Showing 27001 words to 30000 words out of 100116 words

Chapter 10 - UMMIE Hausa Novels PDF By Autar mama.txt

10 Nov 2025

3450

Mamana, ban barki ba dan san raina ba amma ai nasan kinfi jin dadin zaman nan ko?

Da sauri ta daga kai ta ce " Eh kullum sai Uncle Zayd ya kawo min nama da lemo idan zai dawo daga aiki kuma ya ce min yana sonki yana kaunarki wai zai aureki"

Shuru falon yayi, a hankali hawayen da take rikewa suka zubo bisa kuncinta. Da sauri ta sharesu tana daga UMMIE daga jikinta ta ce " A cire uniform ko?

Da toh UMMIE ta amsa tana nufar inda Aunty ta ke ta ce " Na dawo fa"

Murmushi Aunty tayi tana kallonta ta ce " Na ganki fa ai ni ba makauniya bace kamar Mamanki"

Turo baki tayi tana nufar hanyar ɗaki ba tare da tace komai ba.

"Aunty zamu tafi dare yayi" Zarah ta faɗa tana tashi tsaye.

"Baxaki jira ayi sallar Magariba ba lokacin ma Zayd ya dawo sai ya kaiku"

"Aikuwa dai Aunty Zarah mu bari ayi magaribar"

Cewar Juwairah tana kara relaxing a jikin kujera.

"Kiyi ta zama ni tafiya zanyi kinsan bamuyi abincin dare ba"

Da sauri Juwairah tashi tsaye tana fadin " hakane"

"Toh shikenan Zarah sai mun leko ni da Zainab insha Allah"

"Toh Aunty ki gaida ita" Zarah ta fada tana nufar bakin ƙofa.

UMMIE ce ta fito daga daki har ta sauya kayanta. Kallon su Zarah tayi ta ce " Ina zaku?

"Gida" Juwairah ta fada tana jan kumatunta.

" Nima zanje" UMMIE ta fada tana riƙe hijabin Zarah.

Riƙeta Aunty tayi su Sarah suka fita kamar zatayi kuka.

Har dare UMMIE ranta ba dad'i taki cin abinci sai kumbure² take yi.

Da kyar bacci ya dauke ta Aunty ta kaita daki.

Zainab ta rigashi dawowa dan 9 saura zauna ta dawo daga aikin yamma. Tana cikin cin abinci ya shigo.

Takalmansa ya cire sannan ya shigo yana zama a kujerar da Zarah ta zauna dazu.

Jin ya zauna a kan abu yasa shi tashi ya duba, key ne kamar na daki. Daukar key din yayi yana juyawa kafin ya ce " Wannan fa?

Kallon key din sukayi kafin Zainab ta karba tana fadin " Kamar key din dakin Zarah"

"Tazo ne? Ya faɗa yana kallon su.

"Eh tazo ita da kanwar mijinta"

Aunty ta bashi amsa. Bai ce komai ba ya ajiye key din yana tashi ya nufi ɗaki.

"Nifa kwana biyu na kasa gane kan yaron nan, banda Ummie bashi da abokiyar hira yanzu"

"Sai addu'a kawai lamarin nashi har da sharrin zuciya, sosai yanzu yake kaunar Zarah bayan yasan tana da aure"

"Shi ya fada miki hakan? Aunty ta fada tana kallonta.

"Be fada min ba amma na gane hakan, inda ace watarana zaki saurari hirarsu da ummie zakiji yadda yake sakar baki yake fadawa karamar yarinya yadda SOYAYYA ta ke zakiji yadda yake barin zance yana fada mata yadda yake ji a akan uwarta da ace bansan Zarah ba wallahi cewa zanyi asiri ta yi masa"

"Ikon Allah, amma kham lamarin nashi akwai gyara"

Cewar Aunty tana mamakin lamarin.

