Showing 9001 words to 12000 words out of 100116 words
Na ce me wannan?!
"K...kayan abinci" Sarah ta fada tana yin ƙasa da kanta.
"Uban waye ya kawo? Ya faɗa yana kallon Zainab. "Ubanka! Zainab ta bashi amsa a zafafe.
"Ubana? Ya faɗa cike da mamakinta. "Eh na fada ubanka! Kai waye ya baka right din zagar min nawa uban? Ko uba yafi uba ne?
"Zainab" Zarah ta faɗa tana rikota. Kwace hannunta tayi daga na zarah ta ce " Ke idan kina tsoransa ni bana tsoransa wallahi! Shi har ya isa? Ko ance masa kowa irinki ne da yake baki kashi kin cinyewa?
"Waya ce ki bar wannan karuwar ta shigo min gida?
Shehu ya fada yana kallon Zarah da kanta ke ƙasa.
"Karuwa? Ni ce karuwa?
Zainab ta fada cike da jin ciwan kalmar.
"Toh mecece ke? Shekara 30 ba aure, mecece ke idan ba karuwa ba?
Cikin mamaki suka ji saukar mari tassss. Runtsa ido Zarah tayi dan ta saddakar Shehu ya mari Zainab. Amma ga mamakinta taji Zainab na faɗin " Ni ba sa'ar yin ka bace sakarai kawai! Idan kana yi wa Zarah tana kyaleka toh Ni Abu nake ba Zarah ba! Wannan marin ma kadan ka gani wallahi asararrare"
Daga haka ta yarda dauki jakarta kafin ta kalli zarah ta ce " Idan kin ga dama ki biyo ni ko kuma ki tsaya wannan jakin yana dukanki kamar yar uwarsa jaka"
Daga haka ta fice ta barsu cike da mamaki musanman man ma Shehu da yake ji kamar mafarki yake.
Zainab na fita tayi dialing din number Zayd bugu uku ya ɗauka.
"Yaya ni zan tafi gida amma if possible kazo gidan Zarah if not nasan zaku iya daukar gawarta"
Daga haka ta katse wayar.
Shehu kuwa jimamin abun na barinsa ya kalli Zarah da jajayen idanuwansa cikin tsananin ɓacin rai ya nufota tare da shaƙo wuyanta. Ransa na tafarfasa ya ce "How dear you!
Sosai ya shaketa idanunta suka firfito waje saboda azaba.
Sakinta yayi ganin zata daina numfashi. Tari ta fara sosai tana riƙe da wuyanta. Belt din jikin wando sa ya ciro ya saita kan belt din ya fara lafta ma ta tako ina, ihu take tana kokarin guduwa amma be saurara ma ta ba.
Yarda belt din yayi ya nufota ya fara cire ma ta kayan jikinta daga ita sai skirt underwear da vest ya barta. Da sauri ta tashi zata gudu dan tasan dukan yanzu sai yafi na da. Amma ya riƙo ya fara bata maruka da duka ta ko ina. Yana janta a tiles ya dauko belt dinsa ya fara dukanta ba ji ba gani tun tana ihu har ta daina kuma hakan baisa ya daina ba.
Sai da karfinsa ya kare kafin ya barta a wajen ya nufi ɗaki. Be daɗe da shiga dakin ba Zayd ya shigo cikin falon a 360 dan sun kara yin waya da Zainab ta sanar masa da abinda ya faru.
Ganin Zarah a kwance hancinta a fashe haka ma jikinta da fuskarta. Da sauri ya nufeta yana dago da ita ya fara jijjiga amma ko motsi bata yi.
Ransa yayi matukar ɓaci ganin shatin duka da maruka akan fair skin ɗinta.
Shehu ne ya fito daga daki yana goge kanshi da towel. Zayd na jin karar buda kofa ya juya da sauri idanunsa sunyi ja sosai jijiyoyin kansa sun tashi ruɗu².
A matuƙar fusace ya nufo Shehu yana nade hannun rigarsa. Kafin Shehu ya ankara yaji sakar wani lafiyayyan naushin a gefen fuskarsa wanda ya janyo zubar jini ta bakinsa.
Zage karfi Zayd yayi ya fara bashi naushi irin na mazane, ransa a matukar ɓace.
"Idan kana so ka gane kai namiji ne meyasa bazaka gwada kwanji dani ba sai ita only 26yrs macen da take kamar lagwani!"
Zayd ya karashe maganar yana turashi ya faɗi. A galabaice Shehu ya ce " Sai na dau mataki"
Cikin takaici ya bar inda yake ya nufo wajen Zarah ya daukota ko motsi bata yi.
