Showing 12001 words to 15000 words out of 30393 words
/>
“Story for the Gods, ka ga ni kar ka saka ni magana, kaje sama ka kwanta gobe after meeting ɗin sai ka tafi”
Ɗan kallon Ameen yayi, Ameen ya ɗauke kansa daga kallonsa yana pressing phone hakan ya sa ya kalli Mami yace
“Zan ɗauko kaya”
“Use Al’ameen’s” gyaɗa kai yayi ba don ransa ya so ba yace
“Okay” ganin yanayinsa tace
“Idan kuma zaka tafin, amma promise zaka zo goben”
“Ah ah i’ll stay back”
“Toh shikenan, Allah yayi albarka”
Ya amsa da “Amin” ba tare da ya kalli Ameen ba kawai ya mike ya nufi ƙofa Mami ta bishi da kallo. Ba’a jima ba Ameen ma ya miƙe yabi bayansa shima ya nufi ƙofa ta raka su da ido kafin ta sauke ajiyar zuciya ta miƙe ta wuce sama.
Kujera da ke compound Ameen ya ɗauka ya kai har gaban motar Aryaan da ya bar door ɗin gefen a buɗe ya zagaya side ɗin da ke buɗen which is not facing the compound ya ajiye kujeran ya zauna yana kallon Aryaan da ke zaune a driver’s seat kafafunsa na ta waje da cigarette a hannunsa da ya kunna yana sha a hankali, Ameen ya zauna yana kallonsa yace
“Har yanzu baka yi niyyar faɗa mini me ta maka ba kenan?” Ko kula Ameen baiyi ba sai yatsarsa da ya sa yana kaɗe jikin tabar tokar ta zube ya mayar bakinsa yana sha a hankali yana furzar da hayakin, shi kaɗai ya san irin ƙunan da ke damun zuciyarsa.
Ameen ya kai hannu ya zare taba ɗaya daga kwalin da Aryaan ya ajiye a gefensa ya sa a baki ya kalle shi yace
“ina lighter ɗin?” Kamar bazai tanka sa ba sai kuma ya ciro a aljihunsa ya jefa masa, ya ɗauka ya kunna shima yana sha yana taɓa wayarsa, sai da suka kusa shanye duka kwalin kafin Aryaan ya miƙe zai wuce ciki, Ameen yace
“Mami will perceive the smell stay back a little”
Komawa yayi ya zauna yana haɗe rai ya jingina kansa da kujera, shima Ameen ɗin bai kulasa ba ya cigaba da chat ɗinsa abinsa.
Murmushi Ameen yayi bayan wani lokaci ya kalleshi kafin ya ɗaga kiran dake shigowa wayarsa, Aryaan da idanunsa ke lumshe ya buɗe su yana kallon Ameen jin yace
“Kin samu kin ci abincin?” Ganin waya yake ya sa ya mayarda idanunsa ya rufe sai kuma kawai ya miƙe yayi wucewarsa cikin gida ya barshi a nan zaune.
#Banidahujja
#Maimoon
09041426598
https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q
❤️🌺BANI DA HUJJAH❤️🌺
Assalamu alaikum lovelies Bani da hujjah is a paid book, free pages kuma basu da yawa sosai, pls support me by making your payments kafin end of free pages! Thank you so much as you do, ga masu bukatar biya zasu tura 500 kacal zuwaga
7039695535
Palmpay,
Maimunatu Abdullahi muhd
Sai ku tura min evidence of payment ta 09041426598 on whatsapp
Idan kuma katin waya ne zaku tura 500 zuwa ga 07039695535
Thank you❤️
6.
