bushe...."

Aljani AR'TIYAN! ya ɓaɓɓake da wata mahaukaciyar dariya kana ya gimtse bakinsa yace......

"Wanene yake da cikakken iko acikin aljanun wannan duniya idan ba kaiba?yadda kafaɗa shi ne dai-dai ya shugabanmu,dan haka sedai nace wannan shawara taka itace dai-dai domin ni daman da aka faɗamin ZALIMUZ-ZAMAN yanaso ya mallaki wannan TAKOBI dazai mallake mutane da Aljanun dake faɗin wannan duniya ni daman ban aminta ba domin sam bazan yadda muzana aƙarƙashin ikonsa ba"
Wani ɗan dunƙulen aljani dake gefe ya karkace baki yace......

"Oh! Daman ai shugabane yake dankwafar damu idan munyi niyyar ganin bayan sarki ZALIMUZ-ZAMAN,amma yaza'ai ace mutum yana mulkarmu mu Aljannu inba sakaci irin namu ba?ai kawai mu nunamai soyayya mu shiga jikinshi muyi yadda ƴarsa zata yiwa mutane"


Wata dariya Aljani AR'TIYAN!Yake ƙyaƙyatawa saboda jin abinda Aljani DUƘUFUL!yace....Aljani DUUJALA!ya dubesu yace....

"To naji daɗin hakan da kuka yanke da kanku,dan haka kowa yasan me yakeyi mudage muɗauko TAKOBIn nan daga baya saimu zaɓi guda acikinmu yazama shike mulkarmu baki ɗaya,inamai umartarku wasu su shirya su tafi DEENUL-ISLAM domin gano mai GIMBIYA ZULMAT take ciki,iya masifa karku barta ta karɓi addininsu.


⚔️🌍⚔️🌍⚔️

A mamakance SARAUNIYA SINIYYA tajuyo takai dubanta ga GIMBIYA ZULMAT jin kalaman da ke fitowa daga bakinta......

Babu shiri tayi umarni da aka kiramata MUSLIM da MUSLIMAT domin ta nuna ikonta akansu baki ɗaya.....





👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻
DAN ALLAH INA NEMAN ALFARMA"ALLAH KAƘARAWA KHDEEJAH LAFIYA KA TSARKAKE MATA ZUCIYARTA TA DAUWAMA AHAKA"DAN ALLAH ABINDA ZAKUCE KENAN NAGODE.



MORE COMMENT MORE TYPING.....


DOMIN GYARA,SHARHI KO BADA SHAWARA ATUNTUƁENI TA WANNAN LAYIN.....07047530638.





ƳAR GATAN MAMA✍🏻.





⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️



⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️

LABARI/RUBUTAWA
KHADIJA S.SAMINU
(ƳAR GATAN MAMA)



Marubuciyar......


A WANI GIDA
RAYUWAR MU!
MAGANIN KAR AYI!
nd now......


⚔️WATA DUNIYA⚔️


⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️






*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*


NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABAƊAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.ƘURAINABU IDRIS YARO YAHYA ALLAH YAƘARAMATA LAFIYA AMEEN.


⚔️🌍⚔️🌍⚔️
SHAFI NA 29&30.
⚔️🌍⚔️🌍⚔️


❤️❤️❤️❤️❤️❤️
UMMUNAH💖🙌🏻🙌🏻
❤️❤️❤️❤️❤️❤️
Idan kaji ana cewa jinjina ɗaya kenan🤗Ni wannan jinjinawar tawa ba guda ɗaya bace agareki Ummun@h🙌🏻Ke ce wadda koyaushe kike ƙaramin ƙarfin gwiwa abisa duk lamuran da zan dn haka ina matuƙar godiya tare d addu'ar Allah yatsareki d ke da zuri'arki dn arzik'in Annabi da Alƙur'ani👏🏻Allah yashiga dukkan lamuranki,kinfi ƙarfin abaki kyautar page dn dukama littafin mallakinkine saidai fatan nasara.Hayaty son so fisabilillahi❤️💖😍💞💞.
❤️❤️❤️❤️❤️❤️
Ummun@hhh💖🙌🏻
❤️❤️❤️❤️❤️❤️


⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️


Babu ɓata lokaci tayi umarni da a kiramata MUSLIM da MUSLIMAT danta nuna ƙarfin ikonta akansu.Bayan tafiyar ne ta juyo da dubanta ga GIMBIYA ZULMAT fuskarta tamkar hadari dan yadda ta haɗeta baazaka ce ta taɓa dariyaba tace....

