Showing 6001 words to 9000 words out of 33915 words
Chapter 3 - WATA DUNIYA COMPELET HAUSA NOVELZ BY YAR GATAN MAMA.txt
ɗaya ga watan dazai kama"
Gyara zama ZULMAT tayi tukunna tayi gyaran murya tasake duban babannata tace.....
"Yakai babana! Inaso kasanar dani koda kaɗan daga cikin haɗarin dake cikin wannan kogo da za'a ɗauki TAKOBIn acikinsa"
"Bamai faɗuwa bane!! Nace miki bamai faɗuwa bane haɗarin dake cikin wannan kogon,a'iya binciken dana ɗauki shekaru inayi naga tarin musibu kala daban-daban acikinsa wanda tsafin matsafin basa iyawa dashi,kuma bincike ya tabbatar da MUSULMAI ne zasu ɗauketa,sannan wajan ɗaukarta dolene seka ambaci sunan abin bautarsu tukunna zaka ɗauka"
"Cikin zaƙuwa da son jin wannan sirri ya babana! Ina mai buk'atar ƙarin haske awannan bayanin naka,shin koda ba musulmi ba idan yakira sunan abin bautar musulmai zai iya ɗaukar wannan takobin?"
"Hhhhh! Yaro yarone,haka batun yake yake kyakkyawar ɗiyata mai fikira da kaifin basira,ya tabbata koda ba musulmi bane mutum indai har ya isa inda wannan TAKOBI take sannan yakira sunan abin bautar musulmi da girmamawa to babu makawa zai ɗauketa,to amma abinda na fahimta anan yake ƴata! Na fuskanci waɗanda suka saka wannan sharaɗin sun sakashi ne saboda sui sanadin karya alk'awarin damukayi tsakaninmu da iyayenmu na cewa bazamu bar addininsu ba har ƙarshen rayuwar mu,tinda inhar zamuje ɗaukar abu mu nemi temakon abin bautarsu kenan watarana ma zamu yadda dashi kenan?"
ZULMAT tayi murmushi mai sauti sannan tace....
"Inamai farin cikin sanar dakai cewa:Zanyi iya bakin k'oƙarina akan naga nakawoma wannan TAKOBI kota halin ƙaƙa,sannan inason ka kwantar da hankalinka ka kauda kai daga dukkan abinda zaka ga nayi kozakaji nace,komai kaga nayi nayishine domin kai,sannan inaso kasani bazasu taɓa yarda dani ba har se na nunamusu zan iya komai akansu sannan na nuna musu soyayya hakanne zaisa su yadda dani,zanyi duk me yuwuwa domin cikar burinka yakai babana"
Tagama maganar tare da ajje hannunta akan wani tudu da suke zaune agabansa.Sarki zalimuz-zaman shima yaɗora hannunsa akan nata tare da jinjina mata kai alamar yayi mata alk'awari.
Murmushi tayimai sannan tadoshi bangon ɗakin batare da ɓata lokaci ba se buɗe ido tayi awannan ɗakin da akabata amatsayin masaukinta.Bata tsaya yin komai ba tahaye makeken gadon dake ɗakin tare da kwantawa tana maida numfashi sannan ta tsunduma duniyar tinani ahaka bacci yai gaba da ita.
Koda gari ya waye kowa yana ta sabgarsa inda Sarauniya tasa aka kaiwa ZULMAT kayan ci dana sha kala daban-daban,bayan taci tasha ne tagama shiryawa sannan tafito domin zuwa wajan sarauniyar,lokacin data iso inda sarauniya take MUSLIM yana gefenta suna gaisawa inda MUSLIMAT ke zaune itama tana jawa sarauniya yatsun ƙafarta.
"Ina fatan kintashi lafiya ya shugabata"
Abinda ZULMAT tafaɗa kenan sanda ta ida ƙarasowa inda suke gaba ɗayansu.
Faɗaɗa murmushinta sarauniya tayi tare d agyarawa daga kishingiɗen da take sannan ta miƙawa ZULMAT hannunta na dama tace.....
"Rabon ubangiji ya tabbata agareki ya jarumar baƙuwata!"