"Aikuwa dai da ace ma Zarah nada kanwa ne sai a aura masa ita"

"Akwai yara a kauye ai zanje na nemo masa me hankali ko ƴaƴan Dattijo (Yayanta) baza'a rasa budurwa ba"

Numfashi Zainab ta sauka a hankali ta ce " Aikuwa dai karki fada masa wallahi sai dai kawai yaji maganar auren idan ba haka be kinsa bazai yarda ba"

"Ai bazai ma ji maganar auren ba sai dai yaga mace an kawo masa dan banga yana da niyyar aure ba gashi sai kara girma yake yi"

"Aikham dai Aunty, kawai ko zuwa gobe ne tunda bani da aiki sai ki tafi nan da kwana biyu ai nasan bazaki rasa matar da zaki hadashi da ita ba tunda akwai ƴanmata sosai cikin babban gida"

"Hakane kham"

Aunty ta fada tana tashi ta nufi ɗaki. Zainab kuwa wayarta ta ciro a charji ta fara dannawa. Ji tayi a fizge anyi cilli da ita.

Zaro ido tayi tana kallon inda wayar ta fadi dan ko sati wayar batayi ba Hubbyn tane ya kawo ma ta.

"Duk zaman da kikayi a gida na bawa Aunty shawarar ta je ta nemo miki miji a kauye?

Wani kakkauran yawu ta hadiya ganin yadda ransa yake a matuƙar ɓace.

"Ba tambayarki nake ba!? Ya faɗa yana kallonta.

Shuru tayi zuciyarta na lugude. "Answer me! Ya sake faɗa cikin tsawa wanda yasa Aunty fitowa daga ɗaki.

"Me haka ZAYD? Dukanta zakayi ko me? Aunty ta fada tana shiga tsakaninsu. Ransa a matuƙar ɓace ya juya musu baya ya ce " Allah duk ranar da aka daure min aure da wata ba tare da izinina ba billah a lokaci zan saketa! Daga haka ya barsu a wajen.

"Ya akayi yasan da maganar? Aunty ta fada tana kallon Zainab da tayi wuri² da idanu.

"Yaji hirar mu ne fa, nidai na fita daga zancen" Zainab ta fada tana nufar inda wayarta take ta dauka ta nufi daki.

Ran Aunty a ɓace ta nufi dakinsa. A zaune ta ganshi yana rike da kanshi.

"Zayd! Ta kira sunansa fuska a tamke. A hankali ya ɗago ya kalleta idanuwansa sunyi jajir.

"Aure kham dole kayi shi! Ba wani ne ya aikeka kayi zurfin ciki ba ba wani ne yace ka biye abinda kake ji a ka Zarah ba, sai yanzu da lokaci ya kure sannan zaka fito da *SIRRIN ZUCIYAR KA?* Aure kham ya zama dole bazan zuba maka idanu a wannan shekarun naka ace baka da aure ba kuma kana da halin yi bazai yuna wallahi idan baza nemo ma ta ni zan nemo maka na baki nan da wasu lokuta"

Daga haka ta fita barshi a dakin. Iska ya furzar yana me ambaton Allah a fili.

★★

A kwana a tashi ba wuya kwanan amarya hudu su Juwairah suka koma Qatar. A yan kwanakin nan Zarah ta samu saukin masifar Shehu dan yanzu baya bi ta kanta kullum yana wajen amarya abincin dare ma kullum a waje suke ci daga ita sai gate man kawai take yin girkin dare kafin su dawo zata kwanta sai waje gari da rana Sannan zasu kara haduwa, tana fata ace tafiyar ma zata tafi haka dan ta huta da duka da masifarsa.

Yau ta kasance Lahadi kuma yayi dai-dai da satin Sa'adah guda a gidan sannan yau Zarah zata karbi girki duk da cewa tsahon satin ma ita take yi.

Tana zaune a farko tana kallo dan ta gama komai. Shehu ne ya fito daga daki cikin kayan shan iska yana kallonta ya ce " Dama nazo ne ki siyar min da kwananki nawa zan baki?

