Showing 15001 words to 18000 words out of 30393 words

Chapter 6 - BANI DA HUJJAH BOOK COMPELET HAUSA NOVELS PDF.docx

My Moon   

04 May 2026

530

Su lailerh ke kallonsu don basu yi kama da dominsu aka haɗa wanann meeting ɗin ba.

7039695535

Palmpay,

Maimunatu Abdullahi muhd

N500

Thank you❤️

#banidahujja

#Maimoon

09041426598

https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q

🌺BANI DA HUJJAH🌺

Assalamu alaikum lovelies Bani da hujjah is a paid book, free pages kuma basu da yawa sosai, pls support me by making your payments kafin end of free pages! Thank you so much as you do, ga masu bukatar biya zasu tura 500 kacal zuwaga

7039695535

Palmpay,

Maimunatu Abdullahi muhd

Sai ku tura min evidence of payment ta 09041426598 on whatsapp

Idan kuma katin waya ne zaku tura 500 zuwa ga 07039695535

Thank you❤️

7.

Tun bayan meeting Aryaan ke zaune a cikin motarsa, ya ƙure ac ya kwantar da kansa kawai tunani kala kala na yawo a zuciyarsa.

Knocking glass ɗin da akayi ya sa ya buɗe idanunsa da ke lumshe ya kalli sashen da ake knocking ɗin, Ameen ya gani a tsaye a wajen yana ƙoƙarin sake knocking! Ya miƙe zaune tare da winding down yana kallon Ameen yace

“Ɗume?” (Miye?) in his native language wato fulani. Ameen yayi murmushi yace

“Yau kuma?” Bai jira amsarsa ba yace

“Bappah na nemanka……yanzu!” Mayarda kansa yayi ya jinginar after some seconds kuma ya buɗe motar ya fice ya nufi part ɗin bappah

Sallama yayi a ƙofar palourn aka amsa tare da bashi izinin shiga! Bappah dake zaune tare da daddy umar ya ɗaga ido yana kallonsa har ya ƙaraso ya zauna a ƙasa ya sunkuyar da kansa dan kwata kwata baya son haɗa ido da Dad ɗinsa not after everything that happened earlier.

Bappah yana murmushi yace “babban mutum ina ka tsaya har Aminullahi ya shigo kai banganka ba sai da na aika shi nemanka?”

“Ina mota bappah” ya faɗa a hankali yana ƙaƙalo murmushi, bappah ya gyaɗa kai

“To yayi kyau!” Ya faɗa yana mayar da hankalinsa kan ɗansa suk cigaba da maganan da suke yi hakan ya sa Aryaan ya miƙe ya nufi cikin ɗakin grandmum ɗinsu dan basu waje idan sun gama sai ya dawo!

A zaune ya sameta gefen gado tana lazimi, tana ganinshi murmushi ya bayyana a fuskarta tana cigaba da jan cazbah tace

“Wata sabon gani” murmushi shima yayi this time genuine murmushi yana ƙarasawa gabanta yace

“Ba wani wata sabon gani ai baki nemeni ba” tsohuwar cikin wasa ta kawo masa carbi ya kauce yana dariya ya zauna a ƙasa kusa da ita yana cigaba da dariya kafin yace

“Ba dai don halinki ba ina wuni”

“Ka manta da ni Aryaan” ta faɗa tana kallonsa fuskarta na nuna damuwa, ya kamo hannunta yace

“Ni na isa Daada, ya jikinki?”

“Liar! Ka manta da ni mana” Ta faɗa tana ƙwace hannunta, ya sake dariya yana faɗin

“Zaki fara drama ɗinki koh? Ta yaya zan manta ki loml”

“Uhm naji, ya aikin naka? Ya Asiya kana zuwa kana dubata kuwa” ta faɗa tana rage murmushinta, yanda tayi tambayar doesnt show she really cares idan yana zuwa ɗin kawai dai ta tambaya ne, shima murmushin fuskarsa ce ta ɗan fara fading yana matsa mata hannunta yace

“Alhamdulillah Daada, ina zuwa”

“Hmm, To Allah ya kyauta!, yayi albarka” ya amsa da

“Ameen, meyasa baki zo meeting ba kika barshi shi kaɗai ya zo?”

