Showing 90001 words to 93000 words out of 100116 words

Chapter 31 - UMMIE Hausa Novels PDF By Autar mama.txt

10 Nov 2025

3445

tace yunwa take ji, yanzu ma haka daga restaurant muke shine ta dage sai tazo tasha ice cream"

Gyada kai Farooq yayi yana dauke idanunsa daga kanta ya ce " Ok ku gaida gida nima Nawal ce ta fito dani! Bata so ubanta ba saini marainin wayonta"

Dariya Taj yayi yana sauke Nawal a k'asa ya ce " Ai tafi sabawa da kai shiyasa... Juyawa yayi ya kalleta ya ce " Ummie ki zo ku gaisa da abokin Daddy sai mu tafi"

Karasowa tayi a hankali ta ce "Abokin Daddy ina yini?

Murmushi Farooq yayi ya ce "Lafiya lau 'yar Zarah!

D'agowa tayi ta kalleshi sai kuma ta kalli Taj ta ce " Mu tafi kar ice cream din ya narke"

"Toh" Cewar Taj yana kallonta.

Sallama yayi masa sannan suka tafi yabi bayansu da kallo yana murmushi.


Sai da suka dauki hanyar komawa gida sannan ta kalli Taj ta ce " ai na dauka yar sa ce"

Girgiza kai Taj yayi ya ce " Ai sir Farooq be taba yin aure ba!

Zaro ido Ummie tayi ta ce " Haba? Ai ya kusa sa'an Uncle Zayd ko ma ya girmeshi"

"Bansan shekarun uncle Zayd ba but shi 38yrs yake, tun be kai haka ba yake son wata sanadiyyar soyayyarta wata mace yasashi haka! A shekarun baya ma kusan tabin hankaline ya sameshi amma abun beyi tsanani ba Allah ya bashi lafiya! sanadiyyar da suka hadu da Daddy na kenan saboda shi likitan kwakwalwane"

"Ikon Allah! Wannan soyayya haka? Amma matar balarabiya ce?

Cewar Ummie cike da mamakin lamarin"

"Bansani ba, amma tabbas yana sonta kuma soyayyarta ne ya hanashi aure har yanzu! A baya ma fa ya taba aure amma ranar daurin auren ya gudu ya bar amaryar"

Dariya Ummie ta saki tana fad'in " Ya gudu ya barta? Tabdijan toh ya akayi?

"Sakinta yayi bayan wajen shekara da auren"

"Ikon Allah, toh Allah ya kyauta! Ya bashi macen data dace dashi kuma ta gari"

Da amin Taj ya amsa yana kara maida hankali kan tukinsa.

Washe_ gari.

Biki ya tafi yadda ya kamata sosai abun ya k'ayatar ranar Ummie ko kwalliyar ma batayi ba saboda lokaci ya kire me make up din bata zo da wuri ba.

Sai bayan isha'i suka dawo gida, ita da Raham ne kawai a dakinsu sauran yan uwa kowanne yana dakin da aka saukesu.

Wanka Ummie ta shiga bata dade ba ta fito tana goge kanta da towel. Rahama dake kwance a kan gado ta ce " Ummie kinsan me?

"Inaji" Cewar Ummie tana zama bakin mudubi.

Ta shi zaune Rahama tayi tana kallonta ta cikin mudubi kafin ta ce " Ke wai baki lura da komai a yanayin Taj ba?

Juyowa Ummie tayi tana kallonta kafin ta ce " Me ya faru dashi?

Karamin tsaki Rahama tayi ta ce " Wallahi Ummie bakya kwashewa! Duk wannan abubuwan da Taj yake miki kin dauka abotace kawai? Abubuwan sunyi yawa! Nifa nasan sonki yake kuma nasan kema kina sonsa!

Wata dariya Ummie ta saki harda tafa hannuwa. "Tab wallahi ki sake tunani bari ma yanzu idan nayi sallah zanje wajensa nasan yana chan yana karatu kuma zan fada miki yadda mukayi bana sosna baya sona kawai abotace ba irin taki ba"

Shuru Rahama tayi tana kwabe baki maybe ko tayi misunderstanding dinsu ne.

Ummie na idar da sallah kamar yadda ta fada haka ta wuce ta nufi wajen Taj.

Bata ganshi inda tayi tunani ba. Dawowa cikin gidan tayi ta nufi dakinsa. Sau biyu tayi knocking taji ya ce " Waye?

