Showing 3001 words to 6000 words out of 30393 words

Chapter 2 - BANI DA HUJJAH BOOK COMPELET HAUSA NOVELS PDF.docx

My Moon   

04 May 2026

529

ya ci kuɗi, tana yi tana kallon fuskarsa cike da nishaɗi, a hankali ya soma buɗe idanunsa da suka yi ja, saboda bacci da ɓacin ran da bai gama sakinsa ba, akanta ya sauƙe idanunnasa kafin a hankali ya yunƙura ya miƙe zaune

"Hi My love".

Ta faɗa tana kallon sa, da faffaɗan murmushi ɗauke a fuskarta, lumshe idanunsa yayi ba tare da ya amsa ta ba, yana jin yanda kansa ya masa nauyi, sai kuma a hankali ya miƙa hannu da niyyar ɗaukan wayarsa dake gefenta, da sauri ta rigashi ɗauka ta miƙa masa tana faɗin

"Love gani a kusa, komai kake so ka faɗamin in baka mana miye anfanina? Ga matarka a kusa ai baka bukatar yin komai da kanka” ta faɗa tana kashe masa ido still smiling

Wayar ya karɓa ba tare da yace mata komai ba, da wani irin sauri ya dirga daga kan gadon ganin yadda time ya wuce sosai yana bacci gashi ko sallah bai yi ba, itama da sauri ta miƙe tana kallon sa, ganin wanka zai shiga ya sa ta faɗin

"Can i join u?"

Har kamar bazai tanka ta ba amma sanin irin baƙin nacinta kamar tsohuwar mayya ya sa yace

"Aneela! i am not in the mood, so i will appreciate if you leave me alone".

daga haka ya shige bayi tare da rufo ƙofar

Binshi tayi da ido murmushin fuskarta na raguwa, ƙarar sauƙar ruwa da taji ya sa ta miƙe a hankali dan ta tabbata tunda yace mata ta tafi politely to idan har ya fito ya sameta he won’t welcome that, sai da ta tattare masa duk abinda ya zuzzubar a ɗakin which are very few, sannan ta gyara masa gadon kafin ta bar ɗakin tare da ja masa ƙofa, falon ƙasa ta koma ta zauna tana danna wayarta.

takun sakkowarsa da taji yasa ta dago kanta a hankali tana kallonsa, kamar yadda tayi tsammani farar shirt ce tass a jikinsa da jeans harda pcap, tayi shiru tana kallonsa lost in thought, Aryaan mai kyau ne, tasan ana cewa tana da kyau sannan tana ji da kyawunta, but Aryaan ƙarshe ne ga kyau ga iya ɗaukan wanka, bata San ya zata kwatanta shi ba but he’s just sooo different da sauran.

har ya gama sakkowa bata lura ba, bai bi ta kanta ba ya nufi ƙofar fita a palourn, ƙamshinsa da taji na yin nesa ya sata saurin buɗe idanunta sa ta lumshe tana faman murmushi, rufe ƙofarsa kawai ta gani, da sauri ta miƙe ta bi bayanshi, har ya buɗe mota tayi saurin zuwa gabansa ta tsaya, ta marairece cike da shagwaɓa tace

"Love" ya ɗage girarsa alamun “what?” Ganin sai kallonsa take zata ɓata masa lokaci yasa hannu ya mayar da ita gefe, zata yi magana ya rigata

"Aneela!!"

Yanda yayi maganan ya sa ta fasa tata maganar, ta dinga kallonsa ta tabbata wani ne ya taɓosa a can wani wajen daban cause thats not how he behaves with her, tana kallonsa har ya shiga mota ya tayar tare da barin gidan, ta bubbuga ƙafanta a ƙasa kafin ta juya a hankali ta shiga tata motar itama ta fice a gidan.

A bakin restaurant ɗin ya tsaya, ba tare da ya shiga ba ya ɗau wayansa, bugu ɗaya ya ɗaga, a taƙaice yace

"Jameel kawo min ina waje"

cikin mintuna 3 Jameel ya fito da uniform a jikinsa, da leda a hannunsa, window ya sauƙe sannan ya amshi ledan ya ja motarsa ya bar wajen.

