Showing 9001 words to 12000 words out of 30393 words
shi ba ta fito a ɗakin, Ameen ya kalle ta ganin ta sako hijab ɗin har yana jan ƙasa ya nufi ƙofa, bin bayansa tayi tana tattare hijab ɗin kamar zata faɗi tace
“Yaya i dont want to wear this” bai kulata ba har suka fito haraba, ta ja ta tsaya tana kallonsa har ya buɗe gate ya leƙa yana kallon inda suka yi parking ɗazu amma babu motar, ya riƙe kunkumi kawai yana kallon wajen, bai san sanda ya furta “wow!” Ba, da ya ɗauki mota ya barsa da ita anan me yake nufi kenan? Ya juya ya kalli salwa da ta haɗa rai ta ɓata fuska harda tura baki, ranshi yaji yana ƙara ɓaci yana kallonta yace
“Zo ki wuce mana” ta soma takowa tana riƙe hijab ɗin tace
“Yaya wai da wannan abin zan je har gida?” Wani harara ya galla mata bai kulata ba ya kama hannunta ganin ta iso shi ya soma tafiya da ita, binsa kawai take tana tattare hijab ɗin da ke jan ƙasa kamar zata faɗi banda hawaye babu abinda take yi ganin yadda mutanen unguwan suke kallonsu, sai da suka iso titi kafin ya sake hannunta ya fara ƙoƙarin tare abin hawa yana laluba aljihunsa yaji ko yana tare da wallet ɗinsa amma babu kamar yanda ya bar wayarsa a mota haka ya bar wallet ɗin ma, kallon keken da ya tsaya a gabansu tayi in disbelieve kafin ta kalli Ameen da sauri tace
“I dont understand? Meyasa bazamu shiga mota ba? Ni gaskiya bazan shiga abinnan ba” me keke ya wani kalleta daga sama har ƙasa kafin ya ja tsaki kawai ya ja kekensa yayi gaba tun kafin ma Ameen yayi magana, Ameen ya bishi da kallo sai kuma ya kalleta, tayi murmushi tace
“All this poor people and short temper”
“Tunda kin kore shi sai ki tare wani, where’s your phone?”
Tura baki tayi tace “shima ya ƙwace”
Ameen ya gyaɗa kai kawai yana sake ƙoƙarin tare wani keke,
“Yaya pls mu shiga mota”
“Kina da kudin motan?” Shiru tayi tana kallonsa, ya kama keke ya shiga bayan ya tsaya yana faɗa masa inda zasu, kallonta yayi ganin tana tsaye yace
“Kina ɓata mana lokaci ko in tafi in barki ne?” Ganin still tana tsaye yace
“Me keke mu je” me keke ya tayar kuwa zai tafi da sauri tace
“Wait..” kamar zata yi kuka ta shiga kusa da Ameen tana zama a ɗosane kamar ta zauna akan ƙaya, mai keke dai ya ja kekensa yayi gaba bai tanka su ba, sai a lokacin Al’ameen ya kalleta yace
“Tun yaushe ne kike nan ɗin” ta kwantar da kanta a shoulder ɗinsa tace
“Nace maka i never went to morocco yaya Ameen, ai wallahi Allah ya isa na, abinda ya fi bani haushi ma wayata, Raliya will kill me, haka zata ce fake promise na mata banje birthday ɗinta ba bayan we planned everything together, ai bazan taɓa yafe masa ba ko kabarinsa yana balbali da wuta”
“Keee…” Ameen ya dakatar da ita yana dariya, ta tashi zaune da kyau tana kallonsa tace
“Its not funny yaya Ameen”
“Its not daddy’s princess” ya faɗa yana jan hancinta, sake mayarda kanta tayi kafaɗarsa ta kwantar tana kallon hanya, Allah Allah take su iso gida.
