Showing 18001 words to 21000 words out of 30393 words
ɗaga ƙafarta to match his height da niyyar sumbatarsa.
Sai a lokacin ya warware hannunsa yayi wrapping around bayanta ba tare da ya bari ta sumbace shi ɗin ba, ya juyata ya jingina ta da bango yana kallon cikin idanunta, murmushi tayi tana kallonsa itama tare da cije lips ɗinta, ta kama hannunsa ta ɗaura akan ƙirjinta a hankali tana kallon idanunsa, ya sauƙe idanunsa ya kalli inda ta ɗaura hannunnasa kafin ya saketa ya ɗan ja baya a hankali, da mamaki ta dinga kallonsa ya ƙarasa zai ɗauki akwatin da bai ɗauka ba ɗazu tayi saurin riƙo hannunsa idanunta cike taf da hawaye tace
“Aryaan! zaka aureni pls?” Ɗan kallonta yayi na few seconds cause bai tsammaci wannnan tambayan ba, sai kuma ya kamo hannunta ya jata har kujera ya zauna ya zaunar da ita, ya kamo fuskarta ya ɗan sunkuya ya sumbaci goshinta kafin ya ɗago yana kallonta yace
“Lets talk” ta gyaɗa masa kai kawai tana kallonsa dan a halin yanzu babu abinda take son sani irin abinda ke zuciyarsa game da ita.
“Aneela ba tun yau ba kin tambayi this same question idan zan aureki ko ah ah, the answer is No! Aneela kuma kema kin san dalilin da yasa amsata ya kasance haka!” Hawaye ya gangaro idanunta tace
“Saboda Al’ameen yace kar ka aureni koh? Saboda yace maka ni ƴar iska ce koh? Idan ma iskancinne ai tare mukeyi meyasa ni kaɗai zan karɓi consequence ɗin banda kai”
guntun murmushi yayi ya ɗan kau da kansa daga kallonta kafin ya koma yayi relaxing da kujera yana kallonta yace
“Da ni kike iskanci?” Tayi shiru tana kallonsa,
“okay lets get this over with, na farko! Ameen ba shi zai faɗa mini wacce zan aura da wacce bazan aura ba since ba shi zai zauna mini da matar ba! I never said i was gonna marry you Aneela, kuma ke kinsan dalilin da ya sa bazan aureki ba, kinsan dalilin da ya sa i never crossed the line with you, saboda duk abinda i cant own i dont keep, duk abinda is not fully and completely mine i dont attach myself to it.”
Kallonsa kawai take, kafin tace “bangane nufinka ba?”
“Kinga no need for tone tone! I’m been honest with you, idan har kina da wanda kike ganin is more serious gwara ki bashi chance” yana faɗin haka ya miƙe itama miƙewa tayi tana kallonsa tace
“Amma you are a wicked person Aryaan! Ni zaka ci amana? Bayan ka gama ruguza mini rayuwata, bayan komai da na sadaukar saboda kai? Bayan duk soyayyar da na nuna maka? This is what you say? This is how you pay back my love for you? To wallahi billahi Aryaan idan har ina doron duniya kuma ina numfashi ni ce nan matarka kuma baka isa ka auri wata mace a duniya bayan ni ba!”
Daga sama har ƙasa ya ƙare mata kallo kafin ya harɗe hannunsa a ƙirji,
“Na ruguza miki rayuwa in what way? By paying your rent and your school fees? By sponsoring your lifestyle? Sadaukarwa saboda ni? Wanne kenan enlighten me, kinga Aneela i’m not in for this rubbish!”
