Showing 1 words to 3000 words out of 30393 words

Chapter 1 - BANI DA HUJJAH BOOK COMPELET HAUSA NOVELS PDF.docx

My Moon   

04 May 2026

520

🌺BANI DA HUJJA!!🌺

By Maimoon

BISMILLAHIRRAHMANNIRRAHEEM ❤️

Godiya ga Allah buwayi gagara misali da ya sake bani damar dawo muku da sabuwar littafina mai suna BANI DA HUJJA!!

Kamar yadda tafiyar TANGLED HEARTS (RUƊAƊƊUN ZUƘATA) ta kasance smooth and full of wonderful memories, ina fatan BANI DA HUJJA ma zai samu matsuguni a cikin zukatanmu gabaki ɗaya daga ni har ku.

To ga dai BANI DA HUJJA nan. Allah Ubangiji ya sa yadda muka fara lafiya, mu ƙarƙare lafiya.

#ARYAAN UMAR TURAKI

#SALWA AMEENU TURAKI

#FAMILY SAGA

1.

A hankali, cikin nutsuwa ya ke sauƙowa daga benen, but at the same time cikin kuzari da taku irin na cikakkun mazaje, that confident masculine stride of a man da ya

san worth ɗinsa.

ƙarasowa falon yayi, ba tare da ya ko kalli sashen da suke tsaye cirko cirko ba yayi wucewar sa ya buɗe ƙofar palourn ya fice kamar bai gansu ba ko bai san da su a palourn ba, da idanu duk suka bisa kowa da irin abinda ya ke saƙawa a zuciyarsa gabaki ɗayansu ɓacin rai ya bayyana ƙarara akan fuskokinsu, har ya fito babban farfajiyar gidan da akayi parking motoci na alfarma guda 2 banda nasa da ke usual spot din da yake parking a gidan, direct motar tasa ya nufa mai matuƙar kyau da tsada ya buɗe motar ya shiga sannan ya maida murfin ya rufe tare da sauƙe gajeren ajiyar zuciya, whatever emotions he was carrying, he wasnt ready to share it with the world ya dannesa a cikin ƙirjinsa, har lokacin ba'a iya ganin furkarsa, bare asalin yanayin da fuskar ke ciki, saboda p-cap din da ke kansa, da kuma shade ɗin idanunsa, sannan ga nose mask ɗin da ya sa ya toshe hancinsa da bakinsa.

A hankali ya soma driving har ya fice a gidan bayan mai gadi ya wangale masa gate ɗin, ya cilla motar titi, tafiyar da baifi ta minti ashirin ba, ta kawo sa ƙofar wani restaurant, wanda daga samansa aka rubuta Amaira Restaurant and co, sauka yayi tare da nufar ciki kai tsaye yana tafiya a nutse, ƙananun kaya ne a jikinsa as usual dan kafin ka gansa da manyan kaya zaka daɗe he’s always simple on ƙananun kaya, mostly ma white ko kuma black shirt,

cikin sauri wani ma'aikaci da ke sanye cikin uniform na ma'aikatan wajen ya ƙaraso wajensa, ya gaishesa tare da miƙa masa wata leda at the same time yana mamakin shigowarsa ciki da kansa yau kuma, dan on normal days yana isowa yake kira a kai masa har mota.

karɓa yayi bayan ya amsa gaisuwar ciki ciki, ba lallai wanda yayi gaisuwar ma yaji amsar ba ya juya ya fice a wajen ba tareda ya sake ce masa komai ba, shi dai ya bisa da kallo kawai.

Motar ya koma ya shiga ya tada ya bar wajen, sai da yayi tafiya aƙalla ta mintuna ashirin zuwa ashirin da biyar kafin yayi parking a ƙofar wani ƙaramin gida ɗan madaidaici mai kyau, sauka yayi ya tura gate ɗin kasancewar babu mai gadi, sannan ya dawo ya shigar da motarsa, ya maida gate ɗin ya rufe, ledan ya ɗauka sannan ya rufe motar ya nufi hanyar shiga cikin gidan kai tsaye, a bakin ƙofar falon ya tsaya ya ciro makulli a aljihunsa ya buɗe kofar ya nufi cikin falon da ke da duhu kasancewar labulayen ɗakin masu kauri duka a sake suke, karasawa yayi ba tare da ya kunna fitila ba, har ya kai tsakiyar falon, kafin ya ciro wayarsa tare da kunna haske, ɗakuna biyu ne a cikin falon dake kallon juna, ƙarasawa yayi kai tsaye jikin ɗaya daga cikin ɗakunan, ya buɗe ƙofar ɗakin ya zura kafafunsa ciki, yana haskawa da fitilar wayarsa kasancewar nan ɗin ma ba hasken kirki