tun kafin su iso road block ɗin da zai sada su da estate ɗinsu me keke yace
“Ba ma ƙarasawa can fa” kallon salwa Ameen yayi ta wani zaro ido tana kallonsa tace
“da ƙafa? Duk soldiers ɗincan su ganni a haka da wannan abin?no pls yaya” ta faɗa tana nuna masa hijab ɗin jikinta, ajiyar zuciya ya sauke ya kalli me keke da harya ja ya tsaya yace
“Dont worry muje zan musu magana”
“Toh oga” me keke ya faɗa yana sake tada keken ya nufi sojojin, tasowa sukayi suka nufosa ganin wajen ya tunkaro suna daka masa tsawa, Al’ameen ya leƙo daga ciki da murmushi a fuskarsa yace
“Sorry its me” cikin fara’a da girmama juna suka gaisa ya faɗa musu he’s going in with the me keke, hakan yasa suka basu hanya ita dai salwa haɗa rai tayi tana kallonsu ƙasa ƙasa har suka wuce, ko da suka zo gate ɗinma sammakal sai da ya sake musu magana kafin suka buɗe, me keke ya shigar da su har ƙofar “Ameena wazeer turaki” yana yaba yanda masu kuɗi suke sha’aninsu ji wani gida dan Allah, yana gama parking salwa ta sauƙa shima Ameen haka, ganin zata nufi gate ɗin gidansu da ke kallon na su Ameen ɗin, Ameen yayi saurin riƙo hannunta tare da yafito mai gadin gate ɗinsu da ɗayan hannun ganin ya leƙo jin keke a ƙofar part ɗin abinda bai taɓa ji ba,
“Lawal bashi kuɗinshi pls idan akwai cash jikinka” da sauri ya fito yana faɗin
“Akwai ranka ya daɗe” shi kuma ya ja hannun Salwa zuwa cikin gidansu dan ko giyar wake ya sha yanzu bazai bari Salwa ta tafi gidansu a haka ba, Babanta ya ganta a haka su shiga uku.
A palour ya tarar da Mami da yaranta Lailerh da Siyama suna kallo duk suka ɗaga kai suna kallonsa kafin su kalli Salwa da ta sha hijab, miƙewa zaune su siyama sukayi har suna haɗa baki wajen faɗin
“SALWA!!”
#Banidahujja
#Maimoon
09041426598
https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q
🌺BANI DA HUJJAH🌺
5.
Tana tsane gashin kanta da ta wanke shi sosai ba kaɗan ba ta fito daga toilet, baby pink towel ɗaure a chest ɗinta, very fair skin ɗinta sai glowing yake, ta zauna a gaban dresser tana ƙarema ɗakinsu siyama da su kansu su siyama ɗin kallo, ɗakinsu siyama babba ne sosai kuma kasancewar su masu banbancin ra’ayi akan komai yasa ɗakin ya zama kamar wanda akayi splitting gida biyu, ko wacce da side ɗinta with her bed da study area ɗinta, kasancewar lailerh is more girly yasa gefenta nuna hakan, sashinta sai ya kasance is more aesthetic dan har ƙaramin vanity table take da shi a gefenta cike da skin cares ɗinta da perfumes kamar mai sayar da su, itama gefen siyama tana da same table amma nata laptop ɗinta da notebooks da frames na motivational quotes ne akai, kai kana kallo kai tsaye zaka gane cewa ita siyama is a bookworm ita kuma lailerh soft girl life, sai dai duk da haka same dresser da siff suke sharing, Lailerh da tayi tagumi akan gadonta tana kallon Salwa tace
“Wai bazaki faɗa mana what happened ba”
“Eh!, bazan faɗa ba” ta faɗa tana matso cream ɗin Lailerh ɗin da ta zo ta ɗauka a table ɗinta kasancewar same cream suke using unlike siyama da ba irin nasu take anfani da shi ba, ko shower gel da na Lailerh tayi using, ta zauna ta fara lailaye jikinta da cream ɗin kamar tana shafa ƙwai, siyama dake kan gadonta itama tace
“Haba Princess, ki faɗa mana pls”
“Mtsw, sai kuma kuyi, ba dai ni kuka yi ma dariya ba ɗazu! Billah bazan faɗa ba”
“Stop swearing mana ai da Mami ta ce mu bar dariya mun bari, pls tell us what happened, kullum sai na duba status ɗinki har snapchat da insta story ɗinki u didnt post anything about birthday ɗin raliya, pls tell us what happened” kamar ba da ita suke ba ta ƙarasa shafa mai ɗin ta buɗe drawer ta fara duba kaya a cikin nasu zata saka, kamar kuma wacce aka yi wa wahayi ta juyo tana kallonsu tace
“Wallahi bazan taɓa yafewa Aryaan ba” duk buɗe ido sukayi suna kallonta jin ko yayan ma bata sakaya ba wai Aryaan, ji sukayi kamar ta tafka zunubi ambatar sunansa without yaya, kafin su gama comprehending wannan ta cigaba
“I hate him! Stubborn.. arrogant.. st…”
“Ke salwa, are u in your right senses kuwa? Shi yayan?”
