Showing 6001 words to 9000 words out of 30393 words
zo ka je kana acting weird a gida kuma before in sauƙo ka wani wuce ka tafi, idan ka san baka so in zo waya ce ka zo gidanmu nemana?”
“Says who kai naje nema?” Ameen ya hararesa yace
“To me kaje yi?” Sai da ya ajiye cup ɗin a gefen tray ɗin kafin yace
“Mami naje gaisarwa” Al’ameen yayi wani dariya da ya sa Aryaan kallonsa yace
“Ko ba gaishe da Mami ba, u that i know ɗin koh? Kai dai faɗi me ya kaika kawai, amma kafinnan haɗa black tea ɗin da ni banci abinci ba na fito” ko kulasa baiyi ba ya ɗauki tray ɗin ya fita a kitchen ɗin, Ameen ya ƙarasa ya ɗauki well cleaned cup da spoon ya biyo bayansa yana faɗin
“Wannan ɗin zai ishemu ne?” Bai kulasa ba ya ajiye tray ɗin akan dinning, tun kafin ya zauna Ameen ya ja kujera ya zauna tare da ɗaukar toasted bread guda ɗaya ya bar masa ɗaya, ya saka spoon ya ɗibi scrambled egg ɗin ya kai baki, zama kawai shima yayi ya ɗauki ɗayan bread ɗin ya soma ci, Al’ameen ya ɗauki cup ɗin black tea ɗin ya zuba a cup ɗinsa ya raba musu daidai da daidai, kafin ya tura masa nasa gabansa, komai bai ce masa ba ya ja ya fara sha yana ɗan danna wayarsa fuskarsa a haɗe, sai da suka conye duka kafin ya miƙe ya koma cikin palour ya zauna yana danna wayarsa, kwashe kayan Al’ameen yayi ya kai kitchen ya ajiye a sink ya buɗe fridge ya ɗauko bottled water guda biyu ya fito da su a hannunsa, jefa masa ɗaya yayi ya cafe shi kuma ya ƙaraso yana shan ɗaya, ya zauna a wani kujeran daban ba wanda Aryaan ke kai ba yana cigaba da shan ruwan, sai da ya gama sha ya ajiye sauran a center table kafin ya kalli Aryaan dake buɗe ruwan hannunsa a lokacin zai sha, yace
“What happened bro? Tell me mana why are u acting all up haka?” Aryaan ya rufe ruwan ya ajiye tare da ɗan dafe kansa, hakan yasa Ameen putting serious face ya miƙe ya dawo kujeran da yake zaune yace
“Me ya faru ɗan uwa?” Ajiyar zuciya ya sauƙe a hankali ya ɗago ya kalli Ameen da idanunsa da suka ɗan yi ja yace
“I’m tired Ameen! Please tell me miye nayi ma Daddy?”
“What happened?” Ameen ya tambaya sounding concerned! Duk abinda ya faru ya kwashe ya faɗa masa from zuwan su uncle Ameenu zuwa zuwanshi gidan, Al’ameen ya sauƙe ajiyar zuciya yana kallonsa har ya kai aya kafin ya dafa kafaɗarsa yace
“Calm down bro! Yanzu iya wannan abinne ya saka ka ɗaga hankalinka haka? Har ya nuna a face ɗinka cewa ure tensed? Haba aryaan” wani mugun kallo Aryaan ya masa yana ƙwace kafaɗarsa yace
“Bangane iya wannan abin ba, shey u no comprehend abinda nace maka? Cewa fa nayi Dad and his brothers so suke in kawo mata nan da two months, how is this possible Ameen? Meyasa sai ni kaɗai suka gani? What happen to u and hamza and the others? Kai da hamza da kuka girmeni ba’a ce ku kawo mata in so so so time ba sai ni?” Al’ameen ya gumtse dariyarsa yana kallonsa yace
