Showing 99001 words to 102000 words out of 146738 words
Chapter 34 - JALILAH HAUSA NOVELS BY AYUSHER MUHD.txt
yayyarfawa.
Tsorata tayi, tace, " Wayyo Allah na, wanene?".
Bai bata amsaba, suka je kusa da gado ya zauna, jawota yayi ta fad'o jikinsa saman cinyarsa.
Jiyayi wani mugun shock ya shigesa, har sai da yad'an rintse idonsa. Itakam jalilah k'amshin turarensa yasa tagane shine, dan haka saita nutsu, tabar mutsu-mutsun datakeyi.
Hannunta data rufe idon yajanye, ya kwanto da kanta saman k'irjinsa, yasaka hannunsa d'aya ya bud'e idon da k'yau, d'ayan kuma ya tallafo kanta sosai, sannan yafara hure mata a hankali, idon yayi jawur kuwa.
Yanda yake matanne yasakata yin luf ajikin sa, gakuma k'amshin turarensa mai dadi tana shaka.
Ya dad'e yana hura mata idon, sai da ya tabbatar ya huce sannan ya daina hurawar, amma yaki sakinta.
Bud'e idon tayi ahankali ta saukesu akansa, ganin ita yake kallo saita d'anyi k'asa da idanunta, a hankali ta furta "Na gode yaya".
" Uhhm".
Kawai yace mata, sai kuma ya k'ara hura mata iska a fuska.
Ta bud'e idon sosai tana kallonsa.
Da ido ya nuna kanta dake kwance a k'irjinsa, sai kuma yace, "A nan zaki kwana?".
Baki ta d'an turo gaba, ta yunk'ura zata tashi, amma saita kasa, saboda har yanzu yana rik'e da ita.
A shagwabe tace, "to taya zan tashi? bayan kamin d'aurin goro".
Firicin nata yasakashi sakin guntun murmushi, ya janye hannunsa batareda ya tanka ba.
Kanta kawai ta cire daga k'irjinsa, amma bata tashi a cinyarsa ba tace "Yaya wai ina kaje?"
"idan kin gama more cinyar itama saiki d'aga, idan kuma zaki biyane to?."
Baki takuma turowa, ta yunk'ura zata tashi tana k'unkuni
Harta mik'e yarik'o hannunta ya dawo da ita.
"Ah ah, mikuma nai?"
Hannunsa duk biyu yasaka ya zagayeta dasu, yakawo bakinsa kusada kunnenta."kina son sanine?".
Juyowa tayi ta kallesa da sauri, amma batace komaiba, saboda gabanta dake faduwa.
Ya huramata iskar bakinsa a fuska, yana kallon idonta dayay ja yak'ara d'an girma.
Yace "kin tabbatar ba saboda ki zauna kika sa turare a idan naki ba?"
Kallansa tai ta hade fuska tace "Yaya wai......."
Kauda kanta tayi, zuciyarta tana mamakinsa....
Barakai k'arshen tunanin taba taji yasaka hannun damarsa yadawo da fuskarta saitinshi.
Kafin tasamu damar magana taji bakinsa kan labanta.
Waro idanunta tayi saboda mamaki, shima ya waro nasa sosai kamar yanda tayi, sannan yahad'e bakin nasu sosai.
***********
Ummy kuwa koda tashiga d'aki sai ta tadda Abba zaune yana duba wasu takardu, shiru tayi nad'an wani lokaci tana nazarinsa, kafin tayi sallama. ya d'ago idanu yad'an kallrta ya amsa sallamar tata.
Suka d'anyi shiru zuwa 2minutes. Abba yakatse shirun da fad'in "Hassan fa?".
Sanyi Ummy taji aranta kafin tace, " yana lafiya. dama zan sanarma lokacin salla yayi".
Kansa ya jinjina mata, ya ajiye takardun hannunsa yamik'e zuwa bathroom. ita kuma zama tayi abakin gadon tana binsa da kallo, takasa tantance yanayin dayake ciki gaba d'aya. babu dad'ewa yafito, baiko kalleta ba yace, "naje masallaci".
"Adawo lafiya".
Ummy tafad'a tana mik'ewa tashiga toilet d'in domin d'auro alwala itama.
