Showing 135001 words to 138000 words out of 146738 words

Chapter 46 - JALILAH HAUSA NOVELS BY AYUSHER MUHD.txt

23 Nov 2025

5779

banaji ko mai nai ya kamata yaran nan yaci mutuncina, sai dai bayansa zanyi nima nasan ban kyauta ba dana nausheshi, dan Allag Jalila ki bashi hakuri kinji? Ni mahaifinkine ya kamata yasan darajata kinji?"


Bakin Hassan ta tuno a ranar dama jikinta ya bata Dady ne sai dai batasan zargi shiyasa.

Dady zaiyi magana tace "kaje gaisuwar Inna?"

Yace "wani gaisuwa bayan na rabu da matar sannan ko kin manta ne? Yanzu nake miki zancen komo da mamanki."

Jalila cikin takaici tace "Dan Allah dady kai wani irin mutum ne? Wanda zuciyarsa da kansa kawai ya sani? Taya mutum magidanci mai iyalai kamarka za'ace bakasan komai ba sai kanka? Baka tausayin mu? Baka tunanin yanda muke kallanka?
In har ni da Goggo bazaka faranta mana ba taya za'ace wadanda ka moresu a iya tsawon rayuwarkasuma bazakaji tausayinsu ka faranta musu ba? Wannan wani irin tsabar san kai ne?
Sannan maganar Goggo ma ka dainata dan alama ce ta kaidinba mutumin da zai iya rike wani bane, kanka kawai zaka iya rikewa, sai ka cigaba da zama kai kadai har karshen rayuwarka dauke da alhakin 'ya'yanka wadanda Allah ya daura maka hakkinsu, sannan magana ta karshe, Karkayi tunanin Goggo har yanzu a wacce ka sani ne, yanzu tanada gatan da ya wuce tunaninka, dan tanada gidan zama sannan bata rasa komai na duniya ba, insha Allahu kuma Allah zai bata wani mijin ta aura, hakan yasa dama nake neman taimako a gurinka akan in da auranka a kanta ka taimaka ka sauwake mata, ko dan........."

"Jalila ni Abubakar kike fadawa haka? Har yaushe aka haifeki da zaki nemi yimin wa'azi?"

Jalila ta maida numfashi tace "ba wa'azi nake ma ba rokonka nake."

Roko? A banza? Inhar kinasan na saki mahaifiyarki sai kin sa mijinki ya barmin aikina ya kuma barmin company din dana sha wahala gun kula dashi."


Mamaki ya kara kama Jalila idanunta suka ciciko cikin takaici tace "Dady yaushe ka zama haka? Nasan dama can kanada san kanka sai dai bansan abin naka yakai haka ba? Dady wace irin rayuwa ka daura kanka a ciki?"

Dady yai shiru, Jalila tana kuka tace "ka manta wahalar dakaba baiwar Allahn nan? Kasa ta rabu da iyayenta, ta rabu da 'yan uwanta, sannan kai baka bata farin ciki ba sai kunzuga mata dakai, yar data haifa baka taba tausaya mata ba, baka taba nuna mata ko kula da ita kamar yanda Uba ya kamata ya kula da dansa ba, dan Allah dady a tsawon rayuwarka mai ka taba yima baiwar Allahn nan? Wannan wani irin san.........."

Kukan daya kubce mata ne yasa ta kasa magana, dady yai shiru shikansa yanzu jikinsa yayi sanyi dajin kalamanta, da sauri ya kashe wayar sannan ya kwanta rigingine a kan gado.

Hassan na jin kukanta, sai dai baisan me zai ce mata ba, bakin cikin mahaifi ne wanda ba wanda ya isa cire mata shi.

Idanu kawai ya runtse yanajin kukan har ransa, mikewa tai ta bude kofar tana share hawayenta, kusa dashi tazo kawai ta rungumeshi tsam, shafa mata baya ya shiga yi, ta dago ta kalleshi tace "bari nasa abincin a microwave nasan yanzu duk ya huce."

Kai kawai ya daga mata ta dau abincin ta fita dan dama a plate kawai ta zubo mai.


Tana sauka su Ummy na shigowa ta musu sannu da zuwa sannan tai kitchen, Ummy ta kalli Abba tace "Jalila akwai sansanyan hali, yanzu kaga wai matar data mutu fa tayima kuka haka idanta ya canza haka?!

Abba yace "matar data wahalar da ita, gaskiya mu gode Allah."

