Showing 18001 words to 21000 words out of 100116 words
Karki damu Farooq mijinki ne kinji?
Ummie bata de komai ba sai ajiyar zuciya kawai takeyi...
★★★★★
Hadarin daya hado a garin shi ya saka ta fito ta fara kwashe wankin da Zainab tayi kafin ta tafi aiki.
Tas ta kwashe su tana komawa daki, saboda iska da ake yi alamar hadarin ya taso ruwa daf yake da sauka.
Kallon UMMIE tayi dake cin tuwo ta ce " Kyakkyawar Umma an samu abinda ake so ko?
"Eh, Aunty Zauna ta iya tuwo"
"Yau kuma kece da yabon Zainab? Cewar Aunty da ta fito daga uwar ɗaka.
Dariya UMMIE tayi ta cigaba da shan miyar kuka dake cikin ruwan.
"Sannu Zarah, ina ta sauri na fito na kwashe kayan ashe har kin kwashe"
"Eh Aunty, sun ma bushe bari na ninke ma ta"
Cewar Zarah tana fara ninke kayan.
Tayata Aunty ta farayi. Suna cikin ninkin Aunty ta kalleta ta ce " Zarah!
"Na'am Aunty" Zarah ta amsa tana kallonta.
"Maganar aurenki da Shehu! Ni bana so ki koma gidansa cutarwar tayi yawa"
Murmushi kaɗan zarah tayi ta ce " Ya zanyi Aunty?
"Kina nufin zaki koma?
Taji Muryar Zayd ta ziyarci kunnent. Da sauri ta kalli bakin kofar dakin, shine tsaye ruwa ya dan jikashi.
Sunkuyar da kanta ƙasa tayi ba tare da ta ce komai ba.
Karasa shigowa yayi yana kallonta ya ce " Komawa zakiyi Zarah?
" Meyasa zaka titsiyeta haka? Aunty ta fada tana kalllonsa.
"Ku barta ta amsa! Ki fada min zaki koma?! Ya faɗa ransa duk a ɓace.
Shuru tayi ta kasa amsawa, bata tunanin zasu fahimci abinda ta fahimta, babu yadda zatayi shi din mijinta ne kuma uban yaranta.
"Bakya ji na ne? Y fada kamar zai daketa. Matsawa baya tayi dan taji tsoro.
"Uncle Zayd meyasa kake wa Ummana tsawa?
Cewar Ummie tana lashe hannu. Saita temper dinsa ya fara yi idanunsa har sunyi ja.
"Zo muje UMMIE" Aunty ta fada tana kama hannunta.
Daukar kwanon tuwan Aunty tayi suka bar wajen da bata so anayin wasu abubuwan a gaban UMMIE.
Matsowa yayi kusa da Zarah yana kallon kanta dake kasa ya ce " Zarah fada min, kina son komawa?
Sai a lokacin ta ɗago ta kalleshi amma ta kasa furta ko da kalma daya.
"Zarah Please! Enough! Enough Dan Allah bazan iya jurewa ganin ki cikin wahala ba, zuciyarta tana zafi"
"Why? Ta fada tana kafeshi da idanu.
"Kinason kisan dalili? Ya faɗa yana kallonta ransa duk ya kara ɓaci idanunsa sunyi ja.
"Uhm" Ta fada tana dan matsawa baya.
Runtsa idanunsa yayi kadan tana juya ma ta baya tare da yin addu'a a ransa.
Da sauri ya bar wajen kamar wanda ake bi.
Dogon ajiyar zuciya ta sauke tana zama a kan kujera, dagaske idan ta rabu da Shehu Zayd zai aureta? Duk da bata so shi amma tana jin zata iya zama dashi dan bai da wata makusa a tare dashi, kuma tana da tabbacin zai riƙe ma ta yaranta kamar nashi! So zata nemi saki ne a wajen Shehu? Tabbas! Zata kaishi kotu dan a raba auren! Tana wannan tunanin Zainab ta shigo hannunta riƙe da lema, bata wani jike ba saboda Husband to be dinta ne yake ya daukota kuma ya bata lema ta shigo gida saboda kar ruwa ya jikkata kafin ta karaso cikin gida.
"Zarah! Tunanin me kike yi haka? Ta fada tana ɗan yarfa ma ta ruwan dake jikin lemar.
Dogon numfashi ta sauke tana fadin " Har kin dawo?
"Eh, me aikin yamma tazo min da wuri shiyasa, amma tunanin me kike yi haka?
"Kinga bana son dogon surutu ki canza kaya kizo ga abinci muci"
"Shikenan" Zainab ta faɗa tana nufar dakin da Aunty ta shiga dazu tare da UMMIE.