**********
Tunda suka dawo inna takasa zaune takasa tsaye, maganar family d'in Taura kawai take juyawa a zuciyarta, gakuma dadyn jalilah a gefe daya zame mata k'ayar kifi a mak'oshi, Tarawa wace hanya zatabi 'yarta ta fahimci manufarsa.
K'aramin tsaki taja, kafin ta zauna tareda d'aukar wayarta tana dannawa alamar akwai abinda take nema.
" humm" tafad'a tarefa ajiye wayar tana mik'ewa, sai kuma tace, " dukanku nasan hanyar dazanbi nai maganinku aii"
Ni dai nace, "humm".
************
Sun kai adadin wasu mintuna Hassan na baje kolinsa, kafin yacire bakinsa yana guntun murmushi.
Jalila kam kunya tasakata sinne kanta a jikinsa, sai kuma ta zame ta sauka daga cinyarsa takoma kan gado, bai ce komaiba shima yamik'e bayan yakai dubansa ga agogon dake d'akin.
Kallonta yad'anyi ya kauda kai, yanayinsa ne ya canza ya kalleta yace "Jalilah! Har yanzu Abba baice komai ba, kinganshi ne?
Shiru tayi tana kallonsa, shikuma yacigaba da tafiya.
Saida yakama k'ofar toilet d'insu zai bud'e sannan yajiyo muryarta tana cewa "amma Yaya kaimafa nakula matsoraci ne, a haka kamar....."
Kallan daya mata ne yasa tai dif tana sinne kai, fuska ya hade ya nuna kansa da d'an yatsa "ni ne matsoracin?"
Dariya tayi kawai, amma batace komaiba.
Ya jinjina kansa sannan ya ida bud'e k'ofar yana fad'in "lokaci zai nuna a gane wanene matsoraci tsakanin ni da ke yarinya"
Bataji miyaceba sosai, Dan acikin toilet ya k'arasa sauran maganar, babu dad'ewa yafito yana gyara hannun rigarsa alamar yayo alwala, itama alwalar ta tashi tai, dan dazu tai wanka, ita dama bata dadewa intana period.
Lokacin data fito shi harya fara salla, itama saita shinfid'a abin sallah abayansa ta fara tata.
Bayan sun idar ta kalleshi yana zaune inda yai sallar, yayi shiru alamar yatafi duniyar tunani, a wani halin Abbansa yake ciki?
Daurewa tai cikin k'arfin hali tace "Yaya nakawo abinci"
Kansa ya jinjina mata batareda ya kalleta ba ta mik'e tana cire hijjabin jikinta, kafin ta d'akko tiren ta dire a gabansa, yauma bayan tagama zuba masa, harta janyo wani plate d'in zata zubama kanta yarik'e hannun, daga ita harshi suka kalli junansu a tare, sai kuma yasaki ya ture plate d'in gefe, ya d'auki d'ayan spoon d'in yasaka a inda tazuba abincin.
Sai da yafara ci sannan itama tafara cin, babu mai magana acikinsu, har sukai rabin abincin.
Sai can jalilah tace, "Yaya mizai hana ka fara gwada shiga masallaci cikin mutane yin jam'i?"
Ido yad'ago yad'an kalleta, baice komaiba har suka kammala, har ta d'auka bazai ce komai ba. tana tattare kwanikan taji yace "Kina tunanin zan iya?"
Kallansa tai jiki a sanyaye, yace "a koda yaushe inaga taron mutane sai naga kamar lokacin da mutane suka taru akan su Husain."
Shiru tai kafin tace "banyi tunanin hakan ba n......"
Yai saurin cewa "I won't stay like this forever, nagode da shawararki sallah cikin mutane tafi lada."
Kallansa tai cikin jin dadi tace "tam Yaya."
"Humm" ya fad'a yana mik'ewa, kayan jikinsa yafara k'ok'arin cirewa, dan haka Jalila tayi saurin d'aukar tiren tafice.
Binta yayi da kallo, ya d'an saki guntun murmushi, sai kuma ya lumshe idanunsa, ahankali ya furta " kin cancanta jalilah ".