“Uhm bazan iya bane bayana ciwo yake kaikam, ga ƙafa ma ya sakani a gaba” ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa ta ɗauko masa ruwa a fridge

Ganin abinda take shirin yi yace

“Kinga bar ruwanki, ke bazaki bawa mutum abu mai daɗi ba sai ruwa!”

“To me kake so in baka mai daɗi muhammad” Ta faɗa tana komawa ta zauna tana kallonsa

“Kinsan me nake so?” Ta girgiza kai tana kallonsa

“Kudi…” dariya tayi tana ɗan tari kaɗan tace

“Kudi kuma wanne kake so Aryaan? Me zakayi da kuɗi, ai akan kuɗi gwara ma kace mata kake so in sama maka kayi aure tunda ka gagara samowa da kanka, Your dad and uncles kullum cikin complain ɗinka suke Aryaan” kallonta yayi sai kuma yayi shiru walwalarsa na ɓacewa kamar bashi ke murmushi yanzu ba. Ta zuba masa idanu tana ta kallonsa tace

“Idan kana da wata damuwa ne Aryaan ka faɗa ma Daada” ya lumshe idanunsa ya buɗe yana kallonta yace

“Babu” zata yi magana kenan sai ga bappah ya shigo cikin ɗakin yana kallonsu yace

“Miye ake tattaunawa” Daada ta kalleshi tace

“Maganar dai da baya so ita nake mai shine ya wani ɓata fuska kamar wanda nake bashi mummunan labari” bappah ya ƙarasa ya zauna a kujera yana kallon yanda Aryaan yayi kicin kicin da face, yace

“What is your problem Aryaan! Yanzu maganan da muke yi da Umar kenan akanka! Yace ya gaji da halinka kuma lokacin da ya ɗiba maka na aure idan ya kai bazai ƙara maka ba dole sai kayi auren, you will soon be thirty what is the issue?” Shiru yayi yaƙi cewa komai, bappah ya dubi daada yace

“Ko ya faɗa miki matsalar” girgiza masa kai tayi alamun



“Ah, ah” bappah ya sauƙe ajiyar zuciya yana kallonsa yace

“Aryaan! Why do you make things difficult for yourself?meyasa bazaka buɗe baki ka faɗi abinda ke damunka ba kamar yadda kowa ke yi? Duk abinda zaka aikata baka duba miye zai biyo baya sai dai kawai ka aikata, your dad is very angry at you! daga nan dama kaje can ka bashi haƙuri kaji koh?”

Gyaɗa kai yayi a hankali ba tare da ya kallesu ba, bappah ya cigaba yana kallonsa

“Now tell me miye salwa ɗin ta maka uhm sarkin ɗaukan hukunci a hannu?” Bai san sanda ya ɗanyi murmushi ba, Daada ma murmushi tayi tana kallonsa cike da sonsa.

Ya gyara zamansa yana kallon bappah yace

“Bappah ni fa ba kidnapping ɗinta nayi ba”

“To me kayi?” Ya sake gyara zamansa yana kallon bappah yace

“Ban san me yasa duk abinda yarinyar nan za tayi a gidannan kuke kyaleta ba bappah, infact she’s becoming a bad influence to sauran yaran gidannan! Babu mai mata faɗa babu mai taka mata birki fisabilillah?”

“Inji wa ba’a mata faɗa” daada ta katse shi tana kallonsa, ya mayarda kallonsa gareta yace

“Okay kinsan cewa morocco zata je wani stupid birthday wai na friend ɗinta, bday ya wuce all states na nigeria har sai sunyi flying out? Kuma kowa ya zuba mata idanu babu mai kwaɓanta? As small as she’s har zata iya flying out alone for birthday tsakani da Allah fa?” Da mamaki bappah da Daada suke kallonsa dan sam basu san da maganar ba ko da suka ji ta shiru fiye da sati bata lekosu ba Ameenu cewa yayi ta tafi relative ɗin Amminta!