Sai da kalli labulayen ɗakin da suke sake suma kafin ya Hasketa da fitila yana kallonta ba tare da ya ƙarasa cikin ɗakin sosai ba yana tsaye daga bakin ƙofa ya harɗe hannunsa a ƙirji girarsa a haɗe.

A zaune take a gefen gado, ta sanya kanta a tsakanin kafafunta, kanta babu ɗankwali, kasancewar ta haɗa kai da gwuiwa ne ya Sanya gashinta ya sauƙo ya rufe fuskarta har yana taɓa gwuiwarta, baka iya ganin furkarta sam, saboda irin zaman da tayi a cikin duhun ɗakin.

second 5 yayi yana kallonta then as if forced ya Ƙarasa cikin ɗakin ya tsaya akanta yana cigaba da kallonta, idanunsa suka sauƙa akan hularta da hijab ɗinta da ta ajiye a gefenta, juyawa kawai yayi ba tare da yace komai ba ya fice a ɗakin, kusan mintuna 3 da fitarsa sai ga hasken wutan lantarki ya gauraye ko ina na gidan ya dawo cikin ɗakin still with his nose mask and shades on yace

"ke"

bata ɗago ba, kuma bata da niyyar ɗagowar bare ta kulashi, sai kuka da take ƙasa ƙasa, bai sake tanka mata ba ya ajiye ledan hannunsa dake ɗauke da take away ɗin abinci a bedside daga haka ya nufi ƙofa, a hankali ta buɗe idanunta ta ɗagosu daga gwuiwarta da ta kifa ta bisa da kallo idanunta duk sun kumbure saboda kuka, she couldnt believe he is leaving again, sake tafiya zaiyi yanzu ya barta a wajennan?, ta tura baki tana binsa da kallo da manyan idanunta da ke tsiyayar da hawaye, ita babban damuwarta ma yanzu ta san sai ya kashe power ɗin gidan kafin ya tafi, ta shiga uku, gashi yamma ya soma yi sosai dan its past 4, har ya fice a ɗakin kafin ta kalli hularta da hijab ɗinta da tayi sallar la’asar da shi, miƙewa tayi ta sauƙa daga kan gadon ta wuce toilet idanunta na sake cikowa da hawayen takaici da baƙin ciki, gabaki ɗaya duk wani baki da tsiwa nata ya mutu murus kamar ba ita ba, wanke fuskarta tayi ta wanko hannunta tana kallon fingers ɗinta that are so fyn and fragile yadda ruwa ke zuba a tsakaninsu a ƙarƙashin tap ɗin, kafin ta cire su under tap ɗin ta fito cikin ɗakin tana tafiya a hankali kamar mara bone sanin har yanzu yana gidan bai tafi ba tunda ga wuta nan bai kashe ba, dan punishment ɗin da yake mata shine kashe wutan gidan gabaki ɗaya idan zai fita duk da yadda take da mugun tsoro kamar farar kura haka take zama ita kaɗai kamar mayya gashi ya ƙi bata wayarta, wannan punishment ɗinnasa scares her more than anything.

ƙaramin ƙugi da cikinta yayi yasa ta dafe shi a hankali, ba ƙaramin yunwa take ji ba don abincin safe da ya kawo mata da tayi taurin kai ta ƙi ci ɗaukewa yayi ya tafi da shi bayan uban aikin gyaran gida da ya saka ta, bata da zaɓi than ta ci wannan ɗin yanzu, ta ƙarasa gefen bed ta zauna ta ja abincin ta soma ci hawaye na sake cikowa idanunta, sam ba abinda take so bane a takeaway ɗin, kaɗan ta ci ta sha ruwa da ke ciki ta sake jingina da gado tana matsar hawaye, kamar kuma wadda aka tsikara ta saka kuka tana shure shure akan gadon, gabaki ɗaya ji take kamar ba ita ba, kwata kwata bata jin daɗin rayuwarta, duk duniya bata jin akwai wanda ya tsaneta irinsa, kuka ta dinga rairawa kamar an aiko ta ne dama ta yi shi tana yi tana kiran Daddy.

