Showing 9001 words to 12000 words out of 15272 words

Chapter 4 - YASMEEN COMPLETE HAUSA NOVELS BY MAMAN YUSRA.txt

26 Feb 2026

1173

โœ๐Ÿป *~UMMYN LABEEB~*
[02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: ๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž


*YESMEEN*


๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž


*WRITEN BY:*
*UMMYN YSRH*


*ยฎPURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*(P.M.L)*



*Du'a hai ki kamyabi ke har sikhar pe aap ka naam hoga,*
*aapke har kadam par duniya ka salam hoga,*
*Himat se mushkilon ka samana karna hamari du'a hai ki waqt bhi ek din aapka gulam hoga.*
*HAPPY BIRTDAY MY MERMUE*

*Allah karo shakaru masu albarka tsawon rai,da lafiya mai amfani,Allah cika miki burinki na rayuwa yasa jin kirin yazama alkhairi*๐Ÿ‘๐Ÿป



*76~80*

_Washe gari_

Alhaji ya had'a kan iyalanshi ya sanarmusu alherin da Hajiya Habiba ta mishi,nan Hajiya Talatu tace


"Habba dagaji wannan zance shiryayyiyane,ta ina ita Habiban ta sami wannan mak'udan kud'ad'en da har zata baka, saidai idan wani shirin kukayi."


"Haba Talatu cikin filayenta biyu ta saida d'aya,jarin dana baku shi taketa juyawa har yanzu kuma Allah yasa mata albarka ciki."

"wannan zancen k'aryane, jarin kusan shekara uku kenanfa daka bamu,tun yaushe nawa ya karye na bika kaban wani har yau shuru."

"Nasan koda na baki ba juyawa zakiba."

"kasanfa inada yara wasu hidima dole inyi musu,itafa wata ajiye?"

"ya isa haka Talatu!!"

"Aidole kace inyi shuru tunda ba ka adalci adaiji tsoron Allah."

Bud'e baki yayi zaiyi magana sai kuma ya fasa

Hajiya Mama dake gefe tace

"komadai menene ai dole ta maka tunda dama ta dalilinka ta sami dukiyar."

"Yauwa Alhaji batun dubu hamsin da kace inkasami kud'i zakaban na sayan kayan baby da zannuwana,tunda kud'i ya samu sai a ciremin."

"Gaskiya Talatu bazaki sami dubu hamsin ba zandai baki ishirin."

"Habba ishirin mezai min ai gara in hak'ura wallahi."

"Waikai bakasan ciki da goyo yana kashe kaya bane,ai dole zata nemi k'arin tufafi don haka ka k'ara mata."

"Toh Hajiya zan bata talatin."

"Yaushe?
Aigara ka mik'omin yanzu don kana fita dashi nasan bazai dawoba."

Talatin cif ya lale ya bata yaba mahaifiyarshi dubu biyar,taro ya watse,Ummah Habiba dake gefe dama kallonsu kawai take k'ala bata tankaba,taro na watsewa itama ta k'ara wuta.


_Bayan kwana biyu_

ANWAR ya dawo gun Alhaji don jin yadda zancensu ya kwana,ya amince mishi ya bashi daman ya fara zuwa sannan bai buk'atar dogon lokaci da sun fahimci juna sun gama bincikensu za'ai maganar Aure,tafiya yayi don fara shirin zuwa zance yau,ji yake tamkar sallah.


Ummah ke sanarda Yesmeen yau zatayi bak'o don haka tashirya ta kuma zama mai kamunka,nutsuwa da tsare mutuncinta a duk inda take.


_7:30pm_
Bayan sallar isha Malam Anwar tsaye k'ofar gida yana jiran d'an aika ya fito daga k'iran Yesmeen,yasha shaddar sai walwali yake kamar wani sabon ango kamar kullum fuskarshi sake yake d'auke da murmushi.

Yaron ya fito ya sanar mai tana zuwa ya shigo daga ciki,harabar gidan ya shigo ya zauna kan wasu kujerun roba daya gani awajen.


Zaune take amma jikinta na gaya mata tabbas makusancin zuciyarta na kusa da ita,rabon data ganshi tun ranan da suka had'u da Ihsan,Ummah ta lek'o tace tanada bak'o awaje.

Jiki ba kwari haka ta mik'e kamar kullum babbar hijabinta tasa ta nufi hanyar waje gabanta sai fad'uwa yake,gashi ba wuta balle taga fuskar mai k'iranta.


Tana fitowa harabar gida ana kawo wuta daidai fuskarshi wutan ya hasko mata ba k'aramin razana tayiba data ganshi wato har yafara mata gizo kenan har ta juya zata tafi taji yace

"K'araso mana nine."