A cike Babban hall din yake, duk wanda ke cikin gidan turaki yara da manya sun hallara saboda kiran gaggawa da Ameenu wazeer turaki ya Kira, the only people da basa nan are wadanda ke aure outside, hayaniya sai tashi yake kasa kasa a hall din da ke nan well structured, komai co-ordinated, kasancewar kujerun in rows a jejjere gwanin sha’awa kuma kowa ya zauna a inda ya kamata da iyalansa yasa suka yi looking rich and beautiful kana ganinsu kaga one big family, tun farkon ginin Wannan gida aka gina Wannan hall a cikin gidan kasancewar duk bayan wata shida sukan hadu dan tattauna dukkanin matsaltsalu da cigaba da ya faru a cikin gidan, idan disputes ne ayi settling, idan damuwa wani ke da shi a magance masa, wanda hakan ba karamin hadin kai ya janyo ba tsakaninsu over the years, Ba iya ahalin wazeer turaki bane a cikin estate din hasalima shi wazeer turaki and two of his brothers Lameer turaki da Nazeer turaki sune suka hadu suka Samar da Turaki family house! Sai dai Allah bai yi musu tsawon rai ba hakan yasa bayan rasuwarsu ya kasance kamar Wazeer shine Uba kuma kaka ga dukkanin ahalinnashi da na yan uwansa.
Duk da sai bayan wata shida ne scheduled lokacin meeting wanda Akan gayyato har wadanda aure ya rabasu da gidan, amma duk da haka a duk lokacin da wani ya Kira meeting din gaggawa Akan amsa ko da kuwa waye ne dan sauraran matsalarsa. Kamar dai yadda a yanzu aka taru saboda uncle Ameenu.
da yawa sunzo amma still wasu sai uzuri suka bada a cewarsu ya fiye korafi yanzu haka Ba wani Abu mai muhimmancin azo a gani bane.
Salwa ta ɗago daga danna sabuwar wayarta da daddy ya bata jiya bayan ta baro hospital saboda yadda ta saka su gaba da ƙorafin Aryaan ya ƙwace mata wayarta, ta kalli Ammi da ke gaisawa da Mami dake row ɗin bayansu tare da su siyama, juyawa tayi ta kalli su siyama amma before they could wave ta ɗauke kai ta cigaba da danna wayarta tana tauna cingam.
“Tofar da cingam ɗinnan kafin na mareki”
taji Amminta ta faɗa tana hararanta ganin yadda take cin cingam ɗin tana ƙas ƙas da shi
Ɓata rai tayi amma dai ta cire ta riƙe a hannunta tana kallon Amminta da ta mayarda hankalinta suna gaisawa da other relatives da ke side ɗinta, ji tayi zaman ya isheta tun kafin a fara meeting ɗin, ita bata ma san meyasa daddy ya kira meeting ɗinnan ba, bata taba son meeting ɗinnan ba its always boring to her.
jin hall ɗin ya ɗauki tsit sosai ya sa ta ɗaga idanunta da a hankali tana kallon farin tsoho mai ran ƙarfe, katanga kuma madogara ga duk wani ahalin Turaki, wato Wazeer turaki da kansa yana shigowa cikin hall ɗin da ke cike da ahalinsa, Escorted by Maza huɗu da suka kasance inuwa ga duka ahalin, wato Umar wazeer turaki, Aminu wazeer turaki, muhammad wazeer turaki sai lawal Nazeer turaki. kanta ta sunkuyar a hankali har Bappah ya samu waje a gaban hall ɗin ya zauna ya fuskanci ahalinsa for the countless time since them, as always kyakkyawar murmushi kwance akan kyakkyawa kuma kamilalliyar fuskarsa, su Uncle Ameenu ma duk zama sukayi, soldiers ɗin da escorts Umar wazeer turaki suka fice daga hall ɗin dan during that meeting su kaɗai suke kasancewa ahali ɗaya gabaɗaya babu bare.