“Wato yanzu ka yarda mun girmeka da yake zancen is not in ur favour, what happened to watanni ba girma bane? Kuma da kake zancen mu ba’a ce mu kawo mata ba, kai ai ka san dalilin da ya sa suka ce ka kawo mata, baka jin magana Aryaan, i’ll be so happy wallahi idan ma kayi auren ko wasu abubuwanka zasu saitu” Ganin yadda ya haɗe rai ya sa Ameen ya ɗan bubbuga kafaɗarsa yace
“Sorry bro, ka kwantar da hankalinka za fa ka samu mata nan da wata 2” jingina kansa yayi a jikin kujera yana kallonsa yace
“I was thinking about Aneela…” tun kafin ya kai ƙarshe Al’ameen ya haɗe rai tare da hararansa yace
“Over my dead body ne zaka auri yarinyar nan, kai tsakaninka da Allah idan aka barka sai ka auri yarinyarnan? Sai kace ma yaranka wace irin uwa ka zaɓa musu kenan?” Kallonsa kawai Aryaan yake baice komai ba, Al’ameen ya ɗauko wayarsa dake ringing ganin Mami yace
“Mami ce, let me come and get going home”
“Spend the night here mana” ya faɗa yana kallonsa, ɗan shiru yayi sai kuma ya ɗaga wayan yana sauraren Mami tare da kallon Aryaan da ya lumshe idanunsa, can yace
“Eh Mami, ill spend the night here gobe zamu shigo tare da shi” shiru yayi sai kuma ya amsa da
“Amin” daga haka ya katse wayar yana kallonsa yace
“Duk ta damu ta ɗauka wani babban abu ke damunka”
“Okay yanzu ƙarami ne ke damuna kenan”
“Eh mana daɗi ne yayi maka yawa, ni ace in fito da matar a gani mana da tuni na kai an wuce wajen”
“To yanzu ma idan ka kai ai ba zasu ƙi yi maka ba” ya faɗa yana miƙewa
“Ah ah barsu dai su tambayeni first ni ai ina da wacce nake so, jira kawai nake a tambayeni in gabatar da ita gaban kowa da kowa, ba irinka bane ni da kake tunanin auren mace irin zaleena sunanta ko aleena….”
“Aneeela..” suka tsinkawo muryarta daga bakin ƙofa, duk suka ɗaga kai suna kallonta, idanunta cike taf da hawaye take kallonsu hannunta rike da jakarta sai wayarta a ɗaya hannun tana sanye da tshirt mai maɓallai fara da blue jeans, attachment ɗinta ya xubo har gadon bayanta, sai siririn ɗankwali da ta ɗaura a kai as usual.
Kallo ɗaya Al’ameen ya mata ya haɗe rai tare da miƙewa da nufin haurawa sama yana mamakin irin rashin kamun kanta, yo rashin kamun kai mana idan ba haka mai zai kawo mace da ta san darajar kanta gidan mijin da ba nata ba da wannan daren? Halinta disgust him, Ko da yake its not entirely her fault har da na mai gayya mai aikin dan shi ya bata daman haka shi yayi welcoming ɗinta a gidansa anytime idan ba haka ba ai bazata zo ba, wani takaici ya takure shi a wuya ya ja tsaki tare da ɗaukan wayarsa zai wuce sama, ajiye jakar tayi ta ƙaraso palourn tare da shan gaban Ameen tana kallon cikin idanunsa tace
“Al’ameen miye na taɓa yi maka a rayuwarnan da ka tsane ni? Baka ƙaunata baka ƙaunar gani na tare da farincikin rayuwata, mai nayi maka da zafi har haka da kake ikirarin over your dead body ya aureni” wani kallo yake mata irin na malama na miki kama da wanda kika zo wajensa ne, kamar bazai kulata ba sai kuma yace