Murmushi tayi kadan ta ce " Kwana nawa zan siyar maka?

"Sati biyu" Cewar Sa'adah data fito daga daki yanzu tasha kananan kaya masu shegen kayi da nuna tsiraici.

Ɗauke idanunta tayi daga kanta ta mayar kan mijinta ta ce " Ok duk kwana ɗaya zai tashi a dubu dari sai kuyi lissafi"

Ta karashe maganar tana dauke kanta daga kanshi ta cigaba da kallonta.

"Baki da hankali ne?! Ya fadi yana ma ta wani kallo"

Ba tare da ta kalleshi bata ce " Cash zaka bani ba transfer ba idan kana bukatar ƙarin kwana sai na sani"

"Wai ke meyasa kin fiya dabbacin ne? Ya faɗa ransa a ɓace. Itama ranta a ɓace ta mike tana kallon sa ta ce " Dabbanci? Kaga dabba nan" ta faɗa tana nuna Sa'adah.

Cike da mamaki yaka kallonta danshi Zaran daya sani bata iya mayar masa da magana.

"Babyyyy! Ni zata kira da dabba kuma ka barta? Sa'adah ta faɗa tana hawayen gulma.

"Kinaso ya dake ni ne? Zaran ta fada tana ma ta kallon tara saura kwata.

Daga bisani ta ja tsaki ta barsu a wajen. Shehu kuwa kasa koda motsi me kyau yayi. Tabashi Sa'adah tayi ta ce " Wai me yake damunka ne?

Sai alokacin hankalinsa ya dawo jikinsa ya nufi dakin Zarah da sauri sauri. Tana ganinsa ta mike tsaye,ganin ya nufota yasa ta shiga toilet da sauri tana kokarin rufowa ya biyo ta, baya ta dinga yi ganin yadda ransa ya ɓaci. Sa'adah kuwa sai murmushi takeyi.

Fincikota yayi ya sheƙe ma ta wuya ya fara bata maruka masu zafi. Ihu ta saki ta fara kokari kwace kanta amma ta kasa duka yake yi ma ta ta ko ina. Wani azabbaben kara ta kwallah lokacin daya dake cikinta.

Kan wasu lokutan yaji abu me ɗumi na biyowa ta cinyarta, be barta haka ba sai da yaga bata motsin kirki.

Ganin zai juyo yasa Sa'adah fara kwallar karya tana ɗora hannu a kanta.

Fitowa yayi daga toilet din yana kallonta ya ce " Muje"

Girgiza kai tayi tana fadin " Bazan iya zuwa ko ina ba! Kalli fa halin da take ciki!

Ta ƙarashe maganar tana nufar inda Zaran take. Da kyar Zarah take iya yin numfashi duk Kasan banɗakin jini ya bata cikin kyankyami Sa'adah ta juyo tana kallonsa ta ce " Wata kila fa bari tayi"

Ganin irin jinin dake zuba daga jikinta yasa yaji wani iri a jikinsa. Ƙarasows yayi yana kallon su ya ce " Dauko makullin mota"

Wani bakin ciki ne ya ziyarci zuciyar Sa'adah, batayi tunanin zaiji tausayin Zaran ba.

"Kiyi sauri" Ya faɗa yana kallonta. Da sauri ta bar wajen. Jinin data gani a falo yasa ta gane ya fita da Zarah. Bayansu tabi, a jikin mota ta ganshi jikinsa duk jini, mika masa mukullin motar tayi tana fadin " Kuje ni zan kula da gidan"

"Ok, ki gyara inda na ɓata" Daga haka ya shiga mota yabarta awajen.

"Allah ya kiyaye wallahi yadda ka barshi haka zaka dawo ka sameshi".......