A ƙofar gidan ya tsaya, ba tare da ya shigar da motar ba, ya ƙarasa ya shiga gidan, buɗe ɗakin yayi bayan ya saka black shades a idanunsa, a zaune ya sameta tana wasa da roban takeaway ɗin da yayi mata da safe, ta ɓaɓɓarka ledan gabaɗaya.

Ba tare da yayi magana ba ya tura mata ledan hannunshi gabanta,

bata ko kalli ledan ba ta ci gaba da wasa da yatsunta, har ya kai ƙofa zai fice sai kuma ya juyo yana kallonta,

"SALWA!!"

Ya kira sunanta strictly yana folding hannayensa a ƙirji



Idanunta da zuwa yanzu sun koɗe da kuka ta ɗago tana kallonsa da su, wani irin very Innocent face take dashi, wanda zaka yi tunanin ko yatsa aka saka mata bazata taɓa cizawa ba, wanda ke ɗauke da round face da big eye balls ɗinta masu masifar ɗaukar hankali, tana da hasken fata tare da very cute ƙaramin baki ga dimples guda biyu wanda ko da magana take ko kuka ko dariya lotsawa suke a hankali.

kallon second 10 tayi masa ta mayarda kanta ƙasa tana wasa da ƴan siraran yatsunta masu kyau, wasu hawayen da take ta riƙewa tuntuni kar su zubo suna biyowa shar agefen fuskarta.

daurewa yayi kamar baya so, ya furta

“Eat ur food"

daga haka ya juya, har ya ɗaura hannu akan handle ɗin sai kuma ya tsaya cak sakamakon tsinkayo sassanyar muryarta da yayi, Cikin rawar murya na kukan baƙinciki da ke cinta ta soma magana

"Yaya Please ka mayar da ni wajen Ammina, ka min rai, zan mutu anan, ni bana son wajennan, tsoro nake ji wallahi yaya kullum idan baka nan, ni kam ka kaini wajen daddyna...." tana kaiwa nan ta fashe da shagwabaɓɓen kuka that irritates him.

Sai da ya jira ta kai aya kafin ya buɗe ƙofar ya fice abinsa, Wani irin kuka ta sake fashewa da shi tana kallon ƙofa, wannan wace irin rayuwa ce, idan kasheta zai yi gwara mata ya kashe ta ta huta, idan har lissafinta dai-dai ne to aƙalla zata yi sati ɗaya da kwana ɗaya kenan a wannan gidan da ko falo bata ƙaunar fita, eight days fa kenan innalillahi wa inna ilahi raji’un.

Ganin idanunta har wani zafi suke mata da wani irin hazo hazo ya sata lumshe su a hankali tana jinginar da kanta a jikin bangon ɗakin. A hankali take furta “daddy…” cike da shagwaɓa wanda nature ɗinta ne magana a haka.

Sai da ya tsaya yayi isha’i kafin ya wuce gidan, a ranshi yana jin kamar ya fasa zuwa ya wuce gidansa.

Sauƙe glass ɗin motarsa yayi yana kallon soldier ɗin da ke riƙe da bindiga fuskarsa a matuƙar haɗe, ɗaya daga cikin abinda ya sa ya tsani gidannan kenan, ba tare da ya kula maganar da yake masa ba ko na sauran soldiers ɗin da ke gadin wajen ya zuge glass ɗin ganin sun basa hanya ya wuce ciki

A tangamemen gate ɗin estate ɗin yayi horn, ɗaya daga cikin sojojin da ke gadin gate ɗin ya leƙo da kansa, ƙaramin tsaki ya ja ƙasa ƙasa yana kallonsa daga cikin motar, ganin motar Aryaan ɗin ya sa sojan buɗe masa ƙofa da sauri, babban family house ne ko ince estate na gasken gaske wanda yaji komai na rayuwa, ajikin makeken plate name ɗin da ke gefensa an rubuta ‘THE TURAKI'S’. kai tsaye cikin gidan da yake nan tarrr da haske kamar ba dare ba ya nufa da motarsa, sai da yayi tafiya ta atleast 15 minutes akan shinfiɗaɗɗiyar titi dake ko ta ina a cikin gidan yana wuce gine gine wanda dukansu iri ɗaya ne, sai dai banbancin girma da decorations da wasu suka fi wasu, sannan ko wani gidan yana da gate ɗin da zai sada ka da shi, da security mai gadin wannan gate ɗin, a ko wani gate da sunan mai shi a jikinsa wanda duka ƙarshensa ke ƙarewa da TURAKI.

