Showing 15001 words to 15272 words out of 15272 words

Chapter 6 - YASMEEN COMPLETE HAUSA NOVELS BY MAMAN YUSRA.txt

26 Feb 2026

1172

hakan bai dametaba don tanason ruwan sama idan ya sauk'o bata shigaba batajin dad'i.



Yayyafine ya fara sauk'a hakan baisa ta komaba saima k'ara tafiyarta datayi cikin nutsuwa,ta d'anyi nisa kad'an da gida ruwa ya k'ara yawa tsayawa tayi cak ta d'aga kanta sama idonta rufe kamar mai k'irga zuban ruwan.


Yadda ruwan ke sauk'a kan fuskarta jin wani nishad'i take saidai kuma lokaci guda hawaye ya gauraya da ruwa fuskarta ya sauwa daga annuri zuwa akasinshi.


Tunowa tayi da Anwar d'inta adaidai irin wannan lokacin suna manne da juna,yana bayanta ya sak'alo hannayenshi kan k'ugu ko cikinta ahaka zasu tsaya har ruwan ya d'auke suna cikin nishad'i.


Allah sarki ko yana wani hali yanzu ohho?
Wani fad'uwar gaba taji da yadda jikinta ya sauya tabbas duk yadda akayi Anwar na kusa da inda take,da sauri ta bud'e idonta,tsaye taganshi gabanta ya k'ura mata ido,gaba d'aya ya canza,ya rame yayi bak'i ga wani gashi daya sami muhalli a fuskarshi.


Tausayi ya bata ta bud'e baki zatai magana ta fasa ta juya ahankali da nufin komawa gida k'iranta ya shigayi amma Sam tak'i juyowa


"Habba Yesmeen bai kamata ki gujeniba rayuwata tana cikin garari ki taimaka ki tsaya ko lafiyarki inji,zuciyata,ruhina kullum tana tare dake."


Yadda yake maganar duk yabata tausayi juyowa tayi race


"Kabi Umurnin mahaifiyarka,karka manta tace duk randa ka taka kazo gareni zata tsinema,ko mak'iyina bana fatan tsinuwar iyaye ta tabbata akansh,kabi umurnin mahaifiyarka karka manta ana sake mata amma ba'a sake uwa da 'yan'uwa."


Tana kaiwa nan tajuya,shikam yama rasa tacewa harta k'ule yana tsaye,jiki ba kwari shima ya juya.



_Nima juyawar nayi tare da tausayawa masoyan_





✍🏻 *~UMMYN SADEEQ~*

4
5
6

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login