Showing 6001 words to 9000 words out of 15272 words

Chapter 3 - YASMEEN COMPLETE HAUSA NOVELS BY MAMAN YUSRA.txt

26 Feb 2026

1171

๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž

*YESMEEN*

๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž


*STORY & WRITEN BY:*
*UMMYN YSRH*



*ยฎPURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*(P.M.L)*



*56~60*

Labari taci gaba da basu.

"Kamar yadda kuka sani gidaje hud'une kawai tsakanin mu daku agarin Jos,kwatsam wata rana cikin dare aka rink'a cinnama gidajenmu wuta,wuta da yayi sanadiyar salwantarda rayukan al'umma da dukiya mai d'umbin yawa,duk 'yan gidanmu sun k'one nida mahaifiyata kawai muka samu fitowa daga gidan ta k'ofar baya sana diyar wutan bai sami ta wajenba".

"Wani rami mukasamu muka b'uya nida Mamina,kwananmu biyu b'oye cikin ramin duk mungama galabaita,da mukaji fad'an yad'an lafa ansa jami'an tsaro shine muka fito da sand'a muke tafiya kamar wa'yanda za'a kamamu,bamuyi nisa da tafiyarba naji Mamina tace".

"Wash!"
cikin wani azababben murya ,zama tayi arud'e nace

"Mamina lafiya? Meya faru?"

"k'afata Ihsan."

"Dubawa nayi naga wani k'aton kwalbane ya shige ciki ashe tun randa abun ya faru taji ta taka abu tsabar tsoro bata tsaya dubawaba,sai yau data taka k'afar taji.


"Mami ki k'ok'arta mubarnan karsuzo su kamamu."

"Ihsan ki gudu kawai,bazan iya tafiyaba."

"nima bazan iya tafiya ba tare dakeba,gara kawai muzaunanan suzo su k'arasamu."

"A'ah kije kawai."

"Cikin kuka tace"

"me amfanin tafiyar tawa bake,wani jin dad'in rayuwa zanyi? Gara mu mutu tare Maminah."

"Toh muje"

"zaki iya tafiyarne?"

"Murmushin k'arfin hali ta sakarmata tace"
"Eh".

" _Allah sarki mahaifiya mai hak'uri juriya,sadaukarda rayuwarta domin farin cikin 'ya'yanta๐Ÿ˜ฐ_ ".

" _Allah kayiwa iyayenmu kyakkyawar sakamako,kabamu ikon yimusu biyayya har k'arshen rayuwarmu wanda suka rigamu gidan gaskiya ka gafartamusu,kasa aljannah tazam makimarsu._ ".

"Haka ta tashi da k'yar take taka k'afar,muna tafiya tana hutawa,bamukaiga k'arasa fita daga Unguwarba wata moto ta tsaya gabanmu,cikinta da mutane da yawa,sukace mushiga kamar bazamu shigaba amma ganin bamuda mafita yasa muka shiga,ashe masaukin 'yan gudun hijira za'a kaimu,ansaukemu a garin TILDEN FULANI saurankuma aka wuce dasu wasu garuruwan har zuwa garin BAUCHI."


"Kwananmu biyu awajen ba wani kyakkyawar kulawa sai d'ankaran wahala daga cikin garin mutane suke kawomana tallafin abinci da kayayyakin sawa".

"Ganin K'afar Mamina sai hawa yake yasa naje na rok'i wani mai chemist yazo yaga k'afar,sanda yazo masifa sosai yamin ganin yadda k'afar yake,yace maza in d'auketa inkaita asibiti cikin Jos tunda yanzu fad'ar ya lafa,kud'in moto yabamu nayita mai godiya ina kuka haka da rarrafe Mamina ta iso bakin hanya da k'ar muka sami moto don har yanzu ba'ashiga garin sosai".


