Showing 54001 words to 57000 words out of 100116 words

Chapter 19 - UMMIE Hausa Novels PDF By Autar mama.txt

10 Nov 2025

3464

ya cika da yacewa Mama zasu dawo gashi daga Zayd har Farooq baby wanda ya tashi.

"Yawwa Yusuf kayi ma ta magana kullum bata cin wani abin kirki yanzu na taki ci"

Kafin yayi magana wayarsa ta fara ruri.

Dauka yayi zuciyarsa na bugawa ganin sunan Mama. "Muna shirye² na dawowa zan kiraki" Ya fada yana katse wayar dan bai san me zaice ba kuma.

"Amma Farooq b'oyewa mahaifiyarku ba dabara bace! Addu'arta ma wani abu ne sosai. Ina ganin ka fad'a ma ta gaskiya"

Cewar matar ACP tana kallonsa.

Shafa kansa yayi sannan ya ce "Hakane inaso na karbi discharge papers ma Kano nake so mu koma gobe ko jibi"

"Toh Allah ya dashi kafad'unsu" Da Amin ya amsa yana zama kusa da Zarah ya ce " Dan Allah Zarah kici abincin nan, Aunty tana asibiti ita kad'ai kinga said kinci abinci zaki samu energy din zama tare da ita" Hawayen da suka zubo ma ta ta goge tana tashi tsaye ta wuce d'aki ba tare da tace musu komai ba.

"Allah sarki, tausayi take bani, tayi kokari ma da bata suma ba irin wannan abu da kidarmarwa yake ga aurensu sabo ko sati beyi ba wannan abun ya faru"

Matar ACP ta fad'a cike da jimami. "Hakane, Allah ya basu lafiya"

Da Amin ta amsa sannan ta d'auki abincin ta nufi kitchen dashi.

Da yammacin ranar Yusuf ya nemi sallama dan yana so su koma Kano daga nan yana so ayi shirye² na fita dasu zuwa k'asar India domin kula da lafiyarsu.

Shi da ACP sun gama shirya komai zuwa gobe zasu koma Kano tare da marasa lafiyan.

Kashe wayarsa yayi gaba daga saboda jar Mama ta kirashi dan bashi da amsar da zai ba ta.

Washe_gari tun karfe 8 na safe suka shirya babu wanda Zarah takeyi wa magana har Aunty.

Bayan sun dawo kano Yusuf ya rasa courage din da zai kai Farooq gida. Zayd kuwa asbiti aka wuce dashi, Kabir ne ya kai Yusuf gida.

Mama, Ramlah, Ummie da kuma Sabir duk suna compound din gidan sabida ya sanar dasu dawowarsa.

Gadon da suka karbo daga asbitin Kabir ya fito dashi ya hada sannan suka fito da Farooq aka d'orashi a kai.

Da sauri Mama ta nufo wajen tana kallon Farooq kafin ta kalli Yusuf daya sunkuyar da kansa k'asa.

" Me haka? Mama ta fada tana bude zanin da aka rufe farooq zuwa kirji ga oxygen a hancinsa.

"Ina Farooq? Ta sake tambayarsa tana kallonsa.

"Mama na kawo shi ki ganshi yana bukatar a maidashi asibiti kafin a gama shirye² na fitar dashi zuwa k'asar waje"

Ummie kuwa kuka ta saki tana komawa cikin falo da gudu.

Mama kuwa hawaye ta fara tana kallon Farooq. Layin Ambulance Yusuf ya kira basu dad'e ba suka iso aka saka Farooq zuwa asibiti.

Sosai Mama ta shiga damuwa matuka, hankalinta yayi matukar tashi sosai amma ta fawalla wa Rabbi komai.

Yusuf be zauna ba ya tafi booking flight dinsu dan yana so visa ya fito da wuri.


Mama da Ummie ne suja tafi asibiti aka bar Ramlah a gidan.