Yana jinta daga kwance da yake a dogon kujera a palour yana danna wayarsa amma ko kallon hanyar ƙofar ɗakin baiyi ba, jin kukan ya ishe shi ya sa ya miƙe ya fice a falon tare da rufe gidan gabaɗaya this time around bai kashe wutan gidan ba ya shige motarsa ya bar unguwar gabaki ɗaya ya nufi gidansa.

Parking yayi a space ya buɗe motar ya sauƙo bayan ya kashe ta ya nufi cikin gidan yana sake tamke fuska ganin har sannan motocinsu na nan a farfajiyar gidan alamar basu tafi ba suna nan suna jiran dawowarsa, gabaɗaya shi sam ya ma manta da ya barsu a gidan ba don motocinsu da ya gani a farfajiyar ba har sannan alamun suna gidan shi wallahi ya mance da su.

a falo ya same su, ga baki ɗayan su fuskarsu babu yabo babu fallasa, infact zunzurutun ɓacin rai ne ma a kwance akan duka fuskokinsu.

Ciki ciki yayi sallama, ta yadda bayi da tabbacin wani acikin su ya ji shi, bai bi ta kansu ba ya nufi sama.

"Aryan!”

Ya ji an faɗa a bayansa wanda yana da yaƙinin cousin brother ɗinsa hamza ne, ba tareda ya bi takan hamzan ba ya sake cigaba da tafiya, uncle Ameenu ya sha gabansa yana faɗin

"Ba ka ji kiran da yayanka ya maka bane? Ko bai kai ya dakatar da kai ba?, iyakar mu kake so ka nuna mana kamar yadda ka saba? Ina tambayar ka?" ya faɗa tare da saka hannu ya hankaɗa kafaɗar sa, ko gezau bai yi ba, sai idanunsa da suka soma kaɗawa daga farare tass suna surkawa da ja dan yanzu babu shades a idanunsa tun kan ya shigo ya cire shi, ya sauƙe idanunnasa ƙasa ya ƙi ya kalleshi, Uncle muhammad da ke tsaye gefe shima ransa a ɓace ya karɓe da faɗin

"Me ka mayar da mu ? mutanen banza? Kiran duniya an maka kaƙi ɗaukar waya, mu tako Muzo wajenka takanas amma dan raini da wulaƙanci ka sauko ka ganmu, sai ka fita ba tare da kace uffan ba, sannan ka dawo zaka sake hayewa sama, wato ga ƴan iska koh? Kai waye, me kake jin kanka? Me kake taƙama da shi? Yaushe ma aka haifeka Aryan?”

Uncle Muhammad ya ƙarasa faɗa ransa a mugun ɓace dan ba ƙaramin zafi abin ya masa ba.

Har lokacin bai da alaman zai furta wata kalma, sai ma lumshe idanunsa da yayi yanajin wani mugun raɗaɗi a zuciyarsa

Hamza ne yayi ƙwafa yana kallon mahaifinsa uncle muhammad ya ce

"Dad ka gani koh? na faɗa maka wallahi ba zai ce muku ƙala ba, uwarsa ce ta koya masa duk wannan halin gaba ɗaya, yaro an koya masa raini da rashin girmama na gaba da shi, ba iya mu yayunsa ba har ku iyayensa, mara tarbiyya kawai"

ya faɗa yana huci tare da kallon sa har lokacin yana tsaye ƙiƙam, sai dai wannan karan yayi folding hannayensa a ƙirji yana sauraron duk abinda suke cewa, jin Hamza ya ambaci umminsa yasa ya ɗago idanunsa ya dube sa,

"ƙarya yayi ne? Kake kallonsa da waɗannan idanunnaka maye? Ko ƙarya ya mata ne?”