"Lokacin da muka iso abun hawa muka sake hawa wani k'aramin asibitin kud'i mukaje don duk asibitin gwamnati ma'aikatansu sun gudu sai d'ai_d'aiku,suma sunk'i karb'armu,sanda muka iso wani Likita muka samu,namai bayanin komai da kuma rashin kud'in da bamu dashi yace ba komai wanda ya taimaki wani Allah zai taimakeshi.
Yace ya d'au nauyin komai,aka bamu d'akin ba kowa saimu kad'ai".

"Da dare yazo yaba Mamina magunguna ya mata allura,yace insameshi a office".

"Bayan fitarshi bada jimawaba bacci ya d'auki Mamina,kayan abincin da mukaci na tattara na maidasu gefe na jamata k'ofar na fita ba tare da fargabar komaiba".


"Da sallamata na tura k'ofar,ya amsa waje yanunamin inzauna,zama nayi yafara magana kamar haka".


"a gaskiya k'afar mahaifiyarki na buk'atar aiki sosai,da nayi tunanin k'aramin abune saidana duba naga aikin sosaine."

"yanzu doctor ya za'ayi?"

"Abunyi kawai shine nanda kwana biyu kije kinemo wasu kud'i idan ya haura hakan dole saida ayanke k'afan don kwalbar ya riga ya rub'ar mata da k'afa."

"Wallahi ayanzu bamuda komai don Allah ka taimaka."

"taimako zan iyayi miki ammafa inhar kema zaki taimakamin."

"Banda abunda zan taimakama dashi."

"keko kikeda abun taimakamin idan kin yarda ..........................agobema za'aiwa mahaifiyarki aiki."

"Agigice tamik'e donjin kalmardata fito daga bakin likita".

"bafa abundamuwa bace,zab'i nabaki ko kud'i ko kanki daga gobe zuwa jibi kije ki tunani."


Fitowa tayi gaba d'aya bata cikin hayyacinta maganar kawai ke mata yawo a kwakwalwarta.


_ko kisamo kud'i ko ki fanshi lafiyar mahaifiyarki da ni'imar da Allah ya miki_


_Tirk'ashi_




โœ๐Ÿป *~UMMYN YSRH~*.
[02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: ๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž

*YESMEEN*

๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž




*STORY & WRITEN BY:*

*UMMYN YSRH*


*ยฎPURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
*(P.M.L)*



*Tako ina kunchanchanci godiya da jinjina agareku*

*hazik'ai,jarumai,jajirtattu,masana sanin darajar d'an adam*

*Kunyine ta ko'ina๐Ÿ˜*
*Allah k'aramana had'inkai,zaman lfy da hak'urin zama da juna*

*Allah karemu daga sharrin masu sharri, da hassada*

*PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*โ˜บโ˜บ

*UP*
*UP*
*UP*

*KUNA ZUBA K'AMSHI INA BINKU DA HUMRAHโ˜บโ˜บ*

*ALLAH K'ARA D'AUKAKA*



*46~50*

Juyi kawai take sam bacci yak'i d'aukarta,mik'ewa tayi taje tayo Alwala ta fara sallah don kai damuwarta ga Mahaliccinta.

Saidatayi sallar asuba ta kwanta.

K'arfe bakwai daidai Ummah ta tashi,tana mamakin irin nisan baccin da tayi,taji dad'in jikinta kam,yanzu ba jirin sai rashin k'arfin jiki da d'an ciwon kai.


Motsin da YESMEEN tajine yasata bud'e ido,Ummanta tagani tana k'ok'arin tashi tace

"Lahh Ummah kin tashine."

"Eh bayan kinki tashina inyi sallah akan lokaci."

"A'ah bak'in tashinki nayiba,gani nayi kinsha magani nasan kuma shiyasaki bacci,kar in tasheki in k'ara miki ciwon kai."

"Aikam naji sad'in baccin don yanzu jikin da sauk'i."

"Allah k'ara sauk'i Ummahnah."

"Ameen."

"barin in samiki ruwan wanka idan kinyi zaki d'anji k'arfin jikin."

"aiko dakin kyauta.
Allah miki albarka."

"ameen Ummah nah."