*JUMMA MUBARAK*

Autar Mama ce.
✨✨ *UMMIE* ✨✨

_Labari daya danganci soyayya da kuma ƙalubalan rayuwa_

*FREE BOOK*

*MALLAKAR*
*Autar Mama*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)

*Follow me on Wattpad @Autarmama56*

I just published "Chapter 13" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1178404477?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=J%2F7i6DNyMPmYmSRMKbZw8xp3DCUWZ9Un7S9Ohrn6rWZhuSYj56D5cZWLlwVqywLqia8FjoOBrmfPYNOsnYG0izxlTnb%2F9oEQgGdZo%2Bvc2cs%2FoYfJpwgDYuEWB9849oZn

*Idan zaki fara bi ki fara tun yanzu ba sai nayi nisa a dinga cewa daga page one ba, dan na wahala turawa lokacin da nake rubuta Ƙawaye*

*Comment da voting shi zai sa a dinga samun update da wuri*

*Whatsapp group pls banda maza, and idan kina group one kar ki shiga wannan duk abu daya ne*

https://chat.whatsapp.com/I1e40OT9rRwBgFU3xD0aYg

*Aslm inayiwa masoyana fatan alkairi, inamasu bibiyan littafin Momin haneef,tazomuku dasabon littafinta maisuna RA YUWAR SAFEENAT Labari maijike dad'umbun darasi yaudara cin'amana da kuma soyayya zai ilimantar daku kubiyoni acikin Labarin shi wannan littafin dakud'ine kiyi kokari kimallakeshi karkibari astaya baki labari bayida stada akan kud'i kalilan zakusamu 200 naira only kiyi magana tawannan number 07026368879*

*Ina kuma sanar daku zagwaguri zazzafan littafin mu maisuna kamar su d'aya kuyi kokari kunema akan kud'i kalilan 300 naira only👌*

*Taurari biyu kuma Matasan marubuta masu tasowa Sunzo muku da dadadan wanda zai nishad'antar daku masoya wannan Matasan marubuta ba kowa bane illa: 𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼,,𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈(𝙠𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 ) Sunzo muku da sabon novels masu suna.

*𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼* tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝘿𝘿𝘼𝙍𝘼 𝘾𝙀)

𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈( 𝙆𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝) tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝙉𝙒𝘼𝙏𝘼)
Kai dajin sunan labarin ma kasan basai an tambaya ba.

*(K'ADDARA CE)*
*Dandano! Dandano!!*

Hanan meye lefin mu dan muna cikin garin Saudiya? Muma bayin kammu bane K'ADDARA CE ta kawo mu cikin Saudiya. Hanan mai muka yiwa mutane suke jifan mu da mummunan kalma?. Cikin masifa Iman Ta zaburo bata yi magana ba ta damk'i hannun Sultana Tace" Ke Sultana muje ki nuna a hanyar shara-mansoor d'in Uban waye ya fad'i miki wannan maganar yau saina wuk'ance shi fuuu suka bar Hanan anan tasaki baki...


*K'ANWATA*

*Dandano!Dandano!!*


Mama kina ganin Abun da Salma taimin? Kin kasa mata magama. Jijjiga Mama take yi tana kuka mai tsuma rai..Mama ta d'ago jajayen idanun ta da suka ciko da kwalla Tace Rahama kiyi Hak'uri kanwar kice... Sharr! sharr!! Idanun ta suke zubar da kwalla da radadi had'e da zallar bakin ciki,take kallon sama ta daga hannayen ta sama tare da fad'in. Ya Allah ya Allah ka gana ganin Abun da K'ANWATA taimun ya Allah ka..