Sai da tayi rolling idanunta kafin tace “Eh shi? Waye shi? Tunda ba mala’ikan ɗaukan rai bane ai da sauƙi, ni na daina jin tsoronsa wallahi, kuma wannan abin da ya min koh hmm…”
Da ƙyar suka rufe bakunansu da suka sake suna sauraronta
“Me yayan ya miki wai toh?”
“Ku barni da shi, wallahi zai san ni yayi ma haka, wallahi duk abinda ya mini sai na rama” sai a lokacin Siyama ta ɗan ja guntun tsaki tace
“Ko kuma ki rame ba, Shegen cika baki, Salwa duk duniya wa ya fiki tsoron yaya Aryaan, ki faɗa mana me ya haɗaki da shi sai kame kame kike kina zaginsa, Allah ya sa ya jiki”
“To ya jini mana! Sai me?”
“Wai a ina kika ga yayan? Ni fa na kusa two weeks rabon da na gansa”
“Dama a ta ina zaki gansa yana can yana walakantani saboda ni ce karamar katangarsa daɗin tsallakewa”
“Ban gane ba” Lailerh ta faɗa cike da son jin labari.
Ƙin amsawa tayi ta juya ta cigaba da zaɓen kaya da zata saka, da ƙyar ta samu wani plain gown cikin kayan lailerh su dai kallonta kawai suke yi yadda garin ɗaukan kayan take ta wargaza musu siff, yanzu suyi magana cibi ya zama ƙari tunda Mami ce tace tayi wanka anan ta ci abinci kafin ta tafi gida.
Saka rigan tayi ta zauna ta fara drying gashinta, ta gama tayi styling ɗinshi tana yi tana tunanin wayanta da ke wajenshi idan ta tuno ji take kamar ta hadiyi zuciya ta mutu.
Tana gamawa ta miƙe ta nufi ƙofa duk suka bita da kallo, siyama ta miƙe ta tafi siff ɗin ta leƙa taga bata ko taɓa part ɗin kayanta ba, ta ɗan yi murmushi ta kalli lailerh tace
“Sai ki tashi ki gyara kayanki” daga haka ta nufi ƙofa itama, miƙewa lailerh tayi ta bita ba tare da ta gyara ɗin ba itama gudun kar ta tsaya gyarawa Salwa ta je ta faɗa ma siyama abinda ya faru ita kaɗai.
Mami na ganin sun sauko ta nuna musu hanyar dining da hannu, ko kallon dinning din salwa bata yi ba ta nufi hanyar ƙofa, Mami ta bita da kallo kafin tace
“Salwa bazaki ci abinci ba?”
“Bani da appetite Mami i just want to see daddy”
“a haka zaki tafi babu ɗankwali…?” Ko kafin ta ƙarasa har ta fice a palourn, Mami ta sauƙe ajiyar zuciya kawai kafin ta juya wajen su lailerh tace
“Kuje ku ci abinci”
Al’ameen ne ya shigo ɗakin Mami bayan sallar magrib, ganin tana waya ya sa ya ƙarasa ya zauna a kujera yana jiran ta gama, ganin expression ɗinta yasa ya bada hankalinsa kan abinda take faɗa a wayar
“Eh, na gane! Na gane, to ba damuwa idan baku dawo ba zan sa Al’ameen ya kawo ni” Ameen dai ya zuba mata ido har ta sauƙe wayar ta dafe kanta a hankali
“What happened?” Ya tambaya yana kallonta worried
“Salwa ce wai take hospital”
“Hospital kuma? Me ya same ta?”