Daada ta tafa hannuwa tana kallonsa tace

“Amma Ameenu dai bashi da hankali! Kai innalillahi” ta juya ta kalli mijinta da shima ita yake kallo tace

“Kuma fa babanne ya goya mata baya haka wallahi na sani yanzu haka Amminta ta hana suka ƙi hanuwa”

Bappah ya gyaɗa kai yace “you did right amma da ka sani you report to me or your dad ba ka ɗauke ta ka kaita wani waje for this long ba, duk da anyi avoiding drama ɗin da suka faru saboda hakan”

Aryaan ya gyaɗa kai a hankali tare da faɗin “toh ayi hakuri in sha Allah it wont repeat itself” a zuciyarsa kuwa shi ya san ba iya wannan dalilin bane ya sa ya rufeta! Ya jima sosai yana tarata dama already kwata kwata yarinyar bata yi masa ba rawan kanta da rashin kunyarta yayi yawa da ya sa ko kadan baya son yarinyar! Duk cikin ƙannensa she’s one da baya son ko ganinta saboda ya tsani sangarta a rayuwarsa, but duk da haka ba zai iya canza ta a matsayin jininsa ba hakan ya sa da yaji labarin she’s flying out for birthday a bakinsu lailerh kuma wai har Amminta ta hanata amma Uncle Ameenu yace a barta tayi abinda take so ya ƙudurta bazata je ba! dan birthday ne irin na marasa ji marasa kuma Kamun kai zasu je yi can ɗin! Hakan ya sa ya aikata abinda ya aikata, kuma ya tabbatar sai after birthday ɗin kafin yayi releasing ɗinta shima kuma cause of her school da zasu yi resuming cikin week ɗin, cikin satin da take wannan gida ko kaɗan Uncle Ameenu bai kawo Salwa bata Morocco bane saboda Aryaan always replies his messages da yake turawa salwa time to time! Wannan yana cikin dalilin da ya sake harzuƙa uncle Ameenu ganin rainin wayon ya kai rainin wayo! Aryaan wish yarinya ce da zai iya hukuntawa kamar su lailerh da tabbass duk wani rashin ji wallahi sai ta daina shi saboda yadda zai gyara mata zama amma inaa, duk wani abu da ya haɗa da Uncle Ameenu baya son shigarshi, shima wannan ɗin dana sanin shiga maganar yake da ya sani ya barta taje duk abinda tayi ruwanta ita da babanta.

“Allah ya kyauta” muryar bappah ya katsesa dan duk maganar da suke ma shi bai ji ba, bappah yana kallonsa yace

“To kai kuma back to maganar da baka so, akwai ko babu”

Murmushi yayi yana shafa kansa ya kishingiɗa da kujera yace

“Babu Allah bappah” bappah ya daina murmushin da yake yi yana kallonsa yace

“Ban gane babu ba ka ɗauki abinnan wasa koh?” Langaɓe kai yayi yana kallon bappah yace

“Dan Allah bappah kayi ma daddy magana wallahi ni bani da kowa ni ban shirya ma aure ba bappah, Daada pls talk to them! Ga nan Ameen shima ace ya kawo mata mana bappah”

“Sai yaushe kenan zaka shirya ɗin? Banda shashanci shekara kusan talatin kace baka shirya ba! Shi Aminullah ai baya rashin ji shiyasa basu damu ba ko da yaushe ya gabatar da mata is fyn amma kai kam dole kayi aure idan ka ajiye iyali zaka fi natsuwa i’m with your dad and uncles on this”

“Innalillahi! Daada talk to him pls he listens to you! Wallahi idan ba dai auren dole zaku mini ba ni bani da wata i’m serious, kuma a wata biyu ni bansan a ina zan samo ba”

Shiru bappah yayi yana kallonsa kamar wanda wani tunani ya zo masa sai kuma yayi murmushi yace

“Its alright! Tashi kaje ka bawa babanka hakuri kaje sai da safe” ganin yanda bappah ke murmushi yasa yace

“Thank you bappah for understanding me, dan Allah ka musu magana”

“Zan musu, tashi kaje” tashi yayi yana shafa kansa yace

“Nagode bappah, sai da safe! Sai da safe Daada!” Suka amsa masa da

“Allah ya tashe mu” ya juya ya nufi barin ɗakin, sai da ya fice kafin Daada ta kalli bappah

“Amma da ka bari yayi auren wallahi ni bana son rashin jinnan da yake yi wallahi”

“Zaiyi! Kafin ma wata biyunnan zaiyi kar ki damu”

“Ta yaya?” Ta tambaya tana kallonsa

“I just thought of something yanzunnan……..”