Kafin ta fito wanka ta gyara d'akin tsaf,ta ciromata doguwar riga mara nauyi ta shimfid'a mata Sallayah sannan ta fita,gabanta sai bugawa yake tana Addu'ar kar Allah ya had'ata da YAYA SANI.


Duk wayewar gari saitaje ta gaida HaJIYA TALATU kodako bazata amsaba da harsu RUKY take gaidawa dataga iskanci suke mata idan tazo gaishesu ta sauwak'e ma kanta.


Kitchen ta nufa d'auko musu abun karyawarsu,ZAHRA ce kawai a kitchen d'in tanata aiki,ganin YESMEEN ta shigo tace


"Aunty Yesmeen ya jikin Aunty?"

dariya Yesmeen tayi tace

"ZAHRA bako gaisuwa sai tambayar jikin Aunty."


"Allah na damune jiya ban iya bacciba,gashi tun d'azu Hajiya na falo tak'i shiga ciki balle inshaga indubata."


Tana maganar tana kwalla.

"Karki damu Zahrah Aunty taji sauk'i,yanzuma wanka ta shiga."

"Allah k'ara mata lfy,ga abun karyawarku tun d'azu na had'a muku."

"Toh,mungode."

D'auka tayi ta nufi d'aki,tasamu Har Ummah tayi Sallah,tana zaune.

Bayan sun gama karyawa ta shiga wanka,lokacin daya fito ta tadda HANIFA da MOMMYNTA sunzo gaida UMMAH.


Bayan ta gaishesu ta shirya Kud'in magani ta karb'a da takardan maganin.

Ummah tace

"kije shakatafi can k'ofar Central market nan zaki samu duka,Allah kiyaye hanya akula kuma."

"Ameen.
Saina dawo"


Tafiya take amma jikinta ya bata tabbas yana waje,tambayar kanta take


"Meyasa duk inda yake indai ta doshi wajen sai jikinta yabata?"

"meyasa batajin hakan ga sauran mutane saishi kad'ai?"

"Wai meke faruwa da itane?"

Wata zuciyar tace

"Kinfad'a soyayyah Baby,meyuwa shid'in wani sashene na jikinki."


"Soyayyah kuma?yaushe? Mutumin dako magana bai tab'a had'amuba."


Bata kaiga k'arshen tunanintaba taji magana daga bayanta


"Amincin Allah ya tabbata agareki."

Cak ta tsaya ta juyo dan ganin mamallakin wanan muryar, ido biyu sukayi dashi yanata zubamata murmushi, kasa amsamai tayi.

Yace

"ba magana? Dama jinayi zuciyarki nata kirana shiyasa nazo gareki,ashe k'arya tamin."

Juyawa yayi yace

"Nabarki lafiya tunda bakya buk'atata,duk sanda kike buk'atar ganina zuciyarki zaya kirani."

D'agowa tayi taga tafiyar yake azuciyarta tace

"tafiyar kayi kuma?"

Juyowa yayi da murmushi yace

"eh,tunda bakya bukatata kink'i kimin magana"


Rufe bakinta tayi da hannuwanta tace

"Ashe yajini."


"ban jikiba zuciyar da kike magana da ita ita gayamin."


Juyawa tayi tana addu'a yau ta gamu da aljani,harta fita titi bata k'ara juyawaba.

Tad'au lokaci mai tsawo tana jiran abun hawa amma shuru.


Dak'yar tasamu mai keke napep,sunyi gaba kad'an suka sami wata suka d'auketa zata sauk'a wajen
CITY STORE

tunkafinsu k'arasa tsayawa wani shirgegen Alhaji ya fito daga cikin waje wata 'yar matashiyar budurwa biye dashi,hannunta rik'e da manyan ledodi guda biyu wani banzar shiga da tayi ko kad'an baza'a tab'a zaton d'iyar musulma bace.



Tundaga nesa YESMEEN ke mamakin yadda taga yarinyar da suka fito cikin wajen da wannan mutumin,tana tunanin anya itace kuwa? tsayawarsu yayi daidai da shigarsu moto su tayar matar na sallamar mai napep d'in YESMEEN tace

"Malam don Allah mubi bayan wannan moton."