Katsesa tayi saurin yi tana kallonsa tace
“na baka lokaci na, na baka jikina, na baka respect da duka emotions ɗina” bai san sanda yayi dariya ba yana kallonta yace
“Dont deceive yourself kika bani jikinki? Sanin kanki ne i never crossed that line! Saboda kamar yadda na faɗa miki duk abinda ba nawa bane completely bana buƙata”
“Wai kana nufin i sleep around ko miye?” Bai tankata ba ya ɗauki other boxes ɗin ya fitar a palourn ta biyosa tana cigaba da magana, komawa yayi ya rufe ƙofar palourn bayan ya kashe sauran appliances ɗin duka ya ɗauko jakarta ya ajiye a waje, tana biye da shi tana maganganu marasa kai da gindi tana hawaye, ya fito compound ɗin ya nufi motarsa ya buɗe ya saka boxes ɗin, yana saka box na ƙarshe a baya ya rufe motar tare da buɗe murfin gaban motarsa zai shiga ya bar gidan sai a lokacin ta fara kukan gaske ta riƙo hannunshi tana kallonsa tace
“Are u breaking up with me?” Ya wafce hannunsa yace
“I already did! Goodbye” fashewa tayi da kuka tana riƙosa tace
“Pls baby No! Ko bazaka aureni ba na yarda amma kar ka rabu da ni pls” wafce hannunsa yayi ya shiga motarsa ya rufe ta fara buga glass ɗin kamar mahaukaciya tana kiran sunansa, reverse yayi da ya sa ta matsa daga jikin motar tana zunduma kuka ya nufi gate, mai gadi dake zaune tuntuni yana kallon drama ɗinsu ya taso da sauri ya buɗe masa gate! ya dakata ya sauƙe glass ɗin yana kallon mai gadin yace
“Ta fita ka rufe mini gida! Kar wanda ya sake shigo mini gida without consent ɗina, nima zanyi tafiya i wont be around idan kana so zaka iya zuwa kaga gida” gyaɗa kai kawai mai gadi yake yana amsawa da
“Toh ranka ya daɗe” ganin Aneela ta nufo gate ɗin da saurinta ganin yana magana da mai gadi ya sa ya ɗauki kuɗin da ke dashboard ɗinsa ya miƙa masa yana karɓa ya ja motar ya fice a gidan bai ko tsaya sauraren godiya da yake ta masa ba, ficewarshi yayi dai dai da isowar Aneela gate ɗin, ta dakata tana kallon motar har ya ɓace kafin ta rushe da kuka, ta tsuguna a wajen tana tayi, shi dai mai gadi komawa yayi ya zauna yana kallonta, tausayin mata masu hali irin nata na ratsashi, dama a haka suke ƙarewa kullum suna hanyar zuwa wajen maza ƙarshe mazan su wulaƙanta su saboda dama tun farko basu ɗauke su a masu daraja ba, girma, mutunci, ƙima da daraja da Allah yayi ma ɗiya mace duk sun zubar da tasu a gaban mazan, ta yaya bazasu bi kai su taka su wuce ba?
“Allah ya shirya mana haula” ya faɗa a hankali yana gyara zamansa a kujera yana kallonta. Sai da tayi kukanta mai isarta kafin ta miƙe ta tafi ta ɗauko jakarta da ke yashe a compound ɗin ta nufi gate fuuuu, kamar zata tashi sama dan wallahi yayi kaɗan yace bazai aureta ba, wallahi bashi da mata a doron duniya bayan ita zata iya zuwa ko wani extent dan ganin hakan ya faru.
From there Aryaan gidansu Umminsa ya wuce straight, Gidansu Umminsa madaidaicin gidane mai kyau single storey building, yayi horn mai gadi ya buɗe masa ya shigo da motarsa compound ɗin yayi parking. Sai da ya ɗauki kusan three minutes cikin motar kafin ya buɗe motar ya sauƙo riƙe da wayarsa ya nufi cikin gidan.