Nan sukai ciki suna hirarta, komawa tai sama ta taraddashi a zaune yanda tabarshi, kusa dashi taje ta zauna tace "tunanin me kake?"

Yace "ba komai." Amma a ransa yace a satin nan zamu muyi visa.

Haka ta zauna ta bashi abincin har ya koshi, ta bashi ruwa yasha, zata mike ya riko rigarta, kallansa tai yace "wanka nake sanyi."

Cikin mamaki tace "yanzun? Ya zamuyi?"

Yace " ya zakiyi kuwa tunda ke kika jimin ciwo kika karyani, haka nan zaki zo kimin."
Idanunta taxaro tace " ni?"

Yace "sosai."

Haka ta taimaka mai ya cire kaya yasa towel itakam duk kunya ta isheta, sai rokonshi take ya bari yayi wankan gobe amma yaki, haka ta jashi sukai toilet.

Bayata juya saboda kunya shikam ya sa hannu ya jawota cikin bath hub din, kallansa tai da sauri zatai magana ya saki shower gaba daya ta jike, kallansa tai sannan ta kalli hannun daya riketa dashi tace "Yaya?" Ta fada tana kallan hannunsa.

Zata sake magana ya jawota tare da kai bakinshi cikin nata.........



^**********


Ganin magrib ta kawo kai yasa Mumy ta kalli wayarta sannan ta kira Safeena.

Da sauri Safeena ta daga tace "Mumy ina hanyya"

Ahankali Mumy tace "kin dauko takardun?"

Tace "eh Mumy sa'a nai Dady bayanan."

Mumy ta kashe wayar tare da jinginar dakanta jikin kujera.

Matar kawunta ce ta kalleta tace "Fatima ki taimaka kisa abinci abakinki."

Mumy ta girgiza kai alamar a'a sannan tace "karki damu dani, ko nasa abincin ma banaji zan iya taunawa."


#OneLuv💕


🗯 *JALILAH* 🗯


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

*76*


Safeena na shigowa ta shige daki, Mumy ta mike ta bita.

Hijab dinta ta cire sannan ta mikama Mumy katuwar enveloped din dake boye a hijab dinta, Mumy ta amsa sannan ta bude, kamar yanda Inna ta fada takardar gida ne da kuma fili, sai kuma takardar bankinta wanda ke dauke da kudi da dan dama, sannan sai takardun shares dinta na company dinta.”

Kurama takardun ido tai wasu zafaffan hawaye na zubo mata, kuka ne ya kwace mata tanayi tanA cewa Inna ki yafemin...”

Safeena ce ta rungumeta Itama tana kuka, sun dade a haka kafin Mumy tace “in anyi uku ma sanar ma Sultan abinda ake ciki.”

Safeena tace “ai Mumy inaji ma yasan abinda ke faruwa, nasan dai bai san duka ba amma na tabbatar yasan rabi daga ciki, dan ko tambaya ta dady baiyi ba.”

Mumy tai shiru kafin ta share hawayenta tace “Rayuwa ce, nasan mun cuci su Jalila amma ko da wasa banida hakkin mahainfinku, dda zuciya daya nake zaune dashi....”

Safeena ta share nata kwallar tace “Mumy dan Allah ki daina kuka hakanan, sannan kisa tawakalli a ranki.”

Mumy tai shiru tana kallanta, kafin tace “Safeena ban taba tunanin wannan abin bazai shafeki haka ba, ban taba tunanin kece zaki zama mai lalashina ba.”

Safeena tace “Mumy baki san halin dana shiga ba bayan tafiyata, da yanda gaba daya rayuwata ta nemi hargitsewa a lokaci daya, na tabbatar addu’arki ce ta kareni, tun a lokacin na shiga hankalina ganin irin abubuwan dake neman faruwa dani.”

Mumy ta jawota jikinta tace “Safeena nagode sosai, Allah shine ke shiryar da bawansa na tabbatar da irin tarbiya da nuna komai dole ne ki samu da muka nuna miki shi kikai amfani dashi, da yanzu bansan abinda zai faru ba, Allah mungode ma.”

Haka suka kwana cikin wani irin yanayi da su kadai sukasan irinshi, dan Mumy kam bata ko rintsa ba, dan tana matukar san Abakar, ta kuma yarda dashi dari bisa dari...