"kinsansune?"

"Eh kawai tace."


"Toh kud'inafah?"

"muje zanbaka karka damu."



Nidai dake gefe nace
Kunga d'an'uwan kawata MSB masoyan kud'i๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜›




โœ๐Ÿป *~UMMYN LABEEB~*
[02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: ๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž

*YESMEEN*

๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž


*STORY & WRITEN BY:*

*UMMYN YSRH*


*ยฎPURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*(P.M.L)*


*61~65*


Yadda naga rana haka naga dare,bacci ya d'auke a idona,duk tunanina ya tsaya, ina zanje in samo kud'i,anya zan iya saida mutunciga ga wani k'ato kuwa,haka na k'areshi atunani,gari na wayewa bayan nayi sallah nayi wanka,Mamina zaune tayi sallar nasa mata ruwa tayi wanka,Doctor ya kawo mana abun karyawa nikam kasacin komai nayi,nama Mamina sallama zani cikin gari gun 'yan'uwa kozamu sami wani abun,likita yace akwai magungunan daza'a saya kafin afara aikin,Addu'an samun nasara tamin na fice.


Wuni nayi ranan ina zaga gidajen 'yan'uwa wanda rikicin ya shafa da wanda bai shafaba duk cemin suke basudashi inyi hak'uri,rikicinnan yasa duk 'yan kud'ad'ensu sun tafi,daga mai ban naira d'ari,d'ari biyu hamsin,harkan hanya natsaya neman taimako amma ba wanda ya kulani.


Gidanmu na nufa ta gefen da wuta bai ciba kozan samu abun sayarwa saidai ba komai cikin wajen,dama sabon ginine Yaya Kamal yayi inda zai zauna da matarshi,ba'akai ga bikinba ta rutsa dashi.


Fitowa nayi na nufi hanyar asibitin duka duka kud'in dana samu d'ari tara da ishirin,mu masu neman dubu ishirin,sanda na dawo Mami na zaune rik'e da k'afar sai azabar zafi,da zugi yake mata,ga yunwa gashi yau likitan bai lek'oba tun safe dayazo bai kuma zuwaba,na tambayeta ko 'yan'uwanmu sunzo tace ba wanda yazo,fita nayi naje na samomata abinci taci mukayi sallar magriba,office d'in likitan na nufa don ganin ko lafiya ba ba Mami maganindake hana k'afar zugiba,kafin in k'arasa naga sun fito da wata kodaga yanayin shigarta kasan ba d'iyar kirkiceba,wucewa sukayi ko kallon inda nake baiyiba haka na koma jiki ba kwari,haka Mamina ta kwana ranan cikin rad'ad'i da zafin ciwo ga k'afar har ruwa yake,nayi kukan zuci nayi na fili narasa yadda zanyi intaimakama Mamina yanzu rayuwa kowa kanshi ya sani bamai taimakon wani koda ciki d'aya kuka fitoda mutum burinshi yaganka cikin k'askanci, zanbada Mutuncina domin ceton ran mahaifiyata.


Ganin irin wahalar da Mamina keshe yasa na yanke hukuncin bama likita abundaya buk'ata gareni,washe gari na je na sanarmai na amince da fara'arshi baki har kunne yace gobe za'a mata aiki,wunin wunin ranan kula na musamman muka samu,nidai duk jikina ba kwari idan nai runanin fasawa inna tuna yadda Mamina ke wahala sai inhak'ura da dare yazo yaba Mamina magani ya mata wani allura,tambayata yayi yaga jikina ba k'arfi nace kaina ke ciwo yace inje inkarb'i magani a office d'inshi.