Bamusu tabata hannunta tare dayimata murmushi sedai bata bata amsaba.SARAUNIYA SINIYYA taji daɗin yadda taga ZULMAT dan haka tanuna mata kusa da ita tare da mata alamun ta zauna.
Bata musaba ta zauna agefen sarauniyar sannan tadubi MUSLIM tana wani ƙayataccen murmushi mai kwantar da hankalin masoya tace.......
"Nayi farin cikin ganinka lafiya cikin kyakkyawar kama yakai wannan jarumi ma'abocin kyakkyawar mu'amala"
Saida MUSLIM yasaci kallon MUSLIMAT yaga yadda tahaɗe rai sannan ya saisaita fuskarsa ya kalli ZULMAT yace.....
"Lafiya nake,yaya kwanan baƙunta"
"Aini banyi zama kamar yadda baƙi suke zama ba,domin baƙi suna zamane aɗarare basa sakewa,basa samun sakin fuska daga iyayen gidansu,ana ajjesu awajen da ba'a shigarsa harsai irinsu sunzo ake karkaɗe ƙurar cikinsa abasu su zauna,amma ni anbani muhalli wanda yake abin ƙawatawa da birgewa,nikam wannan wane irin karamci ne?"
MUSLIMAT ce tayi murmushi tare da duban ZULMAT tace.....
"Inamai neman afuwarki bisa rashin fahimtar data shiga tsakaninmu jiya,sannan inamai farin cikin sanar dake cewa: Aishi baƙo mutumne wanda ya kamata akarramashi abashi kulawa da duk wani abin buk'ata harsai yaji inama karya bar wannan guri daya zauna"
Murmushi zulmat tayi mata sannan tace....
"Hmm! Wato kudai nafuskanci har rige-rigen aikata alkairi kukeyi ko?
naga kuduka kuna ƙoƙarin kyautatamin kuma kun ciyar dani daga abubuwa masu daɗi"
MUSLIMAT ce tayi murmushi sannan tace....
"Bana sanar dake wani abuba yake jarumar baƙuwarmu mai sanyin halaye?"
"Ina sauraronki gwanayen iya zance"
Tabata amsa tana murmushi.
"Allah maɗaukakin sarki yace:"Ba za ku kai ga matakin ƙarshe na aikin alheri ba har sai kun ciyar daga abinda kukeso" (ali'imran),sannan yasake cewa:"Yaku waɗanda kuka bada gaskiya ku ciyar daga nagartattun abubuwan da kuka samu kuma daga abinda muka fitar muku daga cikin ƙasa,kada ku ɗauki abinda bashi da amfani daga dukiyoyinku(kuyi sadaƙa dashi)"(baƙara ),wato dai ana nufin kada kayi sadaƙa da abinda yake bashi da kyau sai dai kayi da kyakkyawa.Faɗin ubangiji kenan to ta yaya kike tinanin zamu sauke ki awaje mara kyau sannan mubaki abu mara kyau? dole indai muna aiki da abinda muka karanta daga abinda Allah ya saukar mana(ALƘUR'ANI)mu baki abinda mukeso domin kasancewa munji daga majiya mai k'arfi cewa'imanin ɗayanku ba zai cikaba har sai yasowa ɗan uwansa abinda zaisowa kansa' Ina fatan kingane"
MUSLIM ne yatari numfashin MUSLIMAT tare da cewa"Haka kuma Allah maɗaukakin sarki yace:"Wanda duk ya aikata wani aiki na alheri dai dai da ƙwayar zarra zai ganshi" (zilzilah)haka kuma yasake cewa:"Wanda duk yayi aiki na gari don kansa"(ALJASIYAH).
Kinga kuwa wannan kyautatawa da mukai miki kanmu muka yiwa domin ya tabbata duk wanda yayi wani aiki nagari kansa yayiwa,hakanan kuma hanyoyin aikin alheri suna da yawa"
GIMBIYA ZULMAT ta kallesu ɗaya bayan ɗaya sannan tayi murmushi ta dubi SARAUNIYA SINIYYA tace......
"Kinyi dace da ƴaƴa nagari masu yiwa baƙi magana mai daɗi,sedai ke yau bakice dani komai ba".
