Showing 24001 words to 27000 words out of 30393 words
palourn ya ɗauka na few seconds kafin dad Umar yana kallon bappah yace “i’ll head to barrack now akwai abinda zanyi yanzu a can bappah” gyaɗa masa kai bappah yayi dan yasan ba ƙaramin ɓaci ran Umar ɗin yayi ba, Dad Umar ya miƙe ya nufi ƙofa ba tare da ya kalli sashin da Aryaan ke zaune ba, bin mahaifinnasa yayi da idanu, deep down yana jin disappointment in himself for constantly hurting his Dad, ya sauƙe idanunsa ƙasa yana jin wani kalan tsanan Aneela har ƙasan ransa, da dana sanin irin rayuwar saɓon Allah da suka yi da ita dan tabbass wannan ne ya bata lasisin yi masa wannan akuyancin.
Miƙewa Uncle Ameenu yayi yana kallon bappah yace
“I’ll also take my leave” yana faɗin haka ya nufi ƙofa, uncle muhammad ya miƙe ya bi bayansa, dan suna buƙatar iske Aneela kafin ta bar estate ɗin, dama can su suka shigo da ita, uncle muhammad ya zo zai shigo ya ganta a tsaye sojoji sun hanata shiga suna ƙoƙarin humiliating ɗinta, ya sauƙe glass ya tambayi whats happenening suka ce masa wai wajen Aryaan ta zo amma ta gagara kiran line ɗinsa, jin Aryaan yasa yace su barta ta shigo, suka kuwa barta ta shiga motarta ta bi bayansa, sai da ya fara tabbatar da abinda ya kawota zai musu anfani kafin ya sanar da Ameenu shi kuma ya escalating maganar har gaban bappah tare da mata alƙawarin Aryaan ya aureta an gama, now that ta ga ba haka ba they need to silence her ko da kuɗi ne dan su dama burinsu ba wai Aryaan ya aureta bane burinsu Umar da bappah su ga this side of Aryaan da kyau, amma sam Aneela ba dai a zuri’arsu ba.
Bayan fitarsu palourn shiru ya sake ɗauka, daga Aryaan har bappah babu wanda yace komai, kusan mintuna uku kafin Aryaan ya miƙe tsaye a hankali, bappah ya bishi da kallo dan a tunaninsa tafiya zaiyi amma ga mamakinsa sai ya ga ya tafi bookshelf ɗin da ke palourn dake cike da littafan addini ya ɗauko Al’ƙur’anin bappah ya dawo ya zauna yana kallon bappah yace
“I know you are disappointed in me bappah, kuma nasan you wont believe ko miye zance, amma wallahi..” ya faɗa yana raising alƙur’anin slightly
“Ban taɓa having anything with her ba, ba wai ita kaɗai ba, ive never had anything with any woman!” Shiru bappah yayi yana ta kallonsa, ganin yayi shiru ya sa ya sake faɗin
“Trust me pls” gyara zamansa bappah yayi yana jin kaso mai yawa cikin ɓacin ransa na evaporating
“Meyasa baka faɗi haka a gaban parents ɗinka ba?” Shiru yayi ya gagara amsawa, bappah ya jinjina kai yana kallonsa yace
“Toh naji! Yanzu ina so ka faɗa min da bakinka who she is, miye kuma haɗinka da ita?”
“She was my girlfriend, kuma na san na aikata kuskure da hanyar bata too much access to rayuwata, da yin abubuwa da yawa da addinina bai lamunce mini in yi da ita ba amma wallahi bappah babu zina cikinsu duka”
Studying ɗinshi kawai bappah yake yi, duk da yasan ƙarya ba halin Aryaan bane dan tun yana ƙarami he’s a very straight forward person idan yayi abu yayi ne ko yanka shi za’a yi zai ce yayi, haka idan bai yi ba ko za’a halakasa bai yi ba. Ganin bappah yayi shiru yana ta kallonsa ya sake cewa
“I’m not lying!”
