Showing 30001 words to 33000 words out of 44294 words

Chapter 11 - YAR ZINA CE COMPLETE HAUSA NOVELS BY MARYAM PINKY.txt

har takai a mafarki ina Auratayya da wata yarinya,Abin is too worst,bana iya controlling kai na idan na fara feeling d'in, I don knw what to do cox yanxu pills ma basa rik'e ni ko na sha!!!"
Ya fad'a kamar zai yi kuka,
Farouq da yayi sunan zaune tinda Abdul yafara bayani ya kalleshi yace
"Abdul wannen inaga Ai anyi akan gab'a,ina tunanin matsalar nan tazo k'arshe"
Abdul cikin rashin fahimta yace
"Like how?"
Murmushi Farouq yayi yace
"Menene Amfanin Husna tinda kace K'ibd'iyya tayi maka k'ank'an ta?"
Tsoki Abdul ya ja yace
"Farouq ya ina gaba kana mai dani baya?"
Farouq yace
"To fad'i bayan dana maida kai"
Dafa kafad'ar Farouq d'in yayi yace
"Farouq ka fahimce ni mana.."
Katse shi Farouq yayi ta hanyar d'aga mai hannu yace
"Abdul baka da wani sauran bayani,Babu wata hujja da za'a karb'a daga gare ka at this time,your problem ix lyf partner kuma yanzu ankawo maka har biyu,to kuma what next?"
Shiru Abdul yayi sannan yace
"Farouq wallahi har yanxu ban sami wata yarinya da zan iya so ba ko tayi dai-dai da ra'ayina,As for me gaskiya bazan iya rayuwar Aure da wadda bana so ba.."
Farouq da maganganun Abdul suka fusa ta shi yace
"To yanxu su kuma wad'annan na gidan fa?"
Abdul yace
"Nifa su ba damuwa na bane,mummy ce ta Ajiye su not me,don ba wadda nace ina so"
Farouq ya masa wani kallo yace
"To Aikuwa ya kamata ka sanar da Mummyn ta sani tin wuri"
Cikin rashin ko inkula Abdul yace
"It doesn't concerns me"
Farouq cikin kulawa yace
"Okay.... But why not kaje ga Asma'u first idan yaso nangaba idan ka samo dai-dai kai d'in sai ka sake Aura"
Batare da ya kalle shi ba yace
"Nagama magana fa"
Cikin fushi Farouq yace
"Okay...to tinda haka kace kar ka sake fad'a min wani problem Associated with this..kaje can ka k'arata da girman kanka"
Murmushi Abdul yayi ganin yadda Farouq ya fusata,matsowa yayi ya dafa Farouq d'in yana killersmile d'in sa yace
"Farouq nine mai girman kan?"
Farouq yace
"Eh..kai mana"
Girgiza kai yayi yace
"Friend girman kan menayi Yanzu nan?"
Ture shi Farouq yayi yace
"Ni matsa Dan Allah... An fad'a maka best solution kaje ka sauke girman kanka ka rarrashi Husna ka samarwa kanka lfy ka tsaya,"
Tab'e baki Abdul yayi yace
"Godforbbid, ko macen da nakeso bazan iya wani lallashi ba Akan wannan bare wadda bani da wani feeling akan ta After that ma taimakon ta zanyi"
Farouq Murmushi yayi wanda shi kad'ai yasan manufar sa yace
"Okay...Allah ya baka sa'a,Ai Alhmdllh naji dad'i ma da pills d'in suka fara dena yi maka Amfani that means kana kan gab'a"
Yayi wani Murmushin sannan ya cigaba
"Kuma idan tura takai bango kaga dole rak'umi ya sha ruwan ya'n tsaki, At the end of the day kuma girma ya fad'i."
Mik'ewa Abdul yayi without any concern ya nufi bedroom don anfara kiran sallah yabar Farouq yana b'ab'atu shi kad'ai.