***********


Yau kwana goma sha hudu kenan da mutuwar Inna, zuwan Jalila uku gidan gaisuwa, a duk sanda zata je kuma sai Hassan ya hada kayan abinci sun kai, sau biyu sukaje da Goggo dayan kuwa ita kadai taje, wanda shine yau ranar bakwai, su Mumy sun shirya dan yau zasu koma can gidan, dan dama itace tadanyi rashin lafiya shiyasa basu koma da wuri ba, jiya tasa Sultan yaje ya ga gidan shida Driver dinsu wanda sun san yanzu suna tattarawa zasu sallameshi, ga gidan da nisa sosai ga kuma jarabawar Sultan ta matso, jarabawar karshe waec, Mumy tai shiru tana tunani, Jalila ta kalli Sultan tace “yakai minti nawa daga can zuwa makarantar taku?”

Sultan yace “tab gidan fa a can wajen gaba da gida dubu yake, wasu sababbin gidaje agun.”

Cikin mamaki Jalila tace “kai!”

Safeena ta kalleta tace “da nisa sosai ko?”

Jalila tace “nima bansan gun ba nadai taba wucewa sai dai gaskiya da nisa sosai.”

Sultan yai ajiyar zuciya yana cijen lebensa yanda ya saba in ransa ya baci.

Mumy tace “sai dai ka hakura da jarabawar, dan kaga kawunka tafiya zasuyi, dan dama mutuwar goggo ce ta tsayar dasu, ga kuma itama datai rashin lafiya, sannan a yanda suke nuna mana suma yanzu kamar sun gaji da zamanmu ne, kaga ban isa in kara daura musu wani nauyin ba.”


Jalila ta kalli Yasmeen dake jikinta a kishingede sannan ta kalli Mumy, tace “ko zai zauna a gidan Goggo?”

Gaba daya kallanta sukai, Jalila tai murmushi tace “ban tambayeta ba sai dai nasan Goggo bazata taba hanashi ba, mai zai hana ya zauna a can inyaso sai mu nemarmai keken hawa kawai ya dinga zuwa?”

Idanun Mumy ne suka ciciko, tai shiru tana kallan Jalila, Sultan ma kallanta yake kafin yace “Akan me zaki taimakamin Jalila?”

Tace “ban gane ba?”

Muryarsa ta fara rawa yace “kin manta cin kashin da aka miki a gidan mu? Kin manta wahalar da Mumy, Inna, Dady da wannan Safeenar suka miki? Taya zaki........”

Kunnenta ta toshe tace “ya isheni haka nan, oh ni Sultan yaushe ka fara magana haka? Sannan kome ya faru ai dane, sannan ka manta kai wanene a gareni?”

Mumy batasan hawaye sun zubo mata ba sai da Safeena ta kamo hannunta, Mumy ta share kwallarta tace “Jalila nagode, ko ince Mun gode, kin nuna mana yanda ake saka sharri da alkairi, butulci da hallaci, mungode.....”

Jalila tai murmushi tace “bari na kira Goggo na sanar mata inyaso sai mu fara kaishi kafin kuwuce.”

Mumy tace “Jalila dan Allah wata alfarma.”

Kallanta tai tace “tame?”

Mumy tace “ki taimaka kima mahaifinki magana munaso mu kwashi kayan sawar mu.”

Tace “Safeena ta kirashi ta fadamai ko ke mana, ai kayanku ne dole ya baku.”

Mumy tai murmushin takaici tace “tun shekaran jiya muke kiranshi bai dauka ba.”

Jalila ta mike tare da yin sallama saboda muryar Goggo dataji, tace “Goggona!”

Ta fada tare dayin ciki, bayan ta gaisheta ne ta sanar da ita abinda ke faruwa, Goggo ta tausaya musu kafin tace menene a ciki, yazo ya zauna ai duk daya ne.”

Jalila tace “Lanta ga?”

Goggo tace “dama tare muke kwana da ita, shimfida takeyi a kasa, nace ta hau kan gado mu kwanta taki wai ita tafi san kwanciyar kasa, dama dakin a rufe kawai yake.”

Jalila tace “shikenan ma.”
Sun danyi hira kadan kafin suyi sallama, harzata fita daga dakin sai ta kira wayar Dady, yana ganin numberta ne ya dauka da sauri yace “Jalila.”

Tace “Dady kana ina?”

Yace “ba gaisuwa bakomai haba Jalila?”

Ta daure tace “Ina wuni?”

Yace “lafiya ina gida, ya akai?”

Tace “zamuzo dasu Mumy su debi kayansu ne dama shine nake so naji inda kake.”

Yai tsaki yace “sabodasu kika kirani? Wai Jalila baki da wayau ne? Kin manta mai mutanen nan suka miki?”

Tace “sai munzo, kawai ta kashe, tare da zama akan gado tana rike da wayar.”