“I know!..” bappah ya faɗa yana cigaba da kallonsa,
“But still ina so in san dalilinta na aikata hakan”
“Saboda nace i cant marry her”
“Why cant you marry her?” Shiru yayi, bappah ya ɗanyi guntun murmushi yace
“Tashi kaje, i know exactly me zanyi ya kawo ƙarshen komai, idan ma gaskiya kake faɗa ko akasinsa” gyaɗa masa kai yayi a hankali ya miƙe ya mayar da Qur’an ɗin ya dawo ya nufi ɗakin Daada walking slowly….
Karatun alƙur’ani ya sameta tana yi tana ganinshi ta ƙarasa ayar da take karantawa tana murmushi tace
“Muhammad”
“Na’am” ya amsa ƙasa ƙasa yana ƙarasawa dogon kujera dake ɗakin ya kwanta ya lumshe idanunsa, shiru tayi tana kallonsa kamar zata masa magana kuma ta fasa ta cigaba da karatunta a hankali, tun yana jin karatun ƙasa ƙasa har bacci ya ɗauke shi..
Ko minti goma baccin baiyi da ɗaukarsa ba muryarta ya tashe shi, Har tsakiyar kansa yake jin muryar kamar wata gyare banda surutu babu abinda takeyi, tun daga palourn Bappah har ɗakin daada ana jiyota! Kuma ya san bazai wuce ita da bappah ɗin ba dan wannan wasa na jika da kaka tafi kowa yinsa da bappah kuma shima yake biye mata.
Tashi yayi zaune a hankali ya dafe kansa da hannu biyu, Daada ta dubeshi tana rufe alƙur’anin tace
“Ta tasheka koh? Ai wannan yarinya Salwa kam sai a hankali” shiru ya mata bai ce komai ba saboda ciwon da kannasa ya fara masa, dai dai lokacin ta buɗe ƙofar ɗakin Daada, tun daga bakin ƙofa tace
“Daada am” tana shigowa cikin ɗakin ta nufi Daada, sai dai wanda ta gani a zaune dafe da kansa yasa ta ja ta tsaya sai kuma ta juya ta nufi ƙofa, Daada na mata magana ma ko juyowa batayi ba ta fice a ɗakin, ya ɗan ja guntun tsaki tare da miƙewa ya nufi ƙofa shima Daada ta bishi da kallo…
Yana fitowa palour ya tarar bata nan, bappah yace “kai ka korota hala?”
“Ita wa?” Ya tambaya a hankali yana zama a kujera,
“Zaka santa soon” shiru yayi bai ce komai ba, bappah yace
“Baka da lafiya ne?” Ya ɗan gyaɗa masa kai yana nuna masa kansa
“Sannu kaje ka sha magani ka kwanta, bari in ga ko daada na da paracetamol” ya faɗa yana miƙewa ya nufi ɗakin Daada.
Sai da ya sha maganin kafin ya wuce masallaci tare da bappah dan sallar Maghriba kafin ya wuce gida.
A hankali salwa ke haura stairs ɗin without making any sound dan bata son ko su Lailerh su san ta shigo, sannan sai da ta tabbatar Ameen ya tafi masallaci kafin ta shigo, successfully ta gama haura benen ta buɗe ƙofar ɗakin Ameen ta shige ta rufo ƙofar tare da riƙe kunkumi tana kallon ɗakin, bata ma san miye ya kawota ko miye take nema ba abinda kawai ta sani shine duk wani abu nashi mai muhimmanci yana nan, ta fara kalle kalle, ɗakin is very clean babu tarkace bare ta gane inda kayansa suke, wadrobe ta buɗe ta ƙare ma kayan ciki kallo kafin ta rufe, ta ɗan ja tsaki dan bata ga wani abu mai muhimmanci da idan ta lalata masa zai ji haushi ba.
Har ta juya zata fita idanunta ya sauƙa akan laptop ɗinsa dake gefen bed, ta san wannan ba laptop ɗin Ameen bane so definitely nasa ne, haka kawai taji this is it, ta nufi laptop ɗin da sauri ta zauna gefen bed ta janyo laptop ɗin ta buɗe tana faɗin
“Lets see what u got here” wani murmushi tayi ganin screen ɗin babu password this seems easier than she imagine.