Ganin Abdul ya fito d'aure da Alwala yasa shima ya shiga toilet d'in falon shima ya d'auro,bayan sun idar da sallar ne Abdul ya kwanta Agun yana fuskantar Farouq da yake ta cika yana batsewa,Abinma yaso bashi dariya don haka yana d'an Murmushi yace
"Amman dai dama sweetyn taka ta b'ata maka rai jiya shiyasa kazo kake sauke min shi Anan"
Farouq yace
"All those matters A side, I'm tasty ka tashi ka karb'o mana Abinci don naji ya'n uwan nata sun tafi,"
Murmushi Abdul yayi yace
"My one nd only friend over d world,Sweetyn taka bazata dafa mana ba?"
Remote ya d'auka yana neman channel yace
"Ai Dan bata nan ne,buh don't bother by 2:00pm zan d'auko ta,sai ta dafa mana tinda kai na gidan ka bashi da Amfani"
Abdul Murmushi yake tayi tinda Farouq yafara magana yana danna wayar sa,kara wayar yayi a kunnensa sannan yace
"Bala u re very stupid, for almost 3times I've called u.."
Ya d'an tsagaita sannan yaja tsokiii yace
"Mind it...just 2 mins inajiranka @sitting room downstairs"
Ya kashe wayar yana cewa
"Useless guy"
Sai kuma ya mik'e yana saka hula ya dubi farouq yace
"Tashi mukoma downstairs"
Ba musu ya tashi bayan sun kashe kayan kallon,ta gefen part d'in sa sukabi suka sauka cikin sitting room d'in na Alfarma,zama sukayi suka sake kunna TV suna kallo sometimes suna fira akan film din da ake haskawa ta tauraron d'an Adam(setellite)
Sai da sukayi 5 mins sannan Bala ya shigo cikin babbar muryarsa ko sallama babu yana cewa
"Gaskiya BOSS ka cab'a Aradu Kayi dace indai Wannan ce matar da ka Auro mana.."
Abdul cikin takaici yace
"Ina Abinda na Aikeka?"
'Dan durk'usawa Bala yayi yana gyara facingcap d'in kansa cikin d'an diriricewa ya wage baki yana cewa
"Ehh..boss Ai yanzu Amarya zata kawo.."
Cikin tsawa Abdul yace
"Wacece haka kake magana?"
Sake washe baki yayi UA d'an ja da baya yace
"Amaryar ka boss mana,Ai na taho zan kawo na gamu da ita tace nakawo zata had'o muku ta kawo Yanxu.. Gaskiya boss Madam tayi akwai kirki har..."
Dariyar da Farouq yake tayi ce yasa bala yayi shiru yana kallon Farouq Dan tinda ya shigo bai kula da shiba,d'an matsowa yayi kusa da Farouq yana Murmushin sa yace
"Oga ko ba haka bane?"
Cikin rad'a yayi maganar da d'an tsoro,
Farouq yana dariya yace
"Sosaima"
Bala yace
"Ahan nasan dama boss sai... "
Jifan da Abdul yayo masa da filo ne yasa ya fice da gudu yana cewa
"I'm sorry boss"
Dariya Farouq ya cigaba dayi sai da yayi mai isarsa sannan ya tsagaita ya kalli Abdul daya dafe kai da hannu d'aya yace
"Gaskiya Aikin Bala yana kyau.."