Bata daɗe a ciki ba ta fito tana kallon Zarah da ta kuma lulawa duniyar tunani. Abincin ta zubo har ta kawo gaban Zarah ammma bata sani ba.
"Sakko daga kujera muci abinci"
Sai a lokacin ta kalli Zainab ta ce " Toh" a hankali ta sakko ta saka pillon kujera sannan ta zauna suka fara cin abincin duk hankalinta baya jikinta.
Sai da suka kammala cin abincin sannan Zainab ta kalleta ta ce " Kunyi Maganar komawa gidanki da Aunty ne? Naga duk yau dinnan sai a hankali"
"Hakane munyi maganar amma bana tunanin zan kuma komawa idan bazai sakeni ba zan kaishi kotu ne kawai"
Murmushin jin dad'i Zainab tayi kafin ta ce " Amma naji dad'i, ai ba kowani zama akeyi wa hakuri ba ke kham kinyi hakuri iya hakuri Allah dai ya tabbatar mana da alkhairy"
"Amin" Zarah ta amsa tana sauke ajiyar zuciya.
★★★★★
Baya jin zai iya zuwa gida a yanzun dan yasan by now Aunty ƙarama ta kira Mama ta sanar da ita abinda yace da UMMIE dan yasan ba boyewa Ummin zatayi.
Shi kanshi be san inda zai nufa ba tuki kawai yake yi dan bai da wani wajen zuwa gaba ɗaya baya jin dadin yanayin yadda yake ciki, da ace Mama zata kyaleshi yaji da abinda yake damunsa a zuciyarsa da yafi sauki amma yanzu bai san ma da me zaiji ba.
Gefen titi ya gangara yayi parking yana kallon tsirarrun motocin da suke wucewa.
Lumshe idanunsa yayi yana jinginar da jikinsa jikin kujera tare da dafa goshinsa da hannunsa na dama.
Wayarsa ce ta fara ruri, dubawa yayi yaga Yusuf ne ke kiransa. Ɗauka yayi yana karawa a kunne ba tare da yayi magana ba.
"Farooq! Yaji Muryar Mama kamar zata fasa wayar. Runtsa idanunsa yayi yana ɗan cizar lebansa, tasan da ita kirashi bazama lallai ya dauka ba shiyasa ta kira da wayar Yusuf.
"Baka ji ne wai?
Ya sakeji ta fada ranta alamar a ɓace yake.
"Ina kan hanya ne shiyasa" Ya fadi yana whining down Dan taji karar motoci sosai.
"Ok kayi sauri ka dawo ina jiranka"
Daga haka ta katse wayar. Ajiye wayar yayi yana kunna motarsa ya bar wajen ya dauki hanyar komawa gida.
A tsaye ya tarar da ita ranta duk a ɓace, hannayensa ya zuba cikin aljihun wandonsa yana kallonta ya ce " jirana kike shine kika zo nan kika tsaya? "Bansani ba! Wai Farooq me yake damunka ne? Bazaka girma kasan inda yake maka ciwo ba? Ita yarinyar da ka kasa yin gaba a rayuwarka domin ta gata chan har da yarinya ɗaya! Ko yau ta mutu tana da mai yi ma ta addu'a, amma kai fa? Wai wani irin aljanune da kai ka kasa cire mata wani a ranka?
Murmushi yayi kaɗan yana dafa kafadarta ya ce " Relax mana! Shikenan kiyi hakuri bana so kina bata ranki akan petty things irin wannan"
Kwace kafadarta tayi daga hannunsa tana nufar cikin falon ta ce " Ni dai na fada maka kuma ka saka rana ka koma ka bawa UMMIE hakuri dan aurenka da ita babu fashi insha Allah"
Bai ce komai ba ya nufi hanyar matattakala. "Baka ji bane? Mama ta dake faɗa tana kallon bayansa. "Insha Allah" Ya faɗa ba tare da ya jiyo ba.
★★★★★
Tun bayan sallar isha'i ta kwanta tana jin jikinta duk ba kwari. Har bacci ya fara daukarta ta jiyo Muryar Shehu kamar a mafarki yana kwallah mata kira ga kuma Muryar Zayd da ta Aunty har da Zainab ma.
Da sauri ta sakko daga kan gadon tana sai slippers ta fito falon, tabbas Shehu ne.
Yana ganinta ya ce " Mu tafi gida!
Tsayawa tayi daga inda take ta ku ƙarasowa, Aunty, Zayd da kuma Zainab suka juyo suna kallon ta.