Cak tayi mutuwar tsaye ta kasa motsi.



_nima cak na tsaya sanadiyar gajiya danayi da typing๐Ÿ˜›_



โœ๐Ÿป *~UMMYN YSRH~*
[02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: ๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž

*YESMEEN*
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž



*WRITEN BY:*
*UMMYN YSRH*



*ยฎPURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*(P.M.L)*


*66~70*

A storace mutumin yayi kaina ya duba yaga da numfashi,da gudu ya fita duba likita saidai ba likita ba alamarshi,gaba d'aya asibitinma ba kowa.


D'akinsu ya koma ya d'auko ruwa ya sake dawowa d'akin da muke ya yayyafamun,wani dogon numfashi naja zuciyata na rayamin mafarki nake,ahankali na bud'e idona saidai ina gaskene Mamina ta rasu ba mafarki nakeba,wani irin kuka kawai na sake,ga rashin Mamina gakuma kimata dana badashi ga wani k'ato,bakina kawai ba abunda yake furtawa sai kiyafeni Mamina na salwantar da darajata,kimata,y'ancina.


Da taimakon wannan mutumin naje na sanar da 'yan'uwanmu rasuwar,sanda naje kame_kame suka hauyi akan yau zasuje dubata.k'annenta biyu muka taho dasu aka d'au Mamina mukayi gaba,akamata wanka aka kaita makwancinta,tundaga nan nafara fuskantar k'ask'antacciyar rayuwa,gidan k'anin Ma mina,ba wadataccen abinci,sutura,kulawa,bawai don babuba.

Da nagaji nace ya nemamin 'yan haya asa ad'aya gefen dabai k'oneba kud'in sai in rink'ayin wasu uzurina,masifa sosai sukamin na wai na raina abunda sukemin indai hakane in tattara in koma gun dangin mahaifina,haka koma wajensu nanma zaman gashinanne.


Ahaka na had'u da wata k'awa maibin maza tun tana jan ra'ayina inak'i har na yarda.

Da aka fahimci rayuwar da nake ciki shine aka korani wai bazasu iya zama da karuwaba kar in lalata musu tarbiyar yaraba,haka na tattara na koma gidanmu nida k'awata,nan muke fita musaida mutuncinmu abiyamu mu biyama kanmu buk'ata don itama batada kowa yak'i ya cinyesu.


Har gari_gari ake tafiya damu,idan mun gama mu dawo gida,ahaka rayuwata takasance.

Dogon numfashi Ummah taje tace

"ikon Allah."

Yesmeen tace

"ya labarin likita kuma?"


Bayan na dawo hayyacina na koma don ganin likitan sai cemin akayi ai dama an rufe asibitin ba'a aiki cikinta sabida lalata mata da likitan yakeyi,yanzunma ganin fad'an da akayine hankali baya kanshi yasa ya nud'e a boye.

Nayi kuka iya kuka na yadda na salwantarda rayuwata,saidai idan banyi hakanba banda ma fita.

Ummah Ta mata fad'a sosai da nasiha mai shiga jiki,takuma ce idan ta kwana biyu zata maidata gun danginta ta basu hak'uri.

Ahaka muka d'au lokaci mai tsawo kafin muka kwanta.

Ummah ta ware sosai don ta karb'i girki,gashi yau Alhaji zai dawo,kowa murna yake don wannan karon ya jima a Lagos,gashi mafi yawan lokaci ba'a cika samun wayarshiba.

Hajiya Talatu tunda ta kyalla ido taga Ihsan hankalinta ya tashi kullum cikin gori da habaici,yauma tana kan abunda tasaban


"Mutum saidai ya k'are' a kalen dangi azo anacin arzik'i amma badai ya haifaba."

"Hajiya kenan Allahn daya baki ba wayo ko dabararki yasa ya bakiba,nida ya hana ba k'ina yayiba,haihuwa nufin Allah ne,idan yaso ya baka inyaso ya hanaka,da kike batun gado duk cikinmufa ba wanda yasan gawan fari."


"Lah ha'ila ha'illallahu!!!
Kice so kike kawai Alhaji ya mutu,tunda bakida d'a dashi bakida asarah,tah Wallahi ta Allah ba takiba,saidai ke ki mutu kibar Alhaji muguwa kawai,inda kinada yara bazakiso ya mutu yabarsu da maraiciba."


Ta bud'e baki zatayi magana kenan saiga Hajiya surukarsu wani matashi ya shigomata da akwatin kayanta.