Mikewa tai sannan tace musu ta fadamai, sannan Goggo ta amince, murna agun Mumy kamar me, Sultan kam shiru kawai yai yana kallanta, duniya kenan.

Text tama Hassan tace “Yayana ka dawo?”

Da yake dama ajiye tayai akan zai leka gun Abba ya dawo, ganin reply tai akan saura 2mins ya iso.

Murmushi tai sannan ta kalli Mumy tace “Mumy nima tafiya zamuyi da Yaya.”

Cikin mamaki Mumy ta kalleta alamar rashin fahimta, Safeena cikin zumudi tace “ina zaku? Umara?”

Jalila tace “a’a zamu tafi Qatar ne munyi visa shekaranjiya amma bata fito ba tukunna.”

Mumy jiki a sanyaye tace “me zakuje yi?”

Tace “karatu zamu.”

Sultan yace “haba? Kai congrats, kun samu admission ne?”

Tace “wlh a’a tukunna, mun dai cike, sai dai dama zamu samu, ko muna can zata fito.”

Safeena tai shiru tana kallanta yanzu fa da itace take wannan rayuwar?”

Jalila tai murmushi tace “bansan sanda zamu tafi ba, amma daga visa ta fito nasan ba jira.”

Mumy ta jinjina kai tace “masha Allah, Allah ya bada sa’a, ya karo ci gaba.”

Jalila tace “ameen...”
Sakon Hassan ne ya shigo, “Baby am back, ko nazo na kinkimoki?”

Murmushi tai bayan ta gama karantawa sannan tace “Mumy muje.”

Mumy ta mike suma suka mike suka fito, motarsa suka mufa itada Safeena da Yasmeen, Mumy kuma ta shiga motar su itada Sultan.

Tana shiga ta baza tagumi.

Jalila kam tana shiga ya kalleta sam bai kula da Safeena ba yadaiga Yasmeen a hannunta ya wani saki murmushi zaiyi magana tai saurin nunamai baya da idanta, Safeena yaga ta shigo sannan ta gaisheshi, Hassan ya kalleta ya amsa, sannan ya kalli Jalila ya dan matso saboda abin na cinsa yace “kiyi maza nima ki gaifarmin yar baby.”

Harararsa tadanyi tace “zaka fara ko?”

Gyara zama yai tare da gyaran murya sannan yace “me zan fara?”

Jalila tace “Yasmeen ga Uncle.”

Yasmeen tace “ Uncle ina wuni?”

Hassan yadan ja kumatunta yace “Yasmeen ko?”

Kai ta daga tana murmushi, ya mika mata hannu yace “nice to meet u.”

Hannu ta mikamai dan ta fahimci gaisawa zasuyi, tana dariya.

Hassan ya kalleta yace “yanzu ina zamuyi Ranki ya dade?”

Murmushi tai kafin tace“zamu fara zuwa gidan Mumy ne ta debo kaya sai mukai Sultan gidan Goggo mu wuce gida.”

Ya kalleta yace “To angama Hajiya.”

Dariya tasa tace “Yaya?”

Yace “ me? Ohhh na manta ashefa ba’a zama Hajiyar ba tukunna, to ko mu fara zuwa Hajj ki zama Hajiya kafin mu tafi Qatar din?”

Tace “Nayi recording zan fadawa Ummy.”

Safeena tai shiru tana kallansu abin sha’awa, jitai idanunta na neman tara ruwa, da sauri ta maida idanunta jikin window tana kallan titi.

Yasmeen kuwa sai zolayarta yake tana dariya, Safeena kuwa tundaga gaisuwa bai kara ce mata komai ba, har suka isa gidan.

Dady na falo suka shigo, Jalila ce ta fara shiga rike da Yasmeen.

Mikewa tsaye yai yana kallanta, zaiyi magana yaga Mumy ta shigo itada Safeena.

Komawa yai ya zauna yai shiru, Jalila ta kalli gidan gaba daya ya canza a dan wannan lokacin, shikanshi dadyn duk ya wani canza, Mumy ta zuba mai ido ya kalli Yasmeen datazo gunsa da gudu ta rungumeshi, har a jikinsa sai dayaji yace “Yasmeen ya gida?”

Tace “Dady ina kaje? Baka siyomin ice cream ba?”

Ya dagata yana murmushi, shigowar Hassan da Sultan ne yasashi sauketa, yana kallan Hassan.

Hassan ya kalleshi sannan yace “Barka dai.”