Karasowa yayi inda take ya kama hannunta yana faɗin " Ko kwana ɗaya bazaki karayi a gidan nan ba"
Kwace hannunta tayi da sauri tana kallon sa. Shima tsayawa yayi yana kallonta ransa duk ya gama ɓaci.
Sake kamo hannunta yayi ya riƙe gam ya ce " Dole ki bi ni zuwa gida"
Kokarin kwace hannunta take amma ta kasa. Zayd ne yasha gabansa yana fadin " Dallah malam saketa"
Hannu daya yasa dan ya ture Zayd amma ko motsi beyi ba. Sakin hannun Zarah yayi yasa hannu biyu yaturr Zayd yana fadin " Kai har ka isa kayi min iyaka da matata?
"Uban waye ya baka izinin shigo mana gida? Ko nan gidan ku ne? Zainab ta faɗa tana hura masa hanci.
Gyara kwalar rigarsa yayi ya ce " Wannan kike kira da gida? Banda wannan sakaryar ma me zai kawo ni wannan akurkin"
Juyo dashi Zarah tayi zuciyarta na lugude ta ce " Idan ka kara taka kafafunka cikin gidan nan sai kayi daka dani"
"Ke! Ya faɗa yana rike hannunta tare da murdawa.
"Zayd kwace ta mana" Aunty ta fada ganin yadda Zarahn take cije baki alamar da zafi.
Rana duk a bace ya bar wajen dan Zarahn ma ta fara bata masa rai.
Su Zainab naji na gani yaja Zarahn suka bar gidan da tsohon daren dan goma har ta wuce......
Autar Mama ce.
✨✨ *UMMIE* ✨✨
_Labari daya danganci soyayya da kuma ƙalubalan rayuwa_
*FREE BOOK*
*MALLAKAR*
*Autar Mama*
*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)
*Follow me on Wattpad @Autarmama56*
I just published "Chapter 10" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1174739022?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=V7yHLlRAWz61KYtx6X%2BHPlhZeGTLmtHQNEUcjZfi2EnUPqQsvfv4%2FwnDzxrKS2gsNm7g5Lmg%2FJH1GkLFKxcsmXW%2BS5deDziVrbQE7XZAU3u2vzaNP6zPA2uORMLF45La
*Please tun a farko nayi bayani idan zaki fara bi ki fara bi kafin nayi nisa dan bazan iya turawa ta Private ba, fatan zaku fahimta*
*Comment da voting shi zai sa a dinga samun update da wuri*
*Whatsapp group pls banda maza, and idan kina group one kar ki shiga wannan duk abu daya ne*
https://chat.whatsapp.com/I1e40OT9rRwBgFU3xD0aYg
*Aslm inayiwa masoyana fatan alkairi, inamasu bibiyan littafin Momin haneef,tazomuku dasabon littafinta maisuna RA YUWAR SAFEENAT Labari maijike dad'umbun darasi yaudara cin'amana da kuma soyayya zai ilimantar daku kubiyoni acikin Labarin shi wannan littafin dakud'ine kiyi kokari kimallakeshi karkibari astaya baki labari bayida stada akan kud'i kalilan zakusamu 200 naira only kiyi magana tawannan number 07026368879*
*Ina kuma sanar daku zagwaguri zazzafan littafin mu maisuna kamar su d'aya kuyi kokari kunema akan kud'i kalilan 300 naira only👌*
*Taurari biyu kuma Matasan marubuta masu tasowa Sunzo muku da dadadan wanda zai nishad'antar daku masoya wannan Matasan marubuta ba kowa bane illa: 𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼,,𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈(𝙠𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 ) Sunzo muku da sabon novels masu suna.
*𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼* tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝘿𝘿𝘼𝙍𝘼 𝘾𝙀)
𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈( 𝙆𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝) tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝙉𝙒𝘼𝙏𝘼)
Kai dajin sunan labarin ma kasan basai an tambaya ba.
*(K'ADDARA CE)*
*Dandano! Dandano!!*
Hanan meye lefin mu dan muna cikin garin Saudiya? Muma bayin kammu bane K'ADDARA CE ta kawo mu cikin Saudiya. Hanan mai muka yiwa mutane suke jifan mu da mummunan kalma?. Cikin masifa Iman Ta zaburo bata yi magana ba ta damk'i hannun Sultana Tace" Ke Sultana muje ki nuna a hanyar shara-mansoor d'in Uban waye ya fad'i miki wannan maganar yau saina wuk'ance shi fuuu suka bar Hanan anan tasaki baki...