"Taj ni ce ka fito muyi magana"

Bata dade a tsaye ba ya fito yana sanye da single da short nikka, kallonsa tayi ta ce " Me haka?

"Kwanciya zanyi shiyasa, amma ina jinki"

"OK ka saka ko jallabiya ce ka fito! Da toh ya amsa sannan ya koma daki, be wani dade ba ya fito sanye da jallabiya.

Compound din gidan ta nufa tana fad'in " Inaso nayi clearing wani doubt ne"

"OK menene? Ya fada idanusa a kanta.

Shuru tayi itama tana kallonsa azahiri shi take kallo but a bad'ini tunani take yi akan maganar Rahama tasan dai Rahama akwai sa ido da bin kwakkwafi amma ita bata ga wani abu na nuna soyayya a tattare da Taj ba! Beside ma ita a matsayin Yaya aboki ta daukeshi! Infact ma bata son auren yaro tafi son auren babba kamar 30-35yrs haka wanda zai iya yin hakuri da ita dan tasan shes so annoying, duk tasan Taj ma yana da hakuri da kawaici amma ita sam bata ma wannan tunanin a kansa, "Toh ita tana da zabi ne ma? Tana da right din zabarwa kanta miji? Ya kamata ta daina daukar kanta da wani mahimmaci! Yes tasan tana da kyau but menene amfanin kyan nata? Bayan ita din ma yanzu ba cikakkiyar budurwa bace!

Runtsa idanunta tayi tana tuno lokacin da abun ya faru! Hawaye ne suka fara bin kuncinta. "Ummie! Taji Taj ya kira sunanta.

Bud'e idanunta tayi tana saurin goge hawayenta ta ce " Shikenan kawai kaje ka kwanta!

Kallonta yayi ya ce " Ummie wani abu ne?

Kai ta girgiza alamar a'a.

Shigowar motar Daddynsa ce yasa ya kalleta ya ce " Ki tafi ciki sai d safe"

Kallon motar tayi a sanyaye sannan ta wuce ta koma ciki"

Bayan ya gama parking ya fito yana karasowa inda Taj yake yana kallonsa ya ce " Taj! Inyi irinta Ummie.

Murmushi Taj yayi yana kallosa ya ce " Sannu da zuwa Daddy"

"Yawwa! Ya gama fuskarsa wani iri? "Bakomai Daddy!

"OK me kuke cewa da Ummie? Sosa kansa yayi kafin ya ce " Maganar karatune"

Shuru Daddyn yayi yana kallonsa kusan na minti daya kafin ya ce " Ina fatan dai bayan friendship babu wata alaka ko? Kasan dai ba aure zan maka yanzu ba!

Shuru Taj yayi dan baisan me zai ce ba!

"Yawwa muje ciki ko? Da toh Taj ya amsa yana bin bayansa suka shiga gidan.

Ummie kuwa bandaki ta shiga tasha kukanta dan tasan rayuwarta ta lalace! Saleh ya cuceta wallahi!

Har sai da Rahama tayi bacci sannan ta fito.

Washe-gari.

Tun karfe 8am aka fara makeup saboda 11:30 ne daurin auren.

Cikin lace fari kal Rahama ta shirya wanda akayi wa dinkin riga da skirt dan yayi kamar dai gowm amma riga da skirt ne sai farin net me kyau da tsada wanda a kayi pinning dinshi da jikin dan kwalinta ya zauna yayi dam tayi kyau abun ba'a cewa komai.

Sai kusan 11 aka fara yi wa Ummie duk fuskarta baby annuri saboda har yanzu bata bar ahiyar zuciyar kukan da tayi ba.

Cikin atamfa ta shirya dinkin doguwar riga wanda yayi mugun yi ma ta kyau kuma kalar atamfar ta dau fatarta. Suna zaune da kawayen amarya yan bokonsu wayar Rahama ta fara kara.

Gamin sunan mijinta yasa kawayen shewa ana kiyi sauri ki dauka. Daukar wayar tayi ta saka a handsfree ta ce " Hello!

"Sweet mie an daura!

Ihu suka kasa ana fadin Awwwwwwn. Dariya Rahama tayi tana katse wayar.

Kallon Umkie tayi da duk wannan abun ba da ita akeyi ba.

"Ummie lafiya? Murmushi Ummie ta kakalo tana kallonta ce " Bakomai kawai ciwan kai ne"

"Ayya sannu bari na karbo miki magani"

Cewar Rahama tana tashi.

Auntyn Rahama ce ta shigo dakin tana fad'in " Ku fito sun shigo za'ayi hotuna"

Da toh suka amsa duk suka fice har da Rahama Ummie ce kawai bata bi su ba.