Dady ya hade fuska yace “Barka dai? Wace gaisuwa ce hakan?”

Hassan ya kalli Jalila ba tare da ya kara mai magans ba yace “kuyi sauri ina mota.”

Ya fada tare da juyawa.

Dady ya bishi da kallan takaici, ba yanda baiyi ba akan Sageer ya barshi ya cigaba da aikinsa amma yaki, ya kuma tabbatar wannam mara mutuncin ne ya hana.

Shiga su Mumy sukai, Safeena gaisheshi kawai tai ta wuce, Sultan kam ko kallanshi baiyi ba ya wuce dakinsa, Dady ya kalleshi dan duk a yaransa yafi san Sultan.

Mumy ta shiga dakinsu, gaba daya dakin yai kacha kacha, Dady ne ya shigo ciki ya kalleta yace “yanzu ina zaku koma?”

Tace “ko ina zamu koma ai ba kada ta cewa tunda ka koremu daga gidan da yake halak dinmu.”

Dady yace “ku kwashe kayanku duka dan saida gidan zanyi.”

Cikin mamaki ta kalleshi tace “siyarwa?”

Yace “sosai, ina zan kai katan gida haka?”

Haushi ya kamata tace “dan Allah Abakar ka sanar dani menene ribarka na abinda kake aikatawa?”

Yai shiru yana kallanta tace “yanzu ka tabbatar min ilimi bai ratsa kaba, sannan ka tabbatarmun kai bagidaje ne, na dauka daka wulakantamu zan ganka kana rayuwa yanda ya kamata, sai dai menene hakan? Kalleka, kalli gidanka? Sannan siyarwa zakai?”

Zaiyi magana tace “basai kace komai ba, tunda har mahaifiyata ta mutu baka tako ka min gaisuwa ba, ai a tunani na ko zaman kiyayya mukai dakai kaminn gaisuwar mutuwar mahaifiyata balle, ni ai yanzu ka nunamin tabbas ko da wasa baka taba sona ba.”

Ta share kwallarta tana cigaba da kwashe kayanta, zuru yai ya tsaya yana kallanta fitowa tai zata dakin Safeena dan tattara kayan Yasmeen, har ta wuceshi ta tsaya tace “Ahh Sultan zai zauna a gidan Goggo saboda makarantarsa, naga kamar ya kamata ka sani.”

Ta juya zata tafi, da sauri ya fizgota yace “Goggon har gida gareta?”

Tace “eh sirikanta sun siya mata.”

Yace “me?”

Tace “sakeni dan Allah.”

Yace “amma shi Sultan din bazai zauna anan ba har ya gama?”

Tace “ya zauna a ina? Gidan mutumin da bai kaunarsa bai kaunar mahaifiyarsa? Ta ina ma zai zauna a wannan gidan?”

Dady ya fara hucci, fizge hannunta tai ta fita, Dady yai shiru gaba daya yama rasa abinyi.


******

Jalila kuwa tana ganin sun shiga kwaso kaya ta fito inda Hassan yake, tace “Yaya muje kaga dakinmu.”

Fitowa yai ya riko hannunta yace “ahh yau zanga muhallin Baby.”

Tai murmushi tace “Yaya daka dan sake hannuna kar a ganmu.”

Yace “to wai ni in an ganmu menene a ciki? Ahhh dana sani London nace a nemarmana dan su nasan ko me kai ba ruwann wani dakai ko a ina ne.”

Jalila tace “Lalai, wato kai abu ma kake so ka dingayi a ko ina? Oh ni yays ba kunya sam.”

Zaiyi magana tace “Yaya zaka saima Sultan keke?”

Yace “keke?”

Ta kalleshi tace “eh, a gidan Goggo zai zauna saboda exams.”

Yace “ban gane ba.”
Nan ta fadamai yanda sukai, hannu yasa ya shafi kanta ta baya yace “ahh baby na u are sooo kind....”

Tace “kai yaya....”

Tana tura kofar dan dakin yai shiru yana bin dakin da kallo, gaba daya jikinsa yayi sanyi.
Ganin yanda yake bin dakin da kalli yasa ta matso ta rungumeshi ta baya tare da kwantar da kanta a bayansa....


#OneLuv💕


🗯 *JALILAH* 🗯


Written By : *AYUSHER MUHD*
Wattpad: *Ayusher Muhd*


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

*77*


Hannu yasa ya juyo da ita saitinsa sannan ya rike hannunta, janta yai zuwa katifar dakin, kwantawa yai sannan ya miko mata hannu, murmushi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login