Fita yayi da ita daga falon. A back seat ya ajiyeta yana fadin " Ina UMMIE? Bata ganinsa sosai kuma bakinta yayi mata nauyi bazata iya magana ba.
Rufe motar yayi ya dawo cikin gidan ya fara kiran Ummi da ƙarfi.
Tana bacci taji kamar ana kiranta. A hankali ta tashi daga gado, sosai taki zazzabin ya saketa fitowa tayi daga dakin tana kallon Zayd dake kalle² a falon.
"Gani" Ta faɗa cikin siririyar murya. Juyowa yayi yana kallonta be kara ko second biyu ba ya nufotayana daukarta kafin ya kalli Shehu dake zaune har yanzu ya ce " Sakarai"
Daga haka ya fice da UMMIE.
Asibiti ya wuce, karbar Zarah akayi da kyar dan cewa akayi zai yakawo police saboda wannan abuse ne yasha rokonsu kafin su karbeta da niyyar zaije ya dauko police.
"Uncle Zayd me ya sami Ummana? UMMIE ta faɗa tana kalllonsa.
"That idiot father's if yours..... Sai kuma yayi shiru yana huci.
Shuru Ummie tayi tana kwanciya jikinsa dan she's totally weak.
Rungumeta yayi sosai yana me fatan Allah ya bawa Zarah lafiya yasan ba karamin duka Shehu yayi ma ta ba.
Kira ne ya shigo wayarsa, da sauri ya ɗauka ganin Aunty ce. Jin Muryar Zainab ya sakashi fadin "Kinga abinda kikayi causing ko? Me kike tunanin kin aikata ne Zainab?
Cike da mamaki ta ce x Me nayi kuma?
"Au tambayata kike me kikayi? Waya aikeki ki mareshi? Kinga dukan huce takaicin da yayi wa marainiyar Allah? Zanzo gidan yanzu na sameki"
Daga haka ya katse wayar ransa duk abace.
Sake kira akayi, still dai number mahaifiyarsu ce. Dauka yayi har ya fara bala'i sai kuma ya ji Aunty ta ce " kuna ina ne?
Iska ya furzar kafin ya ce " Muna asibitin kusa da gidan su ba nisa sosai Zainab ta san wajen"
"Toh gamu nan"
Daga haka ta katse wayar.
Be mayar da wayar aljihu ba wani kiran ya shigo, ganin SIR YUSUF ya sashi yin tsaki kadan ya ɗauka yana fadin " Hello sir"
"Zayd kana ina ne?
"Asibiti"
Ya bashi amsa a takaice.
"Waye ba lafiya?Yanzu nakira Kabir yake fadawa min ka bar Company"
Yusuf ya kara faɗa daga dayan bangaren.
"Hakane, Zarah na kawo asibiti"
Zayd ya faɗa a ɗan kufule.
"Meyasameta?
"Bata da lafiya sosai Sir"
"Ayyah ok text me the address zanzo insha Allah, Allah ya bata lafiya"
Cewar Yusuf muryarsa cikin ƴar damuwa.
"Amin" Zayd ya amsa yana katse wayar cike da jin haushin Sir dan yatsani wannan so much concern din da yake nunawa Zarah.
Be yi masa texting din address din ba ya mayar da wayarsa aljihu.
Yana cikin tunani yaji Muryar Zainab tana faɗin "Ina Zaran?
Da sauri ya kalleta sai kuma ya cire UMMIE daga jikinsa yana mikewa tsaye ya ce " Me yake damunki? Kinsan abinda kika aikata me ya janyo?
"Kaga yanzu ba lokacin wannan bane, ina ita Zaran? Aunty ta fada tana shiga tsakaninsu.
"Basu fito da ita ba"
Ya faɗa yana komawa ya zauna.
Ajiyar zuciya Zainab ta sauke tana zama a ɗan nesa dashi ta kalli UMMIE ta ce " Zo nan"
Ba musu ta iso inda take ta zauna a kujera, Zainab kuma ta janyota jikinta tana shafa kanta a hankali.
A tsakiyarsu Aunty ta zauna cike da jimamin lamarin ta ce " Nasan ba karamin duka yayi ma ta ba ko?
"Kedai bari Aunty! Ai bazata koma gidansa ba" Zayd ya faɗa cike da bacin rai.
"Gaskiya kham ko ni bazan goyi bayan ta koma ba abun nashi yayi yawa"
Cewar Aunty tana jinjina lamarin.
