Showing 27001 words to 30000 words out of 30393 words
ta tabbata kukan da ta wuni tanayi tun magribh idanunta ya kumbura amma taji shiru. Ta ɗaga kanta tana kallonsa jin takunsa har ya ƙaraso ya zauna a kujerar da ya tashi ya soma cin abincinsa, bata tambayesa ba itama kawai ta zauna ta soma cin nata, two spoons kaɗai yayi ya sake kallonta yace
“Amma taci abinci ne kafin ta kwanta..” Ammi ta girgiza kai bata ce komai ba
“Ta yaya za’a yi ki bar yarinya tayi bacci bata ci abinci ba fisabilillah? Idan ulcer ya kamata what are you going to tell me? Kina abu kamar ba ke kika haife ta ba? Haba dan Allah” ko kallonshi Ammi bata yi ba ta cigaba da cin abincinta, ya ture kujeran ya miƙe tare da goge bakinsa da tissue ya kurɓi ruwa ya wuce sama abinsa, sai da ta kalli abincin da ya bari kafin ta cigaba da cin abincinta abinta….
“Happy birthday to you! Happy birthday to you…” pausing yayi yana kallon Al’ameen, siyama da Lailerh a palourn dukansu kayan bacci ne a jikinsu sai hular birthday dake kansu da cake a hannun Siyama, shi kwata kwata ya manta ma birthday ɗinsa yau ne, ya ƙarasa saukowa ƙasa sanye da workout wears ɗinshi yana ƙaƙalo murmushi yace
“Ba zaku makaranta bane?” Lailerh ta ƙaraso tana ƙoƙarin saka masa birthday cap tace
“Bamu da early lectures dukanmu! Happy birthday Yaya” ya bari ta gama saka masa cap ɗin kafin ya ɗan bata side hug yace
“Thank you lil sis” itama siyama ajiye cake ɗin tayi ta zo gabansa tana faɗin
“Happy 30th birthday Yaya, Allah ya ƙaro shekaru masu albarka”
“Thank you” ya faɗa yana kallon Ameen da shima yace
“Happy birthday” a taƙaice ya amsa da “tnks” yana cire cap ɗin ya ajiye yace
“Ku je ku shirya ku tafi school” Mami ta fito daga kitchen tana kallonsu da murmushi a fuskarta, ƙarasawa yayi kusa da ita yace
“Good morning Mami”
“Morning, Allah ya ƙara maka shekaru masu albarka, ya ƙaro maka hankali ya baka mata ta gari cikin shekararnan”.
“Amin” ya amsa a hankali.. dai dai lokacin kuma aka turo ƙofar palourn aka shigo, duk kallonta suka kamayi, Abida ta shigo cikin palourn tana shining teeth tace
“Happy birthday yaya Aryaan, my favourite cousin” yana murmushi yace
“Thank you Abida how are you”
“I’m fyn fav” kafin ta juya ta kalli Mami tace
“Good morning”
“Morning” Mami ta amsa tana kallonta rabonta da gidan ta manta amma bata yi mamaki ba dan ba ita Mami kaɗai ba kowa ma ya san meya kawota! ‘Aryaan’
Ɗan kallon Ameen tayi tace “good morning yaya Ameen”
“Morning Abida, ya shaheeda kuna waya?”