Sai da bappah yayi adjusting mic ɗinsa kaɗan zai fara Magana duk cikin hall ɗin kowa yayi tsit kafin ya shigo hall ɗin, shirun da hall ɗin ya ɗauka ya sa duk aka juya ana kallonshi aga wani hamshaƙi ne har Bappah ya riga shi isowa, Salwa ta ɗaga idanunta itama tana kallonshi da mamakin ganinsa yau cikin manyan kaya though babu hula akansa amma ba ƙaramin kyau shaddar ɗinkin half jampa ta masa ba, sai dai kamar kullum kamar ko yaushe fuskarnan kamar wanda aka aikowa da saƙon mutuwa, har ya samu waje kusa da Ameen ya zauna a row ɗin farko ɓangaren maza kafin ta ɗauke kanta tare da ɗan jan guntun tsaki ciki ciki, shi dai bappah binsa kawai yake da kallo still da murmushi a fuskarsa har ya zauna unlike uncle Ameenu da kuma daddy Umar da suka haɗe rayukansu kamar basu taɓa murmushi ba.
Sai a lokacin Bappah ya gyara mic ɗin yana kallon dukkanin ahalinsa cike da alfahari da su ya musu sallama suka amsa ya soma da buɗe taron da addu’a kamar ko da yaushe! Duk da yadda shekaru ya ja amma cike da kamala yake magana, with same aura da yake musu magana da shi each and every meeting.
Briefly ya musu nasiha akan haɗin kansu, akan tsoron Allah da kiyaye hakkokin Allah a lamuransu wanda wannan jawabi ne da sun saba jinsa daga bakinsa baya taɓa gajiya da nanata musu wannan.
Sai da ya gama jawabinsa kafin ya juya ya kalli uncle Ameenu dake zaune ya haɗe rai yana hura hanci yana jira a iso gaɓar dalilin da ya sa ya kirawo taron, Bappah yayi gyaran murya yace
“Duk da akwai muhimmin dalili da ya sa aka kira taron but kafin in bada daman gabatar da wannan Umar will add one or two to abubuwan da na faɗa as usual”
Daddy Umar ya gyara mic ɗin gabansa fuskarsa ba yabo ba fallasa ya musu sallama suka amsa, ya soma magana a nitse wanda kamar ko yaushe ƙari ne akan Nasihar da bappah ya riga yayi, shi dai uncle Ameenu ko jin abinda yake faɗa baya yi dan takaici ne ya turnuƙeshi, shi fa ya kira meeting ɗin so meyasa dole sai an bawa wanda ba shi ya kira meeting ba damar magana kafin shi a basa, yanda daga shi har uncle muhammad suka zuba masa idanu zaka ɗauka sauraronsa suke yi amma kowannensu da saƙar da ke cikin zuciyayoyinsu.
Ko da aka bashi damar magana sake haɗe rai yayi kamar yanda ya kanyi idan ya shirya rashin mutunci kafin ya gyara zamansa akan kujera tare da sallama, aka amsa masa ana jiran jin dalilin wanann kira na gaggawa, kowa ya zuba masa idanu banda Aryaan da ko kallon stage ɗin baya yi.
“Ku sani ban kira wannan taro for jokes ba, na kira wannan meeting ɗinne saboda my daughter was kidnapped, locked up, and treated like bata da dangi bata da gata bata da dignity”
Ya juya ya kalli Aryaan dake zaune kamar ba akansa ake magana ba yace
“If anything should happen to my daughter ina so a sani cewa it would not be a family matter anymore! So nake a yi ma Aryaan iyaka da salwa, babu ruwanshi da ita! Bana bukatar ace wai za’a yi ma ƴata discipline i can do that myself, he was reckless with my daughters life da saboda stress da rashin cin abincin kirki sugar level ɗinta yayi dropping drastically, yesterday she coulndnt even stand da kanta! Sannan ina so Aryaan ya kalle ni ya faɗa min dalilinsa na aikata mata hakan”
Gyaɗa kai bappah yayi kafin ya maida dubansa ga Aryaan, Muryarsa calmly yace
“Aryaan” ya ɗaga idanunsa ya kalli bappah, kafin ya miƙe a hankali ya nufe shi, kwata kwata yanayinsa bai nuna damuwa ba sam, bappah dai kallonsa yake har ya ƙaraso ya tsaya a gefensa ya sunkuyar da kansa a hankali.
Sai da bappah ya ɗanyi shiru yana kallonshi na sakwanni kafin yace
“What happened?”