"Ashe daman ke bakya da wayo har haka? me zaisa ki lalata rayuwarki kiƙarar da ita saboda wani ɗa namiji?shin dama kinzo duniya dominshi ne da zaki kashe kanki saboda shi,shin dama soyayyarki ce ta kawoki wannan garin namu ba abinda kikace mana b...."

Saurin dakatar da ita ZULMAT tayi ta hanyar ɗaga mata hannu tare da fashewa da kuka tace.....

"Yake wannan Sarauniya mai ƙarfin iko! Duka waɗannan tambayoyi da kikayimin amsarsu haka ne domin tunda nake atsayin rayuwata bantaɓa neman wani abu na rasaba sai yau,sarakuna da ƴaƴan sarakuna bansan adadin waɗanda sukanemi aurena ba amma nace ba wanda nakeso nace ni bama zanyi aurenba,kwatsam naga MUSLIM na kamu da sonsa kuma na ajje izzata da isata na furta ina sonsa amma shi ya....."

Maganar ce ta maƙale amaƙoshinta sakamakon shigowar su MUSLIM inda suke,sarauniya ta sake ɓata rai ganin bataga MUSLIMAT ba dan haka ta dubi FANTA tare da cemata....

"Shin ina MUSLIMAT take nace kisanar inason ganinta?"

"Allah yaja zamaninki!Munje tare da ni da YARIMA amma bata buɗe ɗakinba kuma mun ƙwanƙwasa cikin girmamawa sedai muna tunanin kota samu wutawa ne?"

Umarni ta sake badawa akan asake komawa abugamata akiramata ita yanzunnan amma yanzunma haka sukaje suka dawo batare da MUSLIMAT ta buɗe ba.Ran Sarauniya yakai ƙololuwa wajan ɓaci dan haka ta taka da kanta suka mara mata baya domin kiran MUSLIMAT ɗin da kanta.
Fitarta keda wuya ZULMAT ta tsige ƙarin ruwan dake maƙale ahannunta tare da zabura taduro daga gadon ta durƙusa tasa gwiwoyinta aƙsa tare da haɗa hannunta alamar roƙo idanunta nacigaba da zub da hawaye tace da muslim.....

"MOSLIM"

A mamakance MUSLIM ya juyo ya kalleta tare ɗan rage tsayinsa akanta ya tsuguna saitin inda take suna fuskantar juna jin ayadda ta ambaci sunansa,kallon juna sukeyi kafin daga bisani tasake cewa.....

"Shin dama haka so yake baya yiwa mai yinsa adalci ko kuma mune bama yiwa masoyanmu adalci?nasan mahaifiyarka mai adalci ce,ina kyautata zaton zatace kazaɓane tsakanin NI ko MUSLIMAT,ina haɗaka da YUSH-SHIBAYIL AMNAS....."

Bata ƙarasaba kuma saitayi saurin toshe bakinta saboda tuna abinda takeson cewa dn haka da saurinta tagoge ruwan hawayen daya cikamata fuska tace....

"MOSLIM!! Kayi haƙuri nasaba da faɗin hakanne domin sunan Ubangijinmune amma ka gafarceni bazan sake faɗinsaba matuƙar ina cikin wannan gari naku,kasani SOn da nake maka zai iya sakani komai kuma komai kyansa ko muninsa gareni ko ga wani na.MOSLIM!!Ina gamaka da girman abin bautarku kasoni koda dai-dai da zarra ni hakanma ya ishe ni,idan kuma bazaka soni ba kasanar dani domin na kashe kaina dan hakan shizai zama mafita agareni"

Ta k'arasa faɗa tanamai toshe bakinta saboda yadda wani kuka mai ƙarfin gaske ya ƙwacemata ba tare data shirya masa ba.
Tunda MUSLIM ya sauke idansa akanta har kawo yanzu bai saukesuba saboda yadda yakejin zuciyarsa na bugawa da ƙarfin gaske yanajin babu daɗi kukan da takeyi agabansa tana neman temakonsa,sunkuyar da kansa yayi tare da ɗagowa ya kalleta yace da ita.....