Tun da suka iso asibitin take tare dashi hannunsa cikin nata sai kuka takeyi tana jin nauyin da zuciyarta tayi ma ta yana raguwa sosai.

Nurse ce ta shigo da kayan dressing, kallon Zarah tayi ta ce " Ya me jiki?

"Da sauki" Ta amsa tana goge fuskarta. Aikinta tayi Zarah na zaune har ta gama tayi masa allura sannan ta fita. Bata dad'e da fita ba Aunty ta shigo. Ajiye kayan hannunta tayi ta ce " Zainab tace zasu zo anjima dazu da je gida na kirata ashe sun kwana biyu da dawowa kano tace tana kirana baya zuwa"

Da toh kawai Zarah ta amsa dan bata son yawan magana.

"Zarah! Aunty ta kira sunanta tana dafata.

"Kiyi hakuri kinji shi dama bawa Allah yana jabartasa da abubuwa sosai duk son da kike yi wa Zayd be kai wanda nake yi masa ba, amma bansawa kaina wannan damuwar ba kinga yadda kika lalace kuwa? Ba hawaye ko damuwarki yake bukata ba adduarki kawai yake bukata Dan Allah ki daina wannan damuwar"

Share hawayenta tayi ta ce " Insha Allah"

"Yawwa ga abinci nan nayi miki kici kinji? "Toh" Zarah ta amsa tana kallon Zayd.



Sa'adah ce zaune ta mik'e kafafu duk a bushe baby rike a hannunta gefe kuma wata dattijuwa ce tana had'a ruwan wankan baby a robar wanka.

Ummie ce ta fito daga kitchen hannunta rike da plate na farfesun nama, a kusa da Sa'adah ta ajiye ta ce " Aunty gashi"

Karbar plate din Sa'adah tayi tana fadin " Inna kinsa yaji sosai kuwa a farfesun nan?

"Ban cika ba saboda kar ya dameki" Dattijuwar ta bata amsa tana d'aukar babyn dake jikin Sa'adah.

Tub'eta tayi ta saka a ruwan ta fara yi ma ta wanka.

"Aunty zan tati makaranta"
Cewar Ummie tana kallon Sa'adah.

"Uwar makaranta zakije shegia me kama da mayu, zan aika Sale ya ce musu bazaki zo ba, jibi kya je tunda gobe suna"

"Toh" Ummie ta amsa tana nufar hanyar d'akinta.

"Zonan" Sa'adah ta kirta.

Dawowa tayi tana kallonta ta ce " Gani"

"Jeki zubo naman kuma karkisa romo"

Washe baki Ummie tayi ta nufi kitchen tana jin dadi.

Murmushi Inna tayi ta ce " Ko kefa! Amma kiyita gallazawa yarinya bayan tana miki biyyyah"

Shuru Sa'adah tayi bata ce komai ba, Ummie kuwa na zubo namanta ta fita compound din gidan inda zata ga Sale.

Aikuwa yana zaune yana busa sigari. Tsaki tayi kadan kafin ta ce " kace Aunty bazata bani nama ba gashi ta bani, kuma va kya shaye²"

Daga haka ta juya masa baya ta koma cikin gida. Tsaki yayi ya cigaba da zukar sigarinsa hankalin kwance.

B'angaren su Yusuf kuwa baby wani cigaba akan marasa lafiyar dan baby wani ya farka kuma yana yiwa zasu iya kai watanni ko shekara ma a wannan yanayin.

Kwanaki na ta shudewa haka ma sattika watan su biyu da dawowa daga Abuja komai ya kammala na fita kasar India, har wanda zasu samu Yusuf ya gama komai.

Da Zarah zasu tafi banda Aunty, sai Ummie dashi Yusuf d'in, duk da Mama taso zuwa amma Yusuf ya hanata dan yasan damuwa kawai zata kara sawa ranta.

Gobe ne tafiyar tasu, Ummie bata san da wasu zasu tafi ba dan sam Yusuf babu wanda ya fad'awa maganar Zayd.