Ni kam danake labe nad'an dara kad'an.😅
*************
Har washe gari Abbah baice komai gameda zancen da Hassan yay masaba, wannan ne yakuma saka Hassan cikin matuk'ar damuwa, amma kasancewar Jalila a gefensa zuciyarsa tana d'an rage nauyi.
Ita kanta Ummy shirun na Abba ya dameta, duk da bai canza fuska ba, amma yanda ya share maganar sai lamarin yake nuk'urk'usarta.
Sageer ma daya kasa daurewa sai da ya tambayeta mi Abban yace gameda maganar jiya.
"Sageer baice komai ba fa, nikaina abin ya dameni, gashi bansan wane hali Hassan yake cikiba, naga har yanzu matarsa bata fitoba".
Ya sageer ya ja ajiyar zuciya, sai kuma yace "insha ALLAHU babu abinda yafaru Ummy, bara muga zuwa 9 idan bata sakkoba sai a bincika"
Ta kalli Sageer cikin jin dadi tace to Sageer.
Ummy batace komai ba tacigaba da aikinta, amma zuciyarta sai sak'e-sak'e take mata akan Hassan da kuma shirun Abbah. tare sukayi komai da Sageer.
*************
Safeena ta kalli RAM tace "ina ne nan din?"
Yace shiga ki gani, tura kofar tai, yan mata ne da maza kowa yasha kaya na duniyanci suna ta cashewa.
Da sauri ta kalleshi tace "menene hakan?"
Yace "baki gane ba? Wannan shine rayuwa ai."
Ta kallesu sannan ta kalleshi da sauri ta juya da gudu tana girgiza kai, yanda taga mata na rungume maza ba kunya? Ina zata iya shiga tai abin nan?
Daki ta shiga ta fada kan gado tana kuka da kiran sunan Inna da Mumy da Dady..........
Nace hmmmmm
#OneLuv💕
*_🗯JALILAH!!🗯_*
Written By : *AYUSHER MUHD*
✔ote me on wattpad : *Ayusher Mohd*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_D home of expert and perfect writer's_💡)
*57*
Har 9 tawuce babu jalilah babu labarinta. Su Ummy suka kammala aiki tsaf itada Sageer, ko ya Ummy taji motsi saita waiga, azatonta jalilah ce.
Shi kansa Sageer hankalinsa yafara tashi, yana daurewane kawai saboda karya k'ara tada hankalin Ummy.
A can kuwa bangaren su jalilah ciwon Hassan ne ya motsa, saboda damuwar daya kwanta dashi a zuciyarsa, akan shiru da Abba yai akan maganar su Husain, gani yake maganar tazama gaskiya shine silar barinsu duniya, shiyyasa Abba yake fushi dashi, dama Jalilah tana fad'an bahaka bane saboda kawai ta kwantar masa da hankali.
Cikin dare sau biyu ciwon natashi, shi yasa sam jiya basuyi wani barcin kirkiba, sunayin sallah da asuba kuma suka kuma kwantawa dansu rage barci.
Dama Hassan jiya a k'asa ya kwanta, duk yanda Jalilah taso yadawo saman gado bai dawo ba.
 Bayan sunyi sallar asubahi ma a k'asa ya kwanta akan sallayar dayai sallah, can cikin barci Jalilah tadinga jiyo kakarinsa, a zabure ta mike cikin tsoro ta kalli inda ya kwanta.
A razane ta sakko kusa dashi ta tsugunna agabansa, hannuwansa daya rik'e wuyansa itama ta rik'e tana kiran "Yaya! Yaya! Innalillahi please Yaya katashi."
 Gaba daya ya canza, abin ya tsorata ta, yau kam ciwon yamafi na kullum tsanani, dan jikinsa har rawa yakeyi, kansa tad'aga ta d'ora a cinyarta tana kuka da tofa masa abinda tasani, tun tana d'aukar lamarin k'arami sai taga yawuce tunaninta, da ciwon yayi kamar zai lafa saikuma jikinsa yafara rawa yakuma damk'e wuyansa yana jawo numfashi da k'yar.