"Zainab ko gida zaki koma saboda jikin UMMIE?
Tashi Zainab tayi tana fadin " Toh dan kuwa zazzabin yana son dawo ma ta"
Sallama tayi musu sannan suka bar asibitin ita da UMMIE.
Kiran wayane ya kuma shigo masa, ganin sunan Sir Yusuf yasa shi mayar da wayar aljihu. Sau biyu tayi ringing be dauka ba.
Daga lokacin kuma ba'a sake kira ba. Kashe wayarsa yayi gaba ɗaya cike da takaici.
Suna zaune aka fito da zara dake bacci duk anyi treating din wounds dinta amma fuskata duk ta canza ta kumbura sosai.
Nurse ce ta kalleshi ta ce " Kai ne mijinta?
Da sauri ya ce " Eh"
"Ok ga doctor chan ka bi shi zai maka baya.. be jira ta gama maganar ba yabi bayan doctor din data nuna masa, ita kuma Aunty ta bi bayan su zuwa dakin da aka kai Zahra san hutu.
Ko zama beyi ba ya ce " Doctor me ya take yanzu?
Zama likitan yayi yana kallon Zayd daga sama har ƙasa kafin ya ce " Ashe kana son matarka haka ka bari akayi ma ta wannan dukan ko na ce kayi ma ta wannan dukan"
Runtsa idanunsa yayi ya zauna a kujera yana kallon likitan ya ce " Ban daketa ba, kawai ka fada min ya take?
"Ok" Likitan ya faɗa yana daga kafada alamar shikenan.
"Tana da ciki na wata uku zuwa hudu kasan da hakan? "Ciki? Zayd ya faɗa cike da mamaki.
"Eh ciki, kuma daf yake da zubewa idan baka kula da ita ba dan banyi tunanin ma zai zauna ba amma Kasan ba yadda Allah baya ikonsa, tana matukar bukatar bed rest na tsahon watanni biyar saboda gujewa hadarin abinda zai iya faruwa, zuwa yanzu dai babu wani internal injury iya ciwukan dake jikinta ne kuma zasuyi healing soon insha Allah, bari na rubuta ma ka maganunguna da allura sai ka siyo tana room 4 sai ka kai akwai nurse da zatayi ma ta, sai a kula da bata maganunguna yadda ya kamata, kuma ta dinga yawan cin fruits sosai da abinci masu kara lafiya ta dinga mixing su carbohydrates protein, vitamin dS saboda zai taimaka ma ta insha Allah"
Ajiyar zuciya ya sauke me karfi sannan ya ce " Ok doctor mungode"
Likitan bai ce komai ba ya cigaba da rubuce² sa, sai da ya gama sannan ya bawa Zayd paper shi kuma ya karba ya sake masa godiya ya fice"
Dan dole ya kunna wayarsa saboda transfer din kudi a pharmacy Dan bashi da cash isassu a hannu.
Sai daya je POS din dake cikin asibitin ya ciro kudi sannan ya siyo kayan marmari ya dawo cikin asibitin.
Room 4 ya nema, be sha wahala ba kasancewar ko wani daki an rubuta a jiki.
Yana shiga wayarsa tayi ƙara alamar shigowar text.
Ajiye kayan hannunsa yayi yana ciro wayarsa ya duba. Credit alert na 50k ya gani daga Yusuf.
Mayar da wayarsa yayi aljihu dan yasan zai ce ya biya responsibilities na asibitin dashi. Ko zama beyi ba kiran sa ya shigo, dauka yayi yana faɗin " Hello"
Daga dayan bangaren Yusuf ya ce " Zayd! Tun dazu nake kiranka meyasa ka kashe wayar?
"Ba charji sir ban dade da sakawa ba sai na kunna, but am so sorry sir"
"Bakomai ya jikin na ta?
Sai daya ɗan kalleta sannan ya ce " Da sauki yanzu bacci take"
"Ok, duk abinda kuke bukata kuyi min magana kaji ko? Sannan kayi min text din address na asibitin zamu zo ko zuwa bayan isha'i ne"
"Ok sir mungode" Ya faɗa yana katse wayar. ..
Zama yayi yana kallon Aunty ya ce " Lokacin sallah yayi bari na tafi masallaci"
"Toh Zayd Allah yayi muku albarka"
"Amin" Ya amsa yana tashi ya fita dan zuwa ya gabatar da sallar Magariba.
Sai da yayi wa Yusuf transfer din 50k dinsa sannan ya wuce masallaci dan yana da enough money din da zai dauki responsibilities din yar uwarsa mesaya kuma zai karbi kudin wani?