*K'ANWATA*
*Dandano!Dandano!!*
Mama kina ganin Abun da Salma taimin? Kin kasa mata magama. Jijjiga Mama take yi tana kuka mai tsuma rai..Mama ta d'ago jajayen idanun ta da suka ciko da kwalla Tace Rahama kiyi Hak'uri kanwar kice... Sharr! sharr!! Idanun ta suke zubar da kwalla da radadi had'e da zallar bakin ciki,take kallon sama ta daga hannayen ta sama tare da fad'in. Ya Allah ya Allah ka gana ganin Abun da K'ANWATA taimun ya Allah ka..
Ga maru buk'atar wannan novels d'in zasu iya tuntub'ar wannan numbobin. 09069080725 our +966599791573
Nomal. guda d'aya N 300 ne
guda biyu N 500 ne
Special guda d'aya N 500 ne
guda biyu N 1000 ne
Zaki iya biyan kud'in ki ta wannan hanyar. 3115484026 Ikilima Adam first bank
✌🏼Fitattu biyu masu ban mamaki🫀Hakika babban goro sai magogin ƙarfe 😍, Hakk'un wani kaya sai amale ke d'auka🐫, Fitattu biyu👯🏽♀sun shiirya tsaf domin nishad'antar daku 🤓 sun shirya tsaf domin fadakar daku🧠 sun shirya tsaf domin dilmiya zuciyoyin ku cikin bege da shauk'in so💋💞, wohoho tabbas ️sahun giwa👣 mai ɓadda na raƙumi 🐪,Fitattu biyu😍✌🏼 masu tafiyar k'asaita, sheƙi, da walwali hak'ik'a koda kud'in ka saida rabon ka😘🏃🏽♀️ Fitattun Ƙarshen shekara😍 salon su daban ne dana sauran domin natsuwa da tunani sunyi aiki pure love and romance abun dai sai wanda yakaranta😍 maza ku hanzarta neman naku karku bari abaku labari🏃🏽♀️
#Oum Sumayya:- *GAMIN GAMBIZA*✍🏽 Nrml 300 Vip 500
#Oum Ikram:- *SOYAYYA CE SILAH* ✍🏽 Nrml 300 Vip 500
Duka biyu 400👌🏼
Vip 700👌🏼
Via 4210014214
Eco bank and send the evidence of payment via 08139624956
Or mtn/airtel credit via 07017296839 banda vtu hoton kati kawai!
*Shafi na goma*
"Indai ina raye Zarah da kuma hankali na bazan taba bari kiji daɗin rayuwarki ba tunda kika zaɓi cin amata tun farkon zaman mu"
Kwace hannunta tayi daga cikin nashi tana masa wani kallo ta ce " Lokacin da nake budurwa banyi zina ba sai dana aureka zanyi?
Matsowa yayi daf da ita yana kallon cikin kwayar idanunta ya ce " Ke kika san wannan amma ni nasan UMMIE ba ƴata bace!
Matsawa baya tayi tana share hawayen dake zubowa bisa kuncinta ta ce " shikenan, tunda ka ce haka UMMIE zata cigaba da zama dasu Aunty"
Daga kafada yayi alamar ko a jikinsa kafin ya dora da fadin "Ban damu ba! Hasali ma an rage min nauyi, inaso ki sani jibi daurin aurena kuma za'a kawo furnitures anjima da yamma idan kika kuskura kikayi musu halin akuyancinki sai na saita miki kanki"
"Akuyanci? Ta fada zuciyarta na zafi.
"Eh akuyanci! Ai akuya ma tafiki daraja a wajena"
Ya karashe maganar yana barin ta a wajen.
Dafa kujera tayi ta zauna tana fashewa da kuka me tsanani.
Sai kusan 11 na safe yayi shirin aiki ya fito yana gyara tie dinsa ya ce " Zan aiko yarona da cefane kiyi musu abinci sannan ki karbesu yadda ya dace dan ba yara bane"
Da toh ta amsa tana dauke idanunta daga kallonsa.
Ficewa yayi ya barta cikin kunci.
Kafin azahar me aiken yazo da kayan masarufi masu yawa, adana komai tayi sannan ta hau girki.
Abinci kala biyu tayi musu sai lemo da ruwa, dibar nata tayi taci ta koshi sannan ta wanke kwanon ta nufi dakinta.
Wanka tayi ta shirya cikin atamfa as usual wadda ta koɗe dan ta daɗe, amma hakan be hanata yin kyau ba.
Kara gyara falon tayi tana jiran isowar bakin.