“Eh munayi” ta faɗa tana bin bayan Aryaan da ya nufi ƙofa zai fita, duk suka bisu da kallo, Lailerh da siyama suka taɓe baki tare da nufar sama abinsu…
Jerawa Abida tayi da shi tana ta masa hira telling him how much she missed him da baya gidan, ya ɗan kalleta yace
“Ke baki da school yau ne”
“Kawai bazan je bane yaya i’m tired of this school wallahi” ya gyaɗa kai kawai bai ce mata komai ba suna cigaba da tafiya a jere, Salwa dake saman balcony ɗin gidansu sanye da kayan bacci dan tashinta kenan Ammi tace taje tayi watering flowers dake wajen sai hamma take yi, hammar ce ta katse hangosu da tayi suna tafiya a jere suna magana ta bisu da kallo tana zuba ruwa a flowers ɗin, haka kawai jininta sam bai haɗu da Abida ba, ko ga maciji basa yi ita da Abida ganinsu yanzu tare da Aryaan yasa ta ja dogon tsaki ta ajiye butan ruwan, a ƙasan ranta tana faɗin
“Birds of the same feather…” ta wuce ta buɗe slide door dake wajen zata shige cikin gidansu, dai dai lokacin ya kalli side ɗin balcony ɗinsu, bayanta kawai ya gani da gashinta da ta tufke ta shige ciki ta juyo zata rufe door ɗin suka haɗa ido, murguɗa masa baki tayi ta rufe ƙofar, yayi shiru yana kallon door ɗin da ta rufe kafin ya ɗauke idanunsa tare da gyaɗa kai kawai ya cigaba da tafiya sam baya ko jin abinda Abida ke faɗa….
Har sai da ya gama duk wani workout da zaiyi Abida na biye da shi, ji yayi kamar ya kore ta amma dai ya rabu da ita.
“Wai yaya har ka gama” ta faɗa ganin he’s heading home
“Eh” ya bata amsa a taƙaice fuskarsa a haɗe, ta bishi a baya jikinta a sanyaye ganin yanda ya amsata kamar suna faɗa.
Suna shigowa layin ya hango motar driver ɗin salwa a pake a wajen gate ɗinsu yana jiranta, ya juya ya kalli inda ya ganta ɗazu kafin ya kalli gate ɗinsu, daidai lokacin ta fito dressed beautifully ta rataya expensive tote bag hannunta riƙe da labcoat da dama shi ta manta ta shiga ɗaukowa, kallo ɗaya ta musu ta shige motar tana kallon driver ɗinta tace
“Yi sauri mu tafi kafin su yaya su iso” tada motar yayi yana amsa mata da “toh” ya ja suka wuce su, Aryaan yayi guntun smirk dan a yanzu ko lokacinta bayi da shi amma tabbass zaiyi lokacintane ta gama guje gujen…
Abida ta tsaya a bakin gate ɗin Mami tana kallonsa tace
“Zan wuce gida Yaya Aryaan”
“Okay” kawai ya faɗa yana tura gate ɗin ta bishi da kallo har ya shige kafin ta wuce abinta.
A compound ya tarar da Siyama da Lailerh musa zai kaisu makaranta suma, ya wuce su ya shige cikin gidan ba tare da ya ce musu komai ba dan gabaki ɗaya idan ya tuno project ɗinnan ji yake ransa na lalacewa.
#Banidahujja
#Maimoon
09041426598
https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q
🌺BANI DA HUJJAH🌺
Last free page….
Assalamu alaikum lovelies Bani da hujjah is a paid book, free pages kuma basu da yawa sosai, pls support me by making your payments kafin end of free pages! Thank you so much as you do, ga masu bukatar biya zasu tura 500 kacal zuwaga
7039695535
Palmpay,
Maimunatu Abdullahi muhd
Sai ku tura min evidence of payment ta 09041426598 on whatsapp
Idan kuma katin waya ne zaku tura 500 zuwa ga 07039695535
Thank you❤️
12.
Sai da yayi wanka kafin ya zauna ya janyo laptop ɗinsa trying to see idan zai iya recovering wani abin, ya buɗe screen ɗin ya tsaya yana kallon folder ɗin aikinsa amma empty ba komai a ciki, ɗaya bayan ɗaya ya duba files ɗin duka empty ya lumshe idanunsa a hankali tare da jingina kansa da headboard sai da yayi taking deep breath kafin ya buɗe idanunsa ya maida su kan laptop ɗinsa ya fara danne danne, duba recycle bin da recently deleted yayi yaga duk ta goge a wajen, ya shiga duba system files da temporary folders amma duk babu wani abu mai anfani a wajajen, at that moment ya sake tabbatar da cewa its gone! Wayarsa ya janyo a hankali ya buɗe ya fara scrolling bai san sanda ya sauƙe gajeren ajiyar zuciya ba, duk da ba wai duka komai ne yake kan wayartasa ba but atleast wasu abubuwan na nan ɗin, hotuna, screenshots da folders da ya tura wayarsa weeks ago ba dan yana saka ran zai yi anfani da su ba yanzu gashi sune zasu yi saving life ɗinsa..