Kallonta sarauniya tayi sannan tagyara zamanta tace.......
⚔️🌍⚔️🌍⚔️🌍
Domin gyara yabo sharhi ko bada shawara atuntuɓeni ta wannan layin👇🏻
07047530638.
'YAR GATAN MAMA✍🏻.
⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️
⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️
LABARI/RUBUTAWA
KHADIJA S.SAMINU
(ƳAR GATAN MAMA)
Marubuciyar......
A WANI GIDA
RAYUWAR MU!
MAGANIN KAR AYI!
nd now......
⚔️WATA DUNIYA⚔️
⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA,ALLAH YAK'ARA MIKI LAFIYA DA TSAWON KWANA🥰💞💞.
⚔️🌍⚔️🌍⚔️
SHAFI NA 15&16.
⚔️🌍⚔️🌍⚔️
......Kallonta SARAUNIYA SINIYYA tayi sannan tagyara zama tace....
"Tom ni sedai naimiki cigaban maganar MUSLIMAT idan kinaso,inba hakaba banda abin cewa"
"Kome zaki faɗa inaso ya shugabata! Domin inajin daɗin yadda kika zauna dani haka kike hira dani babu tsangwama babu wani abinƙi sai kyautatawa"
Murmushi sarauniya tayi sannan tace...
"Daga Anas Allah ya yarda da shi ya ce: Abu Talhatu Allah ya yarda dashi ya kasance shine mafi ansar na madina dukiya ta dabino(yawan dukiya)Kuma dukiyar da yafiso daga dukiyoyin nasa itace BAIRAHA'U (wato lambunsa),wanda ya kasance yana kallon masallaci,kuma Manzon Allah (SAW)ya kasance yana shiga lambun yasha daga ruwansa mai daɗi.
Anas yace: Lokacin da wannan aya ta sauka wato"Ba za ku kai ga matakin ƙarshe na kyakykyawan aiki ba sai kun ciyar daga abinda kukeso" Sai Abu TALHA ya tawo wajen Manzon Allah (SAW)yace: Ya rasulillahi Allah ya saukar maka da aya da tace:"Ba za ku kai ƙarshe na aikin alheri ba harsai kun ciyar daga abinda kuke so",Ni kuma daga cikin abinda na mallaka nafi son lambuna mai suna BAIRAHA'U.Saboda haka na sanyashi sadaƙa saboda Allah maɗaukakin sarki inamai ƙaunar ladan abin daga Allah maɗaukaki.Dan haka ka sanyashi inda Allah ya shiryar da kai,sai manzon Allah(SAW)yace:Madalla,wannan dukiya ce mai matuƙar daraja,wannan dukiya ce mai daraja.kuma naji zancenk..."
"Inada tambaya gareki yake wannan sarauniya mai girma da daraja,idan na fahimta mutumin dukiyar tasa ya ɗauka ya bayar saboda jin abinda abin bautarku yace? hakanne yasa kuma kuke kyauta da abubuwan da kukeso? to kuma lambun nasa ya aka rabashi ga al'umma bayan ya bayar da ita?"
SARAUNIYA SINIYYA tayi ƙayataccen murmushi zuciyarta tanajin daɗin yadda GIMBIYA ZULMAT tasaki jiki tanajin zantukansu kuma alamu sun nuna zata iya musulunta tinda har take sauraron abinda Allah ya saukar musu.......
Saida tagama tinaninta tana sakin murmushi ajejjere sannan ta dubi gimbiya ZULMAT tace....
"Kamar yadda kikaji ya bayar da BAIRAHA'U(wato lambunsa)saboda jin abinda Allah maɗaukakin sarki yace,to amma bayan Annabi (SAW)yagama yabamasa sai yace dashi:"Kuma naji abinda kace,amma ina ganin yafi kyau ka sanyashi ga makusantanka" Sai yace"Haka zanyi ya Rasulillahi" Sai Abu TALHATU ya raba wannan dukiya tsakanin ƴan uwansa da ƴaƴan baffansa.(Bukhari da muslim ne suka ruwaifo shi).
Kamar dai yadda kika gani muna koyine da kyawawan ayyuka kuma muna girmama baƙo.