 Tanaso tatshi taje takira su Ummy amma takasa, bazata iya fita tabarshi shi kad'aiba, dabara ce tazo mata data hango wayarta, da k'yar tamik'a hannu ta d'auka, tashiga laluben number Ummy.
Jikin Ummy har rawa yakeyi wajen d'aukar wayar. Saboda ganin number Jalilah, Sageer nazaune gefenta, yayinda Abbah ke shirin fitowa daga d'aki.
Tana gama jin maganar Jalilah ta jefa wayar a kujera, bata tsaya sauraren tambayar da sageer kemataba, ganin haka shima Sageer yarufa mata baya zuwa sama, dan ya fahimci ba lafiya ba.
Gaban Abba ne yafad'i yabi saman da kallo cikin matuk'ar tashin hankali, badai jikin Hassan bane, da sassarfa yabi bayansu shima.
Sun tarada Jalila tanata kuka har yanzu, gata rik'eda Hassan tana kiran "Yaya katashi!".
Gaba d'ayansu suka rufu akansa kowa yana masa addu'a, Ummy kam tama kasa addu'ar, kuka kawai takeyi, hakama Jalila.
Ganin halin da Hassan ke ciki cikin kidima Abba yakira Doctor, a gaggauce yamasa bayani akan halinda Hassan d'in yake aciki, yana kashe wayar ya matso kusa dashi tare da riko hannunsa.
Babu dad'ewa saiga Dr, Abba na ganin kiransa ya fito da sauri, lokacin ciwon yafara lafawa, sai numfashi da yake fitarwa sama-sama, har yanzu kuma kansa nakan cinyar Jalilah dake share sauran hawayenta, da taimakon Abba da Sageer suka maidashi kan gado, doctor yafara aikinsa....
***********
Mumy ce ta kalli Dady tace "Dadyn yasmeen kayi shiru? ko kafasa zuwan"
Kallonta kawai yakeyi, amma yakasa cewa komai, yarasa miyasa suka damu da zuwansa gidan Taura itada inna, kodai wani k'ullin sukai masa ne? sukeso yaje ya afka.
Hannunsa Momy ta kamo ta kwantar da kanta akan kafadarsa, juyowa yai yana kallonta, kafin ya d'an saki iska a bakinsa.
"Wai shin menene dalilin da yasa kika damu da zuwana gidan taura ne haka?"
Gaban Momy yad'an fad'i, ita kanta tarasa gane dalilin Inna nason Abakar sai yaje gidan Taura, duk da dai tamata bayani a dunk'ule, amma anya babu wata kullalliya a zuciyar Inna kuwa? Itakam sam Inna inta fadi abu akan Abakar hankalinta baya kwanciya, tasan Inna sarai hankalinta nakan company dinta.
"Ya akai? Naga kinyi shiru?
"Uhm ba shiru nayiba, amma nima ina ganin zuwan naka yanada muhimmanci, musamman idan kahad'a bayanan dana maka guri guda, akan abinda aka mana agidan, kuma nasan duk akan komawar Gwaggon tane, a ganina kawai kace kanason gwaggo tadawo nan gidan dazama kawai, ni wlhy nama amince tadawo d'akin Safeenah yanzun, kaga sai a gyara kafin ta iso, idan kuma za a canja mata kayan d'akinme to, duk fa wannan takamar da mukeyi dan munada company namu na kanmu mukeyi ni sam idanun mijin Jalila yanda yake kallanmu hankalina bai kwanta dashi ba, na tabbatar Innama hakan ne yasata fadar cewa kaje din, ai daga Jalila har Goggon naka ne."
Zuwa yanzun kam zuciyarsa tagama yarda akwai wata akasa, wato sai yanzu akasan da Jalila tasa ce?
Yace, "ita inna tayarda da hakan?" Yai maganar cikin zargi.
Da sauri tace "sosaima, itamace tabada shawarar hakan, aganina tahanyar goge laifinmu ne kawai zai hana Taura karbe kud'insa koda kuwa dansa yaso yin hakan, dan wannan dan nasa ni yafi bani tsoro, dafa zai tambayi kana ina cewa yayi wai Inashi mutumin?"