Saida Mamina tai bacci sannan na nufi gun likita,wani kwayar magani yabani da ruwa nasha band'au lokaciba naji gaba d'aya nakasa gane wani yanayi nake raye nake ko amace,bacci nake ko ido biyu nida kamar gunki haka nake jina,haka yafi sama da awa hud'u yana abu guda,sai kusan asuba nafara dawowa hayyacina,yadda naganni nasan mai afkuwa ya afku,tashi nayi nasa kayana da k'ar nakejan kafata don azabar ciwo,d'akinmu na nufa har yanzu Mami na bacci,bayan gida na nufa na zauna naci kuka iya kuna nayi tsarki na yi wanka na fito,nayi sallah ina zaune Mami ta farka mik'ewa nayi da nufin kawo mata d'auki zuwa bayan gida saida ina taka kafata naji wani azabar zafi har kwakwalwar kaina,da kyar nake tafiya Mami ke tambayana lfy nace sulewa nayi a bayan gida,tamin sannu.


Ranan wuni likita yayi yana mana sintiri yanason mukeb'e sam nak'i yarda,danamai maganar Aikin yace sai gobe yanzu basuda wasu kayan aikin sai ansayo.


Muna hira da Mamina tanatamun nasiha kan rike mutuncina da hakuri da rayuwa aduk yadda yazomin likita ya shigo albarka Mami tayi tasamai bisa taimakon da yake mana,yace ba komai yiwa kaine.


Kamar kullum allura yamata ya bata magunguna,ya zauna sunata d'an hira da Mami,can dayaga bacci ya d'auketa ya mik'e yace yama jirana,zuwana shine kwarin gwiwar yin aikin rashin zuwana shine koma baya ga aikin.

Ba yadda na iya haka nabishi yau baiban komaiba saidai naci bak'ar azaba,yana gamawa ya juya yacigaba da bacci nima nayi gaba,nayi sallah ina jiran farkawar Mami shuru,har wajen tara bata tashiba zuwa nayi na tab'ata gaba d'aya jikinta ya saki ba alamar numfashi,jijjigata nashigayi shuru da gudu nanufi office d'in likita bako sallama na bud'e k'ofar na shiga abundana gani yasani fitowa ba shiri,likita nagani da wata ma'aikaciyarsu sunata zabga masha'arsu.


D'akunan asibitin nayita dubawa amma duk ba mutane,d'akin k'arshe naga wani namiji kwance damai jinyarshi nace don Allah su taimaka sudubamin Mamina bata motsi ko dogon suma tayi na duba likita bayanan.


Tare da d'ayan mukazo yadubata

Yace "Saidai kiyi hak'uri wanda yafimu sonta ya karb'i abunshi."


Kawai jinayi nazube wajen asume


Nima sumewar zaune nayi sanadiyar gajiya danayi da typing๐Ÿ˜›




โœ๐Ÿป *UMMYN YSRH*
[02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: ๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž


*YESMEEN*

๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž


*WRITEN BY:*
*UMMYN YSRH*


*ยฎPURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*(P.M.L)*


_THIS PAGE IS 4 U BIEEBEE YAREEMA_
_ALLAH BAR ZUMUMCI SO DA K'AUNAR JUNA_
_ALLAH K'ARA BASEERAH,HAZAK'A 'DAUKAKA,KWARIN IDO DA ZAK'IN HANNU๐Ÿ‘๐Ÿป_





*71~78*

Gaba d'aya mutanen falon sun rud'e kad'an daga cikinsu masu k'arfin imanine suka iyayima Alhaji fatan Allah maida Alkha'iri,yasa da abunda ya tsare,sauran kuwa daga mai tsinewa sai masu koke_koke,ahaka taron ya watse.



Bayan y'an kwanaki al'amura sun fara canzawa,sun fara fuskantar yanayin rayuwa,ga Hajiya Talatu tsurfar yau daban ta gobe daban,haka suka tasa Alhaji gaba ita da Hajiya Mama akan sai Ummah ta rage yaran d'akinta tunda suma yanzu basu wadataba.


Hak'uri kawai yake basu na indai abun da zasucine da yardar Allah bazai gagaraba.

Itama Ummah dataga abun yak'i sauk'i ta tattara Ihsan ta kaita ga y'an uwanta tare da yimusu y'ar nasiha ta dawo gida.