“I’m glad uve been eavesdropping tun ɗazu kuma kinji duk abinda nace, aryaan bazai taɓa auren mace irinki ba God forbid” juyawa tayi ta kalli Aryaan dake kallonsu kansa a kishingiɗe da kujera, kafin ta juyo ta bawa Ameen amsa ya raɓata ya wuce sama abinsa, ta bishi da kallon tsana kafin ta juyo ta dawo kujerar da Aryaan ke zaune tace
“Love ka ji abinda yake faɗa koh? Pls dont listen to him, ure my life ka sani” miƙewa yayi shima zai wuce sama tayi saurin kamo hannunsa ya juyo yana kallonta, ganin yanda take kallonsa idonta cike da hawaye ya sa ya janyo ta jikinsa yana kallon face ɗinta ya sa finger ɗinshi yana share mata hawayen dake kumatunta, ƙasa ƙasa yace
“Go home zamuyi magana later okay?” Ta gyaɗa masa kai tana kallonsa, ya sake ta ya ja da baya yana kallonta da guntun murmushi akan fuskarsa, ƙarasawa tayi ta ɗauki jakarta har ta buɗe ƙofa ta sake juyowa ta kalleshi, kashe mata ido ɗaya yayi, tayi murmushi tana share hawayenta ta fice tare da jan ƙofar, yana juyawa ya ga Al’ameen a tsaye a jikin stairs ya harɗe hannu yana kallonsa, suna haɗa ido ya haɗe rai, kallonsa kawai Ameen keyi har ya zo zai wuce kafin ya ja tsaki da ya tabbatar yaji ransa a ɓace ya furta
“kayi asara” ko kulashi bai yi murmushi kwance a fuskarsa ya wuce sama, juyawa yayi ya bi bayansa saman ransa a mugun ɓace.
Not edited
#Banidahujjah
#Maimoon
09041426598
https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q
🌺BANI DA HUJJAH!!🌺
4.
Al’ameen na fitowa daga bayi da pyjamas ɗin Aryaan a jikinsa ya zauna a gefen bed yana kallon Aryaan dake zaune a kan bed yayi resting bayanshi da headboard, macbook a buɗe akan cinyansa, hankalinsa duka yana kan abinda yake yi a ciki
“Wai haryanzu baka gama project ɗinnan ba?”
“Uhm” ya amsa a taƙaice, jin Al’ameen yayi shiru ya ɗago ya kalleshi yace “ko zaka ƙarasa min?”
“Hmm” kawai Ameen yace yana miƙewa ya dawo bedside ya leƙa screen ɗin yana kallo yace
“Still on commercial complex?” Aryaan ya bashi side eye ba tare da ya amsa ba yana zooming da adjusting kyakkyawan zane dake screen ɗin, Ameen yayi murmushi yana kallon abinda Aryaan ɗin ke nuna masa a screen ɗin, 3D model ne na building ɗin da yake aikinsa yanzu ya dinga rotating yana nuna ma Ameen ɗin ba tare da yace komai ba, sai da ya gama nuna masa kafin ba tare da ya kalleshi ba yace
“Kasan mutuminnan canja facade ɗin ya sake yi?” Ameen yayi guntun murmushi yana kallonshi yace
“Sau uku fa kenan yana canzawa, wannan client ɗin naka sai kai”
“Fourth…” ya faɗa calmly yana jan wani layi across screen ɗin, kafin ya canza zuwa wani tab ɗin daban wanda ke ɗauke da finishing materials, shi dai Ameen jingina bayansa kawai yayi yana kallon aikin cike da burgewa.
“Previous design ɗin kwata kwata baiyi balancing da structural load ɗin ba, idan na biye masa na bi irin abinda yake so blindly, kwata kwata ginin bazai yi making sense ba” Ameen ya gyaɗa kai yana miƙewa feeling impressed but not suprised dan ba tun yau ba yasan Aryaan is perfect at what he does.
“Kaga barmu a bar da cases, mun bar muku buildings ɗin”
“Gobe zaka rakani somewhere” Aryaan ya faɗa yana ɗago kanshi
“Where?”