"Lafiya kuke tsaye cirko_cirko kaman zakaru?"

"Hummm!!!
Inafa lafiya.
Wannan muguwar kema Alhaji fatan mutuwa."

"Mutuwa?
Auko saidai ki mutu kibarshi muna fuka,ai duk bak'in cikinki nakan wannan cikin ta saiya fito duniya saida ki mutu,shiyasa na tattaro kayana na dawo gidan gabad'aya,don kar kije kima Talatu wani mugun abun."


"kiyi hak'uri Hajiya Wallahi ba..........."


"Dallah rufemin baki,da anfara magana ki su kuy da kai kina bada hak'uri kamar mutumiyar kirki,ni b'acen da gani."



Jiki ba kwari Ummah ta wuce,haka ta gama girkinta ita dasu Ihsan,duk wucewa sai an watsomusu bak'ar magana bamai tankasu.

Sai wajen takwas Alhaji ya iso gida,da kaganshi kasan baya cikin hayyacinshi,gaba d'aya ya fad'a yayi bak'i,ba wani walwala sosai a fuskarshi,haka suka mai sannu da zuwa ruwa ya watsa yayi sallar isha sannan yazo yad'an raba abinci kad'an,babban falon gidan ya had'a iyalanshi harda mahaifiyar tashi,nan yake sanar musu tafiyar da yayi ya had'u da 'yan danfara kaf sun yasheshi gashi kusan duk dukiyarshi ya kwashe ya tafi sarin kaya ciki harda na mutane,sunyi binceke amma sam ankasa gane mutanen don gari irin Lagos ganesu ba abune mai sauk'iba.

Gaba d'aya d'akin yad'au salati wasu ihu,wasu ashar suke antayowa.

Hajiya Talatu kam mutuwar zaune tayi,saida d'an cikinta ya motsa tsabar tsoro.


_nima gefe na koma ina tayasu jimami yanzu shikenan ba wani gado dazamuci๐Ÿ˜ญ_






*UMMEEN YUSRAH*
[02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: ๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž



*YESMEEN*

๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž



*WRITEN BY:*
*UMMYN YSRH*



*ยฎPURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*(P.M.L)*


*86~90*

*Jinjina gareku 'yan JUST NOVEL GROUP BY ABBA BESST Allah bar zumunci*



Gidane na sama da k'asa amarya da ango suna sama sai mahaifiyar ANWAR ak'asa,su biyu mahaifiyarsu ta haifa shine babba sai k'aninshi MUNEEB.


MUNEEB d'angatane na k'arshe gun mahaifiyarshi sab'anin ANWAR ko kara ta ajiye baida ikon giftawa ba tare da izinintaba,mahaifinsu ya rasu tun MUNEEB nada shekaru biyar aduniya duk waniso da k'auna ta iza kan Autannata duk hukuncin daya yanke a abu ta zauna.
Yanzu haka yana makaranta a kano.


ANWAR ma'aikacine a maikatar Ilmi dake cikin garin Bauchi,duk da ba wani Babban ma'aikaci bane akwai rufin asiri.

Duk wani aiki na gidan Tasakarma YESMEEN
Masu aikinta ta sallamesu,hakan sam bai damun YESMEEN tunda tasan Uwa take gareta,ga tsana datake nuna mata bata tab'a gayama kowa ba,tana rok'on Allah ya sassauto da k'iyayyar da Hajiyar ke mata.


*BAYAN WATA BIYU*


Yau gidan UMMAH HABIBA d'auke yake da manyan bak'i HAJIYA ASMA'U ne yau Allah yayi zuwanta duk da Umman na fushi da ita amma tayi farin cikin zuwanta,sunyi hirar yaushe gamo sannan suka rank'aya gidan Amarya YESMEEN.


Tayi murna da farin cikin ganinsu,sun tami tarba wajen HAJIYA LAMEE mahaifiyar ANWAR ba yabo ba fallasa,Ummah Habiba ke tambayarta lafiya taga ta fad'a,tace tayi rashin lfy amma da sauki,basu d'au wani lokaciba suka tafi,YESMEEN hadda kuka.


Kwana biyu HAJIYA ASMA'U tayi ta koma ta tausaya masu Ummah halin da suke ciki yanzu don abun ya k'ara ja baya,saidai muce Allah k'ara rufa asiri.


Aikin kawai take amma sam batajin dad'in jikinta ga jirin da takeji sama_sama ga tashin zuciya, saidai bata isa race batada lafiyaba Yanzu HAJIYAR ta farmata,adaddafe ta gama abincin ranan ta gyara wajen tayi sallah ta kwanta.