“da Amminta muke magana yanzu wai bata iya cin abinci babanta ya kaita asibiti”
“Saboda kawai bata ci abinci ba shine za’a kaita hospital to yaushe ma ta dawo ɗin, kuma sau nawa ne bata ci abincin ba?”
“Anan ma ai ƙin ci tayi ina jin da ta je gidan ma bata ci bane kuma dai ka san yanda Yaya Ameenu yake akan Salwa, ni wallahi sam ban ji daɗin abinda Aryaan ya aikata ba har fargaba nake ji na abinda zai faru wlh”
“Ikon Allah” Ameen ya faɗa though ba wai hes very suprised bane kowa ya sani a duka family ɗinnan Uncle Ameenu ko kaɗan baya wasa da lamarin only daughter ɗinshi Salwa, akanta bashi da kara, dama asali ba kirki ya cika ba to akanta kuwa rashin kirkin ninkuwa yake, ko Amminta ba sha take yi ba a wajensa in dai akan Salwa ne, shiyasa yarinyar take abinda taga dama kowa tsoron mata faɗa yake saboda jaraban ubanta dan a gurinshi fa bata laifi, the only people da suke iya mata magana akan abu Mami ne twin sister ɗin Uncle Ameenu, tunda babansu Ameen ya mutu ta dawo gida da yaranta da dadewa tun kafin su Ameen su kai haka, to itace ma atimes takan yi wa Salwa nasiha idan ya kama harda faɗa sai kuma Bappah, thats Wazeer Turaki himself, grandfather ɗinsu shi kuma dama mutuminta ne duk da tsaurinsa amma sosai take sonshi akwai shakuwa sosai tsakaninta da shi, sai kuma Amminta da take shakkah only idan daddynta baya wajen. Maganar Mami ce ta katse masa tunanin da ya tafi
“Amminta tace wai hypoglycemia ke damunta wai sugar level ɗinta yayi dropping! Toh ban dai sani ba since babanta ne dr ɗin komai ma zai iya cewa, kuma ka san already ya kira meeting!” Ameen ya sauƙe ajiyar zuciya yace
“Shiyasa ma na zo yanzu in ce Mami as his twin sister pls babu yadda za’a yi ki ɗan masa magana yayi hakuri da meeting ɗinnan? Lokacin general meeting baiyi ba amma yawanci idan kaji emergency meeting toh its always him, yanzu wannan issue ɗin bazaku iya settling a hankali ba sai an sakko bappah a ciki”
“Kira min Aryaan” Mami ta faɗa ba tare da ta amsa maganar da yake mata ba, wayarsa ya zaro ya shiga dialing lambar Aryaan amma baya connecting ya dube ta yace
“Baya shiga”
“Ai ya kyauta saboda ya san bai shuga abin kirki ba shiyasa ya rufe layukansa, idan kayi sallah isha’i kaje ku taho tare da shi, saboda zai iya cewa gobe ba zai zo meeting ɗin ba, ya ƙara ma kansa wani laifin akan laifi, wallahi ni har yaya Umar tsoron yaji maganar nan nake”
Miƙewa Ameen yayi yana kallonta yace
“Ke dai ki kwantar da hankalinki Mami, duk abinda sukayi babu ruwanki kar ma ki saka ma kanki damuwa please, ai ya san irin haka zai faru amma ya gwammace ya jawo ma kannasa magana”. Daga haka ya fice a ɗakin ta bishi da kallo kawai,
Ummah dake zaune a palour ta kalli uncle muhammad dake sauƙowa daga sama da waya a kunnensa har ya ƙaraso cikin palourn ya zauna a kujera ranshi a ɓace yana faɗin
“Tabbass! To wallahi sai yayi dana sanin taɓa ta Allah ya kaimu goben, toh, toh, shikenan”