“Zaka gani goben”
“Hope its after mun je gida?” Ganin ya maida kanshi zai cigaba da abinda yake Ameen yace
“serious Mami cewa tayi mu zo tare gobe”
“Allah ya kaimu” ya faɗa a taƙaice
Haurawa gadon Ameen yayi ya kwanta dan bacci sosai yake ji, amma yana kwanciya maganar Aneela ya faɗo masa a rai dan ɗazu suna haurowa toilet Aryaan ya shige da ya fito kuma still shima ya shiga so bai ma yi masa maganan ba, juyawa yayi ya fuskance shi yace
“Aryaan!” Ya juyo ya kalleshi
“Are u really going to do it?” Fuskarsa da yaga ya nuna alamun bai gane inda maganar ta dosa ba yasa yace
“Da gaske kana so ka auri yarinyar can?” Ɗauke kansa yayi ya cigaba da abinda yake yi muryarsa ƙasa ƙasa yace
“As if i have a choice!”
“Kar ka raina ma kanka hankali mana, baka da choice as how? Who force u yace dole sai ka aureta, ka kawo wata daban mana, ko yaushe ka fara sonta bani da labari”
Aryaan ya kalleshi yayi shiru kamar zai yi magana sai kuma ya fasa ya miƙe ya ɗauki macbook ɗinsa ya nufi ƙofa, Ameen ya gyaɗa kai yana kallonsa yace
“Allah ya baka sa’a, and dont even bother explaining later” kashe masa wutan ɗakin Aryaan yayi ya koma palour ya ajiye laptop ɗin ya sauƙa ya haɗa ma kansa black tea ya dawo ya baje ya cigaba da aikinsa peacefully cike da natsuwa dan kwata kwata ko zancen aurennan ba so yake yi a masa ba at all.
Washegari suna dawowa daga fajr Ameen ya kunna tv din palourn tare da kwanciya akan kujera yana rage volumn, shima aryaan da kamar zai wuce bedroom sai kuma ya fasa ya kwabe jallabiya da ya daura kan wandon pj dake jikinsa dan shi dama bai iya bacci da riga ba, pillow ya janyo ya sauke kan lallausan carpet ya kwanta yana kallon wrestling da Ameen ya kunna a haka bacci ya sake yin awun gaba da su, sai wajen tara kafin Al’ameen Yayi miƙa daga saman kujeran da yake kwance ya tashi zaune yana sake yin miƙa tare da kokarin miƙewa tsaye sanye da jallabiya da yaje sallah da ita da asuba, komawa yayi ya zauna yana kallon Aryaan da ke kwance akan carpet da dogon wandon pj a jikinsa ba riga yayi matashin kai da pillow ɗin kujera da ya sauƙe ƙasa, ya sa ƙafa ya ɗan shure ƙafarsa da ke kusa da tasa, hakan ya sa ya buɗe idanunsa a hankali ya kalli Ameen da su. wayarsa ya juya masa yana nuna masa agogo yace
“Tashi ka shirya muje gida” ya miƙe zaune tare da saka fuskarsa cikin palm ɗinsa na kamar 2 minutes kafin ya miƙe tsaye ya ɗaga pillow ɗin ya mayar mazauninta ya juya ya wuce ɗaki, Ameen ya bishi da ido kafin shima ya mike ya bi bayansa.
Aryaan ne ke tuƙi Ameen na zaune a gefe yana danna wayarsa, ganin ba hanyar gida suka nufa ba ya ɗaga kai ya kalleshi yace
“Malam ya naga ba hanyar gida muka nufa ba”
“Yes zamu fara zuwa inda zaka rakani ne ba zamu daɗe ba sai mu wuce gidan” shiru yayi yana kallonsa bai ce masa komai ba dan ba haka suka yi da shi ba amma dai ya share bai ce komai ba, har suka iso kofar gidan, kallon gidan yayi ya juya ya kalleshi yace
“Ba kace ka sayar da gidannan ba?”
