Showing 3001 words to 6000 words out of 126726 words

Chapter 2 - ABU ZAID HAUSA NOVELS COMPLETE BY SASAAL.doc

26 Feb 2026

2687

Aunty ta faWa tana kallonta da farin cikin ganin sauyin da Hudayya ta samu.
"Sannu da zuwa,banji shigowar ku ba Aunty" ta faWa da sanyi murya.

"Karki kisa damuwa a ranki Huda,baki da matsala da komai yanzu kinji" Aunty ta faWa ta na dafata haWe da murmushinta.

Nodding kanta tayi ?walla na taruwa a cikin idanuwanta.

"Ina Aunty Zainab da Babynta"
"Zainab ta koma can ?asar da take aure,amma Huda maiyasa kika yiwa Abu Zaid ?arya da Gwarzo bayan ke kanki ba taSa zuwa kikayi da wayonki ba?"Aunty ta tambayeta tana tsareta da kallo.

Kuka ta fashe da shi"Aunty idan nace daga Abuja na ke bazai yarda da ni ba,kuma nazo Zaria ne tunda naji Mama( Ramatu) tace anan gidanki yake,kuma nasan bazaki hanani abinci ba,kuma bazaki na dukana kamar Mama ba".?arfin kukanta ne ya ?aru tana share hawayenta da bayan hannunta.

"Kiyi shiru Hudayya komai yanzu ai ya wuce, munyi magana da Abu Zaid yace zai Wauki nauyin karatunki kinji In Sha Allah kukan ki ya?are. Bari naje gurin su Alhaji,ki daina kuka kinji". Aunty ta faWa haWe da mi?ewa.

Bayanta Hudayya ta bi da wani irin kallon ta ?asan idanuwanta tana taune lips Winta.

Siyayyan kaya designer ma su kyau da tsada Abu Zaid yabawa Aunty tayiwa Hudayya,da duk wani abun bu?atar ?a mace. Wannan dalilin ya?ara haSSaka abinda Hudayya takeji a zuciyarta,a ganinta idan har bayajin wani abu a kanta bazai taSa Sata waWannan manyan kuWaWen wajen yimata siyayya mai yawa haka ba.

Hudayya ta zuba idanuwan shigowar Abu Zaid sashen Aunty har na tsahon kwanaki biyu amma shiru, kuma bata da zarrar yin Breakfast,lunch, Dinner tare da su, sai dai kullum tayi na ta a Waki ita kaWai.

Sai Hudayya ta koma le?en window duk lokacin da ta tashi da ga barci ko Allah zai sa ta hangoshi,amma ba ta taSa samun ganinshi ba. Sai wata rana da damuwa ya hanata runtsawa ta dinga le?a window duk bayan wa su mintuna. ?arfe bakwai da rabi Allah ya bata sa'ar ganinshi, Cikin ?ananun kayan da suka amshi fatarshi da ginannan jikinshi ya yi adonshi mai birgewa, gibgegen Saint Laurent jacket ne asaman ?ananun kayan jikinshi,saboda sanyin safiyar ranar dayafi na kullum, Window ta zuge gaba Waya tana ?aremai kallo da iya ganinta amma har lokacin bataga wani abu Waya na su daya dace da juna ba, amma ita dukka ba wannan ne matsalarta ba,ko shi ya kawo iya ado kuma yafi kowa kyau da kuWi sai ta cika muraWinta a kanshi wannan al?awari ne tayiwa kanta. A kan idanuwanta Abu Zaid ya bar gidan gaba Waya tanajin kamar ta ?walamai kira. To maiyasa tun ranar daya kawota gidan su bai ?ara neman ganin ko da fuskarta ba? Ta tambayi kanta bayan ta zube a kan gado ta na dafe haSarta. KafaWunta ta Waga alamun ko a jikinta.

Daga wannan ranar sai Hudayya ta mayar da tashin ta a irin wannan lokacin kamar ibada har Alarm ta sa,sau biyu Aunty na kamata amma batasan mai take kallo ba. Har shuWewar sati Waya.