Ga maru buk'atar wannan novels d'in zasu iya tuntub'ar wannan numbobin. 09069080725 our +966599791573


Nomal. guda d'aya N 300 ne

guda biyu N 500 ne


Special guda d'aya N 500 ne

guda biyu N 1000 ne


Zaki iya biyan kud'in ki ta wannan hanyar. 3115484026 Ikilima Adam first bank

✌🏼Fitattu biyu masu ban mamaki🫀Hakika babban goro sai magogin ƙarfe 😍, Hakk'un wani kaya sai amale ke d'auka🐫, Fitattu biyu👯🏽‍♀sun shiirya tsaf domin nishad'antar daku 🤓 sun shirya tsaf domin fadakar daku🧠 sun shirya tsaf domin dilmiya zuciyoyin ku cikin bege da shauk'in so💋💞, wohoho tabbas ️sahun giwa👣 mai ɓadda na raƙumi 🐪,Fitattu biyu😍✌🏼 masu tafiyar k'asaita, sheƙi, da walwali hak'ik'a koda kud'in ka saida rabon ka😘🏃🏽‍♀️ Fitattun Ƙarshen shekara😍 salon su daban ne dana sauran domin natsuwa da tunani sunyi aiki pure love and romance abun dai sai wanda yakaranta😍 maza ku hanzarta neman naku karku bari abaku labari🏃🏽‍♀️

#Oum Sumayya:- *GAMIN GAMBIZA*✍🏽 Nrml 300 Vip 500
#Oum Ikram:- *SOYAYYA CE SILAH* ✍🏽 Nrml 300 Vip 500

Duka biyu 400👌🏼
Vip 700👌🏼
Via 4210014214
Eco bank and send the evidence of payment via 08139624956
Or mtn/airtel credit via 07017296839 banda vtu hoton kati kawai!


*Shafi na sha uku*

Zarah na tsakar gida tana alwala yaji an banko karamar kofar dake jikin gate ɗin gidan.

Ta tsorata sosai dan ita kadai ce a gidan, Zayd da Zainab sun tafi aiki Aunty kuma take dauko UMMIE daga makaranta.

Shehu ne tare da matarsa wadda taci ado cikin atamfa wadda akayi wa A shape ta yada wani gyale da ko Budurwar da ta san darajar kanta bazata yafashi ba ballantana ita me aure.

"Ai na faɗa maka har kiba sai tayi! Yanzu daka barta a gidansu waye zai dinga aikin gida? Kuma kana jin bayanin likita ya ce maka ciki ne dani na sati biyu ko? Dan haka bazan iya jurar aikin wannan gidan ba"


Sa'adah ta faɗa tana kallon Shehu dake kallon Zarah.

Wani murmushi Zarah tayi tana ajiye butar hannunta ta taso ta nufo inda suke ta ce " au Allah? Kice har ciki ne dake? Toh abu yayi"

Daga haka ta nufi hanayar falo. Cikin zafin rai Shehu ya janyo hannunta yana matsewa yadda zata ji zafi ya ce " Ko Zayd be isa ya kwace ki ba a wajena dole ki koma gidana"

Kokarin kwace hannunta take yi amma ta kasa hakan yasa tayi kaki ta tofa masa a fuska. Da sauri ya sake hannunta yana wani yamutsa fuska. Hankici Sa'adah ta miko masa tana faɗin " Goge kaci ubanta"

"Yaci ubana? Zarah ta faɗa tana kallonta.

Dariya Zarah ta saki har da tafa hannunta sannan ta ce " U'r not serious Mrs Shehu! Amma kafin yaci ubana ni zan fara cin naki"

Tana kokarin janyo Sa'adah Shehu ya tureta da iya karfinsa hakan yasa ta fadi a ƙasa tana riƙe ƙuju dan ta bige.

Runtsa idanuwanta tayi tana dafe ƙugunta kusan second 40 kafin ta tashi tana kalllonsa ta ce " Baka tureni a banza ba wallahi! Baka dakeni a banza ba! Baka zubar min da ciki abanza ba! Duk sakayya ta zata sameka! Domin bazan taba yafe ma ka ba"

"Karki yafe mana! Ni Baby banga abinda kake nema da matar nan ba wallahi kawai ka saketa kaina ma huta"

"Saki kuma? Shehu ya faɗa yana kallon Sa'adah.