“Eh na sayar”
“So..?” Bai kulashi ba ya sauka a motar bayan yayi parking da kyau a waje, Ameen ya bishi da kallo across motar har yaga ya buɗe gate ɗin ya shige ciki kafin ya sauƙo ya bishi a baya. A tsaye ya ganshi a compound ɗin yana jiransa, yana hangosa ya shigo ya cigaba da tafiya towards ƙofar palourn, Ameen yabi bayansa still wondering dama ashe bai sayar da gidan ba, ya sa makulli yana buɗe ƙofar palourn Ameen da ya iso wajen yana kallonsa yace
“What are we doing here” yana tura ƙofar palourn yace
“Sayar da kai na zo yi” Ameen yayi murmushi yana binshi ciki
“Wane kai”
“To sa wasa” ya ƙarasa yana kallon labulayen palourn that are hanged ya ƙarasa kujera ya zauna yana kallon Ameen da ke ƙare ma madaidaicin palourn kallo, buɗe ƙofar kitchen ɗin da ke cikin palourn akayi, kwata kwata bata lura da Ameen ba, dan straight kujerar da yake yawan zama idan ya zo ta kalla jin motsi a palourn, suka kuwa haɗa ido da shi, da gudu ta wuce ɗakinta hannunta riƙe da ruwan gora kanta ba ɗankwali, Ameen da ya daskare a inda yake tsaye ya kalli hanyar da ta bi da kallo kafin ya mayarda kallonsa kan Aryaan dan he seriously couldnt believe his eyes, Aryaan yayi kamar bai san shi yake kallo ba sai ma wayarsa da ya fara dannawa, nufar ɗakin da ta rufe Ameen yayi dan bai gama yarda da abinda ya gani ba ko dai idonsa ke masa gizo? To ko Aneela ce a gidannan ɗin idanunsa ke nuna masa wata daban da ya tabbata babu dai abinda zai kawota nan ɗin, Aryaan ya bishi da kallo ta ƙasan glasses ɗinsa har ya tura ƙofar ɗakin da ta shiga, a tsaye ya ganta a tsakiyar ɗakin riƙe da ruwan tana kallon ƙofa kamar mai expecting shigowar wani, suna haɗa ido da Ameen ta wani zaro ido tayi cilli da goran ruwan ta nufosa a guje ta shige jikinsa ta rungumesa ta fashe da sabon kuka, gyaɗa kai kawai Ameen yake still in shock yace
“SALWA!?” Ajiyar zuciyar kuka kawai take sauƙewa taƙi ta amsa, ya ɗagota daga jikinsa yana kallonta yace
“Me kike yi anan? What happened to morocco? Birthday ɗin kenan?” Shagwaɓe fuska ta kuma yi tana kallonsa a shagwaɓe tace
“I never went” tana faɗa wasu hawaye na rige rige a kumatunta, ya gyaɗa kai kawai yana lissafa irin tsantsar rashin gudun zuciya da gudun magana irin na Aryaan, shi yanzu idan ba tsantsan nema wa kai fitina ba ko da kudi aka ce ya shiga harkar yar uncle Ameenu sai ya shiga? ba ƙaramin mamaki abin ya bashi ba har hakan ya nuna ƙarara a fuskarsa, sake zuwa tayi zata shige jikinsa ya riƙe hannunta yana kallon face ɗinta da duk ya kumbura tsabar kuka, to dama mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, salwa on normal days ma ya take da kuka bare kuma an taɓa ta, ya dinga kallon face ɗinta lost in thought, har wata rama tayi fuskarta look somehow ko dan kukanne kasancewarta fara sai fuskar tayi ja ta ɗan kumbura. Cire hannunshi yayi a nata ya juya ya nufi palour ransa a matuƙar ɓace sai dai wayam ya samu palourn babu ko mai kama da Aryaan, yayi ƙwafa a hankali ya juya yana kallon salwa da ta biyo shi palourn tana share ido har sannan kanta ba ko ɗankwali, ƙofa ya nufa ganin zata biyo sa a haka ya dakata yana kallonta yace
“Je ki ɗauko veil ɗinki”
“Babu sai dai hijab” ta faɗa tana kallonsa, gyaɗa mata kai yayi yace
“Je ki ɗauko yi sauri” juyawa tayi walking slowly ta tafi ɗakin, hijab ɗinta da Aryaan ne ya kawo mata su guda biyu take sallah da su ta ɗauko guda ɗaya ba tare da ta kula akwatin kananun kayan da ta kwasa that she was suppose to travel to morocco da