Wata ranar Friday wanda yayi dai-dai da sauran kwana biyu a resuming school Win da Abu Zaid ya Wauki nauyin biya mata,ta kasa jurewa da sanWa ta sauko down stairs,ta fita daga sashen gaba Waya duk da tsoron da ke mamaye a cikin zuciyarta.

Ma'aikatan gidan ne ke ta aikace-aikacen su babu wanda yabi takanta.

Turare mai daWin ?amshi daya sauya iskar wajen ne yaketa busowa, kamar kullum da ?ananun kayan da sukafi yimishi kyau yayi ado. Dasauri ta?arasa kusa da shi tana gaishe shi. Bai ganeta ba don haka ya amsa mata kamar yanda yake amsawa kowa. "Yaaya nice Hudayya" ta faWa tana binshi a baya. A tunaninta zai tsaya ko ya nuna wani alamu na farin cikin ganinta,amma sai taga saSanin haka. Maimakon ya bawa ganin na ta muhimmanci sai ya Sige da amsa kiran dake shigowa wayanshi.
Har ya shiga Mota yabar harabar gidan bai katse kiran ba,sai waving hannu da yayi mata lokacin daya rufe murfin motar.

Wani abu ta haWiye mai tsananin Waci a wuyarta,tana shanye ?wallar dake shirin taruwa a cikin idanuwanta.

Aunty dake kallon komai ta Wakin Hudayya idanuwanta ta runtse,tsoron abinda Hudayya ke neman bijirowa da shi na shigarta. Fitowa ?aramin living room Winta ta yi tanajiran shigowarta.

Kamar yanda ta fita da sanWa haka ta koma,amma wannan karon sai ta tarar da Aunty tsaye kan ?afafuwanta ranta a Sace.

"Maiyasa kike bibiyan Abu Zaid duk safiya Hudayya,banaso na?ara gani kina jina?" Kai Hudayya ta Waga mata ba?in cikinta na nunkuwa.

Daga haka ta juya tabar Hudayya da bin bayanta da Kallo.

Jajayen iduwanta ta rintse tana kama kanta da dukka hannayenta. Da jan ?afa ta nufi Wakinta. A wannan ranar Hudayya batayi ko da Breakfast ba,duk Aunty na sane da ita amma bata kulata ba sai da dare yayi.

Takai minti biyar tana kallon Hudayya da ke barcin ?arya.
"Banason ki bani kunya Hudayya, idan zuciyarki na kitsa miki don wata manufa Abu Zaid ya taimakeki to ki cirewa zuciyarki wannan tunanin don haka halinshi yake ga duk wani mai neman taimako. Hudayya bakida banbanci da duk wani ma'aikacin da kika gani a cikin gidan nan,don a kan haka Abu Zaid ya taimakeki kamar yanda kika ro?a, wani dalili zai sa ki hana cikinki abinci ko kinason yin kokawa da abinda yafi ?arfinki ne Hudayya? Abu Zaid bazai taSa amsarki amatsayin da kikeson zuwar mishi ba,saboda ke kanki idan kikaga Matar da take amatsayin mallakinshi zaki gasgata zancena, kuma har abada Alhaji bazai sauya ra'ayinshi a kanki ba".

A zabure Hudayya ta mi?e tana dafe kanta da ke sara ma ta. Kafin ta fara magana a hankali
"Aunty ba fa abinda kike tunanin ba ne,kawai inason mu ?ara gaisawa ne, abinci kuma na?i ci ne saboda ciwon kan dake damuwa" Hudayya ta faWa da danne duk wani gobarar da ke cin zuciyarta.

Zama Aunty ta yi tana sassauta muryarta,"Hudayya ki mayar da hankali kan karatunki kinji karki Sata gobenki wajen son abinda bazaki taSa samu ba Hudayya".