Eye lashes din idanunta ta cire jin hawaye na biyo kuncinta. Sosai tasha kuka dan tana fatan itama tayi aure kamar Rahama kamar ma duk wanda yayi amma ita ko yancin zabar mijin ma bata dashi sabida ko anyi auren ma zai gane after that kuma yayi ma ta wulakanci! Ta yanke shawarar ko ma waye yazo neman aurenta zata fada masa gaskita idan ze aureta ya aureta idan baxai aureta ba shikenan.

*Ni kuwa nace kina da damar zabar wanda kike so Abinda Allah ya rufe shi ai dan adam be usa ya tona ba! Sau da dama ana samu masu cewa wai dan irin haka ta faru da mutun sai duk wanda yazo neman aure ki wage baki kice ke ba budurwa bace! Fir what reason? Idai fyade ne mutun yana karami is not that worst da saki ta shi hankakinki musanman idan kinsamu kulawa lokacin da abun ya faru! Though dai ba abune me dadi amma ba hk yake nuna cewa idan kin boyewa wanda zaki aura kin ci amanarsa ba matukar kika,samu kulawa dinki da abubuwan da zaki gyara kanki toh be zama lallai shi wanda kika aura ya gane ba! Tabbas akwai mazan da suke da karancin ilimi ta fannin wajen! Sai suce lallai sai sunga jini a daren farkon da suka sadu da matarsu! Wannan kuma ba haka yake ba! wani yana ne dake ke kasan mace bawai ina nufin yana fa ta gizogizo ba😂😂 abune kamar tissue kuma bawai ya rufe gaban mace babu kofa a'a! Akwai kofa shi kuma yana daga kasan inda kofa take a turance ana kiransa da Hymen!*

*Toh na wasu matan yakan kasance me kauri sosai, irin wannan matan sune nasu be fiya yagewa ba har aure toh idan anyi sex dasu tabbas za'a jini saboda za'a fara fasa wannan fatar that's why jinin yake fitowa! Sai kuma akwai wanda bashi da kauri sosai sai kuma wanda nasu yake lange² toh masu lange² yana da saurin yagewa! Ta hanyar hawan hawa mashin! Keke! Tsalle! Gudu! Daukar abu ne nauyi d.s, duk yana iya yagewa ta wannan bangaren! So idan ya yage idan aka sadu da mace baza'a ga jini ba sai ya kasance namiji idan bashi da ilimi akan abun ya fara zargin mace da taba saduwa da wani! Wanda sam ba haka be! Maza da yawa sun sa a ransu sai sunga jini a first sex da mace sannan ta zama cikakkiyar budurwa! Kuma b hk bane! Ina fatan bayanina zai wanke wa wasu wannan stupidity din🥴*

Rahama ce ta shigo dakin tana fad'in " Wai kanne ya saki kuka haka? Kin bata kwalliyar fa!

Wani kukan Ummie ta kuma fashewa dashi tana tashi ta fito daga dakin ko dankwali babu a kanta dan ta cire.

Bayanta Rahama ta bi dan da baki a gidan su Ango da abokan Daddy da Daddy duk suna compound ana hotuna itama zuwa tayi kiranta ayi da ita.

Tana fitowa falo Hajiya ta riketa tana fad'in "Me ya faru Ummie?

A jikin Hajiya ta kwanta tana fashewa da kuka sosai zuciyarta nayi ma ta zafi da kuna.

"Har an fara kukan rabuwar kenan? Cewar Hajiya tana shafa bayanta.

Taj ne ya shigo falon yana kallonsu kafin ya ce " Ku fito ayi hotuna Daddy yana magana"

Itama Rahama kukan ta saka tana isowa inda Ummie take! Ummie kuwa tasan kukan me takeyi amma babu wanda zata iya fadawa.

"Oh yau and bani! Cewar kakarsu Taj.

"Kunga Dan Allah Ku daina wannan kukan! Aunty dauko hoda a gyara musu fuskar" Hajita ta fada tana dagowa da fuskokinsu.

Ta Rahama bata baci ba amma ta Ummie tabaci sosai.

"Wannan fuskar Ummie sai dai wankewa" Hajiya ta fada tana kallonta. Aunty ce ta gyarawa Rahama fuskarta sannan ta fita dan har Daddy ya leko.

Ummie kuwa upstairs suka nufa tare da Hajita ta tayata wanke fuskarta sannan ta yafa ma ya mayafi ko dankwalin ba'a daura ba ta ce " Maza jeki kar ayi hotuna babu ke!