Karfe bakwai saura na dare Yusuf ya shi go d'akin da aka kwantar da Zayd. Zainab ce kawai a d'aki hannunta cikin na yayanta.

Amsa sallamar sa tayi tana fad'in" Barka da zuwa"

"Yawwa, Ya me jiki? "Da sauki" Ta amsa tana kallon Zayd.

"Ina Zarah? Ya fad'a yana kallon d'akin.

" Sun tafi gida ita da Aunty amma anjima kadan zasu dawo"

"OK, ga passport dinta dana Zayd tomorrow by 7pm insha Allah"

Karba tayi tana fad'in " Ok"

Zama yayi kusa da Zayd yana kallon fuskarsa, lumshe idanunsa yayi kad'an a ransa ya ce " Allah ya baka lafiya Zayd Allah ya tashi kafad'unka"

Riko hannunsa na hagu yayi ya shafa a hankali zuciyarsa duk ba dadi, ji yake dama shi harbin nan ya samu ba poor innocent Zayd ba mutumin kirki, for more than 10yrs Zayd yana masa aiki be taba neman ko biyar ya rasa ba,millions of cash zasuyi shigo account din Zayd amma ko biyar be taba ragewa ba haka zaije ya ciro kudi ko kuma ya kawo masa, mutane irin Zayd kad'anne a wannan duniyar shiyasa ma be taba tunkarar Zarah da maganar ko zata aureshi ba saboda shi shaida ne irin soyayyar da Zayd yake ma ta.

Ji yayi kamar Zayd d'in ya matse masa hannu. Da sauri ya bude idanunsa yana kallon Zayd din. Amma ko motsi bayayi.

Kallon inda Zainab take zaune yayi yaga babu ita.

Ajiyar zuciya ya sauke tana kokarin raba hannunsa dana Zayd amma yaji Zayd din ya rike gam.

Da sauri ya kalleshi amma ko motsi bayayi.

"Doctor! Doctor! Ya fara kira da karfi. Zainab ce ta shigo dakin dan dama tana waje suna,waya da hubby dinta.

"Menene? Ta fada tana kallonsa.
"Zayd ya rike hannuna yaki saki"

Da sauri ta gyara hijabin jikinta tana duba shi.

Oxygen ta zare masa aikuwa numfashinsa steady. Hawaye ne ya fara biyo kuncinta sai kuma ta kalli Yusuf ta ce " Kira likita"

Kafin ya fita likitan ya shigo yana fadin " Naji kira kamar me'

"Dubashi" Cewar Yusuf yana kokarin raba hannunsa dana Zayd amma Zayd din ya rike hannun sosai.

Matsawa Zainab tayi likitan ya fara dubashi duk wata na'ura sai da ya cire masa, kallon Zainab yayi ya ce " Ina uniform d'inki?

"Ni patient relative ce"
Ta bashi amsa tana kallonsa.

Ajiyar zuciya yayi ya ce " Komai ya dawo dai² amma meyasa be farka ba.

"Ya farka Doctor kawai dai be bude ido bane kasan is hard after all what happened"

Cewar Zainab tana murmushi.
."OK zuwa nan da 10mins ku kirani"

Daga haka ya fita.
"Zayd please open your eyes" Cewar Yusuf yana shafa hannunsa.

Zarah da Aunty ne suka shigo dakin ganin su cirko² a kan Zayd gashi taga an cire nasa oxygen ya sa ta nufosu da sauri tana fad'in me ya sameshi?

Kula ta saki Dan ta d'auka ya mutu.

Jijjigashi ta fara you zuciyarta na wani irin tsinkewa. Ji tayi yasa hannu biyi yayi hugging dinta.

Wani dum zuciyarta ta ba ta. "Z...zarah" Taji ya fada da wata iriyar muryar kamar ba tashi ba. Da sauri ta d'ago tana kallonsa. Haryanzu idanunsa a rufe.