Uncle Ameenu ya faɗa yana kallonshi , a yanda idanunshi suka kaɗa sukayi ja a lokacin zai tabbatar maka da ranshi ne yake ɓaci da tafasa a ƙarƙashin ƙirjinsa amma duk da haka bashi da niyyar cewa komai.

cikin jin daɗin zai tanka ganin reaction ɗinsa Hamza ya sake faɗin

"Oh sorry, the mistress ya kamata ince, dan na tabbata tana can tana abinda ta saba, ta gagara zaman aure!, matar da ke zaman kanta, waya sani ko kaima abinda kake yi kenan, ka biyo footstep ɗinta shiyasa ka keɓe kanka, ka rabu da family house ka dawo gidanka kai kaɗai......"

Kasa ƙarasawa yayi jin numfashin shi na shirin rabuwa da gangar jikinsa, sakamakon wani irin fizgosa da yayi ya buga da bango ya bishi ya shaƙe da iya ƙarfinsa, zuciyarsa har wani racing take yi, nose mask ɗin da ya sa ya toshe fuskarsa da shi ya zame ya dawo ƙasan wuyansa, cikin idanun Hamza yake kalla kamar yadda shima yake kallon nasa da idanunsa da ya zaro waje sakamakon shaƙar da ya masa.

In a very shaky voice ya buɗe baki yana cigaba da kallon Hamza cike da warning yana ƙara shaƙesa da iya ƙarfinsa yace

“Don't you dare, stay within ur limit......" Sai kuma ya kasa ƙarasawa ya cije lips ɗinsa kawai yana haɗiye wani irin takaici da ya taso masa yana kallon idanun hamza da suka soma kaɗawa, Hamza da yaji ƙamshin lahira, idanunsa duk sun firfito waje gabaki ɗaya ga wani yawu da yake ji na taruwa a maƙogoronsa da ya kasa haɗiyewa, ya saka hannayensa biyu ya rirriƙe hannunsa dake wuyansa yana ƙoƙarin cirewa amma ya kasa.

"Aryaan!!" uncle Ameenu da uncle muhammad da ya ga ana ƙoƙarin hallaka masa ɗa suka shiga kiran sunan sa ganin kamar baya cikin hayyacinsa sai sake tightening shaƙar yake yi

"kashe shi zaka yi? Baka da hankali ne Aryaan?, ka sake shi na ce!”

sam babu alamar ma yana jin su dan yanda yake sake shaƙe Hamza da gini, da ƙyar suka iya raba shi da wuyan Hamza da shima ke iya ƙoƙarinsa ganin ya ƙwaci kansa a hannunsa amma ya hanasa ƙwaƙƙwaron motsi saboda yadda yayi cornering ɗinsa a jikin bango, zuwa lokacin ƙoƙarin shurawa kawai yake idanunsa duk sunyi jajir, sai ƙoƙarin dambe yake da shi amma yaƙi bashi space da damar yin hakan.

wani wawan mari uncle Ameenu ya sauƙe ma Aryan a fuska, yana faɗin

“lallai wuyanka ya isa yanka Aryaan, la shakka Asiya ce uwarka, to bari kaji ni da kyau ka faro abinda bazaka iya karasashi ba Aryaan, ka jira hukuncin wannan abin da ka aikata, abin kuma da ya kawo mu dama bai wuce sanar maka da cewa mun baka nan da watanni da basu haura 2 ba ka nemo mata muyi maka aure ko kuma kaga mata a gidannan a cikin dangin da kake gudu, dan wallahi baka isa kana yawo kana abinda ka ga dama da yaran mutane a garinnan ba yana dawowa kunnenmu kana ɓata mana suna ba, da darajarmu da mutuncinmu a garinnan, baka isa ba, idan mu baka jin tsoronmu sannan baka ɗauke mu a bakin komai ba ka raina mu baka ganin mutuncinmu, to tabbass zaka ji kira daga mai kankat wato mahaifinka UMAR kuma na tabbata kasan haduwarku da shi, dan gwara mu da ka raina a kansa, haduwarka da shi ba zai maka daɗi ba mara mutuncin yaro, ɗan iska”

Daga haka ya kama hannun Hamza da uncle Muhammad ke bama ruwa ko ta kansu bai bi ba, idanunsa sunyi jajir suka fice a gidan gabaki ɗayansu suka barshi nan tsaye yana huci da sauƙe ajiyar numfashi.