Baga al'umma aka fitar dashi aka raba ba,an rabashine ga makusantansa domin ya tabbata cewa karka fitar da abinda ka mallaka har sai kafara bawa makusantanka,idan kabasu ne sun wadata,saika bayar ga jama'a domin suma su samu"
GIMBIYA ZULMAT ta kishingiɗa gefen MUSLIM sannan tayi murmushi tace.....
"Lallai bazan bar wannan gida mai tarin karamci ba harsai bayan raina,domin kallon wannan ɗan naki MUSLIM kaɗai yana sanyani nishaɗi,gashi kema kina yimin zantuka wanda suke sanyawa naji farin ciki sai dai ina tsoron abu guda"
MUSLIMAT tai karaf tatari numfashin ZULMAT tare da faɗin....
"Ina fatan dai bason MUSLIM ne ya kamaki ba? Domin kuwa tun muna ƙanana akabashi ni nice wadda zai aura idan muna da numfashi,kuma wane abune wanda kike tsoro?"
Wani matsiyacin murmushi ZULMAT ta saki tare da busar da iska ta bakinta ta lumshe dara-daran idanunta sannan ta buɗesu fes akan MUSLIMAT takashe mata ɗaya sannan tace.....
"Hhhh! Banda abinki wace macece zatayi tozali da kyakkyawan namiji kamar MUSLIM bataji tana sha'awar ya kasance abokin rayuwarta ba? Hakan yasa tun lokacin da idona ya sark'e da nasa naji inason nasake ganinsa,shiyasa da mahaifina ZALIMUZ-ZAMAN yayi umarni da akasheshi ni kuma na tseratar dashi saboda inaso nadinga ciyar da idanuwana duk lokacin da suka buk'aci hakan, abu guda da nake tsoro yakasu gida biyu:gida na farko shi ne BABANA ZALIMUZ-ZAMAN,gida na biyu kuma shi ne abinda zai rabani da MUSLIM annurin rai..."
Wani tari ne bazato yasark'e MUSLIMAT wanda seda MUSLIM yamiƙo mata gorar ruwa tasha inda ruwan nazuwa maƙogaronta taji wani ɗaci mara misaltuwa wanda hakan yai sanadiyar furzar da ruwan ya sauka akan fuskar ZULMAT.......
⚔️🌍⚔️🌍⚔️
Duk wani shiri da NUJBEER ƊAN NAJABURU zaiyi na tafiya 🌍WATA DUNIYA🌍yagamashi jira yake kawai sabon wata yakama domin yau saura kwana tara kenan alissafinsa,kullum yakan shiga wajan sarki KAMALUD-DEEN domin yaji ina suka kwana azancen tafiyar.....
Wannan kenan.
⚔️🌍⚔️🌍⚔️
Koda gimbiya ZULMAT tafita daga turakar ZALIMUZ-ZAMAN zama yayi dirshan adandaryar ƙasa sannan yaɗaga kansa sama yasa hannunsa ɗaya aƙasa tare da dukan wajan.Dukan wajan keda wuya sega ƙasar wajan ta tsage tarabe zuwa gida biyu,batare da ɓata lokaci ba ZALIMUZ-ZAMAN yashige ciki inda ƙasar takoma yadda take tahaɗe tazama guda ɗaya.
Koda yashiga ciki........
⚔️🌍⚔️🌍⚔️
Domin gyara,sharhi ko bada shawara a tuntuɓeni ta wannan layin...👇🏻
07047530638.
MORE COMMENT MORE TYPING.
SANARWA🥳🥳🥳
⚔️WATA DUNIYA⚔️HAR YANZUFA BAMU SHIGA WATA DUNIYAR BA,MUJE ZUWA AMMA SAI KUNYI HAƘURI DANI DAN ALLAH.SANNAN DAN ALLAH INA BUƘATAR ADDU'ARKU GAREKI"ALLAH KA AZURTA BAIWARKA KHADEEJAH DA LAFIYA MADAUWAMIYA KABATA IKON AMFANI DA LAFIYAR DAN ARZIK'IN MASOYINKA"ABINDA ZAKUCE KENAN,DAN GIRMAN ALLAH.NAGODE😍🥰💞💞.