Da toh ta amsa sannan ta sakko. Taj na tsaye yana jiranta tun dazu. Karasowa tayi inda yake takalleshi da jajayen idanunta ta ce " Muje!

Bata hanya yayi ta wuce sannan shima ya bi bayanta.

Dagowarda zatayi taga Farooq, da wani me kama da Farooq sai saurayin rannan da daddare kayansu iri daya! Saurayin kham yana da kyau farin daya cika ne yasa taji bema yi ma ta wani kyau ba! Ni kuwa karfin hali... Lol

Be ganta ba hakan yasa ta sauke idanunta daga kansa.

Karasawa tayi kusa da Daddy, "Ai baku rabu da tukunna! Wannan kuka haka Faty?

Kasa tayi da kanta tana danyin murmushi. Sai a lokacin Farooq ya ganta, kwantaccen gashin goshinta da dogon hancinta yake hangowa dan ta sunkiyar da kanta.

Yusuf ya Tab'a yana fad'in "Ummie! 'yar Zarah!

Direction din wajen Yusuf ya kalla, cike da mamaki ya ce " Haka yarinyar nan ta girma? Just 2-3yrs rabon dana ganta fa!

"Nima nayi mamaki but ni anyi 6yrs rabon dana ganta! Har tafi na Zarah kyau yarinyar kamar wata yar larabawa!

Dariya Yusuf yayi ya ce " Ai kasan babanta mahaifiyarsa balarabiya ce mahaifinsa ne bahaushe kuma Zarah bafulatana!

"Hakane, Masha Allah!
"Zanje nayi wa Zayd magana ina yi wa Sabir kamu kafin ta kara girma shima ya kara ko nan da 2yrs new sai ayi auren! Ko ta yaya dai mun hada jini da Zarah! Ita din abun so a hada jini ne da ita tana da kirki sosai ga hankali da addni"

"Uhm" Cewar Farooq still idanunsa a kanta.

"Yawwa Faty mujea daukemu da abokaina sai ki gaidasu ko? Cewar Daddy yana kallonta. Hannun Rahama taja suka nufin ida su Farooq suke.

Dagowa tayi suka hada ido da Farooq! Kasa daukewa tayi daga kallonsa haka shima. "Farooq, Yusuf ga Ummie babbar kawar Tajudden da Rahama"

A hankali ta ce " Ina yininku? "Lafiya lau! Ummie ya Zarah?

Dagowa tayi tana kallonsa ta ce " Meyasa kowa yace ya Zarah? Ummana dai"

"Exactly yadda take fad'a tun tana karama.

"Shiririta ai su ba Ummansu bace" Daddy ya fada yana dariyar wautarta. Wayarta ce ta fara ruri, tana dubawa taga sunan Ummana❤️

Dauka tayi da sauri dan tun jiya basuyi waya ba.

"Mamana kina lafiya ko?
Murmushi Ummie tayi ta ce "Eh ina kwana? Ya Ucle Zayd, Khaleel da kuma Zaki?

Daga daya bangaren Zarah ta ce "Bana hanaki cewa zakin nan ba"

Dariya Ummie rayi wanda ya bayyana hakwaranta sannan ta ce " Shikenan, yanzu hotuna ake zan kiraki anjima"

"Toh ko gaida amarya anjima zamu shigo Uncle dinki baya jin dadi shiyasa bezo daurin auren ba"

"Me ya same shi? Ummie ta fara tana zaro ido. "Ciwan baya ne amma da sauki"

A sanyaye Ummie ta ce " Allah ya yaye masa wannan ciwan bayan"

Da Amin sika amsa, Rahama da Daddy ma sunbar wajen saboda hotunan da ake tayi su Hajiya da Aunty duk sun fito.

"Wai tayaya kuka san Ummana? Ta fada tana kallon Farooq da Yusuf!

"Ta yadda muka sanki" cewar Yusuf yana kallonta.

Kafin tayi magana Rahama ta kirata su kuma su Farooq sukayi sallama da Daddy sannan suka tafi.....