Ba ta ?ara cewa Aunty komai ba har ta bar Wakin. Ta jima tana kallon waje Waya kamin ta lumshe idanuwanta ?wallar daya cika su na biyowa ?uncinta. Ta na kuma sawa ranta Wannan ne kukanta na farko kuma na ?arshe a kan abinda take ji dangane da Abu Zaid.

A jikin window ta wuni har Abu Zaid ya dawo a kan idanuwanta. Don babu nasihar Aunty Waya da ya shigeta,sai na furucin Abu Zaid yanada Mata,to idan yana da ita tana ina?maiyasa yake rayuwa a gidan iyayenshi tunda ya na da aure? WaWannan tambayoyin da ta yiwa kanta ne ya?ara mata ?arfin gwiwar kawai Aunty na son rabata ne da cikar muradinta.

Ranar Sunday daya rage saura kwana Waya a koma makaranta a bakin window ta zauna har 11am ta wuce amma Abu Zaid bai fito ba. Motar dayake ba?o a idon Hudayya ne a danno harabar gidan...
'
Sosai ta buWe dukka idanuwanta ta na jiran wanda zai fito daga ba?uwar Motar,zuciyarta na wani irin bugun daya sata mi?ewa daga kan kujeran da take zaune,har ?an?ance idanuwanta takeyi saboda tasamu ganin abinda takeso da kyau.

Matashiyace kyakkyawar gaske wanda duk da nisan tazarar da ke tsakanin idanuwan Hudayya da inda take bai hanata ganin tsananin kamanceceniyar su da Abu Zaid ba. Haka kawai taji tanason sanin wacece ita. Kwalin chips Win da take ci ta jefar a kan gado ta nufi Wakin Aunty da sassarfa,batare da tuna kashedinta a kan bibiyar rayuwar Abu Zaid ba.

Har lokacin Aunty bata farka ba,tana barcin gajiyar hidimar Breakfast Win da ya zama wajibi a kanta duk safiya, don Mijinta baya cin abincin ma su aiki sai na nata ko na SIYAA. Gashi da tsarfar son abinci kala-kala musamman na gargajiya.

Bugun Hudayya ne ya tashi Aunty da ga barcin gajiyar da bai gama sakinta ba ta buWe ma ta ?ofa. "Lafiya Hudayya?" Aunty ta tambaya tana kallon Hudayya da kamar ba a cikin nutsuwarta take ba.
Gaisheta tafarayi tana sosa ?eyarta kafin tace "dama Aunty ba?uwa na ga kunyi ne, shi ne nace na sanar dake, Aunty dama Yaaya na da ?anwa ne? na ga suna kama" ta faWa still tana sosa ?eyarta.
Numfashi Aunty ta sauke,haushin Hudayya na rashin son tsayawa a matsayinta nakamata. Sai da ta gama ?are mata kallon takaicin machaciyar zuciyarta sannan tace
"Hudayya sau nawa kikeson na jamiki kunne kan cire idanuwanki a kan al'amuran gidannan eh? Idan bazaki daina le?e-le?en nan ba gaskiya zamu masu babban matsala da ke,ta shi ki fitarmin daga Waki" Aunty ta faWa ranta a Wan Sace.
Da sanyin jiki Hudayya ta bar Wakin,maimakon ta koma Wakinta sai ta zauna a Living room Win Aunty ko Allah zai shigo da ba?uwar gaishe da Aunty daganan ita sai ta tambayeta da kanta. Don bazata iya ha?urewa zuciyarta batare da tasan wacece ita ba.

Kai tsaye Sangaren dayake mallakinta da Abu Zaid Sakuwar da Hudayya ta gani ta nufa. Doguwa ce sosai amma kallo Waya zakayimata ka hango yarintarta.

Tafi minti biyar tana knocking kafin ya buWe mata fuskarshi a Waure,saboda baya bu?atar ganin kowa. Wani irin rungumar da ke nuna tsananin ?ewarta da yayi, yayi mata yana sha?ar ?amshin turaren da suke amfani da shi tare.

Dariyar nishaWi ta sa bayan sun zube a kan kujera.