"Ya ta shi! Ta fada tana kallon sauran al'umar dake d'akin.

Murmushi Yusuf yayi wanda ya manta rabon da yayi irinsa Godiya kawai yake ga Allah, haka ma Aunty da Zainab dake hawayenta farinciki.

"Ka judge idanunka" Zarah ta fada tana shafa fuskarsa hawayenta na d'ogowa a kirjinsa.

Sosai yaji idanuwansa sunyi masa nauyi ga wani zafi da sukeyi amma a haka yake kokarin budesu. Wani irin haske ne ya ziyarci idanunsa sam baya ganin mutane, rufewa yayi da sauri yana jin kansa na ciwo.

"Sorry Zayd ka bude su a haka zuwa 20seconds ne zaka koma gani normal"

Cewar Zainab tana karasowa inda yake.

Sake budewa yayi aikuwa within 1mins ma koma ganin mutane normal, wani bala'in yunwa ne ya ziyarce sa.

"Zan wanke baki, yunwa nake ji" Ya fada yana kokatin tashi zaune amma yaji kafafunsa kamar ba'a jikinsa suke ba ya kasa motsa su.

Cike da tausayinsa ya ce " Zayd ka huta tukunna bari Zarah ta kawo robber da ruwa sai kayi brush din anan"

"Amma meyasa na kasa motsa kafufuna" Ya fada yana kara kokartawa amma ya kasa dan baya jinsu na kwata².

Rugumeshi Zarah tayi tana fashewa da kuka sosai jikinsa ne yayi sanyi dan action din Zarah ya tabbatar masa da bazai sake tafiya ba maybe kuma an yake masa kafa ne"


Jikinsa ne yayi sanyi yana jin zuciyarsa ta karaya. Shima rungumeta yayi yana lumshe idanunsa zuciyarsa cike da rauni........

*Sorry for the typing errors*

Autar Mama ce.
✨✨ *UMMIE* ✨✨

_Labari daya danganci soyayya da kuma ƙalubalan rayuwa_

*FREE BOOK*

*MALLAKAR*
*Autar Mama*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)

*Follow me on Wattpad @Autarmama56*

I just published "Chapter 24" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1189669360?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=emxMgYaXkJf0XdiYSa7ZZ%2F8p5UnKhicP0erjHcPyN3xMVjGHjh0dV%2F7I%2BQBC%2B0UqQXbXIf0n21tvHE%2FJibQPydnbX9PjuOa8uJKZQ6OvHlvpAGW%2Fs947yfdYVdS1A756

*Please subscribe, and like my YouTube channel*

https://youtu.be/9m2j2vaiKjw

Aslm ma abota biyan littafin Momin Haneef ce tana sanar daku littafin ta na ak'idar masarautar.

littafin nakud'ine idan kina buk'ata zaki iya fara biya tunkafin free page yak'are gamai son littafin ak'idar masarautar zai turo da kud'insa ta wannan account👇

Nusaiba Rabi'u Union Bank 0087778987

Idan kuma katine zaku turo katin MTN ta wannan number👇
07026368879

Bamuson vtu bazamu kar b'aba

Idan kinturo kud'in zaki turo mana da shaidan kin biya ta wannan number07026368879

Normal group 300 only
Zakuna samun page d'aya (1 )arana

Special group 400👇
Zakuna samun page biyu (2) arana duk Wanda kikaga yamiki sai kishi ga.

*Taurari biyu kuma Matasan marubuta masu tasowa Sunzo muku da dadadan wanda zai nishad'antar daku masoya wannan Matasan marubuta ba kowa bane illa: 𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼,,𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈(𝙠𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 ) Sunzo muku da sabon novels masu suna.

*𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼* tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝘿𝘿𝘼𝙍𝘼 𝘾𝙀)

𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈( 𝙆𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝) tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝙉𝙒𝘼𝙏𝘼)
Kai dajin sunan labarin ma kasan basai an tambaya ba.