Ummah ta taɓe baki tana kallonsa tace “wa kuma aka taɓa” gyara zama yayi yana kallonta yace
“Wannan ɗan iskan yaron Aryaan ne wai ya je ya kulle Salwa dan bashi da mutunci, ni dai na cewa Ameenu ya duba ta da kyau kar dai ya mata wani abin dan ɗan iska ne yaronnan kowa ya sani”
“Mtsw, dama na san wallahi bazai wuce ita ba, kai ai idan anga kana ɗaga jijiyoyin wuya to akan Ameenu ne, kana yayansa amma wai ƙaninka ke juya ka, daga yayanka har ƙaninka su zauna suna juyaka yadda suka ga dama ba abinda ya dame ka suyi ta passing ɗinka kamar ƙwallon ƙafa kowa yana anfani da kai, ga dai hamza ga nan shaheeda sune dolenka amma inaaa ka ƙare a gindin brothers ɗinka da basu san darajarka ba kowa ɗansa ya sani a cikinsu, nan Aryaan ya shaƙe Hamza ka dinga hayagaga bazaka yarda ba amma shiru kake ji babu abinda kayi akan hakan ya daki banza amma da yake salwa ya taɓa yanzu gashi nan har babanta ya kira emergency meeting an taba ƴar gold, kai kuma kana taya sa kana tada jijiyoyin wuya bayan da aka taɓa naka ɗan shi bai yi wannan baloƙoƙon ba, ka cigaba wallahi takaicinka bazai kashe ni ba” tana gamawa ta miƙe ta wuce sama mugun takaicin halin mijinta yana ƙona mata rai, duk cikin brothers ɗin sun fishi kuɗi, sun fishi alƙibla da sanin abinda sukeyi, they are the leaders shi kawai sai yadda suka yi da shi a ganinta, sun fishi iko da say a gidan.
Aryaan ne a zaune, Mami na tsaye a kansa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba
“What u did is not right, its very very wrong Aryaan, ko ba komai ai yar uwarka ce amma ka ɗauketa ka kaita ka kulle kamar wata mara galihu? Bayan ka san halin mahaifinta sarai? Meyasa duk abinda zaka janyo ma kanka magana shi ka fi so Aryaan, dama gashi nan kana baki already amma kullum sake saka kanka kake a bakin kowa Aryaan, na tambayeka why u did that kuma ka min shiru koh”
Ɗaga idanunsa yayi ya kalleta ya sauƙe kan still saying nothing, ta koma ta zauna tana kallonsa tace
“Shikenan tunda bazaka faɗa min ba gobe ai dole ka faɗa a gaban kowa Allah ya kyauta” shiru yayi kamar bazai ce komai ba sai kuma can yace
“Kiyi hakuri Mami” Al’ameen takaici kamar ya kashe sa yana zaune dai yana kallonsa, Mami ta girgiza kai tana kallonsa tace
“Ah ah ni kuma ina ruwa na, duk abinda zaka yi dai ni dai ina mai tabbatar maka ka dinga tunani, yanzu na tabbata umminka bata ji ba bata gani ba zaka jawo mata magana dan kai ka sani ko miye zaka yi a wajensu fa Umminka ce ta saka ka, bata nan ɗinma bata tsira ba kullum cikin sakata a bakin yan gidannan kake ka dinga mata adalci ni dai na faɗa maka” shiru yayi bai ɗago kansa ba tace
“Yaushe rabonka da kaje wajenta?” Sai a lokacin ya ɗago ido ya kalleta yayi shiru
“Tambayarka nake”
“Three days ago naje”
“Kunyi magana da ita?” Girgiza kai yayi alamar
“ah ah”
“And why is that” shiru yayi bai ce komai ba, ta sauƙe ajiyar zuciya tace
“Tashi kaje sama ka kwanta” ya ɗago kanshi ya kalleta
“Mami zan zo goben i promise”