Later that day da dare suna zaune a dining suna cin abinci, Mami ta kalli Aryaan dake ta juya cokali amma ko loma ɗaya baiyi ba har sannan, kallon Ameen tayi da ke cin abincinsa a nutse ta ajiye cokali tace

“Aryaan ci abinci mana” Ameen ya ɗaga ido ya kalleshi sai kuma ya fara dariya! Mami ta kalli Ameen tace

“Kai kuma fa?”

“Wai fa Daddy Umar ne yace masa ya kwaso kayansa ya dawo cikin gida ya bar wancan gidan nasa with immediate effect shine tun da ya baro wajensa yake ta cika yana batsewa!”

Mami ta ɗanyi murmushi tana kallon Aryaan da ya ɗaga idanunsa yana kallon Ameen fuskarsa a mugun haɗe.

“Da yaushe ne yace maka hakan Aryaan?” Mami ta faɗa tana kallonsa, ya sauƙe idanunsa yana juya rice yace

“Ɗazu ne”

“To miye abin damuwan dan ance ka dawo cikin gatanka Aryaan! Cikin ƴan uwanka!” Shiru yayi bai ce komai ba, ta zuba masa ido tana kallonsa kafin tace

“Idan ma baka son zama can part ɗinku ga nan gidan sai ka tattaro kayanka ka dawo nan kawai kaaji” sai a sannan ya kalleta ya gyaɗa kansa a hankali, feeling a little bit relieved dan tunda Dad yace ya tattaro ya dawo gidan babu abinda yake tunani irin zaman gidan Dad ɗinnasa da baya jin zai iya! Ameen dake murmushi yace

“Gaskiya ya tafi gidansu kar ya takura mini”

“Sai dai kai ka tafi gidanku shikam nan ne gidansu” Mami ta faɗa tana murmushi.

“Yanzu yaushe zaka kwaso kayannaka?”

“Gobe in sha Allah”

“To Alllah ya kaimu” duk suka amsa da

“Amin”

Salwa ce ke saukowa daga sama waya kare a kunnenta tana magana da raliya da sai jiya suka dawo daga morocco ashe, tana sanye da girlfriend jeans da top mai kyau da ya nuna flat tommy da perfect figure ɗinta, kanta ba ɗankwali sai siririn headband da ta sa a ta gaban gashin, ganin Amminta a palour tayi ma Raliya sallama tana ƙarasawa cikin palourn ta ɗan rungume Ammi ta baya kafin ta zagayo ta zauna a ƙasa kusa da ita, Ammi na kallonta tace

“Kinyi isha’i?”

“Nayi Ammi”

“Tsakaninki da Allah kinyi”

“Wallahi Ammi fa nayi” ta faɗa a shagwaɓe

“Idan ma baki yi ba ke kika sani! Tsakaninki da ubangijinki, kuma kin sani Allah yana kallonki”

“Ammi nayi fa” Ammi bata sake kulata ba ta cigaba sauraron voice note ɗin da only sister ɗinta ta mata on whatsapp.

Miƙewa Salwa tayi ta nufi hanyar ƙofa Ammi ta kalleta tace

“Ina zaki da darennan!”

“Wajen Siyama zan duba abu ne a anatomy textbook ɗinta”

“A haka zaki fita babu ɗankwali? Ke kam miye ɗankwali ya miki ne a rayuwarki Salwa? Wallahi ni banga anfanin islamiyyar da kike zuwa ba Salwa kin fi so ki dinga yawo da kai a buɗe mala’iku na tsine miki koh? Kin fi so ki je ki kwaso ma kanki abinda bazaki iya ba koh salwa! Wallahi na gaji da magana akanki ki kiyayi randa zan fara saka hannu a jikinki saboda ɗankwali Salwa!” Tsayawa tayi a bakin ƙofa tana kallon Ammi a shagwaɓe kamar zata yi kuka, ganin Ammi ta miƙe ya sa ta wuce sama da gudu tana hawaye, Ammi ta bita da kallo tana faɗin

“kuma ki cire cingam ɗinnan a bakinki dan ubanki..” ganin har ta riga ta haura ya sa ta koma ta zauna tana cigaba da replying sister ɗinta wanda ba maganan kowa suke ba face na Salwa still.