ƳAR GATAN MAMA✍🏻.
NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA,ALLAH YASHIGA LAMURANKI BABATA🥳🥳.
⚔️🌍⚔️🌍⚔️
SHAFI NA 17&18.
⚔️🌍⚔️🌍⚔️
Koda yashiga ciki bai sauka ko'inaba sai kan wani mulmulallen hamshaƙin wani dutse mai azabar kyau da ɗaukar ido wanda idan kayi tozali dashi saika ɗan kanne idonka saboda yadda yake barazanar kashe idanun,yana da girman gaske wanda girmansa zaikai girman ɗaki guda,gefen dutsen wasu gumaka ne masu matuƙar muni da baƙi na tashin hankali.Zamansa kan dutsen keda wuya wajan yayi wata girgiza tare da juyawa sama ya koma ƙasa,lokaci guda wata guguwa tashigo wajan mai azabar k'arfi,manya-manyan halittun aljanu ne suka fara tittiɓowa takowa ce hanya dake wajan.
"Sai kai sarki mai nisan zamani,ka gagara ka cika ka bunƙasa ka take duk wanda ba masoyinka ba,shin wace buƙata ce dakai haka daka buk'ci ganinmu da gaggawa? Sauraronka muke yakai wannan sarki mamallakin aljannu da bokayen dake faɗin wannan duniya!!"
Wani daga cikin aljanun yafaɗa da muryarsa mai rikitarwa da sanya tsoro azuciyar mutane.ZALIMUZ-ZAMAN ya kece da wata mahaukaciyar dariya wanda saida yaɗauki daƙik'a hamsin yanayi tukunna yagimtse bakinsa ya murtuke fuskarsa kamar wanda yaga mala'ikan mutuwa yace.........
"Hhhh! Ina Alfahari da ƙarfin ikon danake dashi dakuma ɗiyata ZULMAT wadda zuciyarta take ataurare,tana da zafi da kuma tsauri akan ƙudurinta.A....Awannan lokaci inason sanar daku cewa ƴata zulmat ta tafi garin DEENUL-ISLAM domin haɗa kai da maƙiyanmu maƙiya addininmu domin ta shiga jikinsu ta ɗaukomin ⚔️TAKOBIN WATA DUNIYA⚔️wato takobin ɗaukaka,sanin kanku ne abinciken da manyan matsafan wannan duniya tamu sukayi sungano cewa farkon wata makullin ƙofar wata duniya ke buɗewa kuma awannan lokacin ne mai buƙatar wani abu daga cikinta yake shiga domin shigar ƙudurinsa,kuma sanin kankune kwana goma sha biyar za'ayi acikin duniyar afito,domin makullin ƙofar zai rufene idan wata yara ba! Shin wane taimako zakubawa zulmat domin tazama itace wadda zata ɗauki wannan takobin?"
Babban cikinsu wanda ya bayyana amatsayin wani gwoggwon biri baƙiƙk'irin mai azababben muni da ban ƙyanƙyami ne ya buɗe mummunan bakinsa tare da gyatsine fuskarsa taƙara muni ninki huɗun wanda yake dashi da ya kece da wata sheɗaniyar dariya wadda seda ilahirin wajan ya haɗe jikinsa yayi baƙiƙk'irin tare da sanyawa sauran aljanun dake wajan suka saki wani azababben ihu tare da haɗa baki wajan faɗin.....
"DUJAALA!!!"
ALjanin da aka kira da DUJAALA! Ya tsagaita da dariyar da yakeyi sannan ya dubi ZALIMUZ-ZAMAN da razananniyar murya yace........
"Bamusan lokacin da kazama me gajeren tinani kamar sauran mutane ba,sanin kanka ne kai mutum ne amma ba kamar sauran mutane ba,ya...ya za'ai kabar yarinyarka ta shiga cikin mutanen da ba addininmu ɗaya da ita ba?Bayan kasan mutanen nan suna ɗauke da wani shu'umin tsafi wanda mu kafatanin kafirai bamu dashi yanda idan ɗaya daga cikinmu ya shiga cikinsu sai sunyimai abinda mawuyacine ya kuɓuta se sun jashi ya karya alƙawarin dake tsaninsa da iyaye da kakanni.....