Bata daɗe da zama ba ta fara jiyo hayaniya da guda sama², tashi tsaye tayi ta nufi bakin kofar falon tana buɗewa, manyan mata ne kusan su biyar sai kuma Sa'adah.
Tana tsaye har suka iso inda take ko wanne yana yi ma ta kallon kashi.
Jikinta a sanyaye ta koma gefe har suka gama shigowa, Ƙanin Sa'adah ta gani yana tahowa yasha askin banza bakinsa da fuskarsa baƙin kirin, kana ganinsa kaga rikakken ɗan iska.
*SALE?* ta fada a ranta tana ƙare masa kallo yadda ya kuma zama ɗan iska bazai wuce 22yrs ba amma duk ya lalata rayuwarsa haka?
Maganar da yayi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi.
Cikin murya irin ta yan shaye² ya ce " Ai wallahi duk inda gaskiya ta ke a fade ta! Ni nasan Sa'adah taci uwar raina miki hankali taci kuma amanar ki da zata aurar miki miji na tsani munafurci fa Allah wallahi"
Ya karashe maganar kamar zai daki Sa'adah.
Ita dai Zarah bata ce komai ba.
" Zarah kiyi hakuri ko! Ya sake faɗa yana dariya.
"Kai dallah kuje a shigo da motar kayan azo a fara jerawa kafin yamma ta kara yi"
Ɗaya daga cikin matan ta fada tana kallon Sale. Bai amsa ba ya juya ya fara tafiya yana wani cilla hannu.
Ajiyar zuciya Zarah tayi kafin ta juyo ta kallesu ta ce " Sannunku da zuwa"
Mutun daya ce ta amsa ma ta saura kuwa ko kallonta basuyi ba"
Kallon Sa'adah tayi wadda tasha gyaran amarci tayi kyau sosai.
"Sa'adah ya shirye²?
"Mtsww, ke dallah bansan munafurci"
Sa'adah ta fada tana harararta.
Shuru Zarah tayi tana nufar dakinta.
Tana jiyo hayaniyarsu sai bayan magariba suka tafi, fitowa tayi falon. An canza komai har TV ansa Dan da bata da ita Shehu ya cire.
Sosai falon yayi kyau babu abinda basu sake ba, tasan da kudin mijinta akai komai dan su Sa'adah basu da wani ƙarfi.
Sosai falon yayi ma ta kyau. Murmushi tayi ta kalli dining area, sunci abinci kuma har dining ɗin sun canza.
Tasan tsofaffin kayan siyarwa zasuyi, bata damu ba dan ba nata bane.
Zama tayi a kujerar tana kunna TV tana sakin murmushi, har ta manta rabon da tayi wani kallo.
A nitse take yin kallonta hankali kwance.
Har bayan isha'i Shehu bai dawo ba. Tana idar da sallar isha'i ta kashe TVn ta koma daki ta kwanta, da tana da waya data kira Zainab sunyi magana da UMMIE. Lumshe idanunta tayi tana tuno lokacin da ta samu cikin UMMIE.
*****
Fuskarta ɗauke da tsananin farinciki ta nufoshi tare da PT din dake hannunta.
Zama tayi kusa da shi tana fadin " Kalli" Sai daya fara rungomota sannan ya kalli abinda ke hannunta. PT ne ya nuna double red line sosai.
"Me hakan? Ya faɗa yana shafa gefen cikinta.
Ɗan bata rai tayi kaɗan ta ce " Ciki ne dani mana kuma yayi wata uku, dan watan uku banyi al'ada ba.
Maimakon taga farinciki a fuskarshi sai taga ya ɗan bata rai yana matsawa daga kusa da ita kafin ya ce " Auren har wata nawa da zakiyi ciki?
Cike da rashin jin daɗin reacting din da yayi ta ce " Watan mu 11 fa!
Tashi yayi ya barta a wajen. Cike da rashin jin dadi ta biyo bayansa tana fadin " Meyasa baka ji dadi ba?
Tsayawa yayi da tafiyar da yake yi ya ce " Bawai banji dadi bane amma yayi wuri gaskiya" Daga haka ya wuce ya barta a wajen.
Bazata manta ba tun daga lokacin Shehu ya fara canza ma ta tun tana rarrashinshi har ta daina, abun ya kara tsananta lokacin daya bukaci tayi abortion taki, ya daina yi ma ta magana kwata² tasha kuka da rokon yayi hakuri amma sam yaƙi, lokacin mahaifiyarta na raye ita ke share ma ta hawaye sannan ta ce karta yarda ta zubar da cikin domin laifi zata aikata.
Daga baya da cikin ya girma sai ya fara wasu zantuka bai yarda