Tsokiii Abdul yaja ya firzar da iska yace
"He will regret it,zamu had'u"
Murmushi Farouq yayi yace
"Sai hak'uri, dama idan bakai ba wazai iya da bala,kullum shirmen sa gaba yake,Allah ya gyara dae"
Girgiza kai yayi kawai ya ciza d'an yatsan sa yace
"Friend wllh bala kad'ai zai iya samin minor hypertension"
Dariya Farouq yayi yace
"Allah ma ya kiyaye,naturen sa ne haka"
_Bala bodyguard din Abdul ne na cikin gida,Aikin sa gogewa Abdul mota,ko driving d'in sa ko rakashi gu,karb'o jakar sa da dai sauran su,bak'ine mai jiki,gajere amman mai son gayu ne musamman na k'ananan kaya,yana da ban dariya da shirme_
_*PINKY CE*_
[1/26, 3:02 PM] maryam Tahir Author Y4: *'YAR ZINA CE👄*
_......Adulterer's Daughter_
*A TRUE LIFE, TOUCHING HRT & LUV STORY*
_BY_
*MARYAM PINKY*
*®REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
_{We don just entertain nd educate,we touch the heart of readers❤_}
#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*IG PML WRITERS*
#https//www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
2⃣6⃣
Su Ameera kai tsaye tasha suka tafi babu wanda yake wa d'an uwansa magana,sai da suka je tasha suka yi sallar ishaa sannan suka sami motar zuwa jigawa direct,babu b'ata lokaci suka hau sauran passengers ma suka hau kasancewar golf3 ce nan da nan suka d'auki hanyar jihar jigawa,
Tinda suka fara tafiya Ameera ta kifa kanta cikin tsakanin cinyoyin ta tafara kuka Mara sauti,ko sau d'aya bata d'ago ba don kud'in ma kawae Khadija ta bawa,ita kad'ai tasan abin da take ji cikin xuciyarta, Haka ta kasan ce har Around 11:00pm suka sauka A bakin garin,kasancewar lokacin sanyi ne yasa babu mutane sosae sai d'ai d'aiku,Anan bakin shiga cikin k'auyen suka tsaya cirko-cirko,can saiga wani mai mashin zai shiga ciki,Khadija ce har ya gifta su ta tsaida shi,cikin sa'a kuwa ya tsaya,bayani tayi masa nason shigar dasu ciki da yake so yayi,ba musu ya fad'a musu kud'in sukayi goyo suka tafi,
Kwantace Khadija ta dinga yi masa har suka iso bakin wani gidan jar k'asa,bayan sun sauka sun sallame shi ne sannan Ameera cikin rawar sanyi tace
"Inane?"
Taso bawa Khadija dariya amman sai ta gimtse ta nuna mata,tare suka shiga ciki,gida ne k'aton gaske kamar gari guda,babu kowa a tsakar gidan duk mutanen gidan da Alama suna cikin d'akunan su,sai dabbobin su da ya'n tarkacen su,sallama Ameera tayi cikin muryar ta mai Daddan Amo,shiru har sau kusan biyar,Khadija ce tace mata
"Inaga fa sunyi bacci yanxu fa kusan 12:00,zo mu wuce kawai,"
Ba musu tabi Khadija a baya inda ta nufa wani siririn lungu,suna fita daga ciki sai gasu a wani sashin Amman ya d'an fi wanda suka baro kyau,kaitsaye wani d'aki daga gefe taga Khadija ta nufa,A bakin k'ofar suka tsaya sukayi sallama, shiru nanma,duk suka dubi juna,sake wata sallamar sukayi,daga ciki sukaji Anyi gyaran murya,yaye labulen Khadija tayi Suka shiga ciki,Aikuwa dai saiga Baba larai tana sallah, kan wani k'aramin gado Khadija ta haye ta tukuikuye cikin zunbulelen hijjabin ta don ba k'aramin sanyi take jiba,itakuwa Ameera gefe ta d'an takure itama ta shige cikin hijjabin saboda yadda wani irin zazzab'i ke neman shigarta.
Baba larai tana idarwa ta juyo ko Addu'a batayi ba don cike take da tsoro ta dube su tana mik'ewa tsaye
"Ku!..Lafiya kuwa?"
Ta zauna bakin gadon tana kallon Ameera dake k'asa,
"Kunyi shiru,daga ina kuke a Daren nan?"
Tasake tambayar su,
Khadija ce tayi juyi ta sauko daga kan gadon tace
"Kingan tanan ita ta dage sai mun taho wai su Mama da Ya Haidar ne suke neman ta zasu kashe ta.."
Mama da tinda Khadija tafara magana ta zazzaro ido da rik'e baki tace
"Kisa!..?to me yayi zafi haka?"
Ta fad'a tana sake kallon su,
Khadijan ce dae ta sake magana dan Ameera har yanxu ko motsi ba tayi ba tace
"Gata nan dai,Nima daga hanyar makaranta muka had'u dan ko gidan banje ba muka taho nan d'in"
Gyad'a kai Baba larai tayi alamar gamsuwa sannan ta kalli Ameera tace
"Me kikayi musu toh?"