Ya shiga zooming yana bin detail ɗin komai da ke jiki da kallo kamar mai haddacewa, thank God yana da structural note a wayarsa still shima zai taimaka duk da theyre still not enough amma theyll go a long way.
Ajiye wayar yayi ya koma kan laptop ɗin ya buɗe sabon file ya fara sabon aiki afresh, ya san ba lallai ya gama before date ɗin presenting ba which is next week! Amma duk da haka he’ll try his luck sannan zai demanding for extention of submission ɗin idan Allah ya taimakesa he’ll make it.
Wuni yayi aikin, sau ɗaya ya sauƙa yaci abinci shima Mami ce ta zo har ɗaki ta matsa masa ya zo yaci abinci, ciwon da kansa yake masa ya ƙaru sosai dole ya ajiye laptop ɗin around four dan zuwa Sallahn la’asar, a palour ya tarar da Ameen da ya dawo aiki ya baje a palour yana gisting Ammi akan law firm ɗinsu tunda itama retired lawyer ce kuma field ɗinta ne.
Ganin Aryaan zashi masallaci ya miƙe shima ya ɗauro Alwala a banɗakin palour ya bi bayansa zuwa mosque.. suna dawowa Aryaan ya kuma haurawa sama Ameen kuma ya yi zamansa ƙasa.
Mami tana kallonsa tace
“Aikin miye Aryaan kam yake yi ne? Yau fa wuni yayi aiki da ƙyar na samu yaci abinci..”
“Hmm” kawai Ameen ya faɗa yana danna wayarsa, Mami tace
“Why humming?”
“Salwa ce wallahi ta goge masa wani project da yake yi kusan wata huɗu fa kenan kuma next week zaiyi submitting ɗinsa..” Mami ta ɗan buɗa ido tana kallonsa tace
“Kai haba dai? Subhanallah amma gaskiya bata kyauta ba miye ma ya aiketa taɓa masa aikinsa ko bata sani bane?”
“Ta sani wallahi” ya faɗa yana miƙewa tsaye, Mami ta yi shiru tana ta kallonsa har ya fara haurawa kafin tace
“Amma zai iya sakewa ne a wannan guntun lokacin, tunda kace next week ya kamata ya bayar?”
Ameen ya ɗanyi murmushi kawai yana haurawa yace
“Maybe zai iya, kinsan shi da naci kamar kuturu, amma gaskiya fa kamar wuya…”
“Kai Allah ya kyauta, amma gaskiya ban ji daɗi ba wallahi” Ammi ta faɗa tana jin haushin abinda salwa ta aikata masa da kuɗira aniyar idan dai ta shigo sai ta mata faɗa.
A zaune Ameen ya tarar da shi still yana aikinsa, Ameen ya zauna gefen bed yana cire takalminsa yace
“Take it easy on yourself pls, kaima kasan bazaka iya sake yinshi kafin due date ɗin ba…” ko kulasa Aryaan bai yi ba, Ameen ya shiga wanka.
Bayan Sallar isha’i Aryaan ya fito toilet yana gyara gashin kansa da ya jiƙo da ruwa ya zauna a gaban side mirrow yana goge gashin da towel! Ameen da ke shan coffee yayi murmushi yana kallonsa yace
“Toh wa yace maka zuba ruwa a kai yana rage ciwon kai ai sai dai ma ya ƙara!” Shiru ya masa, Ameen ya kuma murmushi yana cigaba da kallonsa yace
“To ni yanzu laifin miye na maka kake wani shashshareni sai kace ni na goge maka aikinnaka…” sai a lokacin ya kallesa, fuskarsa a haɗe yace
“Kasan Allah either you ko babanta gwara ku fara neman kuɗin biyana abinda ta mini asara idan ba haka ba wallahi duk abinda nayi ma yarinyarnan a gidannan babu ruwan kowa da ni..”