*Autar Mama ce*
[3/16, 4:47 PM] Brother❤: ✨✨ *UMMIE* ✨✨

*Mallakar*

*AUTAR MAMA*

*Wattpad @Autarmama56*

I just published "Chapter 40" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1203067518?utm_source=android&utm_medium=com.fmwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=HQbCASDyy970vPuKZhVLZgKhhto%2BL3mvqQgwKFB%2FI%2BOUEfX1i9bivcimP20L%2B9%2Bemde%2F5VXoYNu0hpWdhldWmom7gZSIAeYI32Bba78jTjrWGlZfhUWrdCyATaXcKdX2

*Exquisite writer's forum*

*Shafi na arba'in*

Shuru Taj yayi ya zuba ma ta idawansa masu ban sha'awa amma banda wajen UMMIE.

"Ka Daina kallona! Ni Ina ganin idan ya kirani zan ce masa toh na yarda! Banga amfanin zaman ba! Auren shine mutuncina"

"Yayi Miki kenan?
Taj ya fada still idanuwansa a kanta.

" Ni zan aureshi ne kawai! Ai bani da zabi! Indai yayi wa Ummana da kuma Uncle Zayd shikenan"

Shuru Taj yayi ya kasa cewa komai.

Dukansa tayi kadan da handout din da ke hannunta.

Numfashi ya sauke yana fad'in "Mu koma class ko kina da inda zakije ne?

Tashi tsaye tayi tana kallon agogon wayarta ta ce " Saura away d'aya fa mu koma! Mu d'an zagaya for 30mins ragowar 30mins din sai muyi karatu!

"Me zamuyi idan mun koma?

Sai data jiya idanunta kadan kafin ta ce " Electricity!

"Zan wuce gida kawai kiyi min attendance!

Cike da mamaki take kallonsa dan tasan baya missing din class kowa ma ya sani but meyasa zai tafi yanzu?

Kusa dashi ta dawo tana kallon sa ta ce "Taj?

Gyara wuyan rigarsa yayi yana kallonta ba tare da ya amsa ba.

"Meyafaru? Ta fada a sanyaye.

"Nothing kawai dai zan koma ne ki zauna zanzo daukarki anjima"

Be jira cewarta ba ya tafi ya barta a wajen.

Da kyar ta iya kaiwa 4pm amakarantar.

Ta jirashi na kusan 30mins amma bezo ba, wayarsa bata shiga. Fitowa tayi baking gate din makarantar. Da kyar ta samu napep zuwa qtrs dinsu.

A kofar gidansu taga Farooq a tsaye jikin mota.

Karasawa tayi tana kallonsa cike da mamaki.

Murmushi yayi lokacin daya ganta. "Ina yini? Ta fada tana kallonsa.

"Lafiya Lau 'yan mata! Yanzu na aika a kiraki ashe ma kina makaranta"

Kafin tayi magana me gadi ya fito ya na fad'in " Bata dawo ba!

"Baba gani nan! Cewar Ummie tana masa murmushi.

"Toh toh sannu ya makarantar? "Lafiya Lau Baba" Ta fada tana Kara fada² murmushin ta. Komawa cikin me gadin yayi.

Dubanta ta mayar ga Farooq da ya kafeta da idanunsa.

"Nifa ko Taj baya min wannan kallon ka bari!

Ta fada a dan shagwabe.
"Taj? Waye kuma haka?

"Friend! Ta bashi amsa a takaice.

"Friend?! Ya maimaita Kalmar. Basarwa yayi ya ce " Dama zuwa nayi na ganki! And ga wannan Mama ta ce a baki"

Ya fada yana bude front seat ya fito da bag me kyau maidai²ciya.

Kara tayi ta ce "Wacece Mama?

Sai da yayi murmushi kafin ya ce "My mom!

Zaro idanu tayi kadan tana fad'in "Har ka fada ma ta me?

"Har na fada ma ta na samu matar aure mana!

"Hmm, wasa kake yi nasani ai"

"Allah! Ke kawai nake jira! Inhar na miki kin amince yanzu za'ayi insha Allah ni ba bakon Zayd da Zarah bane sun sanni na sansu tun kafin a haifeki!

Turo Baki tayi chan kasan zuciyarta ta ce 'Eh naji!

"Magana kikayi?

Da sauri ta girgiza kanta ta ce " A'a!

"Ok, ki shiga gida kar na tsayar dake kin dawo agajiye!

"Toh nagode Farooq? Ko?

"Yes! Zaki iya kirana da haka! Murmushi tayi ta ce " Zan kiraka da Omar!

"Wow! Ya fada yana kallonta.

"Nagode ka cewa Mama nagode kabani number dinta zan kirata na ma ta godiya"

Jinjina kai yayi lallai UMMIE ita ba ruwanta ko kunyar sirikar nan ma babu? But is better ai.

"Zan turo miki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login