Numfasawa tayi ta goge Kwallarta batace komai ba,baba larai tafara fusata tace
"Kinga ke matsalar ki ,Ace ayi ta yiwa mutum magana amma bazai ce komai ba eyeee?,wannan shirun da kike ina fad'a miki idan kika yiwa mai zuciya a kusa wallahi idan bai dake ki ba sai ya mangare ki,"
Tad'an ja saki zata tashi,
Da sauri Ameera ta rik'e ta tana hawaye da girgiza kai don tama kasa magana,Baba larai ta sake cewa
"To..idan bazaki fad'a ba matsa ki bani guri"
Sai da ta sai-sai ta kanta sannan tayi musu bayanin duk Abinda ya faru tin daga farko har fitowar ta.
"Innalillahi -wa-inna-ilaihir-raji'un.."kawai Baba larai take furtawa,iya tashin hankali kam ya shigeta a yanxu, don gani take kamar yanxu Akan idon ta Abin ke faruwa,sai da tagama jimamin sannan tace
"Sannu kinji,Barka ma da bai miki komai ba," sannan ta d'aga hannu sama tace
"Ya ubangiji ka shirya Wannan bayi naka,Allah mun gode maka,kai ne Abin godiya,Allah ka karemu daga duk wani sharri duniya da lahira"
Duk suka Amsa da Amin,
Khadija da jikin ta yagama yin lakwas da jin baya nin Ameera tace
"Chaiii,wllh bakiji ciki na ba,sai na zagaya"
Wani d'an Murmushi ne ya bayyana kan lips d'in Ameera jin Abinda tace,itama baba larai sai da ta d'an dara sannan tace
"Matsoraciya kawai,abin kad'an sai ya hautsina mata ciki"
Murmushi Ameera ta sake yi kawae,itakuwa Khadija tuni ma ta fice.
Bayan ta dawo ne ta zauna kusa dasu tace
"Mama kamar naji Ance anyi mutuwa?"
"Eh...inna beld'o ce ta rasu,yau kwana hud'u,dama bari nayi sai Anyi bakwai sai na taho kuma sai gaku"
Ameera tace
"Ayyaa Allah sarki,Allah ya jik'an ta"
Baba larai tace "Amin Amin,Ae tasha jinya"
Ameera tace
"Wayyoo..itace Gwagwgwan Ku d'in nan ko Mama?"
"Eyyiii...itace dama ta rage mana,Abokiyar zaman mahaifiyar mu ce"
Khadija tace
"Allah sarki Allah yayi mata rahama,"
Suka Amsa da Amin,sannan baba larai tace
"Idan Anyi Addu'ar bakwai sai mu wuce kawai..."
Zabura Ameera tayi kamar zatayi kuka tace
"Ina zamu wuce?"
Duk ta basu dariya, sannan Khadija tace
"Kano mana,kinji ki da wata tambaya" ta fad'a tana yiwa Ameera hararar wasa,ita kuwa Ameera marairai cewa tayi ta dubi Baba larai tace
"Dan Allah Mama kar mu koma,kashe nifa za suyi,.."
Dariya sosae Khadija tayi tace
"To ba sai a d'aura muku Aure ba kawai.."
Ta fad'a tana kashewa Ameera ido d'aya,
Ameeran kuwa goge k'ollar ta tayi ta dubi Khadija tace
"Ke yanxu sai ki min fatan wannan?,...Mama kinji abinda Khadija tace min koh..?,"
Murmushi Baba larai tayi zuciyarta cike da k'aunar Ameeran tace
"Rabu da shirmen ta Ae ke In Allah ya yarda mijin ki na musamman ne"
Ta fad'a tana shafa kanta,
Kunya ce ta kama Ameeran Dan haka ta sunkuyar da kanta tana Murmushi,
Khadija tace
"Wai! Waya ga mijin Ameera?"
Sai kuma ta tintsire da dariya tana rik'e baki,
Baba Larai ce ta sa tsintsiya ta jefi Khadija tana yi mata dak'uwa tace
"Ungo nan Dije,...Ai zaki ganshin dama"
Ita dae Ameera tana sunkuye tana jin su Amman cikin zuciyar ta cewa take yi
"Ni wama zai Aure ni A yanda nake?..ni fatana Allah ya sada ni da fuskar Mahaifiya ta na ganta ko da once in a lyf ne.."