“Mu biyaka? Mu biyaka fa ka ce…” Ameen ya faɗa yana dariya, kafin Aryaan ya amsa, wayar Ameen ya hau ringing ganin bappah ya ɗaga tare da gaishe shi har sannan da murmushi fuskarsa…
“Eh muna tare da shi gashi nan…Okay..toh” kallon Aryaan yayi bayan ya katse kiran yace
“Meyasa ka kashe wayarka ana ta nemanka” ya ɗaga idanunshi ya kalli Ameen
“Wa ke nemana?”
“bappah ne ya kirani yanzu wai idan muna tare da kai kaje yana nemanka yanzu” ɗauke kansa Aryaan yayi yana ajiye towel ɗin da ya gama goge kansa
“Kaji ina?” Ameen ya maimaita masa yana kallonsa da sipping coffee ɗinsa
“Ba zuwa zanyi ba.” Ya faɗa yana miƙewa daga gaban mirrow ya nufi kan gado..
“Kiran bappahn?”
“Eh” ya amsa a taƙaice
“And why is that” kamar bazai amsa ba sai kuma yace
“Aneela ce ta je ta same su wai na mata ciki na sa tayi aborting and many other sharri su kuma they believed her, bappah yace ta je zai ɗauki mataki shine wato har ta dawo saboda ita mayya ce.” Ameen ya buɗa ido sosai yana kallonsa yace
“Is she Mad?, why on earth will she do that!”
“Yes She’s indeed Mad, a kuma gabana ta faɗa”
“Amma lallai yarinyar nan ta cika mahaukaciya, kai kuma sai kace musu miye? Kaga irin yarinyar da kake so ka aura ina koh? yanzu a gaban su bappah tace ka mata ciki?.”
“You dont have to remind me” ya faɗa yana jingina kansa da allon gado..
“Yanzu dai tunda na riga na ce masa ga ka nan kawai kaje kar ka ƙara ma kanka laifi, da na san hakane da cewa nayi ma bama tare..”
“Ka rakani toh…” Aryaan ya faɗa yana kallonsa daga kwance
“Ah ah kaje dai zan zo kafin ka dawo bari na gama shan wannan..” ya faɗa yana ɗaga masa cup ɗin hannunsa, amma a zahiri shima tsoron zuwa yake yi kar a je a haɗa da shi
shiru yayi kamar ba zai tashi ya je ɗin ba sai kuma ya miƙe kawai ya nufi ƙofa yana gyara white shirt ɗin jikinsa Ameen ya bishi da kallon yana kai cup bakinsa..
Duk da dare ne amma ko ina tarr da haske ƙoyayen fitulun waje, a nutse yake tafiyarsa ransa duka a dagule, abubuwa ne da yawa suka haɗe masa a yanzu da ya rasa yadda zaiyi da su, kamar ance ya ɗaga kai ya hango salwa zaune saman motar Hamza, shi kuma yana tsaye a ƙasa, ta tanƙwashe ƙafafunta tana danna waya suna hira, ya kalli agogon hannunsa ƙarfe takwas da rabi, kasancewar dole ta gabansu zai wuce yasa suka hangosa tun kafin ma ya iso, buɗa idanunta Salwa tayi ta soma ƙoƙarin sauƙa a saman motar tayi ta kanta Hamza na mata magana ma ko kulashi bata yi ba ta samu ta sauƙa zata ɗiba da gudu, dan bata san meyasa ba haka kawai wani irin tsoronsa ne ya ɗarsu a ranta tun bayan abinda ta aikata masa, tana ƙoƙarin guduwa amma tuni Aryaan har ya iso wajen saboda yadda Hamza ke ƙoƙarin hanata guduwa yana tambayarta abinda ya haɗata da Aryaan ɗin da zata gudu dan ta gansa.. wafce hannunta tayi daga na hamza bayan ta galla masa uwar harara ta ɗiba da gudu Aryaan ya rufa mata baya, ko kaɗan bata kai labari ba dan bata yi nisa a gudun nata ba Aryaan ya cafkota tare da haɗe hannayenta biyu waje ɗaya ya ɗauke fuskarta da Mari, da sauri hamza ya nufo su kafin ya ƙaraso har Aryaan ya ƙara ɗauke ɗaya gefen da mari ya ƙara mata da ranƙwashi mai azababben zafi ta kurmu ihu tare da fashewa da mugun kuka, Hamza ya hankaɗa Aryaan ɗin yana faɗin
“Kai mahaukacin ina ne? Uban miye ta maka” dai dai lokacin Ameen da ya biyo bayansa ya hango abinda ke faruwa, ya nufosu da sauri yana faɗin “Subhanallah” Aryaan ya sa hannu duka biyu ya hankaɗa Hamza har sai da ya bugu da mota, ya juya ya koma kan Salwa da ke kuka wiwi tana bashi haƙuri, ganin yana ƙoƙarin zare belt ta fara ƙoƙarin riƙe hannunsa amma sam ta gagara miƙewa tsaye bare ta saka ran guduwa.