#banidahujja

#Maimoon

09041426598

https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q

🌺BANI DA HUJJAH🌺

Assalamu alaikum lovelies Bani da hujjah is a paid book, free pages kuma basu da yawa sosai, pls support me by making your payments kafin end of free pages! Thank you so much as you do, ga masu bukatar biya zasu tura 500 kacal zuwaga

7039695535

Palmpay,

Maimunatu Abdullahi muhd

Sai ku tura min evidence of payment ta 09041426598 on whatsapp

Idan kuma katin waya ne zaku tura 500 zuwa ga 07039695535

Thank you❤️

8.

Kamar yadda ya faɗa ma Mami washegari ya je gidan dan ɗauko boxes ɗinshi, har cikin zuciyarsa ba son komawa family house ɗinnan yake ba amma yadda ran Dad ke ɓace ba yadda ya iya, babu any room for musu.

Boxes uku yayi na kayansa waɗanda zai buƙata dan ya riga ya sa a ransa ba wai ya koma gidannan bane forever, ko ya zaiyi zai shawo kan dad ya barsa ya bar gidannan, yanzu dai he’ll be there for the meantime tukunnan.

Dakatawa yayi da haɗa kayan ya riƙe jikin siff ɗin yana kallon akwatunan sai kuma ya ɗan ja tsaki ƙasa ƙasa, kwata kwata rayuwarsa is messed up! Baya jin daɗin rayuwarsa ko misƙala zarratin! Duk da kasancewar mahaifinsa babban soja, family ɗinsa well reputed sunansu ya zaga ko ina, amma deep inside of him ya rasa what is the missing piece da babu a rayuwarsa da yake sa yake jin rayuwar a wargaje, menene wannan missing piece ɗin da ya kamata ya tattaro rayuwarsa duka ya saka glue ya manne su waje ɗaya.

Yana saukowa da akwatinan palour ya fara kakkashe appliances na gidan aka buɗe ƙofa, ya juya ya kalli Aneela da ta shigo cikin palourn tana kallon boxes ɗin da ke palourn kafin ta mayarda idanunta kansa ganin ya kashe tv da wutan passage ɗin yana ƙoƙarin kashe wutan palourn gabaɗaya tace

“Love” kamar bai ji ta ba ya wuce kitchen few seconds later ya fito, tana nan tsaye inda ya barta tana ta kallonsa confused.

“Baby whats going on?” Ta faɗa finally bayan tayi mastering enough courage ta ajiye jakarta ta ƙarasa ta riƙo hannunsa.

“Ina zaka haka da duka boxes ɗinnan?”

“Gida” ya bata amsa a taƙaice

“Wani gida?” Ɗan kallonta yayi ya zare hannunsa a nata ya ɗauki box ɗin ya kai bakin ƙofa ya dawo sai sake ɗaukar wani

“Okay kafin ka tafi can i talk to you for a moment?” Ya ajiye akwati ya rungume hannunsa yana kallonta da idanunsa da ya sa taji jikinta ya mutu, ta ɗan langaɓe kai ta ƙaraso ta rungumesa a hankali duk da baiyi hugging ɗinta back ba amma bata damu ba ta cigaba da magana

“Baby ka min magana mana, me yake damunka? Yaushe rabon da ka ɗaga wayata? Yaushe rabon da ka zo apartment ɗina ko school ɗinma na manta rabon da ka zo da sunan ganina, dan Allah dont punish me for laifin da bansan na aikata ba kaji kasan ina sonka sosai kai ne rayuwata ka sani” ta faɗa tana zagayo hannunta a wuyansa ta ɗago face ɗinta tana kallon nasa, ta ɗan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login