“He’s actually stupid, wa ke barin stuffs ɗinsa without password yanzu..” ta faɗa a hankali tana gyara zamanta a kan gadon.
Tana buɗe screen ɗin taga already it was opened to his work, ta zuba ma screen ɗin idanu tana kallon kyakkyawan 3D model na zane dake kan screen ɗin da bata wani gane kansa ba, abinda kawai ta sani shine it was beautiful and massive too, ɗan matso da fuskarta tayi kusa da screen ɗin sosai tana kallo ba ƙaramin birgeta zanen yayi ba
“Whats this..” ta faɗa amused, ba wai building bane kawai, zane ne da ta gagara gane miye ne, abubuwan da ta gane a ciki kawai highways da yayi mapping, inda yayi indicating ruwa, da kuma skyscrappers, ko ma dai menene wannan ba ƙaramin abu bane, komai was engineered to perfection. a can saman screen ɗin taga an rubuta
Arewa crown development
pan african financial and cultural district
Lead architect: Aryaan Umar Turaki
Ɗan buɗa idanunta tayi tana cigaba da kallo a zuciyarta tana mamakin shi yayi duka wannan ɗin? Tanƙwashe ƙafafunta tayi ta cigaba da kallo tana clicking tana buɗe other files ɗin, babu abinda bai tsara ba, interior layouts, phase of construction, and many more.
Babu tsoron komai ta hau deleting files ɗin tana yi tana kallon ƙofa sai da ta goge su tass har waɗanda bata buɗe ba kafin ta miƙe da sauri jin taku outside door ɗin dai dai lokacin ya turo ƙofar ɗakin ya shigo….
#Banidahujja
#Maimoon
09041426598
https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q
🌺BANI DA HUJJAH🌺
Assalamu alaikum lovelies Bani da hujjah is a paid book, free pages kuma basu da yawa sosai, pls support me by making your payments kafin end of free pages! Thank you so much as you do, ga masu bukatar biya zasu tura 500 kacal zuwaga
7039695535
Palmpay,
Maimunatu Abdullahi muhd
Sai ku tura min evidence of payment ta 09041426598 on whatsapp
Idan kuma katin waya ne zaku tura 500 zuwa ga 07039695535
Thank you❤️
11.
Daga sama har ƙasa ya ƙare mata kallo ganin yadda tayi tsuru tsuru a tsaye, kana ganin idanunta ka ga mara gaskiya kafin ya juya ya kalli gadon inda laptop ɗinsa ke ajiye a buɗe, bai san sanda ya haɗe girar sama da ta ƙasa ba yana takawa zuwa cikin ɗakin sosai, Ameen dake biye da shi a baya shima ya ƙaraso ciki yana kallon Salwa yace
“Me kike yi anan?”
“I….i…na zo ne… ina so..” ganin Aryaan ya ɗauki laptop ɗin tayi hanyar ƙofa da gudu zata fita, shi dai Ameen bai ga sanda Aryaan ya ajiye laptop ba sai gani yayi ya cafko ta, ta fasa ihu tare da tsugunawa ƙasa tana kallonsa har ta fara hawaye
“Wallahi ban sani bane yaya…” da Sauri Ameen ya matso yana faɗin
“Sake mata hannu mana dan Allah kar ka karyata miye ta maka?” Janyota ya soma yi zai mayar da ita gaban laptop ɗin, ta lanƙwashe a ƙasa tare da taƙarƙarewa ta kurma ihu ko Mami zata ji ta ta zo ta taimaketa!