Da wannan tunanin ya isar da alwala sannan ya shiga Masallaci.
Sai da aka idar da sallah kafin yayi masa test din address din.
Waya ya tarar da Aunty tana yi da alama da Zainab suke yin waya jin yadda yake jiyo Muryar Ummie tana rigima ita Ummanta take son gani.
Kallon Aunty yayi bayan ya zauna ya ce ' Bani nayi wa UMMIE magana"
Miƙa masa wayar tayi shi kuma ya karba yana karawa a kunne.
"Ummie! Ya kira sunanta, cikin rigima ta ce " Uncle Zayd ni dai ka kaini wajen umma na"
"Gobe Aunty ki zata kawoki kinji amma idan kikayi rigima babu inda zaki"
"Toh na Dena" Ta fada cikin Muryar yarinta. "Good girl" Ya faɗa yana ɗan sakin fuskarsa.
Kashe wayar yayi yana ajiyeta a kusa dashi. Zarah ya zubawa idanu cike da tausayinta.
★★★★★
Cikin kufta ya shirya wadda akayi wa dinkin zamani sosai yayi kyau. Yana gyara hular kansa ya sakko hannunsa riƙe da mukullin mota sai wani khamshi yake.
Mama dake kallo a falo ta kalleshi ta ce " Yusuf ina zuwa?
Kafin Yusuf yayi magana Farooq dake sakkowa daga stairs cikin 3qtr da t-shirt ya ce "Asibiti zamuje"
"Asibiti kuma? Waye ba lafiya? Mama ta fada tana kallonsu.
"Zarah" Cewar Farooq yana yin gaba ya bar Yusuf a tsaye.
Be jira cewar Mama baya fice daga dakin. Tasowa Mama tayi tana kallon Yusuf ta ce " Zarah kuma?
"Eh Mama, zamuje dubata ne, ko ba komai yarinyar tana da kirki duk da cewa aikin 3yrs mukayi da ita kafin mijinta yahanata but har yanzu muna dan gaisawa"
"Gaisawa? Wai me yake damunku ne kai da Kaninka?
Hannunta ya riƙe ya ce " Mama not now please sai mun dawo"
Daga haka ya saki hannunta ya fita ya barta cike da jin haushin Zarah ganin ta mallake ma ta zuciyar yara musanman ma dai Farooq da yake sonta kamar zeyi hauka, ta samu da kyar ya dawo dai² shine Yusuf yake kuma kokarin kulla wata alaƙa da ita?
Kwafa tayi ta koma kujerar ta zauna ranta duk a ɓace.....
Autar Mama ce.
✨✨ *UMMIE* ✨✨
_Labari daya danganci soyayya da kuma ƙalubalan rayuwa_
*FREE BOOK*
*MALLAKAR*
*Autar Mama*
*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)
*Follow me on Wattpad @Autarmama56*
I just published "Chapter 6" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1171239230?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=4Y2gQG0j84rehZe0yQn4KxIg78D3ngmIhYq24zcNRKOKXwtocd5hCuRlkyL0kgQJAHwrhIILXMvByIdlDHcgw7DahgIvfa2Z%2F4SVGo%2BVI82gmUGNQSfrPkTmbF6q8pX8
*Idan zaki fara bi ki fara tun yanzu ba sai nayi nisa a dinga cewa daga page one ba, dan na wahala turawa lokacin da nake rubuta Ƙawaye*
*Comment da voting shi zai sa a dinga samun update da wuri*
*Whatsapp group pls banda maza, and idan kina group one kar ki shiga wannan duk abu daya ne*
https://chat.whatsapp.com/I1e40OT9rRwBgFU3xD0aYg
✌🏼Fitattu biyu masu ban mamaki🫀Hakika babban goro sai magogin ƙarfe 😍, Hakk'un wani kaya sai amale ke d'auka🐫, Fitattu biyu👯🏽♀sun shiirya tsaf domin nishad'antar daku 🤓 sun shirya tsaf domin fadakar daku🧠 sun shirya tsaf domin dilmiya zuciyoyin ku cikin bege da shauk'in so💋💞, wohoho tabbas ️sahun giwa👣 mai ɓadda na raƙumi 🐪,Fitattu biyu😍✌🏼 masu tafiyar k'asaita, sheƙi, da walwali hak'ik'a koda kud'in ka saida rabon ka😘🏃🏽♀️ Fitattun Ƙarshen shekara😍 salon su daban ne dana sauran domin natsuwa da tunani sunyi aiki pure love and romance abun dai sai wanda yakaranta😍 maza ku hanzarta neman naku karku bari abaku labari🏃🏽♀️
#Oum Sumayya:- *GAMIN GAMBIZA*✍🏽 Nrml 300 Vip 500
#Oum Ikram:- *SOYAYYA CE SILAH* ✍🏽 Nrml 300 Vip 500
Duka biyu 400👌🏼
Vip 700👌🏼
Via 4210014214
Eco bank and send the evidence of payment via 08139624956
Or mtn/airtel credit via 07017296839 banda vtu hoton kati kawai!