⚔️🌍⚔️🌍⚔️
Wani tari ne bazato ya sarƙe MUSLIMAT wanda seda MUSLIM yamiƙo mata gorar ruwa tasha inda ruwan na zuwa maƙogaronta taji wani ɗaci mara misaltuwa wanda hakan yai sanadiyar furzar da ruwan,koda ruwan yafito bai sauka ko'inaba sai fuskar gimbiya ZULMAT.
A mamakance ZULMAT take dubanta sanda tafurzo mata ruwan domin ita tahaƙik'ance azuciyarta da gangan MUSLIMAT tazuba mata afuska babu wata ƙwarewa da tayi,afusace ta kalleta da niyar nuna mata kuskurenta na ɓatamata fuska ta tsinkayi muryar SARAUNIYYA SINIYYA tana nacewa......
"Nikam kuyimin hak'uri zanshiga daga ciki domin gabatar da sallar walha"
GIMBIYA ZULMAT tadawo da hankalinta ga sarauniya tace....
"Nasha ziyartar garuruwan musulmai kuma naga suna sallali biyar ne arana daga wannan lokaci zuwa wannan lokaci amma banga sunayi a irin wannan lokacin da kikace zakiyiba!Shin ko su sunrage watane daga wanda aka saukar muku"
Murmushi sarauniya tayi sannan ta numfasa tabata amsa kamar haka.....
"Hmm! Hakane zancenki kyakkyawar bak'uwata,haƙiƙa ubangiji mamallakin kowa da komai ya saukarmana da salloli guda biyar ne ta hanyar Annabinsa,kuma wannan guda biyar ɗin sune sallolin farillah wanda suke wajibi akan dukkan wani musulmi saidai munayin nafilfili alokuta mabanbanta domin cike inda baicikaba afarillarmu kasancewar ba wanda yakeyin dai-dai sai Annabin Allah maɗaukakin sarki.Yazo daga Abu Zarri Allah ya yarda dashi cewa Manzon Allah (SAW)Yace:Idan kuka wayi gari kowace gaɓa daga ɗayanku akwai sadaƙa daga gareta.Domin kowane tasbihi sadaƙa ne,kowace hamdala sadaƙa ce,kowace hailala sadaƙa ce,kowace faɗar ALLAHU AKHBAR sadaƙa ce,yin umarni da kyakkyawan aiki sadak'a ne,hani ga mummunan aiki sadaƙa ne.Amma yin raka'a biyu da walha zai iya tsayawa amaimakon wannan.(Muslim ne ya ruwaitoshi).
To kinji yadda zancen yake hakan yasa nakeso nayi raka'a biyu yanzu domin nasamu wannan ladan"
"Yayi kyau,nikam me yasa idan zakui zancen kuke tsarashi fiye da yadda mukeyin namu"
"Saboda mu mun kasance muna faɗine daga abinda Allah maɗaukakin sarki yafaɗa,shi kuma zancen Ubangiji mai girma da buwaya atsare yake babu gyara acikinshi".
GIMBIYA ZULMAT ta numfasa tare da gyara zamanta tukunna tace....
"Tom shiga kiyi sallar inyaso nima zanshiga daga ciki kafin kidawo"
Shiga SARAUNIYYA SINIYYA tayi inda ZULMAT ta tashi tanufi masaukinta dake daura da ɗakin sarauniyar tabar MUSLIM da MUSLIMAT azaune.
"Me yasa kake sakarwa wannan kafirar fuska hartake cewa tana sonka baka ɗauki wani mataki ba? Shin ko kaima ka kamu da sontane bamu sani ba? Meyasa! Meyasa!!"
MUSLIMAT ta faɗa cikin mabayyanin ɓacin rai jikinta har rawa yake inda idanunta suka kaɗa sukayi jawur se wura hanci takeyi.
"Allah yaƙara miki lafiya jarumar masoyiyata! Banda abinki me ZULMAT take dashi wanda baki dashi da zaisa na sota? Shin kodai kinfara tantama game da sonda nake miki?amatsayinki na macen da tasan kanta bazaki iya kishi da ZULMAT bane?"