Ameen yayi saurin riƙe belt ɗin da ya ɗaga zai sauƙe a jikinta yana faɗin
“Aryaan miye haka!” Wani kallon banza ya masa tare da sake masa belt ɗin da ya riƙe ya kalli Salwa da ke hawaye ga shatin hannunsa kwance a farin kumatunta ya nuna ta da yatsa cike da kashedi yace
“Ban gama da ke ba…” yana gama faɗin haka ya nufi part ɗin bappah! Ameen ya ɗago Salwa da ta ƙara ƙarfin kukanta kamar zata shiɗe, Hamza ya miƙe zai bi bayan Aryaan Ameen yayi saurin hanashi yana faɗin
“Dan Allah ka rabu da shi kar ka biye masa, ba girmanka bane” kallon banza shima yayi wa Ameen ɗin zuciyarsa na tafarfasa ya juya ya nufi part ɗinsu, Salwa dai banda gunjin kuka babu abinda take yi, Ameen ya sa hannu yana duba face ɗinta da yayi ja yatsun Aryaan kwance ɓaro ɓaro yace
“Salwa bakya ji, yanzu dubi abinda kika ja ya miki, baki kyauta ba, wata da watanni ya ɗauka yana aikinnan kuma cikin sati mai kamawa zai yi submitting gashi kin masa asararsa, yanzu gashi kin ja ya doke ki a banza da hofi… sorry!” Ya faɗa cike da rarrashi
Sheshsheƙan kuka kawai take yi tana sauƙe ajiyar zuciya kamar zata mutu tana kallon wrist ɗin both hannayenta da suma suka yi ja saboda riƙon da yayi mata, rabonta da a dake ta har ta manta lokacin, shi dai Ameen ya cigaba da rarrashinta dan ko kaɗan baya son kukanta amma kuma this time around bashi da bakin magana tunda itace bata da gaskiya…
Sai da ya tsaya yayi composing kansa kafin yayi sallama tare da shiga palourn bappah, yanayin fuskokin parents ɗinsa a yau ya sa haka kawai yaji zuciyarsa ta buga da ƙarfi! Bappah na zaune fuskarsa expressionless, Uncle Ameenu ma na zaune idanunsa sunyi jajir har wani ruwa ruwa ne a cikin idanun na ɓacin rai, kasancewarsa fari yasa farar fuskarsa har jajaja tayi tsabar ɓacin rai, Dad ɗinsa ma fuskarsa a matuƙar haɗe, ransa a ɓace irin ɓacin ran da ya jima bai gani tattare da shi ba, uncle muhammad sammakal, kai harta uncle lawal da bai cika ɓacin rai ba shima yau fuskarsa a haɗe yake tamau! This time around harda Daada a zaune gefen Bappah itama fuskarta babu yabo babu fallasa…
Waje ya samu a ƙasa ya zauna yana lissafa duk wani laifi da he possibly did da zai ɓata musu rai har haka amma bai iya tuno ko da ɗaya ba.
A nutse ya gaishe su, bappah da Daadah ne kaɗai suka amsa sai uncle lawal. Bappah ya gyara zamansa ya fuskancesa tare da fara magana, daga yadda yake magana kaɗai ya tsinci ɓacin