Baba larai ce ta katse mata tunanin da ta fara yi ta d'ago fuskarta tace
"To...mama Dan Allah muzauna A nan garin karmu koma kanon"
Murmushi kawae Baba larai tayi tace
"Karki damu Ku kwanta da safe mayi zancen"
Kwanciya sukayi daga nan bacci ya d'auke su.
★★★★★★★★★★★★★
*@ 5:00pm*
Harabar _MARHABA EVENT CENTRE_ dake tarauni,jeran gwanen motoci ne Manya-manya na Alfarma sukayi parking a cikin gun,babu Abinda ke tashi agun sai bushe-bushe da sauti mai sanyi,duk inda ka kallah agun furannine different colours an k'awata gun,tindaga sama kuwa rainbow balloon's ne anyiwa ko wacce kusurwa ta gun kwalliya da su ga fitilu red&blue suna on and off,
Mutanen ciki ne suka fara fitowa daga cikin motocin fuskar su kowa ka kalla agun farinciki ne shimfid'e a kan fuskar sa,sunyi kwalliya cikin wani codelaces Ash and red color,Masha Allah sunyi kyau,banda sound d'in cameras babu abinda kake ji,daga can kuma sai ga wata long lexis itama bak'a wuluk,glasses d'in ta masu duhu baka ganin komai,ta shigo cikin gun a guje,gefe itama tasamu tayi parking, nan da nan ya'n Bikin suka nufi gun motar ana gud'a da fesa turaruka,wasu dattijai ne sukazo jikin motar suna jira a bud'e, sai da aka d'auki kusan 20minutes sannan aka bud'e, Masha Allah ganin fitowar Angwaye da Amare da sukayi,sunyi kyau har sun gaji,Abdul da Husna ne A gaba sai Farouq da Fareeda a bayan su,daga baya kuma manya-manyan Abokai da ya'n uwa ne suka take musu baya zuwa cikinhall d'in da Aka tana da don fara gabatar da lunching d'in biki mai tarihi na d'an gidan _Alhaji Abdulfattah mai Nasara_, Bikin daya zagaye kowace Kafa ta media kowa Allah ya sanya Alkhairi yake cewa,Abdul dae fuskar nan laba'asa za'a ce don kai tsaye bazaka iya fahimtar yanayin dayake ciki ba,hadae Akayi taro aka watse daga nan.
Da misalin 10:00pm Aka kai Amare gida jen su dake street d'aya,but different side,bayan sun sha nasihohi daga b'angarori,suma Angwayen haka,mummy tayiwa Abdul fad'a sosae akan ya kula mata da su gaba d'aya,shi dai tinda tafara bai ce komai ba har sai da tagama sannan yace _Insha Allah mummy,_ daga nan ya wuce zuwa gun da Farouq da Sauran Abokan sa suke,daga nan suka tafi suka raka Farouq,
Abdul a harabar gidan yaci burki Dan cewa yayi bazai shiga ba gun yaran nan Dan baiga Abinda zai ce musu ba, tinda ya rako Farouq din kawae shikenan ya wuce bai saurari tsokanar da sauran friends d'in sa suke masa ba,dama shi cewa yayi baya buk'atar rakiyar kowa kar su ja masa raini. _Allah yabada zaman lfy_
11:33pm yagani lokacin da ya shigo cikin main falon gidan,shiru ko ina kamar bashine fal da mutane d'azu ba,kakkashe lights d'in yayi ya haura saman,part d'in sa ya nufa direct,falon sa ya shiga ya Ajiye Leda da keys d'in daya shigo da su,bedroom ya nufa yana shiga ya fad'a toilet yasaki shower mai d'umi, ya dad'e a toilet d'in sannan yafito sanye da bathrub iya gwiwarsa,stool ya janyo ya zauna a gaban mirror yafara tsane ruwan kansa,ya d'ago kenan daga shafa lotion d'in dayayi rubbing a k'afar sa sai yaji kamar Numfashi a kan gadon sa,A hankali ya tashi ya nufi bedside d'in ya kunna lights d'in haske ya gauraye ko ina,ga mamakin sa K'ibd'iyya ya gani kwance ta lullub'e duka jikinta da bargon sa tana ta bacci,Ransa ya d'an b'aci don Shi A plan d'in sa bedroom d'in sa nashi ne for only him don haka ya yaye bargon ya d'an dake ta,da sauri cikin firgita don ita taji zafi ta tashi zaune tana mitsitstsike ido,zama yayi gefen gadon yana kallon ta yace
"What re u doing here...?"