"Eh mana idan bagaja ba ka shiga uku wallahi"

"Ok amma aikin gidan da waye zai miki?

Ya fada yana kallon ta.

" Karka damu! Zan samo yar aiki sannan zancewa Sale ya dawo gidan da zama saboda to cefene ko a BQ ne sai ya zauna"

Shuru Shehu yayi yana kallon Sa'adah.

Dogon tsaki Zarah taja tana faɗin " Idan baki sa ya sakeni ba bakya kaunar Allah wawiya kawai"

Daga haka ta shige daki ta barsu a wajen.

Har ta idar da Sallah bata ji sun shigo ba kuma bata ji fitarsu ba.

Tana cikin addu'a taga Shehu ya shigo falon yana jefe ma ta farar takarda.

Kirjinta ne ya buga lokacin da takardar ta sauka akan sallayar da tayi sallah.

Daukar takardar tayi taga me ya rubuta.

Tun kafin ta karanta ya ce " kije na sakeki saki ɗaya"

Kasa magana tayi shi kuma ko minti ɗaya be kara ba ya bar falon.

Hannunta na ɗan rawa ta dauki takardar ta karanta saki ne gashi nan, toh me na damuwa? Ba abinda take so ba kenan? Tambayi kanta tana share hawayen da suka zobo ma ta.

Jikinta duk ba dad'i a haka Aunty ta dawo ta tarar da ita.

Sai data shirya UMMIE ta tafi islamiyya sannan ta sameta a ɗaki.

Zama tayi kusa da ita akan gado tana fadin " Ko dai jikin ne Zarah?

Tashi zaune Zarah tayi tana sauke ajiyar zuciya ta ce " A'a Aunty, dazu dai Shehu yazo"

"Yazo kuma? Me yazo yi?

Aunty ta fada cike da mamaki. Karkashin filo ta ɗaga tadauko takardar sakin da Shehu ya bata ta miƙawa Aunty.

"Ya sakeki ko? Aunty ta faɗa ba tare da ta karbi takardar ba.

"Eh" Zarah ta faɗa a hankali.

"Mutuwar aure ba dadi amma ke kham sauki kika samu Zarah! Allah yasa hakan shine mafi alkhairy"

"Amin" Ta amsa a hankali.

"Ki huta ko? Aunty ta fada tana kallonta.

"Toh Aunty" Zarah ta amsa tana kwanciya.

Har dare Zarah ko fitowa falo batayi ba Zainab kawai Aunty ta fadawa zancen sakin amma banda Zayd.

Sai wajen 9pm ya dawo gida. Dakinsa ya wuce yayi wanka sannan ya fito falo. Kallon Zainab yayi dake tsefewa Ummie kai ya ce " Sai dare akeyin tsifar?

"Hmm baka san halin wannan yarinyar bane idan idanunta biyu ba'a yin tsifa kuma ba'a yin kitso shiyasa kullum kala ce a kanta gashi ita gashi ba kadan ba, sai naji dama ni ce da wannan gashin wallahi"

Zainab ta karashe maganar tana kara shafi gashin.

Tsaki yayi kadan yana kallonta ya ce " Bani abinci"

"Bari na zubo maka" Aunty ta fada tana tashi ta nufi kitchen.

"Ina Zarah? Ko har tayi bacci? Ya tambaya yana kallon Zainab.

"A'a tana ɗaki"

Be jira Aunty ta dawo ba ya nufi dakin Zarah. A zaune ya ganta tana tunani.

Gyaran murya yayi yana haɗawa da kwankwasa kofa kafin yayi sallama.

"Shigo" Ta fada a hankali.
Shigowa yayi yana kallon.

Sosai ya karanci damuwa a fuskarta.

"Me ya faru ne? Ya fada yana kallonta.

"Aunty bata fada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login