Tunda ANWAR ya dawo yaganta kwance yasan ba lafiyaba sanda ya tambayeta tamai bayanin yadda takeji,shiryawa yace tayi suje asibiti.


Gwajin farko ya gwada tana d'auke da ciki na wata uku,duk kunya ya rufeta ANWAR kuwa yarasa inda zaisa ranshi don Murna,haka suka koma gidan cike da farin ciki.


Sanda ya sanarwa mahaifiyarshi ba laifi tayi murna,dalilin cikin harta d'an sami sauk'in wasu aiyukan,tana samun kulawa ba laifi.


Ummah Habiba tayi murna sosai sanda labarin cikin ya isketa,har gida tazo taga d'iyar tata.


*BAYAN WATA HUDU*

cikin YESMEEN yana wata shida yanzu,yau sun tashi da shirye_shirye,d'an lelen Hajiya zai dawo,anmai girke_girke iri iri an k'ara gyara gidan kaman wani shugabane zaizo,shima ANWAR baki har kunne yana murnar dawowar k'anin nashi,YESMEEN kuwa sam ta kasa gane wani yanayi take tana murna amma hakanan zuciyarta takejin wani iri.

K'arfe Uku daidai MUNEEB ya iso gidan bako sallama sai Ihun k'irar mahaifiyarshi da yayanshi da kuma AUNTY YESMEEN
da sauri Mahaifiyar tashi ta fito suka rungume juna cikin murna,ANWARMA ya sauka daga samansu suka rungume juna cikin d'oki tace

"Wai ina My Aunty ne?
Inga ko yayan nawa ya iya zab'e,idan bataiminba acanzota."

Dariya dukansu sukayi daidai lokacin YESMEEN na sauk'owa daga sama sanye da Hijabi,juyowa sukayi duka lokaci guda, wani kallon tsana MUNEEB ya mata lokaci guda,har abada bazai tab'a mantawa da wannan fuskarba,yau wai itace cikin gidansu kuma matar YAYANSHI ina sam bazai yuwuba,saidai tabar musu gida,itama wani mummunan fad'uwar gaba taji sanda taga MUNEEB




TOH FAH๐Ÿค”

WAYE WANNAN MUNEEB DIN?

MUJE ZUWA

TAKU HAR KULLUM


*UMMYN YUSRAH*
[02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: ๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž



*YESMEEN*

๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž


*WRITEN BY:*
*UMMYN YSRH*



*ยฎPURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*(P.M.L)*




_Dole in jinjina muku๐Ÿ‘๐Ÿป_
_Hameebrah mai babban Duwais๐Ÿ™Š_
_Aunty Ruma_
_Mom Sultan_
_Bahijjah_
_Xinniey Smart_
_Hajiya Ameerah_
_Iya mai taushe_
_Ameshty_

_kai kunada yawa๐Ÿค”_
_dukanku fatan Alkhairi_



*81~85*

"Ki k'araso mana,ko baki farin cikin zuwata bane in koma?"

Juyowa tayi ahan kali ta nemi waje ta zauna,kanta sunkuye,Sallama ya mata ta amsa ahankali zuciyarta tas ji take kamar anbata kyautar kujerar saudiya.

Bayan gaisuwa tareda d'an tak'aitaccen bayaninshi,da kuma musabbabin zuwanshi gareta.


Lokaci k'ank'ani soyayya mai k'arfi ya k'ullu tsakaninsu,soyayya mai tsafta,basu yini guda batare da sunga junaba.


Lokacinda yaji labarin Yesmeen ya tausaya mata matuk'a yamata Alk'awarin duk rintsi duk wuya yana tare da ita.


Yau anwayi gari Hajiya Talatu ta tashida nak'uda,banda ihu da surutai ba abunda take,ahaka aka kaita asibiti,bayan dogon nak'uda da tayi dak'ar aka samu yaron ya fito,baidai wani lokaciba Rabbi ya karb'i abunshi tayi bak'in ciki sosai don taci buri sosai kan wannan haihuwar.

Bayan gama bincike da manya sukayi akasa ranar biki lokaci k'alilan,saida ansha Artabu da mahaifiyar Anwar kafin ta yadda da auren acewarta sunfison 'yar dangi dak'ar ta yadda da auren.


Shirye_shirye aka sadidan,Ummah duk wani abu da akema d'iya tayima d'iyar tata,lokacin da aka aikama K'anwar Maman Yesmeen Hajiya Asma'u zancen Auren cewa tayi bazata sami halartan bikinba don Alokacin zasu tafi Ummura da Alhajinta,ta Turo musu da gudumawar Dubu ishirin,Ummah Habiba taji ciwon abun sosai wato ta gwada kud'i yafi d'an'uwa,batada lokacinsu tunda ta maidasu mabuk'ata barita turomusu kud'i.