#banidahujja

#Maimoon

09041426598

🌺BANI DA HUJJA!!🌺

2.

Iskar da ya cika bakinsa ya furzar cikin matuƙar ƙunar rai yana cigaba da bin ƙofar da suka fita da kallo.

Two months? Is this a joke? Mata a wata biyu? wannan ma ai ba mai yiwuwa bane kamar wani shirin film, a ta ina zai nemo matar a wata biyu kacal, infact shi bai ma shirya zama tied to ko wace mace yanzu ba at all, baya buƙatar aure kwata kwata a rayuwarsa a yanzu, juyawa yayi ya wuce sama jikinsa har tsuma yake.

"Yaya UMAR baka ga abinda ɗanka ya mana ba, wallahi ko kare bazai ci ba, tabbass yaron nan shaiɗani ne fiye da yanda muka yi zato, bashi da mutunci bashi da tarbiyya sannan bashi da hankali" Uncle Aminu ya faɗa yana huci, uncle muhammad da shima ranshi har sannan ke ɓace ya karɓe da faɗin

"Kai ba ma wannan ba, ka ga dukan da ya ma Hamza?ya shaƙeshi yana neman kashe shi kawai dan ya faɗa masa gaskiya, gashi nan duk wuyansa yayi jajir sai da aka shafa masa man zafi, kuma a gabanmu saboda bai ɗauke mu a bakin komai ba ya gama raina mu, wallahi tallahi bazan taɓa barin wannan abin ya wuce a banza ba, kawai dan ya faɗa masa gaskiya, wallahi bai isa ba"

uncle Muhammad ya ƙarasa faɗa yana nuna masa wuyan Hamza da yayi mugun ja abinku da fari sai ƙyallin man zafi yake.

Dad dake zaune ƙafarsa ɗaya akan ɗaya, da cup na coffee a hannunsa wanda shansa ya kasance al'adarsa ya ajiye cup ɗin hannunsa a kan center table tare da gyara zaman newspaper dake kan table ɗin kafin ya miƙe tsaye, sam bazaka iya karantar a wani yanayi fuskarsa take ba, baya ya juya musu tare da folding hannunsa duka biyu ta baya kafin a hankali cikin kamilalliyar muryarsa yace

"kun isar masa da saƙo na?”

Cikin zafin yanda baice komai akan abinda Aryaan yayi ma hamza ba, uncle Muhammad yace

"Ameenu ya isar masa "

bai sake cewa komai ba yayi wucewar sa ya barsu a tsaye a wajen, zuciyoyinsu cike da takaici, da baƙin cikinsa.



Tun daga bakin ƙofa take kare masa kallo tana wani irin shu'umin murmushi, a hankali ta soma takowa zuwa cikin ɗakin tana tafiya a hankali saboda yanda kayan jikinta ya kamata duk da atampa ce a jikinta amma an mata wani irin ɗinki na rakani gantali, ga wani uban hill da ke ƙafarta,ta zubo da kitson da aka mata da gashin kantin da yayi matuƙar mata kyau har gadon bayanta, sai wani ɗan siririn gyale sharara da ta ɗaura bisa kai wanda da shi da babu duk uwar ubansu ɗaya, black beauty ce kyakkyawar gaske, komai yaji masha Allah da ita.

a hankali take tafiya tana murmushi ganin yanda yake kwance akan gadon ko takalman ƙafafunsa bai cire ba, daga gani baccin ya ɗaukesa ne ba tare da ya shirya ba dan half ƙafafunsa na ƙasa gefen gadon other half na jikinsa kuma yana kan gadon, gashin kansa ya rufe masa kusan rabin goshinsa saboda yanda ya kwanta a rigingine.

A hankali ta zauna a gefen gadon tare da shafa fuskarsa tana murmushi, gashin nasa da take mugun so ta sa hannu ta shafa a hankali kafin ta cigaba da shafa gashin da ke da matuƙar santsi ba sai an faɗa ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login