Tun kafin ya ƙarasa palourn yake jin hayaniyan yara sama sama, ya tura ƙofar palourn da sallama ƙasa ƙasa ya shiga, Umminsa na zaune a kan kujera hannunta riƙe da Marwah tana bata indomie sai juya kanta take bata son ci, Maman marwah ƙanwar umminsa na zaune itama a palourn tana dariya ganin yadda marwah ke kuka bazata ci ba ummi kuma tace sai fa taci yarinya kwata kwata taƙi abinci sai Nono ƙatuwa da ita, babban yayan su Ummi dake zaune shima a palourn yace
“Asiya ki rabu da ita idan bazata ci ba dan Allah” sauƙeta tayi ta ɗan daki jikin pampers ɗinta da wasa tace
“jeki ƴar ƙaniya” dai dai lokacin suka ji sallamarsa, duk suka ɗaga ido suna amsa sallaman. Ganin wanda ya shigo ya sa Abbah Usman sakin fuskarsa sosai yana faɗin
“Ahh Aryaan kaine?” Ya cire glasses ɗin idanunsa yana ƙarasowa ya zauna a ƙasa yace
“Ina wuni Abba..” ya juya yana kallon maman marwah yace “ina wuni ummah” itama tana murmushi tace
“Ahh lallai Aryaan yau dai da rabon zamu haɗu ashe a gidannan! Wato sai dai a haɗu da kai a hanya kai baza dai kazo ma mutum har gida ba koh?” Murmushi yayi ya juya ya kalli umminsa da ta daina murmushin da take yi tun shigowarsa yace
“Ina wuni Ummi”
“Lfy lau” ta faɗa tana miƙewa ta nufi kitchen dan taimakawa anty husaina matar Abbah usman dan yau full house gidan yake sun zo duba jikin gwaggo.
Ummah ta miƙe ta nufi ɗakin gwaggo tana faɗin
“Gwaggo guess wa ya zo gaishe ki…?” Shi dai Aryaan binta da ido yayi har ta shige ɗakin kafin ya kalli Yayan Umminnasa yace
“Abbah haidar fa?” Second son ɗin Abbah sa’an Aryaan ɗin, dan ya ma bawa Aryaan ɗin watanni.
“Tare muke da shi ai, yaje kai Malam check up ne na san sun kusa dawowa ma, bakwa magana a waya da shi ne”
“Munayi” Aryaan ya amsa yana gyara zamansa
Abbah yace “to yayi kyau, Ka shiga ka duba gwaggon”
gyaɗa kai yayi a hankali ya miƙe ya nufi ɗakin gwaggo,mahaifiyar umminsa,
farar tsohuwan na kwance a kan gado kana ganinta kasan tana ɗan jin jiki duk da yadda Ummi ke kula sosai da ita, tana ganinsa ta miƙa masa hannu tana murmushi, ya ƙarasa ya zauna a gefen bed tare da sa hannunshi a nata ita dai ummah na zaune a bedside tana kallonsu ɗauke da murmushi, hannun ya kai bakinsa ya sumbata yace
“Ya jikin gwaggo?”
“To Alhamdulillah muhammad, ina ta cigiyarka shiru abinka”
“Aiki ne ya ɓoye ni gwaggo kuma bansan baki da lafiya ba”
“Aikam dai jiki yaƙi daɗi, sai fatan Allah ya sa mu cika da imani”
“To ke wa ya faɗa miki cuta mutuwa ce? Sai ki ga na rigaki mutuwa ma..” da sauri ta girgiza masa kai tana kallonsa tace
“Kul, in sha Allah ba yanzu zaku mutu ba Aryaan sai ka ga ƴaƴanka har da jikoki, nima in sha Allah sai na ga har ƴaƴanka in sha Allah” murmushi yayi ya ɗaga idanunsa ya kalli Ummah ta harareshi, ya shafa kansa a hankali yace
“Ummah tun yaushe ne bata da lafiya?”
“Ban sani ba, ai da ka damu da sani da ka sani” shiru yayi bai sake cewa komai ba,
After some seconds ya kalli gwaggo yace “kina son wani abu ne gwaggo in je in samo miki?” Shiru tayi tana kallonsa sai kuma girgiza masa kai
“In sayo miki fruit?” Ɗan murmushi tayi kafin ta jinjina masa kai, yayi murmushi shima ya miƙe ya nufi hanyar fita Ummah ta bishi da idanu.