MUSLIM ya bata amsa fuskarsa ɗauke da murmushi tare da kashe mata ido ɗaya.Kallonsa tayi tare da wurga masa wata narkekiyar harara wadda saida ya tintsire da dariya sannan tace....
"Dole ka kalleni kayi dariya tinda kana shirin cin amanata saboda wata ƙasurgumar kafira wadda bata da makoma,da kake cewa meta fini aikai bakaga hakanba tinda ina kallon yadda kake yimata wani kallon ɗaukar hankali,ada bana kokwanton sonda kakeyimin amma yanzu inaji ajikina kashirya yaudarata tinda idonka yahau kan farar mace maraba da cuta,hmm! Gaka gata nan kaje nabarka da ita jahilcima ya isheka!!"
MUSLIMAT ta faɗa cikin ƙololuwar ɓacin rai ta tashi tabarshi awajan tana sakin wani kuka mai cin rai.Koda tafice ta barshi awajan dafe kai yayi tare da tashi shima yanufi ɓangarensa.
Koda ZULMAT tashiga sashenta bangon ɗakin ta shige inda ta bayyana aturakar mahaifinta sarki ZALIMUZ-ZAMAN........
👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻
DAN ALLAH INA ROƘON ALFARMA GAREKI IDAN KINGA SAƘONA"ALLAH KABAWA KHADEEJAH CIKAKKIYAR LAFIYA MAI ƊOREWA KABATA IKON AMFANI DA LAFIYAR DAN ARZIƘIN ANNABINKA"ABINDA ZAKUCE KENAN DAN GIRMAN ALLAH NAGODE🤝🏻🥰💞💞.
MORE COMMENT MORW TYPING.
DOMIN GYARA,SHARHI KO BADA SHAWARA ATUNTUƁENI TA WANNAN LAYIN....👇🏻
07047530638.
ƳAR GATAN MAMA✍🏻.
NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN BAKI ƊAYANSHI GA MAHAIFIYATA HJY.K'URAINABU IDRIS YARO YAHYA,ALLAH YAƘARA MIKI LAFIYA DA TSAWON KWANA MAI AMFANI AMEEN.MUCH LUV🥰🥰.
⚔️🌍⚔️🌍⚔️
SHAFI NA 19&20.
⚔️🌍⚔️🌍⚔️
🥰🥰GUDALIYAR BABANTA GUDALIYAR YARGATA WANNAN SHAFIN NAKI NE KIYI YADDA KIKESO DASHI NAGODE.SON SO FISABILILLAHI🥰🥰💞💞.
⚔️🌍⚔️🌍⚔️
Koda ZULMAT tashiga sashenta bangon ɗakin tashige inda ta bayyana turakar mahaifinta sarki ZALIMUZ-ZAMAN,koda ta ganta aciki saita shiga duban mahaifinnata bata ganshiba,ko'ina na ɓangaren ta duba amma babushi babu dalilinsa.
Koda taga zata wahala seta nufi inda kayayyakin tsaface-tsafacensa suke domin ta duba taga inda yashiga.Dube-duben ƙasa ta fara inda taga zata ɓata lokacinta dan haka kawai ta kunna wutar tsafinsa tare da zaman dirshan aƙasa tana ɗiban wani ruwa me kalar shuɗi tana watsawa acikin wutar,watsawa takeyi inda idonta yake arufe bakinta yana karanto wasu ɗalatsiman tsafi masu wahalar riƙewa acikin abinda take cewa baka fahimtar komai se inda take faɗin"YUSH-SHIBAYIL AMNASH,YUSH-SHIBAYIL AMNASH"Kalmar da tafi maimaitawa kenan inda cikin daƙik'a ɗari uku da saba'in sega hoton ZALIMUZ-ZAMAN ya bayyana shida gungun Aljanun da suke tare aƙarƙashin ƙasar ɗakinnasa.Sake kallon ALJANI DUUJALA tayi tare da zare ido jin kalaman da yake faɗawa mahaifinta akan shigarta garin musulmai yanaso ya wargaza mata shirinta gaba ɗaya.Sake ɗiban ruwannan tayi tare da watsawa akan