"Siyaa ?auyen Tofa duk ya mayarmin dake ?ar ?auye,duk kinyi duhu" ya faWa don ya tsokaneta.

"Yaaya=?? duhu fa kace? Ni da Kaaka tace namayi fari,to ai kaine kayi duhu ka rame" ta faWa don dagaske Win ya rame amma baiyi duhu ba.
"Na Wauka bazaki dawo ba,don naga sam bakiyi Missing Wina ba"
"Tayaya zan?i dawowa bayan komai nawa na nan"
"Kamar me da me?"Abu Zaid ya faWa ya na kallon fuskarta mai tsananin kamanceceniya da na shi fuskar.
" Kamar Aunty,Daddy da Mijina" ta faWa tana Soye fuskarta a tafukan hannayenta"
" Allah!=?3? Ashe kinyarda ni Mijinki ne bansaniba?" Abu Zaid ya faWa da sigar wasa. Dasauri ta tashi zata dugu.
"Karki gudu Siyaa, come nd make me something to eat I'm starving".ya faWa da Wan Waga murya yanda zata ji shi.

"Ba guduwa zanyi ba ai Bedroom zanje na dawo"ta faWa dai-dai lokacin da ta fita daga living room Win gaba Waya.

?ofar Wakinta dake kallon na shi ?ofar tasa key ta buWe. Komai na ?aramin Parlon pink ne hakama wadataccen Bedroom Winta shima da komai pink aka ?awa ta shi,ko ina a gyare tsaf.

Wanka tafarayi da ruwa mai zafi sosai sannan ta kimtsa cikin Varley Tracksuit mai taushi da kauri, Brown Veil ta yane kwataccen sumar kanta da shi,wanda ya?ara fito da kyawun fuskarta.

Kitchen Win dake tsakanin ?ofofin su ta shiga,a gurguje ta dafa mishi noodle da sunny side up sai coffee. Saboda ta na son shiga wajen Daddy da Aunty.

Da sallama ta murWa handle Win kafin ta fara tafiya cikin sanWa. Har lokacin yana kwance hannunshi dafe da kanshi.

"Siyaa"ya faWa da murmushi yana mi?ewa zaune. Turo siraran laSSanta ta yi alamun bataji daWi ba.

Maimakon ta kawo gefenshi kamar yanda tayi niyya sai ta wuce Dining still tana turo baki.

Tana shirin juyowa taji mutum a bayanta ihu ta saki,don taji tsoro sosai.
?aramin dariya ya saki yana shafa ?asumbarshi haWe da kashe mata ido Waya,alamun ya mata 1-0.

Tana zaune a kujeran dake opposite da na shi har ya gama ci. Yana goge bakinshi ya furta kalmar da duk duniya shine kalmar dayafi ?ona mata zuciya. "Allah Ya kawo Miji nagari ?ammata na" ya faWa yana ?o?arin jarumtar haWiye ?wallar dake ?o?arin cin galaba a kanshi.
Kamar kullum batacemai komai ba tayi hanyar fita. "Siy.." "zanje gaishe dasu Daddy ne" ta tari numfashin shi,itama tana ?o?arin haWiye nata kukan.
"Ki jirani kinji" "okay" kawai tace tana komawa da baya ta zauna kan kujera.
Yana shiga Bedroom ta fashe da kuka mai sanyi. Jin alamun fitowar shi yasa ta faWa wash room Win dake Parlon.

Bakin Alhaji ?alhatu kamar zai yage saboda dariya,duk girman Sacin ran dayake ciki idan yaga Siyama da Abu Zaid a tare sai farin ciki ya maye gurbin wannan Sacin ran. ?akyar ya bar su suka tafi gaishe da Aunty,da sunan za su dawo.

Har izuwa wannan lokacin Hudayya na kwance a living room Win Aunty kamar mai barci. Ta kuma yi sa'ar har lokacin Aunty bata fito ba.

Tana ji ana knocking ta mi?e dasauri ta nufi ?ofar wanda yayi dai-dai da fitowar Aunty cikin adonta mai birgewa.