Biki yataso k'awayen Ummah daga kano,Kaduna,sokota,maiduguri,da wasu jahohin duk sun sami Hallartan biki Hajiya Mermue (Mrs Jabo) ita tad'au d'awainiyar gyaran amarya,tayi kyau tayi shar da ita.

Angaida mutan Sokoto,Su Hajiya fatima (Mom sultan) suma sun samu isowa,ga iyalan Ummyn Ysrah novel grp duk sun sami hallarowa tsabar yawan jama'a gidan saida ya kasa musu,wasu gidan su Hanifah aka sauk'esu,Ummah da Yesmeen sunyi kukan farin cikin ganin irin cikowar da akayi dukda basu da dangi yau Allah ya basu wasu dangin masoyansu.


Cikin Kwanciyar hankali akayi biki lfy aka kai amarya d'akinta sai fatan Allah basu zaman lfy da hak'urin zama da juna,Allah kad'e fitina.



โœ๐Ÿป *UMMYN YSRH*
[02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: ๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž


*YESMEEN*

๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž


*WRITEN BY:*
*UMMYN YSRH*


*ยฎPURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*(P.M.L)*


_K'aunarku gareni ta musammane๐Ÿ˜_
_har kullum kuna raina_
*FATY AXLAN*
*Maryam s bello*
*(M.S.B)*
*MY YESMEEN TAFEESU*
*MY SISTO FHARIEEDART*
*SUHANA*
*JANNART*
*DELU CHOGAL*
*MR FAWWAZ*
*AUNTY KHADY*
*SADNAF (LALATA๐Ÿ˜‚)*
*ZAHRAH SURBAJO*
*AYSHA ALI GARKUWA (NAMIJI BAYA KA'DAN)*
*UMMU YAHYA SISIN MAMA (GOYON KAKA)*
*UMMI HAMBALI*
*UMMI GARKUWA*
*DIJA WAZIRI*
*HUSNAH BAUCHI*
*WALIDA WAZIRI*
*RUFAIDA*
*HAFSAT MUSA*
*RAFEE'AT*
*SAMRAH*
*BIEBIE DEE*
*BIBA WADATA*
*SEEMALUV*
*MMN KHADIJA*
*MMN SULTAN*
*UMMU HANEEFAH*
*NANA FA'AD*
*XARAH*
*FATY KHALID NA SHUKA*
*SHAFA ABDULKADIR*
*MARYAM ABDOOL*
*SUMY BASH*
*SALMA*
*ROOKY KAZ**
*NEERATLUVE*
*AYSHA HANWA*
*AYSHA GANA*
*ZEE YABOUR*
*UMMU SAFWAN*
_ALKHAIRIN ALLAH YA TABBA GAREKU 'YAN P.M.L DA WANDA TAGA SUNANTA DA WACCE BATA GANIBA AYI HAKURI IDAN DAMBU YAYI YAWA......_
_INASONKU KAWAYEN KWARAI๐Ÿ˜˜_
_INA ALFAHARI DAKU AKODA YAUSHE_๐Ÿ˜
_ALLAH K'ARA DAUKAKA P.M.L YA RABAMU DA SHARRI MAKIYA MAHASSADA_
_ALLAH KARA DAUKAKA P.M.L YASA MUFI HAKAN๐Ÿ‘๐Ÿป_


*91~95*
Nunata yake da yatsa yace
"Kece matar yayan nawa,keda kika gama yawon barikinki,kika gama saida mutuncinki a titi,shine aka lallab'i yayana aka mak'ala mishi ke,Wallahi ba agidannanba, Hajiyata 'yar iskacefah."

"Kai auta kasantane?"

"Nasanta Hajiya,Ranar da muke party jarabawar jam d'inmu harda ita,aranar muna cikin murnar ta sha wasu kwayoyin zubarda ciki,mu muka kaita asibita akace ciki ta zubar,kinga ai wannan ba matar aure bace."

"zubar da ciki!!
Kasan abunda kake cewa kuwa?
A cikin hayyacinka kake kuwa?
Kalleta da kyaufa matatace,ban tab'a ganin alamar bin maza atare da itaba,karka kuskura ka kuma gayawa matata irin wannan kalama,na yarda da ita nasan irin tarbiyarta."

"Dakyau kasan irin tarbiyartako tunda tare kukazo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login