*(K'ADDARA CE)*
*Dandano! Dandano!!*

Hanan meye lefin mu dan muna cikin garin Saudiya? Muma bayin kammu bane K'ADDARA CE ta kawo mu cikin Saudiya. Hanan mai muka yiwa mutane suke jifan mu da mummunan kalma?. Cikin masifa Iman Ta zaburo bata yi magana ba ta damk'i hannun Sultana Tace" Ke Sultana muje ki nuna a hanyar shara-mansoor d'in Uban waye ya fad'i miki wannan maganar yau saina wuk'ance shi fuuu suka bar Hanan anan tasaki baki...


*K'ANWATA*

*Dandano!Dandano!!*


Mama kina ganin Abun da Salma taimin? Kin kasa mata magama. Jijjiga Mama take yi tana kuka mai tsuma rai..Mama ta d'ago jajayen idanun ta da suka ciko da kwalla Tace Rahama kiyi Hak'uri kanwar kice... Sharr! sharr!! Idanun ta suke zubar da kwalla da radadi had'e da zallar bakin ciki,take kallon sama ta daga hannayen ta sama tare da fad'in. Ya Allah ya Allah ka gana ganin Abun da K'ANWATA taimun ya Allah ka..


Ga maru buk'atar wannan novels d'in zasu iya tuntub'ar wannan numbobin. 09069080725 our +966599791573


Nomal. guda d'aya N 300 ne

guda biyu N 500 ne


Special guda d'aya N 500 ne

guda biyu N 1000 ne


Zaki iya biyan kud'in ki ta wannan hanyar. 3115484026 Ikilima Adam first bank

✌🏼Fitattu biyu masu ban mamaki🫀Hakika babban goro sai magogin ƙarfe 😍, Hakk'un wani kaya sai amale ke d'auka🐫, Fitattu biyu👯🏽‍♀sun shiirya tsaf domin nishad'antar daku 🤓 sun shirya tsaf domin fadakar daku🧠 sun shirya tsaf domin dilmiya zuciyoyin ku cikin bege da shauk'in so💋💞, wohoho tabbas ️sahun giwa👣 mai ɓadda na raƙumi 🐪,Fitattu biyu😍✌🏼 masu tafiyar k'asaita, sheƙi, da walwali hak'ik'a koda kud'in ka saida rabon ka😘🏃🏽‍♀️ Fitattun Ƙarshen shekara😍 salon su daban ne dana sauran domin natsuwa da tunani sunyi aiki pure love and romance abun dai sai wanda yakaranta😍 maza ku hanzarta neman naku karku bari abaku labari🏃🏽‍♀️

#Oum Sumayya:- *GAMIN GAMBIZA*✍🏽 Nrml 300 Vip 500
#Oum Ikram:- *SOYAYYA CE SILAH* ✍🏽 Nrml 300 Vip 500

Duka biyu 400👌🏼
Vip 700👌🏼
Via 4210014214
Eco bank and send the evidence of payment via 08139624956
Or mtn/airtel credit via 07017296839 banda vtu hoton kati kawai!


*Shafi na Ashirin da hud'u*

Yammacin ranar alhamis Zarah na zaune a falo tana karatun wani English novel irin na dabbobin daji taji knocking daga change gate d'in waje. Hijabi ta saka sannan ta fito tana fad'in "waye?

"Ummana ni ce" Taji muryar Ummie. Baki ta wangale tana saurin bud'e k'ofar. Ummie ce tsaye tare da Shehu yasha ado cikin shadda me kyau dama shi d'in me kyau ne.

"Barka da yamma" Zarah ta fad'a tana kallonsa. Mirmushi yayi kad'an kafin idanunsa su sauka akn cikin dake jikinta. Wani irin kakkauran yawu ya had'iye ransa duk ya dagule murmushinsa ya koma ciki.