"Wa nake gani kamar Abu Zaid da Siyama Zaid" Aunty ta faWa da sigar tsokanar da ta saba yi mu su. Dasauri Siyaa ta saki hannun Abu Zaid ta rungume Aunty da dariyarta.

Har suka zauna Aunty ba ta daina tsokanar su ba.

A iya maganganun Aunty Hudayya ta Wan Wauki hasken wacece Siyama( Siyaa).

"Aunty Ba?uwa kikayi" Siyaa ta faWa tana kallon Hudayya da murmushin ya?e ke kwance a kan fuskarta."eh sunanta Hudayya ?ar ?anwatace".
"Hudayya ga Matar Abu Zaid kuma ?anwarshi" Aunty ta faWa tana kallon Hudayya.

Kamar sukar ?arfe haka taji maganar Aunty a zuciyarta,banda zuciyarta kafaffene da babu abinda zai hanata sakin kuka mai ?arfi. ?ara gaishe da su tayi ta na mamakin Abu Zaid da har lokacin bai nuna ya santa ba. To ai dagasken bai sanki ba Hudayya tunda a ranar daya taimakeki ko cikakken kamannin ki bai sani ba ya Wamka?i a hannun Yayar Mahaifiyarki taimakone dama ya haWaku, amma lokaci bai ?uremiki ba kina da damar zana masa sunanki a cikin zuciyarshi wanda har abada bai isa ya manta ba,to taimakon da yayimin fa bai kamata na sakamai da sharri ba,to ai saiki zauna ciwon zuciya ya kashe ki. Hudayya nayin waWannan shawarwarin ne da gurSatacciyar zuciyarta mai tsananin son kanta.

Ko na sakan Waya takasa Wauke idanuwanta daga kallon Siyaa da Abu Zaid, dai-dai da yatsun ?afarsu dake kusa da na juna iri Waya ne,haka siraran laSSansu ba?i da sirkin ja iri Waya ne.

Kanta mara kikakken gashi ta shafa lokacin da ganinta yakai kan kwantaccen gashin dake gaban goshin Siyaa.

Yanayin maganar Siyaa mai haWe da murmushi da Wan zare ido yafi komai tsayawa Hudayya a rai,ga shi ta lura Siyaa macece mai?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? tsananin kunya don bata hirar minti Waya bata rufe fuskarta ba.
Gaba Waya sai zuciyar Hudayya ya fara sa?a mata yaya zata gusar da wannan murmushin na Siyaa zuwa kuka mai tsananin raWaWi da ciwo? Dole akwai hanya kuma sai ta nemoshi.

Kiraye-kirayen sallar azahar ne ya tashi su Abu Zaid zuwa sashen su.

Da wani irin kallo mai ma'anoni da dayawa Hudayya ta bi bayan su, kafin ta mi?e zuwa na ta Wakin.>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?>?x?