Kowa ya zuba ma Aryaan idanu yana jiran amsarsa, banda uncle Ameenu da yake jin bai ma kamata a tambayi Aryaan what happened ba kamata yayi kawai a yanke masa hukunci dai dai da abinda ya aikata ma Salwa.
Jin yayi shiru Bappah ya kuma magana yana kallonsa yace “me ya faru Aryaan menene dalilinka na aikata hakan?” Shiru ya kuma yi bashi da niyyar amsawa, daddy Umar da ke kallonsa shima yace
“Ba da kai ake magana bane?” Girgiza kansa kawai yayi a hankali ba tare da yace komai ba still, Bappah yayi murmushi yana kallonsa yace
“Je ka zauna”
“thank u” ya faɗa ƙasa ƙasa kafin ya wuce ya koma wajen zamansa, uncle Ameenu ya bishi da kallo kafin ya kalli mahaifinsa ransa idan yayi dubu to ya ɓaci duka sai dai babu daman magana, sai a yanzu yake da ya sanin kiran meeting ɗinnan, da ya sani da da kanshi ya ci uban Aryaan, ai ya manta cewa shi Aryaan ɗan favourite child ne kuma favourite jika babu abinda za’a masa.
“Salwa” kiran da Bappah ya mata ya katse tunanin da ya tafi, ta taso a hankali with her phone in hand ta iso har gabansa, yana murmushi yace
“Me ya faru ne Salwa tsakaninki da yayanki?” Sai da ta ɗan tura baki kaɗan kafin tace
“Babu!” Ba uncle Ameenu kaɗai ba har shi Aryaan sai da ya kalleta, Amminta ta yi ƙwafa kawai a hankali dan dama ta san za’a rina sai da tace masa kar ya kira meeting ɗinnan ƙaramin aikin Salwa ne ta kunyatasa gaban kowa da kowa, Bappah yace
“Tell me the truth! Me ya haɗa ki da shi? Me kuma ya miki?”
“Babu bappah” ta faɗa tana wasa da phone ɗin hannunta ba tare da ta kalli side ɗin babanta ba.
Daddy Umar ya haɗe rai yana kallonta yace “ke ba wasa aka kiraki ba tell us what happened”
“daddy babu fa” ta faɗa tana kallonsu duka, Daddy Umar zai kuma magana Bappah ya dakatar da shi tare da umartarta da taje ta zauna, tayi godiya itama ta nufi mazauninta tana ƙin haɗa ido da su Siyama da suke kallonta with mouth agape, duk da kowa a wajen ya san thats not what happened amma since ita wadda aka ma tace babu dole kowa yayi shiru kawai yana jiran hukuncin Bappah, uncle Ameenu ya bi ƴarsa da kallo ransa na kuma ɓaci da abinda Salwa ta aikata, toh ko dai he threatened her ne Aryaan ɗin dan zai aikata fiye da haka ma.
Bappah dai Nasiha ya shiga musu once again cike da fasahar sarrafa magana, ya musu nasiha akan fushi! Ɗaukar hukunci a hannu, da kuma barin emotions ɗinsu yana shiga tsakanin zumuncinsu, ba ko wani issue bane ya kamata yayi turning into war, ƴaƴa duka nasu ne sannan duka iyayensu ne suma, ya sake tabbatar musu da cewa ba’a shiga tsakanin yara dan yanda sukayi handling case ɗin is far better than yadda iyayensu sukayi! Sosai yayi magana kafin ya bada damar a cigaba da gudanar da meeting ɗin kamar yadda aka saba idan akwai wani mai matsala ya gabatar da shi da dai sauran abubuwa da aka saba yi a kowace meeting!
Ba’a jima sosai da cigaba da meeting ɗinba Aryaan yayi excusing ɗin kansa Ameen na tambayarsa inda zashi ma bai basa amsa ba ya fice a hall ɗin dan ji yayi ya gaji da zama a ciki, ya ɗan tsaya a wajen hall ɗin yana kallon motoci birjik dake harabar kafin ya fara tafiya a hankali da ƙafa expression ɗinshi unreadable.