Fita yayi a palourn Abbah na tambayarsa inda zashi yace yana dawowa. Bayan Thirty minutes ya dawo gidan da niƙi niƙin kaya, Abbah ya zuba masa idanu har ya gama shigowa da duka cefanen da yayi kafin yace
“Yanzu wa ya saka ka wannan aiki Aryaan” ya sunkuyar da kansa yayi shiru
“Toh Allah yayi albarka” da “Amin” ya amsa ya ɗauki ledan fruits ɗin gwaggo ya wuce ɗakinta,
sai a lokacin Abbah ya kalli Ummi dake zaune a palourn yace
“Asiya meyasa kike haka ne? Idan baki ja ɗanki a jiki ba wa zai ja miki shi ne wai” shiru tayi bata ce komai ba, ya sauƙe ajiyar zuciya yana miƙewa yace
“Allah ya kyauta! Bari in ɗauko su malam a hospital wai motar Haidar is faulty”
“No wonder naji su haryanzu shiru” ta faɗa tana kallon yayannata , bai ce mata komai ba dan haushin yanda take treating ɗanta yake ji har ransa ya nufi ƙofa ya fice abinsa.
Bayan fitansa Ummah da anty husaina suka fito daga ɗakin gwaggo, ummah ta zauna tana kallon Ummi ganin yadda tayi shiru lost in thought kuma tasan baya rasa nasaba da zuwan Aryaan gidan.
Anty husaina tace “Yanzu Asiya har yanzu bazaki cire abinnan a ranki ki nunawa ɗanki soyayya ba? Kina wahalar da kanki kina cutar da yaro?”
Ummah tayi ƙwafa tace “wallahi anty husaina lamarin yaya Asiya sai ita! Dan Allah shi miye laifinsa a duk abubuwan da suka faru yana ƙarami! Me ma ya sani shikam?” Kafin ta basu amsa Aryaan ya fito a ɗakin wanda hakan yayi dai dai da shigowar malam tare da Abbah da yana fita yaci karo da sunyi bolt ma ashe har sun iso sai kawai ya dawo ciki tare da Malam ɗin ya bar Haidar a waje yana waya.
Malam na ganin Aryaan ya buɗe ido yana faɗin
“Ahhh lallai manyan baƙi ne a gidannamu ashe” murmushi yayi a hankali yana gaishe sa, Malam ya zauna a kujera yana faɗin
“Kuma a cikinku a rasa mai sanarmin Muhammad ya zo?” Ya faɗa yana directing question ɗin to su Ummi.
“Ban daɗe da zuwa ba ai” ya faɗa yana ƙarasowa ya zauna a ƙasa gefensa,
“Toh masha Allah ya gidannaku? Ya bappahnku da su Daada, how’s your Dad? Da kowa kowa?”
“Lafiyansu lau Alhamdulillah suna gaishe ku”
“Muna amsawa masha Allah, amma zaka kai dare ai koh tunda gashi naga har yamma ta fara yi”
“Ah ah yanzu zan wuce but zan dawo gobe in sha Allah” Sai a lokacin Umminsa tayi magana tana kallonsa tace
“Ce maka akayi kar kayi dare a nan ɗin kenan” ya dubeta a hankali amma bai ce komai ba.
“Da sun sani ai kar ma su barka ka zo kwata kwata, ko da kai ko ba kai zan rayu” tana faɗa ta miƙe zata wuce ɗaki, Aryaan ya miƙe ya tsaya yana kallonta yace
“Ummi..” juyowa tayi tana kallonsa, yana kallonta shima yace
“What wrong have i ever done to you? Miye laifina a duk abubuwan da suka faru? Meyasa laifin wasu ke shafana? Meyasa kika tsaneni? Me na miki?” Kallonsa kawai take idanunta yayi ja, har ta juya sai kuma ta dawo tana kallonsa tace
“Idan har abinda zai kawo ka kenan Aryaan kar ka sake zuwa inda nake! Kaje can wajen dangin ubanka da suka fini, zuwan ganin daman da kake mini ma bana so na yafe!” Tana kaiwa nan ta juya zata wuce, Aryaan yayi wani murmushi mai ciwo kafin yace
“Ko da ban zo ba na san ba zai dame ki ba ummi.. cause u never cared, idan da ace u cared bazaki barni at five years ba, da zan iya da na jima da daina zuwa inda kike…” pauuu marin da ta ɗauke shi da shi ya sa ya tsayarda maganar ba tare da ya ƙarasa ba da sauri Ummah ta taso tana ƙoƙarin riƙeta, Malam yana kallonta yace
“What kind of behaviour is this Asiya” tana huci ta kalli Aryaan tace
“Idan ka kuma mini magana in that tone zaka san ni ce nan na haifeka ba kai ka haife ni ba! Rashin tarbiyyarku ta gidanku ta tsaya iya gidan ubanka! And get out of my house!”