Ummah Habiba cikin shirin bacci ta nufi d'akin Alhaji hannunta d'auke da wani bak'in leda,waje ta samu ta zauna kasancewar Alhaji na wanka,saida ya yafito ya gama shiryawa tsaf sannan Ummah ta mik'omai ledar data shigo dashi.


Dubawa yayi yace

"Wannanfa na meye?"

"Nakane Alhaji."

Cikin mamaki yace

"nawa!!"

"Eh. Naka."

"Ai yanzu banda kud'i mai yawan wannan."

"Tunda ina dashikam ai tamkar nakane."

"ke ina kika samo kud'i har dubu d'ari biyar haka?"

"Filayena guda biyunnane nasaida d'aya dama na bari sai Auren Yesmeen ya tashi sai insaida ayi hidima tunda wani matsalar ta fad'o kaga gashi yayi amfani."


"Toh amma shine zakiban wannan kud'i haka? Kemafa kud'inki na sarin kaya ya salwanta atafiyannan,ni ya kamata in k'ara miki jari idanna samu bake ya kamata ki bannakiba."


"Habba Alhaji don k'addara ta gifta sai ince ka biyani kud'ina?
Kaifa ka bamu jarinnan har na juyashi ya zama kadarori,don yau baka dashi sai in kasa tallafama,idan nayi haka nayi butulci."


Godiya ya shiga jero mata ta dakar dashi

"Habba ba godiya tsakaninmu,kaina gatanmu arayuwa,ka cancanci fiye da haka arayuwarmu,kacirema masu binka dubu d'ari biyunnan sauran sai a lallab'a Allah k'ara rufa asiri."

"Ameen nagode."


"kinga na manta d'azu da magriba nayi suruki,yazo neman izinin zuwa neman Auren 'yata Yesmeen,bisa ga yanayinshi naga yarone mai nutsuwa da kamun kai,ban amince mishiba nadaice sainayi shawara da mahaifiyarta idan yaso sai ya nemeni yaji amsarshi."


"Habba Yesmeen ai d'iyace agareka,duk hukuncin da zaka yanke kansu Zahra itama haka zaka yanke kanta,indai ka yaba dashi,ba matsala."


"Gaskiya ne nagode ka karramawarki gareni,yaron da gani baida matsala,sab'anin matasan yanzu zaiyi wuya kiga anzo tambaya kafin fara hira da budurwa,saidaimai idan ya iso ya danna horn na moto ko mashin ko k'iran waya,ita kuma jiki na rawa zata fita."

"Ummah na dariya tace

"Ashe Alhaji kasan komai."

"Nasani mana bagani da 'yaranba duk cikinsu wa yatab'a zuwa neman izini,saidai kiga yarinya na rab'e_rab'e zata fita,da kayi magana ace kafiya tak'urama yara kabarsu lokacinsune,yanzu taurarinsu ke haskawa,duk Hajiya ke d'aure ma Talatu ta ke yadda taso baka da ikon yimusu magana amatsayinka na Uba,son jikoki ya rufe mata ido."

"Hummm!
Sai hak'uri Alhaji Hajiya Uwace fah haka zamuyi mata biyayya domin aljannarka na gareta,Addu'a zakayi tamusu,da fatan Allah shiryasu ya karesu da fad'awa mummunan rayuwar wannan zamanin."


Lokaci mai tsawo suka d'uka suna tattaunawa kan matsalolinsu daga baya suka kwanta.


Cikin sand'uwa yake tafiya kaman tsohon b'arawo har ya isaga k'ofar d'akin ya murd'a saidai yauma arufe kamar kullum,ciza leb'enshi yayi cikin ta kaici ya juya yace

*YESMEEN duk randa kika shiga hannuna kun kad'e,sau uku ina kawomiki hari bana samun nasara,muje zuwa idan kere na yawo zabo na yawo za'a had'une saikin raina kanki."



_nidai nace in Allah ya yarda Allah bazai baka nasara kan marainiyar Allah ba akan mugun nufinka SANI_




Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login