"Shin zaki iya sanar dani wane irin SO kikeyimin?"

"Ina yima SO irin na matar da bata taɓa haihuwaba tsawon shekaru,kwatsam seta samu ciki ta haifi yaro ko yarinya,sannan tinda ta haifi wannan cikin bata sake samun wani ba dan haka ta ɗauki son duniya ta ɗorashi akan wannan abinda ta haifa,to inamai tabbatar maka da inamaka SO wanda yafi wannan domin ni nawa son da nakema bansan silar farawarshiba kuma bansan danme nake sonka ba nidai kawai na tsinci kaina asoyayyarka kuma zan iya komai saboda soyayyarkaa"

Jinjina kai yasakeyi tare da kallon cikin k'wayar idanunta sannan yasake cewa......

"Kince zaki iya komai saboda SOna to idan nace ki kashe kanki zaki iya?"

Cikin hanzari yaga ta mik'e da sauri tanufi can lokon gadon data kwanta ta tsugunna tare dasaka hannu cikin wani k'aton kwando wanda aka shaƙeshi da kayan marmari ta ɗauko wata sharɓeɓiyar wuk'a da aka saka acikin kwandon tare da zare murfinta ta saita maƙogaronta da ita.........

"Koba komai zanyi alfahari da wannan rana da wannan lokaci dazan kashe kaina kuma marubuta zasu dinga rubuta labarin SOYAYYATA domin tasha ban-ban data sauran masoya,sai dai SOYAYYATA tasamu naƙasu daga ɓangaren masoyina,kuma naso ace kaine zaka kasheni da hannunka yadda bazanji zafin yankan dazakai yayin kasheni ba sai dai naji daɗi kasancewar soyayyace tasa zaka kasheni ba ƙiyayya ba,ina sonka!ina sonka!!ina sonka mosleem!!!"

Tana faɗin haka ta sake saita wuƙar tare da rintse idanunta,zata burmata kenan Muslim yabuɗe iya k'ololuwar muryarsa tare da sufa ya dira kusa da ita ganin tana daf da aikata abinda ta faɗa ya hankaɗata kan gadon dake kusa da ita.........


⚔️🌍⚔️🌍⚔️


SARKI KAMALUD-DEEN yana zaune cikin shigarsa ta alfarma anata fadanci kwatsam sarkin zance yace.....

"Allah ya temake ka! Tun ɗazu wasu bafulatanai guda biyu suka iso kusa da wannan fada kuma da alama kai suke son gani"

"Tom madalla!Sarkin zance meyasa baka sanar mana tunda wuri ba saida suka gaji da jiranmu?"

"Allah yaja zamaninka!Ayimin afuwa ajizanci ne irin naɗan adam na manta ne ranka shi daɗe"

Nan take sarkin yayi umarni da ashigo dasu fada domin aji meke tafe dasu.Hakan kuwa akayi bayan sun kwashi gaisuwa sunzauna ne aka Umarci ɗaya daga cikin manyan garin wanda asalinsa bafulatani ne aka umarceshi daya tambayesu meke tafe dasu..........








🙌🏻🙌🏻🙌🏻🙌🏻anzo wajanfa mutane na🤗🤗ko yaya za'a ƙarke da ZULMAT da MUSLMAT da MUSLIM⁉️



Muna daf da tafiya ⚔️WATA DUNIYA⚔️🌍dan haka kowa yai shirin tafiya nidai nagama nawa.Dan Allah kudinga min uzuri sbd yanayin posting ɗin nawa👏🏻.


👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻

DAN ALLAH INA NEMAN ALFARMARKU"ALLAH KABAWA KHADEEJAH LAFIYA MAI ƊOREWA DAN ƘARFIN IKONKA"ABINDA ZAKUCE KENAN DAN ALLAH.NAGODE🥰😍


MORE COMMENT MORE TYPING.



DOMIN GYARA,SHARHI KO BADA SHAWARA ATUNTUƁENI TA WANNAN LAYIN👇🏻
07047530638.




ƳAR GATAN MAMA✍🏻.
⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️



⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️

LABARI/RUBUTAWA
KHADIJA S.SAMINU
(ƳAR GATAN MAMA)



Marubuciyar......


A WANI GIDA
RAYUWAR MU!
MAGANIN KAR AYI!
nd now......


⚔️WATA DUNIYA⚔️


⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️






*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*



NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.ƘURAINABU IDRIS YARO YAHYA ALLAH YAJA DA RAI YAƳARA LAFIYA AMEEN.




⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️
SHAFI NA 31&32.
⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️


Bayan ya tambayesu ne nafarkon ya matso inda aka umarceshi tare da fuskantar sarki yanamai sunkui da kansa yace.....


"Allah yuttin zamanma ardujo min emijodi eh wuttudo gelle ma amma emi lei undalma ehlamuma,Allah rene amma emi shoggumarle bel eh na i eh bali miwadi shoggu eh goddo hadiyan shede an moyi mocyamide mohokkitata yande hanjun wadi bimi dun tetanayan halal an"

Bayan ya gama bayaninsa ne aka buƙaci ɗayan shima yafaɗi ƙarar daya kawo dan haka nan da nan ya matso tare da cewa.....

"Allah yuttin zamanma ardujo emider lamorde de e de fulbe riskube mihokki goddo cymade amma bo mosalake mohokkitatayande mo cyamide"

Bayan sungama bayaninsune sarki yabuƴaci wannan bafulatanin dakejin HAUSA daya fassara musu domin su san kalar hukuncin dazasu yankewa maganar tasu.

Jin haka shikuma ya gyara zamansa cikin ladabi yace.....

"Allah ya temakeka! Na farko yace 'Allah yaja zamaninka!Ni na kasance ina agefen wannan gari naka amma ina ƙarƴashin kulawar wannan masaurata taka.Allah yaja zamaninka! Na kasance ina cinikayyar dabbobi da shanu,dan haka munyi ciniki da wani amma ya hanani kuɗina sannan yace ma yacinye bazai biyaba shiyasa nakeson aƙwatar min haƙƙina'.Shikuma na biyun yace'Allah yaja zamaninka!Ina daga cikin bafulatanan wannan masaurata masu arziƙin shanu,nabawa wani mutumi rance na kuɗaɗe masu yawa amma ya hanani ya cinyemin kuɗina'.Wannan shi ne abinda suka faɗa Allah yaja zamaninka,amma ni aganina duk kusan abu ɗayane yake damunsu"

Nan sarki yayi gyaran murya tare da faɗin.....

"Amm! Ka tambayar mana su shin suna da shaida?"

Cikin bin umarni ya kalli na farkon tare da cemasa......

"A wodi shaidujoba?"

Nan bafulatanin ya kalleshi tare da sunkuyar dakai yace......Bashi da shaida.

Sarki da kansa ya gyara zama tukunna yace dasu.....

Ayanzu baku da shaida ko hujjar da zatasa akama waɗanda suka riƴemuku kuɗi saboda faɗin Allah acikin alƙur'ani maigirma yana cewa' Ya ku waɗanda suka bada gaskiya! idan kukayi mu'amala ta bashi (ko sautu ko rance)izuwa ajali abin ambato,to,ku rubuta shi(don ujiyewa ga jayayya)marubuci yayi adalci(acikin rubutun ,kada yayi daɗi acikin dukiya da ajali ko ragi)kada marubuci yaƴi rubuta irin yadda Allah ya sanar da shi ya rubuta,(don abinda aka rubuta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login