Malam zai kuma magana Abbah ya masa alama da ya barta, tsayawa Aryaan yayi dafe da kuncinsa idanunsa sun yi ja, Ummi ta fizge hannunta daga na ummah ta tafi ta kama hannunsa ta ja shi har ƙofa a zuciye, binta kawai yake yi dafe da kuncinsa ta buɗe ƙofa ta tunkuɗa sa waje tana kallonsa tace
“Sanda ka koyi respecting uwarka da iya magana da ni u come back! I’m still your mother ko ma miye za’a yi brainwashing ɗinka a nuna maka ba zai taɓa canza matsayina na uwarka ba and for that bazan ɗauki disrespect from my own child ba” tana gama faɗa ta rufe ƙofan.
#banidahujjah
#Maimoon
09041426598
https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q
🌺BANI DA HUJJAH🌺
Assalamu alaikum lovelies Bani da hujjah is a paid book, free pages kuma basu da yawa sosai, pls support me by making your payments kafin end of free pages! Thank you so much as you do, ga masu bukatar biya zasu tura 500 kacal zuwaga
7039695535
Palmpay,
Maimunatu Abdullahi muhd
Sai ku tura min evidence of payment ta 09041426598 on whatsapp
Idan kuma katin waya ne zaku tura 500 zuwa ga 07039695535
Thank you❤️
9.
Ya kai three minutes a tsaye dafe da kumatunsa kafin ya juya a zuciye ya nufi motarsa kamar zai tashi sama, ba tare da ya ko kalli Haidar da ke zaune yana waya a compound ɗin ba ya buɗe motar ya shiga mai gadi ya buɗe masa gate ya fice a gidan Haidar ya bishi da kallo.
Driving kawai yake amma zuciyarsa wani irin mugun bugawa da ƙuna da ciwo take masa, dukan steering yayi karo na babu adadi wanda instead of hakan ya sanyaya masa zuciya sai ma sake zafi da zuciyarsa ke yi!
Ganin idanunsa ya fara zama blurry yasa ya gangara gefen hanya ya fara bincika cikin motar inda yakan ajiye cigarette ɗinsa har ya samo kwalin, ya buɗe motar ya fito ya zaga gefe ya fara kokarin kunna lighter a jikin tabar, da ƙyar ya iya kunna cigarette ɗin da ya saka a baki saboda yadda hannunsa ke shaking ya zuƙa tabar sosai kafin ya furzar da hayaƙin yana jin kamar zuciyarsa zata kama da wuta.
Sai Wajen ƙarfe shida ya shigo gidan, sau ɗaya ya kalli motar hamza da ya kusa bumping into him wajen gate saboda how reckless yake driving amma ko kaɗan bai biye masa ko ya bi ta kansa ba ya wuce part ɗin Mami, yana gama parking ya fito har sannan idanunsa bai washe daga jan da yayi ba, ƙofar shiga gidan ya nufa dai dai lokacin salwa ta fito daga cikin gidan riƙe da babban textbook na anatomy da wayarta a hannunta Siyama dake bayanta tana tambayarta ko zata shiga school gobe dan a goben zasu yi resuming, dama ita da siyama suke studying same thing madicine suna 200level yanzu haka, apart from rashin ji Salwa is a gifted child, in dai ƙwaƙwalwar kwashe karatu ne Allah ya bata, Lailerh kuma mass communication take yi itama tana 200level ɗin.
Ko amsa gaisuwar da Siyama take masa bai yi ba ya wuce cikin gida, Salwa tayi dariyar