Tun da ya tunkaro gate ɗin gidan mahaifinsa yake jan tsaki ƙasa ƙasa saboda sojoji da ke nan burjik suna gadin gate ɗin kamar zasu hana waɗanda ke ciki mutuwa, tun kafin ya ƙaraso ya fara horn har ya iso gaban gate ɗin wanda da alama ginin wannan gidan yafi na kowa a cikin Family house ɗin gabaki ɗaya, duk kuwa da yawan gidajen dake cikin estate ɗin.

Buɗe masa gate ɗin sukayi ba tare da sun kula shi ba kamar yadda shima bai kula kowa a cikinsu ba, gate ɗin mai kyau sai dai bai kai na Main entrance na gidan girma ba, a gaban wannan part an rubuta CDS. UMAR WAZEER TURAKI, a babban parking space ɗin da zai iya haɗiye a ƙalla motoci 10 ko ma fiye yayi parking, sannan ya fito daga motar yana sake haɗe fuskarsa, a hankali yake tafiya kamar baya son yayi ya nufi main entrance na wani babban part wanda yafi ko wani part girma a gidan, murɗa ƙofan falon yayi a hankali ya shiga bayan ya zare glasses ɗin idanunsa, ya ƙare ma babban falon da ya gaji da tsaruwa kallo, ƙamshi ne kawai ke tashi a falon mai sa nutsuwa ga sanyin ac da ya ƙarama wajen wani pleasant daɗi, ba tare da ya zauna ba kawai ya wuce ya fara hawa stairs don ya tabbata kowa na gidan na ɗakinsa, sanin yanayin mai gidan na rashin son hayaniya sam yasa komai a nutse a keyi a gidan. har yakai sama sannan ya dakata yana kallon ɗakunan da ke jere a saman guda uku ta gefen daman sa bai bi ta kansu ba ya murɗa wata ƙofa dake gefen hagunsa, wata haɗaddiyar falo ne ta bayyane mai matukar kyau wanda ke ɗauke da ɗakuna biyu kacal a cikinta, sai wani ƙofa da zai sada ka da falo na biyu, sosai ya lumshe idanunsa jin kamshin da ke tashi a falon kafin ya ƙarasa ciki, nan ma babu kowa, ɗan jim yayi kafin ya nufi ɗayan falon yana addu'ar samun Dad anan.

Tura ƙofan yayi a hankali da sallama ɗauke a bakinsa, a zaune ya samesa a kan ɗaya daga cikin manyan kujeru na alfarma, a falon da ya ma gaji da tsaruwa, dan ya ma fi falon farko kyau sai dai bai kaisa girma ba, ƙafansa ɗaya akan ɗaya ga cup akan center table ɗin gabansa, da wata ƴar karamar littafi da yake rubutu a ciki that looks like jotter or a diary book.

ɗago idanunsa dake cikin fararen medicated glasses yayi ya zuba ma ɗan nasa idanu, kafin ya kawar da kai daga kallonsa ya cigaba da abinda yake yi ba tare da ya amsa sallaman ba, a hankali Aryaan ya ƙaraso gabansa, ya zauna a ƙasa ya sunkuyar da kansa yana kallon haɗaɗɗen carpet ɗin dake malale a ƙasa, cikin sanyin murya yace

"Ina wuni DAD"

bai amsa ba sannan bashi da niyyar amsawa sai ma miƙewa da yayi, yayi folding hannuwansa a baya ya soma tafiya towards ɗakin dake cikin falon.

Cikin sauri muryarsa har rawa take Aryaan yace

"Dad please!"