Dady ya cije lebansa, daya tuna ma rainin hankalin da Hassan yamasa randa sukaje asibiti, wai ka fito da kudi kuwa? Ya tuna sanda ya miko mai 1000, kamar shi??
Momy takatse tunaninsa da fad'in "kagani zuwan naka yanada muhimmanci kaji Darling? koba komai zaka lallaba Jalilah, ai komin lalacewa naka naka ne, mu fa kosamun damar kebancewa da ita bamuyiba."
Dady yai shiru kafin can yace "Shikenan, babu damuwa, zanje din, amma kafin natafi zan shiga wajen Inna inji miya kamata nafad'ama Jalilah idan naje, kinsan yarinyar tana jarabar son uwarta, sam bata damu da ni dana haifeta ba.
Mumy ta kalleshi, jawota yai jikinsa ya rungume ta a ransa yace wato yanzu dalilin 'yata shine na samu 'yancin roko? Da ai komai sai dai a yanke min hukunci, danasan mijinta kafin aurenn lalai dana dade da canza shika.......
*********
Alhmdllh komai ya dai-daita, Hassan yadawo dai-dai, amma kallo d'aya zaka masa kahango idanunsa da sukai ciki, har wata yar karamar rama yayi.
Tun d'azun idonsa nakan Abba, kallonsa yakeyi ko kiftawa bayayi. ita kanta Ummy ganin kallon da Hassan kema Abban nasu yasata maida kallonta kansa, tasan soyake yace wani Abu, amma Abba sam bashida alama.
Hannun Abba Hassan yakamo, yarik'e sosai acikin nasa, wannan yasaka Abba maido gaba d'aya hankalinsa kan Hassan, ya zubamai ido cikin wani yanayi da shikadai ya san me yake nufi.
Wasu hawaye masu matuk'ar zafi suka ziraro daga gefen idonunsa.
"Abba nasan ban cancanci a yafe min ba, ni kaina nakasa yafema kaina wannan laifin, nasha addu'a inama tun sanda nayi jinya nima nabi bayan su Husain, na roki Allah akan inhar mutuwata shine mafi alkairi ya daukeni, sai dai da alama ba yanzu ba......"
Ya kara kallan Abba da idanunsa da suka canza yace "Abba kamin dukkan hukuncin dakaga yadace dani kaida Ummy, duk hukuncin da kukamin bazan taba ganin tsaurinsa ba, Ummy! Abba dan ALLAH Ku hukuntani ko nima zuciyata xata samu sukuni.
Kasa karasawa yai saboda gaba daya zuciyarsa ta yi rauni, hannu yakai yarik'e wuyansa yana k'ok'arin janyo numfashi.
Lokaci d'aya Abba da Ummy sukai kansa, Jalilah kam fita tayi daga d'akin tana kuka, shi kansa sageer yakasa jarumta dan tuni shima kwalla tacika masa idonsa har suna neman zubowa.
 Addu'oi Ummy da Abba kemasa, ahankali numfashin yafara dai-daita, Sageer yamik'o gorar ruwan daya d'akko, Abba ya taimakama Hassan yatashi zaune ya jingina da fuskar gadon, bayan yasaka masa fillo.
 Ummy tabashi ruwan yasha sosai, kafin ya janye bakinsa.
Idonsa yayi jajur, kalle-kalle yafara yanason ganin Jalilah amma bata d'akin.
Ummy Ce talura da hakan, ta juyo tana fad'in "Sageer! Jalilah fa?".
Shima waige-waige yafara, kafin yace, "inagafa tafita".
Abba yace, "Sageer jeka kirata".
Yace "To Abba"
Afalo ya isketa tacusa kanta a cinya tana rusar kuka, tausayi tabashi ya kura mata ido, murya a sanyaye yace "Jalila"
Shiru kamar bata jishiba.
Ya sake cewa "Jalilah!"
Batare data kalleshiba tace "Naam." Cikin muryar kuka ta amsa.
"Kizo inji Ummy."
Abinda yafad'a kenan yajuya yakoma cikin d'akin. saida ta goge hawayenta sannan tamik'e tabi bayansa.
Tunda tashigo Hassan ya kura mata ido, a hankali ya lumshe idanunsa, garin yaya ya bari yarinyarnan ta gama kama zuciyarsa? Ummy tajawo hannunta ta zaunar kusada ita tana lallashi.