Stammering ta shiga yi tafara k'ok'arin sauka daga kan gadon,
Wani razanannen kallo ya jefa mata yace cikin huskyvoice
"Idan ki ka k'ara one more step frm there.."
Kafin ya k'arasa tace
"Yaa Assignment na nazo ka koyamin ban iya ba kuma Antyn mu yace sai ta daki duk wanda bai yi b..."
Da sauri ya katse ta cikin fad'a yace
"U dey mad!...why can't u wait for me to come?"
Shiru tayi ta sunkuyar da kai k'asa,
Ganin tayi shiru ya sake hasala shi don baya son yayiwa mutum magana yayi masa shiru don haka yakai mata wata cafka yana cewa
"So..I have to repeat my self right..?"
Da sauri ta goce tana girgiza kai tace
"No...I'm sorry"
Tsokiii yaja yace
"Sorry for ur self..useless girl"
K'ibd'iyya ganin ya mik'e tsaye yafara nufo inda take yasa ta fara kuka tare da ja da baya shima yana binta sai da sukaje jikin bango sannan ta runtse ido hawaye na zubowa babu k'ak'k'autawa tana sauraren ta inda zai fara tafkar ta ya kalleta for some minutes ganin yadda ta rufe ido,bin hawayen yayi da kallo yadda suke zuba sai kuma yaji duk ba dad'i,sassauta murya yayi yace
"Oyaa open ur eyes.."
A hankali ta bud'e idon tana kallon sa itama,
"Waya ba ki permission na shigowa part d'ina talkless of entering my bedroom haaa?"
Sai da ta share hawayen sannan tace
"'D'azu ne da aka kawo Anty Husna shine friends d'in ta suke ta disgracing d'ina,shine da Bala ya shigo d'azu mummy ta Aiko sa nace ya bud'e min part d'in na dawo."
Tinda tafara magana ya zuba mata ido har ta gama sannan ya nisa yace
"Are u sure?"
Gyad'a kai tayi tace
"Allah.."
Yace mata
"Okay...but don't Eva and Eva come to my part without my permission, are u clear?"
"Yes"
Ta bashi Amsa yanxu hankalin ta yafara nutsuwa,
Shima ganin haka yasa yace mata
"Jeki falo ki jira ni"
Books d'in ta ta d'auka a kan gadon cox shi sai yanxu ma ya kula sannan ta fice.
Shiryawa yayi cikin wasu pitted cotton pyjamas farare tas masu zanen Rose's masu d'an shara-shara, sunyi masa kyau sosae don sun fito da Ainahin zatinsa na cikakken Giant man of 30yrs,perfume yayi spraying wanda ya had'u da k'amshin bathsoap d'in da yake using,slifas ya zira masu taushi ya fito falon,Azaune kan rug ya hango K'ibd'iyya tana kallon TV,kan 2seater ya zauna yana facing d'in ta,sai da ya d'auki remote ya rage volume d'in sannan ya kalle ta yace
"Ina Assignment d'in?"
Da sauri ta d'auko ta dawo kusa da shi ta nuna masa,sai da sukai kusan 30minutes yana koya mata tana shigarwa sannan suka gama,Murmushi yaga tayi da suka gama ita kad'ai tace
"Thank God..I'm safe"
Cikin ransa yace
"Har yanxu bata san duka"
Kallon sa tayi taga ita yake kallo,d'an diriricewa tayi,ganin haka yasa yace
"Uhuuumm..."
Sosa kai tayi sannan tace
"Yaa yau mummy bata ce tana gaishe ni ba?"
Wayarsa ya d'auka sannan yace
"Tace"
Mik'ewa tayi ta d'au littafin ta tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login