Ameen that is confused ya sake biyo sa yana faɗin
“Wai miye ta maka ne? Meyasa idan bakayi mugunta ba baka jin daɗi” ko kula Ameen baiyi ba, yana riƙe da hannunta da hannunsa ɗaya ita kuma tana tsugune a ƙasa ya buɗe laptop ɗin, he was so shocked da bai san sanda ya sake hannunta ya dafe bakinsa ba, tunda ya ga laptop ɗinsa a buɗe yasan ta taɓa kuma ganin zata gudu ya san ɓarna ta masa amma bai taɓa expecting abinda ta aikata kenan ba, project ɗinsa na wata da watanni? Idan bai halaka ta ba sai dai idan ba sunansa Aryaan ba, a zuciye ya juyo sai dai wayam har ta tattare skirt ɗinta ta gudu ta bar ɗakin, Ameen ya matso ya leƙa screen ɗin yana faɗin
“Wai miye tayi ne” kanshi da already ke ciwo yaji ya sake sara masa, idanunsa suka kaɗa lokaci ɗaya yana kallon Aryaan kamar wanda baya son yayi believing abinda ya gani yace
“She deleted Arewa crown development project” zaro idanu Ameen yayi yana kallonsa yace
“No way! you dont mean it… innalillahi” ya faɗa yana janyo laptop ɗin yana dubawa, Aryaan ya samu waje ya zauna a gefen bed ya dafe kansa, project ɗinnan bai taɓa babban project irinsa ba, his hardwork for months ta goge cikin mintuna? Wace iriyar yarinya ce Salwa?
Fuskar Ameen cike da alhini yace
“Subhanallah kuma baka da any back up” shiru yayi kawai ya gagara magana.. Ameen ya miƙe yana sake jinjina lamarin yace
“Kayi haƙuri haka Allah ya ƙaddara…” wani banzan kallo ya masa daga sama har ƙasa kafin ya miƙe yana kallon Ameen yace
“Ai wallahi idan kaga abinda ya hanani karya yarinyarnan rasuwa nayi, gobe ko tsinke aka ce mata nawa ne zata kiyaye sa..” yana gama faɗin haka ya nufi ƙofa zai fita, Ameen yayi saurin shan gabansa yana kallonsa yace
“Kar ka taɓata please yarinya ce…” bai san sanda ya hankaɗa Ameen ba yana huci yace
“Motsin gado ce ba yarinya ba, kasan girman Allah ko da kuɗi aka bata ta bi hanyar da na bi ma bazata sake bi ba..” Ameen dake ta kallonsa yace
“Akan project ɗin banza zaka taɓa lafiyarta ta?”
“Ba na banza bane, its my hardwork, wahalata ce na months, why am i even explaining it to you? Ka zauna kana son Yarinya ƙarama shiyasa duk inda raini yake ta rainaka to billahi ƙaryarta ta rainani ba sunana Al’ameen ba kuma banyi mata kama da saurayinta ba..” sororo Ameen ya tsaya yana kallonsa har ya kai ƙarshe kafin yace
“Bismillah je ka, idan ka barta da rai yau baka cika Aryaan ba, kuma sanin kanka ne ni ba soyayya nake da ita ba bare kace saboda haka ta raina ni infact respect ke tsakanina da ita more than you could imagine, to idan ma soyayyarce why is it your problem? Ko dan Albarkacin son da ka san ina mata ba zaka mini kara ka mata uzuri ba? Amma a gabana kake cewa zaka daketa?”
“Ai ka san girman Allah ko kai ne ka goge abinnan duka zan maka bare wata wacce kake so na banza da hofi…” yana faɗa ya raɓa gefensa ya fice a ɗakin Al’ameen ya bishi da kallo
Ganin yadda ta shigo cikin palourn tana ƙoƙarin haurawa sama da gudu ya sa Ammi dake shirya dining faɗin
“Zo nan..” sai da ta kalli sama ta kalli ƙofa kafin ta nufi wajen Ammi jikinta na mazari, dan daga yadda taga yayi reacting ba ƙaramin ɓarna ta aikata masa ba
“Miye haka? Meyasa zaki shigo mini gida da gudu wa ya biyo ki?” Tana yi tana kallo ƙofa tace
“Babu!”
“Bazaki faɗa mini wa ya biyo ki ba sai na kwaɗa miki cokalinnan...” Ammi ta faɗa tana dakatawa da jera abincin..