ABU ZAID
By Nafisat Aliyu Sasaal

Page 5

A wannan dare sam Hudayya ba ta samu nutsuwar yin barcin arzi?i ba, kyakkyawar fuskar Siyaa murmushinta kunyarta,su su?a ma?alewa idanuwa da zuciyar Hudayya, zumuWin son zuwanta Makaranta duk sai ya kau a ranta.
Kamar yanda Hudayya bata runtsa ba haka itama Siyaa,sai dai matsalarta dana Hudayya sun sha ban-ban duk da dai sunyi tarayya ne kan abu Waya.
Duk lokacin datayiwa Mijinta hidimar girki,haWa ruwan wanka da sauransu sai yayi mata addu'ar da sai ya hata barci a wannan rana. Yaushe mafarkinta zai zama gaske? Batajin akwai wani sila da zuciyarta zai zaSi rabuwa da Abu Zaid duk tsanani duk wuya.yaushe zai daina tuna mata abinda tajima da sani? Kwantacce kuma cikakken sumar kanta dake ?ushe cikin hula ta birkita,tsabar kukan da takeyi jikinta har rawa yakeyi. Kamar daga sama taji ana knocking. Dasauri ta goge fuskarta ta shiga Bathroom ta?ara wankewa da ruwa,?aramin hijjabi ta Wora akan Pyjamas Win jikinta.
Hannuwanshi ya harWe a lafiyayyen chest Win shi yana kallonta da rinannun idanuwanshi,da tsabar cigarette Win dayasha ne ya kaWasu.
"Zo" ya faWa yana mata alama da hannu. Jiki a sanyaye ta?ara matsawa kusa da shi. Har lokacin kallonta yakeyi ta cikin farin tabaran dake ma?ale a jajayen idanuwanshi cikin tsananin tausayi da sonta mara gushewa aranshi har abada.
Su na sha?ar ?amshin juna duk na shi ?amshin ya surka da warin cigarette Win da yasha.
Bayan ta zo daf da shi sai ya mayar da ita abun kallo da iya ganinshi ya na kuma tantance damuwar dake kwance kan fuskarta mai tsananin kamanceceniya da nashi fuskar kafin ya furta"yaushe zaki fahimci kalamaina har su daina damunki Siyaa? Ko da kin amince da yi min al?awari a irin wannan lokacin wata rana zaki ?alubalanceni,nasan bazaki jure ba".ya faWa ?walla na taruwa a jajayen idanuwanshi.
Kamar ba dare ba haka Siyaa ta buWe muryarta cike da raWaWin wutar dake cin zuciyarta"Yaushe zaka daina furtamin irin waWannan munanan kalaman? Ashe a kwai wani sauyi da zai sa kayi tunanin mallakawa wani namiji ni kai ka rabu dani?,yaushe zaka daina shan abinda zai ?arasa nakasa lafiyarka duk da al?awarin dainawa da kayimin?bazan gujeka ba kuma bazan sauyawa Soyayyarka ba har ?arshen numfashina, sai dai idan kaine ka sauya komai da kanka." Ta ?arasa faWa kuka mai raWaWi da ciwo na ?wace mata.
"Siyaaa"ya faWa shima yana fashewa da kukan zafin dayake ji
Maimakon ta tsaya ta saurareshi sai ta koma Waki haWe da bugo ?ofar da ?arfi ta murza key.a jikin ?ofar ta jingina ita da shi duk sunajin yanda sautin kukan kowannen su ke fita. Kafin tabar jikin ?ofar da sauri. Ya saba yi mata kuka da al?awarin ya daina shan abinda yake sha tun wa su shekaru baya,amma har yanzu bai daina ba,da wanne zasuji?
Tabbacin tabar wajen ?ofar yasa Abu Zaid komawa nashi Wakin ya na cire tabaran fuskarshi haWe da goge hawayen daya cika mai fuska. Da kuWi da Mace tagari ne kaWai farin cikin rayuwa to da yafi kowa farin ciki, amma dole sai da cikakken lafiya komai zai tabbata. Sai yaji ya matsu gari ya waye ya?ara ganin fuskarta da kuma addu'ar Allah Yasa ta ha?ura.
&da sassafe Hudayya ta shirya cikin uniform Win da suka haskata haWe ta fito da kyawunta dai-dai misali,amma ita a yanda takejin kanta sai take ganin kamar tafi kowa kyau.
A gurguje ta fito harabar gidan.ta kuma yi sa'ar samun Abu Zaid yana jingine da Motarshi yana bankawa cikinshi haya?in da Siyaar shi ta tsana.Ba?aramin kyau yayi mata ba,cikin off white shirt da jeans. Tayi tunanin da ta matsa kusa dashi zai ji nauyinta ya Soye abinda yakesha amma sai taga sama-sama ya amsa mata,sai tayi tunanin ganeta ne baiyi ba sai da taji yace ta matsa wajen motar Drivern da zai kaita Makaranta. Jiki a saSule ta koma ta tsaya duk da haka a saitin da zata dinga hangoshi.
Kallo take ?aremai sosai. Duk da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login