Bai nisa a tafiyar ba ya jiyo kamar murya a bayan motar da ke pake a ƙofar Muhammad wazeer turaki, hakan ya sa ya ɗan dakata.
“Haba sweetheart! Ke fa daɗina da ke you look and act like kin waye amma sam baki waye ba! Ke kinsan ina sonki amma kiyi ta wani behaving kamar yar ghetto”
Harararsa tayi tace “ni dai ka sake mini hannuna yaya hamza bana so or else i’ll tell daddy” ya sake mata hannunta yana murmushi yace
“To komai ne sai kin faɗa ma daddy ehn daddy’s princess! Amma tell me meyasa kika rufa ma yaroncan asiri bayan duk abinda ya aikata miki” jingina tayi da ɗaya motar da ke wajen tana pressing phone ɗinta tace
“Cause da kaina nake so in rama ai na san ko na faɗa babu abinda za’a masa da ya wuce nasiha ko faɗa ni kuma i want to make his life a living hell, zai san ni yayi ma……” maƙalewa maganan yayi bayan haɗa ido da shi a tsaye a wajen facing them! Ta miƙe daga jikin motan tana kallonsa tare da ɗan ja da baya, hamza ma ya ɗaga idanunsa ya kalli direction ɗin da take kallo ganin Aryaan ya miƙe shima daga jikin motar yana haɗe rai yace
“Whats the meaning of that?” Ko kallonsa baiyi ba sai Salwa da yake kallo da ta saka hannu ta riƙe gefe da gefen gown ɗinta, ya ƙare mata kallo daga sama har ƙasa dan shi bai ma san sanda ta fice a hall ɗin ba kafin yace
“Zo ki wuce ki koma” ta ɗan ja baya tana kallonsa tare da shagwaɓe fuska!”
“Are you deaf? Dumb? Both?” Ya tambaya strictly yana kallonta, da sauri ta zo ta wuce shi tana tura baki idanunta cike taf da hawaye.
Hamza ya kalleshi rai ɓace yace
“kai a su waye zaka ce sai ta koma? Miye haɗinka da ita” kallo ɗaya kawai ya masa ya juya bi bayanta, sai sauri take yi kar ya cimmata gashi heels ne a ƙafafunta, ya harɗe hannunsa a bayansa yana tafiya a hankali a bayanta ba tare da ya kulata ba, saurin da take yi ya sa ta take gefen gown ɗinta tayi baya baya zata faɗi yayi saurin ja da baya ta faɗi a ƙasa ta fasa ƙara tana yarfe hannunta hawaye na gangarowa kan kuncinta, tana kallonsa ganin yadda ya ɗan ja baya ya barta ta faɗi, he didnt even attempt to help her kuma fa da yayi niyya da zai iya tare ta tunda ba wani nisa ke tsakaninsa da ita ba amma shine ya matsa ya barta ta faɗi har ƙasa, ganin tana ƙoƙarin kifa kanta ta cigaba da kuka yace
“Ta shi ki wuce ciki” ta ɗago idanunta da ya jiƙe da hawaye tace
“Ni bazan iya ba!” Ganin kallon da yake mata ya sa tace
“Ƙafana ne ya bugu fa yaya”
“Tashi nace before i slap you” ya faɗa yana mata mugun kallo, a hankali ta soma ƙoƙarin miƙewa yana kallonta har ta miƙe kafin yayi gaba ya barta a tsaye, ta bishi a baya tana tafiya a hankali a cikin zuciyarta kuwa Allah ya isa kawai take ja masa tana karkaɗe jikin gown ɗinta da ya taɓa ƙasa, haka ta bishi a baya har cikin hall ɗin tana kallon yadda yake tafiya a nutse gashin kansa ya kwanta ta bayan kansa da yake babu hula kayan jikinsa kamar wanda yayi highlighting haske da haibarsa.
Shi ya fara shiga cikin hall ɗin kafin ta shigo tana biye da shi a baya, Ameen ya dinga kallonsu da mamaki kamar yadda