“Ammi dama yaya ne ban sani ba na…..” dai dai lokacin ya buɗe ƙofar palourn ya shigo, ta kurma ihu ta nufi sama da gudu, Ammi ta bita da kallo, amma ga mamakinta sai taga Aryaan ya bita saman, Ammi tayi saurin ajiye spoon dake hannunta tana faɗin
“Lafiyanku kam?” Ta faɗa tana nufar saman itama, a bakin ƙofar ɗakinta ta same shi salwa ta shige ta rufe da makulli, Ammi ta tsaya tana kallonsa kafin tace
“Laifi tayi hala?” Sai da ya sauƙe ajiyar zuciya kana ganinsa kasan ransa a ɓace yake kafin ya juyo ya kalli Ammi yace
“Ina wuni”
“Lafiya lau miye tayi maka?..” ta sake tambaya tana kallonsa
“Babu!” Kawai ya faɗa yana nufar stairs ta bishi da kallo har ya gama sauƙa ƙasa kafin ta nufi ƙofar salwa ta buga tace
“Zo ki buɗe mini..”
“Ammi yaya yana nan?”
“Ban sani ba ki zo ki buɗe mini nace” a hankali ta buɗe ƙofar Ammi ta tura ta shiga tana kallonta tace
“Me ya haɗaki da shi da ya biyo ki har nan?”
“Wallahi Ammi ni babu abinda na masa kawai dan na ɗan taɓa laptop ɗinsa ne shine….”
“Ƙarya kike yi akan haka ba zai biyo ki har nan ba na san halinsa, ba za dai ki raba kanki da wasan banza da mazan gidannan ba koh? Ban hanaki ba? Idan ya karyaki a banza wa yake da asara? Ki janyo babanki yayi ta jarabar da ya saba koh bayan ke kike fita kike nemo duk wani abu da ke samunki koh? Na rabaki da hamza kinki ji yanzu kuma Aryaan kike neman maganarsa? Baki san har yanzu haushin ɗaukarki da yayi nake ji ba? Da kinji maganata a lokacin kin hakura da zuwa da zai ɗauke ki ne? Yanzu uban miye ya haɗaki da laptop ɗinsa ko sa’anki ne shi da kike wasan banza da shi har yake biyoki har nan zai dokeki”
“Ammi fa…” gwaɓe mata baki Ammi tayi ta dafe bakin tare da fashewa da kuka
“Na rabaki da su wallahi in banda gaisuwa na sake ganinki da su kina wasan banza sai na ci miki mutunci mara hankali kawai” tana gamawa ta fice a ɗakin ta barta a durƙushe tana kuka..
sake leƙowa Ammi tayi tana harararta tace
“kuma wallahi ki rufa mini baki tunda ba dukanki nayi ba kar ki fusata ni in miki shegen duka dan ubanki, tunda dalilin kuka kike so ni zan baki dalilin yin kukan mai lasisi..” tana faɗa ta rufe ƙofar ta sauƙa ƙasa dan ƙarasa aikinta.
Ƙunshe kanta salwa tayi a ɗaki taƙi saukowa har sai da Daddynta ya dawo, itama Ammi ko bi ta kanta bata sake yi ba.
Uncle Ameenu bayan yayi wanka ya sauƙo dan cin abinci, har ya zauna ya kalli Ammi dake ƙoƙarin serving ɗinsa yace
“Ina princess..”
“Tana ɗaki” Ammi ta faɗa fuskarta ba yabo ba fallasa
“Why is she in her bedroom by this time? Bata da lafiya ne?”
“Lafiyarta ƙalau yallaɓai..” tura kujerar yayi baya ya miƙe ba tare da ya kuma kula Ammi ba ya nufi sama, Ammi ta bishi da kallo kawai dan ta san miye zai biyo baya…
A kwance ya sameta ta lulluɓa da bargo har kanta, ya ƙarasa ya zaune gefen gadon yana kallonta yace
“Princess” jin shiru ya sauƙe bargon kanta, gani yayi idanunta a lumshe tana bacci, tayi parking gashinta Ya kwanta lub a goshinta, shiru uncle Ameenu yayi yana kallonta kafin ya kai hannu ya taɓa goshinta jin ba zafi ya taɓa wuyanta shima ba zafi hakan ya sa ya miƙe ya nufi ƙofa, Ammi na ta jira taji ya fara faɗa dan