Bayan wasu 'yan mintuna Abba yai gyaran murya, har yanzu hannunsa nacikin naHassan.
Cikin kakkausar murya yace "Hassan!"
Abba yakira sunansa cikin muryar damuwa.
Kallonsa kawai Hassan yayi amma bai amsaba.
Abba ya kalli Sageer yace "Sageer zauna anan."
Gefensa kadan ya nunamai, Sageer ya zauna kusa dashi.
Abba ya kalli Hassan yace " me kake san ji Hassan? Me kakeso kaji daga bakina?"
Hassan ya kalleshi yace "Abba!"
Yanda ya kira sunansa sai da Ummy ta juya kai saboda kwalla, Abba ya sa hannunsa akan kafadarsa yace "kasan me yafi damuna akan abinda ya faru?"
Hassan ya kalleshi, Abba yace "gani nake duk nine mai laifi ba kai ba, alamace ta ban nuna ma kulawa ba, ban nunama duk kaddarar data samemu mu dogara da Allah ba, sannan ban nunama duk wani abu daya faru ka sanar dani ba, ban nunama ko me ya faru bazai zama laifine ba."
Hassan kallansa kawai yakeyi kafin ya juya kansa gefe, tare da runtse idanunsa, Abba yace " baka taba tunanin ko baka fita waje ba su sai sun fita kuma sai ajalinsu ya kama a gun? Hassan ina karatunka? Har ka bari zuciyarka ta damaimaiye da zargi? Ta hanaka walwala? Ta hanaka sukuni? Ta maidakai gaba daya wani mutum wanda baza'ai magana dashi ba? Ta maida ma baccinka nightmare?"
 Hassan ya kalleshi yace "Abba ni na jaa su....."
Abba ma idanunsa ma gaba daya sun canza kala ya sa hannu ya jawoshi ya rungumeshi yace "Ko kaine hakan ta faru dakai, ace misali dukanku ne ajalin ya kama akanku alokacin, ace bare ne wanda yasaku kuka hau titin, bazanso ya zargi kansa ba har tsawan wannan lokacin bare kai dana, Hassan babban abinda yafi damuna shekarun daka diba kana zargin kanka."
Sageer ya riko hannun Hassan rungume juna sukai a tare suka saki kuka, Abba ya kallesu sannan ya kalli Ummy.
Murmushi tamai tare da jinjina kanta alamar hakan yayi.
Jalila kam na kwance a cinyarta tana share kwalla, a yaushe Hassan ya zama haka a rayuwarta????
**********
"Wai zaliha wacce irin rayuwa kika saka kankine? nifa nace ki kwantar da hankalinki, sai Taura yadawo hannunki, kima bar damuwa darashin d'aga wayarki dayakeyi. nifa nama fara zargin kodai wayar tasace tafad'i? Dan nasan aikinmu ba k'aramin aiki bane dazai bar jikinsa dawuri haka"
"To amma Anty idan kince wayarsa fad'uwa tayi miyasa har yanzu bai sake zuwaba? tunfa daga d'aga wayar wannan d'annan nasa shikenan ba labarinsa, Dan ALLAH kibarni naje gidan nasa kamar yanda nafad'a miki tun farko"
"amma dai Zaliha bakida hankali ko? shin kin manta sharad'in aikin nan ne? Sannan da kankifa kika sanarmin bak'ak'en maganganun da d'ansa yamiki awaya, ko an fad'a miki Na daina sonkine dazan bari a illata minke abanza? kodai sake shawara amma ba wannanba".
"To Anty yazanyi?"
Lakwai abinda zamuyi kuwa, kibani nanda kwana uku, zanyi tunanin mafita"
"Shikenan Antyna, shiyyasa nake matuk'ar k'aunarki wlhy" ta kwanta akan cinyarta.
Murmushi Anty tayi, batace komaiba ta shafa kanta, Dan halinsu d'aya babu wani banbanci.
***********
Tun bayan fitarsu Abba Jalila ta duk'ar dakai tana murmushin jin dad'in kalaman Abba, ga fuskar Yaya tanuna