ɗan dakatawa yayi kafin cikin dakakkiyar voice ɗinsa da ke cike da command yace

"ARYAAN UMAR TURAKI! Leave immediately, sannan saƙon da baffaninka suka isar maka, make sure ka cika umarni, kwanaki 59 suka rage cikin sittin ɗin da na ɗibar maka, bring a wife before then if not you will leave me with no choice bayan na ɗaura maka aure da koma wacece, in tura maka gidanka, since ka fi ƙarfin zama a cikin ƴan uwanka".

daga haka yayi shigewarsa ɗaki tare da rufo ƙofan.

Wani irin zuciya ke cinsa yana dannewa, why! Me yasa shi da mahaifinsa are not in good terms at all, ya zo ne ya gana da shi akan aurennan but sam yaƙi sauraransa, ya ake so yayi? Ta ina zai nemo mata a wata 2 kamar wani magnet? Aneela ce ta faɗo ransa cikin sauri ya shiga girgiza kai

"Nooo banda Aneela" sai kuma ya miƙe dan yasan bayi da choice bayan Aneela ɗin.

#banidahujja

#Maimoon

09041426598

https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q

🌺BANI DA HUJJAH!!🌺

By Maimoon

3.

Zuciyarsa a dagule, fuskarsa a haɗe ya fito daga sashen mahaifinnasa, yana kokarin ficewa daga ɓangaren gabaɗaya suka kusa cin karo da mummy ya matsa baya a hankali ya bata hanya ganin shiga zata yi wajen Daddy, a taƙaice ya gaishe ta shima ciki ciki

“ina wuni” ko kallonsa bata yi ba ta shige ciki abinta ya bita da side eye kafin ya buɗe ƙofar shima ya fice a gidan, ba tare da kallen kallen komai ba ya buɗe motarsa ya shiga ciki ya tayar aka buɗe masa gate ɗin Cds. Umar wazeer turaki ya fice yana driving gently, a gaban gate ɗin barr Ameena wazeer turaki yayi horn ba tareda ya ko kalli opposite house ɗin da shi kuma aka rubutu DR Ameenu Wazeer turaki ba, aka buɗe masa gate ɗin ya shiga yayi parking yana kallon motar AMEEN dake parking space ɗin which means yana gida as expected. Bai samu kowa a palourn ba sai sanyin ac da ƙamshin turaren wuta mai daɗi nan ma, stairs ya nufa kanshi tsaye yana jujjuya key ɗin hannunsa.

“Aryaan?” Dakatawa yayi tare da juyowa yana kallon Mami da fitowarta kenan daga kitchen, ta ɗan buɗa ido tana kallonsa tace

“ashe dai kai ɗinne hamshaƙi” ɗan murmushi yayi kaɗan ya fasa haurawa ya dawo palourn ya zauna a kujera yana sake ƙirƙiro murmushi

“ina wuni Mami”

“Da ban wuni ba zaga ganni ne aryaan?” Shiru yayi kawai dan ya san dama dole sai tayi ranting in dai ta gansa, rabonsa da gidan ya kwana biyu tayi mita har ta gaji.

“Yau kuma Allah yayi ka tuna mu kenan Aryaan, yanzu abinda kake yi ya kyautu kenan? Yaro ɗan gata amma ka mayar da kanka kamar maraya?” Ta faɗa tana zagayowa ta zauna a kujerar da ke facing ɗinshi tana ta kallonsa keenly, Nan ma bai ce mata komai ba sai murmushi kawai da yayi, ta sauƙe ajiyar zuciya a hankali tace

“To Allah ya kyauta, ya kake toh? How have u been?” Sai a sannan ya amsa da

“Alhamdulillah Mami”

“Are u sure?” Gyaɗa mata kai yayi, tace

“Toh Allah yayi albarka, ya tsare gabanku da bayanku, ya baku abinda kuke nema duniya wa lahira, a cigaba da hakuri a kuma cigaba da yayyafawa zuciya ruwan sanyi, zama lafiya da kowa ya fi zama ɗan sarki, komai lokaci ne da shi haka zaka ga watarana kamar ba’a yi ba”