"G..ga Ummi nan zuwa sunday sai nazo na d'auketa an basu hutun ismaliyya kuma kinsan suna hutan k'arshen term na shiga Jss 1"

Mirmushin Zarah ne ya fad'ada tana rike hannun Ummie ta ce " 'yan matana an girma"

Dariya Ummie tayi tana matsowa jikin Zarah.

Kallonta ta mayar ga Shehu ta ce " Nagode"

Daga haka ta ja hannun Ummie suka shiga cikin gidan.

Runtsa idonsa yayi lokacin da Zarah ta rufe kofar dake jikin gate din.

'Gaskiya yayi wauta da abinda ya dinga yi wa Zarah! Me ya hau kansa ne? Yarinya kamar Zarah har ya dinga wulakantawa? Kodai rabon wannan cikin ne ya saka ya saketa? Karamin tsaki yayi yana fad'in " Wannan Sa'adah ce useless human being" Ya fada ransa a b'ace.

"Anyway Bayan bari ko mai ya sub'uce min ba"

Juyowar da zaiyi yaga ana fito da Zayd daga cikin mota an d'orashi a kan wheelchair machine d'insa.

"Nagode Sir, Allah ya saka maka da alkhairy" Yaji Zayd din ya fad'a yana kallon Yusuf.

Murmuahi Yusuf yayi masa yana fad'in " Soon zan samo maka driver da me gadi dan bude maka gate da kuma fito dakai ina me kara baka hakuri nayi sanadiyyar rashin tafiyarka ni da d'an uwana nayi sanadiyyar kashewar rabin jikinka"

Yusuf ya k'arashe maganar yana sa tissue a idanunsa. Rike shi Zqyd yayi yana d'an murmushi ya ce " Hakan rubutacciyar k'addara ta ce Sir karka wani damu nagode sosai"

Wheelchair machine din ya danna ya fara tafiya dashi zuwa kofar gidansa sai a lokacin yaga Shehu, had'e rai Zayd yayi Yusuf kuwa yana baya yana kallonsu. Da kallo kawai Shehu ke binsa, murmushi yayi sosai dan ya san abinyi dole ko Zayd bayaso ya saki Zarah shi kuma ya nayar da ita.

Fito yayi kad'an sannan ya bar kofar gidan ba tare da yace masa komai ba.

Knocking yayi ba'a dade ba Zarah da Ummie suka bude masa kofa.

Murmushi kawai tayi wa Yusuf sannan ta rufe gidan.

"Uncle Zayd meyasameka a kafa? Ummie ta fad'a tana kallonsa.

"Ciwo naji amma soon insha Allah zan warke"

"Allah ya warkar da kai ka cigaba da tafiya uncle Zayd" Ummie ta fada tana shiga falo.

Zarah na kokarin shiga d'aki wayarta ta fara ringing, Ummie ce ta mik'o ma ta wayar shi kuma Zayd ya nufi cikin d'akin.

Private number ta gani, dauka tayi tana yin sallama.

"Ashe abinda ya faru kenan Zarah! Allah yasa ba ya gurgunce kenan ba! Tun yaushe hakan ya faru?

Taji muryar shehu, cikin takaici ta ce " Baa dade ba sai anjima" Daga haka ta katse, shi kuwa ya samu abinda yake so ko ana ha maza ha mata sai ya dawo da Zarah cikin gidansa ya bata kulawa da soyayyar da ta rasa a wajensa.

Tana shiga d'aki taga Zayd yana danna wayarsa fuskarsa a hade.

Zagayowa tayi ta bayansa tana saka hannu cikin rigar da ya cire mab'allanta ta shafa kirjinsa a hankali ta ce " Menene?

Lunshe ido yayi kad'an kafin ya furzar da iska me d'umi ya ce " Idan ze kawo Ummie ya kirani zanje na d'auketa bana so ya k'ara zuwarmin gida"

A kafad'arsa ta dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login