*Aslm inayiwa masoyana fatan alkairi, inamasu bibiyan littafin Momin haneef,tazomuku dasabon littafinta maisuna RA YUWAR SAFEENAT Labari maijike dad'umbun darasi yaudara cin'amana da kuma soyayya zai ilimantar daku kubiyoni acikin Labarin shi wannan littafin dakud'ine kiyi kokari kimallakeshi karkibari astaya baki labari bayida stada akan kud'i kalilan zakusamu 200 naira only*
*Ina kuma sanar daku zagwaguri zazzafan littafin mu maisuna kamar su d'aya kuyi kokari kunema akan kud'i kalilan 300 naira only👌*
*Shafi na shida*
" Farooq wai me kake yi a ɗaki ne?
Karamin tsaki ya saki yana kallon Yusuf ya ce " Hutawa nake sonyi"
"Ok but abinci fa? Ko na kawo maka nan? Room slippers dinsa ya cire yana kwanciya a kan gado tare da jan duvet ya rufe jikinsa.
A kusa dashi Yusuf ya zauna yana taɓa kansa ya ce " Me yake damunka?
Lumshe idanunsa yayi yana furzar da iska kadan ya ce " Bakomai"
"Nothing? Kana tunanin zan karbi nothing a matsayin amsa?
Yusuf ya faɗa yana kalllonsa. Tashi zaune yayi yana riƙo hannun Yusuf ya ce " Dawowata Nigeria yasa komai ya dawo min sabo! Bana tunanin zan iya cigaba da zama Yusuf! Banaso ya kasance ina tunanin abinda bai dace ba"
Dafa kafadarsa yayi cikin son kwantar masa da hankali ya ce " Dama shi haka so yake, yana shiga faradɗaya amma yana daukar shekaru kafin ya fita gaba ɗaya wani lokacin ma baya fita gaba dayan sai dai ya ragu, inaso ka cire komai a ranka ka manta da dasuwar soyayyarta a zuciyarka lokuta da dama muna son abinda bazai zama alkhary a gare mu ba, ka cigaba da addu'a perfect match Dinka tana nan zuwa insha Allah"
Ture hannun Yusuf yayi daga kafadarsa yana faɗin " Bazan iya ba!
Daga haka ya tashi ya saka slippers dinsa ya bar ɗakin.
Ƙasa ya sakko ransa duk babu dad'i. Mama data fito daga kitchen yanzu hannunta riƙe da tray din abinci.
Karasowa tayi inda yake yake tana ajiye empty tray din a gefensa ta ce " Me ya faru naga kamar ranka a ɓace?
"Bakomai" Ya faɗa kamar anyi masa dole.
"Saboda Zarah ne, bansan menene matsalarsa ba matar nan tana da aure 8yrs da aurenta amma ya kasa cireta a ransa"
Yusuf ya faɗa yana karasa sakkowa daga stairs ɗin.
"Ai kuwa ko da ace yau mijinta mutuwa yayi bazan taba bari ya auri widow ba gwanda ma ka cire rai da ita! Nan da wata biyu ma zamuyi maka aure!
"What? Ya faɗa cike da mamaki.
"Sosai ma kuwa Farooq! Kuma *_UMMIE_* zaka aura ƴar Aunty ƙarama"
Da sauri ya tashi tsaye yana kallon Mama ya ce " _*UMMIE?*_ "Tabbas, da so nake ka huta sai muyi magana amma tunda ka zabi na faɗa ma ka yanzu gashi na faɗa ma ka kuma ka shirya gobe kaje wajenta"
"Mama UMMIE fa kika ce? That 18yrs old child?
"She's not longer a child Farooq! Kuma ko 10yrs gareta ba 18yrs ba wallahi sai ka aureta kaji m na rantse tunda baka da kirki"
Mama ta fada ranta a ɓace. " Calm down Mama, abun bai kai haka ba ai basai kin bata ranki ba"
Tashi