“Amin Mami” ya amsa yana jinginar da kansa da kujera, miƙewa tayi tana kallonsa tace

“AMEEN ɗin ai yana sama kaje bari nima in duba girki ya kusa gamuwa ma su lailerh zasu kawo muku” gyaɗa mata kai kawai yayi bashi da niyyar tashi, ta miƙe ta wuce kitchen, 10 minutes later ta kuma fitowa, da mamaki take kallonsa ganin har sannan yana zaune a wajen yana danna wayarsa, hakan yasa bata kulashi ba ta wuce sama dan kiran Ameen ɗin da kanta, tare suka sauƙo da wani matashin saurayi kyakkyawa wanda zasu yi sa’o’i da Aryaan sai dai ya fi Aryaan hasken fata da glasses a idanunsa dressed casual, ya kalli Ammi bayan ya sauƙo cikin palourn yace

“Ammi where is he?” Ammi ta ƙaraso cikin palourn tana kallonsa tace

“Ji iskanci! Anan fa na barsa shine ya kama hanya ya wuce bai ce min zai wuce ba? Kuma fa har abinci nace ya jira amma shine ya wuce ya tafi abinsa koh? Kirawo min shi kace nace ya dawo yanzu ya zo yaci abinci”. Ameen ya ɗan sauƙe ajiyar zuciya yana zama a kujera yace

“Ki ƙyaleshi kawai tunda ya tafi ba juyowa zaiyi ba kin sani” zama tayi itama a kusa da shi tace

“Al’ameen me ke damun ɗan uwanka ne?” Ya buɗa mata hannu alamun bai sani ba shima yana murmushi,

“Ya zaka ce min baka sani ba, bayan ure closer to him than anyone”

“Allah Ammi ban sani ba, but bari na watsa ruwa inje gida in same sa inji if there’s anything i should know” gyaɗa masa kai tayi tace

“Idan ya faɗa maka pls ka zo ka faɗa min”

“Okay Mami” ya faɗa yana miƙewa ya wuce sama murmushi kwance a fuskarsa

“Lailerh ta kawo maka abinci yanzu?”

“Ah ah idan na dawo zanci”

“Toh” ta faɗa tana kallonsa har ya haura kafin ta wuce kitchen dan duba abinda su lailerh da siyama ke yi.

Yana driving yayi dialing lambarsa yana ajiye wayar a gefensa bayan yayi connecting da speaker ɗin motar, sai da kiran ya kusa yankewa kafin ya ɗaga, Al’ameen yayi gyaran murya yace

“Malam kana ina ne?”

“Why?”

“Ban sani ba! Kana gida ko baka gida?”

“Bana gida!”

“Kana ina?”

“Doesnt concern u!” Murmushi Ameen yayi kawai ya katse kiran yana nufan gidan nashi bayan ya kalli agogo ƙarfe 10 saura.

Buɗe masa gate mai gadi yayi bayan yayi horn once, ya shiga yayi parking a kusa da motar Aryaan dake space kafin ya fito ya nufi cikin gidan, ba tare da knocking ba ya tura ƙofar palourn ya shiga ciki yana kallon ko ina, ganin baya ciki ya gyara glasses ɗin idanunsa ya nufi hanyar sama da takalmansa, motsi da yaji a kitchen ya sa ya dawo da baya ya nufi kitchen ɗin, a bakin ƙofa ya tsaya ya harɗe hannu a ƙirji yana kallonsa, yana tsaye a jikin counter da singlet baƙa a jikinsa against fair skin ɗinsa, yayi pairing ɗinshi da three quarter iya guiwarsa dat looks loose, Al’ameen ya kalli plate ɗin scrambled egg dake plate da toasted bread guda biyu a gefe, black tea da yake haɗa ma kanshi a lokacin ya kalla kafin yace

“Yaushe ka koyi girki bawan Allah” ko kallonsa baiyi ba, barin jikin ƙofan yayi ya nufe shi yana faɗin

“Wulaƙanci ne bana so, sai in juya in koma in da na fito, da ina da zuciya ma wallahi ba zaka ganni a nan ba, ko da yake Mami ce tace na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login